BOYAYYIYAR KULLI Page 41 to 50 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / BOYAYYIYAR KULLI Page 41 to 50

BOYAYYIYAR KULLI Page 41 to 50

BOYAYYIYAR KULLI Page 41 to 50

Ana Kai su kurkuku, a ka fara d’aure Sadeeq da wata katuwan igiya Wanda bazai tab’a iya kwance wa ba in ba kwance shi akayi ba.

Ita Kuma kibd’iyatu kafafuwa kawai a ka d’aure mata da hannu sab’anin Sadeeq da aka d’aure shi jikin gini.
Wuta suka fara hurawa ana zuba wasu k’arafuna a ciki, yayin da wasu ke gyara wasu Manyan bulalai tamkar Wanda za’a duka jaku na dashi.
Zaro Ido Sadeeq yayi  ganin Abubuwan da suke yi, Yana tunani a cikin Zuciyar shi badai duk su za’ayi ma Azaba da wannan Abun ba.
A hankali ya fara karanto Addu’a dake bakin shi Yana Mai Neman agaji gurin Ubangiji.
Kawai ji yayi an d’ora mai wannan k’arfen na cikin wuta a saitin bayan shi.
Ihu yayi Yana Kiran Ubangiji, Sosai kibd’iyatu taji wani k’arfi yazo Mata Wanda Bata San lokacin da ta kwance kan ta ba, Nan aka fara fafatawa tsakanin ta da sojojin kurkukun.
Yayin da Sadeeq ko ya dad’e da Suma Saboda Azaba.
Wasu Mata ne suka fara durowa ta sama sun rufe fuskokin su, kafin kace me sun gama da sojojin. Haka suka d’auki Sadeeq suka fice tare da kibd’iyatu. Sosai ake fafatawa har suka samu nasaran fita daga kurkukun, Nan da Nan labari ya Kai kunne Sarki cewa Kibd’iyatu ta gudu ita da bak’on nan, dai dai lokacin da Amrita ta iso taji Abun da ake sanarwa Mai martaba kafin yace komai, ita ta rigashi cewa aje a had’a manyan mayak’an garin su shiga dajin Nan duk inda take su dawo da ita. A tabbatar an kawo ta ita da bak’on nan.
Haka aka had’a mayak’an kace zasu je yak’i ne suka watsu domin kamo su kibd’iyatu da Sadeeq.
*************************
MAIDUGURI
Dai dai shigowar Alhaji Madou mijin Mama Hanifa. “Barisster Habibullahi Ina Amana ta da na baka, ya akayi Kuma baka Mutu ba,? Bayan naje office din ka da ke Kaduna ance mun ka rasu.?
“Ya kamata duk mu natsu muji komai. “Ka dubamun k’anwa ta da yarinya ta. Bayan an duba su Zahra ne sun Farfad’o kowa ya natsu a falon sannan Hajiya Jiddah tace ma Daddy Habibullahi Ina d’an uwan ka Sadeeq da Matarshi, kullum dasu nake kwana nake tashi.?  Ina Kuma ka samo wannan Mai zubin indiawan.?
“To Alhmdulillahi nasan dai yanzu kowa Anan ni yake sauraro yaji Mai ya faru.
Da farko dai lokacin da Yan fashi suka shiga gidana dama nasan da zuwan su, domin naji Mata ta Laurat suna waya dasu domin tabbas gida na in har ba jagora baza ka tab’a iya shigowa ba. Bayan naji duk yanda suka shirya da yawan kud’i da suka ce zasu bata ne, sai na tattara duk wata dukiya ta da kadarori na da na Dan uwa na da ke hannu na na Damk’a Y’ata Zahra domin nafi yarda da ita, tunda a lokacin Sadeeq ya yi fushi dani Saboda nace bazan Aura Mai Yar uwar shi ba. Bayan na tura ma kowannen su Miliyan biyar biyar a Account d’in su ita Kuma Laurat Miliyan goma, duk Abun da nakeyi Laurat bata sani ba, sai na bar kad’an daga cikin Abubuwa da na Mallaka a gidan don Inga iya gudun ruwan Laurat.
Bayan Yan fashin sunzo dama cikin d’ayan biyu ne ko su kashe ni ko inyi rai Amma burin su su kashe ni haka burin Laurat ma. Sai dai dama na riga na sanar ma Yan Sanda suna farawa Yan sanda suka zo. Haka yasa da sauran rai na a duniya aka d’auke ni sai Asibiti, bayan munje Asibiti dama mun riga mun gama magana da Doctor kasancewar shi dama Aboki na ne, yayin da Laurat suka gama magana da yan fashin akan cewa zasu biyoni Asibiti su k’arisa kashe ni.
Hakan yasa doctor ya mun wata Allura na tsawon Awa Arba’in da takwas ma’ana kwana biyu kenan, in akayi ma wannan Alluran zakayi tamkar ka Mutu.
Hakan yasa kuka ga Tamkar na mutu bayan an Kai ni da wasu Awanni Doctor yaje ya cironi a cikin k’abarin yayin da muka Kama hanyar Zuwa Cameron ni da Fannah da Doctor ya cigaba da kula damu a can.
Nasan zaku so kuji wacece Fannah.?  Wannan Amsa Alhaji Madou ya Kama ta ya baku ita.
Kowa juyowa yayi Yana kallon Alhaji Madou.
“Alhamdulillahi Fannah dai wata Baiwar Allah ce da na tsince ta, Kowa yasan ni din babban Soja ne, akwai watarana mun fita zagaye don ganin yanda aikin Yara na yake tafiya nida Mahaifin su Barisster Habibullahi da Dan uwan shi Sadeeq, sai muka tsinci Baiwar Allah Nan a yashe a cikin daji tamkar Bata Numfashi da farko mun yi tunanin Aljana ce Saboda tsananin k’yawun ta, haka Sadeeq ya yi k’okari ya bata taimakon gaggawa kasancewar shi likita Mai kula da sojoji. Bayan ta Farfad’o ne muka rasa yanda zamuyi da ita, a lokacin tun da ba lokacin zamu koma gida ba, Haka dai Genaral  Muhammad ya d’auke ta ya dawo da ita gidan shi dake Cikin Maiduguri. Bayan mun dawo da watanni a Nan muka gane ba Musulma bace ita duk da kaman ta samu tab’in hankali. Sai muka sa Mata Suna Fannah muka musuluntar da ita. Da yake ni na tsince ta sai General ya nema ma Dan shi Barisster Habibullahi Auren ta, bayan tsawon lokaci ni Kuma an turani wani course a can Uk na dawo na tarar da mummunan Labarin cewar Genaral da iyalan shi gaba d’aya sun Mutu.  Iyakan Abun da na sani kenan.
Daddy ne yaci gaba daga inda ya tsaya gurin cewar, “tabbas haka ake ta cewar Mun Mutu Amma ba gskya bace ya Basu Labarin yanda suka bar Maiduguri. Ya Kuma Basu Labarin cewa Fannah dama tana Kaduna tana ganin likita a can shiyasa dasu ka bar garin suka yanke shawarar kawai su koma kaduna da Zama.
Innah Jidda sai dai kiyi hakuri Saboda tun bayan barin mu Maiduguri aka tura Sadeeq K’asar Mali ya d’auki Matar shi suka tafi bamu k’ara jin Labarin su ba naje Barack din nasu yafi a k’irga Amma har yanzu shiru ba Labarin su. Ya k’arisa maganar cikin jimami.
Bayan mun koma da wasu watanni kawai Fannah ta samu ciki Sosai nida Umma ta mukayi murna haka, sai dai cikin Yana matuk’ar bata wahala a haka aka maidoni Zaria yin wani aiki haka na dawo Zaria na bar Umma tana kula da Fanna. Bayan wasu tsawon watanni Fannah ta Haifa sankacecen yaron ta Wanda gaba d’aya ita ya biyo ga k’yau kaman shi yayi kan shi, sai dai doctor yace bazata iya shayar da yaron ba balle rainon shi tun da har yau bata cikin hayyacin ta, sai dai mu nemi wata ta shayar dashi Koda da Madara ne ana biyan ta.
Ana haka ne muka had’u da Laurat banyi wani tsawon bincike ba ganin yanayin yanda ta Nuna mu ita d’in na Allah ce, Kuma na gan ta Ainihin Shuwa Arab shiyasa na Amince Mata mukayi Aure bayan munyi Aure da wata shida Umma ta dawo Zaria ita ma, sannan ne na bijiro ma da Laurat cewan zata rik’e mun yaron dan uwa na da ya mutu ya barmun da k’yar ta Amince sai da Umma tasa baki tun daga Nan rainon Sadeeq ya dawo hannun Laurat Sosai ta bashi tarbiyan da ya kamata kasancewar ta Mai fuska biyu Kuma ta Nuna Mai so da uwa zata Nuna ma d’an ta, sai dai daga baya na fahimci cewan tana rik’on shi ne Saboda nace Mata Mahaifin shi ya mutu ya bar Mai dukiya masu tarin yawa, Wanda kusan dashi muke rayuwa hakan yasa ta k’ara jawoshi a jiki kaman ta had’iye shi.
Kunji Abun da ya faru, bayan mun koma Camaroon da Fannah cikin ikon Allah mun had’u da wani Malamin Musulunci Wanda yayi k’okari ya karya tsafin da ke jikin Fannah inda har yanzu bata gama warkewa ba, don har yau bata San komai game da ita ba, sai dai an karya duk wani siddabaru na jikin ta. Abun da yasa ko kuka ganni a Nan Ina bibiyar duk wani labari dangane da iyalaina da Laurat ta tarwatsa mun, ta haka ne na gane cewar Zahra y’ar kace, sai dai nayi Mamakin ganin y’ar uwa ta d’aya tilo Wanda muka dad’e da cire rai da ita a gidan Nan ita da k’annin Mahaifiyar mu da Kuma Laurat duk Mai ya kawo su Nan.?
Alhaji Bukar ne ya kwashe Labarin komai game da Fad’imatu da Zahra da Laurat.
Sai ga Daddy Yana kuka, ya bud’e Hannayen shi yace “zo gareni y’ata shiyasa nake Miki Soyayya na daban a cikin zuciya ta. Da sauri Zahra ta k’arisa ta rungume Daddy.
“Yaya wato kafi son y’ar ka Dani Koh,? Ta fad’a Tana maiyin tamkar zatayi kuka. Gaba d’aya falon dariya aka Mata.
“Yi hakuri Autan Umma zo kema da sassarfa ta k’arisa gurin Yayan nata ta had’a da Zahra ta rungume su.
“Mami na tana kishi dani don Daddy yafi Sona Zahra ta fad’a cikin dariya da kuka.
Gaba d’aya jikin Mami yayi sanyi. Tura keken guragun ta tayi ta Isa gaban Daddy. “Don Allah Habibullahi ka yafe mun wlh yau na k’ara tabbatar da hukuncin Ubangiji, Kuma wlh nayi Nadaman Abun da na Aika ta wlh sharrin shaid’an ne. Zahra y’ata ki yafe mun don Allah.
“Mami ni na yafe Miki duniya da lahira sai dai banjin Zan iya yafe ma Yar uwan ki ba, ta rabani da Ahalina ta sa Mahaifiya ta gararin rayuwa. Kawai ta k’ara fashewa da kuka.
Fad’imatu ne ta jawo ta ta rungume ta, “y’ata ki yafe Mata kamar yanda nima na yafe mata, kin San Ubangiji yana son masu hakuri.
“Shikenan Mami na yafe Mata duniya da lahira Allah ya yafe Mana baki d’aya, gaba d’aya suka Amsa da Ameen ya Allah.
Nan su Mami suka tarkata suka tafi Mami tana da na sani.✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 😏😏🙄
💖😍🥰😍💃💃Love you fans.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 31
*************************
MAIDUGURI
“Mami ke ce.! Ta fad’a cikin kuka Mai ya sameki a kafan ki,? Shine kika tafi kika barni.
“Zahra me kikeyi anan,? Wace wannan Mai Kama da ke, ta fad’i haka tana Nuna Fad’imatu.
Murmushi Zahra tayi Mai Had’e da hawaye tace “Mami wannan da kike gani itace Mahaifiya ta wannan Kuma Mahaifina ta nuna Alhaji Bukar, Alhmdulillahi sanadiyar rabuwa da ke na had’u da Ahalina.
Asabe ne ta Nuna Zahra jiki na rawa tace, “kina nufin kice mun kece Yarinyar Fad’imatu Wanda ta bar gidan nan da cikin ki 🤔. Allah Mai iko Mai yadda yaso cikin da mukayi ta k’okari zubar dashi Ashe da rabon sai yazo duniya. Don Allah ku yafe mun nasan in har baku yafe mun ba Allah ba zai tab’a yafe mun ba.
“Da farko dai Sunana Asabe Wanda ake ma lak’abi da Uwar sharri. Ni Asalin Yar garin Zulum, na kasance tun farko na bana jin magana domin kuwa Mahaifiya ta ita take d’aure mun gindi bata son Laifi na Saboda sunan Innan ta aka Samun Kuma mu kad’ai ta haifa daga ni sai Yar uwa ta, gata ta Nuna Mami inda Mahaifin mu ke tsaya gurin bamu tarbiya yayin da Mahaifiyar ta ke lalatawa. In da tun Ina yarinya na iya had’a sharri nasha kashe Aure a garin mu yafi a k’irga,
Mahaifiyar mu ta kasance Mace Mai son Abun duniya inda Zaki kawo Mata kud’i ba ruwan ta da tanbayar in da kika samo, duk k’auyen mu mu kad’ai muke makarantar Boko daga mu sai yaran Mai gari, Mahaifiyar mu ta tsaya tsayin daka don muyi karatu ko ma samu mu Auri masu kud’i Saboda Allah ya wadata mu da k’yau, Dukan mu Mahaifiyar mu muka biyo Saboda ita d’in Asalin shuwa Arab ce. In da Mahaifin mu ya kasance Buzu ne.
Sosai muke Alfahari da k’yan mu nida Yar uwa ta muna ji tamkar duk garin ba yamu. Yagana ta kasance k’awar Yaya ta.
Bayan Auren Yaya ta da wani Mai kud’i a garin Maiduguri, da shekaru Masu yawa ita ma Yagana tayi Aure a K’auyen dake makwafta ka da garin mu in da Masifan ta da shedanancin ta ya hana ta Zama ta fito da ciki.
Kwatsam sai ga Yaya ta an sako ta ta dawo gida Wai bata Haihu Mijin Kuma kullum sai ya bige ta yayi Mata gori.
Bayan wani lokaci Yaya ta ta tafi kaduna gurin wata K’awar ta sai da tayi kusan shekara biyu tazo gida tana Fad’in ma Inna tayi Aure a Zaria.
Kar in cika ku da surutu bayan wasu shekaru Masu yawa Yagana ta haihu ta haifi yarinya Mace har ta girma sai tana Zuwa birni don yin aikatau a biya ta ni Kuma lokacin na had’u da wani Saurayi na Yana zuwa Lagos sunan shi Alhaji Shamsu Ana ce Mai Shamo, haka ya dunga mun b’arin kud’i, hakan yasa ba kalar hotel din da bamu ziyarta ba a garin Maiduguri, haka Zan kwana biyu bana gida, Amma indai Zan dawo in kawo ma Inna kud’i ita ba ta da Matsala. Kwatsam Ina Zaune wata rana na dawo daga gantalina sai ga Yagana, na tarbe ta muka gaisa nake tanbayar ta kwana biyu tunda ba Yaya Laure ko ganin ta ba’a yi. “Ke dai bari kawai Asabe, kin San wani Abu kuwa.?
“Sai kin fad’a Ina jin ki.”
“Wani taimako nake so ki mun don Allah, kin San yanzu gidan Alhaji Bukar Mai Dala nake aiki.
“Ke don Allah.!  Tab kice kin Zama Hajiya gidan da akace in kana aiki Albashin gidan bai yi K’asa da dubu d’ari ba.
“Ke dai bari kawai so nake ki taimaka mun mu Zubar da cikin matan gidan Kuma mu kore ta, Bintu ta Aure shi.
“Tab babban magana taya kenan.?
Tunani na fara a Zuciya ta ai tamkar dama ne na samu ta yanda Zan ma Yagana wayau in Aure Alhaji Bukar.
Nan da Nan na Amince inda a lokacin nima Ina d’auke da ciki ban sani ba Saboda cikin ba Mai irin wahalan nan bane, Kuma ko alama bai fito ba a jiki na sai dai Kara bud’ewa da nayi da jikina yayi lukui-lukui.
A haka muka ajiye ranar da zamu gidan Boka inda mukaje muka karbo magani da yarjejeniyar cewa in komai ya Kammala Yagana zata ban Miliyan biyar jin kud’in da ta Anbata ne ya sa ni na janye kudiri na na Auren Alhaji Bukar, Saboda ni ma Allah yayo ni Mayyar kud’i ce.
Haka mukaje gidan ta nunani a gurin matar gidan a matsayin kanwar ta Zan dunga Taya ta aiki.
Bayan wasu kwanaki duk mun Gama Anfani da Magungunan da Boka ya Basu jira kawai suke Alhaji ya dawo, domin Sosai muka sama Fad’imatu kasala gurin yin Ibada, bayan ta kasance Mace Mai son ibada haka muka dunga k’ulle k’ulle mu har uwar Maigidan bamu kyale ba har gidan ta naje na barbad’e magani a gadon kwanciyar ta.
Lokacin da Alhaji ya dawo lokacin na samu naje na zuba Magani cikin girkin da Matan gidan tayi ma Maigidan, har d’akin shi sai da aka barbad’e magani. Na Kira wani yaron Shamo yazo don ya shiga D’akin Matar gidan don aikin mu ya tafi yanda muke so.
Haka ko akayi komai ya watse, mun watsa family mun haddasa Rashin zaman lafiya, daga k’arshe mukayi k’ulle k’ulle mu a gurin Boka inda bamu wani Sami matsala ba gurin Auren Alhaji da Bintu yarinyar Yagana, Nan Yagana suka bud’e duniya sabuwa inda suka mance da kowa, ciki kuwa har dani hakan yasa na kudiri aniyar sai na d’au fansa, kwatsam sai ga Alhaji Shamo yazo ya d’auke ni muka fita K’asar inda anan na gane Ashe shidin fashi yakeyi Kuma Yana cikin kungiyar Asiri mafi muni, haka yayi matuk’ar tsorata ni. Kwatsam wata rana na tashi da Nak’uda inda Shamo ya kaini Asibiti na haifi zankadediyar y’ata K’yakk’yawan gaske, sai dai inda aka samu matsala Ina haihuwar ta ce sai na bashi ya sadaukar da ita ga kungiya, hankali na ba k’aramin tashi yayi ba, hakan yasa nayi duk wani Abu da zanyi Saboda kullum kud’i yake turamun a Account d’ina shiyasa bansha wahalar gudu Zuwa dawowa gida ba, Ina dawowa na tarar da Yaya ta tazo ita da Mijin ta zasu tafi ban bari mun had’u da Mijin nata ba sai dai na bata kyautar y’ata.
Kunji Abun da ya faru kenan don Allah ku yafe mun nazo Ina rokon ku.🙏🙏.
“Ni Alhaji Bukar da Ahalina mun yafe Miki albarkacin Yar Uwar ki da ta rainamun y’ata duk da Azabtar wan da tayi Mata. Allah ya yafe Mana, sanan muna son ki bamu Labarin inda kika tsinci Zahra.
“Bayan mun zo k’auyen mu da Mijina muna kan hanyar mu ta komawa, kasancewar ta Jos muka bi mun iso wani k’auye da ake ce ma jingir muna gab da fita garin Motar mu ta lalace, tsayawa mukayi ga yarinya sai kuka takeyi haka Alhaji ya fita domin Neman inda zai samu ruwa don da alama injin Motar ne tayi zafi, kawai Ina Zaune Ina jiran shi na ganshi da akwati da yarinya niki niki.  “Alhaji lafiya Ina ka samo wannan yarinyar fa.?
*Laurat Ina so ki had’a yaran Nan ki rikesu karki tab’a nuna musu cewar  ba mune iyayen su ba Ina son Yarinyar nan.
“Ya za’ayi kawai kazo mun da yarinya baka mun bayani ba kace mun in rik’e ta, haka fa mukayi da Kai akan Sadeeq, haba Alhaji ya za’ayi in raini Yara biyu lokaci guda.?
“Kinga Laurat zintar yarinyar Nan nayi a cikin dajin nan, Kuma indai raino ne Zan samu Miki Mai Taya raino.
“Shikenan Allah ya tayani rik’o.
“Ameen ya Allah 🙏 ko kefa.
“To kunji inda muka tsinci Zahra.
Sosai Fallon akayi ta kuka. Ana cikin haka ne aka ce an k’ara yin wasu b’aki Maza biyu Mace d’aya, aka ce su shigo.
“Daddy dama baka mutu ba,? Baya tayi ta zub’e yayin da Daddy idon shi akan Fad’imatu.
“Fad’imatu dama kina rayee…..?
*************************
MASARAUTAR AMRISH
Zagaye d”akin ta fara yi, tabbas suna cikin had’ari matuk’ar Ansh ya tona musu Asiri.
Shiru Sadeeq yayi Yana zare ido, gaba d’aya ma ya k’asa yin Addu’a.
Da sauri kibd’iyatu ta juyo ta Kama shi ya mik’e domin har yanzu bai gama warkewa ba da raunikan jikin shi. Wani mayafi ta samu ta nad’a Mai ta rufe Mai fuska ta kamo hannun shi sukayi hanyar fita, dai dai lokacin da Maman ta da baban ta suka shigo d’aki ga fadawa biye a bayan su.
“Dama na fad’a Miki duk wani Abun da kike b’oye wa sai ya fito fili, wato bak’o kika shigo Mana dashi bayan kin San dokan Masarauta Koh, tabbas ko da kike y’ata Dole a hukun taki domin ke d’in Mai laifi ne.
“Y’ata Mai yasa kika aika ta wannan mummunan zunubin,?  Yau Ina cikin tashin hankali a kan Zan rasa ki gashi ke kad’ai na Mallaka a duniya.
Kin San Dole Masarauta ta hukunta ki da horo Mai tsanani na tsawan wata biyar da kisa ta hanyar jefewa. Kaico na yau y’ata ta aika ta wannan  zunubin, Kai Kuma bak’o wani tsautsayin mutuwar ce ta biyo da Kai ta Masarauta na.?
“Abbiyyu ba yajin me kake cewa baya jin yaren mu, Abbiyyu Ina Neman Alfarma ga Masarauta cewa don Abun bauta a mun duk hukuncin da za’a mun Amma kar ku kashe shi ku barshi ya tafi.
“Ke dakata.! Har ke Zaki fad’a Mana Abun da ya dace to baki Isa ba, Dole a hukunta ku dukan ku, sarkin yaki ku tafi dasu kurkuku mafi Azaba ayi ta gana musu Azaba har Nan da wata biyar kafin ita a Mata kisa ta hanyar jefewa  shi Kuma ta hanyar rataya. Ta k’arisa maganar Tana mai fashewa da kuka na munafunci Wanda Bai Kai ciki ba, rungume ta sarki Bijay yayi Yana mai bata hakuri da cewar zasu zauna da Masarautar don ya rokan ma Y’ar shi sasaauci don bazai tab’a iya yarda a kashe Mai y’a ba Kuma ita kad’ai gareshi ita yake ta gaje shi.
Jin haka yasa hankalin gimbiya Amrita ya tashi ta k’ara fashewa da wani kukan, dole yau ta ziyarci dodon Zafin ta don ganin ba a ma kibd’iyatu sassauci ba, don hakan zai kawo Mata matsala gurin Samun kujeran Mulkin Masarautar Wanda shine burin ta da na Mahaifin ta.
Haka aka Kama su Kibd’iyatu aka tafi dasu, Sadeeq bai k’ara rud’ewa da Masarautar ba sai da aka fito dasu, tabbas Masarauta ce Mai Matuk’ar birgewa da girma Wanda in kana cikin ta Tamkar kana wani dausayi ga Ni’ima ko Ina ga kwalliyar furanni kala kala Wanda suka k’awata garin, ga kanshi ko ina, ko Ina na garin a tsaftace ko tsinke bazaka gani a k’asa ba, haka aka ratsa dasu ta tsakiyar gari yayin da mutanen garin suke firfitowa suna binsu da kallo wasu na Tausayi wasu na Allah ya k’ara.
Tana fita bata zame ko Ina ba sai kogon da Dodon ta yake bayan tayi badda Kama tasa wani riga da ya rufe har fuskan ta.
Tana Isa Dodon ya fara Mata magana cikin damuwa.
“Mai girma uwargijiya ta tabbas wannan bak’o da yazo garin Nan babban matsala ce da barazana gare ku duka Yan garin domin na duba Naga cewa akwai Abubuwan Mamaki da yawa a tare dashi, tabbas karki bari ya k’ara kwana uku a garin Nan ba tare da kin kashe shi ba, in har ba haka ba to akwai Matsala Sosai ki tafi! Ki tafi! Uwar d’aki na ki hanzarta bamu da isasshen lokaci.✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Nima din dai Banda isasshen lokacin🙄🤪🤣
Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 💪👊
Share
Comments
Like
😍💖🥰🥰💖🥰🥰🥰🥰
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Ranar muke jira yau gashi tazo kowa da tanburan shi gashi munzo Yaya Sadeeq ya angwance da Gimbiya kibd’iyatu 🤪🤣🤣.
SADAUKARWA
Wannan page d’in na sadaukar dashi gareki sisto Adama Allah ya baki lafiya yasa kaffara ce agareki, fans ku sata a Addu’a 🙏.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE  33
…………….Sosai su kibd’iyatu suke gudu tamkar walkiya, wani guri suka iso tamkar wani gari Amma ba kowa garin bud’e kofar garin sukayi suka shiga.
Masha Allah wannan gari ma yafi Masarautar Amrish had’uwa Sosai, bayan sun shiga ne suka wuce cikin wani guri suka ajiye Sadeeq suka fara Basu taimakon gaggawa. Bayan ya farfad’o ne suka ce Mata “ya shugaba dole ku bar gurin Nan yau don Mahaifiyar ki bazata barki ba, domin yanzu haka ta had’a jarumai domin nemo ku.
“Tabbas maganar ki haka take, a yau zamu bar garin Nan, ku kawo Mana kayan marmari bayan wasu Awanni sunyi shiri Sosai aka fitar musu da ingarman dokuna suka hau suka fara tafiya.
Sunyi guzuri Sosai, bayan tafiyar su ba dad’ewa mayak’an garin su suka iso cikin birnin basu gansu ba. Haka suka zagaye dajin basu samesu ba, gashi Sarauniya tace karsu sake su dawo ba tare da sun gansu ba.
*******    ********     *****
Sosai sukayi tafiya Mai nisa sannan suka yada zango a gurin wani bishiyoyi masu tsawo, Kibd’iyatu ta Kama Sadeeq ya sauko ta zaunar dashi ta k’ara duba mishi Ciwon nashi ta samishi magani, ta bashi Abinci ya ci tace Mai ya kwanta ya huta bari ta Dan zagaya gurin ta gani. Binta kawai yayi da Ido don gaba d’aya ya zama wani iri ko magana ba ya iya yi, Saboda Azaban da yake ji a jikin shi, barci ne ya fara d’iban shi, kukan dokunan su yaji da haniniyar su da sauri ya farka yaga kibd’iyatu ta dawo da wani irin gudu ta kamashi ta d’ora shi kan doki ita ma ta haye da gudu suka bar gurin.
Gudu sukeyi ba kad’an ba domin kuwa mayak’an garin su ne suka kusa gano inda suke da taimakon Sarauniya, domin duk ta inda suka bi tana ganin su da taimakon dodon tsafin ta.
Sunyi tafiyar kusan kwana uku kafin su fara isowa wani dajin mai matuk’ar duhun bishiyoyi.
Dole suka kunna fitillar da suke haskawa, suna cikin tafiya sai ganin wani gida sukayi a dajin da akayi shi da katako da ganye, tsayawa sukayi suna kallon gidan a hankali kibd’iyatu ta sauka taje tana zagaye gidan sai ta jiyo tamkar maganar Mutane Kuma irin yaren Sadeeq sukeyi da sauri ta kutsa Kai cikin gidan.
Ji tayi an rik’e ta an sa Mata wuk’a a wuya, “wacece ke yau tsawon shekara Ashirin da hud’u muna dajin Nan ba wani mahaluki da ya tab’a shigowa Nan sai ke.?
“Mai gaskiya sake ta, tabbas lokacin barin mu dajin Nan yayi domin dama ita muke jira shekara da shekaru, Amma Ina saurayin da kuke tare dashi.?
Mamaki ne ya cika kibd’iyatu jin wannan tsohon na mata magana da yaren garin su. Cewa tayi gashi can a waje, ta fad’a haka tana mai juyawa tana kallon matan da ta fito D’auke da wasu kyawawan Yara da aka musu ado da ganye tamkar sutura a jikin su, sai dai sudin bak’ak’e ne kamar yadda Mahaifiyar su take Amma irin bak’in Nan Mai k’yau.
“Mai gaskiya ku fita ku shigo da Saurayin Nan domin bamu da lokaci Sosai yau ko gobe ya kamata mu bar dajin nan in ba haka ba komai zai iya faruwa.
“Baba Taya zamu bar dajin Nan bayan kasan so gurin Tara muna kwatan ta barin Amma bamu gane hanya.”
“Tabbas hakane Amma fitillan mu ta iso domin na dade Ina Mafarki game da Yarinyar nan zata zo ita da wani Saurayi da zaran Mun had’a su Aure zata Musulunta Kuma daular Masarautar su zata ruguje, Mahaifiyar ta dodon tsafin ta zai cinye ta, mu Kuma zasu zamo Mana jagoran zuwa ga Ahalin mu.
“Masha Allah yarinya muje a shigo dashi.
A hankali hawaye ya fara zubowa daga idon Matan Nan tana mai Fad’in Alhamdulillahi lokaci yayi Mafarki na zai Zama gaskiya.
Sai gashi sun shigo rirrik’e da Sadeeq domin Yana jin jiki Sosai suka ajiye shi, a hankali Sadeeq ya fara tuno komai na Rayuwar shi bayan baba yayi Mai Addu’a a cikin ruwa ya bashi.
A hankali ya fara furta “Daddy Ina Zahraty na, please karku kashe ni Banga Zahraty ba.
“Alhamdulillahi hankalin shi ya dawo Normal.
Yaro ya sunan ka?
“Suna na Sadeeq.”
“Masha Allah Nan Kibd’iyatu da baba suka bashi Labarin duk Abun da ya faru da Kuma bukatun su, Amincewar shi kawai suke jira.
“Yaro ka taimaka Mana wannan hanyar ne kawai zai fitar damu ya tseratar mu daga sharrin Masarautar Amrish.
“Shikenan Baba na Amince, Amma da sharad’in cewa daga baya Zan sake ta in Auri y’ar uwa ta Wanda nake so.
Har mai gaskiya zaiyi magana Baba tsoho ya dakatar shi yace Mai “ba damuwa yaro.
Ita ko kibd’iyatu dama burin ta kenan don ita ta dad’e da kamuwa da Soyayyar shi a ran ta, ita jin shi takeyi tamkar jinin ta ko wani bangare na Ahalin ta.  Kuma Kama yake Mata da k’anwar Mahaifin ta Safni.
Haka aka d’aura Auren kibd’iyatu da Sadeeq akan sadakin na agogon zinarin da Mai gaskiya ya bayar domin shi ya zama waliyin Ango yayin da Baba tsoho ya zama waliyin Amarya. Suna gama d’aurawa suka fara Shirin tafiya bayan Sadeeq ya rama duka sallolin da ake binshi, Suma d’in basu d’auki komai ba  sai guzurin Abun da  zasu ci. Matar shi da yaran aka sa akan doki d’aya sai Sadeeq da Baba tsoho a doki d’aya yayin da kibd’iyatu da Mai gaskiya suke tafe a k’asa domin su din sun fisu lafiya.
*************************
MAIDUGURI
Sosai Family d’in ke jin dadin su yayin da aka ware ma Daddy sashi guda a gidan, ba a wani b’ata lokaci ba aka maida Auren Alhaji Bukar da Fad’imatu, yayin da suke Shan love d’in su don ji yake tamkar ya maida ta ciki Saboda Soyayya.
Gefe guda Kuma Jannat da Hanif sun tare a gidan sunki komawa gidan su Saboda Zahra yayin da Hanif yake shige ma Zahra Sosai tun bata kulashi har ta fara biye mishi, don shi mutum ne Mai tsokana. Ya dunga had’a su ita da Jannat Yana tsokanar su, in kaji hayaniyar su kace Yan dambe ne.
Yayin da Hanif yaje ya sanar da Momy granny shifa Zahra yake so.
“In ban da abinka Hanif Ina Kai Ina Zahra Kuma kana dai ji Zahra tana da Wanda take so, Kuma baza muyi Mata dole ba.
“To shikenan granny ai dama na dad’e da sanin baki son farin ciki na, wlh zaku iya rasani indai ban Auri  Zahra’u ba. Ya k’arisa maganar Yana Mai ficewa cikin sauri,
“Oh ni Murjanatu ya zanyi da yaron Nan ne, d’aukar waya tayi ta Kira Mama Hanifa tace tazo tana Neman ta.
Zahra ne take kwance cikin makeken gadon ta sai juye juye takeyi barci ya k’aurace Mata sakamakon wani mummunar Mafarki da tayi Wai ga Yaya Sadeeq ya Auro wata Yar India. Sosai Zahra take kuka tanajin Zuciyar ta tamkar zata tarwatse, tashi tayi tayo Alwala tazo ta fara Nafilfilu tana fad’a ma Ubangiji Allah ya Yi mata zabin Alheri.✍️✍️✍️✍️✍️
Nasan yanzu zaku faramun Surutu maiyasa Sadeeq ya Auri kibd’iyatu haka Labarin yazo.
Team Yaya Sadeeq da Zahra sai dai fa kuyi hakuri domin Sadeeq na gimbiya kibd’iyatu ne🤣🤪🤪🏃🏃🏃.
Share
Comments
Like
Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 😏🙄🤣🤪😍💖🥰.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Wannan page d’in k’yau ta ne gare Yan k’ungiyar Arewa writers Ina yin ku son so fisabilillahi, Allah ya k’ara d’aukaka kungiya.🙏🙏
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
PAGE  34
*************************
MAIDUGURI
Daddy ne yake ta zarya a D’akin shi, gaba d’aya hankalin shi Yana kan d’an shi kar maganar Laurat ya zama gaskya fa don cewa tayi tasa an kashe shi. Shi Kuma Daddy Bai yarda Sadeeq ya mutu ba.
Sallaman da Hanif yayi ne yasa Daddy dakatawa  tare da ba Hanif izinin shigowa. Shigowa Hanif yayi tare da durkusawa Yana Mai gaida Daddy, daga Nan Kuma yayi shiru ya kasa cewa komai.
“Mallam Hanif lafiya kuwa,? Da alama akwai Abun da ke damun ka.?
“Eh Daddy dama akan Maganar Aunty Zahra ne, umm umm.
“Ka saki jikin ka Hanif kayi maganar ka, ka d’auke ni tamkar Mahaifin ka.
“Daddy wlh tun ranar da na fara ganin Zahra Allah ya jarabceni da son ta Kuma wlh in har ban Aure ta ba Zan iya rasa rai na.
Ya k’arisa maganar cikin kuka tamkar k’aramin yaro.
Numfasawa Daddy yayi yace, “yanzu in banda Abinka Hanif Ina zaka Kai Zahra, Zahra Kuma ta girmeka ta baka kusan shekara uku, Anya bakayi zari ba.?
“Wai Daddy meyasa kuke cemun haka, Taya Mace zata fi karfin Namiji bafa dambe zamuyi ba daddy, Aure zamuyi Kuma wlh bata fi k’arfi na ba, in Kuma baku yarda ba ku Aura mun ita ku gani Next year insha Allah Kuna da jika.
Zaro Ido Daddy yayi yace “jeka Hanif Zan Neme ka, zamuyi shawara kaji.
“To Daddy don Allah a duba buk’ata ta Kuma ayi mun Adalci🙏. Yana gama Fad’in haka ya fice daga d’akin da Zahra suka ci karo Alamun duk taji Abun da suka yi da Daddy.
Wani kallon tsana da rashin so tabishi dashi, juyawa tayi ta fasa shiga d’akin Daddy.
Bin ta yayi da gudu Yana k’wala Mata Kira”Zahra’u!  Zahra’u!.
Zahra tana Zuwa ta shige d’aki ta fad’a akan gado, ta fashe da kuka tabbas Hanif Yana so ya rabata da Masoyin ta, duk da Mami  tace tasa an kashe Yaya Sadeeq ita bata yarda ba ta naji a jikin ta cewa bai Mutu ba Kuma zai dawo gare ta, suyi Aure su haifi Yara.
“Zahraty kukan me kikeyi.?
“My Jannat Hanif ne.”
“Haba Zahraty na yanzu har Hanif ne Zaki zauna kina mishi kuka, to Wai ma meya Miki.?
Kwashe duk Abun da taji suna magana da Daddy tayi ta fad’a ma Jannat.
“Tabdijam lallai ma Hanif bai da kunya kedin ce zaice Yana so,?  Wlh bai Isa ba duk runtsi ko Nan da shekara goma ne sai mun jira Yaya Sadeeq ya dawo.
“Baku Isa ba kuwa.”
Duka juyawa sukayi suka tarar da Mami da Daddy a bakin kofar d’akin, Mami ne tace ma Zahra Basu Isa ba.
“Haba Mami Ina Hanif Ina Zahra, Zahra ai tafi karfin Hanif, in ba rigima irin nashi ba.
“Jannat ki rufemun baki, to Wai da kuke Maganar ku ma Ina Sadeeq d’in yake,? Ina ce a gaban ku Laurat tace tasa an kashe shi. Daddy ya fad’a haka Yana goge kwalla a gefen idon shi.
Da gudu Zahra tazo ta rungume Daddy tana mai fashewa da kuka, “wlh Daddy inaji a jiki na Yaya na bai Mutu ba Kuma zai dawo gareni, don Allah kar kumin haka daddy Zan shiga wani hali.
“Kiyi hakuri Zahra ki ceci ran yaron Nan gashi can ya yanke jiki ya fad’i bayan fitowan shi daga bangare na, an d’auke shi rai a hannun Allah sun tafi Asibiti.
Zaro Ido Jannat tayi jikin ta na rawa take tanbayar Daddy wani Asibiti ne.?
Jini d’aya ba Wasa ba ita ma Zahra sai da taji wani iri a Zuciyar ta kawai bazata iya cin Amanar Yaya Sadeeq ba ne.
Niko nace sai kiyi ta rike Mai Amanar, gashi can shi yayi Auren shi ai🙄.
************   ***********
Likitoci sunkai goma a kan shi don ceto rayuwarshi yayin da Momy Kaka da Mama Hanifa suke ta zarya sun k’asa Zama, su Daddyn Zaria ne da Daddyn Maiduguri da Mami da Matar Dadfyn Zaria da Jannat suka iso Suma a rud’e suka k’ariso, “ya jikin nashi to”?.
“Alhmdulillahi Amma har yanzu likitocin tun da suka shiga basu fito ba, Mama Hanifa ta k’arisa maganar Tana kuka.
Dai dai wani likita ya fito, “kune relative na Hanif Madou.?
Har rige-rigen Amsawa sukeyi, yayin da doctor ya basu Umarni su biyoshi office din shi.
Haka duka suka dunguma yayin da Maman Sadeeq ita ta Zauna, duk da har yanzu bata wani dawo Normal ba Kuma har yanzu bata jin yaren mu Sosai, shiyasa in ana wani Abu sai Daddy yayi Mata bayani take fahimta. Har yanzu Kuma bata tuno da d’an ta.
Bayan sun zauna likita ya fara musu bayani, “Tabbas Zuciyar shi ta tab’u k’adan Saboda wani Abu da ya firgitashi, ko kuma yake tsoron ya rasa wani Abu lokaci guda sai Zuciya ta samu matsala matuk’ar bai samu Abun Nan ba, in har so samune ya kasance da ya farfad’o ya fara tozali da Abin da yake so, haka zai sa Zuciyar shi ta daidaita.
“Ba damuwa Doctor insha Allah.
Da gudu Zahra ta juya daga kofar Office din.
************  ************
Sunyi tafiya Sosai bani da tafiya ba, yayin da Kibd’iyatu ita take nuna musu hanya, domin ita d’in tana da sani Sosai game da dajin Abun da ke tsayar dasu kawai Sallah, a wannan yanayi ne Kibd’iyatu taga ita ma ya dace ta karb’i wannan addini Saboda ta lura cewa Addini ne Mai k’yau sannan mutanen cikin ta suna da had’in Kai tunda gashi sun had’u da su Mai gaskya Basu San su ba Kuma sun taimake su,  Baba Tsoho ta fad’a ma tana so ta Musulunta.
Dukan su sunyi Farin ciki da haka take ta Musulunta gurin Baba Tsoho. Hakan yasa Sadeeq ya fara sakewa da ita, har zasu danyi hira, Kuma Sosai take kula dashi yayin da ta dage gurin koyon addini da sauran Ibadu gurin Baba Tsoho, hakan yasa Sadeeq har ya fara jinta a ranshi.
************ *************
MASARAUTAR AMRISH
Sosai suka tashi da wani firgici a garin yayin da  kogin da ta zagaye garin ta fara Anbaliya hakan ya faru ne duk Saboda Musuluntar da kibd’iyatu tayi, domin Alkawarin Abun bautan su ne cewa duk randa wani yaron sarkin da ke mulki a lokacin ya karb’i wani Addini ranar zai kifar da garin su.
Sosai Sarki ya shiga tashin hankali,  Mahaifiyar sarki ne ta fito domin ita d’in ta dad’e tana Addini Musulunci sai dai ba Wanda ya sani domin tana jin tsoron Mai zai je ya dawo, dalilin Musuluntar ta kuwa shine ta fita kewaya, wani dodo ya biyo ta duk masu tsaron ta suka gudu, ta sadakar da zata  mutu kawai sai ganin wani mutum da fararen Kaya tayi Yana karanto wasu Abubuwa take dodon Nan ya k’one, Aiko taje ta rungume mutumin Nan tace Mai meyake so ta biya shi da shi, sai yace Mata ta karbi addini nin shi take ta karb’a, Kuma ya umarce ta da ta b’oye Addinin har sai lokacin da ya kamata ta Bayyana, sai ya zamana duk ranar jumma’at Yana zuwa ya koya Mata Abubuwa da ya danganci ibadu.
Fitowa tayi dai dai lokacin da Mujahedeen ya iso Addu’a suka farayi a tsakiyar garin take Anbaliya ruwan ya fara komawa, garin ya dena girgiza komai ya tsaya cak. Farin ciki ne ya mamaye sarki yaje ya rungume Mahaifiyar shi Yana Fad’in “Amma mun gode, Amma wannan wani irin tsafi ne kikayi.?
“Wannan ba tsafi bane Addu’a ce.
Nan da Nan Mujahedeen ya fara musu wa’azi Yana janyo Ayoyi da hadisai Yana fassara musu cikin harshen su, jikin wasu yayi sanyi, wasu ko daga ciki ko a jikin su sai ma tafiya da suka fara yi ciki kuwa har da Amrita da Mahaifinta direct gurin Dodon su suka Nufa.
Shi Kuma dodo Yana Nan bakin ciki yakusa kashe shi za’a daina bauta mishi, suna Zuwa Bai ko saurari Mai zasuce ba ya yi musu Loma d’aya bayan haka shima ya kashe kan sa.
*************   **********
Sosai shak’uwa ta shiga tsakanin Sadeeq da kibd’iyatu, Wanda yanzu Sunan ta ya koma Fad’imatu Zahra’u ita tace a samata wannan sunan bayan baba Tsoho ya bata tarihin Mai sunan, da darajar ta, Nana Fad’imatu Allah ya Kara Mata yarda.
Shi Sadeeq ma bai sani ba, sun fita farauta da Mai gaskya sun dawo yace Mata “kibd’iyatu zo ki had’a Mana wuta mu gasa Naman Nan.
“Ni Sunana Fad’imatu Zahra’u, ko kace mun Zahraty. Ta fad’i haka tana mai hararan shi irin na Soyayyan Nan.
Da sauri ya d’ago Yana kallon ta, “da yaushe kika koma sunan Nan ban sani ba,? Ya fad’i haka cike da Mamaki a fuskan shi.
“Mijina ko sunan bai maka bane,? Naji tarihin Mai sunan ne da darajan ta yasa nace a Samun sunan, Ina matuk’ar son suna, Kuma Ina son duk wacce take da irin sunan. Ta k’arisa maganar Tana ruko hannun shi.
Samun kanshi yayi da Mata Murmushi, murmushinda yake matuk’ar kashe Mata zuciya a duk lokacin da yayi Mata, ta jita ta Kara tsunduma a kogin son shi.
“Karki damu Sunan yayi Sosai Saboda nima sunane Mai daraja a guna Kuma mafi soyuwan suna kinji Zahra’u.
Rungume shi tayi tana maijin farin ciki. Maman Yara ne ta fito “oh Zahra kina Nan kina shirmen ko baki had’a wutar ba, ko da yake Allah ya sa ma kin iya had’awa domin nasan ku komai yi muku akeyi a matsayin ki na gimbiya.
“Kai Maman yara, na iya Mana in mun fita kewaya Ina ganin yanda kuyangina ke had’awa shiyasa na iya ai.
Haka suka cigaba da aikin su suna hira cikin Nishad’i da kwanciyar Hankali, yayin da gefe guda Kuma Baba Tsoho da Mai gaskya suke tattauna wani magana da nima Kai na ban ji me suke cewa ba.
**************   *********
MAIDUGURI
Yau kwanan Hanif Bakwai a Asibiti bai Farfad’o ba, haka Kuma kowa ya rok’i Zahra taje ta dubo Hanif taki Zuwa, hakan Kuma yayi ma Mama Hanifa ciwo sosai, duk da bata Nuna ma Zahra hakan ba.
Mami ko Sosai take fushi da Zahra ko gaisuwan ta bata Amsawa haka daddy a gidan a gurin mutum hud’u kawai take Samun relief Suma din kawaici kawai suke mata, daga Momy Kaka, sai Mama Hanifa, sai Jannat, sai Fannah Maman Sadeeq, Saboda Sosai jinin su ya had’u da Zahra.✍️✍️✍️✍️
Tom ya zarah zata kasance zata Amince kuwa ko bazata Amince ba,
Ga Kuma Sadeeq da Amaryan shi Zahra’u.
To wannan chakwakiya insha Allah zai kare ne a page na gaba wato page d’in k’arshe.
Taku Yar mutan Zazzau sarauniyar kanawa 😏🙄🤣💃🥰😍💖
Share
Comments
Like.
*’BOYAYYAR ‘KULLI*😭😭😭
STORY
           AND WRITING
               BY
ZEE ‘YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Wannan page d’in naku ne duk wani masoyi na littafin Boyayyiyar K’ulli son so fisabilillahi Ina yinku iya wuya🥰😍🥰💖💖
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE  35
*************************
KANO
………..”James ka tabbatar  kayan Nan sun iso, domin bana so a samu Matsala fa.
“Karki damu Hajiya. Ba wani matsala da za’a samu.
“Ok hakan Yana da k’yau.”
Wucewa sama tayi Abun ta tana taku d’ai-d’ai.
Waya take dannawa ta d’ora a kunnen ta Alamun Kira takeyi.
“Hello Hajiya Bahijja ya maganar mu ne kin San kayan fa yau zasu iso, kin ce Alhajin zai kirani bai kirani ba, kin San ni ban harka da k’ananun  mutane Koh, Ok Alhaji Shamo sunan shi,? Ba damuwa sai ya iso.
Murmushi tayi had’i da cewa, “Alhaji Shamo zaka shigo hannun y’ar, Wanda kayi yunkurin kashewa baka samu dama ba to ita zata kashe ka. Domin sai na d’aukar ma uwa ta fansa.
Niko nace wooh Khausar d’in mu aikin ki na k’yau fa.🤣🤣
*************************
MAIDUGURI
Zuwan Hajiya Jiddah ne da Maman Jos suka tasa Zahra a gaba sukayi Mata tatas sannan suka ce Aure ba fashi Kuma sai ta Auri Hanif.
Momy Kaka tace bazai yuwu a takura ma yarinya ba in bata son shi ya hak’ura.
Hajiya Jiddah tace bata Isa ba Dole ta Aureshi Hajiya Jiddah irin matan nan ne masu zafi.
Sai ya zama kowa lallashin Zahra yakeyi a gidan don ta Amince.
Mama Hanifa har k’asa ta durkusa gaban Zahra tana rokon ta, ta Amince ta Auri Hanif tayi Mata Alkawarin duk randa Sadeeq ya dawo Hanif zai sake ta ta Auri Sadeeq.
Sosai Zahra ta fashe da kuka, Saboda ita kad’ai tasan meke damun Zuciyar ta, ba Wanda zai tausaya Mata ne. Rungume Mama Hanifa ta yi tana kuka Tabbas baza ta tab’a iya kin mata wannan Alfarman ba. Ita wacece da k’anwar Mahaifin ta zata duk’a a gaban ta. Zata faranta musu rai Amma tasan har Abada Yaya Sadeeq shine farin cikin ta, Kuma Nan ba da dad’ewa tasan zata Mutu.
“Na Amince Zan Auri Hanif indai hakan zai sa Ahalina a farin ciki.
Gaba d’aya suka had’a baki gurin Fad’i “Alhamdulillahi.”
Ita ko Jannat tashi tayi ta rungume Zahra suka cigaba da kuka.
Alhamdulillahi Hanif ya farfad’o, Kuma anyi mishi K’yakk’yawan Albishir d’in Auren Zahra, Wanda haka ya Kara mishi Samun sauki.
Kwana biyu aka sallamoshi. Sosai Zahra take bashi kulawa duk da ba Wai tanayi ne a son ran ta ba sai don farin cikin Family d’in ta.
Wanda hakan ba k’aramin dad’i yayi ma kowa ba na wannan Family. An tsayar da ranar Auren Zahra da Hanif Nan da wata uku, Saboda zasuje ummara su dawo sannan ayi bikin.
*************************
Sosai Soyayya ta shiga tsakanin Sadeeq da Zahra’u, inda har ya kasance mu’amula na Aure ya shiga tsakanin su. Tun daga lokacin Allah ya dasa ma Sadeeq Soyayyan Zahra’u yake jin bazai iya rabuwa da ita ba.
Bayan sati d’aya……..
Sosai Zahra’u take Zazzabi inda take Maman Yara ta fahimci Ciki gare ta, Aiko Sosai su baba Tsoho sukayi farin ciki yayin da gaba d’aya kunya ta rufe Sadeeq da Zahra’u.
Haka dai suka wanzu suna tafiya har sai da suka Kai tsawon wata uku kafin su iso garin Zulum.
*************************
BAYAN WATA UKU
Sosai Zahra ta saki ran ta ta mik’a ma Ubangiji lamuran ta da fatan hakan ya zama Alheri a gareta Amma duk da haka Yaya Sadeeq na nan a ran ta.
Yau suka tashi da Shirin zasu k’auyen su Mami don su k’ara tuntub’an ta akan Maganar Yaya Sadeeq.
Kowa ya shirya ya fito yayin da Hanif ya fito ran shi a b’ace, don ganin yanda Zahra take ta wani rawan jiki akan tafiyar don shi har ga Allah Yana jin ya tsani wannan Sadeeq d’in.
*************************
K’AUYEN ZULUM
Suna isowa garin Zahra’u ta fara Amai Sosai, Nan suka tanbaya wani don Allah suna so a kaisu gidan Maigari.
“Ba damuwa kuzo muje, duk inda suka bi sai an kallesu Saboda yanayin shigan su.
Kasancewar gidan Maigari mak’ota  ne da gidan su Mami, hakan yasa ta kofar gidan su Mami suka zo wucewa ji kawai sukayi ance, “Sadeeq Kai ne.?
Da Sauri suka waigo duk da irin Raman da Mami tayi da bak’i da kod’ewa bai hana Sadeeq ya gane ta ba, da sassarfa ya isa gareta ya rungume ta Yana Mai cewa. “Mami meya sameki, me ya kawoki Nan garin.? Dai dai lokacin da Motocin su Zahra suka iso, da gudu  Zahra ta fito Motar ko gama tsayawa ba tayi ba.
“Yaya Sadeeq Sadeeq.!!!
Da sauri ya saki Mami ya juya don jin muryan Wanda duk duniya bazai mance da muryan ta ba.
“Zahraty kece haka, kin ga inda kika k’ara girma da gudu ta k’ariso zata rungume shi, dai dai lokacin da Zahra’u ta tare ta, “Malama karki tab’a mun miji. Ta fad’a a zafafe. Kasancewar yanzu taji hausa sosai.
Wani  gigitaccen Mari Zahra ta Kai ma Zahra’u, had’i da nuna ta da d’an yatsa, “ke kin Isa kice mun Yaya Sadeeq d’ina zaici Amana ta ya Aureki.
A rud’e Sadeeq ya rungume Matarshi ya d’aga hannu tamkar zai Mari Zahra, ko Mai ya tuna sai ya fasa.
“Haba Zahraty meyasa Zaki Mare ta baki ga bata da lafiya bane.
“Oho Yaya Sadeeq da gaske kenan matar ka ce Koh.? Lallai na yarda Maza baku da Amana ni na tsaya jiran ka Kai har Aure kayi, kawai juyawa tayi zata tafi ta yanke jiki ta fad’i. Gaba d’aya sukayi kan ta.
Yayin da kibd’iyatu tasa ma Sadeeq kuka “dama haka jinsin ku suke da son kansu,? Wlh sai ta koma K’asar su tunda a gaban shi har wata zata mare ta ya k’asa rama mata.
Baba Tsoho ne yayi gyaran murya, sannan duka suka dawo da kallon su gareshi duk da fuskokin su shida Mai gaskiya da Matan shi duk a kulle ne da rawani.
“Ya kamata ku mu tafi gida sai a warware komai a can, tunda an ga juna komai yazo da sauki.
Sun dunguma sun koma gida a babban falon bak’i na Alhaji Bukar suka yada zango, bayan an zauna ne baba Tsoho ya bud’e fuskan shi, Daddy jiki na rawa ya Mike Yana Fad’in, “Baba dama kana raye,?  Bai gama Mamaki ba Sai da Mai gaskiya ya bud’e fuskar shi shima,
“Sadeeq.!!
Daddy da Hajiya  Jiddah suka had’a baki gurin Fad’in “Ina Khadijatul kubrah.?
“Mama gani nan,” cewan Maman Yara da ta mik’e tazo ta rungume Mahaifiyar ta.
“Alhmdulillahi Allah Mai yanda yaso, shiyasa tun da Naga yaron Nan nasan jini nane. Ashe yaron ka ne Habibullahi, Nan da Sadeeq ya kwashe duk Abun da ya faru da shi ya basu Labari, ba Wanda bai mai kuka ba a falon.
Bayan haka ne Mai gaskiya ya fara bada labarin su…..
“Bayan an turamu K’asar Mali da wata biyu, wani dare Ina Zaune a bayan d’aki na a cikin barack Ina yin waya sai naji maganar wasu Mutane suna Fad’in, “ai mun riga mun gama shirya duk wani plan don har oga ma ya Amince za’a yi ma Sadeeq Mai gaskiya sharrin cewan shi dan ta’adda ne. Kunga life in prison, sannan Kuma ni Zan Aure Matar shi.
Sosai hankali na ya tashi na lallaba na koma gida na tarar da Khadijatul kubrah na zaune ta kasa barci. Kiran ta nayi nace ta had’a Kayan mu zamu bar Barack di’n nan, Khadijatul kubrah ta kasance Mace Mai biyayya bata tab’a mun musu a duk Abunda nace mata.
Haka muka bar K’asar Mali muka yanki Daji duk da nasan zamu iya had’uwa da Yan ta’adda, Amma zuciya ta ta kek’ashe akan gara mu Mutu a hannun Yan ta’adda da A b’atamun suna.
Munyi tafiya na tsawon watanni muna tafe muna yada zango, Bayan shekaru Masu yawa muna tafe a daji har Mata ta ta haihu ta haifi Yan biyu, duk wani d’awainiya nida ita mukayi dama muna tafe da Akwatin mu kafin lokacin da mu ka rabu da Akwatin sanadin wasu Yan ta’adda da suka biyo mu, haka da k’yar muka Sha.
Kwatsam wata rana sai gamu a wani had’add’en daji Mai Ni’ima, anan muka had’u da Baba ya gina gida Yana zaune lokacin da muka ga juna munyi farin ciki munyi Mamakin cewan Baba bai mutu ba.
A Nan yake bamu Labarin cewan Yan ta’adda suka d’auke shi, da k’yar ya samu ya kub’uta daga hannun su, Kuma ya kasa gane hanya.
Haka muka cigaba da Zama a dajin Nan tsawon wasu shekaru, kafin zuwan wad’an Nan Yara shine muka samu hanya kunji tak’aitaccen Abun da ya faru damu.
“Ikon Allah,! Ubangiji Mai yanda yaso tabbas kud’iran Ubangiji da buwayan shi ya girmama , shine mai tsara komai yadda yaso.
Allah mun gode ma da ka k’ara had’a fuskokin mu, muna rayayyu.
“Ke Kuma Fannah ga Yar uwan ki nan domin yanayin shigar ta da suturar ta iri d’aya ne da na jikin ki lokacin da muka tsince ki.
“Baba Tsoho ko baka fad’a ba wannan itace k’anwar Mahaifina da ta b’ace Safni don Ina ganin ta na gane ta, domin akwai k’aton pic din ta a ko Ina na cikin gidan Sarauta.
Da sauri Fanna ta taso ta rungume Zahra’u, daga lokacin komai nata ya fara dawowa Nan take ta tuno da komai.
Nan fa kowa ya kaure da Murna, Ashe ma Yar uwa ta na Aure cewar Sadeeq, bayan yaji Labarin komai daga bakin Daddy.
Bayan komai ya lafa da kwana biyu aka k’ara taruwa kan maganar su Zahra.
Baba Tsoho ya fara magana “to ke yanzu Zahra wa kike so cikin Sadeeq da Hanif.?
“Ni Baba na hakura da Yaya Sadeeq don bazan tab’a iya Zama dashi da kishiya ba, gara in Auri Hanif.
Tsalle Hanif yayi had’i da fad’in Alhamdulillahi.
“Haba Zahraty karki mun haka, kin San duk duniya kece Mace ta farko da na fara so.
“Nima tabbas ka Auri Zahra sai ka sakeni na koma K’asar mu in yaso a kashe ni. Cewar Zahra’u, tana gama Fad’in haka ta tashi tayi tafiyar ta.
“To Yaya Sadeeq sai kayi hakuri ka rungumi Matar ka Zahra dai tace ba tayi ehee🙄, taso mu tafi my Zahraty. Mik’ewa sukayi suka fice daga falon, tana fita ta fashe da kuka.
“Haba Zahraty Wai da me Yaya Sadeeq ya fini ne, ko don Kinga shi fari ni bak’i.? Don Allah ki daina kukan nan in ba haka ba nima Zaki sani kuka, haka ya dunga rarrashin ta har sai da yaga ya sata dariya sannan.
*************************
Bayan Wata d’aya
Kowa ya koma gida Yayin da Alhaji ya bama su Daddy kyautan gidaje kusa dasu.
Baba tsoho ya Auri Hajiya Jiddah ba’a wani d’auki lokaci ba suka tare gida d’aya da su Daddy sai dai kowa Sashin shi da ban.
Yayin da ake ta shirye-shiryen Auren Zahra da Jannat.
Bayan wata uku
Yau ne ya Kama dubban jama’a sun shaida Auren Zahra da Hanif Jannat da Mukhtar, Aure ne da ya samu halartan Manyan mutane daga wurare da ban da ban.
Bayan wasu shekaru
Zahra ne na hango d’auke da ciki, ga Kuma wasu kyawawan Yara Nan a falon suna ta Wasa, magazine d’in da ke Hannun ta ta ajiye “ke Momy Hani kun dameni fa, Daddy junior ku tashi kuje kuce ma Mama Zahra’u in tayi girki ta zubo mun.
Gaba d’ayan su tashi sukayi harda Wanda ba a aika ba ma suka fita suna hayaniya.
Yara ne su Biyar Daddy junior shine babba yaron Sadeeq na farko, sai Hanifa Wanda suke ce Mata Momy hani, ita da Fati kanwar junior shekarun su d’aya sai yan biyun Zahra’u duka Mata Hassana da Hussaina.
Sai Momyn Sadeeq da ta k’ara Haihuwa ta haifi Namiji da Mace,
Sai Mami ita ma ta k’ara Haihuwa har uku biyu Maza d’aya Mace.
Nan family sunyi Albrka yayin da farin ciki ya wanzu cikin zuri’a su.
“Aunty Zahraty na shigo Ina ta Sallama shiru tunanin me kikeyi ne haka.?
Hararan shi tayi had’i da jefa mishi magazine d’in hannun ta, “ka ga ka daina cemun Aunty Nan, sannan Ina tunanin rayuwa ce.
“Da fatan ba tunanin Yaya Sadeeq kike yi ba, ya fad’i haka cikin zolaya da Wasa.
“Haba ni yanzu Ina da Wanda ya fi mun my sweet husband d’ina ne Mijina yaro Mai halin manya Wanda ya iya tattalin Mace Allah ya barmu tare 🥰.
“Ameen ya Allah 🙏 Mace ta gari, muje ki bani Abinci in ci, ya fad’i haka Yana d’ago ta.
“Ya kamata ka fara yin wanka tukun na don naji kaman tsami kake yi.
Ta k’arisa maganar Tana dariya.
“Kai Kai lallai ma yarinyar Nan kinci bashi kuwa🙄.
*************************
A gurguje bayan tsawon lokaci Zahra’u da Momy Fannah da duk Ahalin sunje Masarautar Amrish inda suka tarar da komai ya canza har an gina Masallatai a garin, a Nan sukaji mutuwar Amrita da Mahaifiyar Momy Fannah bayan sunyi kwanaki suka dawo da Sha tara na arziki.
*************************
“Mahauka ta.! Mahauka ta.!
Wasu gungun Yara ne suke bin wasu mahaukata gunin ban Tausayi domin d’ayan ma jini ke zuba a jikin ta d’ayan ko duk Yara sun fasa Mata Kai da jifa. Kura Ido nayi da k’yau sai Naga Ashe Yagana ne da Bintu. Nace ikon Allah,
Allah kayi Mana K’yakk’yawan k’arshe……✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Alhamdulillahi Tammat bi hamdulillahi. Wa subhanakal lahumma wabi hamdika Ash hadu Allah ilah ha illallah.
Ya Ubangiji Ina rokon ka Abun da na rubuta dai dai ka bani ladan shi, Wanda Kuma nayi kuskure ka gafarta mun.
Yau na kammala littafina Mai suna Boyayyiyar K’ulli da fatan ya fad’akar Kuma ya nishadantar daku.?
Nasan da yawa zasu ce Basu ji ya Labarin Khausar ta k’are ba, to ku biyoni bashi a Littafi na na gaba Mai Suna waye Masoyi na gaskiya. Insha Allah zaku ji Labarin Khausar. Taku har kullum
Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 😏😏💖🥰😍😍😍
I love you All
Mu had’u a Next Novel d’ina Mai suna Almajirai ma y’ay’a ne Wanda Zan fara posting jibi insha Allah 🙏.
Share
Comments
Like.

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements