Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / ALFARMA

ALFARMA

ALFARMA

ALLAH KA ALBARKACI ZURI ARMU”BAKI DAYA
KABAWA BABY KHAYRAT LFY๐Ÿคฒ๐Ÿป

Page 2

Dadan saurina naketafiya danganin 9 tagota, banyi wanitafiya mainisaba na isa bakin get in makarantar,dake bayan layinmu,
Inadaga kaina mukahada ido da hafsat yar ajinmu,tadagamin hannu alamar insaya,takaraso inda nake’ayya dan allah RUMAINA kin iya haddan da malam nuhu yabada?Eh na iya” todan allah koyamin,ido naware kai hafsat yaushe harna koyamiki bakiganin munyi Letti ne yaushe harna koyamiki kidai bari inmuntashi saina koyamiki,
Tariko hannuna,dan allah RUMAINA kitaimakeni wlhy nasan yauduka zansha kinsandai abinda malam nuhu yafada jiya akan duk wanda bai haddace shafinda yabada jiyaba,kitaimakamin,danjim nayi daga bisani kuma nasunkuya naciro KUR’ANI” itama sunkuyawar tayi nafara bitamata shafi daya wandake dauke da aya daya dakecikin suratul BAQARA,batabani wahala wajen daukaba saida natabbatar ta’iya kafin namike lokacin har10 tayi, mukashiga cikin makaranta”
Sorone yakamani danganin malaminda ketare letti,yana ganinmu kuwa yadaure fuska.muka karaso inda yake jikinmu nabari tunkan yabamu umurni mukazube kasa bisa guiwowinmu,
Mikewa yy daga kujerar dake zaune akai cikin fusata sai yanzune zakuzo makatanta?wato zuwa makarantarkuma naganin damane ko,yadaga dorinan dake hannusa ya zubawa hafsat yakuma karamata saida yamata bulala biyar lafiyayyu,kafin yace tatashi”yanufo kaina nandana jikina yakama cirawa,kafin nayi wani aune saisaukar bulala naji nayunkura zanmike dan nagama dimaucewa,
Saijin saukar wani bulalar nayi wanda yasani kwalla kara maikarfi “wanda yahaddasa fitowar dalubai da malaman makarantar,
Hannuna nadaura kan fuskata danaji keyimin radadi kamar yazubamin barkono”saijuya kai nake hawaye nasauka daga idona daya wanda yakemin masanancin radadi “dasauri malam nuhu yakaraso yana fadin yy lfy meyasameta?inda nake durkushe yamaso yanafadin wani abunne yashiga miki ido?dan ganin hannuna akan fuskata, nidai saihawaye nake dayarfe hannu,bawai zallar rakibane naji zafin dagaske saimurkusa idon nake duk tanbayar dayamin ban bashi amsaba,dansawa yamin badake nakeba?zabura nayi tareda cire hannuna akan fuskata.yakalli idona sanna yakalli malamin daya bigemu,rai bace yace kayi meyekena yanzu idan dayazo dasausayi yataba idontafa,
Kada kasake dukanta,toma wani letti tatiyanzu dahar zaka yimata irin wanna raunin,
Yasunkuyo yanafadin sannu yasaka hannu a aljuhu yaciro wani roba nidai bansan kotameyeceba yamikamin”hungo shafa agun,nakai hannu nalakata nagoga agun.
Jama ar’gurin kaf hankalinsu nakammu,wasu malamanmu biyu malam haruna da malam yusif,malam haruna yamaso kusa da malam yusif kaduba kagani mehakan yakenufi tunda nake amakarantarna bantaba ganin dan anyiwa daliba hukunci malam yy maganaba sai akan wanna yarinyar,malam yusif yy murmushi nima abinda nakekan sakawa araina kena.gadukkan alamu akwai wata akasa,ammako indai hakane malam yamin shigarsauri”uhm ay hakane yarinyar tayi sosai bawanda zaiganta bai yababa allah yabata kyau kuma tasami tarbiya kodaga lafazinta zakagane sansar tarbiya, cewar malam haruna, hakanekam,amma bakomai dankuwa sundace matuka…

Malam nuhu yamike yace kowa yakoma aji yakallene yacedani tashi kitafi aji,nameke nakade hijjab ina nashige aje nanimi guri nazauna,dasauri hafsat ta iso indanakezaune,dan allah RUMAINA kiyihakuri ninajanyo akabigeki har akamiki rauni,gergeza kainayi naceda ita karkidamu haka allah yahukunta…kafin takumacewa komai malam yashigo dan haka tanimi guri kusadani tazauna,nan yafara karbar hadda,layi layi yakebi haryazo layinmu wadanda sukegefena subiyu dagasu saini bayan sunbada,yasallakeni saiyanuna wacce take gabadani,atunaninsa bazan iyayin karatunba dannaji ciwo…niko ganin haka yasani saurin gyarazamata tareda lumshe idona nafara karatu cikin muryata,shiru ajin yy kamar bamutane ciki hatta ajinda muke makota dasu malaman dasuke zirgazirga asakar makarantar tsit sukayi, suna sauraron karatundake fitadaga bakina,saida nakai karshen ayar kafin nabude idona,kabbara jama’ar dasuke ciki dawajen aji sukayi,nashajin mutane sunafadin muryata yanada matukar dadi musamman idan ina karatun (ALKUR’ANI) kaina asunkuye inadagawa kuwa muka hada ido da malam nuhu gadukkan alamu nidamacan yake kalla,nayi saurin kawarda kaina,shima yamike baikumabi takan sauran dalibanba yafita…
Dagana malamai sukarika shiga suna bamu darasi,harlokacin tashi yy 6:pm akatashemu, inafita daga aji nanufi office nayi sallama abakin kofa nasaya batare danashigaba “dagaciki akace nashigo, inashiga naga malam nuhu ne shikadai azaune yana duba wasu littatafai na isa inda yake namikamasa kudin waigashi ayihakuri in allah ya yarda za aciko sauran, saida rubutunda yake yy yadago ya kalleni saikuma yamaida dubansa kan wata takardan dake gefensa,yajanyo yasoma rubutu “daga indanake ina iyahango abinda yake rubutawa,ido naware danganin abinda yarubuta kamar haka,(RUMAINA adamu”tabiya kudin makaranta nashekara, wato har adadin gamawartaโˆš) yanakaiwa na yature files in gefe yacigaba da abinda yake,dada mikomasa kudin nayi gashi malam,idonsa nakan abinda yake yace jeki narubuta”ai gakudin baka karbaba…hannu yadagamin jeki nace,
Jiki bakwari najuya nafice,ahanya narikasake sake araina,komeyasa malam nuhu yy haka oho” tafiyata nake ahankali harna karyo kwanar layinmu,daga inda nake ina iya hango kofar gidanmu,baba nagani dawani saida na iso daf kafin nagane wanda suke taredashi.dam naji kirjina yabuga alhj ayuba ne babban aminin alhj tijjani mahaifin sadam,wato sadam dagaske yake nasan ba abinda zaikawo abokin mahaifinsa kofar gidanmu inba abinda sadam yaceminba,
Na isa nagaidashi ya amsa cikin sakin fuska,masha allah gadukkan alamu wanna itce surkuwar tamu “gaskiya sadam ya’iya zabe maikyau,nidai saurin barin gurin nayi,koda nashiga gida bakowa dakin mama naleka batana hakan yatabbatarmin tana bayine danhaka nashige dakina.ina aje jakata nazube saman katifa ko hijjab ina bancireba” tunani nake cikin raina “lallai sadam yasaba lamba,toni ko auren zanyima ai bazan aureshiba “mutanenda basusan darajar dan adamba,sune zanje nazauna dasu’ dukda karancin shekaruna ainasan abinda yadace dawanda baidaceba,kumanasan yakamata,danni bajahilabace addinina yakoyardani abubuwa dadama” gidansu kuwa suntake sani danbazance basusaniba,toni mezan dawanna ahalin”
zuwacan namike nacire uniform injikina nadaura zani nasaka karamin hijjab nafito”nadibi ruwa najenayi wanka inafita nayi alaula dan magrib tagabato, inadhiga dakikuwa anakiran sallah,nashinfida sallaya nagabatar dasallah, jinshiru da mama tayi bata jimosinaba yasata lekowa dakin,RUMAINA wainikam kullum sai ancedake kici abincine kam.tun bakiyi wayoba nakesaki gaba harkuma yanzu waimutum dacikinsa amma sai an tilasta masa”tofito maza yanzu kici agabana,mama tafita tanacigaba da magana wanna yarinyar kodai batada lfyne amma ace tun karin safe takai hardare batasa wani abu abakintaba,kuma inda tacimma sai anyitafama da ita tukun.
Nidai murmushi nayi dankuwa nasan lfyta kalau,yanayina kena saina iyacin abinci sau daya arana inhar za abarni, nafito rike dakudin makaranta dadazu tabani” nasami mama harta zubomin abinci.zauna nan. tanunamin kusada ita nazauna taturamin abincin gabana,bana bukatar kokadan aciki dukazaki cinye kiban kwanon yanzunna”nawari ido mama dukawanna yaushe zan iya cinyewa.
Duka zakicinye “mama gashi namikamata kudin karbatayi tana juyashi wanna kudinfa daga ina yafito?kudin makarantace nakaiwa malam nuhu saiyace naje kawai.sabodame kobazasu hakuranbane?nima bansaniba” mama tadanyi jim daga bisani tace gobe idan kinje kidada basu hakuri,baban nakima zaije dakansa yabasu hakurin,naceto”tace tosa hannu kici” haka nasa hannu narika danna abincin saida kuwa nacinye kamar zanyi amai,dataga nacinye saitamike tashige daki……….

 

Comments and Share

 

MAMYN TWINS CE
[10/20, 8:06 AM] Hayat: ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
ALFARMA!
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

byโœ๐Ÿป
Rasheeda S’ Director

ALLAH KABAWA BABY KHAYRAT LFY๐Ÿคฒ๐Ÿป

Page 1

Wata bishiyace maitaren inuwa”mutanene zaune agindinta,gadukkan alamu sunajin da din iskar dake kadawa daga jikin bishiyar” yawancin mutanen dake zaune agun dattijaine, ahan kali nake tafiya cikin nusuwa da kamala,wanda mutane sukewa tafiyata lakabida rigimace kesani yinta”harna iso dafda bishiyar,harkasa naduka nagaida wadanna tsoppin “dukansu suka amsamin cikin hadai baki”namike nawuce”
Wanna yarinyar yar albarkace tasamu tarbiya allah yayi mata albarka tareda namu zuriyar bakidaya”hakanekam ameen ya allah”abinda mutanen dana gaidasu suke fada kena”
Bayau nasabajin hakan daga bakin mutane ba dan haka nima na amsa da ameen”nacigaba datafiyata”harna iso kopar gidanmu RUMAINA! cak nasaya sakamakon jin irin wanna kiran tabbas nasan wadanna samarin unguwarmu zauna gari banza nanne “saikawai nasa kai nashige ciki
Daya daga cikin samarin yace sadiku kaga yau mutumiyarka taki juyowo bare muga wanna kyakyawar fuskar nata”wanda akakira da sadiku yace aykam naso ace naga fuskarna kozanyi barci maikyau yau”sadiku yajuya yana fuskantar abokin nasa, lawan allah ni yarinyarna wani sa in soro take bani.akwai wani rana tafito isalami nasareta akan kwana wlhy data kallene da idonta saida naji gabana yafadi”kyan yan yy yawa saikace aljana”dariya lawan yy ai ni narigaka fadan haka” kyan yarinyar yy yawa wani lokacin nakanyi tunanin hakan”amma allah mutumce allah ne kawai yahalitta abinsa haka” wanna idan ka ajeta agidanka ai ko kopar gida bazaka lekaba”haka suka rika jajantawa junansu”
Dasallamata nashigo gida mama dake zaune kan kujera yarsuguno ta amsamin sallamar”nakaroso inda take”sannu dagida, mama yauwa RUMAINA harkuntaso,Eh muntaso mama na nimi guri kusa da ita nazauna tareda cire hijab ina”mama tadubeni cikeda kulawa “RUMAINA jeki dauki abincinki kici dannasanki yanzuhaka saiki kai hardare bakiciba”kuma gashi bawani abincin kirki kk ciba kafin kitafi”to nace namike nanufi kitchen inmu dake gefe da dakin mama,nashiga nadauki abincin nadawo nazauna inda natashi”mama yau malaminmu yace karna sake zuwa saida kudin makaranta”nawata uku da akebina gawanna watanma takusa karewa,numfashi mama tasauke hakane kam ai sinyi kokarima to bari babannaki yashigo nadada tunamasa”dan nasan shima bai manceba,to nace nasaka hanu cikin abincin
Nashiga sakurar abincin bawani meyawa naciba namaida sauran narufe shi a kitchen,sanna nawuce daki natube uniform injikina”nasaka kayan zaman gida,na dauki jakar makarantar bokona nazo nazauna kasan nadi sanna naciro book nafara bita kamar kullum”
Duk dakasancewar bana zuwa makarantar boko yanzu hakan baihanani bitar abinda na iyaba”jin sallamar baba yasani aje book in nafito” na isa inda yake naruko hannusa,sannu da dawuwa baba, yauwa mamana ga sarabarki yasaka hanu a aljuhu yaciro dabino kwara hudu yamikamin”hanu biyo nasa nakarba tareda yingodiya,yadaura hannusa akaina allah yamiki albarka ameen nace sanna najuya nakoma daki,
Inda mama take yakarasa tayi hanzarin shinfida masa taburman dake gefenta,yazauna sanna tayimasa barka dashigowa. Mama tadaukowa baba abinci ya gyara zamansa yanaci suna hira,mama tanisa tace malam yau mlmn makarantarsu RUMAINA sunce kada tasake zuwa saida kudin da ake binta nawata uku,numfashi baba yasauke hakane sunyi kokarima wlhy kullum da kudinsu nake kwana araina banaso yarinyarna tasake zama babu makaranta dukabiyu,allah yaga zuciyata kumanasan zai dafamin amma ga yan wasu kudina barinabaki koda nawata biyone ki aje gobe inzata makarantar saiki bata takai musu suyi hakuri insha allah zannimi sauran sai abasu,yasa hanu a aljuhu yaciro kude yan dari biyu guda biyar allah bayataba toshemaka hanyarsamu duka saidai in bakatashi kanimaba,kinga wanna kudin fina nazu nawuce gona dan indan cire ciyayinda suka toho cikin shinkafarna,bayan nagama ina fita bakin titi saina hangi wata mota direbar yanata fama da ita,sainaje inda motar take.naketambayar mai motar ko lfy nan yake shaidamin haka kawai tasaya,
Nacemasa barina dubamasa cikin ikon allah kuwa motar tatashi aiko yytamin gdy yaciro wadanna kudin yamikamin nakikarba harna gutashi yabiyoni yasaminsu a aljuhu, allah mai iko mama tace kwarai kuwa allah baya toshewa bawansa hanyarsamu.kaduba kaga dazu bakadasu yanzukuma sai yabaka allah abin godiya, karbi wanna. yamikamata dari hudu’takaimu nawata buyun idan allah yayarda zan ciko musu dayan dana wanna wata maikarewa, mama takarba tana fadin allah ubangiji yabuda”
Rinsa idonuna nayi daga cikin daki inajiyo abinda suke tattaunawa. Najiwani irin radadi acikin zuciyata.aduksanda naga mahaifana cikin halin rashi sainaji duk badadi, harnarikaji ina ma ace ni namijine da nataimakawa mahaifina,amma dukda kasancewata mace hakan baihana zuciyata bugawa,zankuma cigaba dayimusu addu’a kamar yadda kullum nake musu” hawayenda yazubomin nashare” jinsunyi shiru dazancen yasani cigaba da bitar karatuna.
Wani yarone yy sallama su mama dake zaune awake suka amsa masa,daga inda yaron kesaye yace wai ana sallama da RUMAINA,
Baba yanumfasa sanna yaceda yaron kajekace haryanzu ba abata damar sayuwa da samariba,to yaron yace yafita.kasakasa nakejin maganar su saidai banji abinda suke fadaba,sai fitar Baba dana hanga gadukkan alamu masallace yanufa dan lokacin sallah yy”
Namike nafito dannayi alaula,mama takirani daga inda nake RUMAINA yimaza kiyi sallan kidauko mana markade”tonace namike nashige daki nagabatar dasallah,ina idarwa nafito.nashiga dakin mama nakarbi kuden markaden nafita,
Ahankali naketafiyata cikin nutsuwa harna iso kwanar gidan maimarkade. gani nayi anfitomin agaba bashiri najanasaya, saikuma nanimi kaucewa gefe dannawuce yakuma tare hanyar,yanafadin RUMAINA meye nufin mahaifinki dakullon idan anje gunki saiyace haryanzu baibaki damar sayuwa da kowaba,kojari yakeson kafawa dake dan yaga kinada kyau! Kindaisankoni wayene agarinna ko idan nanimi abu tofa sainasamu kota karfice kisani bazan taba barin wanna kyakyawar fuskarba, kifadawa mahaifinki kinasona kuma gobe zanturo iyayena….tunkan yakarasa zancensa nadakatar dashi dankuwa nafiskanci abin nasa cinfuskace”hannu nadaga masa dafadin,dakata malam katausa harshenka kasan maganar dazaka rikafada akan mahaifina.idan kasake kace zakaci zarafin mahahaifina bazan taba kyalekaba,kai kahaifamasani?dazaisa doka akaina kanimi janye dokar? karka sake kasake tareni dawanna zancen danni nasan darajar mahaifina. Madadin yaji haushin abinda nafada saima kalmasa hannu da yy akirji yakurawa bakina ido yana murmushi da lumshe ido tareda lankwasar dakansa duk inda najuyar dakaina shima saiya juya,naja dogon tsaki naraba gefensa nawuce
“koda nadauko markaden nafito nan nakuma taddashi saye,yana ganina yakuma masowa inda nake banko saurareshiba nayi saurin wuceshi”
Narasa meyasa wasu masu kude sukedaukan kan kamar sunfi kowa aduniya,sadam”tijjani yana daya dagacikin jeren wadanna masukuden”tabbas nasan kamar yadda sadam” yafada idan yanimi abu tofa saiyasamu kota halin yy dan saboda mahaifinsa maikudene nagaske,kuma duk abinda sadam keso tofa mahaifinsa alhj tijjani saiya samar masashi kada karfin dukiyarsane”
Ta allah batakaba nafaษ—a inashigewa cikin gidanmu,,babu kowa asakargidan nakarasa gun wankewanke nasauke markaden saman dakalin gun, najanyo ruwanatace kullun sanna nagyara gun dana bata,naje nayi alaulan magrib,saida nashiga dakin mama nasanar mata nadawo kafin nawuce dakina.bayan nayi sallah,najanyo jakar islamiyata nafara bitar ALKUR’ANI “maigirma”dankuwa gobe zamubada hadda,saidanaji barci yacikarfina sanna narufe KUR’AN “din, tareda mikewa nahaye saman dan madaidaicin katifata dake gefe adakin,batare da bata lokaciba barci yatafidani”

Washegari bayan nayi salla nafito madaidaicin sakar gidanmu nashare saf,na tarkasa kwanuka naje nawankesu saf,kafin nashiga kitchen nahada wuta na daura ruwa”sanna nakoma daki nakuma kwanciya,kasancewar yau asabarce dasafe mukezuwa islamiya,tun 9:am muke tafiya mutashi 6:pm,haka ranar lahadi ma,bakamar sauran ranakunba”
Dankwanciyar danayi barci yasamu damar daukata,saiji nayi mama natashina”ke RUMAINA yaubazakije makaranta bane?kiduba agogo kigani…dasauri nabude ido tareda saukowa daga saman katifar saikuma nasaya ina kallon mama,itama nitake kalla tanafadin au sayuwa zakiyi bazakiyi azaman shiriba, juyawa nayi dasauri nafita na isa bakin rijiya naja ruwa,natafi bayi nayi wanka inafita nashiga shiri cikin sauri,fitowa nayi ina rikeda hijjab dajakata ahanu,nanufi kofar kitchen inda mama kezaune’saman kujera yartsuguno nazauna,
Mama naganina taturamin koko da kosai gabana da hanzari nakarya “sanna namike saye nasaka hijjab ina,mama natafi,to allah yabada sa’a gashi kibasu wanna kudin kicedasu suyi hakuri insha allah za aciko musu,tamikomin dari hudun da baba jiya yabada.nakarba ina fadin toh” ,kodanazo bakin kopargida sanda nakaranto addu’ar fita daga gida kafin nasaka kafata tadama nafice agidan…………

 

Comment and Share

 

MAMYN TWINS CE
[10/20, 8:06 AM] Hayat: ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
ALFARMA
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

byโœ๐Ÿป
Rasheeda S’ Director

ALLAH KA ALBARKACI ZURI ARMU”BAKI DAYA,
KABAWA BABY KHAYRAT LFY๐Ÿคฒ๐Ÿป

Page 3

ALFARMA FANS LOVE 2๐Ÿ’—
Kuji dadinku kuyi lasting๐Ÿคธโ€โ™€๐Ÿ˜˜

namike nakai plt in kitchen,sanna nakoma daki.inata zubakunne kozanji shigowar baba har barci yadaukeni.washegari kodanaje makaranta har offece nakuma zuwa natadda malam nuhu”nayi sallama tareda gaidashi,malam waidan allah ayihakuri….saurin dagamin hannu yy batareda yabarni nakarasa maganarba,jeki aji “yacedani atakaice,tsumetsume najuya na nufi aji”
Bayan tafiyata aji dadan jimawa kadan,lokacin har malami yashigo yamana darasi yafita” najuyo dafuskata ina kallon window dagacan nahango baba yanashigowa cikin makarantar,wani sanyi naji araina dankuwa nasan baba zaibasu hakurine”hanyar offece yabi,malam nuhu”naganinsa yataso dasauri yanufo inda baba yake,cikeda girmamawa yadan risina yagaida baba’baba ko mikamasa hannu yy dansuyi musabaha,cikedajin kunya yamika hannu sukadada gaisawa”
baba yanisa yace nazone dakaina nabaku hakuri akan kudin makarantar RUMAINA”kudada yimin hakuri insha allahu zan cikomuku adai yihakuri dan allah”gawanna kudinda jiya tazodashi akace tamaida,yamiko masa,ay baba andauki nauyin karatun RUMAINA hartakammala karatunta “malan nuhu yafada kansa akasa, da mmk baba yace to wakena yadauki nauyi karatun nata? um..um..makarantace tadau nauyinta” atoh madallah allah ubangiji yasaka da alkhairi,ubangiji ya haskaka rayuwarku,malan hunu yayi saurin cewa ameen dan kuwa yaji dadin addu’ar da baba yy “nikuwa ido nakura musu bawaidan inajin abinda sukefadaba,saigani nayi baba yy gaba malan nuhu nabiye dashi harbakin get”saida baba yafita kafin shikuma yakoma offece”numfashi nasauke tareda maida kallina kan littafin dake gabana,
bayan gama darussa akatashemu nayigida”
kwana uku da zuwan alhj ayuba,banji baba yace komaiba danhaka nasaki raina….

Yau juma’a hakankuwa yy daidai da saura kwana uku watan azumi yakama, zaune muke asakargida inataya mama aiki,mama tadubeni tace RUMAINA tashi maza kije gidan adama mai adashe ki karbomin kudin adashe tun shekaran jiyafa yakamata ta aikomin gashi harya kara kwana biyu, toh nace namike naje nawanke hannuna nashiga daki nadauki hijjab nasaka nafito,
Nadau hanyar gidan adama mai adashe,ina isagidan dasallama nagaita batama bari nafadi abinda yakawoniba tashigw daki tadauko kudi tamikamin tanafadin kicewa mamanki tayihakuri bana zamane kwana biyu shiyasa ban aikamataba.nakarba nafita…kodanazo bakin titi nasaya dan ababen hawa suwuce..ganinsun wuce yasani sako kaina zan sallaka daga can wata mota takaryo kwana harnasaya sainaga bawani gudu takeba inaganin zan iya sallakewa kafin ya iso, na haura kan titin kafin na ankara saiganin motar nayi dafdani,nayi baya dasauri kafin nakarasa saijina nayi akasa timm”sabar nadimauce bansan sa’ilin dana mike sayeba,
Cikin hanzari aka paka motar ,dasauri direbar dakejan motar yafito kafin yakaraso inda nake wata mata tafito cikin sauri ta isagareni tana fadin subhanallah sannu kinji, yayi kokarin yakauce dan kiwuce amma saida sausayi yagefta”tariko kafadata tana jujjuyani dafadin allah dai yasa bakiji rauni maisananiba,muje asibiti adubaki” ah babo komai basaimunje asibiti ai banji wani ciwoba,tariko hannuna a’a mudaije adubaki kar azauna abawani masala saidare yy jiki yace baiyardaba muje asibitin kawai”
Shiru nayi dan banaso nayi jayayya da babba dan matar babbace dukda hutun dayaboye girmanta zata iya girmewa mama kusuyi sa’a da ita,
Ganin nayi shiru yasata cewa direban muje maza yanzu abisiti,tajanyo hannuna takaini jikin motar shiga maza muje kinji.tarjewa nayi tareda kurawa motar ido ni tundanake bantaba ganin irin motarba ko akan titine irin masu wucewarna,motar bakace hatta glass inta bakine katuwar gaske,tunani nake inda nataba ganin irin motar,sai asa’ilin natuna a’ TV nataba gani wani rana da mama ta ai keni gidan alhj tijjani lokacin dana shiga palon gidan natadda TV akunne ana labarai irin nakasashen waje anan naga iri motar”agunne sadam ya iskeni haryace yana sona”
Bakinabude ina cigaba dakallon motar “wato ashe anasamun irin masu irin motar anan gida Nigeria cab ashe Nigeria mu babbace”matar takatsemun tunani dafadin shiga mujemana karmu bata lokaci ana kisa allah daya aranki saikishiga kinji tadubeni tana murmushi”sunkuyar dakai nayi wato tafahimci soroce yahanani shiga,nasaka kafata cikin motar da bismillah,nazauna kan kujerar dakanta tamaida marfin tarufe,kafin tazago dayan gefen direban ya isa dagudunshi yabode mata tashiga shima yakoma mazauninsa yy wa motar key”
Yasubhanallah”anya wanna motace”raba ido narikayi acikin motar badun ina kallon ababen hawa suna shigewaba sainace ba mota bace,wani irin sanyi ne keshiga jikina wanda nakasa gane daga ina yake fita,natakure guri daya,ina addu’a araina”
Nasinkayo muryar direbar nafadin hajiya wani asibiti zamujene? Muje nan (kula hospital) inaga yafi kusadanan.to rankishidade, (kula hospital) cab asibitin masu kudenefa masu kudin garinmu kadai kezuwa wanna asibitin.ni tundanakema bantaba shiga koda harabar asibitinba bare cikinta,ina cikin zance dazuciyata naji tace sauko muje ko”nasha mmkn kaina ashe har an iso tasauka tazo gefen danake harta bode bansani saida tayi magana kafin na ankara”
Nasako kafata kasa” tana gaba inabiye da ita harmuka shiga cikin asibitin, wasu ma aikatan asibitin guda biyu naga sun mike sunnufo inda muke,barka dazuwa hajiya sannu dahanya mutanen suke fada kamar zasu zube kasa dan sananin girmamawa, yauwa tace dasu,sanna takara gaba,babban falon asibitin mukashiga,masha allah lallai (kula hospital) akwai kyau” nanma kafin mukarasa shiga wasu sukakuma isomu,suna zuba gaisuwa kamar zasukai guiwarsu kasa,hajiya dakanki mara lfy kk kawone? nan take fadamusu dr take son gani.dasauri daya daga cikin mutanenna yajuya yanufi wani offece gadukkan alamu shine offece in dr muna saye agun tanata karbar gaisuwar jama’a wanna mutumin yafito,hajiya bismillah yace da ita yana nunamata hanyar offece in” taruko hannuna muka nufi offece in,abin mmk gamutane masubin layi sunfi 30 amma mudaga zuwanmu ance mushiga,
Muna shiga dr yamike saye barka dazuwa hajiya aidakira kkyi sai axo basaikinzo dakankiba “saida yagyara kujerar dake fuskantarsa kafin yy mata nuni da fadin bismillah “tazauna bakomai ay yanzunma banzata zan zonanba sausayece tagifta wlhy shiyasa,akan hanyarmu nashigowa garinna muka bige wanna yarinyar,juyawa dr yy danganin wacce akabigen, hajiyar tajanyo hannuna nazauna kusa da kujerarta. Kuramin ido yy saikuma yakalli hajiyar,amma hajiya ai banga kamar jinciwo atattare da itaba,hajiya tace hakane itama tace bataji ciwoba amma kasan doledai zata bugu hakan kuma zai iya zamo mata illa koda agon kwanciyace,dr yasauke numfashi yajuyo yana kallona,inada inane keyimiki ciwo?shiru nayi danganin irin kallon dayakemin,sanda hajiya tatabani kifada masa inake yimiki ciwo,nan nace nanuna guiwar kafata,amma shima bawani sosai yakeminba, bude muga gurin yafada idonsa akaina,najanye zanina sama iyaguiwar dan kwarzanewa nayi bawani maiyawaba,jin yy shiru baice komaiba yasani kallon fuskarsa.kafata yakuwarawa ido ganin haka yasani sauke zanina cikin hanzari,
ok nagani bawani ciwo mai yawaba so bari arubuta mata magani”koda buguwar cikima zata warware,ya danyi rubuce rubucensa,daga bisani yadanna wani abu dake daure kan table in gabansa,yan mintuna kadan wani yashigo,yamika masa wanna takardar yafita”wayar hajiyar yy kara tadaga ok nima inaga gobe zan ko “tace kawai takashe wayar,batareda bata lokaciba yadawo dauke da laida ahanunsa,ya aje bisa kan table in, hajiya tamike saye nima namike tariko hannuna ,dr dakansa yadauki laidar yamika mata,ta ansa tasa hannu cikin jakarta taciro kude batareda takirgaba tadaura kan table in,sanna tace dani muje,shiko yarika zubamata godiya,harmukafita”tana rike da hannuna, muka isa jikin motar,yauwa to muje musaukeki akida ko,cewar hajiyar”nayi saurin cewa a a kibarshi kawai ngd bagidama zaniba mamace ta aikeni, kallona tayi dansin gaskata abinda nafada, nayi saurin sunkuyar dakaina kasa,dan nata tabbata har idan muka hada ido tofa zata gane bagaskiya nafadaba,toshikena ga maganin kitabbata kinsha kina komawa gida,tamikomin nakarba tareda yimata godiya,nakama hanyar fita,ya sunanki?tayimin tanbayar daga inta take saye,saida najuyo nace RUMAINA sunana…………..

 

Comments and Share

 

MAMYN TWINS CE
[10/20, 8:06 AM] Hayat: ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
ALFARMA
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

byโœ๐Ÿป
Rasheeda S’ Director

ALLAH KA ALBARKACI ZURI ARMU”BAKI DAYA,
KABAWA BABY KHAYRAT LFY๐Ÿคฒ๐Ÿป

 

Page 5

Wanna page in nakine anty fati na grp in ๐Ÿ†’NOVEL MEKEUP AND KITCHIN kiji dadinki kiyi lasting๐Ÿคธโ€โ™€๐Ÿ˜˜

 

“”””Hakana isagida bawalwala tattare dani.naisa nazauna kusa da mama,tadubeni yau kosallamarma babu ita hakafa kk shigo babu sallama,nayifa mama bakiji bane kawai.yanayin danayi maganar yasa mama dada dubana cikeda kulawa dan fahimtar yanayina,abinka da uwa kallo daya tafahimci inacikin damuwa.RUMAINA meke damunki?kamar jira nake tayi tabbayar nayi saurin ruko hannuta mama wai musabaqa zamuyi,to shine zaki damuhaka saikace yau kksabayin musabaqar.mama wanna musabaqar ba irin wanda nasaba yintabace.wanna nakasace bakidaya kuma a abuja zamuyi mama inajin soro gawanna takardar malam yace mukaigida.namikamata takarba tana dubawa.
Muna cikin haka baba yashigo,nan mama keshaidamasa,shima dayaji zancen saida yajinjina amma dan yakarfafamin guiwa saiya. to mamana zamu tayaki addu’a saiki maida hankali sosai kamar yadda nasanki.maza tashi kijekici abinci kisamu guri kinutsu sosai dan kisami damar yinbita”to nace namike nashige daki .ranar ko waigen abincinci banyiba saida mama tazaunar dani agabanta kamar kullom kafin naci,
Inayin sallar isha nafara bita,inacikin karatun sainaji harshena nahardewa abin mmk saina tike saikawai nafashe dakuka, dasauri mama tashigo dakin tataddani nasaka KUR’AN gaba saikuka nake,rufe KUR’AN in tayi takamo kafadata namike saye tajanyo hannuna zuwa bakin katifata,kwanta kiyi barci idan kktashizakiji kin’iya,kaikawai nagyada mata ,saida taga nakwanta kafin tafita.aiko banjima dakwanciyaba barci yadaukeni, karfe shabiyu daidai nafarka,naje nadauro alaula nazo nayi sallah raka’a biyu,sanna nabude AL’KUR’A’NI nafara karatu abin mmk saigashi inda dazu nakasa yanzu na iya,banbar karatunba harsaida akakira sallar asuba”shima ina idarwa nacigaba….hakakullon nakeyi abinda ketadani salla saikuma cin abinci,saida wani lokaci mama tashigo tarufe KUR’AN din tace naje nakwanta kuma da ikon allah idan nayi barcin natashi sai inji kamar ankaramin iyawarce…
Yau juma’a’inazaune bayan na idar dasallar isha mama tashigo dalaida ta aje gefena tafita.najanyo laidar sainaga kayan da baba yasayomince har an dinka,naji dadi sosai.naturasu gefe nacigaba dabita kamar kullum. Yau karfe daya mama tashigo tatadani tace nakwanta haka tadauki KUR’AN din tafita dashi adaren mama da baba ko rinsawa basuyiba…washe gare da asuba mama tatadani tace naje nayi wanka koda nashiga bandaki natadda takaimun ruwan wankan maidumi,nawanke jikina saf nafito..bayan nayi sallah nasaka daya daga cikin sabin kayana masha allah bakaramin kyau kayan yaminba.ina gamawa mama nashigowa dauke dakayan karyawa.itada kanta tahadamin tea kasancewar yanzu alhmdllh tea and bred mukekaryawa dashi wani sa inma harda kwai, tace nayi maza nakarya kar lokaci yakure..
bayannagama baba yy kirana waje.yashiga yimin nasiha maishiga jiki.daga bisani mama tadaura nata nidai saisharar kwalla nake..baba yadubeni taso muje narakaki.namike nadau jakar danasa kayana kala biyu muka fita mama tanayimin fatan alkairi…harcikin makaantar mukashiga da baba,dalibai da malamai kaf sun hallara.can nahango malam nuhu sai duba agogon dake daure ahannusa yake kamar ance yajuya yana ganinmu yanufomu, yarissina yagaida baba baba ya amsa dafadin kace ita akejirama tundazu naga gayan uwanta duk sun halarci gurin,dan murmushi yy baba kasan yaune za afara musabaqar na kuma sunce bayan sallar azahar za afara gashikuma dagana zuwa abuja da dannisa shiyasa zamutafi dawuri,baba yace gaskiya kam gara ajedawurin dangudun makara.sai alokacin nagaidashi.baba yace to allah yasare yakuma bada sa’a.malam nuhu ya amsa da ameen.baba yajuya yafita amakarantar najuya zantafi cikin dalibai karaf mukahada ido da malam nuhu nayi saurin yin kasa dakaina nagotashi nashige cikin dalibai…
Motocine guda uku daya namalamai biyu kuma nadalibai sai’alokacin nasan asheduka za’atafi bamu yan musabaqa kadaiba harda daliban daza ayaye ,acan za’agudanar da yayen, aka umurcemu damushiga mota mukashiga.
Batareda batalokaciba.motacin sukabar harabar makarantar.muka lula titi…..
12:15 pm”
Mukashigo babban birnin taraiya abuja” direct masaukinda akatanadar mana motocin sukashige ,suna parking mukafirfito yan agajine hadeda sojoji zagaye dagun.munafitowa cikin sauri sukazo inda muke.hanjin cikinane yakada sakamakon ganin sojojinna danayi nandana jikina yasoma bari,tun ina yarinya nakemugun jin soron soja kotafiya zamuyi da mama idan mukazo (road block) (checking point) rufe idona nake gam harsaimunwuce kafin nabude.nayi baya dasauri nashige sakiyar dalibai narike hijjab inwata nayi kasa dakaina harsaida mukashiga cikin masaukinmu”suma sojojin musulunce wato yan’agaji,dasu sojojin gomnatin sukajuya danganin munshiga.
Masaukine maikyan gaske muzallar dalibaine aciki malamanmu dai awaje mukabarsu.mukazazzauna asaman kujerundake cikin katon falon,yan agaji sukashigo dauke da manyan kuloli nan sukafara zubana abinci sukarika mikawa kowa acikinmu sanna sunagamawa sukafita. Mukasunkuya cin abincin.da abinshan dasuka ajemana agabanmu.
Munagama ci anakiran salla wani dan agaji dake saye abakin kofa tashigo.gabayican kushiga kuyi alaula yace damu,to mukace.mukarika shiga munayin alaulan.mukazo muka gabatar da sallah,
Munazaune wasu yan agaji su uku sukashigo daya nagaba biyunabiye dashi koda ya iso indamuke yaja yasaya biyunna suka saramasa”tareda kamewa.sannuku yacedamu”mukahada baki wajen gaidashi.yy murmushi dafadin kutaso muje,duka mukamike mukabi bayansa,muna fita wadanna sojojin suka yisaurin zuwa inda muke sunrirrike bindiga kamar sunafilin daga.yandanayi dazu hakama nayi yanzu harmuka isajikin mota
Motocin kungiyace guda biyu mukashige ciki motocin sukaja…
Tafiya mukayi maidannisa..kafinmuka isa babban filin taro dake cikin abuja”tundaga bakin get in mukafara ganin mutane masu yawan gaske “direbar yasamu gefe yafaka dasauri yan agajinda ke sassaye abakin get din suka zo jikin motar tareda bude murafen motocin mukarika fitowa.suka budemana get mukashige ciki, ya’ilahi’yalillahi”ido naware bisakan mutanen dake cikin wanna filin taron,jama a kamar kasa.haka akarika kusawa damu cikin gurin har muka isa wani guri wanda akasa iyaka da jama ar dake gurin daya sallaken kujerune ajere dawasu mata wadanda suka sa kaya iri daya gawani tambari agefen hijjab insu wanda akarubuta da arabiq ALMU’ASSASA TARBIYATUL’ISLAM” hakan yanunamin suma dalibaine,takowace kusurwa agun da dalibai daban daban na jahohi daban daban,kuma kowacce da tanbarin makarantarsu, bangare daban aka bamu muka zazzauna…

Karfe 2 daidai..
Aka bude bilin da addu’a.megabatarwan yafara jawabi kamar haka.alhmdllh cikin ikon ubangiji yanzu za afara gudanar da gasar ALKUR’ANI maigirma,damm kirjina yabuga..irinwanna guri taya zan iya koda mosimaikarfi…mai gabatarwan yacigaba.
Daliba nafarko itace hafsat salihu abdullahi daga jahar kaduna state………….

 

Comments and Share

 

MAMYN TWINS CE
[10/20, 8:06 AM] Hayat: ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
ALFARMA
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

byโœ๐Ÿป
Rasheeda S’ Director

ALLAH KA ALBARKACI ZURI ARMU”BAKI DAYA,

KABAWA BABY KHAYRAT LFY๐Ÿคฒ๐Ÿป

Page 4

 

“”Tayi murmushi RUMAINA to kigaida gida,to nace nafita a asibitin,nadauki hanya mafi sauki dazai kaini gida”
Ina isa gida natadda mama zaune ainda nabarta.tunkan inakaraso inda take tafara yimin fada,ke RUMAINA nan dagidan adama shine kk je kk zauna yanzu idan da babanki yadawo yatadda bakyana fa,nikaina banason kirikafitanna dan kawai banada dan aikene”amma tun dazu kinje kinzauna madadin idan bakisametaba kidawo kawai”ayya mama wlhy tun dazu nakarbo kudin,ahanyar dawowatace mota tatureni,matar kuma tace sam saitakaini asibiti,dukda nacemata banji ciwoba amma tace saimunje likita yadubani kingama maganin da tasayamin”mama tace ikon allah lallai tsautsayi baya wuce ratarsa,to allah yadada kiyaye nagaba,ameen nace namikamata kudin, nashiga daki na aje laidar maganin,sanna nafito nazauna mukacigaba da aiki, ganin narike aikin yasa
Mama tamike tashiga daki, sallama akayi daga bakin kofa,na amsa wai ana sallama da yarinyar data shigo gidanna,wanda yy sallamar yafada.dasauri namike nazo inda yaron kesaye nayi kasa damurya dan kada mama taji,kaje kace bawata wacce tashigo gidanna,saidai in ko nan makotanmu,natura keyan yaron yafita.nakoma nazauna allah yasoni mama batajiba,haushin mutumin yakamani nikaina banason narika fitanna “maza fitinata suke duk sanda nafita tofa sai sun tareni inko naki sayuwa zasu biyoni gida”mama ko tarinka yimin fada kena waini nake gaiyatosu,niko banmasan yadda zanfara hira da samariba,inbanda mazama ai nayi kankanta da soyayya,dudu 15 years gareni shimadin saura 6 month nacika…
Ina kamla aikin namike nashige ciki nima…
Ana gobe za’akama azumi,baba yahado mana kaya rigis atalakance. Duk shekara idan watan azumi yakama akan juyamana lokacin zuwa islamiya, munazuwa 8:am mutashi 12:pm kasancewar zallar KUR’AN akemana….
Shiri nake cikin sauri dan gudun kada namakara, nafito nasallami mama natafi, ina isa bakin get malam nuhu na faka mashin insa, na isa nagaidashi harzan wuce yakirani najuya kaina akasa, idanzaki sallaka titi kisaya kirika subawa dakyau koda sausayin zaigifta zaizamo dasauki” nace to ngd nasakaiciki,wanna ko aina yasamu labarin mota tatureni oho,…

Azumi yy nisa ibada natacigaba dagudanuwa cikin ikon ubangiji, kwanta tashi babu wuya agurin ubangiji gashi yau idan munkai azumi munkai ashirin da tara”
Kwance nake kankatifata inatajuyi dan bakarya yau azuminna yymin kamu,muryar baba naji aiko dasauri namike nafito sannu da dazuwa baba,yauwa mamana yanaganki haka duk agala baice? Allah baba yau azuminna yakamani dayawa,nayi maganar cikin shagwaba tareda riko hannusa nalangobe kaina”yy yar karamar dariya yadaura hannusa akaina sannu ko mamana dama idan aski yazo gabangoshi yafizafi.kidaure saura kadan kinji,nagyada kai,yauwa mamana to bari naje nasayo mana kayan miyar sallah yajuya yakalli mama datasamu gaba tana kallo yace da ita “sannuki da gida tunda ni baza ayimin sannuba. Uhm inako zakajini kasa yarka gaba tun shigowarka naketayimaka sannu,bakatani, baba yace waneni nace banata fadimatu yar mutan yola, murmushi mama tayi to yaukuma zolayace yatashi, shima murmushin yy mata”
Ganin sohuwar soyayya nason tashi yasani zamewa nayi ciki.
Bankuma fitaba harsaida baba yatafi yadawo,muka sunkuya aikin kajindaya kawo guda uku da kayan miyarmu nasalla” damuka gama mama tasani natsefe kisonkaina dan tamin nasalla nafi awa ajikin kwaya biyu dan tsifa namugun bani wuya, karshe itace takarasamin.tanayimin kiso tanayimin fadar randa bama tare zataga wazai rikatsefemun…daf magrib tagamamin naje nayi wanka dannaji karfin jikina inafita anakiran sallah…harda yarkwallata danazo shanruwa waiyau munkare azumi..mama tace gulma saikace badazu nagama narkewaba wai azumi yy yimin kamuba,baba kam bakina yakarba,yace ay nayikokari..washegari duk duniya ana farincikin nayau ranar sallah.nayi wankan sallah na amma ko kofar gida banlekaba har akaci akagama shagalin sallah banfitaba…..

_____________________________
Bayan wasu watanni
“””zuwayanzu kararu nasa agabana tukuru, danmunkusa ayayemu, shinkafar gonar baba tayikyau matuka da akacirota bakaramin alheri baba yasamuba,harzakka saida yafidda aciki, da akasaida shinkafar kudi maiyawa akasamu, ranar baba yayi alheri wayan unguwarmu,nida mama kuwa munsan baba nacikin wadata…
Ranarda yarage saura sati daya ayayemu,baba yashigo gida rikeda babbar laida ahanu,kantaburma damuke zaune da mama ya isa yazauna.mama tayimasa sannu dashigowa nimahaka, yaturomin wanna laidar gabana.gashi mamana kayankine aciki gara mufara shiri tun yanzu,dabarin jiki nabude laidar nashiga ciro kayakin dakeciki. Zannuwace turmi shida sai hijjab kala uku da takalma guda biyu harda kayan kwalliya masuyawa,bakina kasa rufuwa yy dan murna mama kigani kigakayana da baba yasayamin naturawa mama kayan.itama murnar tayi sosai dasanya albarka”
Baba yaciro kudi yamikawa mama gashi gobe idan allah yakaimu saiki bada dinkin kayan dan asamu ayi kar lokaci yakure,mama tasa hannu biyu takarba,baba yagerazama tareda gyaran murya yace.kunga ikon ubangijiko shikeyi dabayinsa yadda yaso yanzu kuduba kuga yanda yawadatamu da abinda zamu gudanar darayuwa cikin ikonsa.allah kena maji tausayin bawansa,mama tace hakane ubangiji mungode maka..baba yacigaba. dazunna naje mukayi cinikin wani shago maidauke da kayakin abinci nabiya kudin zanfara sana’ar saida kayan abinci.ina bukatar adda’arku kamar yanda kuka saba,sanna ke mamana zaki koma makarantarki bayan kingama hidimar gama islamiyar ki,mikewa nayi narika salle inafadin allah mungudemaka.su mama saidariya suke dafadin yarinta dangin hauka..
Washe gari cikin ikon allah baba yafara zuwa sabon shagonsa.aranarma munga nasara dankuwa rabin kayan abincin masaya suka saye.saizuwa yy yakuma saro wasu…
Fitowa nayi cikin shirin tafiya islamiya, ina isa natadda dalibai kaf anhadu. Malam nuhu yashigo aji yafara yimana jawabi. Ayau za abaku hutu sai ranar asabar shine zaikasance ranar daza a yayeku.amma kafinna akwai wata sako datashigo mana yau dasafiyarnna.cibiyar makarantarna datake cikin birnin tarayya abuja.AL’MU’ASSASA”ISLAM”ta aiko dasakon cewa kafin ayi yaye dole sai anyi musabaqa, tabukaci dalibai guda biyu daga cikin wadanda za’a yayesu,domin gudanar da musabaqa nakasa baki daya acin birnin na abuja wanda za’a gudanar ranar’asabar mezuwanna.sanna suna bada hakuri akan rashin aiko da sanarwan dawuri.yanakaina yasauke numfashi.kunji sakonda ya isomuko,tsit yan ajin akayi kowa sai raba ido yake da sakar zuci.tirkashi wanna wani irin musabaqa ce haka bazato basammani kuma acikin kwanaki biyar dayarage ayi yariskemu.kuma bana iya jahaba nakasa baki daya,maganar malam nuhu yakasemun zancen xucin danake, khadeeja umar”RUMAINA adamu,kubiyoni yana fadar haka yajuya yy waje.
Kulululu cikina yabada mukahada ido da khadeeja itama daga kurinta hakan takasance, muka mike jiki asabuli mukafita.can muka hangoshi gindin bishiya shida sauran malamai muka karasa inda suke muka sunkuya kasa gefe dasu, RUMAINA khadeeja malam nuhu yakira sunanmu,hada baki mukayi gurin cewa na’am, kune zaku kasance mutum biyunda akabukata dan gudanar da musabaqa takasa dan haka kudage daga yau harzuwa ranar asabar idan allah yakaimu kuzage wajen yin bita,kunajiko? Ai babakin amsa saidaikai kawai mukagyada,suma sauran malaman sukayi kalar nasu jawabin,wai kada mubasu kunya,malam nuhu yamikamin wata farar dakarda yabawa khadeeja ma,yace kukaiwa iyayenku wanna takardar.daga karshedai sukace mutafi gida,
Duk jikina yagama mutuwa haka nadauki hanyargida jiki bakwari,karar mashin danaji abayana yasani jangefe dan tawuce.koda najuya sainaga ashe malam nuhu ne.yafaka akusa dani.yadubeni cikin tausashen murya dafadin RUMAINA nasanki da hazaka kikara akan nada kinga wanna karon musabaqa ce nakasa bakidaya inaso kibada hankalinki sosai kada kiyi wasa.to malam insha allah zan maida hankali.nafadi hakannekawai bawaidan nasamu kwarin guiwa damaganar dayafadaminba.to allah yataimaka jeki gida.nakama hanya………………

 

Comments and Share

 

MAMYN TWINS CE
[10/20, 8:06 AM] Hayat: ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
ALFARMA
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

byโœ๐Ÿป
Rasheeda S’ Director

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da ฦ™asaita take saukowa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.