BOYAYYIYAR KULLI Page 11 to 20 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / BOYAYYIYAR KULLI Page 11 to 20

BOYAYYIYAR KULLI Page 11 to 20

BOYAYYIYAR KULLI Page 11 to 20

ZAZZAU BIRNIN SHEHU

Khausar ne ta tashi Tana yamutsa fuska sakamakon wani Mummunan Mafarki da tayi.
“Twinny Lafiyan ki kuwa.? Ki tashi  kije ga ruwan wanka can na had’a Miki kiyi ki Alwala kizo kiyi Sallah ga Abincin ki Nan a dining.
Tashi tayi ba tare da tace Mata k’ala ba ta shige toilet.
Ita Kuma ta tashi ta fita don yi musu wankin Uniform kasancewar lokaci Damina ne shiyasa take so ta wanke da wuri Saboda ta samu su Sha iska kafin su tafi islamiya. Sai ta kwaso komai dare in sun dawo ita zata goge musu. a haka ma in Khausar najin wulakanci tace Wai Basu fita ba kayan ko Basu gogu ba.
Wanki ta keyi Tana muraji’an karatun Zadul muslimat don yau shi zasuyi, Kuma ustaz Hassan duka yakeyi duk wacce bata iya ba.kuma kusan kullum sai anyi daru da Khausar akan bata iya ba,Kuma ko tace tazo tayi Mata tilawa bazata zo ba sai dai ta d’auko wayar Mami tayi ta game.
*************************
Kwanci tashi ba wuya a gurin Ubangiji gashi yau su Khausar sun kammala Exam.sai farin ciki sukeyi sai dai ance baza’ayi taron Senth forth ba Saboda halin da kasa ke ciki game da rashin tsaro da kwanciyar Hankali.
“Mami yaushe Daddy zai dawo da Yaya Sadeeq .?
“Daddy ku ya tafi Abuja wani shari’a kuyi mishi Addu’a Allah ya basu sa’a.
“Insha Allah Mami ai mun San Daddy mu mai gaskya ne da Amana Kuma Allah Yana bayan mai gaskiya.ko Khausar.?
“Hakane Zahra.ni Mami fa na gaji da zaman gida ne, yauwa Mami Wai mai akayi ma Yaya ranar da zai tafi naga ran shi a b’ace.?
“Nima ban sani ba Khausar.shi da Daddy ku ne.ku tashi kuje kuyi Sallah Time d’in Sallah yayi.
*************************
LAGOS
Gudu takeyi na fitan hayyaci Amma Basu fasa binta ba kanta ba ko d’ankwali  kafar ta ba ko takalmi ta cikin kasuwa suka ratso.Abun da zai baka Mamaki ba Wanda yayi yunkurin taimakon ta sai dai ma ratsewa da akeyi ake bata hanya.ta gaji iya gajiya Amma bai sa ta fasa gudun ba,Kai daga gani kasan gudun ceton rai takeyi.dai dai zata fita daga cikin kasuwan ne cikin Wanda suke binta ya samata kafa ta fad’i Tim a kasa,Amma duk da haka kokarin yunkurawa take ta gudu.Amma Ina ta makara kafin ta tashi sun k’ariso sun zagaye ta kowa Yana hura hanci da ka kallesu kaga irin Manyan Inyamuran Nan marasa Imani.
  “Oga this girl na tired us Abeg let us kill stupid girl woo.
“No oya bring her to my House I wanna sleep with her. You Anybody like come do.
Sakin ihu tayi Tana musu magiya don Allah su rufa Mata Asiri, wlh bata yaudare shi ba guduwa mai da kud’i zatayi ba.Amma ko sauraran ta Basu Yi ba haka suka sab’a ta a kafad’a.tana ihu gwanin ban Tausayi.suna isa wani katon gida Wanda ko ta Ina a gidan Security ne gasu Nan birjik daga ganin idanun su ba alaman Imani a idanun su.wani d’aki a ka bud’e aka jefata a ciki,tun karfe Sha biyun Rana suke kanta gaba d’aya Security gidan in wannan yayi ya sauka sai wannan yayi,wasu ma a cikin su ta baya suke Amfani da ita tun Tana kuka har ta kasa gaba d’aya idon ta ya bushe haka makogwaran ta don komai Basu bata ta ci ba. a gaban suka ci Abinci suka dawo suka cigaba da sukuwa a kanta tamkar jaka ranar batayi tunani zata farka ta ganta da rai ba,don Suman ta bakwai suna yayyafa Mata ruwa in ta farko su cigaba.gaba d’aya jikin ta yayi weak Nan da Nan ta fara Nadaman shigowa Bariki ta fara tunanin yanzu in sun kashe ta sun kashe banza.bata da wani gata a matsayin ta na karuwa, ta tuna irin Abubuwan da ta aikata a baya tabbas bata tab’a nadama irin ta yau ba,In Allah yasa Tana da sauran Shan ruwa a duniya zataje ta warware B’OYAYYIYAR KULLI  da ta had’a sannan ta nemi yafiyan iyayen ta in suna raye.tana wannan tunanin ne taji wani abu ta duburan ta tamkar karfe shine har cikin cikin ta,bata gama jin wannan Azaban ba ta karajin wani ya shigeta ta gabanta ji tayi sun kwashe da dariya.tun daga Nan bata Kara sanin inda kanta yake ba.
“Hello Shamo kana jina wallahi har yanzu Uwar Sharri bata dawo ba yau kwana uku kenan,wallahi Abun yayi Matukar d’agamun Hankali kar yazo taje ta fad’a a hannun gang din Yan Yahoo ko Yan cult kasan Zaman Legos sai da ta ka tsantsan. Ok don Allah kayi sauri sai muje mu nemo ta.
*************************
JOS
“Hajiya akwai Sakwara.?
“Eh akwai Alhaji shiga Bari a kawo ma,komawa tayi tama wata yarinya magana taje ta kaima Alhaji Sakwara a falo.ta Amsa Mata,ta tafi domin Kai Mata can na hango Dije Tana zaune tayi shiru tana kallon kan titi.k’arisawa Hajiya tayi hannun ta d’auke da plate din Abinci.”yauwa Dije ga Abincin ki ci sai kizo in Miki wanka.karbe Abincin tayi.tana mai k’ale Mata kafada Alamun bata son wankan.
“Aiko sai kinyi wanka yau satin ki guda fa kenan bakiyi wanka ba. Turo baki tayi Tana hararan Hajiyar🙄.
“Duk ki gama yau sai kinyi wanka.ta fad’i haka Tana Mik’ewa taje ta cigaba da aikin ta.
*************************
Daddy ne ya shigo cikin gidan had’i da Sallama.
Da gudu Yan gidan duka suka fito suna murnan ganin Daddy.
“Alhaji shine baka sanar damu kana kan hanya ba.
Ina so in baku suprise ne.kuma gashi yanzu na baku ya fad’i haka Yana murmushi.zaunawa yayi yace My Beautiful babbies kuzo Nan in muku wani albishir. Da sauri suka k’arisa kusa da Daddy suka sashi a tsakiya.”oya duk ku rufe idon ku.bayan su rufe ni ya ciro musu wayan su sabbi a kwali kirar Infinix Smart 5 Aiko suka rungumeshi suna murna 💃💃.
“Dama Daddy Ina taso ince ka siya Mana Saboda duk freands din mu suna da phone Ashe ma Yana ran ka.inji Khausar.
“To yanzu dai gashi Nan na siyo muku gift d’ina kenan na graduation.sannan Kuma gashi na samo muku Admission ke Khausar za kiyi Al-kalam University Katsina,Ke Kuma Baby Zahra zakiyi Sky land University Kano murna Zahra ta fara ta kwararo ma Daddy Addu’a,sai ta ga Khausar ta bata rai ita da Mami,daddy shima ya lura da hakan sai yace musu “Hajiya lafiya ko bakiyi farin ciki bane.?
“No Daddy yara gani nayi gara a Kai Zahra Katsina tunda tadan fi Khausar wayo zata iya kula da kanta,Ita Kuma Khausar a dawo da ita Kano Saboda yafi kusa Kuma kaga Khausar Ba lafiya ta cika ba.
“To shikenan tunda Kinga hakan yafi.ke Zahra sai kiyi hakuri kije Katsina ita Kuma Khausar din taje Kanon.
“To Daddy indai hakan shine farin cikin Mami da Yar uwa ta na hakura Allah yasa hakan shine mafi alheri.da Ameeeen duka suka Amsa.kowa ya tashi yayin da Zahra kwata-kwata bataji dadin haka ba.✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
More Comment more typing ehee🙄🙄
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI 😭😭😭
STORY
         AND WRITTEN
                   BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B’OYAYYIYAR K’ULLI.
DEDICATED
         TO
Duk wani Masoyana da Wanda na sani da Wanda ban sani ba Ina son ku nima💖💖💖💖💖
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKEEL.
(School preparing)
PAGE 10
*************************
ZARIA
D’aki suka shige kowa taje ta jona wayar ta a chaji,a jikin bed d’in ta kasancewar kowacce kusa bed d’in ta akwai sucket.
Fita Zahra tayi don Zuwa Kitchen had’a musu Abincin dare,kasancewar Daddy na gida Kuma kar yayi Fad’a shine Khausar ma ta bita kitchen din suna aikin tare.duk da rabi da kwatan aikin Zahra keyi.bayan sun kammala ne suka jera a dining.Suka koma d’akin su don yin Sallah Magrib.
Kowa ya iso gurin cin Abinci,sun zauna suna cin Abinci.Bayan sun kammala ne suka koma falo suka Zauna a ka fara hira.
“Daddy yaushe zaka siyan Mana Mota.?
“Oh Khausar yaushe kuka isa hawa Mota ku Bari sai kun Kai 300L sai in siya muku,kin ga a lokacin Kuna da 22years kenan.
“Amma dai Daddin yara ya kamata ka siya musu ko guda d’aya ce su dunga sharing, Saboda a gidan Nan fa Motoci biyu ne fa daga naka sai na Sadeeq.kuma gaskya Mota biyu a gidan Nan sun Mana kad’an.
“Bari mu gani to bayan na gama musu registration.in har naga Ina da hali sai in siya musu.
“Yauwa Daddy Allah ya Kara bud’i.
“Ameeeen yaran Daddy nidai Abunda nake so daku please ku daure kuyi karatu Sosai kunji yara na.Zahra na Law zata karanta ke Kuma pathologist ko.? Kice gaba kad’an zaki canza ma Mamin ku fata😀. daddy ya karishe maganar Yana murmushi.Yanzu dai ku shirya gobe in Allah ya kaimu zan kaiku kuyi shopping d’in makaranta, da duk Abunda kuke bukata,kunga sai inji da registration din.
“To Daddy mun gode Allah ya ja kwana, ya Kara bud’i ya saka da Alheri.
“Ameeeen Yan Albarka.ku tashi kuje ku kwanta dare yayi.
“Mami gud night sweet dreams, daddy gud night sweet dreams too.
“Ok my children kar ku manta da Addu’a.
Washe gari……..
Kowacce ta had’a wayar ta,sun d’ora layin da Daddy ya siya musu har Kati ya sa musu da Numbers d’in Yan gidan, Number Shi da na Mami da na Hajiya Guggo.bayan sun had’a ne Zahra ta Kira Number Yayan nasu don tabbass tayi Missing d’in shi Sosai, ringing D’aya ya dauka kaman Yana jira.
“Hello dawa nake magana.? Jin muryan shi da tayi sai taji wani farin ciki da sanyi a ran ta sai taji duk wani damuwar da take ciki ya tafi Saboda jin muryan Yayan ta mai son ta mai share Mata hawaye daga shi sai Daddy take jin dadin su sai ko Guggo in tazo.
“Hello Wai dawa nake magana an kirani anyi shiru.
“My sweet heart Yaya.”ta fad’a muryan ta a sanyaye.
“What kind of surprised my baby.? Ya kike da fatan kina lafiya wannan phone din waye.?
“Kai Yaya duka wannan tanbayar ni kad’ai zan Amsa.”
“Sosai ma kuwa, Da fatan kina cikin koshin lafiya,ba Abun da ke damunki.? Da fatan Mami basa takura Miki.?
“A’a Yaya na, Wai yanzu kana inane.? Daddy ya siya Mana waya nida twince sister na,shine na Kira in fad’a maka.
“Baby please karki sake kiyi wani Chat in ba WhatsApp,Saboda ban son ki koyi shirme da hauka, karki bama kowa Number ki.kinji ko my Baby. I miss you too baby ki kulamun da kanki kinji karki fad’a ma su Daddy munyi waya,har da twince sister naki.
“To Yaya insha Allah bazan fad’a musu ba.I love you too my Yaya.tana fad’in haka ta kashe wayar Tana mai rufe ido,murmushi d’auke a fuskar ta.
*************************
MAIDUGURi
“Haba Yagana kin San tsawon lokacin Dana d’auka Ina fatan Samun ciki a gidan Nan sannan kice mun Wai in Zubar,to Bari kiji ni har na tura ma Alhaji Text ma Ina d’auke da juna biyu,tun a wayar ya bani kyautar Motar shi da duk Nigeria shine na biyu a hawa irin ta.ina ga na haifi yaron ko Yarinyar.kai wallahi bazan iya zubarwa ba, to Yagana maganar Boka maganar Allah ce,ni Kinga ma kashe wayata zanyi in har bazaki mun maganar arziki ba.kit ta kashe wayar ta tayi cilli dashi kan kujerar dake falon.
Safa da marwa ta farayi Tana zagaye Falon.wata Dattijuwan Mata ne ta shigo d’auke da wani Dan karamin faranti d’auke da karamin Cup cike da Madara mai sanyi, tazo ta duk’a a gaban ta had’i da sunkuyar da Kai.
“Ranki ya dad’e lokacin Shan Madarar ki tayi.bata Gama rufe baki ba ta d’auke ta da Mari had’i da fad’in,
“Dallah Fice mun a Nan waya fad’i Miki Ina bukatar kowa kusa da ni a yanzu.madarar ta d’auka ta juye Mata a fuska had’i da jefar da kofin ya fashe,ta juya a fusace ta shige bedroom.”kar in fito Kuma inga datti a gurin nan.ta fad’i haka tana mai bugo kofa.
Girgiza Kai tsohuwar tayi Wanda a haife ta haife ta Amma tayi Mata wannan tijarar.haka ta tashi jiki sanyaye ta fita don kwaso Abun da zata gyara gurin kafin ta dawo tayi Mata wani cin Mutuncin.
************************
LAGOS
Lungu da sako duk inda suka San zasu ganta sun duba Basu ganta ba. Hankalin Shamo gaba d’aya ya tashi.
Bayan sunyi Mata fata fata ne.washe gari da Safe suka fita suka jefar da ita a saman gada,ko suturar  arziki babu a jikin ta.Kowa yazo sai dai ya wuce abinshi don irin haka ba sabon Abu bane a Lagos,in har ka kalle ta baza kaso ka k’ara kallon ta ba.don tamkar Matacciya. Shamo ne suka zo wucewa har sun gota suka dawo baya.
  “Kai Mutumina kamar Uwar sharri fa nake gani kwance.
“Kai Ina ba ita bane, mai zai kawo ta Nan.
“Kai kwarankwatsa itace saboda wannan kayan tasa randa muka rabu da ita.
Haka suka k’arisa kasancewar gari ya fara duhu a lokacin sai suka kunna toch light din wayar su.
“Innalillahi Aradun Allah itace ,haka suka ciccibeta sukayi shatan taxi sai gida✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
More Comment more typing ehee 🙄🙄
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYIYAR
                 K’ULLI😭😭😭
STORY
         AND WRITING
                  BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
YA HAYYU YA K’AYYIM
PAGE 12
Kwanci tashi bai da wuya
 a gurin Ubangiji yau gashi watan su Zahra uku a school.  Inda Mami har ta gaji da kewan Yan matan nata ta hakura. Gashi yanzu Daddy sai k’arshen sati yake dawowa yayi kwana biyu ya koma,Saboda wani shari’a da suke ta fafatawa. Sadeeq ko tunda ya tafi Abuja Neman aiki ya samu aiki a gidan shugaban k’asa Wanda a ka bashi matsayin mai yad’a labarai na gidan gwamnati gaba d’aya. Sannan Yana fushi da su Daddy a kan maganar Zahra, don shi Yana tunanin sun b’oye mai wani abu ne, hakan yasa yak’i dawowa gidan, a kan cewa har sai sun sakko sun Bayyana Boyayyiyar K’ulli da suke B’oyewa zai dawo.
Wata rana ne da ya zame ma su Mami ranar Bak’in ciki Wanda baza su tab’a mance ranar ba. Ranar da suka rasa Hajiya Guggo sakamakon gajeruwan jinya da tayi. Cikin dare jikin nata yayi tsanani Sosai ga Daddy ga Mami suna zaune a gefen ta a Asibiti A.B.U  Shika, da k’yar ta daga Kai ta dubi Daddy tace mai….”Habibullahi Ina ji a jiki na bazan tashi ba, naso a ce kafin in Mutu naga Abubakar Sadeeq domin in Mallaka mishi Abun da ya ke so, duk da cewan ban so hakan ta faru ba Amma Ina ji a jikina sai K’ullin da muke b’oye musu ya Bayyana duk daren dad’ewa. Saboda haka ko bayan Raina ku Aura ma Sadeeq Zahra.
“Don Allah Hajiya ki dai na fad’in haka Zaki tashi insha Allah, in har kika mutu wa nake dashi kuma.? Na rasa Dan uwa na mafi soyuwa a rai na a lokacin da nake buk’atar shi, kema kina Neman ki tafi ki barni.
“Kayi hakuri Habibullahi mutuwa dole ce, nasan ko yanzu Ubangiji ya d’auki rai na nasan b’uri na ya cika, na baka tarbiya Kai da D’an uwan ka na baku ingantaccen ilimi ka mallaki komai a yanzu.k’asa k’arisa maganar tayi Saboda tarin da ya sark’e Mata wuya.Kalman shahada ta farayi, bata d’au dogon lokaci ba rai yayi halinsa murmushi kwance a fuskar ta.  Fad”in tashin hankalin da Daddy ya shiga ma b’ata lokaci ne.
Washe gari su Zahra suka iso ita da Khausar. Sun ci kuka kaman ba gobe karma Zahra taji gashi sun nemi Number Sadeeq Basu samu ba kwata-kwata. Haka gida ya cika yawanci Yan uwa da Abokan Arzik’i  ne Saboda kowa ya San Hajiya Guggo Mace ne mai Tausayi da mutunci.
*************************
JOS
Tun safe yau Ciwon Dija yayi tsanani, don k’okarin guduwa ta dunga yi, Sai fisge-fisge takeyi. Maza ne da yawa suka rirrik’eta. Ba Abun da Hajiya Hauwa takeyi in Banda kuka 😭 Saboda Tana matuk’ar tausayawa Dijah Halin da take ciki.
*************************
MAIDUGURI
Tafiya sukeyi a cikin wani taxi, Ashawo ne rungume da Uwar sharri da ta Zama daga kallo sai kallo ko Zama batayi, dai dai wani maraba a ka kawo su, mai taxi d’in ya sauke su, Wani mutumi ya tayashi suka kamo ta suna Mata sannu suka shimfid’e ta, kafin su samu A kori-kuran da zai Kai su cikin k’auyen Ashawo sai tsaki yakeyi.
Sai Can Yamma suka samu Motan da zai k’arisa dasu Cikin K’auyen.
*************************
ZARIA
Anyi bakwai kowa ya watse  Su Zahra ma sun koma Makaranta. Inda har lokacin ba’a samu Number Sadeeq ba.
Bayan Wata d’aya
Daddy ne Zaune a D’akin shi Yana Had’a wasu takardu  a cikin wani akwati, Wasu hotuna ya D’auko da wasu Fararen Abu mulmulallu farare tas dasu sai d’aukar ido sukeyi a k’ulle a wani leda da yawa shima ya saka a Akwatin. Bayan duk ya birkice D’akin nashi ya had’a komai,. Wani k’aramin akwati ya k’ara D’auko wa ya zuba wasu takardu a ciki, ya maida ya k’ulle su duka ya ajiye a gefe. Wayarshi ya jawo ya cire Security Transfer kud’i yayi ma Sadeeq  a Account d’in shi na miliyan Ashirin. Sannan yayi ma su Zahra na Miliyan goma-goma. Sannan ya kashe wayar shi ya kwanta.✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍
BOYAYYIYAR
                 K’ULLI😭😭😭
STORY
         AND WRITING
                    BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISSMILLAHI RAHMANIR RAHEEM.
ALLAHUMMA INNI AUZUBIKA MINAN NARR.
PAGE  11
*************************
LAGOS
“dole in d’auki Uwar
 sharri gobe in koma da ita k’auyen su,don ni bazan taba iya jinyar ta ba Ina naga kud’in da zanyi jinyar ta, duba fa ka gani ta bayan ta har hanji ne ke lekowa.Kalli gaban ta kamar kofar d’aki Ina Kuma take da sauran wani Anfani yanzu,kawai zan maida ta garin su a hakan ma ai nayi k’okari ko ya ka gani Shamo.?
“Gaskya kam Ashawo tunda dama Bariki ai da mai Anfani akeyi, daga lokacin da mutum ya zama haka ai bai da sauran Amfani.Kawai ka maida ta ai ka Mata ma halarci.
*************************
ZARIA
Dawowan su kenan daga shopping su da Daddy. Mai gadi ne ya dunga shigo da kayayyakin da suka siyo. Mami ne ta fito daga D’aki  “Daddy Yara kun dawo sannun ku da dawowa.
“Yauwa Mamin Yara dama gobe insha Allah nake so Mukai Zahra makaranta,tun da na riga na kammala Mata komai.
“To ita Kuma Khausar fa sai yaushe zata tafi,? Ko ita ba’a kammala Mata registration d’in bane.?
Ta fad’i haka Tana yamutsa fuska.
“Haba Mamin Yara Wai ya kike haka ne naga da Zahra da Khausar duk d’aya suke,Kuma ke kika haife su,ni bana son Abunda kikeyi din Nan. Naga Zahra garin da za’a kaita makarantar Nan yafi na Khausar nisa yakamata dukan mu harda Khausar din mu Rakata muga gurin da zata zauna, sai mu dawo Mukai Khausar Koh. Amma bana bukatan irin haka zai jawo mun rabuwan kan yarana Kuma kin San duk duniya bacin Mahaifiya ta Ba Wanda nake so Sama dasu.
“Kayi hakuri Alhaji insha Allah na Bari bazan sake ba, gobe da wuri Zamu fita.?
“Yauwa Uwar gida ta insha Allah karfe takwas zamu fita ki fad’a musu su shirya da wuri.kin san yaran naki akwai shiriri ta.ya karishe maganar Yana shigewa d’aki.
Tsaki Mami tayi had’i da yamutsa fuska. “Aikin ka kenan kullum kar a raba maka kan Yara, sai kace a kanshi a ka fara yara.ni wallahi hakurina ya kusa Zuwa k’arshe a kan tijaran da kake mun a kan Yara.dole in d’auki mataki a kanka kuwa.ta karishe fad’in haka Tana wucewa d’aki itama.
*************************
MAIDUGURI
Tafiya sukayi Sosai a kafa, tunda sun bar motan su a bakin hanya.  “Wallahi Yagana kafafuwa na sun gaji fa.”
“Wai Bintu yau muka fara Zuwa gurin nan, duk kin dameni haba don Allah duk Abun Nan da nakeyi a kanki ne fa, ba don Boka ba kin San ko Kallo baki ishe  Bukar ba.
A haka dai har suka isa gurin bukkan bokan da shi kad’ai ne a dokan Daji.
“An gaida Boka Duna mugun Boka, ka kashe ka haukatar kasa anbi duniya,ka raba d’a da mahaifi,ka raba y’a da uwa.
“Angai da fara mai bak’in Zuciya, ai nayi tunanin bazaki zo ba.
“Ai dole ne in Amsa Kiran Duna.  Boka gata na kawo maka ita kayi Mata bayani da kan ka.
“Hhhhhhhh!!! Tabbas kin kyauta da kika kawo ta, ke Bintu ki sani cewa shekara ta Hamsin Ina wannan harkan,ba Wanda ya tab’a mun gardama sai ke, ki sani wannan cikin nake dole sai an ba Aljani mai gizo yasha jininshi sannan aikin mu zai cigaba da tafiya,in har mai gizo bai Sha jinin shi ba komai zai iya faruwa don duk wani Boyayyiyar K’ulli sai ya warware.ku tashi ku bani guri. Ku dakata ku dakata. Dole ki bar Sallah in cikin ki ya Kai wata takwas, Saboda a lokacin   Aljani mai kitso zai zo ya shanye cikin, Kuma kidai na jin karatun kur’ani, kar Kuma ki ajiye kur’ani a d’akin ki.ku tashi ku bani guri da fatan zaku kiyaye Abunda nace muku.
“Eh! Eh! Boka zamu kiyaye.
*************************
Duk sun fito kowa yayi Shirin tafiya, Daddy kawai suke jira ya fito.sai gashi ya fito. Dama komai ya kammala tafiya kawai ya rage musu.
Sun Kama hanyar Katsina. Suna tafe daddy Yana ta ma yaran nashi Nasiha, Sosai Nasihan ya ratsasu tun daga Mota suka rumgume juna ita da Khausar suna kuka mai Tsuma zuciya,har Mami sai da tayi kwalla taji Tana kewar yaran nata. Karfe Sha d’aya suka isa Cikin garin Katsina, bayan sun shiga Makaranta D’aki guda Daddy ya Kama ma Zahra a hostel komai an sa Mata a D’akin har da kayan kallo, Haka Khausar ta taya ta suka shirya komai a kitchen d’in ta da ke d’akin, bayan sun kammala suka fito da Abincin da Mami tayi musu tun daga gida suka ci, har dambun Nama Mami tayi ma su Zahra Kuma Daddy yaji dadin haka Sosai. Sukayi sallar Azahar suka fito don su tafi, Aiko Zahra taje ta rungume Mami Tana kuka, Khausar ma Zuwa tayi ta rungume su, duk da bawani shiri sukeyi ba Amma wannan shine karo na farko a rayuwan su da bazasu kwana guri d’aya ba.sai da Daddy ya zare su ya sasu a Mota sannan suka rabu.ya Kuma lallashi Zahra ya Kara Mata Nasiha. Sannan suka tafi ita Kuma ta koma Hostel.
Sun koma gida ana Kiran sallar Magriba.sai da dare Yayi taje kwanciya Nan ta Kara kewar Yar Uwar tata, waya ta d’auka kaman zata kirata sai Kuma tayi tsaki ta jefar da wayan.ta juya kwanciya.
Washe gari haka su Daddy suka Kai Khausar Makaran ta Kano. Tunda Mami ta dawo taji gidan ya Mata fad’i gashi ranar Daddy ya koma Kaduna.
Kenan haka zata kasance in ta Aurar da yaran nata.✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Like
Comments
Wlh Rashin Comments din ku shi ke sani kasalan yin muku typing.Amma da Ina ganin Comments kacha kacha wlh kullum zaku dunga ganin posting.in kun gyara in gyara Ehe🙄🥴
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰💖💖💖.
BOYAYYIYAR
              K’ULLI😭😭😭
STORY
        AND WRITING
                  BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
LAA YUKALLIFUL LAAHU NAFSAAN ILLAAH HUS’AHAA.
PAGE  13
Da Asuba Dadddy ya d’auki wad’an Nan akwati Nan ya sasu a Mota, Yana fitowa Masallaci sallar Asuba, Ya Kama hanyar Katsina.  Karfe takwas na Safe Daddy ya isa Katsina direct School d’in su Zahra ya wuce,ya kirata, bugu d’aya ta D’auka lokacin ta fito wanka kenan Tana Shirin Zuwa aji, Saboda suna da aji karfe Tara na safe.
“Assalamu alaikum Daddy Ina kwana, da gaske daddy kana makarantar mu to ganinan fitowa shaf-shaf ta sa Kaya ta shirya ta fita bakin hostel.
Tun daga Nesa yake kallon ta cike da tausayawa  Saboda bai San wani irin rayuwa zata shiga ba in bashi a raye, gashi yanaji a jikin shi tamkar ya kusa barin iyalan shi, Kuma duk ciki yafi son Zahra Saboda hakurin ta, Yasan duk irin musgunawan da Mami takeyi Mata, kawai dai Yana kau da Kai ne.  Har ta k’ariso bai sani ba ya shiga duniyar tunani.
“Daddy lafiya kuwa Ina ta Sallama kayi shiru,? Kuma na ganka duk cikin damuwa.?
“Lafiya lau Zahra jiya kin ga Alert Koh.?
“Eh Daddy na gani, Allah ya k’ara bud’i yaja kwana daddyn mu, Yauwa Daddy Wai har yanzu ba’a samu Number Yaya Sadeeq d’in ba.?
“Ameen ya Allah baby Zahra, Allah ya Albarka ci rayuwan ku duk in da kuke, Har yanzu ba’a Samu wayar Yayan ku ba, Nasan ya kashe ne Saboda Yana fushi dani. Bud’e boot d’in Motar shi yayi ya fito da Akwati babba guda d’aya ya mik’a Mata. “Fatimatu Zahra. Da sauri Zahra ta d’ago Kai don tasan in dai Daddy ya Kira ta da wannan sunan magana mai Muhimmaci zai Mata.
“Na’am Daddy.”
“Wannan akwatin da kike gani, Abubuwa ne Masu Matukar Mahimmaci a rayuwarki da na Yayan ku, na kasa yarda da kowa Wanda zan Damk’a mai wannan Akwatin sai ke, Ciki kuwa har da Mahaifiyar ku na k’asa yarda da ita,  Ina so ki tabbatar kin samu guri mai Muhimmaci kin Adana shi Amma Banda gida, don bana buk’atar inda Akwatin Nan ya fito gida ya koma,don babban Had’ari ne zaman shi a gida.  Sannan Ina so karki tab’a bud’e Akwatin Nan har sai Labarin mutuwa ta ya riskeki.yana Gama fad’in Haka ya shige Mota ya tafi.
Kuka Zahra ta fashe dashi duk jikin ta yayi Sanyi da kalaman Daddy sai Tana ganin tamkar  bankwana yake Mata.  Dafata taji anyi ta baya da sauri ta waigo, ganin Ruk’ayya ce da sauri ta rungume Ruk’ayya Tana kuka, Haka Ruk’ayya ta ja ta da Akwatin suka shige hostel.
Dadddy bai tsaya ko Ina ba sai Kano. Direct Makarantar su Khausar yaje. Ya dunga Kiran wayar ta bata d’auka ba sai ya fara tunanin ko Tana Class ne, wani Abokin shi ya Kira da yake lecturing a school, Cewan Yana Neman Khausar Habibullahi Zaria, yace zai sa a duba mai ita Wasa-wasa sai da Daddy yakai karfe biyar na Yamma ba’a ga Khausar ba, Kuma har Class d’in su anje ga Yan Class d’in Nan ma suna Lecture Amma ita ba ta Nan, Abun yayi Matukar ba Daddy Mamaki.  Haka ya shiga Motar shi Yana Shirin tafiya sai ya hango Khausar an sauke ta a Mota tasa wasu matsiyatan Kaya harda Attarch kamar ba y’ar Musulma ba. Jiri ne yaji Yana Shirin d’iban shi, me  hakan ke Nufi tarihi zata mai-maita kanta kenan. Ina tarbiyan da ya ba su Khausar, Tun daga Nesa Khausar ta Hangi Daddy yana jingine da Motar shi, gaban ta ne ya fad’i don tasan Daddy bai iya fushi ba.
“Daddy Sannu da Zuwa Amm amm dama ban dad’e dama fita ba na d’an je Neman wani Book ne gashi ma ban samu ba.
“Dakata Khausar d’auki Akwatin can ki bar gurin Nan kafin Rai na ya Gama Baci dake.  In kin so ki Adana in kin so ki wulak’antar.yana Gama Fad’in haka ya shige Mota Abin shi.  Gaba d’aya Khausar ta shiga Damuwa don ta San shirun Daddy ba Alheri ba ne, Zai iya Zuwa ya k’are a kan Mami.  Haka dai jiki a sanyaye ta d’au Akwatin ta shige Hostel.
*************************
MAIDUGURI
Zaune takeyi a Falo ta zabga tagumi gaba d’aya Abun duniya ya dame ta.
“Ranki ya dad’e na gama Had’a Miki ruwan wankar .  Hannu kawai ta  d’aga Mata, ta fahimci  me take nufi,  sum sum ta wuce Abun ta, Tana mamakin me ke damun Uwar d’akin nata kwana biyu.
*************************
Da tambaya tambaya har Ashawo ya isa gidan su Uwar Sharri, lokacin dare yayi Sosai karfe Tara na dare. Wani Tsoho ne ya fito jin irin Sallaman da ake ta rafkawa.  “Lafiya Mallam daga ina.?
“Yauwa Baba don Allah Nan ne gidan Mallam Tsalha.?
“Eh yaro Nan ne, nine ma Mallam Tsalha.
“Ok to ko ka San wannan.? Yana mai Nuna mai Uwar Sharri.
Jiki na rawa tsohon Nan ya fara Nuna Uwar sharri da Hannu jikin shi na rawa….”Asabe kece a Haka.?  Asabe Kinga inda duniya take bida Mutum Koh.!! Fashewa yayi da wani kuka Mai cin Rai, Yana juyawa gida da sauri Yana k’wala Kiran “Tasallah fito ga Asabe.
************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
Tunda Daddy ya dawo gida ya shiga Damuwa Sosai ganin Halin da ya ga Khausar a ciki, ga Shari’an da sukeyi gaba d’aya a sark’ak’e yake, jiya dai da yaje Kano ya Kara tattaro wasu shaidun da Yana gabatar dasu anzo k’arshen Shari’ar. Ciki kuwa har da wani USB Camera da wani Recording. Duk Daddy ya gama tattara komai ya Zuba su brief case d’in shi Yana jiran gobe in Allah ya kaimu yaje ya gabatar dasu a gaban kotu.
Karfe  D’ayan Dare  1:00AM
Dare ya tsala ba Abun da akeji sai harbe-harbe, Daddy ne ya Mik’e firgigit.  Mami ne ita ma ta tashi tun lokacin da ta fara jin harbe-harben. K’aran ihun mai gadi suka ji, Basu Gama jimami ba sukaji an bankad’o kofar Falon…✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Like
Comments
More Comment more typing
Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍😍
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B’OYAYYAR
               K’ULLI 😭😭😭
STORY
       AND WRITING
                 BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
ALHMDULILLAHI NA GODE ALLAH DA YA BANI IKON DAWOWA DON CIGABA MUKU DA LITTAFINA MAI SUNA A SAMA. ABUNDA YASA KUKA JINI SHIRU MUNYI WALIMA SAUKA NE NA ISLAMIYA.
INA SON KU FANS💖💖💞💞
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
WAMAN YATAWAK KAL ALAL LAH FA HUWA HASBUN
PAGE 14
Daddy da sauri ya Mike zai fita, Mami tayi sauri ta rik’o shi. “Don Allah Daddy Yara kar ka fita.  Bata Gama rufe baki suka bankad’o kofar, wasu Manyan mutane ne gwanin ban tsoro sun rufe fuskokin su da mask suka shigo d’akin hannun su d’auke da Manyan bindigogi.  Sai da suka k’are ma d’akin kallo tukun na suka ce. “Barisster Habibullahi Sadeeq Koh.?  Wato Kai Mai gaskiya Koh…? Ka tashi ka D’auko Mana CD da wad’an Nan takardun da ke hanun ka, ko yanzu ka gangara lahira.
“Don Allah..! Kar ku kashe shi zai baku. Dadddy Yara don Allah ka basu. Mami ta fad’i haka cike da rud’ewa.  “Gaskiya bazan tab’a iya bayarwa ba sai dai ku kashe ni. Daddy ya fad’a cike da kwarin gwiwa.
Bai gama rufe baki ba suka rufeshi da duka da kasan bindigan su, sai da suka tabbatar ya ji jiki suka Kara tanbayar shi. “Zaka fad’a Mana ko bazaka fad’a ba.?  Suka fad’i haka cikin tsawa.
“Don Allah Daddyn Yara ka basu mu huta.
Ogan ne Yana yaran shi umarnin suje su bincika Mai gidan ko Ina da ko Ina. Suna cikin Haka ne suka fara jin jiniyar Yan Sanda, Aiko ogan nasu ya ba daddy wani duka a Kai da K’asar bindigan su tuni Daddy ya sume. Haka suka Fice a gidan a guje, Nan aka fara musayar Wuta da Yan Sanda, da k’yar suka samu suka gudu. Nan da nan aka fito da Daddy aka tafi dashi babban Asibiti A.B.U. .
Mami taci kuka tun dare ta sanar da su Zahra, Asuba ya musu a cikin Zaria ne Haka suka had’u suna ta kuka. Suna cikin wannan halin ne sai ga likita ya fito yace musu, “zaku iya shiga ku ganshi Amma karku dame shi da surutu, Haka sukayi rige-rigen shiga D’akin.
 “Sannu Daddy. Kawai binsu yayi da kallo Yana hawaye. “Ku matso kusa Dani Yara na. Laure kema ki k’ariso, Laure Abunda na dade Ina B’oyewa shekara da shekaru sai ya Bayyana, Tabbas mutuwa Mai tonon Asiri, Ni na san bazan tashi ba. Amma don Allah ki cika ma Hajiya Guggo wasiyyar ta na had’a Auren Zahra da Sadeeq. Da sauri su Zahra suka d’ago suna kallon Daddy fuskan su cike da alamar tanbaya. Tabbas ba ciki d’aya kuka fito da Sadeeq ba, Mahaifiyar ku zata baku Labarin wata Rana. Tari ne ya sark’e Daddy ya fara yi, can sai ya fara Aman jini had’i da kalmatush shahada. Nan Daddy yace ga duniyar ku Nan.
Ihu Zahra ta saka Tana girgiza gawar Daddy, Nan da Nan  likitoci su shiga Aune-Aune suka tabbatar da Rasuwar shi sannan suka Mika musu gawar shi. Haka suka dawo gida. Tun a Mota Zahra ke gwada Number Yaya Sadeeq da k’yar ya shiga.
“Hello Baby kiyi hakuri wlh wata yafiyar gaggawa ta taso mun Zuwa India sai jiya na dawo. Yasu Mami da Daddy, da Yar tsohuwa ta. Fashewa tayi da kuka.”Yaya kazo gida ba lafiya. “Zahraty Lafiya me ya faru.? Ya fad’i Haka cikin rud’ewa. Khausar ne ta fige wayar tace mai “to ai sai ka dawo gida Daddy ya rasu.  “What! Daddy ya rasu fa kika ce.? Ya fad’a a rud’e.
Cikin sauri yayi waya yace ayi mishi booking na flight da zai kaishi kaduna yanzu-yanzu. Cikin mintoci aka Gama komai ya Kama hanyar Kaduna.
Ya iso gida yazo ya tarar da gida a cike tun daga kofar gida har cikin gida, kawai ya yanke jiki ya fad’i.✍️✍️✍️
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍
Well come back na dawo insha Allah da Zafi na👊👊👊
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 15
*************************
Haka aka d’auki Sadeeq aka shiga dashi ciki Ana mishi fifita, Nan aka Kira family doctor d’in su. Bayan ya iso ne yayi Mai gwaje-gwaje da Allurai, yace su barshi ya huta Saboda jinin shi ya hau sosai. Zahra ce ta zauna dashi, yayin da Khausar ta d’ukufa bincike a D’akin Daddy,wani Deary ta gani a D’akin Daddy cikin wani karamar kit Yana ta d’aukan ido. Jikin ta na rawa ta bud’e Deary ta fara karan tawa, wani zufa ne ya fara keto Mata   jikin ta har rawa yakeyi, Dama Sirri da Mami take cewa sai ta tona kenan, ta shiga uku ita Khausar indai haka ne to ba Wanda ya can-canci Auren Yaya Sadeeq sai ita. “Wallahi indai Ina raye ni Zan Auri Yaya Sadeeq, Zama tayi a gefen gadon Daddy tamkar Wanda take tunanin wani Abu. Zunbur tayi ta mik’e ta fita, d’akin su ta shiga ta fara kaiwa da dawowa.
 Zaune suke a Falo kowa shiru-shiru  Mami ne taga fitowan Khausar daga d’akin daddy, da sauri ta tashi ta bita Zuwa d’akin su. Ko Sallama ba tayi ba, tace “ke Khausar me kikaje yi d’akin daddy ku.?  Tanbayar a bazata tazo ma Khausar. “Wai dama Mami Abunda kuka Dade Kuna b’oye Mana kenan.?  Ta jefa Mami da wannan tanbayar. Jikin Mami ne ya fara rawa,  “Zo Khausar fad’a mun me kika gani,? Kwashe duk Abun da ta gani a deary d’akin Daddy tayi ta fad’a ma Mami, Murmushi Mami tayi tace Mata”Alhmdulillahi Khausar tun da kin riga Kinga Abunda muka dad’e muna b’oye muku, yanzu kin sani Saboda Haka nake so in sanar dake cewa Sadeeq baida wata Matar Aure sai ke. Da sauri ta rungume Mami Tana mai jin wani farin ciki a Zuciyar ta don ita yanzu tun da taga wannan Deary d’in take da wani Manufa a Zuciyar Wanda b’oyayyiyar sirrin ta ne.ko Mami ma bazata sani ba, Haka suka rabu kowa da nashi kud’irin a Zuciyar shi.
KAUYEN ZULUM
Kuka Sosai Asabe takeyi Tana rokon baba Tsalha da Inna Tasallah akan su yafe Mata, “Inna tabbas Bariki ba riba, don ban kwashi komai a ciki ba sai tarin nadama. Allah na tuba  Innah Ina so naje in warware sharrin da nayi domin Ina ji a jiki na shi ke bibiyata. “Wai Asabe sumbatun me ki keyi Haka ne.?  Wani sharri ne Zaki warware kina kwance Rai a hanun Ubangiji. “Innah Ina ajiya ta.?  “Ajiyar ki na gurin Yar Uwar ki.
*************************
MAIDUGURI
Ta Kama yau Alhaji Bukar Mai Naira ya shigo cikin garin Maiduguri, in da ya sauka cikin farin ciki da Nishad’i don ya kosa ya isa gida don ya ga cikin Bintu, don har ya cire Rai zai Haihu a duniya.
Da gudu Bintu ta fito taci Ado da wani rantsattsen Lafaya ta nad’a shi ta fito a Kanurin Asali, Dan cikin ta ya fito yayi Mata das a gaba. Rungume Alhaji tayi ta na Mai sannu da Zuwa.  Bayan ta taimaka Mai yayi wanka ya shirya suka fito falo ya zauna don cin Abinci, Yana ci Tana zuba Mai shagwaba tare da kisisinar ta. Bayan sun Gama ne sun koma falo suna zaune, Alhaji yace….”Bintu ki fad’i duk Abunda kike so tukuicin farin ciki da kika sani a yau, gaskiya nayi farin ciki da cikin nan. Dole za’a Nemo Doctor da zata cigaba da kula da cikin don ban son Abun da zai sameshi Allah ya sa ki haifi Mace in sama Mata Fad’imatuz Zahra sunan Mahaifiya ta. Murmushi Bintu tayi had’i da kashe murya da k’ara shagwabe fuska, “Alhaji ni gidan gonan ka na Borno nake so ka bani. “An gama Uwargida ran gida daga ke ba wata. Wani farin ciki ne ya lullube Bintu…
*************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
“Sannu Yaya Sadeeq, ya jikin naka yanzu.?   “Naji sauki Zahraty shikenan Daddy ya tafi ya barmu a wannan duniyar, Cikin garari, yanzu ba mu da kowa sai Mami da Yan uwan ta gashi har yanzu Mami taki Bari mu San Family d’in ta, ko zuwa zatayi sai dai ta tafi ita kad’ai Kuma su Basu cika Zuwa Nan ba, shi Kuma Daddy dama su Uku Hajiya ta Haifesu kamar yadda ya haifemu. Sai dai su biyu Maza ne Mace d’aya Asalin su Yan Maiduguri ne wani Hari da Boko Haram suka Kai ne yasa suka dawo Nan da k’yar in da Yar Autan su Daddy ta b’ace ba’a ganta ba har yau. Ya k’arishe maganar Yana share Hawaye. Zahraty yanzu kece Matsala ta, don nasan Mami ta tsaneki daddy ne ke dakatar da ita Amma zanyi iyakan k’okari na na ganin na baki farin ciki.
Yau ta Kama sati biyu kenan da Rasuwar Daddy inda Mami ta Tara yaran nata domin yin musu bayani Abunda Daddy yace, sai dai ta canza nata.
*************************
JOS
 “Tabbas Hajiya wannan yarinyar Tana tare da Sihiri Mai karfi a jikin ta, Wanda kafin a karya shi za’a Sha bakar wahala. Amma insha Allah zamuyi Anfani da Ayayoyi karya Sihiri da sauran Magungunar da suka dace sai dai Zaki barta anan har sai mun Gama Mata duk Abun da ya dace. “Shikenan Mallam ba damuwa Allah ya taimake mu ya bamu sa’a…….✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
Vote
Insha Allah Zeey Yar mutan Zazzau ta dawo da karfin ta comments din ku shine karfin gwiwa ta Ina son ku fans🥰🥰🥰🥰
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍💖🥰
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Yanzu aka fara wasan kudai kawai ku cigaba da bin Yar mutan Zazzau.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 16
*************************
“Abun da yasa na Tara  ku Anan shine Sadeeq zaka Auri Khausar. Da sauri suka d’ago fuska suna kallon Mami cikin Mamaki, Banda Khausar da ta cigaba da Danna wayar ta. Ko ta d’ago Saboda ta riga ta San komai. “Mami bamu gane me kike Nufi ba ki Mana bayani Taya Zan Auri Khausar Tana k’anwa ta.?
“Haka Daddy ku ya bar wasiyya Saboda Khausar da Zahraty ba ni na Haifesu ba. Sadeeq kai kadai na Haifa Su Zahra D’auko su nayi a gidan Marayu ni da Daddy ku. Kuka Sosai Zahra takeyi yayin da take jin wani Soyayyan Yayan nasu Yana ratsa ta,  meyasa to Mami tafi son Khausar a kan ta. “Mami in dai Haka ne to ni Zahra nake so ba Khausar ba. Da sauri Zahra da Khausar suka d’ago kan su a tare, suna kallon Sadeeq d’in. Fashewa da kuka Khausar tayi ta rungume Mami, “Wai me nayi ma ka Yaya Sadeeq ka tsaneni, meyasa kafi son Zahra a Kai na da Mai Zahra ta fini eyeh!.?
“Bari kaji Sadeeq in dai ni na haife ka baka da Matar da ta wuce Zahra ita zaka Aura Dole kaji na gama magana. Ta tashi ta Basu guri.  Khausar ne ta Mike ta yima  Zahra wani wulak’antaccen kallo sannan taja tsaki tayi gaba. Sadeeq ne ya jawo jikin shi ya iso gurin da Zahra take zaune, da tunda aka fara maganar Bata ce komai ba sai kuka da take yi. Don ta dad’e da ji a ranta dama Bata da gata Daddy ne da Yaya Sadeeq gatan ta, Bata tab’a tunanin ta kamu da Soyayyar Yaya Sadeeq ba sai yau. “Zahraty kiyi hakuri ki dai na kuka duk runtsi duk wuya bazan Auri Khausar ba ke Zan Aura.”
“Ka dai na Fad’in haka Yaya, kabi Maganar da Mami tace don yi Mata biyayya, ni Zan iya hakura da Abun da nake so don farin ciki Twinie na, har yanzu Ina son Khausar Soyayya ta ko digo bai goge a Zuciyata ba. Tana gama fad’i haka ta tashi ta shige d’aki ta bar Sadeeq a gurin.
ONE WEEK LATER
Sadeeq ne ya fito D’auke da Akwatin shi a hannu gasu Mami duk sun fito domin rakashi.
“Kadai ji me na fad’a ma Koh ka dunga Kiran mu a waya Kuma kana dawowa weekend Saboda yanzu ba da bane, Sannan maganar Auren ku bana so ya d’auki lokaci in ka dawo dai zamuyi magana. “To Mami ba damuwa.
Bayan tafiyan Sadeeq su Zahra sun koma school yayin da Khausar ta cigaba daga inda ta tsaya, domin yanzu ya Kai ma da cewa kaf School ba Wanda Bai San khausy babban Yarinya ba. Domin duk wani fati da za’ayi a School d’in sai da ita zai tafi dai dai, duk wani Club ta sanshi. Ga shaye-shaye da Less da tasa ma gaba.
Zahra ko ta dukufa karatu, don duk department d’in su ansa Zahra disntintion  don tunda suka fara Abun da take d’auka kenan. K’awar ta d’aya ce a Makarantar Murjanatu Babagana Asalin ta Yar Borno ce. Ita ma akwai k’ok’ari sosai, shiyasa nasu yazo d’aya sai suka koma Room d’aya Abun su suna zaune tare,  dukan su bawan zai  b’oye ma y’ar uwan shi damuwar shi, Shiyasa Khausar ta ba Murjanatu Labarin Abun da ke damun ta sai dai Bata sanar da ita sudin D’auko su akayi gidan Marayu ba. “My sweet Zahraty karki damu ki cigaba da Addu’a wallahi indai Yaya Sadeeq mijin ki ne sai kin Aure shi. Nifa har Kama kukeyi  mun dashi kawai kin fishi fari ne, Kuma wlh kunfi dacewa dashi. Nifa kin San Allah na tsani wannan Twinie d’in naki, tun randa tazo Nan d’in nan tayi Miki wannan rainin,  wallahi bazan iya d’aukan rainin Nan ba, Tana ji kaman an d’aura ma mucciya zani, da tsawo kaman falwaya… “Kai sweet Janah wannan cin fuskan ya isa haka, kin tasani gaba kina ta kushe mun Yar uwa. Ta fad’a cikin bacin Rai😔.
“To Mai Yar uwa.!  Yar uwan da Bata K’aunar ki, Amma ki wani Nace Mata, ba dama a fad’a laifin ta, Tashi Murjanatu tayi ta Fice Abun ta cikin fushi.
Lokaci na tafiya yayin da Abubuwa suke ta juyawa,  Khausar ta Zama cikakkiyar Yar duniya bama ko da yaushe take attending Lecture ba, Saboda ta samu goyan bayan tantiran lecturers Tana Abunda take so.
Yau ta Kama anyi hutu inda kowa ke murnar Zuwa gida, Yayin da Zahra take ji kamar kar ta koma gida Saboda irin wulakancin da Mami da Khausar suke Mata. Bayan anzo an d’auki Murjanatu ta tafi, Zahra ta shirya tsaf don Zuwa Tasha ta hau Mota don dai tasan driver bazai zo D’aukan ta ba, fitowan ta get yayi Dai dai da k’arisowar  Sadeeq. Da Mamaki ta kalleshi tace “Yaya Sadeeq yaushe ka dawo ne.?
Murmushi yayi Mata Yana k’okarin fitowa, ya d’auki Akwatin ta yasa a boot yace Mata “muje Madam Tambaya. Ya fad’i haka Yana Murmushi.
Bata rai tayi ta fara Yi tamkar zatayi kuka, “Nidin ce zaka cema Madam Tambaya koh, Allah ni ba sunana kenan ba🙄, Kuma na fasa shiga Motar taka kaje Zan biyo ta haya.
Kama kunnen shi yayi  “Sorry My Baby Zahraty,  shiga mu tafi kin San hanyoyin namu babu kyau. Shiga tayi Tana ta b’ata fuska, yaja suka tafi.
Sun Isa gida karfe Tara na dare, Khausar kawai suka tarar a Falo tasa wasu matsiyatan Kaya, Wanda gara babu kanta yaji Attached dama ita Bata da wani gashi Sosai. Tana kwance  Tana latsa wayar ta kirar Apple plu. Binta sukayi da kallo gaba d’ayan su, ita ma wani kallon gefen Ido tayi musu ta kawar da kan ta ta cigaba da latsa wayar ta.
“Twinie baki ganni bane…? Ko well come bazakiyi  mun ba. Ta karishe maganar ta Tana Zama kusa da ita, ta Kai hannu zata rungume ta.
“Karki sake ki tab’ani ko cewa akayi Dole sai na kula ki iyee? Tashi tayi  ta  shige d’aki Abunta ta bar Zahra zaune gurin.
Jiki sanyaye Zahra ta tashi ta ja trolley d’in ta, Dama shi Sadeeq tunda suka shigo ko tsaya bai yi ba yayi wucewar sa.
Washe gari tun karfe hud’u Mami ta tashi Zahra tace ga wankin da Khausar ta dawo dasu can daga School ita ma nata na Nan a cikin Basket Laundry. Gashi Washing machine d’in su ya lalace, Haka Zahra ta tashi taje ta fara wanki….✍️✍️✍️✍️
Ban ganin Comments din ku fa more Comment more typing ehee 🙄🙄.

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements