BOYAYYIYAR KULLI Page 1 to 10 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / BOYAYYIYAR KULLI Page 1 to 10

BOYAYYIYAR KULLI Page 1 to 10

BOYAYYIYAR KULLI Page 1 to 10

PAGE  1
Tsugun ne take tana kuka tana bata hakuri.  “don Allah Mami kiyi hakuri, Wallahi ban san da kayanta a gurin bane.”
“Dallah!  Malama ki tashi ki ban guri…ban son surutun Banza da hofi.” Jiki ba k’wari Zarah ta mike.  tayi hanyar waje tasa kai zata fita kenan Khausar ta hankad’eta ta bugu da murfin kofa. Aiko Khausar tasa ihu. “Wayyo Mami ta karya mun kafa, na shiga uku.” Da gudu Mami ta taso tazo ta rike ta, tana Salati. “Wallahi Mami ban mata komai ba.  Ita ta bugani da kofa fa.  “Dallah rufemin baki muguwa Azzaluman yarinya. Zaki kama ta mu kaita ciki Kokuwa zaki tsaya kina kallo na da shegen idanu kamar na Mayu.!!  Da sauri ta duk’a ta Kama Khausar da tayi rasha_rasha tana sharb’an kuka.  kamar da gaske an ji mata ciwon. K’arasawa ciki sukayi da ita suka ajiye ta a kan three seater dake Falon. Sai Numfarfashi ta keyi. “Kije d’aki ki dauko mata Maganin Athsma d’in ta. “To Mami” haka ta juya da sauri ta Kama hanyar d’akin tana tafe tana hawaye. Saboda Khausar ta buga ta da kofan nan da karfi. Kuma taji shigan shi sosai. Ba yanda zatayi ne. Ko tayi magana ma bashi da Anfani. A haka taje ta d’auko mata Maganin ta kawo mata, ta shak’a sannan Numfashin ta ya dai_dai ta. “Mami ina jin shan Coca oad kar a cika Madara. “Ok bari a had’a miki kinji My Khausar. “Tsayuwar me kike yi to? Ko bakiji abun da tace tana b’ukata bane?.
“Naji Mami bari in had’o mata. Da sauri tayi hanyar kitchen don had’o mata. Bayan tafiyar ta ne Khausar ta kalli Mami tace “Mami wai yaushe Sadeeq zai dawo ne? Wallahi nayi Missing d’in shi sosai. “Uhmmm jiya munyi waya dashi, yace mun yana nan zuwa karshen watan nan. “To Daddy fa nayi zaton ma zan dawo in ganshi ya dawo. “Bai dawo ba, Amma na san yana hanya shiyasa na k’osa wancan Mayyar ta kammala komai kafin ya dawo kin san ji suke kamar su Maida ta ciki a gidan nan. Tab’e baki Khausar tayi ni Wallahi Abun nan b’atamun rai yakeyi Mami, har fa Yaya Sadeeq yafi son ta a kai na fa. Ni Wallahi kamar in bud’e ido in ga ban ganin ta a gidan nan. “Ai ki kwantar da hankalin ki Kawai my sweet Khausar akwai shirin da nakeyi a kan haka. “Yauwa Mami na shiyasa nake son ki. Sallama tayi ta shigo tace “Mami ga shi. Sai da Mami ta harare ta sannan ta Amsa. “Kiyi maza kije ki k’arishe wankin can,  sannan ki zo ki d’ora mana girkin Dare kin san Daddy ku na dawowa yau. “Da gaske Mami!!? Allah ya kawo mana shi lafiya. “Dallah wuce ki bamu guri, har da wani Farin cikin ki don kinji ance Daddy zai dawo. Cewar Khausar. “Bar shegiya Mai idon Mayu. Sum sum Zahra ta fita don kariahe wankin da takeyi. Bayan ta kammala ta shiga kitchen ta dora ma Daddy tuwon shinkafa miyan Egusi saboda tasan yana son shi sosai. Sai to dora jolouf din Macaroni da vegetables saboda Khausar bata cin tuwo. Sai ta d’auko zob’o da b’awon Abarba ta wankeshi ta dora shi a wuta, kafin ta kammala blanding kayan miyan So,  Sob’on ya tauso ta juye shi a container ta tace shi nan da nan ta samishi duk kayan Had’in  ta yan_yan ka Cucumber a ciki ta sashi a fridge. Nan da nan ta kammala ayyukan ta.  Sai ta d’auki flask din Abincin taje ta jeresu a kan dinning.. Ta wuce d’aki don yin wanka tayi Sallah magrib. Da sallaman ta ta shiga D’akin khausar ta gani kwance tana Game da wayar Mami. “Sister Khausar baki ji ina Sallama bane kika yi banza da ni?.
     “Naji sai akayi yaya ban ga daman Amsawa ba.
“Allah ya baki hakuri. An kira Sallah magrib ki tashi kiyi.”
   “Ya Salaam wai ke Zahra wani irin shisshigi ne gareki iyeh!?. Nace ki rabu dani.”
   “Na rabu da ke Amma kin san a Matsayin ki na yar uwa ta dole in dinga fad’a miki gskya. Ta karishe Fad’in haka tana shigewa Toilet. Don tasan in dai ta cigaba da tsayuwa. Zasuyi Fad’a ne, k’arshe ya kai su har gaban Mami kuma ita za’a ba rashin gaskiya. Don tun suna yara ake Nuna mata wannan ban banci har Mamaki ta keyi da kokwanton Anya Mami ta Haife ta kuwa.?  Haka dai ta kammala wankan ta ta d’auro Alwala ta fito. Har yanzu khausar na kwance bata tashi ba.
   “Banza kawai Hala kin tsaya Kashin fama,  ke da ko da yaushe kika shiga toilet sai kinyi Kashi Mtswww kazamiya kawai.
“Lallai ma yarinyar nan to ki hanani yi mana naga ko shugaban k’asa ma Kashin nan yi yakeyi, balle ke. Ki kwana biyu ba kiyi ba Allah Mami sai ta kai ki Asibiti..😜
     “Sai kiyi ai tashi tayi ta shige toilet tayo wanka da Alwala ta fito ta tarar da Zahra na Sallah. D’ayan Sallayan ta d’auko ta shimfid’a ta tada sallah.
Bayan sun idar ne suna zaune suna Azkar, aka kira Isha’i nan suka tashi sukayi Isha’i sukayi Shafa’i da Wutiri. Bayan sun idar ne sukaji Alamun tsayuwar Mota. Aiko da gudu suka fito suka Nufi haraban gidan suna fad’in
    “Well Come Daddy.”
Da sauri ya fito daga cikin Mota ya Nufi yaran nashi cikin Farin ciki, yayin da Mami ma ta fito da sauri domin taryan maigidan nata, suna zuwa gurin shirt kowa ta ja ta tsaya.  shima tsayawan yayi yana kallon su fuskan shi d’auke da murmushi.
“To wa zan fara ma Well come d’in.?
“Daddy kasan nice dai Babba ni zaka Fara ma. Zahra ta Fad’i haka tana turo Cute lips d’in ta.
“Gaskiya Daddy ita taci girma kawai a faramun.
  “To shikenan duka Kuzo my y’ammata na. Gaba d’aya sukaje suka rungumeshi.
 “To ai sai ku sa ke shi haka Malamai, nima ku bari inyi ma Mijina Well come d’in. Gaba d’aya dariya sukayi. Mami ta karb’i jakar Hannun shi da rigar da ke Hannun shi na Baristoci kasancewar shi Babban lauya da yake Aiki a Kaduna.
K’arisawa ciki sukayi  Mami ta jashi ciki don ya yi wanka ya kintsa sai ya fito su ci Abinci. Su kuma su Khausar suka zauna a falo suka fara kallo.
Bayan su Mami sun fito gaba d’aya dining suka Nufa don cin Abinci. Sun zauna Zahra ta tashi tayi Saving din kowa kafin ta Zuba nata ta zauna.
Khausar ne take kallon Mami tana b’ata fuska kaman zatayi kuka.  Tana yamutsa fuska. Mami ne ta mata Alama da ido akan tayi hakuri taci  haka saboda kar Daddy yayi fad’a. ✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Like
Yar mutan zazzau ce😍😍😍😍
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
MY LOVELY KAKA TA ALLAH YAJA KWANA DA LAFIYA MAI AMFANI.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
INNAL LAHA TA’ALA D’AYYIBUN LA YAK’BALIL LAHU ILLAH D’AYYIBAN.
(OUR FAMILY)
PAGE 2
……………. Bayan sun kammala cin Abincin ne suka kwashe komai na dining din suka kai kitchen. Khausar ta fara tsaftace gurin ita kuma Zahra ta shiga domin wanke kayan da suka ci Abincin.
“Yauwa My Hajiya ta wai yaushe ne su Zahra zasu fara Exam ne.?
“Eh naji suna cewa Next week zasu fara.”
“Ok ina son in sani ne saboda akwai gift dana tana dan musu, sannan ina son suyi Jamb ne.  kin ga duk sai in result d’in su ya tashi fitowa ya fito gaba d’aya. Saboda bana so su b’ata lokaci a gurin karatun saboda kin san yara Mata lokacin su a k’ure yake.
“Haka ne Daddy su. Wai yaushe yaron nan zai dawo ne k’annin shi nata kewan shi.?
“Ina tunanin cikin Satin nan zai dawo fa, kinsan sun kusa kammala Service d’in nasu. Amma naji yana cewa yana dawowa zai yi Applying Air force ne.”
“Ban gane ba Alhaji wani irin Air force shi da ya karanci aikin Jarida. Kuma ma wai ni banji kuna maganar Aure ba ne kai da shi. Ko kuwa bokon Zai Aura Nifa na gaji da ganin shi ba Aure.  Kuma na fad’a maka so nakeyi a Had’a shi da Khausar.”
“What!! Kin san abun da kike fad’a kuwa?  Meyasa kike k’okarin fallasa Abun da ke rufe, kin san na riga na Fad’a miki ko bayan ba rai na bana b’ukatar Yara na su san wani Abu game da wannan zancen, kuma had’a Khausar da Sadeeq tamkar Fallasa wani K’ulli ne da sirri da ke cikin Family na. Kuma bana fatan hakan kinji na fad’a miki. Tashi yayi rai a b’ace ya shige d’aki.
“Wallahi indai ina raye khausar bata da Mijin da ya wuce Sadeeq. Kuma wannan B’OYAYYIYAR K’ULLI da baka so a fallasa sai na Bank’ad’a shi. Indai ina da rai ni Hajiya Laure.
Tunda ya  shiga d’aki  yake ta safa da Marwa. Tunani ya fara “Meyasa Laure ta ke son yin mishi, to meye Nufin ta da haka.ya Allah ya kawo mai Mafita ya kare mai iyalan. Kar Allah ya Nunamai ranar da Yaran shi zasu Fahimci wannan B’OYAYYIYAR K’ULLI. Ya kara had’a mai kan su.  su zama tamkar tsintsiya madaurin ki d’aya. A haka ya hau kan Bed d’in shi yayi Addu’a barci ya kwanta.
*************************
LAGOS
“Wai ni Sadeeq ya maganar komawa gidan ka ne.? Naji ba ka cemun komai ba ne.
Hotunan da suke Hannun shi ya ajiye ya mai da kallon shi a kan Abokin nashi. Sai a lokacin na k’are mai kallo, chocolate colour ne don baza’a kirashi Fari ba. But skin din shi yana glowing tamkar na jarirai dogo ne Amma ba can can ba, yana da siririn fuska mai d’auke da dogon hanci wanda ya dace da fuskan shi, yana da lumsassun sexy eyes, had’i da madaidaita pink lip d’in shi, ga wani zagayayyan saje da ya kara ma fuskan shi kyau. “Kai tsayawa ma lissafa muku kyau shi b’ata lokaci ne.
“Abokina Soyayya bata mun Adalci ba ta rasa ina zata jefani sai gurin k’anwa ta kuma jinina. Meyasa please ka fad’a mun meyasa haka. Dama mutum na jin haka? Yaji yana ma kanwar shi wanda suka fito Ciki D’aya Soyayya irin ta Aure.? Ka fad’a mun mana kayi shiru.
“Innalillahi wa innah ilaihirraji’un Sadeeq Lafiyan ka kuwa taya za’ace mutum yaso k’anwar so irin na Aure. Kai ina ko a Labari ban tab’a jin wannan ba. Ka dai k’ara tunani zallah shak’uwa ne yasa kake jin haka a Zuciyar.
” No! No!  Ahmad ina jin in ban Auri Baby Zahra ba bazan iya Rayuwa ba. Itace rayuwa ta,  ita ce Farin ciki na, Kuma in ban Aure ta ba zan iya rasa rai na ko in shiga wanin Mummunan Hali.
“Wai ya kake Fad’in haka ne Sadeeq ya kamata ka dawo hankalin ka kasan mai kake fad’a. Ahmad ya fad’a ma Abokin nashi rai a b’ace. ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Like
. kudai cigaba da bin yar mutan Zazzau.  😍😍😍😍
*B’OYAYYIYAR*
                 *K’ULLI 😭😭😭*
*STORY*
         *AND WRITTEN*
                   *BY*
*ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.*
*MARUBUCIYAR*
*GIDAN GADO*
*WAZAN AURA 1&2*
*AND KNOW*
*B’OYAYYIYAR K’ULLI*
*DEDICATED*
         *TO*
_*SHUGABA TA GARI AUNTY HAUWA S ZARIA (MAMAN USWAN) ALLAH YA BARMANA KE YA KARA D’AUKAKA YA RAYA MIKI ZURI’A AMEEN.*_
_*BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.*_
_*LAA’ILAH HA’ILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN.*_
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
_*(MAMI    AND DADDY)*_
PAGE    3
*************************
“Tabbas Abokina sai dai in har ba ciki d’aya kuka fito da Zahra ba, indai haka ne akwai wani boyayyan Al’amari a tare da ku, dole ka bincika.”
Dafa kafad’an Ahmad yayi yace mai. “Ahmad  tabbas Zahra k’anwatace daga ni sai Zahra sai Khausar, kasan Zahra da Khausar Twince ne. Sanin kan ka ne munfi kama da Zahra sosai a kan Khausar da Mami domin khausar da Mami tafi kama shiyasa Mami ma tafi son ta. Lokacin ina makaranta na dawo na tarar da Mami ta Haifi su Zahra nayi Farin ciki sosai, don a lokacin nima ina so inga ina da k’anwa da Mami  ta tashi sai ta Haifo min har k’anni biyu. Tun da Mami ta Sami ciki Daddy yake ta farin ciki har ranar da ta Haifi su Zahra. Lokacin ina da shekara takwas a duniya, to makarantar da Daddy ya kaini shi ne mafi tsada a garin Zaria, kuma kwana akeyi sai weak end zaka zo gida to dawowa na weak end na tarar da Mami ta haihu. Tun daga lokacin da na d’ora ido na a kan Zahra naji wani Soyayyan ta da k’aunar ta a raina har rana irin ta yau da nake fad’a maka wannan zancen Aboki na. Kuma kullum soyayyar ta k’aruwa takeyi a cikin raina.
Ajiyar zuciya Ahmad yayi. “To nidai Abokina ban san kuma mai zan cemaka ba don ni gaba d’aya lamarin naka yasani a cikin tunani da kokwanto mai yawa. Sai dai kawai mu cigaba da Addu’a.
“Insha Allah Aboki na. Bari ma in kira Mami nasan yanzu suna nan suna cin Abincin da Yammatan ta, Assalamu Alaikum Mami na.
Amsa mai tayi had’i da fad’in “My only yaro na d’aya tamkar da dubu da fatan kana lafiya.? Muna ta kewan ka, yaushe zaka dawo?
“Nima ina kewar ku My Only Mami na. Ina k’annina.?
“Ga Khausar nan kwance Athsman ta ya tashi, ita kuma Zahra tana kitchen tana wanke_wanke.”
“Ok Amma Mami nace miki in samo miki yar aiki saboda naga kamar Aikin nan nama Zahra yawa, kinga ita kuma khausar bata cika lafiya ba.”
“Kaga Son dakata in har basu saba da aiki tun yanzu ba sai yaushe kake so su sa ban.?  Ko so kake in kai yaran nawa gidan Aure a ce basu iya komai ba.?
“Haka ne Mami yanzu da basu mu gaisa.”
“Ok”ta mik’a ma khausar wayar.
“Hello Yaya Sadeeq I miss you too don Allah yaushe zaka dawo  please.?
“Insha Allah Baby Khausar Next zan dawo… Ina Baby Zahra kai mata wayar kinji.
“To Yaya.  tashi tayi daga kwancen da take ta Nufi kitchen “Zahra Yaya na waya.
“Da gaske.?  Ta fada cikin jin dad’i da farin ciki. Harara Khausar ta balla mata had’i da mika mata wayar tayi gaba abin ta don tasan in ta tsaya zata kwashi kayan Haushi ne.
“Hello Yaya na yaushe zaka dawo please. Ina ta kewan. Ta Fad’i haka cikin sigan shagwaba wanda ya sanya Sadeeq gaba d’aya jin kasala da wani shauki a cikin Zuciyar shi, yayin da duk wani gab’a na jikin shi ke kai mishi wani sako zuwa zuciyar shi da kwakwalwar shi. Lumshe ido yayi yana cigaba da Sauraran ta.
“Hello Yaya kana jina kuwa? Na ji kayi shiru ne.?
“Ina jin ki Baby na da fatan ba Abun da ke damun ki ko? Mami basa takuramiki?
“Kai yaya wannan irin tanbaya ni ba Abun da ke damuna sai kewar ka. Please kayi ka dawo, gashi mun kusa fara Exam.
“Da gaske kina kewa ta? Ok karki damu na kusa dawowa kinji. To Allah ya baku sa’a my beautiful sisters, Amma ki dan dunga taimaka ma yar Uwan ki kin san khausar sai a hankali kinji.
“Ayyah ba komai Yaya insha Allah Karka damu duka zamu fita da A A.
“Ke Zahra ban waya ta ki k’arasa aikin da ke gaban ki, ke kina da abun yi tunda naga alamar baida nayi. In kun fara waya kamar zaku kwana.
Ta Amshe wayar ta tayi gaba. “Sadeeq in ka dawo ina son magana da kai.
“To Mami sai na dawon bye bye. Ya kashe wayar.
D’ago kan da zatayi suka Had’a ido da Daddy ranshi a b’ace yake kallon ta. “Wallahi Laure matuk’ar kika fallasa mun B’OYAYYIYAR K’ULLI da ke gidan nan a bakin Auren ki.
          Da sauri ta juyo tana kallon shi. fuskan ta cike da fargaba ga tsoro. “Haba Alhaji a bakin Aure na fa kace.?
“Eh haka nace. Ya Fad’i ya tashi ya bata guri..✍️✍️✍️
More comment more typing inna ga ruwan Comment in kara yawan page ehe😏
Share
Comment
Like
Yar mutan zazzau ce😍😍😍😍
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
TO B’OYAYYIYAR K’ULLI FANS INA YINKU IYA WUYA YANZU NA FARA JIN KWARIN GWIWAN TYPING KUN SAN COMMENT NA ZABURAR DA WRITERS. LOVE YOU LODI LODI 💖💖💖.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKEEL.
(Our problem )
PAGE 4
*************************
One week later
Gaba daya gidan ya karad’e da kamshin girki,   yau har da Mami da Khausar a a kitchen.  saboda dan lelen Mami zai dawo. Anyi girki yayi kala biyar. Bayan sun gama kowa ya shige d’aki don shiryawa don jirgi zai biyo zasuje kaduna su d’auko shi.
Daddy ne ya fito cikin shirin shi da ya Had’e cikin dinkin jamfa da wando had’i da Babban riga da yasha d’inkin surfani da Aska.
 (Note ga masu bukatan dinki irin na manyan kaya kama daga d’inkin rumi, surfani Aska, d’inkin d’ai_d’ai, d’inkin design, phonix cunko duk munayi. Zaku iya tuntuba na ta wannan Number 08037420816).
“Mamin Yara kufa nake jira kun san baya son jira yanzu sai tayi fushi.
“Sorry Daddy yara gani nan fitowa, Mami ce ta fito tasha wata dakakkiyar geziner wanda taji Stone work d’inkin doguwar riga, ta murza d’auri bazaki taba cewa ita ta Haifi su Zahra ba.
“Kai Masha Allah  My wife kinyi kyau fa, kullum k’ara kyau ki keyi bakya tsufa. Ya fad’a cikin sigan zolaya.
“Kai Daddy yara har na kai ka ni tunani na kar Yan mata su kalle mun kai.
Uhmm uhmmm Khausar ce tayi gyaran Murya “kai Mami wannan kalamai da kike ma Daddy ai sai kisa ya kasa karo mana Aunty 😂.
“Keee!!  Khausar gidan ku nace ni kike ma mugun fata. Kaga mun yar banzar Yarinya dai.
Gaba daya dariya suka sa har da Zahra da take fitowa cikin shigar wani less popul tasa takalmin ta popul hijab tasa har k’asa sab’anin Khausar da ta sa wani Arabian gown ta yane kanta da gyalen rigar pitch colour.tayi kyau sosai kasancewar ta fara sosai  don tafi Zahra Haske.
“Wai ke Zahra me ke damun ki ne? Baki ga shigar da y’ar uwan ki tayi bane, kin wani zurma hijabi kamar Matam liman. Dallah wuce kije ki d’auko mayafi ko kuma wlh mu fasa zuwa da ke.
“A’a ba haka ya kamata ba Mamin yara ki bita a hankali mana, kin san kowa da ra’ayin shi, ki bar ta tayi abun da take so Matukar bai sab’ama shari’a ba.
Ba don Mami taso ba suka tafi.
*************************
Saukan su kenan a jirgi inda yayi dai_dai da isowar su Mami. Tun daga Nesa ba wanda ya fara hangowa sai Zahra tayi matukar yi mai kyau ta k’ara girma. Yayin da Khausar ita kuma ta shagaltu da kallon Yayan nasu inda take jin wani abu a cikin zuciyar ta na  mata yawo, da sauri ya k’ariso ya rungume Daddy ya bashi peck a goshi, ya koma gurin Mamin su da take ta zuba murmushi take kallon d’an nata cike da so da k’auna da kulawa.
K’arisawa yayi kusa da Mami ya rungume ta “I miss you Mami.
“Miss you too my sweet Son.
“Au ni bakayi Missing d’ina ba, my Yaro na.?
“Sorry Daddy na. To ku kuma duk kun wani k’ame kaman Sojoji baza Kuzo ku yimin well come ba.
Da sauri Khausar tazo ta rungumeshi tace “well Com my sweet brother we miss u too.
Kallo ya maida kan Zahra da ta tsaya ta kasa daga kan ta. Kura mata ido yayi, da k’yar ya tattaro ragowan kuzarin shi, yace mata “Baby Zahra baza kimun Well come d’in bane.?  K’arisowa gurin shi tayi sai ta duk’a zuwa k’asa tana fad’in “ina yini Yaya Well Come back. Kafin ta kai k’asa ya d’ago ta ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya.
“I so much miss you my one and only lovely sister. Duk a cikin kunnin ta ya rad’a mata wannan kalaman. Shiyasa su Mami basuji ba.
“To Son sake ta Muje Mana. Dare nayi duk da Zaria da kaduna ba wani nisa bane.
“Ka barshi kawai Daddy Yara, ni fa Abun Son mamaki yake bani inda yake Nuna banbanci a tsakanin Yaran nan. Haba don Allah to ni ban son haka. Har suka karisa Mota Mami tana Fad’a har sai da Daddy ya dakatar da ita tayi shiru.
************************
Sun isa gida ana kiran Magriba.shiyasa suna isa su Daddy da Yaya Sadeeq suka wuce Masallaci, su kuma Su Zahra suka wuce cikin gida don yin nasu Sallah.
Sai da sukayi Sallah isha’i sannan kowa ya hallara a Falo don cin Abincin.
Suka zauna suka fara cin Abinci. Bayan sun gama ne. Suka fara hira yaushe rabo, duk wanda ya gansu yasan Happy family ne.
“Yauwa Daddy gobe insha Allah ina so in shiga cikin City gurin Guggo.
“Ok tunda Lahadi ne sai ku tafi da k’annin  ka. Tana ta korafin sun rabu da zuwa gaishe ta.
“To shikenn Daddy Allah ya kaimu, Amma islamiyan fa.?
“Zan kira Islamiyan in sanar bazasu samu zuwa ba. Ai hakan yayi.?
“Eh yayi Daddy. Yauwa tsarabar ku yana cikin d’aki Zahra ki d’auko muku sai Mami ta raba muku ke da Khausar.
“To Yaya.” Mik’ewa tayi da nufin zuwa d’aukowa.
“Zahra dawo. Ku barshi sai da safe…. Ku tashi kuje ku kwanta kar ku manta kuyi Addu’a. Mami ta Fad’i haka fuskan ta d’aure ba wani alamun walwala a ciki.
Daddy ya tashi “to ni zan shiga ciki, kar dai ki manta da abunda na fad’a miki satin da ya wuce. Bayan ya gama fad’a mata yayi shigewar shi ciki.
Yayin da Mami gaba d’aya jikin ta yayi sanyi ga k’oshi ga kwanan yunwa, don tana Matuk’ar son Auren ta, kuma tana san Daddy kaman yadda take son rayuwar ta. To Amma ya zatayi da Alk’awrin da ta d’aukar ma kanta cewa Khausar bata da Miji sai Sadeeq don ta haka ne kawai zata cika B’oyayyiyar burin ta. Gashi Daddy yana so ya hanata cika burin ta, Kai akwai Matsala fa.
“Mami matsalar mene.?
Figigit tayi don batayi tunanin Maganar ta fito fili ba. “Son ina cikin Damuwa ka tayani da Addu’a kaji.
“Mami Damuwar mene? Ki fad’a mun abun da ke damun ki, kin san duk d’a na gari bazai so yaga Mahaifiyar shi cikin damuwa ba.
“Sorry my Son kawai ka tayani da Addu’a komai zai warware insha Allah.
“To shikenn Mami Amma don Allah kicire Damuwar nan a ran ki.
“Karka damu d’an albarka farin ciki na ina alfahari da Haihuwar ka.
*************************
Washe gari
Wasu had’addun takalma ne da dogayen riguna masu kyau ya siyo ma su Zahra kowa bibbiyu. Uku Mami taba Khausar taba Zahra D’aya tace mata. “Ke ai irin wad’an nan kayan ba so kikeyi ba.  Asali ma ba son kwalliyan kikeyi ba gara a ba wanda tasan darajar kwalliya.
Wani takaici ne ya rufe Zahra kaman zatayi kuka, kuma duk masu kyau ta kwashe ta ba Khausar ko bazata sa ba ya kamata a bata tunda hakk’in ta ne.
“Amma Mami ina son kayana ai kuma ni bance bazan sa ba. Kuma hakk’ina nane. Mami ko dai ba ke kika Haifeni ba.?  K’iyayyar da kike Nuna mun yayi yawa Haba don Allah.
“Ke baki da hankali ni kike Fad’a ma haka Zahra yaushe kika zama Mara kunya.? Duk duniya kina da Uwar da ta wuce ni ne, in d’au cikin ki wata Tara in haifeki in rai ne ki, sannan ki bud’e baki ki fad’a mun haka. Mami ta karishe Maganar cikin fushi.
“Don Allah Mami na kiyi hakuri ban Fad’i haka da nufin in bata miki rai ba don Allah ki yafe mun.
” naji ku tashi kuje ku shirya kar Yayan ku ya shigo baku shirya ba, kuma saura ki fad’a mai abun da ya faru. ✍️✍️✍️✍️✍️
More comment more typing
Comment
Share
Vote
Like
Yar mutan zazzau ce😍😍😍
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
TO B’OYAYYIYAR K’ULLI FANS INA YINKU IYA WUYA YANZU NA FARA JIN KWARIN GWIWAN TYPING KUN SAN COMMENT NA ZABURAR DA WRITERS. LOVE YOU LODI LODI 💖💖💖.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKEEL.
(Our problem 2 )
PAGE 5
*************************
“Insha Allah Mami bazan fad’a ba.
Khausar ne ta bita da Harara had’i da tab’a baki. “Wai ni Mami meyasa ki haifemu tare da wannan yar kauyen.? Komai nata sai tayi kauyanci, kwata_kwata bata waye ba kamar ba jinin ki ba. Nifa ji nake banjin ko d’igon son ta a rai na.
“Ke Khausar!! Ashe baki da hankali ban sani ba. To Zahra yar uwan ki ce duniya da Lahira baki da kamar ta don ciki d’aya kuka fito ke da ita. Kar in kara jin haka.
Kuka ta saka.  “Haba Mami shine zaki wani rufeni da fad’a don na Fad’i Abun da ke zuciya ta. Tashi tayi cikin fushi had’i da tab’ara zata tafi. Da Sauri Mami ta rungumo ta jikin ta.
    “Haba yar lelen Mami kiyi hakuri kin san ban son in ga kina fushi. Kece kika b’atamun rai kin san in Daddy ku yaji wannan zance duka daga ni har ke bazamu ji dad’i ba, kuma ni zai d’ora ma laifi karshe ma yace in bar mai gidan shi. Kin san Daddy ku bai had’a ku da kowa ba da komai a duniya kullum burin shi yaga kan ku a had’e   yaga kuna son junan ku. To yanzu ke a tunanin ki in har Daddy ku yaji abun da kike fad’a, sai ran mu ya b’aci.
“Insha Allah Mami bazan kara ba kinji Mami.
“Yauwa Ke Khausar kun shirya ne ku fito mu tafi. Ina Zahra.?
“Kai Yaya har ka shirya bari in je kaya kawai zan sa na riga nayi wanka, Sister ma nasan ta shirya tunda ita shirin ta ba wuya yakeyi ba.
“Ok ku Sameni a Mota. Ya wuce yaje ya tsugguna a gaban Mami.
       “Mami na kin tashi lafiya.?  Da fatan kina cikin koshin lafiya.?
“Ina lafiya lau yaron kirki meya hanaka fitowa muyi breakfast.? Ya kuma gajiyar tafiya.
“Lafiya lau Mami Wallahi gajiya da barci ne ya hanani. Kuma ina son inje insha Kokon Guggo mai dad’in nan, saboda nayi Missing din shi daga nan ince ta koya ma su Zahra saboda suzo su dunga damamun kinga na huta da zuwa can sha.
“Kai Yaron kirki Lallai Guggo ta iya dama Koko, da Alama dashi zata siye Zuciyar Mijin nata.
“Ai kaman kin sani Mami. Ya Fad’i haka yana Mik’ewa, “to Mami na sai mun dawo.
“To a dawo lafiya dan Albarka. Allah ya tsare mun ku ya dawo mun da ku lafiya.
“Ameen ya Allah Mami, don Allah kice musu suyi sauri su fito don na kosa in ga Uwargida ta.
“Ok gasu nan bata gama rufe baki ba sai gasu sun fito, sunyi Matukar kyau don kaya kala d’aya suka sa, haka gyale ma sai dai gyalen Zahra kato ne ta lullubashi a kanta har jikin ta. Sabanin na Khausar da yake k’arami a kafad’a ta d’ora shi.
“Masha Allah yaran Daddy sunyi kyau, sai ina za’a da Safen nan.?
“Daddy Zamu gidan Guggo ne cikin City.
“Daddy su ka manta kenan na fad’a maka zasuje.
“Ke dai Bari Mamin Yara wallahi na Mance. To a dawo lafiya a gaidamun ita da kyau,  ku cemata insha Allah inanan shigowa.
“To Daddy, Mami mun tafi sai mun dawo suka Fad’i suna ficewa daga Falon.
         Tun da suka doso idon Sadeeq na kan Zahra inda tayi mai wani Masifan kyau, duk da Khausar tafi Zahra komai, Amma shi kawai Zahra shi yake hange in ta doso tana disashen duk wani kyawu na y’a Mace a idon shi.
“Yaya tunanin mai kakeyi muna ta Magana kayi shiru.?
“Oh sorry ban san ma kun kariso ba. Ke Khausar ban fad’a miki cewa in Zamu fita ki dena Hawa front seat ba,?  koma baya Zahra dawo gaba.
Fita tayi tana zunburo baki.
“Yaya Sadeeq da ka barta a gaban ni in zamu dawo sai in hau gaban.
   “Shut up dama shawaran ku nake Nema. Zaki dawo ko sai ranki ya  B’aci ne.?  ai a tsorace sukayi exchange na seat don sun san halin Yayan nasu baya musu da wasa.
Tun da suka fara Tafiya idon shi a kan Zahra yake, ganin inda ta d’aure fuska, haka da ya leka khausar ita ma. Murmushi yayi “Haba my Twince Sisters d’ina fushi kukeyi da Yayan naku kun san bai jure ganin kyakkyawan fuskan ku a d’aure. Ku muje Apple white kusha Ice cream. Sai mu wuce.
Suna jin haka sai kowa ta fara Washe baki don suna matuk’ar don Ice cream, karma Zahra taji.
“Hello Guggo kin tashi lafiya.?
“Lafiya lau Habibullahi, ya yaran naka, wai mijina ya dawo kuwa.?
“Eh Guggo ya dawo jiya suna hanyar zuwa ma gidan ki yanzu haka.
“Kai kai har da Yan biyu kyautar Allah, kace Zama bai ganni ba bari in tashi in tarbi mai gida, don ni ban ta kishiyoyi.
Dariya Daddy yayi.
“Yauwa Hajiya Guggo ina neman wani alfarma gareki, ko da Sadeeq ya tambaye ki wata Magana game dasu don Allah kar ki Bayyana musu B’OYAYYIYAR K’ULLI nan.
“Ikon Allah Habibullahi mai ya kawo wannan zancen kuma,?  Nayi tunanin an dad’e da rufe wannan babin.?
“Maganar Bazai yuwu ta waya ba, Amma sai na shigo unguwar✍️✍️✍️✍️🤣
Share
Comment
Like
Vote
ZEEY YAR MUTAN CE😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
DILLALAI FAMILY
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
INNALLAHA MA’ASSABIREEN.
(Our problem 3 )
PAGE    5
*************************
Sun isa gidan Guggo karfe Tara na Safe. Tun daga kofan get d’in gidan su Zahra suka fara kwala ma Guggo kira.
“Y’ar tsohuwa.! Y’ar tsohuwa.!
“Oh Ni Fadimatu wa’innan fitinannun Yaran sun iso kenan. Ta Fad’i haka tana fitowa daga falon ta.
  Rungume su tayi duka su biyun tana jin k’aunar su a cikin ran ta.
     “Munyi Missing d’in ki kwana biyu, muna ta cewa Daddy ya kawo mu bai kawo mu ba.
“To ba gashi yanzu Yayan ku ya kawo ku ba.
“Wai ni haka a ke tarban Mijin, kin wani shareni sai ta kishiyoyi kikeyi.
“Wayyo Yi hakuri Mijin. Sakin su tayi taje ta rungume shi, mu shiga ciki na tanadar ma hadadden Kokon ka yasha kayan kamshi.
“Yauwa my sweet Uwargidas. K’arisawa cikin Falon sukayi. Falon komai tsaf saboda Hajiya Guggo akwai tsafta komai nata tsaf_tsaf ne. Zazzaunawa suka yi a falon kowa ta ciro Ice cream din ta ta fara sha.
Guggo kuma ta shige kitchen, sai gata ta fito da Jug a hannun ta da kananun Cup, ta ajiye musu ta kawo musu  k’osai yaji kayan miya da yaji.
Duka suna ganin K’osan suka ajiye Ice cream d’in suka sauko suka Baje a falon. Zahra ta Zuzzuba musu Kokon a Cup ta mik’a musu ita ma ta zauna suka fara sha. Suna sha suna Santi.
Bayan sun kamnala sha ne, Suka kwashe kayan sukaje kitchen, Zahra na wankewa Khausar na d’aurayewa tana sasu a inda ya dace. Har suka gama suka gyara komai na Kitchen d’in.
“Guggo don Allah ina son muyi wata Magana ko zamu je baya ne.?
“Lafiya dai ko Mijin.?
“Lafiya Lau akwai Abun da ya shige mun duhu ne. Nake son k’arin Bayani.
 “To shikenan muje, ka d’auko mana kujerun Roban nan sai mu zauna a kai.
  “Angama Hajiya kin san ni mijin Hajiya ne ai, sai abun da kika ce. Ya Fad’i haka yana dariya.
  Bayan sun Zauna ne. Hajiya Guggo ta dubeshi tace mai. “Ina jin ka mai gidan.
“Guggo don Allah ki Fad’a mun Mami da Daddy su suka Haifemu gaba d’ayan mu ba wanda yake bare a cikin mu.?
“Sadeeq Lafiyan ka kuwa,?  meyake damun ka? Meya kawo wannan shirmen.
“Ke k’adai ne nake da kwarin gwiwan da zan fad’a ma abun da ke Damuna, Wallahi Kaka tun da aka Haifi Zahra nake mata wani Mahaukacin so, na zata kawai irin So ne na jini na Yaya da K’anwa sai yanzu da Zahra ta k’ara girma na kara tabbatar da Son Aure Nake Mata,  So kuma na har Abada wanda bazan iya jure Kallon ta da wani D’a Namiji ba a Matsayin Miji in ba ni ba. Don Allah ki taimaka ki Fad’a mun, in har Zahra Cikin mu d’aya da ita mai zai sa inji haka. Don Allah  ki Fad’a mun Kaka ta. 🙏🙏
  “Haba Sadeeq wannan wani irin Hauka ne.?  Rana tsaka zaka zo ka tada mana hankali ina ka taba jin anyi wannan kwamacala.?  Kar in karajin wannan maganar kaji koh.?  Ko Mahaifiyar ku ban yarda taji Maganar nan ba, tashi kaje ka d’auki K’annin ka ku tafi.
Jiki ba kwari ya tashi, idon shi yayi jajawur.
Da sauri Khausar  ta bar bakin Kofan bayan ta  gama jin duk Abun da ya faru tsakanin Yaya Sadeeq da Kaka.
   “To me hakan yake Nufi,? Shin dama yawan kulawar da Yaya yake Bama Zahra, da yawan goyan bayan ta da yakeyi dama Son ta ya keyi. Innalillahi Allah gamu gareka wannan wani irin Jarabawa ne Allah zai D’ora musu, ace jinin su kuma yana son Yar uwan ta, kuma kanwar shi Ciki D’aya. Dole Mami taji Labarin nan domin ta d’au Mataki.✍️✍️✍️✍️✍️
Comment
Share
Like
More comment more typing..!
Zeey yar mutan zazzau 😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
Kamal bakano😜😜
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
ALLAHUMMA ANTA RABBEEY LA’ILAH HA ILLA ANTA KHALAK’ATANI WA ANA ABDUKA WA ANA ALA AHDIKA WAWA ADIKA MASTAD’A ATIKA FAGFIRLEEY FA INNAHU LA YAG FIRUL ZUNUBA ILLAH ANTA. 🙏🙏
(Continue  )
PAGE 7
*************************
Sun kama hanyar gida kowa da abun da take sak’awa a ran ta, Yayin da shi kuma Sadeeq tuk’in kawai yakeyi Amma baya cikin hayyacin shi. Ikon Allah kawai ya kai su gida. Haka kowa ya fita shiru_shiru, shiga sukayi Falon Had’i da Sallama, Tarar da Falon sukayi ba kowa Alamun Mami bata a Falon. D’akin su suka wuce suka fara ciccire Mayafan su. Khausar duk ta kosa taje gurin Mami ta Fad’a mata abun da ke faruwa. Fita tayi Zahra na mata magana ko kallon ta ba tayi ba ta fice.
D’akin Mami direct ta Nufa, ta kama Handle d’in kofan zata Bud’e sai taji kamar Mami na wani Magana. Dakatawa tayi don Zahra tayi lafiyar yin lab’e.
“Kina jina koh Hajiya Halima Wallahi ina cikin Damuwa don da alama burina bazai cika ba, domin kuwa Alhaji Habibullahi yana neman kawo cikas a gurin cikar Burina. Kin san dai Plan d’in da muka shirya a kan Cewa zan Aura ma Sadeeq Khausar.  Saboda Khausar tafi Zahra wayo da komai, ita zata Zama tsani na cikar Burina. To Wallahi Alhaji Habibullahi ya ce duk randa na furta wani Abu da zai Bayyana B’OYAYYIYAR K’ULLI a bakin Aure na, Hankali na ya tashi na rasa meye Solution.? Ok shikenan sai kin zo. Kashe wayar tayi ta fara Zagaye d’akin cike da damuwa.
    “Tabdijam Aure kuma nida Yaya Sadeeq. Wai meke shirin Faruwa ne wannan wani irin kwamacala ne kodai akwai Abunda su Mami suke Boye mana ne. Tabbas koma meye sai na binciko shi. Juyawa tayi ta fasa shiga D’akin ta koma D’akin su, Tarar da Zahra tayi tana duba takardun ta.
  “Sister wai Yaushe ne za’a Fara Exam d’in.?
“Wannan Weak d’in da zamu shiga, Amma Sister wani Course kike son yi ne in mun ci Jamb din mu.?
“Ina tunani Kamar genocolgy zanyi fa. “Masha Allah Course d’in nada matuk’ar kyau kice Sister nawa Likitan Mata zata Zama. Allah ya bada sa’a. “Ke kuma mai Zaki karan ta.?
“Ni ina son in gaji Daddy ne Law nake son karantawa tunda Yaya Sadeeq yaki ya cika ma Daddy Burin shi, shine nake so ni in cikamai.
   “To Allah ya cika mana burin mu duka, bari inyi wanka. “Ok sai kin fito.
*************************
Wata Hamshakiyar Mata na hango tana Zaune a kujera ta Dora kafa d’aya kan d’aya, ga fruit a gaban ta tana sha. Ga wata yarinya a gefen ta tana Matsa mata kafafu.
“Ke je ki d’auko min ruwa cikin fridge.”
     “To Momy. Yarinyar da ke Matsa mata kafan ne ta tashi don zuwa kitchen d’auko Abun da wannan Hamshakiyar Matan ta aike ta. Sai a lokacin na kare ma Matar kallo Mace ce Hamshakiyar mai kimanin shekara Arba’in a duniya Fara ce sosai tamkar ka Taba jini ya fita, da ka ganta kasan hutu ya zauna tattare da ita, Kuma Mace ce ita mai Izzah mai son a girmama ta, kuma a girmama Izzan ta, Ba kowa bace Face Hajiya Nafisa Matar Hamshakin D’an kasuwan nan wanda kaf Africa an san da Zaman shi, saboda yawan Companonin shi da gida je da kadarorin da ya Mallakar, Wato Alhaji Bukar Mai Naira ba wanda bai san shi ba.
 Sai dai ya kasance bai taba Haihuwa ba duk da yayi Aure_Aure da yawa  kowa tazo sai dai ta fita ba tare da ya samu Haihuwa ba.Hajiya Nafisa itace Uwar gidan shi ita kadai ce ta iya jure Zama dashi haka. Ita ma d’in tana Zaune dashi don cikar wani B’OYAYYIYAR K’ULLI nata wanda tana cimma Nasara zata k’ara gaba.  Tun Abun na damun Alhaji Bukar har ya hakura ya  Fawwala ma Ubangiji.
Sallaman da akayi yasa ta tashi da Saurin ta. “Lale lale da Masoyi shine baka sanar mun kana Hanya ba.
   “Kar ki Damu Masoyiya, akwai taron da zamuyi ne na wani Sabon Company na da zan B’ude a Kaduna.
“Ok to mu shiga ciki kayi wanka, in sama ma abin da zaka ci.
*************************
ZARIA
Makaranta ne Babba wanda ta tara d’alibai kala_kala wato Gifat International School makaran ta ne sai wane da wane. Hall ne Babba inda na hango D’alibai cike a Hall din  yayin da wasu ke  bitan karatu wasu Kuma na hira, Can karshen Hall na hango Zahra tana Zaune ta na karatu. “Lah Zahra dama kina nan nake ta Neman ki. “To in banda abinki Eshart kin san inda zaki sameni ai. “To nidai duk ba wannan ba kin san Abun da wancan figaggiyar mare kunyar Kanwar ki taje tana cewa.? “Sai kin Fad’a.”
 “Wai Zuwa tayi tana ce ma su Zuhra da Zakiya da Jafar wai Baki da gata kudin ba yan biyu bane shiyasa ma ta fiki Haske aiki kikeyi a gidan su shine Daddy ta ya taimake ki. “Kai Eshart ni wallahi inda Sabo na saba da halin Khausar to mai zai dameki da ita. Yarin ta ne da shirme ke damun ta wataran zata bari. Tashi muje ki rakani Library in duba wani Abu.
“Ni wallahi Zahra kar Allah ya ban hakuri irin naki in zauna k’anwata ta rai nani. Juyawa tayi da sauri tana mai jin haushin Halin k’awar na ta. Zahra tana kwala mata kira ko waigen ta ba tayi ba. ✍️✍️✍️✍️
Like
Share
Comment
More comment more typing
Zeey yar mutan Zazzau ce😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
To Maccido Ina godiya Dan uwa Allah ya bar Zumunci.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKEEL.
(Different town )
PAGE 8
*************************
JOS
Kowa ya San garin jos gari ne Wanda in lokacin Damina da lokacin sanyi yayi suna da matsanancin sanyi. To hakan ya kasance lokacin Damina Kuma ba’a dad’e da d’auke ruwan sama da aka kwana a nayi a ka Kuma kusan yini Ana yi hakan ya takura ma mutane da yawa gurin fita harkokin su.Can na hango wata Mata ta rakub’e a jikin wani shago Tana ta rawar Sanyi,gaba d’aya kayan jikin ta sun jike,ga yunwar da take ji har ya galabaitar da ita  da k’yar  ta ke fitar da  Numfashi.wata Mata ne ta k’ariso gurin da take rike da Lema a hannun ta,Saboda har a lokacin ruwan bai Gama d’auke wa ba.
    “Subhanallahi Wai Dije a Nan gurin dama kika kwana ga ruwa kina gani me ya hanaki shiga cikin rumfa na ki kwanta gashi da alama har Mura ta kamaki da Zazzabi.taso muje ki cire kayan Nan in baki wasu kisa.bige hannun ta tayi had’i da mak’e Mata kafad’a ,Alamun baza ta bita fa.  “Yunwa nake ji  banci Komai ba…Kai ciwo.   “To naji zo muje in  baki Abinci sai ki Sha magani. Ta fad’i haka Tana d’aga.sai a lokacin na k’are Mata kallo K’yakk’yawa ce Sosai Kuma ta Manyan ta Amma duk da haka bai Hana k’yawun ta fitowa ba.Amma ga dukkan Alamu bata da Hankali. Amma duk da haka bata da wani Mummunan Kama.  “A’a  Hajiya ke da Mutuniyar taki ce.?
  “Eh wallahi Habu,ka ganta Nan taje ta kwana waje ruwa ya bige ta ga Zazzabi ya kamata,jiya ni shaf na manta ruwa ya rud’ani na shige gida ban Mata shimfid’a cikin rumfa ba,gashi indai ban Mata shimfid’a sai dai ta kwana a waje Kuma a zaune,gashi kwata-kwata ba zata shiga gida ba,Ina tunanin ita Kuma kalar nata haukan kenan.
    “Allah ya yaye Mata,gaskiya Hajiya kina k’okari wannan Zamani Ina za’a samu kamar ki masu Taimako,tun da Baiwar Allah Nan tazo gurin Nan kike d’awainiya da ita.Allah ya biyaki ita Kuma ya Bayyana Yan uwan ta.
        “Ameen dai ya Allah 🙏.Kai ta rumfa tayi ta shiga gida ta dauko Mata Abinci da Paracetamol da kaya,da k’yar ta Bari a ka canja Mata kayan ta bata Abincin ta fara ci.tsayawa tayi Tana kallon ta cike da Tausayi da k’auna ita dai tun da taga yarinyar Nan Allah ya d’ora Mata Tausayi da K’aunar Yarinyar a cikin Zuciyar ta Kuma Tana ji a jikin ta akwai wani B’OYAYYIYAR K’ULLI   a tare da ita Kuma zata cigaba da Addu’a Allah ya Bayyana Mata wannan K’ullin.
*************************
LAGOS
“Kai Ashawo kana shanawa fa,Ina uwar sharrin naka.?Ina son zata mun wani aiki ne.
   “Kai dallah Shamo kyale Yar durun uba Wai ni zata kawo ma Bariki bacin ni na yaye ta a Barikin Nan.karamar Yar Tasha kawai yanzu na gama jibgan shegiya,Kama ta nayi da wani Shegen Inyamuri fa a d’akina tirmi da tabarya.shine kawai na K’addamar musu shine ta gudu.
      “Amma dai wallahi ta ban Mamaki Dan Maicin Uwan ta ai gara da ka jibgi shegiya.zama ta dawo tunda ai bata da kowa sai Kai.
   “Ba dolen ta ma ta dawo ba.jiran shegiya nakeyi yau in kwana huce Haushi na a kan ta.
“Shege Ashawo kaji dadin ka,ka Shana kawai Aljannan na mai rabo ne, mudai mun San ko uwar mu take rabawa ba dole ta bamu ba.
 Tafawa sukayi suna dariya,ya wuce Abinshi.shi Kuma yaci gaba da hura sigarin shi.
*************************
ZAZZAU BIRNIN SHEHU
Dawowan su Makaran ta kenan aka tsuge da ruwan Sama.
   “Zahra!!Zahra!! Mami ne take kwala ma Zahra Kira da taji shigowar su yanzu.
“Na’am Mami ganinan Zuwa Ina cire Uniform ne.da sauri ta k’arisa cire Uniform d’in ta Nufi d’akin Mami,tura kofan tayi had’i da Sallama.”Mami sannu da gida mun dawo.
“Yauwa sannun ku da dawowa,ga cefane can a Kitchen kije ki d’ora girki.kafin Nan ki samama Khausar Abunda zataci kin San dai bata jure Yunwa.tashi ki tafi Kuma kiyi ki gama karki tsaya wannan shiriritar naki har Yayan ku ya dawo baki gama ba.
    “To Mami,ta fad’i haka Tana Mik’ewa don Zuwa Kitchen din.haka ta tarar da kitchen din kaca-kaca ga kayan wanke-wanke tun na safe.haka ta fara gyara kitchen din sannan ta d’ora girkin ta Kama wanke-wanke kwanoni kafin Ruwan ya tausa.tana kammalawa ta je d’aki don yin Alwala tayi Sallah la’asar kafin ya dafu, dama ta riga ta kaima Khausar Comflesk.tana Zuwa ta ganta sai Barcin ta takeyi cikin kwanciyar Hankali don ko Uniform d’in bata cire ba.girgiza Kai tayi ta shige toilet ta d’auro Alwala ta fara Sallah.✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
More Comment more typing.

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements