BOYAYYIYAR KULLI Page 21 to 30 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / BOYAYYIYAR KULLI Page 21 to 30

BOYAYYIYAR KULLI Page 21 to 30

BOYAYYIYAR KULLI Page 21 to 30

Sosai ranar Zahra ta wanku don Bata kammala wankin Nan ba sai karfe Sha biyu, sanan ta samu ta karya, ga kayan sunyi masifan datti don harda su panties da breziya da su boom short.

Bayan ta zauna Tana hutawa sai ga Khausar ta fito Tana wani mik’a had’i da yamutsa fuska. Ke Zahra ki had’a mun oat yanzu. Tana gama fad’i haka ta juya Abun ta, girgiza Kai Zahra tayi ta tashi ta shiga kitchen don had’a mata, jitai kamar ana kallon ta, waigawa tayi da sauri had’a Ido sukayi dashi Yana jingine da kofa Yana Mata murmushi. “Zahraty baby wa yayi wankin can,? In ce dai ba ke kikayi ba.?
“A’a Yaya  a washing machine ne fa. Ta juya ta cigaba da k’okarin juya oat d’in da take damawa.
“Zamu Sha oat kenan.?
“Uhmm na Khausar ne ma Yaya sai dai Kai in kana so  In dama ma wani.
Kallon da yayi Mata ne ya hanata k’arisa maganar da takeyi, langwabar da Kai tayi Alamun kar yace komai.
Fita yayi cikin fushi, Tana Kiran shi ko waigota baiyi ba.
Direct d’akin su ya shiga ya same ta a kwance Tana Danna waya, wani tsawa da yayi Mata sai da wayar ta fad’i a hanun ta, ta Mike a tsorace don duk iskancinta Tana tsoron shi.
“Me na fad’a Miki eyeh,! Ita d’in Baiwar kice ko Yar aikin ki da Zaki dunga sata aiki, ba laifin ki bane laifin Mami ne da ta d’aure Miki gindi ki ke Abun da kike so, Kuma yanzun Nan zanyi maganin ki. Zare belt d’in da yake jikin shi ya farayi.
*************************
JOS
Rirrik’eta akeyi Amma Tana dad’a watsar da mutane, kuka Sosai Hajiya takeyi don ita ji take tamkar jinin ta ce Dijah,zata iya biyan ko  nawa ne don  ta Samu lafiya. “Hajiya kiyi hakuri insha Allah komai yazo k’arshe duk wahalar Nan da suke bamu in har suka ji wuya da zafin Ayoyin Ubangiji zasu fita, suna da tsananin taurin Kai ne ko magana sun k’iyi, Amma ba Abunda yafi karfin Ubangiji.
Sosai Hajiya ke kuka tana fad’in “Allah ya yaye Miki Dijah ya Kuma saka Miki duk Wanda yayi Miki wannan Abun Allah ya mayar Masa.
*************************
K’AUYEN ZULUM
Sosai Uwar Sharri ke jin jiki yayin da Innah Tasallah take iya k’ok’arin ta gurin Mata Yan jike-jike irin nasu na Yan k’auye Amma har yanzu ba wani cigaba sai Uwar wari ma da gaban ta yakeyi Yana fitar da wasu irin Manyan tsutsotsi. Duk da girma ya Kama Innah Tasallah Amma tsakanin d’a da mahaifi sai Allah, Haka take wannan d’awainiyar. Kullum maganar Asabe Allah kar ya d’auki ran ta Bata je ta kwance K’ullin da ta d’aura ba.
Haka zata zauna Tana sunbatu da maganganu kamar mahaukaciya.
*************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
Dukan ta yakeyi kamar ya samu jaka, gaashi Mami Bata Nan a gida ta je unguwa. sai da Zahra tazo ta rungume ta, tace sai dai ya dake su tare, Tana kuka Khausar na kuka. Yar da belt d’in yayi ya fita ransa a b’ace.
Kama ta tayi ta d’aga ta ta zaunar da ita a bakin gado, da sauri ta shige toilet ta had’a Mata ruwa Mai Zafi ta Kamata ta kaita toilet tace ta gasa jikin ta.
*************************
MAIDUGURI
“Muddin ba’a bayar da jinin jaririyar Nan ba ga Mai gizo komai zai iya wargajewa don kun San cewa dai ba a hayyacin Alhaji ya Auri y’ar ki ba Koh.?  To ku tabbatar cikin na cika wata Tara a kawo mun ita Nan, ki tashi ki tafi Boka ya Gama magana….✍️✍️✍️✍️✍️✍️
More Comment more typing.
Bafa na ganin Comments din ku fa ko bakwa bukata ne.?
*Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰*
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 18
Mami ce ta shigo taga Khausar kwance, jikin ta duk ya fashe, Alamar duka.
“Baby Khausar wa yayi Miki wannan dukan haka.?
Mami ta fad’a Rai b’ace. Tana d’aga Khausar da  Zazzabi ya lullub’e ta, ta d’ora ta a jikin ta Tana Shafa Mata kai.
Kuka Khausar ta saka, Tana Fad’in “Zahra ce tasa Yaya Sadeeq ya mun dukan tsiya, haka kurum ban musu komai ba.
“Tabdijam lallai ma wlh yau sai tasan cewa ruwa ba sa’an kwando bane, Tashi muje a kanta Zaki Rama dukan Nan.
Jin haka yasa Khausar ta Mike Zuciyar ta fal farin ciki.
Zahra Tana cikin fere doya a kitchen Tana ta sauri don kar Mami ta dawo bata gama girki ba. Ga Khausar bata ci komai ba, kawai jin duka tayi ko ta Ina sun rufe ta da shi.
“Don Allah Mami kiyi hakuri, menayi muku ne.?
Sai da sukayi Mata duka Sosai sannan Khausar ta d’auko tukunya da ke kan wuta ta d’ora ma Zahra a cikin ta, wani k’ara ta saka yayi dai-dai da shigowar Sadeeq falon.
Da gudu ya k’arisa kitchen din, ganin su Mami a tsaye Tana zazzaga ma Zahra Masifa, ita Kuma Khausar hannun ta d’auke da tukunya Tana zazzare Ido.
“Haba Mami me tayi Miki ne? Don Allah ki daina Azabtar da yarinyar Nan Haka Kuma wallahi kinci Amanar Daddy. Don Amanan mu Daddy ya bar Miki.
Juyawa yayi a fusace zai tafi, “Sadeeq zonan.”
Mami ne ta kirashi tunda yake da Mami Bata tab’a Kiran sunan shi ba sai yau. Zuwa yayi ya zugunna a gaban ta yace,  ” gani Mami.”
“Sadeeq daga yau ni Mahaifiyar ka Hajiya Laurat nace duk ranar da ka Kara kula yarinyar Nan Allah ya isa ban yafe ma ba, ko ka Kara ganin Ina Mata wani Abu kayi magana.
Gaba d’ayan su d’agowa sukayi cike da firgici da Mamaki suna kallon Mami, Ashe har tsanar da  Mami tayi ma Zahra ya Kai haka, Sadeeq ne yake Fad’in haka a Zuciyar shi yayin da hawaye ya wanke Mai fuska.
“Mami don Allah kiyi hakuri ki janye wannan kalaman naki a Kai na, wlh yamun tsauri da yawa.
“Ka tashi ka bani guri kafun in tsine maka ka bi duniya, kasan inda na tsani yarinyar Nan kuwa,?  Tunda tazo gidan Nan Alhaji ke nuna Mata Soyayya ya fifitata akan kowa, har Kai da kake d’an shi, ta kanta Alhaji yace zai iya Saki na fa.” Ke Zahra na tsaneki har cikin zuciya ta. Tana gama Fad’in haka ta juya Abun ta, Khausar binta tayi tai shigewan ta d’aki.
Kuka Sosai Zahra takeyi tabbas yanzu tasan gatan ta ya rasu, Jan jiki tayi ta shige kitchen don k’arisa Abunda takeyi.
Karfe bakwai na Yamma dai dai Sadeeq ya bar garin Zaria, do yau yace komai Dare sai ya bar garin, bazai tab’a dawowa ba har sai Mami ta janye kalaman ta a kanshi, Takarda ya ajiye ma Zahra a kitchen ya tafi kowa baiyi ma Sallama ba.
Fitowan ta kenan daga kitchen ta kammala wanke-wanke da kimtsa kitchen din, tsayawa tayi tana tunani, da sauri ta koma kitchen din dai dai gurin sink taga wani takarda taga Kuma an rubuta Zahraty. Jikin ta na rawa ta bud’e takardan ta fara karantawa.
“Zahraty kiyi hakuri ki rungumi kaddara, ki dage da karatun ki, na tafi bazan dawo ba sai ranar da Mami ta Neme ni da kan ta. Ki kulamun da kanki, karki manta har Abada Ina son ki, sannan na Mai da sunan ki a Asusun Albashi na duk wata Albashi na zai shigo ta Account d’in ki ne, kiyi duk wani hidiman karatun ki dashi, ban so ki roki kowa, Sannan akwai takardun kadarorin daddy da yake hannu na, yace akwai fake din a hannun ki da Kuma na kananun kadarorin shi, yasan meyasa yayi haka sannan a cikin Abunda ya baki akwai wani Akwati karami ki Adana shi da kyau duk Randa mukayi Aure zamu bud’e tare muga meye a ciki.
Bye bye Zahraty ki kulamun da kanki.
Kuka Sosai Zahra ta zauna takeyi, “Allah ya tsaremun Kai yayana a duk inda kake.tana Gama fad’an Haka ta tashi ta tafi d’aki.
*************************
JOS
“Hajiya gaskiya za’a d’au tsawon lokaci kafin Yarinyar Nan ta warke, kin San Asiri farat d’aya yake shigan mutum Amma fitan shi sai anyi da gaske.
“Shikenan Mallam nidai fatana ta samu lafiya Allah ya dubemu. Ta fad’a Tana mai Mik’ewa “to Mallam na tafi Allah ya saka da Alheri.
“Ameen ya Allah Hajiya ai ba damuwa wannan Abu tamkar jihadi ne.
*************************
K’AUYEN ZULUM
Fisge-fisge takeyi tana ihu Saboda wani Azaba da take ji a fatan jikin ta, inda gaban ta yake fitar da wani ruwa Mai kauri had’e da jini ga wani uban wari, Haka take cisge gashin kan ta, Tamkar Mahaukaciya.
Kuka Sosai Inna Tasallah takeyi, “Mallam ka taimaka ka sauko daga fushin Nan da kakeyi da ita kayi Mata Addu’a ko taji Salama.
“Kinga Tasallah ki kyaleni Abunda Asabe ta shuka shi take girba fa, ba Abunda Zan Mata Kinga fita ta ma, ya shura takalman shi yayi gaba abinshi.
Kuka Sosai Inna takeyi don Asabe tana tsananin Shan Azaba.
*************************
MAIDUGURI
Kwance take jikin ta ba inda Bai Mata ciwo, ga wani Azaban Ciwon ciki da take fama dashi yau gurin sati d’aya kenan, gashi komai taci sai tayi Aman shi, Hankalin Alhaji duk ya tashi, an Kira likitoci sunkai goma don suga Mai ke damun ta, Amma Amsar d’aya ce Lafiyan ta k’alau.
Ita Kuma ita kad’ai tasan Azabar da take Sha a jikin ta da cikin ta.
*************************
Khausar ne d’akin Daddy tayi watsa watsa da d’aki kamar Mai Neman wani Abu.
Wani drawer ta janyo  zaro Ido tayi ganin me ke cikin drawer, jikin ta na rawa ta jawo jakan da ke hannunta ta shiga loda kud’i Nan a ciki sai da ta kwashe zaf ta Mai da ta rufe ta fito, ficewa gidan tayi taje banki ta sa kud’in. Ta ja Motan ta tayi gida Tana Zuwa ta d’auuki trolley d’in ta ta saka a jaka, ta kwashe duk wani Abu nata tasa a boot d’akin Mami ta shiga taji Alamun kaman Tana wanka, bincike ta farayi a D’akin da sauri da sauri gwala-gwalan Mami ta tattara tasa a cikin handbag d’in ta, biro ta fito dashi a Jakarta da takarda tayi rubutu ta ajiye, ta fice Abun ta.
Tana Zuwa ta hau Mota ta fita a tsiyace, dai dai lokacin Mami ta fito wanka kenan, idon ta ne ya kaima ta kan takardan da ke side drawer nata, da murmushi a fuskar ta ta k’arisa Tana “Yan matan Mami har an Fice kenan Allah ya dawo mun da ke lafiya.
Maganar nata ne ya mak’ale lokacin da taga me ke cikin takardan.
“Mami karki sake ki nemeni, Kuma karki nemi gold d’in ki, sannan in kin koma garin ku kin tarar da Uwata kice Mata na tsane ta har Abada.
Ki Kuma bar Zahra ta Auri Yaya Sadeeq don da ita yafi dacewa ba Dani ba, ni burina ya riga ya cika na samu Abunda nake so, ki manta da wata Khausar a duniyar ki.
Kiyi jimami lafiya.🤣
Wani jiri Mami taji Yana d’iban ta kawai jitai ta zub’e a gurin…✍️✍️✍️✍️✍️
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍
Nasan wasu da yawa zasu ji dadin page d’in Nan koh
Ni Kuma bakin ciki nakeyi wayyo Mamin mu😭😭.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
🤣🤣🤣🤣🤣🤣Yau Ina so Inga comments din ku fa.
Masu farin ciki sai ku Kara farin ciki.don Naga alama bakwa K’aunar Mami🙄🙄.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
PAGE 19
Take stroke ya Kama Mami.  Ihun da tayi ne yasa Zahra fitowa da gudu Tana shigowa d’aki ta tarar da Mami kwance b’arin jikin ta ko motsi baiyi.
“Innalillahi wa’innah illaihirraji’un Mami meya same ki.? Fita tayi ta dawo ta d’auko Kaya ta sa Mata, ta Kama ta ta d’ora ta a gado, Tana yi tana kuka waya ta d’auka ta Kira doctor. “Hello doctor please kazo yanzun Nan ba lafiya.
Bayan zuwan doctor yayi Aune-aunen shi ya gama, rubuta Magunguna yayi ya mik’a ma Zahra.
“Kiyi k’okari ki siyo maganin Nan sannan Kuma jinin ta ya hau sosai, ta kamu da ciwun barin jiki.
“Innalillahi wa’innah illaihirraji’un ya Allah ka yaye Mata wannan cuta.
Sallama doctor ya Mata tare da Addu’an Allah ya kawo sauki. Ya tafi.
Sosai Mami take barci Saboda Alluran Barcin da likita yayi mata.
Haka Zahra tayi ta fama da jinyar Mami har sati biyu gashi an koma school, da k’yar ta samu wata tsohuwa da zata cigaba da kula da Mami, ita Kuma tayi Shirin komawa makaranta.
Three months later
Khausar ne Zaune a katafaren falon ta, na gidan da ta siya, ta ci Ado tayi masifan kyau hannun ta rike da roban ice cream Tana Sha hankalin ta kwance.
“Ranki ya dad’e Kaya fa sun iso.
“Ok  James ka tabbatar  sweet 18 ne don kasan ni na fi bukatar Wanda basu San har ka ba Wanda ni da Kai na Zan d’ora su akan hanya. Don sunfi kawo kud’i don kasan ni bana wasa da kud’i.
“Eh Hajiya na tabbatar Kuma baki da matsala, Zaki samu yanda kike so.
“Ok a Kira mun Hajiya Laila kace Mata Kaya sun iso.
“Ok ba damuwa Hajiya. Juyawa yayi ya fita ita Kuma ta jawo wayar ta ta fara chatting.
“Ma ana Kiran ki a waya.”
“Waye ne,?  A duba a gani in Ina da appointment dashi to ayi received in Kuma Babu ayi rejected.
Tana gama Fad’in haka ta tashi ta haura sama Tana tafiya cikin k’asaita da Isa irin na Manyan Mata.
(Niko nace lallai Khausar kin samu duniya, Sister Adama da sister Nafeesat ya kuka ga Mutuniyar taku ne🤣).
Zaune take ta zabga tagumi, gaba d’aya ta shiga cikin tunani, Murjanatu ne ta shigo ta dad’e a tsaye Tana kallon k’awar tata da gaba d’aya ta rame kamar ba ita ba.
“Haba sweet Zahraty Kinga  tunanin Nan naki Yana Neman ya shafi karatun ki, please Addu’a ya kamata ki dunga yi ba Abunda yafi karfin Ubangiji insha Allah Mami zata warke.
Rungume ta Zahra tayi tace “nagode Sosai my Jannat insha Allah na dai na tunani, Zan Yi k’okari gurin mik’a lamurana ga Ubangiji.
*************************
MAIDUGURI
Sosai Bintu take jin jiki don Ciwon yau da ban na gobe da ban, ga cikin ta sai k’ara girma yakeyi tamkar  Wanda zata haifi Yan biyu.
Yagana ne ta tasa ta a gaba Tana kuka.”yanzu gaba d’aya Bintu kin canza an rasa gane kan Ciwon dake damun ki, Dole Zan koma gurin Boka don wannan Ciwon da alamar tanbaya Abu yak’i ci yak’i cinyewa, ko mak’iya ne suke so suga bayan mu. Ta k’arisa maganar Tana share hawaye, ta fice a D’akin da k’udirin yau zata gidan Boka taji Mai ke damun Bintu.
“Kar ma ki k’ariso Nan Yagana nima Ina cikin rud’ani da fargaba domin da Alamu aikin mu Yana Neman warwarewa domin Aljani d’an tsito yazo min jiya a rud’e jikin shi a k’one Yana fad’a mun akwai matsala babba.
Zaro Ido Yagana tayi “Boka ka taimakeni kar Asirin mu ya tonu.
Juyawa tayi ta tafi Tana kuka a hanya, Dole yau taje k’auyen Zulum don taji kamar ance Asabe ta dawo, Dole taje taji wani Mafita zasu samu.
*************************
PLATAEU  STATE
Zaune take hannun ta rike da hisnul Muslim tanayin Azkar, kaman an tsikareta ta tashi ta shiga d’aki ta d’auko wani Akwati kato, ta bud’e kayan jarirai masu kyau ta dunga fitowa dashi Tana cikin fitowa dasu wani pic da Envelope ya fad’o a ciki, da sauri ta d’auki Envelope din ta fara bud’ewa.
*************************
ZARIA BIRNIN ILIMI
Garin da ba Zazzau ba dajin Allah karfa kuce na so garin mu da yawa🙈🙈🤣🤣🤣.
Sosai Mami take jin jiki duk da Baba Suwaiba na tsananin kula da Mami, Amma Mami Bata ganin Abun da take mata, kullum k’orafi haka Baba Suwaiba take hakuri da ita.
Wataran karfe Sha biyun dare aka tashi da wani firgici, Wanda kawai aka ga gidan Su Mami ya fara kamawa da wuta.
Gashi daga part din Mami ne wutan ya fi ci, Baba Suwaiba ne ta fito a rud’e Tana buga gidan kusa dasu Tana ihun a taimake su wuta a gidan su.
*************************
KANON DABO
“Ok ka tabbatar suna cikin gidan James.?
“Eh Hajiya na tabbatar.
Kuma ita Yar Uwar taki Bata dawo ba sai gobe kin San yau sukayi celebrate na kammala karatun su.”
“Ok good haka nake so kace musu zasu ji Alert gobe. Zaka iya tafiya.
“To Hajiya angama. Juyawa yayi ya tafi, Yana tunani a Zuciyar shi, wannan wani irin rayuwa ce kice a Kona gidan ku…..✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 20
Zagaye d’akin ta takeyi, daga ganin ta kasan tana cikin damuwa.  Zama tayi a gefen gadon dake bedroom d’in tana share hawaye a hankali ta furta  “Sorry Mamin mu dole ne tasa na kashe ki don bana buk’atar jin Asalina don inaji a jiki na bani da Asali Mai k’yau daga yanayin halayya ta da d’abi’una. Nasan tabbas ni ba Yar halak bane, don duk Yar halak bazata aikata Abun da nake aikatawa ba.
Tana gama Fad’in haka ta fashe da kuka, “Allah sarki masoyiyata Mai K’yakk’yawar zuciya Har a cikin Rai na ban tab’a tsanar ki ba Asali ma Ina son ki Allah ya Bayyana Miki Asalin ki ya Aurar daku ke da Yaya Sadeeq, don nasan ke kin fito daga Asali Mai k’yau k’addaran ki ne yazo Miki a Haka.
Tashi tayi ta fito falo wayar ta ta d’auka da yake kan kujera, Kira ta fara yi ringing D’aya tayi aka d’auka, “Hello James Ina so ka bincika mun Halin da y’ar uwa ta take ciki ta koma gida kuwa,?  Sannan Mami ta mutu ko Tana da rai.?  Yanzun Nan fa nake buk’atar jin komai, tana gama Fad’in haka ta kashe wayar ta.
ZARIA BIRNIN SHEHU
*************************
Haka mutane ke ta watsa ruwa kaman ana k’ara wutan ne.
“Don Allah ku taimaka ku fito da Hajiya tana ciki.
Tana cikin maganar sai ga wasu sun fito da Hajiya duk ta kone, Haka akayi Asibiti da ita ana Zuwa likitoci suka Anshe ta sukayi Emergency da ita.
Washe gari doctor yace Yana Naiman Yan uwanta Yana son magana dasu, baba Suwaiba tace “sai dai in baka Number yarinyar ta ka kirata.
Zahra shigowar ta layin kenan a Motar ta da Yaya Sadeeq ya bar Mata taga gidan su a k’one.
“Innalillahi wa’innah illaihirraji’un Mai ya faru ne, wani mak’ocin su ta hango ta fito da Sauri Tana tanbayar shi meya Sami gidan su.?
Duk Abunda ya faru ya kwashe ya fad’a Mata, wani jiri taji ya fara d’iban ta, nan da Nan ta zauna ta fara fad’in Innalillahi wa’innah illaihirraji’un Allahumma ajirni fi musibati wa aklif ni khairan minha. Haka ta dunga nanatawa har taji ta samu Natsuwa a Zuciyar ta.
Ta shiga Motan ta kenan taji Kiran likita tace mai gatanan Zuwa ma.
Bayan ta Isa doctor yake cemata gaskya sai anyi ma Hajiya Aikin fata don wannan fatan nata gaba d’aya ya lalace, Kuma likita d’aya ne yake zuwa yin aikin duk shekara, ya kusa Zuwa Kuma a k’allah kud’in zai Kai Naira Miliyan biyar.
Zaro Ido Zahra tayi don gaba d’aya kud’in da ke hannun ta ko Miliyan d’aya Bai Kai ba, Gashi kud’in da Yaya Sadeeq yace zai tura Mata Basu shiga ba ko sau d’aya Kuma ta dunga Kiran wayan shi baya shiga.
Fita tayi a Asibitin jikin ta a Mace, komawa Mota tayi ta zauna ta fara tunanin ya zatayi, tunawa tayi da Zinaran ta da Yaya Sadeeq ya siyo musu lokacin da yaje Dubai, ita kala hud’u ya siya Mata yace ta b’oye kar Mami ta gani da sauri ta kunna Motar ta juya taje gida, tana Zuwa d’akin su ta wuce tunda ba ko Ina ya k’one a gidan ba, bincike ta fara yi a drawer ta, da k’yar ta ga guda biyu Bata ga sauran ba.
Da sauri ta Nufi kasuwa don siyarwa.
“Hajiya gaskiya da Zan baki shawara karki sayar da Zinaren kin nan.” Don ainihin masu kyau ne zai Kai kimanin Naira Miliyan d’ari duk guda d’aya, ni a yanzu ma Banda kud’in da Zan siya.
“To Alhaji don Allah ka taimakeni ka rike sarkan Nan duka ka bani Aron Miliyan biyar Mahaifiya ta ce a Asibiti za’a Mata aiki, insha Allah Zan kawo maka kud’in ka in karb’i sark’ata.
“Ok ba damuwa, Hudu ka Bata Miliyan biyar.
“Nagode Sosai Allah ya saka da Alheri.
“Ba komai Hajiya, don Allah ko Zaki iya bani phone Number na ki,?
Sunana Aliyu  ana ce mun Haidar nine Mai shagonNan. Ya k’arishe maganar Yana Mata murmushi Mai birgewa, tabbas Aliyu ya had’u don black beauty ne ga Lulu eyes ga sajen shi da ya k’ara k’awata fuskan shi, Wanda dogon hancin shi ya k’ara fito da k’yawun shi ga dimple din shi, Kai in tak’aita muku Aliyu Haidar ya had’u ko ta Ina.
Samun Kai na nayi da mayar mishi da murmushi nima.
“Ba damuwa ga card d’ina nan, ta mik’a mishi dai dai lokacin da aka kawo k’udin ta karb’a ta k’ara mishi godiya.
Tana tafe a hanya tana Murmushi ita k’adai tabbas mutumin Nan Yana da kirki Sosai ba don shi ba da sai dai ta rasa Mamin ta Wanda ita kad’ai ta rage mata yanzu take gani taji d’adi.
Bayan ta biya kudin ne taje d’akin da aka kwantar da Mami ta tarar da Baba Suwaiba tana gyara mata kwanciya.
“Sannu baba Suwaiba nagode Sosai da hidima.
Sannu Mami ya jikin.?
Duk da Ciwon da Mami keyi but bakin ta Normal ne Ciwon Bai Kama mata baki ba.
“Lafiya lau Yar Albarka,” sai ta fashe da kuka “Zahra ki yafe mun duk Abun da Nayi miki. Yanzu kin samu kin biya kud’in aikin.?
“Haba Mamin mu karki damu ba komai, komai ya wuce naje na biya kud’in aikin, Nan ta kwashe yanda ta samu kud’in ta fad’a ma Mami.
Albarka Mami ta dunga Sama ta da Neman gafarar ta.
*************************
KAUYEN ZULUM
…….Sauri take tayi bani da Sauri Ba kasancewar Yamma tayi Kuma hanyar k’auyen ba’a cika Samun Abun hawa ba, ga matsala rashin tsaro da K’asar mu ke ciki.
“Yauwa Rabe tsaya ka k’arisa dani Mana.
“Yagana kece da wannan yamnan,? Yaushe rabon ki da k’auye kin gujemu Saboda kin samu duniya ke da y’ar ki.
“Nifa Matsala ta da Kai kenan Rabe Shegen surutu ne da Kai.
Yauwa Rabe Wai naji Labarin ance Asabe Uwar Sharri ta dawo.?
“Ai ke dai Bari kawai Yagana wato dai in fad’a Miki Bariki ba riba in Kinga Uwar Sharri sai ta baki Tausayi bakyace itace Asaben Nan Yar gayu ba.
“Da gaske Rabe.?
“Wallahi da gske nake fad’a miki, sai kinje Zaki ganta.
Jikin Yagana ne duk yayi sanyi ga wani tsoro da ya k’ara Kama ta.
*************************
JOS
“Niko Ina Zan ganki Baiwar Allah Ina kika shige yau shekara Ashirin da biyu kenan, ko a wani hali kike ciki ban sani ba Nasan yanzu yarinyar ki tayi girma, Allah yasa Kuna gurin hannu na gari. Share hawayen ta tayi ta d’auki Envelope din da ya fad’o ta maida cikin Akwatin ta rufe Akwatin ta fito.
*************************
“Hajiya karki damu gaskiya muna ganin Sauki Sosai akan da insha Allah zamu samu Nasara.”
“Allah ya yarda Mallam ya kawo Mata k’arshen matsalar Nan.🙏
“Ameen ya Allah Hajiya.”
*************************
KANON DABO
Koda me kazo anfika Wai inji kanawa🙄🙄 nidai nasan fad’i suke ba gskya bace.😏🤪.
“What ba ta Mutu ba.! Ta fad’a cikin d’aga murya, “sai da na fad’a maka kar a samu matsala James. Yanzun tana wani Asibiti ne.?
Dole ne a bita har Asibitin a k’arisa ta.
“Angama Hajiya…..baza’a k’ara Samun Matsala ba.
“Ok ban bukatar jin wani labari in ba na mutuwar Mami ba.
“Sorry   sweet Zahraty dole in rabaki da wannan Matar don Bata can-canci kulawar ki ba, ta hakan ne kawai zai sa kije ki Nemo Asalin ki.✍️✍️✍️✍️✍️
Sister Nafeesat saura inji bakin ki kince ya Miki kad’an sai na tafi yajin aikin typing ehee 🙄🙄😏😏🥴🥴
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 21
“yauwa Zahra ko,?
Dama Ina so in sanar da ke zamu maida Hajiya Abuja domin a can za’ayi Mata aikin. Doctor yace bazai samu daman k’arisowa Nan ba.
“Ba damuwa Doctor yaushe ne za’a tafi da itan.?
“Eh yau da karfe Tara na dare anriga ma anyi booking flight da zaku tafi a Kai.
“Doctor waya biya kud’in flight d’in.?
“Eh wani ne ya zo d’azu yace shi relative d’in ku ne duk Abunda ake buk’ata a fad’a mishi zai bayar ba sai an nemeki ba.
“But Amma Doctor ban gane ko waye ba fa.
“To Malama Zahra nidai haka ya cemun, ya k’arisa maganar Yana tafiya Abun shi ya bar ta Nan tsaye Tana Mamaki da tunanin ko waye haka.
Yaya Sadeeq ne ya fad’o Mata a rai to kodai shine ya dawo. Kai Ina bashi bane ma da shine da ya Kira ta.
Sun sauka Abuja lafiya,  bayan sun huta ne Likita yayi duk Abunda ya dace yanzu sai su jira ranar aiki Nan da sati biyu.
Karfe Sha biyu na dare yayi musu a cikin Asibitin Shika don cika aikin Hajiya Khausar Mai Zamani.
Sai dai an samu akasin don Basu ga Mami ba a d’akin, sunyi  Mamakin yanda akayi Basu ganta ba.Haka suka koma suka fad’a ma Khausar Basu ganta ba, bata so haka ba but duk in da suke ma zasu had’u Alkawari ne tayi ma kan ta sai ta kashe Mami.
*************************
KAUYEN ZULUM
Sosai Yagana ta tsorata da ganin yanayin Asabe.
“Asabe haka kika koma,? mun shiga uku, ni da nazo ki kaini gurin wani Bokan domin Naga Alamun Boka Duna yanzu aikin shi ba yayi, sai in zo in ganki cikin wanan halin. Ta k’arisa maganar Tana kuka
Waiyo ni Yagana Ina Zan sa Kai na Anya ba K’ulli da muka b’oye bane yake bibiyan mu Asabe.”?
“Ga Bintu can da tsohon ciki ga matsanancin Ciwon ciki da yaki barin ta kullum cikin firgici, ke Kuma ga halin da kike ciki Anya ba sakayya muke gani ba Asabe, na fara karaya ni, na fara jin tsoro.
“Yagana Ina so ki taimaka ki kaini gurin Alhaji Bukar don mu warware K’ullin nan.
“In banda abin ki Asabe in mun ce zamu warware K’ullin nan ta Ina zamu fara.? Bari dai in tashi inje gidan Guggo Hajinjin  in kwana gobe Zan dawo mu k’arisa maganar mu.”
*************************
JOS
Driver ne da sauri ya taso yazo ya Karb’i kayan da ke hannun Hajiya ya zuba a boot, ya zagaya ya bud’e Mata kofa sai da ya tabbatar ta zauna sannan yaje ya tada Mota.
“Hajiya gidan Marayun muka nufa.?
“Eh Haruna, Amma kafin Nan ka biya dani ta kasuwar Taminus akwai inda wasu mabuk’ata suke Zama suke bara.
“To Hajiya angama Uwar Marayu.
Sun isa kasuwar haka almajirai suka mamaye  ta suna farin cikin ganin ta, da kan ta ta fito ta rarraba musu Sadaka tana rokon su su taya ta Addu’a Allah ya bayyana Mata Yar ta da jikan ta a duk inda suke. Haka suka dunga zubo Mata Addu’a kamar ba gobe da fatan Alheri, har kuka sai da Hajiya tayi suka shige Mota suka wuce gidan Marayu haka Nan ba ta raba musu duk kayan da ta kawo. Suna ta farin ciki da mata Addu’a, daga Nan suka wuce Masallatai ta bada Sadaka don asa y’ar ta a Addu’a,Daga Nan gida suka dawo.
“Masha Allah Hajiya an samu yanzu ta fara magana fa.”
“Da gaske Mallam,?  Alhmdulillahi ta fad’a wani Abu game da ita kuwa.?
“Gaskiya bata fad’a ba, kawai cewa take Ina yarinyar ta.”
“Zan iya ganin ta Mallam.?
“Kiyi hakuri Hajiya bazai yuwu ki ganta ba, sai dai Zuwa Nan gaba in ta k’ara jin sauki.
“To shikenan Mallam Allah ya kaimu ya k’ara mata lafiya, bari in tafi na bar gurin sai da Abinci na ba kowa.
*************************
ABUJA
……………Bayan sati biyu
Anyi ma Mami aiki cikin Nasara, Kuma aiki yayi kyau Sosai inda nan da Sati d’aya za’a warware Bandage d’in da aka  nad’e ta dashi. Sosai Zahra ke kula da Mami yayin da Mami tayi sanyi Sosai tare da alkawarin Sadeeq na dawowa zata Yi musu Aure, don Sadeeq bai da Matar Aure sai ita. Sosai  Zahra  taji dad’i  maganar Mami.
Inna Suwaiba ma na iya k’ok’arin ta.
*************************
“Ka tabbatar bincike da kayimun dai dai ne.?
“Eh ranki ya dad’e wallahi iyakan binciken kenan, ko waye Zaki sa haka zai Miki.
“Ok good job, kaje Zan nemeka.
Wani murmushi tayi mai ma’anoni da-ban da-ban.
“Ranki ya dad’e su Esther fa sun sauka suna Airport, Kuma yau Hajiya kulu daga Adamawa zata turo da kayan nan Kuma tace masu kyau ne Sosai Zaki tura mata da Miliyan d’ari biyar in ciniki ya kama, Saboda kayan nata zafafa ne.
D’aga Mata Hannu tayi da mata alama da ido, nan da nan ta tashi ta je ta mik’a mata wayan ta, Kira ta danna ta d’ora a kunnen ta. “Hello Hajiya Kulu kin San ni ban son yawo da hankali Kuma bana siyan k’anan Kaya in har kin San kayan ki ba masu zafi bane kar ma su k’ariso Kano kin dai gane ko,?
Daga can bangaren aka ce “haba baby ke kin San nima bana harkan k’ananan Kaya ai zasu iso ai zaki gansu za Kuma ki tabbatar. Yauwa Baby wallahi Alhaji Lawalli ya matsamun fa akan maganar ku, ki bashi dama kawai ki dama wallahi sai kin ninka darajan ki.
“Dakata Hajiya Kulu bana son shirme kin gane ko, kin San dai ni ba Yar iska bace, duk iskanci na inayin Mai lasisi ne, ban shirya zubar da mutunci na ba na y’a Mace kin gane ai, ganina a bariki bashi zai sa na Zama Yar ta zubar ba, Saboda haka ki fita Ido na,har yanzu tarbiyan Daddy da Mami bai gama tafiya ba.  Tana gama Fad’in haka ta kashe wayar ta.
Zama tayi a kujera ta fara jera tsaki. “Ke Hanna ki fad’a ma Jame yaje Airport ya d’auko su Esther, tana gama Fad’in haka ta haye sama.✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Much love 💖💖💖💖💖💖💖
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
🙄🙄🙄Kar Wanda ya fara yace mun yayi kadan fa ehe😏😏😏
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
PAGE  22
Sosai Zahra ta ke ta cigiyar Yaya Sadeeq a Abuja, Amma duk yanda take tunanin Samun information a kan Haka bata samu ba, ga Mami ta damu akan shirun Sadeeq d’in gani takeyi duk laifin ta ne, ta Zama uwa Mai son zuciya da musguna ma y’ay’an ta idon ta ya rufe akan son zuciya da Cika burin ta na Boyayyiyar K’ullin da ke ran ta. Gashi tana Shirin rasa d’an ta d’aya tilo ita Ina zata ganshi, “Ya Allah ka Bayyana mun yaro na,” ta fad’a Haka tana mai goge kwallan idon ta.
Haka sati ya zo aka  warware ma Mami aikin, Kuma Alhmdulillahi aiki yayi k’yau Nan da kwana uku za’a Sallame su.
“Yauwa Suwaiba kindai ji Mai na fad’a miki Koh karfa ki bari a samu matsala.?
“Insha Allah Hajiya baza’a samu Matsala ba gidan ma angama cinikin shi Naira Miliyan dubu d’ari.
😲”Kai haba Suwaiba,?
“Wallahi kuwa Hajiya kud’in na gurin Aliyu, da kud’in Zinaren nata,yace gobe da karfe Sha d’aya na dare Visa  mu zai fito sai mu d’aga sai Dubai, wato Hajiya kinyi dubara fa in ba haka ba haka Zaki tashi a tutar babu.
“Ke dai bari kawai Suwaiba aini wannan k’una yazo mun a dai dai, kin San Ina ta tunanin dama ya zamuyi. Sai ga Mafita yazo Mana. Kinga in har muka tafi sai taje ta k’arata Kuma ta Nemi iyayen ta nidai nayi gaba su Inna ma na dunga musu sako kam don bazan iya Zaman k’auye ba. Dariya sukayi suka tafa, “Amma Suwaiba kin iya zubin mutanen kirki fa.
Washe gari Zahra tayi ma sweet Jannah waya tunda dama tana Zaria akan cewa taje mak’otan su ta bada ajiyan kayan ta ta karb’a ta ajiye Mata a gurin ta gobe suna nan dawowa.
………..karfe Sha d’aya dai-dai na dare, Mami ne ita da Suwaiba suke ta sauri a cikin Asibiti yayin da doctor ke binsu a baya, bayan ya tabbatar da ya ba Zahra maganin barci sai nan da Awa biyar zata farka. Suna Isa kofan get suka mik’a ma doctor kud’in shi sukayi Mai godiya dai-dai Motan da zai d’aukesu ya iso suka shige.
*************************
JOS
“Ku su waye Ina Baby na,? Ina Hajiya ta.? Ku fad’a mun ta K’arisa maganar tana mai fashewa da kuka.
“Alhmdulillahi, Masha Allah Khadija kina jina.?
“Na’am ku su waye Nan a Ina nake,?
“Assalamu alaiki Hajiya kizo fa yau munyi Nasara, aiki yayi k’yau.
“Mai Napep kayi sauri mana.
“To Hajiya kiyi hakuri kin San yau akwai go slow ne.
“Allah dai ya kaimu lafiya ance y’ata ta warke, Mallam Mai Napep ka tayani murna yau kimanin shekara Ashirin da uku tana fama da lalura sai yau Allah ya yaye Mata, Lallai Ubangiji maji rokon bawa ne.
“Lallai Hajiya Naga kina son wannan y’ar taki, Allah ya Kara mata Lafiya.
“Ameen ya Allah 🙏, dai dai lokacin da suka iso Alhuda Islamic center, dubu d’aya ta mik’a ma mai Napep ko ta kan Amsar chanjin batayi ba.
Barci takeyi Amma firgigit ta farka, Addu’a ta farayi, kafin ta Shafa ya Allah kasa mafarkin na ya zama gaskiya Dija y’ata ta dawo gareni.
Tashi tayi tayo Alwala tazo tayi nafila raka’a biyu kowacce raka’a  ta karanta fatiha da kulhuwallahu, bayan ta idar ta Mai da goshin ta a k’asa tayi ma Annabi S.A.W  salati sai ta karanta  la ilah ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zaleem kafa arba’in da d’aya, sannan ta fara yo ma Ubangiji kirari da sunayen sa kyawawa sanna ta roki bukatun ta.
Yar uwa wanna Sallah sadaka ce na baku ku gwada ki gani in dai ki daure kika rike wannan Sallah baki da shamaki gurin Amsar Addu’a ki insha Allah,sannan Ina barar Addu’an ku duk Wanda yayi Sallah Nan ya sani a cikin Addu’a shi Allah ya cikamun buri na na Alheri🙏.
Game da matsalan da muke fama dashi Kuma a kan garkuwa da mutane da Yan bindiga.
In har kika rike wannan Yar uwa insha Allah Allah zai kareki daga sharrin masu garkuwa da mutane.
Duk bayan Sallar Asuba in kinyi Azkar kin Gama
 Ki karanta
Salamun k’aulin min rabi Raheem.
Kafa d’ari da talatin da d’aya 131.
Bayan Sallah la’asar ma haka Zaki Karan ta
Da bayan Sallar Magriba.
A kalla ki samu kwana talatin kinayi, insha Allah Yar uwa Allah sai ya tsare ki daga sharrin su.
Allah yasa mu dace.
Bayan ta gama duk wani Addu’an ta ta Shafa sannan tayi shafa’i da wutiri. Ta kwanta tana mai Addu’a.
*************************
MAIDUGURI
Sosai ake rik’e Bintu tana fisfisgewa kamar Mai Ciwon farfad’iya.
Da Sauri Yagana ta shigo gidan a rud’e, Saboda wani mummunar Mafarki da tayi da Bintu  tana Zuwa tarar da Bintu inda take wani juye juye kamar Macijiya tana kanan nad’ewa ga ciki, gashi jini ya b’alle Mata sai zuba yake yi tamkar an bud’e fanpo. Wani ihu ta yi ta k’arisa gurin Bintu da gudun ta tana rungume ta,  sai ji kawai tayi anyi jifa da ita, da gudu Bintu ta shige kitchen d’in gidan ta d’auko wuk’a ta bi Yagana dashi tana fad’in “wallahi sai na kashe ki Yagana tana fad’a tana dariya da kuka a had’e. Sosai Yagana take gudun ceton ran ta, haka suka dunga zagaye gidan nan da k’yar aka samu manyan Samari su goma ma’aikatan gidan suka rik’e ta aka k’wace wuk’ar suka sata a d’aki suka kulle.
         Sosai Yagana ke kuka tana Dana sanin Abun da suka aika ta gashi sanadiyar haka zata rasa y’ar ta d’aya tilo. Sosai Bintu take jijjiga kofar d’akin, take fatali da kayar d’akin ga jini na ta zuba mata yaki tsayawa. Cike da tashin hankali aka Kira Alhaji da yaje wani Meeting a Abuja akan yazo gida yanzu ba lafiya.
*************************
ABUJA
Sun isa Airport suna jiran kawai zuwan jirgi ne yayin da Aliyu yake Zaune kusa da Mami Yana mata bayanin yanda komai ya tafi dai dai jakar kud’in ya mik’a mata ita Kuma ta bud’e shima ta bashi kason shi yayi musu Sallama ya tafi Yana mai murmushi masu ma’anoni da yawa, Yana barin gurin ya Kira Jame ya sanar dashi komai is set up, cemai yayi ba damuwa zakuyi magana da Hajiya tana jiran ka guest house d’in ta dake maitama.
“Ba damuwa shikenan, ya kashe wayar shi ya hau motar shi sai gurin gimbiyar shi Khausar yarinya Yar k’walisa Mai tashe Wanda yanzu duk wata Hajiya da take irin harkan nan tasan Baby Khausar.
Mami ne ta mik’e jin an fara sanarwan ga jirgi nan, kawai ji tayi Suwaiba ta samata bindiga a wuya tace mata wuce muje……✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🤣🤣🤣🤣🤣More Comment more typing ehee.

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements