BOYAYYIYAR KULLI Page 31 to 40 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / BOYAYYIYAR KULLI Page 31 to 40

BOYAYYIYAR KULLI Page 31 to 40

BOYAYYIYAR KULLI Page 31 to 40

Jikin Mami na rawa ta kalli Suwaiba tace “lafiyan ki k’alau kuwa Suwaiba meye kikeyi haka.?

“Hajiya Laure kenan kema kin San Zan iya yin komai akan kud’i, kamar yanda kema kika aikata ciki kuwa har da Had’a baki da ke gurin kashe Mijin ki, da Kuma Batar da d’an shi da kikayi don kin San ba ke kika haifeshi ba Koh.?
“To Bari in fad’a miki nasan duk wani k’ulle-k’ulle naki, nima siyata akayi da kud’i ninkin Wanda kika bani da alkawarin Ina kawoki Zan d’aga sai Dubai 🤷. Kinga Ina zanyi Wasa da dama ta, oya shiga Mota muje ko in fasa kanki da bindigan hannu na.
Jiki na rawa Mami ta hau Mota, tana shiga suka had’a Ido da Aliyu, zaro Ido tayi tana nunashi “harda kai ma,?  Lallai duniya ba masu Amana yanzu.”
“Hajiya kenan ke har Zaki fad’i masu Amana bayan ke ne no one na maciya Amana, kin tarwatsa iyalan ki Saboda son Abun duniya irin naki, kin sa y’ar marainiyar Allah cikin gararin rayuwa, shine kike tunanin Allah zai barki. Ya k’arishe maganar shi Yana mata murmushi da ya zama tamkar taken shi, yaja Mota suka tafi.
Fito da ita akayi suka sata a Mota duk tana barci, jakar ta da takardan da Mami ta saka Mata duk Yana rik’e a hannun ta bata saki ba, can hanyar fita garin Abuja suka je wani daji suka jefar da ita a gefen titi. Suka hau Motar su sukayi gaba abinsu.
Sosai Alhaji Bukar yake sharara gudu, hankalin shi duk a tashe jin Halin da Matar shi ke ciki da cikin jikin ta da ya kwallafa rai Yana so yaga gudan jinin sa a duniya kafin ya mutu.
Duk da Yana cikin wannan halin bai hana shi hango kamar mutum ne kwance a gefen titi, Kuma kamar Macece ma haske ta yayi da fitillar Motan shi yaga tabbas fa mutum ce, sai ya fara tunanin Anya ba irin y’an fashin Nan bane da suke irin haka, shiyasa Alhaji Habib yace ya bari ya biyo jirgi yaki bari, a haka har yazo ya wuce ta sai yaji bazai iya tafiya bai taimaka mata ba, yasan shidin Yana tare da kariyar Ubangiji Saboda shi mutum ne mai yawan addu’oi da dogaro ga Ubangiji, haka ya dawo baya yazo dai dai gurin yayi parking d’in Motar shi ya fito, k’arisawa yayi ya tsugunna ya yaye hijab d’in ta da ya rufe mata fuska da sauri ya mik’e,Yana mai ja baya tare da dafa kanshi da yaji ya wani Sara mishi, a Ina ya San wannan fuskan shi kuwa yayi yayi ya tuna ya kasa haka ya kinkimeta yasa ta a Motar shi ya dawo ya d’aukar Mata jakan ta yasa mata, yaja Motar shi suka fara tafiya.
Zaune take da wasu matsiyatan Kaya da su gara babu ta d’ora kafa d’aya kan d’aya in da zuk’a zuk’an Yan mata ke ta kaiwa da dawowa a falon suna shirya ma Masoyin Hajiya Abinci, wata budurwa ce da bazata wuce shekara Sha bakwai ba ta iso ta duk’a tare da mik’a ma ta wayar tana mai cewa “aunty ana Kiran ki a waya. Tana gama fad’i ta tashi ta tafi, dai dai lokacin da wayar ta k’ara ruri Alamun wani Kiran Yana shigowa, d’auka tayi ta Kara a kunnen ta “hello Suwaiba ya ake ciki komai yayi normal,? Ina Masoyi Kuma.?
“Eh baby komai Normal mun kusa isowa ma gidan yanzu haka, Masoyi Kuma gashinan Yana tuk’i.
“Ok sai kun iso, ku kula da kyau fa Koda nasan Masoyi ai baida matsala.
*************************
JOS
Hajiya na shiga ta rungume Dija tana Fad’in “Alhmdulillahi Allah Kai ne abun godiya.sannu Dija kinji, Mallam yau zaka Sallame mu koh.?
“Eh insha Allah Zan had’a muku wasu Magungunan da na shafawa da su hayaki da sabulun wanka duka, da Wanda zata dunga Sha da naci da Abinci.
Bayan Mallam ya Gama ma Hajiya bayanin Magungunan da ya basu sannan ya k’ara da cewa “karta dunga Zama ba Alwala sannan ta yawaita karatun kur’ani ko sauraro. Godiya tayi Mai Sosai suka kama hanya don komawa gida Hajiya sai jera ma Dija sannu takeyi, ita ko Dija sai binta da kallo takeyi tana mamakin wacece wannan matar.?
*************************
Hajiya ne ta fito hannun ta d’auke da tasbaha tana tasbihi, don ita ta kasance Mai yawan ibadu.
Sannan yawan yin Tasbihi na k’ara kusan ta bawa Zuwa ga Ubangijin sa, ma’ana  Subhanallahi wabi hamdihi subhanallahil Azeeem.
Wata Yar dattijiwa ne ta shigo falon tana mai gai da Hajiya tare fad’in “Allah ya bayyana mana Dija hajiyan mu, fara mai farar zuciya. Sosai Hajiya Jiddah taji dadin Addu’a Mama Hansai, har tana Murmushi jerin fararen hak’oran ta sun bayyana cikin sassanyar Muryan ta mai d’adin tace “Ameen ya Allah Hansai nagode Sosai, har kin shigo,? Ya iyalan naki.?
“Lafiya lau Hajiya Suma suna miko gaisuwa da fatan bayyanar tauraruwan mu, don Ina ji a jikina ta kusa Bayyana insha Allah.
“In Allah ya yarda kuwa Hansai don nima Ina ta mafarkin ta, Allah dai ya kawo mun ita cikin Aminci.
Haka dai suka wanzu suna ta maganar bayyanar ta, don in har kana son kaga hiran Hajiya da farin cikin ta ka kawo Mata hiran y’ar ta masoyiyar ta, to zaku jima kuwa Kuna hira.
*************************
MAIDUGURI
Sosai Bintu tayi b’arna a gidan daga dare Zuwa safe. Kowa ka kalla a gidan Yana cikin tashin hankali duk da rashin Mutuncin da Bintu take ma Ma’aikatan nata bai hana sun tausaya mata halin da take ciki ba. Don duk mai Imani ya gan ta sai yayi kuka, ga ciki haka dai suke zaune suna kallon ikon Allah,
Alhaji Bukar bai iso Maiduguri ba sai Sha d’aya na rana,tun a hanya yayi ma likitan shi waya ya sameshi a gida Yana Isa gida baiyi ta kan kowa ba ya ciccibo Zahra ya kaita bangaren shi ya kwantar da ita, kwata kwata ya kasa fita ya barta ji yake yana mata wani irin son da zai iya rasa komai nashi a kan ta. Soyayya irin ta y’a da Mahaifi, doctor ne ya shigo da sallama. “Yauwa Doctor ka dubamun ita mai ke damun ta,? Ya fad’i haka cikin damuwa.
“Karka damu Alhaji insha Allah zata samu lafiya. Dubata ya farayi bayan ya kammala ya kalli Alhaji yace “Alhaji muje falo ko. komawa falo sukayi suka zauna, “Alhaji ba wani matsala ke damun ta ba illah maganin barci da aka bata yayi mata yawa Saboda yafi karfin jinin ta, zata Kai tsawon kwana biyu tana barci kafin ta farka, Amma akwai Alluran da Zan mata yanzu zai karya maganin zata farka nan da Awa goma insha Allah.
“Ba damuwa Doctor ayi mata indai kasan ba Abun da zai same ta.
“Ba abunda zai faru insha Allah.✍️✍️✍️✍️✍️
Jumma’at Kareem 💝💝 to you Masoyana
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍🥰🥰
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE  24
Yana zaune cikin d’aki ya tasa Zahra a gaba ya kasa fita ko nan da falo ne, Sallah ma a d’aki yayi Yana mai Addu’a Allah ya farfad’o mishi da ita.
Ji kawai yayi an hankad’o kofa ba ko Sallama, da sauri ya mik’e daga kan darduman Sallah Yana mai kallon Yagana da ta koma tamkar Mahaukaciya ga wani irin rama da tayi.
“Hajiya ai da kin bari nazo basai kin….. ta katse Mai maganar da yake Shirin yi ta hanyar fad’in.
“Kaga dakata Alhaji..! Wato Ciwon y’ata bai dameka ba ance mun tun Sha d’aya ka shigo gidan nan d’auke da budurwan yarinya, dama cin Amana y’ata kakeyi,?  Shine bari kazo har gida ma kowa ya gani. Yau ko sai na illata karuwar yarinyar da kazo da ita Mai budurwan zuciya kawai. Tana gama Fad’in haka ta juya aguje kaman Mahaukaciya, shiko Alhaji Bukar rasa ma Mai zaiyi yayi Saboda shi mutum ne mare son tashin hankali gashi Bai iya fad’a ba. Bai gama tunanin da yakeyi ba ya hangi Yagana da tab’arya zata kwala ma Zahra, Ai Bai San lokacin da wata zuciya ta zo mishi ba ya finciko Yagana ya tsinka Mata mari, dai dai lokacin da Zahra ta Farfad’o tana Fad’in, “Daddy don Allah karka k’ara tafiya ka barmu.”
Gaba d’ayan su juyowa suka suna kallon ta don ta tashi ta Zauna.
A matuk’ar firgita Yagana ta yarda tabaryan tana Nuna Zahra da hannu “Fadimatu mai ya dawo dake gidan nan.?  Alhaji wallahi bamu San komai ba akan Abun nan, Fadimatu kiyi magana da fatan dai baki fad’a ma Alhaji komai ba. Ai da gudu Yagana ta fita d’akin sai gurin Boka.
*************************
JOS
Sosai Hajiya ke ji da Dija, tana bata kulawa Sosai har yanzu Dija ta fara sakin jiki da Hajiya don yanzu har magana takeyi mata Amma ba sosai ba.
Sai dai wataran tayi ta ma Hajiya kuka tana Kiran Baby na, da k’yar Hajiya zata lallasheta.
Bayan sati d’aya Hajiya ta shirya Dija tsaf don suje su dubo y’ar uwan ta Wanda ita k’adai ta rage mata a duniya gashi ita Allah bai bata Haihuwa ba shiyasa take matuk’ar son Dija. “Hello rabin jiki yau fa Ina Nan Zuwa Zan kawo miki y’ata da nake ta baki labari Wanda nace Miki tana fama da matsalar tab’in hankali Amma yanzu taji sauki fa. Wallahi kuwa duk shekarun Nan Kuma baki tab’a ganin ta ba, kedai bari kawai ni sai tana mun Kama da Aunty Fad’imatu, bari dai sai munzo Zaki gan ta.
*************************
ABUJA
Zagaye ta takeyi tana tafi fuskan ta d’auke da Murmushi, “Mamin mu kenan Yar Dubai, Ina Mai tabbatar miki da baki can-canci Zuwa Dubai ba da K’auyen Zullum kika dace, bayan  na karya kafafuwan ki sai kije ku had’u da kanwar taki Asabe take ko wace,?
Wahalalliyar Uwar ku Wanda Bata iya tarbiya ba tayi jinyar ku, da shi Uban naku da yake k’okari shi uwar ku na warware wa, ok kar in cika ki da Surutu Hajiya Laurat kin San nasan komai, ni Yar k’anwar ki Asabe ce Wanda ta haifeni a yawon ta Zubar d’in ta, ta Kuma tsallake ni ta tafi gantalin ta Legos bayan ta tafka wani b’arnan a gidan da take aiki, bayan taje Lagos duniya tayi mata juyin Masa ta dawo da cuta kala-kala Wanda Uwar ku take jinya, nasan baki San ta dawo ba Koh,? We’ll dama bazaki sani ba tunda rabon ki da K’auyen tun lokacin da Daddy ya matsa kuje shine kuka d’auko ni kikayi mishi karyan cewa Uwa ta ta rasu, a hanyar ku ta dawowa kuka tsinci Zahra, shine kika Had’a kika raine mu tare, yayin da ki fifitani a kan ta ni Kuma baki San hakan na matuk’ar b’atamun rai ba, don duk duniya ban da Daddy sai ita sai Yaya Sadeeq sune mutanen da nafi so, Saboda haka a yau Zaki fuskan ci hukunci daga gurin Baby Khausar d’in ki🤣.
“Masoyi.”
“Na’am Masoyiya ta.”
“A sallami Suwaiba jirgin su ya kusa tashi, sannan a dan kiramun Samuel yazo ya dan karyamun kafafuwan tsohuwar nan yanda bazazu Kara wani Anfani ba.
“Haba Khausar yanzu da Abun da Zaki sakamun kenan, Mami ta fad’i haka cikin kuka Wanda tun da Khausar ta fara magana tayi suman wucin gadi.✍️✍️✍️✍️
🤣🤣🤣🤣🤣🤣Wlh yau tsokana nakeji shiyasa nayi Dan wannan page d’in
In kuna son kari anjima ku taimako da Maltina da Madara🤪🤪🤣🤣🏃🏃🏃
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰🥰💖
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE   25-26
JOS
Hajiya da Dija sun Isa gidan Hajiya Jiddah, sun shiga falon ba kowa sai Karan AC da TV da yake aiki.
Dattijuwan mai aikin gidan ne ta fito tana ma Hajiya sannu da zuwa, had’i da ajiye musu drinks a faranti da ta d’auko tare da fad’in “Hajiyar na ciki bari a Kira muku ita.
“Barshi bari mu k’arisa cikin kawai, Hajiya ta fad’i haka had’i da kamo Hannun Dija suka haye sama, ita Kuma Mai aikin ta koma kitchen.
Sun shiga d’akin dai dai Hajiya Jiddah tana Shirin Mik’ewa ta fito, “kice mun kun iso ma, Ina y’ar tawa,? Kin San tunda kikace mun tana Kama da Aunty Fad’imatu na kosa in……maganar ce ta kasa k’arisawa sakamakon ganin jidda da tayi, jikin ta har Yana rawa tana Nuna ta da hannu,,,,, “Alhmdulillahi ya Allah 🙏 ka Anshi Addu’a ta ka dawo mun da d’iyata gida,  Dija kece? Da sauri ta k’ariso ta rungume Dija. Gaba d’aya Hajiya kan ta ya kulle ta tsaya kallon ikon Allah.
“Yar uwa ta Ina kika samo ta,? Tsawon shekarun Nan kina tare da ita ban sani ba, garin ya hakan ta faru.?
“Yar uwa ta labari ne mai tsawo mu zauna.
“Shekaru Ashirin da d’aya da suka wuce na fito Ina Shirin bud’e rumfa Abinci na ga hadari ya had’u sosai, Ina bud’ewa ruwan sama na b’allewa haka na d’auki lema na dunga kaiwa da dawowa tsakanin gida da rumfa ta, kawai na fito na k’arshe da yake lokacin gari bai gama haske ba kawai sai naji na buge mutum da tukunyar da na ajiye, har naji tsoro Sosai da na haska sai Naga wata a kudundune tana ta rawan sanyi ga ruwa Yana ta dukan ta, Nan da nan na ajiye tukunyar na kamo ta muka shiga rumfa na zaunar da ita. Fita nayi naje na samo Mata wasu Kaya a gida Nan fa ta kafe bazata cire jikakkun kayar ba, sai ta nemi ma da ta gudu, haka na hakura na kyale ta sai na kunna mata wuta na kawo kusa da ita ko ta rage rawan sanyin, tana zaune ni Kuma Ina ta aiki na har yaran da suke taimaka mun suka zo, bayan mun gama Abinci ne Naga tana ta kallon Abincin da Alamu Kuma akwai yunwa tattare da ita, sai Na zubo mata Abinci cikin flate da ruwa na kawo mata sai naga ta bini da kallo ita bata karb’a ba ita bata dai na kallo na ba. Sai na ajiye mata na tafi na cigaba da aiki na, bayan anjima da dad’ewa na dawo naga bata ci ba ga Alamu tana son ci Amma bata San yanda zata cin ba don har yanzu kallon Abincin take, Zuwa nayi na zauna kusa da ita na debo Abinci na mik’a mata Nan ma kallo na ta tsaya Yi, sai da na bud’e bakin ta na zuba mata, shima bata son yanda zata tauna ba balle ta had’iye, in tak’aita miki Yar uwa har cin Abinci sai da na koya mata, na tanbaye ta sunan ta sai tace mun Dija tun daga nan bata k’ara magana ba, sannan ita haukan nata basa son gida duk yadda nayi k’okarin shiga da ita gida to sai nayi wata d’aya ban k’ara ganin ta ba, haka muka dunga rayuwa da ita da dad’i ba dad’i wataran sai in shafe wata uku ban gan ta ba haukan ya tashi kenan haka Zan ta bi lungu da sako Ina cigiyar ta, Amma haka Zan dawo ban same ta ba inyi kuka in share hawaye, Saboda tun ranar da naga yarinyar nan Allah ya jarabceni da son ta, Ashe kina da alak’a da ita, Yar uwa ki bani Labarin meye alakar ki da ita don ni dai a iya sanina baki da wasu y’ay’a ban da Habi da ta Auri dan gidan Aunty Fad’imatu Wanda mu duka mun San basu duniya.
*************************
“Tabbas Yar uwa Ina ji a jiki na wannan yarinyar Aunty Fad’imatu ce, wata rana naje Maiduguri kamar yadda na Saba zuwa domin in Kara duba wa ka anji Labarin wani daga cikin Ahalin mu,? Kamar kullum dai haka na dawo ba ko Labarin so ko Mai Kama da su, muna tafiya mun kusa fita cikin garin Maiduguri Naga kamar ana tare mu, lokacin Kuma Asuba ce to kin San yanayin hanyar garin namu sai a hankali, driver na yace mu wuce kawai haka Yan ta’addan nan keyi su samu su farma mutum dai dai munzo wucewa ta gaban wacce take tsayar damu din, na ce ma driver na ya tsaya muji me take so ba don yaso ba ya tsaya, fitowa dukan mu mukayi muka k’ariso gurin ta “Baiwar Allah lafiya Ina Zaki da wannan tsohon ciki haka ga kaya.?
Fashewa tayi da kuka tana mai durkusawa bisa gwiwan ta, “don Allah Mama ki taimaka mun, Inna koma gida kashe ni zasuyi dani da Abun da ke ciki na.
Ina jin haka nace ma driver na yasa Mata akwati Nan ta a boot, ni Kuma na kamata muka shiga Mota, bayan mun Isa gida da kwana biyu ta kwashe duk Labarin ta ta sanar da ni anan na fahimci cewa tabbas ita din jinin mu ce, don dai mu di’n mun dai na Zumunci da Yar uwan mu ta sanadiyar Mahaifiyar mu da ta kwaso mu ta gudu da mu Jos kasancewar ta ita Yar Jos ce, sai muka tashi bamu San wasu dangin mahaifin mu da yawa ba, sai Yar uwan mu guda d’aya Wanda muke uba d’aya Mace Mai son Zumunci tana Aure ita a Maiduguri ta Auri wani Babban soja inda ta haifi Yara uku biyu Maza d’aya Mace itace Auta Wanda tun da aka haifeta bamu tab’a ganin ta ba Saboda lokacin mun dai na zuwa gurin Yar uwan mu Saboda sabanin da muka samu da ita akan Auren yarinya ta da yaron ta, a haka Kuma sai da akayi Auren ni Kuma a lokacin bana so na fison ta Auri wani Dan uwan Mama na, haka ta dage sai da ta Auri dan Yar uwa ta tun daga nan muka yanke Zumunci da su, bamu k’ara Neman su ba sai wani fad’a da akayi na bokon Haram muka je nida Yar uwa ta muka tarar an Kona gidan su ance kawai an wayi gari ne aka ga gawar Mijin ta da wasu a gidan Wanda ake kyautata zaton sune, haka muka ci kuka muka dawo gida muna Nadaman Abun da muka aikata.
Dija taci kuka yayin da su Hajiya ma suke ta kuka gaba d’aya suka rungume Dija suna jin wani son ta a Zuciyar su Saboda irin Soyayyan da suke ma Mahaifiyar ta Mace Mai son Zumunci da Yan uwan ta.
“Tabbas a lokacin da kuke tunani Mahaifiya ta da yan uwana basu Mutu ba, mahaifin mu dai ya mutu a wani yak’i da sukayi da Yan Boko Haram, lokacin da aka zo Kona gidan lokacin Yaya Sadeeq shi Yana zaune a Abuja ne yana aiki har da matan shi suna can da Zama, ranar yazo Maiduguri, kawai ji sukayi ana hayaniya a kofar gida Yaya Sadeeq ne ya lek’o kawai sai yaga Yan ta’adda ne suke Shirin Kona gidan su, to dama akwai wani kofa ta baya haka su Umma da yayyina biyu suka d’auke ni lokacin Ina da shekara goma a duniya muka fice ta kofar baya, haka su Umma suka dunga cin gudu ga k’aran Harbe harbe, kawai basu an Kara ba suka ji harbi ya sauka a Kai na dai dai hannu na, ihun da nayi ne da Karan harbin ya k’ara gigita Umma na, ni Kuma bayan an harbe ni kawai na tafi luhh, Sosai Umma ta saka kuka tana girgiza ni tana Kiran sunana, Amma ina basu ankara ba Umma tayi tuntub’e muka fad’i nida ita take ni na dunga gangarawa Rami ga ramin Mai Matuk’ar zurfi, gashi wad’an Nan mutanen sun kusa kamo su, haka Ina kallon su Umma suna kallona suka tafi suka bar ni. Ta k’arisa maganar Tana kuka, cigaba tayi da cewa “tun daga Nan ban Kara sanin inda Kai na yake ba sai bayan wasu kwanaki Wanda ban San ko tsawon kwana nawa bane na farka na ganni a wani had’add’en d’aki ga hannu na da bandage jiki na duk naji rauni, da gudu naji wata Matashiyar yarinya ta fita tana cewa Momy ta Farfad’o, haka suka shigo suna ta mun sannu, haka nayi jinya ta har na warke, na cigaba da rayuwa a gidan cikin kulawa da Soyayya tamkar Yar gidan tabbas su Momy sun min karamci, ana cikin haka yaron Momy ya d’awo daga K’asar India inda tun da ya ganni yace shi ya samu matar Aure.
Haka akayi mana Aure muka tare cikin kulawa da k’aunar juna inda Hanifa kanwar miji na take matuk’ar Sona Koda yaushe tana gida na indai Mijina baya Nan har Momy na mun tsiyar na kwace mata Yar Auta, haka muka Kai shekara biyar bamu tab’a haihuwa ba, tun Abun bai damun mu har ya fara damun mu, Momy ne ke lallashin mu, kwatsam aka ce Hanifa zata tafi karatu America, haka muka Yi kukan rabuwa tamkar kafin ta dawo d’aya zata mutu a cikin mu.
Tushen bakin cikin______________,
Sanadiyar wani rashin lafiya da nayi aka d’auko mun wasu Yan aiki su biyu da Yar Dattijuwa da budurwa Wanda zamu zo sa’a d’aya da ita suna mun Yan aikace aikace Amma ban yarda sumin girki ba,  Ashe Ciwon da nake tayi ciki gareni tunda masu aiki na suka fahimci haka sai Naga gaba d’aya sun canza, iya k’okari na Ina kyautata musu Amma Basu taba gani su burin su in bar gidan yayin da Asabe take tuggun in bar gidan ta Auri Alhaji, ita Kuma Yagana burin ta in bar gidan yarinyar ta ta Auri Alhaji, Momy kullum cikin zuwa gidan take domin dubani, ta dunga tanbaya ta Mai nake so, Mai ke damuna, ni har kunya ma nake ji, bayan ciki na ya Kai wata bakwai ne na dai na ganin  Asabe na tanbayi Yagana tace mun ai Asabe ta tafi k’auye bata da lafiya, kwatsam ranar wani safe Ina kwance sai ga Asabe tazo mun da ciki kato kamar nawa ta tsayamun a Kai “Aunty ki tashi kiga aikin da Mijin ki yayi mun don shi yayi mun ciki Kuma Ina haifewa Zan ajiye Miki ki had’a ki Rai na da naki don ita ma gidan uban ta ne, Mik’ewa nayi da k’yar na nuna Asabe da yatsa nace “karya kike yi Asabe Mijina yafi karfin ki, na yarda da miji na Ina gama Fad’in haka na shige d’aki na fad’a gado na fashe da kuka zuciya ta tana ta mun wasiwasi akan al’amarin ranar ko Alhaji ya dawo bayan na had’a Mai ruwan wanka na fito naje kitchen don in sama Mai Abun da zaici, don duk halin da nake ciki ban barin masu aiki suyi ma miji na girki, na Fito rike da farantin Abinci don yace in kawo Mai ciki ne bazai ci a Falo ba, dai dai na Kai benen k’arshe naga Asabe ta fito daga d’akin shi taci uban ado cikin ta ya fito yayi Mata kyau kasancewar Asabe shuwa Arab ce farace Sosai don ta fini fari, Nan da Nan naji wani kishi ya turnik’eni Amma sai ban nuna Mata komai ba. Murmushi ta mun tayi fari da Ido tace mun, “Hajiya naje ma rabin Rai na sannu da zuwa ne kuma su gaisa da yaron shi don nasan Namiji Zan Haifa Kinga kuwa mu ke da gida. Ta k’arisa maganar Tana murmushi ta wuce ta tafi, wani kuka ne yazo min Amma haka na danne na shiga D’akin da pant da breziya na fara cin karo a kan gado, ajiye Abincin nayi na juya da sauri ban Kara komawa d’akin ba Wanda hakan shine shiga na d’akin na k’arshe inda da dare Ina cikin barci na naji ihu a cikin d’aki na da sauri na tashi na kunna fitillar d’aki wani mutum na gani kwance kusa Dani daga shi sai gajeran wando ga Kaya Nan ya Zubar ko Ina, da sauri na mik’e jiki na na rawa dai dai lokacin da Alhaji ya shigo, “dama cuta ta kikeyi Fad’imatu, bazan tab’a yafe Miki ba, haka nake binshi nake rokon shi ya saurareni yaki saurara na wayata ya jefo mun yace wad’an Nan text din Kuma fa daga Ina suke.?  Jikina na rawa na d’auki wayar Ina dubawa text ne kala kala har Wanda Wai ni na tura Ina fad’a ma wani Ina d’auke da cikin sa, Amma zance na Alhaji ne, haka na duke a gurin Ina kuka Sosai, ana haka sai ga Momy tazo naje da gudu na rungume ta a tunani na Zan samu sauki da fahimta a gurin Momy, ga Mamaki na sai Naga Momy ta hankad’e na fad’i Haka Momy ta rufe Ido tamun korar kare ita da yaron ta suka ce inje in nemi uban ciki na Kuma har Abada kar in k’ara dawowa gidan nan, haka da k’yar suka barni na kwashi wasu kayan da sauran kayan jarirai da Alhaji yasa don ba Abunda ba’a siyama baby ba har d’aki musamman aka gyara ba Abun da ba’a sa ba na yarinya, yace in har na haihu zai Sama ta Fad’imatu Zahra zamu dunga ce Mata Zahra Saboda sunan Momy ne nima sunan Umma na ne Kuma suna na, haka na fita Ina kuka Ina waigen d’aki na Ina fitowa harabar gidan Naga Asabe da Yagana suna shewa suna farin ciki, “Allah ya raka taki gona, kafan gaba ya cin ma na baya. Ahayye duka suka Kara tafawa, girgiza Kai na nayi na tafi bance musu komai ba.
Bayan na fito ne na lura wasu mutane na bina shine fa na tare Abun hawa na hau muka dunga yawo na rasa Ina zani shine ya sauke ni a gurin da kika ganni.
*************************
“To yanzu Ina yarinyar an haife ta,? Kuma a Ina aka haifeta anan gidan koko ta bar gidan Nan da ciki,?
“Eh ta haifi santaleliyar yarinyar ta Mace Mai Kama da ita, bayan zuwan mu da sati uku, komai nayi ma yarinyar an samata suna Fad’imatu Zahra, inda bayan haihuwar Zahra da wata uku aka nemi Dija aka rasa bata ba Dan Akwatin Zahra da kayan ta masu Muhimmaci yake, irin su dan kunnin diamond da mahaifin ta ya siya Mata da wani katon envelope na tarihinta da Dija ta zauna ta rubuta Wai Koda ta mutu a ba Zahra ta gani, had’e da hotunan ta da na yayyin ta Dana ba Dija da katin haihuwar Zahra duka Yana cikin karamin Akwatin, kawai Neman ta nayi da Akwatin na rasa, nayi cigiya Sosai har gidan Radio bata ba Labarin ta, haka na hakura na zuba ma sarautar Allah Ido.
“Kawai Ina kwance cikin dare naji kaman ana kirana, kawai na tashi na had’a kayan Zahra a karamin Akwatin na goye ta na fita, tun daga Nan ban k’ara sanin inda Kai na ke ciki ba, ban San yanda akayi na rabu da y’ata ba kila ma ta mutu yanzu, Allah sai ya saka mun tsakanina dasu Yagana sun cutar dani. Kara rungume ta sukayi suna Mai jin tausayin Yar taso tabbas tasha wahalar rayuwa.
“To meyasa kike ce Mata Dija Yar uwa,?
“Lokacin da na tsince ta ne tace mun sunan ta Dija…………..,
*************************
ABUJA
Ba Imani ba komai James ya karya kafafun Mami Kuma irin karayan Nan rugu rugu Haka Mami tana kuka tana ba Khausar hakuri Amma ko kallon ta Khausar batayi ba ta juya ta shige d’aki ta fad’a gado ta fashe da kuka, “Mami kiyi hakuri Dole ne ki fuskanci wannan hukuncin. Haka ihun Mami na Azaba ya karad’e gidan, bayan an gama la’anta Mata kafa ne suka d’auketa domin tafiya da ita, sai ga Khausar ta fito lokacin kuwa Mami ta sume Saboda Azaba. Sawa tayi aka watsa ma Mami ruwan sanyi da aka fito dashi daga fridge. Firgigit Mami ta Farfad’o tana had’a wani uban zufa.
“Mami kiyi hakuri dole ne in hukunta ki akan laifin ki, duk da halin ki Ina son ki, in kinje ki gaidamun da uwa ta da Kaka ta, Zan dunga lek’owa muna gaisawa, ga dubu d’ari nan ku dan rage zafi……….✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🥰🥰🥰😍😍😍😍😍
Yau dai nasan na biyaku Saboda haka Inga comments da yawa..
In har banga comments ba sai wata satin Zan Kara yin wani posting 🤪🤪.
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰🥰.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Wanna page d’in sadaukarwa ce gareki Kaka Raliyatu duk Wanda  ya karan ta yasa ta a Addu’a 🙏🙏.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE  27
ABUJA
“James ku dawo da ita.
Dawo da Mami sukayi, “gata Hajiya.
“Mami Ina kika Kai Yaya Sadeeq,? Tabbas anan na gaza cikawa Yan uwa na burin su na Auren juna, Tabbas kin San inda Yaya Sadeeq yake ki fad’a mun yanzun Nan.
“Baby ko kashe ni zakiyi bazan tab’a fad’a Miki inda Sadeeq yake ba, domin ta haka ne nima Zan kuntata miki kamar yadda kika kuntata mun.
“Ok shikenan Mami karki fad’a Amma ki sani duk wani motsin ki da zakiyi a kan Ido nane. James ku tafi da ita, sai nazo k’auyen.
*************************
MAIDUGURI
Zaune yake ya tasa Zahra a gaba ta Zama Mai Tamkar Madubi a hankali tunanin shi  na shekaru suka fara dawo Mai, Wai Ina Fad’imatu take, ko ta haihu. Da sauri ya mik’e zai fita dai dai lokacin da Momy ta shigo d’akin hankalin ta a tashe, “Bukar Ina y’ata Fad’imatu da Abunda ke cikin ta kullum sai nayi Mafarki da ita tana cikin wani Hali ita da y’ar da ta Haifa……maganar tace ta mak’ale lokacin da tayi Ido hud’u da Zahra. “Bukar wacece wannan a Ina ka samo ta irin su d’aya da Fad’imatu.?
“Momy wannan tanbayoyi haka wanne kike so in Amsa Miki, mu zauna tukun na. Zama sukayi kowa yayi shiru da Abunda yake sak’awa a ran shi, kawai ganin ta sukayi ta fad’o d’akin ko Sallama babu tana kuka Sosai. “Momy Ina Zahraty meyasa tun da na dawo K’asar Nan shekara kusan Ashirin da biyar ban tab’a tunawa da ita ba sai yau, waccan da take Fallon take ta Hauka wacece ita,?
Duk maganar da sukeyi Zahra na tsaye na kallon su cikin Mamaki to su suwaye wad’an Nan mutanen Ina Mamin ta ita da suke Asibiti Mai ya kawo ta nan,?  Karfin halin tanbayar su tayi tace musu “Su waye ku Nan Kuma inane.?
Gaba d’aya juyawa sukayi suna kallon ta an rasa Wanda zai bata Amsa, wayar Hajiya Hanifa ne yayi k’ara da sauri ta d’auko wayar ta kara a kunnen ta “Hello Jannat kin iso ne,? Ok Na turo Hanif ya d’auko ki Yana Airport d’in. Tana gama Fad’in haka ta k’arisa ta kamo hannun Zahra ta zaunar da ita kusa da su, sai ya kasance sun sata a tsakiya.
“Yammata ya sunan ki.?
“Sunana Fad’imatu Zahra Habibullahi Amma ana kirana da Zahra. Ku su waye Nan Kuma a Ina nake Ina jakata kuma.?
Har rige-rigen maimata sunan sukeyi  “Zahra Ina Maman ki take.?
“Mama ta tana Asibiti a Abuja sakamakon gobara da mukayi ta k’one, ni baku Amsa mun tanbaya ta ba ni Mai ya kawo ni nan.?
Duk yanda akayi ya tsince ta Alhaji Bukar ya bata labari, kuka ta fashe dashi tana Fad’in “Ina jaka ta, Hajiya Hanifa ne ta mik’a mata jakar ta fara zazzage jakar wayar ta ne ta fad’o tare da wata farar envelope, da sauri Zahra ta d’auki envelope din ta fara karantawa.
          “Zahra kiyi hakuri ban so nayi Miki butulci ba na gujeki Amma burina yafi mun ke, ki mance dani a Rayuwar ki karki k’ara tunawa da ko Mai Kama Dani.
Tana gama karantawa ta fashe da kuka, “shikenan ni yanzu Banda kowa a duniya, Mami ta gudu ta barni bayan na gama d’awainiya da ita.
Jawo ta jikin ta Momy tayi ta rungume ta, tace “karki damu yarinya ki d’aukeni tamkar Kakan ki wannan Kuma ki d’auke ta matsayin uwa, shi Kuma wannan a matsayin uba, dukan su da kike kallo y’ay’a nane Kuma zamu rik’e ki Amana kinji, yanzu ki bi Maman ki ku tafi gidan ta don bazai yuwu ki zauna a Nan ba, Kuma ga yarinyar ta can ta dawo daga kaduna taje bautan k’asa baku wuce sa’o’in juna ba, duk da nasan Zaki girmeta ita d’in girman dare d’aya ce, Amma fa zakiyi hakuri da sarkin k’orafi Dan uwan haihuwar tane da yake su Yan biyu ne, Kuma shidin akwai son girma…. “Kai Momy kin zauna sai ma yarana sharri kikeyi….”karbi nace tayo ma Mama Hanifa dakuwa, yo karya akayi Mai Yana ji da Kai k’ato kaman murhu.
“Kinji y’ata tashi mu tafi nasan yanzu haka su Hanif sun koma gida.
“Momy Mai yasa bazaku barta a Nan gidan ba, ji nake in kuka tafi da ita Zan iya shiga wani hali. Alhaji Bukar ne yayi wannan maganar da tun da suke magana bai ce komai ba sai yanzu.
“Bukar kayi hakuri sai gidan ka ya kintsu tukun Zan iya dawo da Fad’imatu nan don Ina jin tsoron Abun da zai Kara faruwa, ku tashi muje. dukan Mik’ewa sukayi ba Wanda ya k’ara magana suka fice a falon yayin da Alhaji Bukar yaji kamar sun tafi Mai da Rayuwar shi ne gaba d’aya.
Suna fitowa suka tarar da ana rirrik’e Bintu tana fisfisgewa tana cewa wlh sai na tona Asirin Yagana kin kori Fad’imatu don in Auri Alhaji Koh,wani k’ara ta saki.
Maganar da tayi dai dai su Momy sun fito Kuma taji Mai take fad’i, kawai ganin Momy sukayi tayi baya zata fad’i da Sauri Zahra ta rik’o ta, had’e Kiran Driver, da gudu driver yazo suka sa Momy a Mota mama ma  ta shiga sai Asibiti aka wuce da Momy.
*************************
K’AUYEN ZULUM
Inna Tasallah ne ta fito da buta a hannun ta zata bayi taga wasu samudawan mutane suna shigo musu gida ba ko Sallama. “Bayin Allah lafiya kuwa,,,,,maganar ne ta mak’ale lokacin da taga an shigo da Mami kafafuwa na lilo, “innalillahi wa’innah illaihirraji’un 🙆 Laure me Zan gani haka hatsari kikayi ne.?
Sudai suka jingine Mami suka jefa Mata jakar ta da wayan ta suka k’ara gaba.
Fashewa Mami tayi da kuka, “Innah Kinga inda rayuwa ta juya Mana baya koh.? Shiyasa ake cewa mutum yabi duniya a hankali, tabbas nayi kuskure Ina Asabe ta haifomin Masifa da bala’i  dama duk Wanda aka cema shege sai yace Uwar shi ba tayi komai ba, Asabe tazo ta fad’a mun waye uban Khausar,?
Rarrafowa Asabe tayi ta dafa bango ta fito a dudduk’e, zaro Ido Mami tayi tana Nuna Asabe “meya sameki Asabe.?
K’arisowa tayi ta rungume Mami suka ci kukan su, sannan Asabe ta Bata Labarin Abunda ya faru da ita, itama Mami ta Bata Labarin komai. “Yanzu kina nufin kice mun Khausar ta karya ki,? Ta fad’a cikin Mamaki da jimami, Tabbas Khausar bata Yar a k’asa ba domin Baban gagarumin Dan fashi ne mare Imani gashi matsafi yanzu haka ma shi ya dawo dani gida daga Legos tun daga haka bai k’ara waiwaya ta ba, Saboda a yanzu Banda wani sauran Anfani a gurin shi.
“Tabbas Khausar bata Yar a k’asa ba Ashe magaji mafiyi, yanzu haka zamu cigaba da rayuwa a haka,?
“Ba gara ke ba ma kinyi Aure Niko da na biye ma Yagana na tashi a tutar babu, Kuma Alkawarin kud’ad’en da tayi mun Taki cikawa. Ina son inje in tona Asirin Yagana a gidan Alhaji Bukar Mai Dala. Zaro Ido tayi Mami tana Fad’in “yanzu Asabe shaidanancin naki har ya Kai wannan katafaren gidan,? Wanda kin San duk duniya anaji da mutumin nan, Tabbass kashin ku ya bushe.
“Uhmm yarinyar Yagana ne fa take Auren shi bayan mun Kori matar gidan.
😲Zaro Ido Mami tayi tana Fad’in “kina nufin wannan bak’ar  Yarinyar nan nata Bintu ita ce take Auren Alhaji Bukar d’in.?
Lallai kam Asiri yayi aiki, ya kamata kije ki kwance K’ullin da kukayi kuwa.
“In Allah ya so kuwa don yanzu Naga darasi a rayuwa ta, duk inda na zauna na tashi sai dai kiga gurin ya jike da ruwa Mai wari ga tsutsotsi.
“Ai naji Alama shiyasa duk na kosa ma ki tashi ki tafi.
*************************
Jeji ne da ya Amsa sunan sa jeji, Wanda wasu dogayen bishiyoyi da ganyayyaki suka tsagaye shi ga wadataccen Ni’ima a gurin inda ga wani k’orama  ruwan cikin shi k’ar-k’ar Yana ta gudu, wata K’yakk’yawan yarinya ne Zaune gurin ta saka k’afafun ta a ruwan tana wasa dashi, da sauri ta ciro kafafuwan ta tana kallon ruwan da k’yau, in har ba gizo idon ta yake Mata ba tabbas jini take gani a cikin ruwan nan, Bata Gama tunani ba ta hango kamar mutum a cikin ruwan, da sauri ta fad’a ciki tana wani iyo tamkar kifi Nan da nan ta Isa gurin da ta hango mutum din ciroshi tayi da k’yar, Nan ta fara Danna Mai ciki Nan da nan ruwa ya fara fitowa daga bakin shi, da sauri ta koma ta d’auko jakar ta ta fito da kayayyaki ta fara gyara Mai raunin da ke jikin shi, gani tayi kamar an yankeshi ne da wuk’a, Nan da Nan ta wanke Mai Ciwon tas ta d’aga shi ta jingina shi da jikin bishiya, Kara kunnen ta tayi saitin Zuciyar shi taji tabbas Yana aiki.
Kallon mutumin nayi da k’yau sai Naga tamkar Yaya Sadeeq fa..✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Yar mutan Zazzau ce 😍🥰🥰
Kar Wanda ya ban hakuri daga baya Inna cireka rashin yin Comments ya ja maka🙄😏…🏃🏃🏃🏃
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Wannan page d’in naku ne Masoyan Asali son so fisabilillahi tabbas Ina jin dadin Comments din ku Sosai.
Sister Adama
Maman Ahmad
My kakus
Sister Nafeesat
My sweet Aboki inkiyan ka sai fa na fad’a Saghiru bakano🤪🤪🤪
Da duk Wanda ban ambaci sunan su ba Kuma Ina yin ku irin Sosai d’in na love you Lodi Lodi 🤣🥰🥰💖.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE 28
A hankali ya fara bud’e idanuwan shi, sai dai dishi-dishi yake gani, yanayin gurin da ya ganshi ne yasa ya ware idon shi gaba d’aya.
K’okarin tashi ya Zauna yake yi Amma ya kasa tashi. Yarinyar da ta tsinto shi ne ta shigo d’akin hannun ta d’auke da wasu Magunguna, ganin shi ya farfad’o ne yasa tayi sauri ta k’ariso gurin gadon da yake ta ajiye farantin Magungunan a kan wani dan k’aramin teburi dake jikin gado. D’akin yake k’are ma kallo domin ya had’u an k’awata shi da wasu labulaye ga wasu shimfid’un kafet tamkar katifa masu launi da ban da ban ko wani lokaci canzawa sukeyi, ga wasu fulawowi da aka ma jikin bangon d’akin kwalliya dasu tamkar an shuka su sai bada wasu kalar kanshi suke, gadon da yake kwance ya kalla gado ne irin Mai rumfar nan an sa ma labulaye masu canza launi  irin shimfid’un kafet din d’akin, a jikin labulayen ga wasu kwayayen wuta suna haskawa suna d’auke wa, duk da d’akin ba wani girma da tarkace gado ne kawai sai wani korido da akayi mishi wasu decoration na fulawowi sai ya bada kofa Mai angle da zai Kai ka cikin koridon inda wasu kyawawan kujeru ne aka jerasu a gurin ga fulawowi gefe da gefen su ga wasu kyawawan tsuntsaye suna yawo a gurin suna ta rera wak’oki.
Sosai d’akin ya birge Sadeeq.
Hakan yasa tana ta magana bai ji ta ba, sai da ta tab’a shi sannan ya kalle ta, Magana ta k’ara yi Mai sai dai bai gane yaren da take yi ba, hakan yasa ya bita da Ido  da ta Kara magana sai yace ma ta, “ke ni bana jin Abun da kike cewa fa, ke waye Nan Kuma Ina ne,? Wannan duniyar bata yi Kama da duniyar Mutane ba don kema kanki wannan kyan naki ya zarce na mutane sai dai aljanu.
Tsayawa tayi tana kallon shi, duk da bata jin Abun da yake cewa sai taji gaba d’aya yaren da yayi Mata magana dashi ya burge ta, shidin ma gaba d’aya ya burge ta hakan yasa take ta kallon shi tamkar zata had’iye shi.
“Ke Wai lafiya kike ta kallona tamkar mayyah,?
Ya Allah Wai waye ni,? Mene suna na daga Ina nake.?
Motsi taji Alamun kamar ana tab’a kofar d’aki, da sauri ta tura Sadeeq ya kwanta ta rufe shi da wani tattausan blanket ta sauke duk wani labulaye na gadon kafin ta tashi taje ta bud’e kofar d’akin.
Wata K’yakk’yawar Mata ce take tsaye a bakin kofar da alama Mahaifiyar ta ce, tasha wasu Kaya tamkar Sari ta nannad’e jikin ta dashi har kan ta tayi mayafi dashi ga wasu zobuna da  sarka masu kyau da tayi ado dashi kafa da hannaye da kan ta Wanda ya ratsa ta tsakiyar kan ta a tak’aice dai tasha k’yau Sosai Kuma baza ka tab’a gane tsufan ta ba. Rab’awa tayi zata shiga D’akin y’ar nata, da sauri ta tare ta tana Fad’in  “Ummiyu ya haka Zaki shiga mun d’aki ba tare da izini na ba, kin San dai wannan babban zunubi ne da in Abbiyyu yaji zai iya hukun ta ki fa.
“Wai ke kibd’iyatu Mai kika d’auki kan ki ne a Masarautar nan,? Kar ki man ta nifa Mahaifiyar ki ne, Kuma tabbas Ina ji a jiki na da Abun da kike b’oye mun a D’akin nan, Kuma Mai yasa kika sallami Hadiman ki.?
“Meye matsalar ki da ni,? Bana buk’atar su Hadiman ne shiyasa na koresu, tana gama Fad’in haka ta shige d’akin ta ta kullo kofar ta bar Ummiyyo a  tsaye a bakin kofar.
Karkad’a Kai tayi tace “wlh yarinya Zaki zo hannu na sai Naga bayan ki a Masarautar nan tamkar inda Naga bayar y’ar uwan mahaifin ki ta bar garin Nan domin bana buk’atar kowa ya gaji sarautar Masarautar nan sai ni, ciki kuwa har da ke y’ata da na haifa da ciki na, don ban da Imani a kan Mulkin nan.
Juyawa tayi tana tafiya cikin isa da tak’ama.
Masarautar  Amrish kenan wani gari ne da ke kan iya ka da Maiduguri da Mali, Wanda Asalin su daga India suka taso,
Wani mutum ne da iyalan shi dan Yana yawon fatauci, Wanda yake shine shugaban tawagar,  suna da yawa ciki kuwa har da matan su da y’ay’an su, shi ya kasance Yana da Mata d’aya da Yara biyu Mace da Namiji, shi shugaban tawagar sunan shi Amrish yayin da sunan Matar shi Zinta sunan babban yaron shi Biju da k’anwar shi Safni. Sosai Amrish ke son yaran shi, Yana da wani Aboki Wanda ya kasance tamkar shine Wazirin shi, Yana da y’a sunan ta Amrita Wanda suke matuk’ar son juna ita da Bijay, in da kwata kwata Safni bata son ta Saboda Amrita ta cika rawan Kai ga rashin Natsuwa ga wulak’an ta na k’asa da ita, Wanda hakan na b’ata ma Safni rai kasancewar ta Mai Tausayi da son na k’asa da ita.
Abun da yasa Amrish ya tsabi su zauna a dajin nan Saboda guri ne tamkar dausayi ga k’oramu masu kyau da fulawowi masu k’anshi, a tak’aice dai guri ne Mai cike da Ni’ima ga K’asar Noma, shi Kuma mutum ne Mai Noma da kiwo da safara, hakan yasa ya kafa Masarautar shi anan kasancewar shi dama can jinin Sarauta ne shi a birnin Mumbai na India, bayan wasu shekaru Masu yawa Amrish ya rasu sai Matar shi Zinta da Bijay da yake mulkan Masarautar shida k’anwar shi Safni ita ce Waziriyan shi, yayin da yake Auren Amrita, har a lokacin ba jituwa a tsakanin Safni da Amrita, lokaci guda aka Nemi Safni a ka rasa tun daga Nan Kuma ba Wanda ya k’ara tunawa da ita. A ka d’ora Amrita a matsayin ta, yayin da Mahaifin Amrita ke juya duk wani Akalan sarautar ta fanni y’ar shi da take Auren sarki yayin da Mahaifiyar sarki ta Zama tamkar Yar kallo a Masarautar, sai dai tun da aka haifi kibd’iyatu ta fara basu matsala don ita halin ta d’aya da Safni don har Kama ma suna yi tamkar ita ta haife ta, hakan yasa kwata kwata Amrita bata son ta, shi Kuma Bijay Yana matuk’ar son Kibd’iyatu Saboda kaman ta da k’anwar shi, Wanda bazai tab’a iya tanbayar Ina take ba.
Sanan su suna da wani doka a garin duk Wanda aka Kama ya shigo da bak’o kashe shi akeyi shi da bak’on, Kuma duk wani ahali na garin suna da wani tab’o a jikin su Wanda in har kana da alak’a da garin sai an haifo ka da wannan tab’on.
Wannan shine tak’aitaccen tarihin Masarautar Amrish.
Bayan kibd’iyatu ta koma d’aki ta tarar da Sadeeq ya mik’e Yana kallon agogon da ke d’akin Alamun lokacin Sallah yayi to yanzu ma Salloli na  kwana nawa ne a kanshi, to shi taya ma zai ma wannan Aljanar magana ta gane, turanci yayi Mata sai yaga ta maida Mai domin suna jin turanci kasancewar tana fita duk k’arshen shekara yawan bud’e Ido ta fi Zuwa k’asashen Turai, hakan yasa take da bud’e Ido fiye da Yan garin, ita Kuma ta kasance jaruma tana son wasan harbi da kibiya shiyasa tana yawan sa gasar duk k’arshen wata ita take cin gasar, da Kuma gasar tseren cikin Ruwa.
Maganar da ya Kara Mata ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.
Ta tanbayeshi da d’an karamin turancin ta Wanda Bata wani goge ba, “me kake so.?
“Ina son inyi wanka Kuma in Yi Sallah.
“Meye Sallah Kuma.?
Zaro Ido yayi Yana mai cewa “Wai baki San Sallah ba,? To me kuke bautawa.?
Yaye Mai wani d’an  guri tayi a D’akin kawai sai yaga wani d’an k’aramin gunki a ajiye, anyi Mai kwalliya da Zinarai.
Dama har yanzu akwai masu bautar gunki a duniya, lallai tabbas Akwai Abun da Allah ya tsara Mai shiyasa ya kawo shi gurin nan, dole yayi Anfani da damar shi gurin ganin sun dawo hanya madaidaiciya.
Yana cikin wannan tunanin yaji hannun ta a jikin shi ta Kama shi domin ya tashi, ji yayi Hannun ta Tamkar Auduga Saboda laushin shi, a hankali har ta Kai shi gefen Daman shi ta yaye labulen gurin kawai sai ga kofa ta Bayyana wani Abu ta matsa gefen kofan kawai sai ya bud’e shiga dashi tayi har cikin bayin, Haka ya zama tamkar d’an k’auye don tamkar ba a cikin Band’aki yake ba, k’ok’arin cire Mai Kaya takeyi nufin ta zata Yi Mai wankan, rik’e Hannun ta yayi yace ke mu a Addinin mu ba haka akeyi ba, babu kyau Mace ma ta tab’a Namiji Haramun ne, tsayawa tayi tana juya maganar a cikin ran ta, nunnuna Mai komai tayi ta had’a Mai ruwan wanka Wanda yaji turaruka da filawa, sannan ta fita ta bashi guri.
Wai su komai sai sun sa filawa ne lallai fure na da Muhimmaci a gurin su.
A haka har ya gama ya fito gani yayi bata a D’akin sai wasu Kaya masu k’yau da aka ajiye Mai a gefen gado da mayuka da turaruka sun Kai kala biyar, zaunawa yayi Yana shiryawa duk da har yanzu Ciwon hannun shi na mishi zafi, riga ya d’auka Yana Shirin sawa dai dai lokacin ta shigo d’akin, zaro Ido tayi ganin tab’on da ke kafad’ar shi da sauri ta k’arisa cikin d’aki tana mai tab’a gurin tab’on, ” a Ina ka samu wannan tanbarin,? Kai waye.?
“Wani tanbari Kuma,?  Ni Kai na ban San ko waye ni ba, Abun da kawai na sani ni musulmi ne, kaman Zan iya tunawa sunana Sadeeq.
*************************
JOS
“Tabbas Ni yarinyar Fad’imatu ne da yayyina biyu da Habibullahi da Sadeeq sai yanzu na tuna da wani Abun.
“To yanzu Ina zamu gansu,? Suna raye ko sun Mutu.?
Hajiya Jiddah ce ta fashe da kuka, Zan so in k’ara ganin y’ar uwa ta da y’ata d’aya da na haifa a duniya, yanzu ya zamuyi a gidan radio zamu sa cigiyar su ko ya zamuyi.?
“Addu’a ya kamata muyi da mik’a lamuran mu ga Ubangiji domin shi zai Bayyana Mana su, sannan mu had’a da cigiyar su. Sannan yanzu yaushe zamu Maiduguri,? Domin Dole zamuje mu samu Alhaji Bukar domin duk inda suke yanzu nasan Asirin da ke tare dasu ya karye.
“Yar uwa ta ba inda zamu domin ai su suka Kori Zahra a gidan su Saboda haka sai sun Nemeta da kansu.
“Shikenan Yar uwa ba damuwa duk yadda kika ce Haka za’ayi.
*************************
MAIDUGURI
Bayan an Kai Momy Asibiti ne, Mama Hanifa ta Kira yaran nata tace su same su a Asibiti sai su tafi da Yar uwan su da tazo, daga Nan su zo musu da Abinci da Abubuwan buk’ata.
Suna zaune sai ga su Hanif sun shigo lokacin Zahra tana Sallah.
“Wai Mama Mai ya samu grany ne?
“My Jannat kece….! Zahra ta fad’a lokacin da ta idar da Sallah.
Zaro Ido Jannat tayi taje da gudu ta rungume Zahra tana cewa “my sweet Zahraty Ina kika shiga Ina ta neman number ki baya shiga.? Ta fad’a cikin kuka……✍️✍️✍️✍️✍️
Nasan yanzu wani zai ce na sa shi a duhu, daga baya yazo Yana cikamun bakin Wai yasan Mai zai faru a k’arshe, alhalin Bai sani ba, Dole yayi hakuri ya biyo shugaban shi Yar mutan Zazzau ta warware K’ullin da tayi🤪🤪🤣🤣. Kowa yayi zagi a kasuwa, na feceeee🤣🤣🏃🏃🏃. Amma fa ba tsoro naji ba🙄😏.
Share
Comments
Like
Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍🥰.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
PAGE 29
MAIDUGURI
“Dallah Malamai a Asibiti muke fa kun wani cika ma mutane kunne da koke-koke kaman gidan mutuwa, sai ance ma mutum yarinta na damunshi yace shi ba haka ba mtswwwww!.
Cewan Hanif da tunda suka shigo bai tanka ba sai yanzu.
“Eh d’in Ina ruwan ka damu,? Dan rainin wayo kawai dadin Abun ma Awa d’aya ka bani a duniya ba girma ta kayi ba ehe 🙄.
“Wai ku meke damun ku,?  cewar Momy da ta Farfad’o yanzun Nan.
“A Asibiti ma sai kun nuna hali.?
“Wallahi Kaka shi ya fara tsokana ta.
“Ai ba sai kin rantse ba takwara nasan halin Mai katon kan nan dallah fice a D’akin nan.
“Haba Momy Wai meyasa ke kullum goyon bayan Jannat kikeyi ne, ko don Kinga takwarar kice shiyasa, kaji my boy kyalesu nima Ina bayan ka.
“Yauwa Mama na ta Kai na, ya fad’i haka cike da miskilanci.
“Mama Wai ita bak’uwar bata iya gaisuwa bane da baza ta gaidani ba. Ya k’arisa maganar Yana satar kallon Zahra, Wanda in ba idon shi ne yake Mai karya ba Zahra tana Kama da Maman shi ta gurin idanuwan su, sai dai Zahra ita fara ce ta d’auko hasken Mahaifiyar ta jikin ta da hancin ta duk irin na Maman ta ne, idon ta da dan kumatun ta da dimple di’n da ke kumatun ta guda biyu duka irin na Maman shi ne, Asali ma da tayi Magana sai yaji Muryan ta Tamkar na Jannat Tabbas wannan suna da alak’a na jini da ita.
Take yaji wani Soyayyar ta a cikin Zuciyar shi Wanda in har bai mallake ta ba hankalin shi bazai tab’a samun Natsuwa ba, tabbas ya samu matar Aure. Duk a zuciya yake wanna tunanin sai wata Zuciyar tace Anya Hanif baka d’auko Abun da ya fi karfin ka ba, don tabbas wannan daga ganin ta ta girmeshi, wata Zuciyar tace to sai me don ka Auri Wanda ta girme ka ai ba a kan ka a ka fara ba.
Niko nace Hanif ba ruwa na zaka had’u da Yan b’oyayyiyar K’ulli fans fa yanzu su kakus da sister Nafeesat, da su Sister Adama, da Maman Ahmad,da sister Sadiya, da sister farida,  Kai na gaji duka dai baki bazai iya lissafo ku duka ba.
Wlh in ka matsa zasu zo har Maiduguri su cinye ka da Masifa don kana neman yi ma Masoyin su kwace fa🤣.
Nidai ba ruwa na kar Wanda yace mun wani Abu haka Labarin yazo sai dai kuyi hakuri 🙈.
“Tab lallai ma yaron nan bai da kunya, Zahraty ta girmeka kai ya kamata ma ka gaida ta 🙄.
“Dallah Small girl waya kasa dake,? Yar shisshigi kawai. Kinji Baby kin zo lafiya, ya fad’a Yana mai kashe ma Zahra ido.
Sai taji Abun ya Mata wani iri Wai Baby. Dariya Jannat ta kwashe dashi harda rike ciki, “Wai Baby dallah dubeshi Maman shi nace Mai Boy Yana ce ma wata Baby.
“Dallah malama ya ishe ki ba da ke nakeyi ba.
“Kai wayyo Allah na ni Hanifa, Wai ku don Allah yaushe zaku San kun girma ne,? Dallah Malama ki zuba ma Kaka Abinci ki zubo muku kuci, ku gama ku wuce gida da Zahraty ta huta. Dai dai lokacin Alhaji Bukar ya shigo a rud’e, “sister ya jikin nata,? Wlh Ina can jikin Bintu yayi tsanani sai tuge gashin kanta takeyi, ga jini na ta zuban Mata, yanzu haka likita yayi Mata Alluran barci za’a yi Mata aiki a cire Baby.
“Uhmmm Allah yasa ma Baby ya Mutu, cewar Momy ta fad’a ran ta a b’ace.
“Haba Momy in rai ya b’aci hankali ke nemo shi bai kamata kice haka ba, Ubangiji Yana fitar da Mai k’yau a cikin mare k’yau duk tsiya dan da zata haifa jinin ki ne tun da D’an d’an Yaya Bukar ne.
“Ki mun shiru Hanifa! Bana buk’atar had’a jini da wannan zuri’a, Zahra kad’ai ta isheni rayuwar duniya ita da yaran ki, domin tabbas Ina ji a jiki na Zahra y’ar Bukar da Fad’imatu ne, Saboda haka yanzu duk inda Fad’imatu take a doron duniya insha Allah sai na Nemo ta domin itace matar da ta dace da Ahalina😭. Ta k’arisa maganar Tana kuka.
“Don Allah Momy kiyi hakuri kamar inda Ubangiji ya Bayyana Mana Zahra haka zai Bayyana Mana Fad’imatu. Daga yau Zan bada sanarwa Zan sa kud’ad’e masu tsoka ga duk Wanda yaga Fad’imatu, Momy ma haka tace.
Gaba d’aya kan Zahra ya kulle ta kasa fahimtar inda zancen su ya dosa, tanbayoyi ne cike fal a ran ta.
“Momy Ina jin tsoron kar ya kasance tunanin da mukeyi akan yarinyar Nan ba haka bane yazo iyayen ta su kwace ta.  Inji Alhaji Bukar yayi wannan maganar.
“Ai duk duniya ba Wanda ya isa ya kwace yarinyar Nan a hannu na. Cewar Momy da ta yunkura ta tashi zaune.
*************************
JOS
Fad’imatu ne kwance a kan cinyar Hajiya Jiddah tana Mata tsifan Kai, ita Kuma tana rike da remote a Hannun ta tana canza tasha daga zee world zuwa Tashar Arewa, dai dai lokacin da hotan ta ya Bayyana a saman tv ana cigiyar ta ga duk Wanda ya gan ta za’a bashi kyautar Miliyan biyar, sannan in ita taji sanarwan ta hanzar ta Kiran Number waya kamar haka Saboda y’ar ta tana cikin wani hali a Asibiti Wanda tabbas likitoci sun gwada ta sun tabbatar da cewar tana buk’atar wani Abu ne, ita Kuma y’ar tace Mahaifiyar ta kawai take son gani kafin ta Mutu, Hoton Zahra aka Nuno kwance gadon Asibiti, wannan Kuma gata tana ta murmushi fuskan ta ya fito Sosai.
Da sauri Hajiya Jiddah da Fad’imatu suka mik’e, “Mama yarinya ta Zahra tabbas ita ce a Ina suka samo ta, ta fad’a Tana mai fashewa da kuka.
“Don Allah Mama mu tafi yau kar in rasa y’ata, Sosai Hajiya Jiddah ta tausaya ma Fad’imatu domin rashin d’a ba dad’i.
“Karki damu y’ata yanzu Zan Kira Yar uwa ta shiryo mu tafi, bari in sa ayi Mana booking d’in flight.
“Nagode Mama da gudu ta shige d’aki ta fara had’a Kaya domin yau zata ga rabin ran ta.
*************************
MAIDUGURI
Anyi ma Bintu Aiki an ciro yarinya katuwa sai dai yarinyar gaba d’aya tazo da wani irin siffa Wanda sai da likitocin ma suka ji tsoro, inda ya zamana sun kasa fito da yarinyar, kwanan Yarinyar d’aya ta mutu sakamakon tsotse Mata jini da Aljani duna yayi dama y’ar shi ce don cikin ma nashi ne.
Hakan yayi ma Momy dad’i daga Nan tace ya bata takardan ta su bar gidan, Haka Alhaji Bukar ya saki Bintu saki Uku, Yagana ita ma karamar Hauka ne kawai batayi ba, ga wasu k’uraje da suka feso Mata a matse-matsin ta da ta sosasu sai su dunga jini had’e da wani ruwa Mai k’arni.
Haka suka Kama hanyar k’auyen Zulum, suna isa Yan uwan Yagana suka ce Basu San wannan ba, don lokacin da suka samu duniya mantawa tayi dasu sai yanzu ne zata kwaso Mahaukaciya ta kawo musu gida.
Aiko sai ga Asabe ta lallabo tazo ita da Mami da take tuka keken guragu da Khausar ta Aiko Mata dashi.
“Hajiya Yagana surikar Alhaji Bukar, Ashe Kuma kema kin fara girban duk Abun da muka shuka, kamar yadda nima nake girba Koh.?
“Hhhh Amma fa naji dad’i, to yanzu Ina kuka dosa ne?
“Uhmmm Yagana kenan Ashe kina duniyar Nan naji duk Labarin k’ulle k’ulle da kuka yi ai, Allah ya kyauta yanzu sai a San nayi.
Juyawa sukayi suka tafi Abun su.
“Kece Yagana ko,?  Dama Mai gari ne ya Aiko ni yace An bada umarni tun daga sama cewar kar a barki ki zauna a garin Nan Saboda haka an baki Awa d’aya ki gama Abun da zakiyi ki bar garin Nan.
Fashewa da kuka Yagana tayi yau ne ranar farko da tayi ainihin nadama na gaske a Rayuwar ta.
MASARAUTAR AMRISH
“Kai ka fad’a mun gaskya Kai waye ne.?!
“Ke na fad’a Miki ban San ni waye ba, dallah sake ni ya fad’a haka Yana mai kwace jikin shi daga rukon da tayi mai, shimfid’a wani tattausan Abu yayi tamkar dadduma ya fara Sallah, Jero Salloli ya dunga yi har sai da yaji Zuciyar shi ta natsu akan ya gama biyan sallolin da ke kanshi.
Tun da ya fara Sallah take ta kallon shi ita dai tun da take yawan Zuwa k’asashe bata tab’a ganin masuyin irin wanna Abun ba kodai don bata lura bane,  da sauri ta d’auko wayar ta, ta shiga ta fara searching meye Sallah Nan da Nan aka turo Mata, kasancewar ba wani turanci ta iya Sosai ba sai ta sa translation d’in shi to hindi, haka ta dunga bi tana dubawa har ta kammala.
Ta d’ago ta tanbayeshi sai ta ganshi ya tasa Abincin da ta shigo dashi Yana ta ci dama yunwa yake ji Sosai, bai tab’a cin Abinci Mai d’adi haka ba. Zuwa tayi ta tasa shi a gaba tana kallon shi tamkar TV.
Alama yayi Mata da hannu Wai lafiya take kallon shi, girgiza Mai Kai tayi da yimai alama da cewa kawai Yana burgeta gashi yanayin skin d’in shi da gashin kanshi iri d’aya da na Abbiyyu har hasken fatar su ma.
Murmushi yayi Mata yayi Mata Alaman ya gode….suna Zaune kawai ji sukayi an shigo d’akin.
*************************
*************************
K’asar Cameron
“Alhaji gaskiya ya kamata ka koma gida kasan halin da iyalan ka suke ciki don nasan dole Laure bazata tab’a iya rik’e tarbiyan da ka basu ba.
“Doctor kenan ai Ina Nan ne Amma duk Abun da ke faruwa na sani sai dai har yanzu an kasa gano min inda d’ana d’aya tilo yake Wanda Ina jin tsoron farkawan Mahaifiyar shi tace mun Ina yake ban San Amsar da Zan Bata ba…….✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
*Yar mutan Zazzau ce. 😍😍🥰🥰💖💖*
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE 30
CAMEROON BIRNIN GABON
………”Abun da ni yafi damu na shine yanda kafin  Fannah ta Farfad’o in samo Mata d’an ta.
“Ranka ya dad’e Wai ni Abun da nake ta jin Mamaki Wai dama iyalan ka basu San kana da wata Mata bane,?  Gaskya ni Ina son inji yadda akayi ka Auri Fannah, Kuma gata ita tamkar ba ta cikin jinsin bak’ak’en fata, a Ina Kuma kukayi rayuwa da ita.?
“Doctor kenan da alama ka Zama Dan jarida ne Koh.?
“Ran Barrister ya dad’e ai dole in Zama Dan Jarida tun da Ina tare da kai, ni dai kawai a fitar da ni duhu nasan Yan Boyayyiyar K’ulli fans ma zasu so jin ya’akayi haka, daga k’arshe sai in basu Labarin basajan da kayi musu na cewa ka mutu, bayan ba ka mutu ba🤣.
“Wato Kai Doctor k’ok’arin ka ka tuna mun Asiri kowa yaji Koh😔, to shikenan ka gyara Zama yanzu zakaji Mai ya faru da sanadiyar Aure na da Fannah.
Ah so o’o har an gyara Zama aji labari to kwalelen ku mu had’u a Next page in ma Naga Comments din ku da yawa🤪🏃🏃.
*************************
JOS
Su Hajiya Jiddah da Hajiya Haulat da Fad’imatu sun Isa airport, bayan Hajiya Jiddah tasa anyi musu booking d’in flight da duk wani Abu da zasu buk’ata sun iso da mintoci jirgin su ya Iso suka shige suka d’aga sai BORNO.
*************************
MAIDUGURI
Zaune suke gaba d’aya a falon gidan Alhaji Bukar inda daga kwana biyu Zuwa uku har an canza ma gidan fasali an k’ara gyara gidan inda aka ware ma Zahra Falo guda had’e da d’akunan barci biyar, ko wanne da kalar furnitures d’in da yake d’akin. Kai tsayawa fasalta muku Falon Zahra da had’uwar da yayi ma b’ata lokaci ne kawai ku kwatan ta k’yan shi da aljannar duniya. Ruwan kanku bazai k’are ba sai ma kunga Sashin Maman Zahra Anan ne dukiya tayi kuka tamkar ba a San zafin ta ba ba Abun da babu a sashin sai dai in har bashi a duniyar ga Kuma wani safaya sashi daban a gidan shima.
Kullum sai sun taro a falon tun daga ranar da aka fara sanarwan cigiyar Fad’imatu har yau, kullum tunanin su Fad’imatu tana hanyar Zuwa. To tabbas yau hasashen ku ya zama gaskiya domin Fad’imatu ma yanzu haka ta sauka a Maiduguri.
Saukar su kenan a filin jirgin Saman suna k’okarin Samun Abun hawa, bayan mintoci kad’an suka samu Taxi, Fad’imatu ne ta hau gaban Motar duk da shekaru da yawa Amma ba Abun da ya goge a Zuciyar ta daga sunan unguwar har Zuwa layin gidan Alhaji Bukar Mai Dala.
“Hajiya Ina muka nufa ne Ina ta magana tun d’azu.
“Yi hakuri Malam pompomari zaka Kai mu layi na hud’u.
“Tom ba damuwa k’udin ku dubu d’aya.
“Muje Malam ba matsala. Haka suka Kama hanya har suka iso unguwar, unguwa ce ta masu hannu da shuni Wanda duk Wanda ka gani a unguwar ya Amsa sunan shi.
Da kwatance har suka iso kofar gidan, fita sukayi suka sallami Mai Taxi suka fara buga gate din gidan.
“Dallah waye zai damemu da buga gate ya jira inzo in bud’e Mana, cewar Mai gadin gidan har yazo zai bud’e Yana mita, yanzu haka irin Yan Maulan Nan ne da sassafe a damu mutane…… Maganar tashi ce ta mak’ale lokacin da yayi tozali da Fad’imatu don ba zai tab’a iya manta wannan fuskan ba a rayuwar shi.
“Don Allah ranki ya dad’e ki mun rai tuba nake, da gudu ya koma gida Yana cewa “ranka ya dad’e Hajiya ta dawo tabbas yau Rahman gidan Nan ya dawo, haka har ya shiga falon ya Fad’in Alhaji Hajiya ta dawo Yana fad’i Yana nuna hanyar kofa, kafin kace kwabo sai gashi ana rige rigen fita da Alhaji da Momi da Mama Hanifa yayin da yaran suka rufa musu baya don gani wacece wannan da iyayen su suke d’okin gani haka. Kan kace Mai duk ma’aikatan da ke gidan sun Bayyana a bakin gate din gidan.
Alhaji Bukar Yana isowa yaga farin cikin rayuwar da gudu ya rungume ta sai ga hawaye Yana zubo Mai shar Shar. Ba Wanda bai ji tausayin su ba a gurin, tun da Matar ta shigo Zahra taji duk duniya bata da kamar ta duk irin son da take ma Mami Ashe ba so bane, sai da tayi Ido biyu da wannan Matar, kawai ji tayi an rungume ta, kallon Wanda ta rungume tan tayi taga Ashe Matan ne, a hankali take jin wani irin farin ciki, Natsuwa, da kwanciyar Hankali Yana ratsa dukkan wani jijiyoyi na jikin ta tabbas wannan wata bangare ne na Rayuwar ta.
“Zahraty ki yafe mun na gaza kula dake ba laifi na bane laifin Laluran da ya sameni ne.
Haka dai suka dunguma suka koma falo, Nan a ka zauna kowa ya natsu Zahra aka fara cewa ta bada Labarin ta, Nan ta kwashe duk Labarinta  ta basu ba Wanda baiyi kuka ba a Falon. “Tabbas y’ata kin rayu cikin k’unci ta wani fannin Kuma kin rayu cikin gata tunda kin samu ilimi da kulawa a gurin daddy ku da yayan ki, Zan so Inga hotonan bayin Allah Nan da suka rainamun y’a.
Dubowa Zahra tayi ta mik’a Fad’imatu tana Fad’in ga Hoton daddy Nan in kikayi gaba duk Zaki ga na sauran harda Kaka.
Mik’ewa Fad’imatu tayi had’i da jefar da wayan kawai sai tayi baya luuu zata fad’i gaba d’ayan su taso wa sukayi suna rige rigen rik’e ta.
“Hanifa Kira doctor don Allah, to Wai ma me ta gani a wayar cewar Hajiya Jiddah tana mai d’aukar wayar ta duba.
“Ikon Allah Mai yadda yaso wannan ai Habibullahi ne Yayan Fad’imatu, da gaske kusan a tare suka had’a baki gurin Fad’i.
Mamaki ne ya cika Zahra, tana mai k’ara Imani da Ubangiji Mai tsara dukkan komai, wato ma wan Mahaifiyar ta ya rik’e ta, don yanzu ta fara gane cewa duk da ba’a fad’a Mata ba tasan Fad’imatu Mahaifiyar ta ce. Bayan ta Farfad’o ne tazo ta rik’e Zahra tana mai cewa”Zahra Ina Yaya na yake ki fad’a mun dama suna raye harda Mahaifiya ta.
Girgiza Kai Zahra ta fara yi, “kiyi hakuri Mami ko wani Mai rai Mamaci ne tabbas Dadddy da Hajiya tsohuwa sun rasu.
Wani kuka Fad’imatu ta fashe dashi.
Sai da sukayi Mai isan su duka ba Wanda ya dakatar dasu sannan Fad’imatu ita ma ta basu Labarin duk yanda akayi.
Kowa dai a tak’aice ya bada Labarin Abunda ya sani.
Suna Shirin tashi suje suyi Sallah ne aka ce musu sunyi bak’i sunce akwai Abu Mai Muhimmaci da zasu sanar da Alhaji, Momy ne tace ace musu su shigo.
Can sai gasu sun shigo, gaba d’aya kowa na falon sai da ya toshe hanci, yayin da kan Zahra ke duke bata d’ago ba sai taji muryan Wanda baza ta tab’a mancewa da ita ba tace “Zahra’u.!
*************************
MASARAUTAR AMRISH
“Kibd’iyatu wanene wannan dama Abun da kike b’oye wa kenan a D’akin shiyasa dana fad’a Miki Zan zo Miki hira kikace a’a.?
“Dakata Ansh Ina ruwan ka dani eye da zaka zo kana mun ihu a d’aki, Soyayya ce nace banyi ana Dole ne eye🙄.
“To shikenan Ina rantsuwa da Masarautar mu sai na tona Asirin ki yau d’in Nan.
Yana gama Fad’in haka ya biga kofar ya fita.✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Comments
Like
Share

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements