DOCTOR ESHA Page 1 to 10 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / DOCTOR ESHA Page 1 to 10

DOCTOR ESHA Page 1 to 10

DOCTOR ESHA Page 1 to 10

Doctor Essha👩‍⚕️
          By J hajara
 Bismillahi rahmani rahim
               1️⃣&2️⃣
Tafiya take a hankali kamar bazatayiba Kuma gashi gari ya akwai hadari sai iska mai karfi hade da kura ama ko ya damaita, tafiyanta kawai take ciki kwanciya hankali kamar ba komai.
A gaban ta kadan na hango Yar black beauty
Ta juyu tace” Essha Essha takirata har sau biyu kiyi sauri fa imbahakaba walahi zan wuce kisan zamu iya rasa Nepep a yanda gari yake a haka ko? Ama wance aka Kira da Essha ko d’ago kanta batayi ba sai murmushi ta kawai takeyi,
can naji wani sauti murya lalausa nacewa haba bestie nasa  ki,Kona ki tafiya nasa dole ne kijirani,wance aka Kira da besty ta nufota ta zungure mata kai tace” walahi Allah Essha kina kureni.tace”haba  bestie yihakuri kimin afuwa ta rike kunne,
ok naji yi sauri munkarasa gida, Essha ta amsa da tomuje.
 Suna fitowa baki hanya sukayi sa’a Nepep. Bestie tace” mishi Mai Nepep Bukar Ari’i zamuje ta Yumaco, mai nepep ya amsa da ok nagane shigo muje. Suna shiga suka Soma hira biki da suka fito na  wata Yar ajisu. Essha tace”
 kisan maiye besty? Bestie tace ni akuyane da zan sani, sai kawai duk suka fashe da dariya, ama wlh guri KAMU na ya burgeni da kiyyi niyya aure kenan sai mugayato Mai decoration din ta miki cewa Essha.
Bestei tace” Lallai yariya ki rainani ke baki ce zakiyiba sai ni. Essha ta Bata amsa da iyye toh ni wlh Banda niyya aure.inshaallah sai nayi karatu likita.
 Ni da Allah kiyi shiru da wanna batun  bakisa fa nufi Allah.ba sai dai kice haka.  Cewan bestei.
 daidainan mai nepep yace”   mun’iso fa cewa Mai Nepep;
 yawwa ga kudika mun gode.
Bayan sun sauka Essha tace” Toh besty saina shigo anjima tafada tana murmushi,da Allah min shiru haka jiya kika shayani baga ki ba, please forgive me natsaya waya da Khalid ne har nayi bacci . Naji ,Khalid kam Yana ban tausayi tundashi yayi niyya aure yanzu kekam ba tabbas cewa besty.ni da Allah ki kyalleni Bata soyaya da aure nakeyiba,karutuna kawai.toh Essha Allah yazabe mana mafi alkhari. Ameen ta amsa ta shige gida.
Assalamualaikum? Wa’alaikumusala Amir ya amsa kanita Mai bi mata.mufeedat autarsu ta taso da gudu tazo ta rugumeta, Oyoyo Sis Essha ,yawwa autar mummy. Ina mummy ? Tana kitchen,kisan daddy Yana  azumi yau alhamis,  Eh hakane.baza naje na same ta, Wai Walid baka gani bane? Oh sorry sis,game Dina ne yatafi dani,kisan motar race Dina inbaka concentrate ba zaka fadi, dats y naki juyawa,Kuma sis saina fiki iyawa. Common jare yimin shiru naji. Daddy ya dawone? Eh ama su fita da khairat sunje chemist ta taka kusa. Subhanallahi 😣 Allah yakiyaye na gaba.Ameen duk suka amsa.
Ta wuce kitchen wurin mummy. Mummy? Mummy? Mummy? Na’am haba Essha wana Kira haka kamar kiyi makanta,ko sallama fa bakiyi min sai kwala Kira cewa mummy.ohh so sorry mummy na.ya gida? lafiya lau.ya Kamu toh,wallahi mummy baki ga guri ba ya hadu,bara kigani. A Ina akayi mummy ta tambaya. A Ta’al Conference Hotel ne. Tafito da wani hadede waya daga ciki jakata sai walkiya yakeyi( iPhone x+)kenan.
Mum kigani,wow ama ya hadu, amarya ma turbakallah .ai mummy Bari kawai sufito amare. Kedai kalleni da shirmeki kije ki chanza Kaya kizo kishirya mun kan dinning daddy ku yakusan dawowa cewa mummy. Essha tace Wai wazai gamin khairat yanda za’a ririta kafana.kedai baruwaki jekiyi aiki Dana saki. Kk mummy. Ta wuce dakita gwani kyau dashi.tana chanza Kaya ta dawo ta Taya mum na jera Kaya aka dinning.suna gamawa aka fara Kira sallah mahgrib .
Doctor Essha👩‍⚕️
      By J hajara
    3️⃣&4️⃣
  Kowa yatashi sukayi sallah,suna jira daddy su yadawo.can sai gashi sun shigo shi da khairat.
Assalamualaikum? Wa’alaikumusalam duk suka amsa. Welcome back dad? Yawwa Amir. Wai Ina autar gida na ne? Walid ya amsa da cewa ai Tana jika daddy Wai tayi fushi da Kai,kafita da khairat baka fita da ita ba. Haba autar daddy zo yi hakuri,kiga khairat ciwo taji a kafa zo ga ice cream na kawo Miki ke kadai Zaki Sha Kar kiba kowa kijiko? Eh ta daga Kai Tana musu gwalo. Duk suka za zauna a dinning, mummy tayi serving nasu.wata hadadiyar farfesu kazane   ,sai white rice& stew da coslow da coconut juice.kowa yayi shiru ba abunda kakeji sai Kara cokali.  Daddy yakashe shiru da cewa Essha kiduba  Jamb naki ko?  A’a ,sai da safe Ina shiga gidasu summaiya( besty)zan duba .saboda nayi register da number tane,ok Allah yabaki nasara.Ameen.
Mummy tace toh Abba Essha ya magana tafiyamu bikin kaduna gashi gobe Friday? Yace eh dazun muyi waya da hajiya na tace itama zantaje,na mantane ba fadamikiba.mummy Nima zanje? Cewa walid.a’a maganar haddu ku,Kai da amir, khairat babu inda zukuje, mum nifa inji mufeedat? A’a autar daddy zabarki a gida da sister Essha da daddy ko,saura naji wani yatabata acikiku, kuga abinda zamuku. Oh mummy ki shagwaba yariyana Allah amir cewar amir.eh  din kubar min kayana.
Daddy yakalli mummy yace my dear inaga fa bazaki samu zuwa ba Essha ne zantaje ita da hajiya na. Essha  da ji haka nandanna ta kore . Kowa na rige rige Bata ruwa. Mummy tace ya’akayi haka? mummy korewa nayi. Sannu ,ko magana tafiya ne? Ta amsa da a’a daddy . Toh gobe kishirya da misali karfe biyu zaku wuce da hajiya da driver,Nan take taji gabanta ya fadi tayi shiru. Amir yace Sis Essha daddy na magana fa, na take ta dago Kai tace toh dad Allah yakaimu ameen daughter bakiso tafiyane ? Cewa daddy,mum ta amsa da cewa ai dole taje, kasan Bata taba tafiya ba. Walid yace Nima mum banta ba bafa . A’a  ku sai next tym zakuje inshallah.toh daddy.   Akira sallah Isha duk suka Mike. Amir da Essha suka kwashe plates zuwa kitchen,  khairat na tsokanarshi,yace Zaki warke ai Kuma zan Rama, Eh din ta amsa. Zan kamaki ai, mum ta amsa da cewa khairat baki da kunya ko? Yaya ki  kegayama haka? Mummy kiyi shiru ki kyaleta zan kamata ai.
Essha tace haba babba yaya,Yaya amir kamata afuwa kasan Bata ji dadi jikita.naji. duk suka Gama kwashe kaya.su amir da daddy suka wuce massalaci ,mum ta wuce room dinta,su khairat ma haka.
Essha na shiga dakita ta fada wanka sanan tayi alwala ta fito, Tana fitowa tasami wayata nata Kara.tana dubawa taga k♥️.suna data sa a number Khalid.tayi pick yanata sallama taki amsawa, daya bangare naji Yana cewa Haba soulmate harda sallama ne kike fushi dashi?  Ta tura baki kamar Yana gabata tace toh bakai bane .haba love kiyi hakuri bazan karaba, ta amsa da cewa aguri nafa munjira ka,har tsawo two hours baka zo ba har aka fara iskana fa. Da Allah kiyi hakuri love, Allah daddy na ne ya tsayar dani. Ohh shikena tunkace daddy ne ba matsala. Yawwa tawa, toh yakike,lafiya lau, ya biki kamu. Lafiya. Saura namu Koh? Tayi shiru Bata amsaba.yace yakikayi shiru ? Can ta amsa da Allah yanunamuna. Essha yakamata kibar magana school dina. I promise u inkizo gida na zanbarki ki karasa . Tace ni gsky a’a don bayarda da cigaba karatu mace a gida mijitaba, gwara kawai tayi a gidasu. Ama love bakiyarda dani bane nayarda mana . Hmmm yaja dogo nufashi, toh yanzu sai yaushe zangaki?  Ina ga fa sai Monday ranar da zamu dawo. Ina zaki? Biki zamuje ni da hajiya a kaduna. Eyya ni gaskiya tafiya biki na bai kwanta min ba ya fada.  Wlh Nima haka don inaji wani matsanaci faduwar gaba narasa dalili. Kita addu’a kiji ko? Allah ya shige mana gaba ta amsa da ameen. Da Allah love ki kulamin da kaki? Kar kadamu. Ok ki gaida mun hajiya zantaji good night sweet dreams.take kashe wayata. Ta nufi baki gado ta zauna,  inta fa gaskiya tafiya kaduna nan bai kwanta mata ba.  Ta naji a jikita kamar wani abun zai samaita. Can tace auzubillahi
Chimaa🥰 I miss u♥️
*Doctor Essha*
 👩‍⚕️
Writen-by- j hajara
5️⃣& 6️⃣
   Tace” auzibillahi ta kori shaidan ta Mike ta shimfidar danduma ta gabbata da sallah Isha Tana idarwa ta gabatar da Azkar tana gamawa ta Mike ta nufi wardrobe ta ciro wata simple pink gown na bacci tasa yakai mata har kasa. Ta dauki hijab tasa,ta fito parlor.
 tasamu suna kallo tashar   B4U movies asa film din ENTERTAINMENT kowa sai dariya( sbd film din na barkwaci ne). Jiki a sanyaye ta nufi daddy ta tsuguna, daddy yace” ya akayi daughter?
Daddy dama inaso naje gidasu sumy ne,inaso zaduba jamb.
Daddy yace” Essha maiyasa baza kibari da safe kiduba? Essha tace” A’a  daddy gobe fa da karfe 7:00am ina da lecture Kuma fa bazan  dawo ba sai 6:00pm,
toh kije Kar ki Dade, ga amir ya rakaki.
Oh daddy amir ya fada Yana tura baki,
daddy yace” yimin shiru basan tauri kai tashi kuje  .
Suka fito suka shiga gidasu sumy( bestie) dayake tsakanisu ba nisa. Gate nasu Essha na kalo nasu sumy . Suka shiga da sallamarsu . Aka amsa,
su tarar da dad, mom sai Yaya nazeer (babba yaya sumy).  Amir sai mita yakeyi kasa kasa Yana tura baki. Mum ta tambeyeshi   Wai wayataba kane?
Ya amsa da cewa ba Sis Essha bane nandana ba nisaa shi ne sai na rakata. Yaya nazeer yace” haba boy, inbaka rakata ba waye zai rakata? Essha tace” shareshi da Allah big Bros ka kulashi ne.
 Amir yace mum kijita fa? Yi hakuri amir.
Mum Ina besty? Tana daki,tace” okay bros one minute ta daga ma amir yatsa. Yamaka mata harara, sai sanan daddy su sumy yace” amir ya school, lafiya klau, toh Allah yabada sa’a, Ameen daddy.
Daddy yace”yanxu dai amir ku girma ku daina Kira mana sallah koh? a’a daddy ba time ne. Toh a gyara kajiko,
Inshallah daddy.
    Essha daki sumy ta haura, daki yayi kyau, teddy ne manya manya guda biyu sucika sama bed, tayi sallama bataji ba, da allamu waya takeyi. Don sai murmushi takeyi. Essha tace” ke Wai da Allah dawa kike waya ne? Sauri fa nake zan wuce. Ta” amsa da Rabin Raina mana, Wai bashir? Eh man. Toh da Allah ki katse Kira Nan don nasa bagamawa yanzu ba, abun zanduba a wayaki, ga amir na jira na a kasa.bestie tace”   Naji naji Essha. Sweetheart zankiraka  anjima kasan inbana kashe yanzu ba Essha hanamu sakewa zatayi.daga cikin wayan ya amsa da okay bye  ki gaisheta,
Tace”zantaji bye.ta katse kira.essha Tace”
Bestie wayaki zakiban jamb Dina zan duba sauri nakeyi.
Ok gashi , sumy ta Mika mata. Tana dubawa, Sumy  tace “dazu muka Gama waya da mutumiki, Wai da Allah zakije kaduna da gaske?
 eh Esshata amsa da Kai,
 sumy ta marairace fuska tace “eya bestie zanyi missing naki gashi zaki wuce bani. Karkidamu bawani dadewa zamuyi ba Monday zamu dawo, Kuma kiga shiyasa na shigo na sallameki gabadaya, Allah sarki ni Khalid ne yaban tausayi, Wai yanaji wani iri a jikishi kamar kar kiyi tafiya na.   Wlh Nima hk bestie tun lokaci da dadnina ya fadamin nakeji faduwar gaba. Toh Allah yasa yazama alkhari ameen. Can sukaji Kara shigowar message a wayar sumy. Suna budewa suka sa ihu  sanda su mum suka firgita, ya nazeer da gudu ya hauro . Yana tambayasu Mai ye samaiku, ba mgn sai murna. Sumy ne ta Mika mishi wayata, Yana dubawa yaga jamb results din Essha tasamu  252🤗. Yace” wow little sis congrats,
 Thanks Yaya ai dole kiyi ihu, Essha buriki yakusa cika. Mum da dad suka hauro . Maiye faru? Ya nazeer ya gayamusu. Wow congratulations daughter ; Thanks ta amsa . Ta juya tace mum sai da safeku da murnata, sumy tace” bazaki jira na raka kiba? a’a na hutar dake . Tana sauka tasamu amir tace” tashi muje yace yadai sis da wuri haka? Eh ta fada. Suna tafiya a hanya Tana bashi labari Jamb nata har suka karaso ciki gate nasu, sai murna yakeyi kamar shine yasamu. Suna karasowa ta tsaya Tana ma gateman  mgn aka ya kulle gida bamai fita. Ya amsa da toh. Amir ya wuce ciki ko sallama baiyiba yace” mum,dad sis Essha tasamu 252.   Mum tace Allahu akbar, alhamdullila. That’s my daughter ai tayi gado na ne, daddy yace” ah ‘ ah abun gori ne, ai sai duka suka fashe da dariya, dad yace” Ina Essha din? Amir yace Tana zuwa daddy kafi yagama rufe baki sukaji sallamarta, su amsa kosa na mata congrats.   Walid yace” sis Essha dole na poping Miki champagne a jiki kiyi kokari . Tace” walahi Kar ka kuskura, Allah daddy kayi mishi magana.
A’a  walahi daddy sai na mata ai Ina tayata celebration ne Koh? khairatTace” eh man, Nima zantayaka.    Duka su  biyu suka nufi dinning area, khairat ta bude fridge ta fitar da champagne guda ta rike daya tabama Walid daya.  Duk suka nufota,suka balle murfi, suka fara mata wanka dashi, daddy ne ya dakatar dasu, yace”ya isa kar kusamin likitana tayi mura.  Essha wani University kikasa? Tace’ Dad A.B.U(Ahmadu bello University z). Daddy yace”Oh natuna, yanzu dai kowa yaje ya kwanta kuga har autana yau tariga ku bacci. Amir da Walid suka amsa da ok dad, good night, yawwa  good boy’s Allah yatashemu? Ameen. Mum tace” Essha zo ki dauki mufeedat ki kaita daki,toh mum. Khairat tama mum,dad peck a kumatu , tace” mum dad goodnight? Daddy yace kiyi addu’ a fa kamin ki kwanta dun nasaki. Daddy I will inshallah bazamantaba. Good yace. Suma suka nufi nasu daki.  Essha na kwantar da mufeedat itama ta wuce zuwa nata daki. Wanka ta karayi sanan ta canza kaya, ta dauki wayata, ta bude WhatsApp ta daura results nata a status, friends nata mata  congrats, Tana musu reply. Sai around eleven tayi addu’a bacci ta kwanta. Aciki bacci Bata samu nutsuwa ba sai mugaye mafarke mafarke take tayi,nandana ta farka da wani Kara sanda mum da dad suka farka, da gudu suka karaso dakita, da sauri su karaso wurita. Dad yace”  lafiya Essha? Maiye samaki?  Bata iya amsawa ba, sai ajiya zuciya da zufa ta ketayi. Mum ta dauko ruwa Mai sanyi ta bata, ta yayye mata gashi kanta da ta barbazo a fuskata tace” sannu Essha, maiye samaiki, zatayi magana daddy yatare ta da cewa yi shiru Essha ba ‘ afada mugaye mafarki. Ta gyada Kai Alama gamsuwa. Mum tace” yi addu’ a ki canza gefe kwanciya kijiko? Eh ta amsa murya na rawa. Mum da dad suka fita a daki jiki a sanyaye . A zuciya ta tace ya Allah ka kawomin dauki basan maike shiri faruwa Dani ba.
   Washe gari a makare ta farka around 7:00am tayi sauri sauka da addu’a tashi a barcci a bakita, tayi sauri shiga toilet ta Dora alwala tafito da shimfidar danduma ta gabbata da sallah asuba ta Dade zaune Tana addu’a, Tana shafawa, ta Mike ta dauki wayata Tana dubawa taga missed calls din Khalid ne Dana besty, suka cika waya, batayi harama kirasuba, dun tasan besty ta shiga lecture , Khalid Kuma intakirashi ,. Za su iya jimawa suna waya gara taje ta gaida su dad, inta dawo ta kirashi,. Ta jawo teddy slippers nata dake karshi gado ta saka, ta fito jiki a sanyaye, ta Tara dasu amir a parlor suna karatu,  duk suka hada baki sukace” good morning sis ? Ta amsa da fara’a da morning my joygivers, how was ur night? Suka amsa da alhamdullila, Ina mum da dad?  Dad yaje dauko hajiya,
 dakashi? Amir ya amsa da eh Wai batask driving bala driver Wai yacika gangaci, toh Allah yakawo su lafiya, ameen. Ina mum da Kareema(Yar aikisu) ta tambaya? Suna kitchen suna hada ma hajiya koko da kosai. Walid yace” wlh hajiyan nan tacika iyayi,mum tafito daga kitchen ta amsa iyye Walid mamana kake cewa tacika iyayi? A’ a mum afuwa da khairat nakeyi, oh nine sa’a ka koh? A’a goggo khairat (😅) mayarda  wuka. Taja kwafa.  Ina kwana mum, lafiya. Mum tace” zonan Essha ta taho a hankali. Zauna mgn zamuyi, maike damuki? Na lura tun lkc da daddy ki yamiki mgn tafiya ki ka rage walwala, kobakison tafiya ne? Aa mum. Toh kisanki ranki kinjiko baby, Yan uwanki na kaduna Basu da matsala Kuma ai ba wani dadewa zakuyi ba, yau Friday, Sunday ko Monday zakudawo inshallah ,ki sanki ranki kinji ko, eh  ta daga kai. Yawwa  humaira n, bani wanan smile naki nan, ta washe hakora sai shining sukeyi, yawwa dats my doctor ( inkanaso ga ni fariciki Essha toh ka Kira ta da doctor). Toh ki Taya  Kareema hada Kaya breakfast, kinga daddy ki sun kusa da gari lafia, sai kinje ki hada kayaki ko? Owk mum, ta wuce kitchen ta Tara da Kareema na jerewa a ciki tray, tace” kawo natayaki,  Ina kwana aunty Essha? Llfy , yasu ummaki? Lfy. Yawwa hada flasks sai kizo ni zanfitar da wanan. Kareema tace” nagode anty, suna Gama jerewa tace “mum  baza naje nashirya, okay sai ki fito.
More comment more typing
Comment
and
 share🙏🙏🙏😘
Doctor Essha
  👩‍⚕️
    Written-by j hajara
7️⃣&8️⃣
   WACECE ESSHA
Asali sunata *AISHA AHMAD*  haifafiyar gari uke ne, dake jahar Nasarawa . Mahaifita cikaikenyin suna shi AHMAD YUSUF NOMA,  Dan asali gari uke.    Aiki ne ya dawo dashi gari Lafian bare bare da zama.
Matar daya  hajiya Fatima, Yana da kanne biyu, Alhaji Adam(daddy karami) da Aunty Jamila suna kirata da(big mum)Tana aure  a kaduna,
 Mahaifisu ya jima da rasuwa, yanzu maihafiyarshi ne kadai a raye, sunata Hajiya maimuna , ama suna kirata da hajiya uke, Tana zama a uke , anyi anyi ta dawo lafia  da zama taki.
Daddy yata mukammai kala kala  tun daga kan councilor,har zuwa Dan majilasa, yanzu  hk Yana aiki ne a government house dake lafia.
Mummy Kuma business woman ce Tana safara zanuwa, Tana da babba shagota a shendam road.
Allah ya albarkaci su da yara biyar, Aisha( Essha), Yusuf(amir), ummulkhairat, Abdullahi( Walid) sai autarsu mufeedat.
  Alhaji Adam  Wanda akafi sanni da daddy karami, matarshi daya, Mai kirki ( anakirata da auntyn yara) yara shi bakwai, Abdulhamid, salis, aina’ u, khamis, hafsat , hanan sai Hassana daya ta koma.
Sai big mum( aunty Jamila) yara ta itama hudu, usman, Yusuf anakirashi da Abba, hunaisat, Sameer tunda daga kanshi Bata Kara haihuwa ba, ayi magani har agaji. Mijata babba Dan kasuwa ne, big mum ta rige su dad aure don Tana da shekara sha bakwai babasu ya aure da ita.  Yanzu haka hunaisat za’a aurar.baya tayi candy nata, tace ita aure kawai take so.
Essha tayi primary and secondary school nata a Hall mark international academy dake ciki gari Lafia, Ta sauke alqur’ani maigirma da saura littafai na addini, ta zana WAEC nata da jamb last year, batasa mu jamb ba, shiyasa tasake maimatawa har Allah ya Bata sa’a tasamu a Wana shekara, Amir na jss3, khairat da Walid suna Jss 1, mufeedat na nursery 2.
Essha hadadiyar yariyace  wance bazata wuce shekara shabakwai ba, Tana nan fara ba can ba, baza a sata a siririya ba bakuma za sata a Mai jiki ba, fuskana Mai Dan tsayi, hanci har baki, idon na ya manya manya ba Sosaiba, farare kal kal, lumsheshu, kullum kamar maiji bacci, bakita Dan karami, pink lips gareta,  a jiki kuwa ba a magana, dun tana daga ciki jere yanmata da akekira masu coca cola shape,  dukiya fulani nan a cike yake dam🙈, haka hips kamar zansu fado.
Kawanta daya tak ko Kuma ice aminiya, *summaiya*, tare suka tashi, tun suna yara har girmansu, sumy ya ce ga Doctor Abbas jibrin, daddyta babban likatane, sai mahaifiyarta hajiya ikilima.
Su biyu Allah yaba iyayasu, nazeer, sai ita summaiya, sumy tun last year da suka zana jarabawa tasamu FULAFIA ( federal University lafia) Tana karata mass com.
Essha tun da taso da buri karatu likita  ta taso, sallah ta biyar a kullum sai ta roki Allah yacika mata buri ta. Shiyasa ma Bata kulla samari, komai naci saurayi hk zaigaji ya barta. Sai a kan *khalid*, sun hadu ne a wata super market taje shipping shima naci da magiya yayi ta mata  sanan ta kulashi,Kuma ashe abokin Bashir ne saurayi bestie. Shiyasa takara bashi dama .
Wanna biki da zasu je a kaduna na yariya big mum ne wato hunaisat.
 CIGABAN LABARI
Ta gama hada kayata tsab a karamin wani purple trolley, Tana Gama hadawa, tajiyo sallama kareema. Ta amsa.
KareemaTace” aunty inason na gyarami ki dakin.
Essha tace’ huta abiki Kareema zan gyara.( Essha iri yarane nemasu tausayi da jikan Dan Adam). KareemaTace” toh aunty.
Tana aje trolley a gefe bed, ta soma jin ringing din wayata dake gefe side bed.
Tace” kareema” da Allah Mika min wayana , tayi sauri ta dauko mata dun tana matukar Bata girma, tana dubawa taga sis hunaisat. Ta daga waya oh amarya .
Hunaisat tace” karkimin magana nayi fushi dake, nagama gayawa friends Dina special sister na zata zo tun biki na sati daya, shine kika gwasileni, wato ma ba dun dad yace”  ki zo ba bara kizo ba koh? Essha tace”    Haba mana my amarsu Allah jamb ne ya rikeni  .
Toh naji yanzu da wani lokaci Zaki zo? Ina ga fa sai two zamutaso.  Eya sis  sai two maiyasa? Nine ban dan jin dadi  ba,
Eya Allah ya baki lfy sis aman ban ji dadin ace duk event din bikina ace ba ki aciki, Wai Kuma sai two zakutaso, haba yantzu fa 9:00 da Allah kuta so da wuri gasu yaya Abdulhamid, su aina’u da hafsat tun shekara jiya suka  zo, ama ke har yau. Haba cewa hunaisat.
Yi hakuri sis Allah hajiya uke nake jira. Tace” toh dole ne sai ki zo da ita?? Essha  tayi dariya ai dole sai dan tsofofi.  Oho dai naji saina gaki, ok sai munzo ta kashe waya.
Oh ni Essha Wana surutu na hunaisat kamar ba amarya ba,
kareema tace”ai aunty zatayi ta daina, hk yayana ana saura kwana biyu daure aure ta adabi mu da surutu, ranar daure aure kuwa sai kuka Essha tayi dariya tace” lallai kam 😁
comment and share🙏♥️😘
Doctor Essha
👩‍⚕️
Written-by -j hajara
9️⃣&🔟
Suna ka hira sukaji sallamar mufeedat suka amsa. Tace sis Essha inji mum Wai ki fitoh muyi breakfast.ok gamuna zuwa, kareema muje ko? A’a aunty zan gyara daki Kai kareema kenan toh sai ki fitoh.
Tana fita ta samaisu dukasu a dining table.
Walid yace sis Essha kiyi sauri kinyi serving Dina ni yunwa nakeji, yimin shiru aci ci kawai, ai gwarani Ina ci Ina jiki nafi Wana yanuna amir da hkl shi ke waya. Kuma ace ci ba kiba asara gari 😅.
Essha tace nidai baruwana. Amir ya sauko da niyya Kama walid da gudu ya boye a baya Essha. Sis kibashi hakuri,ni banza karaba,
Amir yace” Kama Kara kaga yanda zanyi dakai,amir kamishi afuwa cewar Essha, wallahi Allah ya taimakeka sis ta kareka.
Sis ni da Allah kiyi serving am hungry mufeedat ta fada, toh autar mummy ke zanfara serving zauna, Ina mummy? Tana wanka suka amsa. Ok yanzu Mai zan samuku?
Amir yace sis mufa baza musha koko da kosai ba na hajiya ne ok naji.
Ta serving nasu plantain, soyaye kwai da tea.
Walid yace”sis zanyi missing naki two days fa ya fada baki shi cike da abinci mufeedat tace sis Essha a islamiyar mu a hana mu magana baki mu cike da abinci.
Khairat tace fada mishi dai, yanzu dai kowa yayi shiru kuyi koyi da Amir, amir Kai na Kato ana yabeshi.
Amir yace sis da Allah inzaki tafi inaso kiban aro charger din laptop naki nawa ubaid (abokishi) ya dauka, ok badamuwa Yana kan side drower na. Thanks sis.
Sunakayi breakfast sukaji sallamar daddy hajiya da daddy karami. Da gudu mufeedat ta nufesu Oyoyo ta rugume daddy karami, Oyoyo autar daddy, ykk ya school? Ta amsa da lafiya klau.
Hajiya tace” wato wanna Mai suna aljanu na bazata min Oyoyo ba babata kadai ta sani ko, mufeedat ta Bata fuska zatayi kuka dun bataso hajiya nakirata da Mai suna aljanu nandanna sai tayi kuka aikuwa kamar jira take ta fashe da kuka daddy karami ya lalasheta, su amir suka taso suka masu hajiya sannu da zuwa,  hajiya ta nemi guri ta zauna tace” Kai Amiru zo karage abun sanyi na, wanna ai sai yasa na bushe ana 😅. Amir yabata fuska hajiya tazo kenan da Bata ma mutani suna, ya dauki remote din A.C yakashe gaba daya.
Mummy ta fito sanye da gown baki ta je gefe hajiya ta gaisheta har kasa sanan ta gaisa da daddy karami. Ta musu iso zuwa dining table,hajiya na zama daddy dakashi yayi serving nata.
Baya sugama breakfast. Hajiya ta kalli daddy tace ” badai Bala driver ne zai tukani har kaduna ba ko? Daddy yace eh shine hajiya, tun bai rufe baki ba ta tareshi da cewa in har Bala driver ne zai kaita kaduna ita walahi ta fasa zuwa har da kukata, Walid dasu khairat sai dariya suke Tamata .
Mummy ta ce” yihakuri hajiya kidaina kukana Ina ga baba su khamis sai yakaiku ko? Daddy ya amsa” bazai iya tuki ba, saboda Yana da ciwo a hannu, kawai yadan za’ayi za Kira baba driver yakaiku . Ya dauki waya yakira baba driver yace mishi yashirya zai Kai su hajiya kaduna, yace toh Alhaji ba matsala, da karfe nawa ne tafiya? Biyu ne toh Alhaji sai nazo.
Da misali karfe biyu su Essha su shirya tsaf za su dauki hanya kaduna kaduna gari governor.tasha dogo rigata na less Black yana da digo pink aciki, fuskana bawani makeup ama duk da haka ta fito, tayafa gyaleta Pink, takalmita hk, ta fito gwani sha’awa son kowa ki Wanda yarasa. Har zata shiga motar, sai ta tuna ta Manta da jaka Kuma a akwai wayata aciki da abubuwa da baza arasaba, ta fita da sauri ta shiga ta dauko.
Tana fita taci karo da mum nata rike da calendars da jaka da yawa na biki, ta Mika mata gashi kiba hunaisat, daddy yafito da bandir din hamsin hamsin yabata daya, ta amsa tayi godiya, daddy yace Essha banda yawo kinjiko ta gyada Kai, ta duba daya daga ciki jaka taga Kaya cinye cinye ne na biki.
Tace” gsky mummy na kiyi kokari. Abu fariciki ma tana duba baya jakakuna taga hotuna hunaisat da angota suyi kyau, a kasa Kuma asa Courtesy by Sis Essha.wow mum nagode, ta rugume meta, baba driver sai horn yake ta yi Alama tayi sauri, baya San dare yamusu a hanya, Kuma gashi yau Friday. Da sauri ta bude boat ta zuba Kaya ta shiga mota, mufeedat sai ihu takeyi zatabi ta, Walid da khairat har da gutu hawaye, daddy yajasu zuwa ciki, yace addu’a zakumusu, Allah yaqiya hanya ba kukaba, daker mum ta lalashi mufeedat tayi shiru sanan bacci ya bigge da ita.
Essha ta texting ma Khalid da bestie mun wuce, Khalid ne ya reply. Da Allah ya tsare hanya dear.
*************************
   ABUJA, NIGERIA.
Wani tamgameme gida ne na gani a fada, girmashi kamar mansion, na lura duk girma angwan ba gida da yakai Wana girma da haduwa, baki gate din kuwa duk security ne, gaba da baya, dukanisu sanye da black suits. Ciki gida Kuma ba’a magana dun ciki kamar outside country,
Gida ALHAJI UMAR TYCOON kenan, shaharare Dan kasuwa, Kuma cikake Dan boko, daya nimi yataka dangote a kudi, da shahara, yakai yakawo ma yayi kwari suna tun daga kasar mu Nigeria har kasa waje, bawanda zaka tambaya waye Alhaji Umar tycoon baisaniba, koda karami yaro ne,
Alhaji Umar tycoon bafilatanine, da asali jahar Nasarawa , haifafar gari uke, mahaifishi shine sarki gari, subiyu aka Haifa, Tycoon da kanishi Mai mulki gari a yanzu, Mai martaba Yusuf isa, a babba masauratana Mai take Yakanaji. Maihifisu ya jima da rasuwa.
Saboda shahara shi a kasuwanci ne yasa abokainashi suka masa suna TYCOON(tycoon na nufi babba business man).
Matashi biyu, hajiya hajara itace uwargida anakirata da Ammi, sai hajiya Khadija, itace amarya anakirata da Mami.
Duk tari dukiyanshi nan yarashi bakwai kacal Allah ya azurtashi dasu, alhamdullila dai toh, don a zamani yanzu wani ma na nema baisamu ba .
Yara Ammi uku, Aliyu, rukaya anakirata da siyama,sai autarsu Sofia, Mami na da hudu, idriss , fauziyya, Isa, sai hammatul Rahman suna kirata da Rahman,
Duka yarashi a kasa waje sukayi karatu.
Aliyu ne babba cikisu,  shine Dan gaba goshi tycoon, sbd Aliyu akwai hankali da biyaya, da tun yana karami aka fitar dashi wajen saudia, yayi shekara goma cib, sanan tycoon ya yawuce dashi Russian , idriss yagama karatun law, Babba barista ne Mai zama kanshi, sai fauziyya Tana aure da yaro governor katsina state, sai rukkaya, babba ma’aikaciyar gomanati wace kasa ke dama da ita, sai Isa yagama karatun shi, ya dawo gida service, Yana service a illori, sai Sofia da rahma suna mataki secondary, suna jss2 a Turkish international School dake abuja.
Yara gida suna da tarbiya Sosai, ga ilmi addini, basu da raini ko Kuma kaskatar da talaka kamar yanda waesu yara masu kudi keyi.
Mahaifiyar Aliyu wato Ammi, Yar kaduna ce,  family house nata na kaduna, yayita uku, uncle bello, uncle Fahad, uncle auwal, mahaifisu ne kadai a raye, suna kirata da ummi( kaka Aliyu).
Yau ko wani Dan family din tycoon na gida, sbd yau za’atarbi  shalale baba, kowa a family din sai murna sukeyi yau big brother Aliyu zai dawo.
Yanmata family su Sha wanka, masu aiki sai safa da marwa kawai sukeyi a goge nan a gogecan, so ke Wana Dora wancan, kamar za’ayi sukai dari, haka aketa jera abinci yafi kala ashiri a kan dinning,
Da misali karfe biyu jirgisu zai sauko, Aliyu shekarashi shida kenan rabon shi da Nigeria, sai yau zai shigo kasarshi ta gado.
Akala shekarunshi sunkai talati da daya.
NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA
Sai jijiniyar mota kawai kakeji a airport.
Motoci su Kai talati kowani baya mota ansa TYCOON baro baro da number shi.
Yau dakashi yazo airport don tarba shaleleshi, duk sun fito ana jira isorwashi.
Can a jirgi , mutani nata sauka, can na hangi wani hadade guy yafito, kyakyawa na karshe, ko shi yayi kansa iya yanda zaiyi kenan, Aliyu kenan,
Aliyu fari ne ama ba kal ba, dogone ama ba zankaleleba, dai dai, shi ba ramame bane ba Kuma Mai kiba ba, a tsayakiyake da kirjisa me fadi normal, hanci sa Mai kyau da tsari, baiyi tsini can da yawa ba, gashin kasa, Wanda ya yarashi luf dashi, baki ga santsi da laushi kamar na India, gira sa Mai yawa ga kyau, idanu na Dara dara, farare kal kal, habarsa Mai Dan tsayi, bakisa das dan daidai, lips dinsa su ba pink ama kamar light pink, ya bude baki yayi murmushi hakoransa Yar yar, farare kal kal, ga wani dimple nasa Yar ciki Yana lotsawa gwani sha’awa, fatarsa kuwa shar2,  subhanallahi Aliyu yagama haduwa.
Jikishi sanye yake da black jeans, da top fari, kafarna kuwa tasha👟farare, hannu shi kuwa zobe azurfane, sai agogo rolex, sai kamshi ketashi.
A hankali yake sauka a matakalar jirgi, a kasa zuciya shi yace Alhamdullila.
Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by j hajara
1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣
Yace” Alhamdullila yau na shaki iska kasana” yacigaba da sauka a hankali, Yana kan sauka yaji wani muguwar faduwa gaba, nandana yariga karato inalilahi waina ilaihi raju’un.  Haryaji ya daina ji.
Yana waigawa ya hangi su Ammi da dad.can gefe daya security ne, ai nandanna ya hada fuska, don shi arayuwashi yatsani ya farka ya ga security Dina, suna daga ciki dalilai da bayaso zuwa Nigeria, anashi tsari, security kamar takura rayuwane.
Aliyu Yana da sanyi amfa a kwai zuciya inkatabashi, ga tausayi da jikan Dan Adam, ko duma yayi girma kasa waje ama baya shaye shaye, baya Nima mata, mata ma Basu a agender nashi.
Sai kwanaki ne yariyar aboki daddyshi suka hadu a Russian, Tana nacce mishi Wai Tana sonshi.
Sunata SUHAIMA, suhaima yargatace, duk abunda ta keso daddy ta na mata, kyakyawa ce a fuska, ama ba diri ta tafi kamar pencil😂.
Tana gayama daddy yazo yasamu tycoon, yaminshi magana,🤦dayake abokanaine. Yace” ba damuwa zai ma Aliyu magana, shi Kuma Aliyu duk abun daddy shi yasashi yanabi, shiyasa yace ya amince da aure.
Suhaima tana makale mishi har yasoma saki jikida ita, har ayi musu bayko,ansa Rana, aure sai nan da wata uku tukun.
Aliyu nada abokanai gudu hudu Wanda yake ji dasu, Kuma duka atare sukayi karatu,
Haydar namesake nashi, Suleiman, hafiz, fawaz. Aliyu da Hafiz su karata business,fawaz da haydar medicine, Suleiman civil engineer.
 dukasu mazauna abujane.
Da fara’a a fuskarshi ya nufi tycoon, wani daga ciki security yayi sauri ya amshi trolley nashi, Yana mishi barka da zuwa ya amsa aciki sankewa fuska.
Tycoon yace” welcome back son ya rugumeshi, su Ammi da Mami suna gefesu.
I really miss you dad yafada murya a shagwabe” tycoon ya shafa mishi Kai yace” ai kadawo kenan.
Mami tace” son daddy ka kadai ka gani ko?
A’a Mami na ya je gefeta da sauri, ya daura hanushi aka kafada ta yace” yaza’ayi na Manta da Mami na inaa.
Ammi tace” toh zai kuzo munkarasa gida, in muje ko cigaba, duka su ka fashe da dariya.
Tycoon yace jealousy” eh naji.
Aliyu ya shagwabe fuska kamar karami yaro yace” Ammi ko Kimi sannu da zuwa ko?
A’a yihakuri yaro mamishi barka da zuwa ammi tafada.
A’a ni nayi fushi,
Mami tace” Ammi tunda har kikasa boy Dina yayi fushi toh Zaki biya Tara.
Niwa kumun afuwa ammi ta fada”
Tycoon yace” amiki kuzo mukarasa gida.
Duk suka karasa ciki mota, akatashi motoci sai gida.
Suna karasa gida, sun a nufo gate abun mamaki Naga yabude da kanshi, aka sanke yi zangaye kamar roundabout tukun suka isa guri parking, Kai gidana yagama haduwa a rayuwa.
Suna parking bodyguards da sauri suka bude musu mota,  kowa na haraba gida ana jira fitowarsu.
Aliyu na fita da gudu Sofia da rahma suka karaso wurisa da Oyoyo ya Aliyu”
Kai Kai yanmata Ammi ne suka girma haka ya fada” sai murna kawai suke ya Aliyu ya dawo,
Rabonshi da ganisu tun su seven years,
Yakuke yanmata Mami?
Lafiya klau Yaya.
Su siyama, idriss da Isa suka karaso da cewa” welcome bck home big bros
Yace thanks dear
Ma’aikata suka karasa mishi da Kaya izuwa part nashi da aka gyara sab sab.
Tycoon yace” toh don sai kaje ka fresh up ka huta, sai kazo a gaigasa ko,
Toh dad ya fada” suka wuce ciki.
Sofia da rahma zasubishi , Mami ta hanasu, a’a kubar min yaro ya huta, zaku wani je ku dameshi.
Rahma ta tura baki tace” Ammi kiji Mami Wai baza mubi Yaya ba,
Zo zo yanmata na karkudamu,  ai kudiga ganishi har ku gaji dashi,  muje ku amshi milkshake 🥤 naku Ammi ta fada”
Sofia ta amsa da yawwa Ammi”
Siyama tace” ko ji dashi nasa anjima kadan za’ajiku da Ammi din.
Ai sharesu kawai daughter Mami ta fada”
Oho dai inji Ammi” ta jasu suka wuce ciki .
Aliyu yace ” Mami I really miss home,
Ai dole son, yanzu jeka yi Sallah ka huta, sai kazo muyi hira.
Toh mamina”
Yanufi part nashi, idriss na biye dashi, suna hira gwani burgewa har suka karaso ciki, ko’ Ina kal kal, kamar ba”ataba shiga ba, komai yayi cib cib, katuwar plasma ne a falo, sai su cushion Mai ruwan gold da sirri fari a ciki, sai rug a tsakiya da center table.
Paint din part din white ne gabadaya, gefe guda Kuma dining areane, sai wani passage da dai sadaka da guri motsa jiki,
Machines na motsa jiki ne kalla kalla a guri,
Kai faduwar tsaruwa part din Aliyu wani Bata lokaci  dun ya tsaru, yagama tsaruwa, kamar a turai
Idriss yace”  barana na barka ka huta, ni zan wuce office, akwai wani case da akazo dashi zanmika ma wani friend Dina duni zanyi tafiya, Kuma yau Friday.
Ok barrister (haka Aliyu ke Kira idriss da barrister), Ina zakaje? Aliyu ya tambeyeshi.
Ya rage murya ya zo daidai kusa da shi yace” big bro guri princess Dina zanje a kano, biki yayarta za’ayi gobe.
La kace guri inlaw na zakaje” Aliyu ya fada.
Eh Yaya.
Toh ka gasheita, Kuma u should take care of yourself Aliyu yafada”
Okay bro I will, kila ma said Monday na dawo”
Okay safe journey.
Idriss Yana fita yadawo da saurishi yace” Yaya Aliyu da Allah in Ammi ko Mami suka tambeyaka ni, kace musu kawai akirani wani case ne a kano.
La see dis boy oo, so kake nayi karya daga dawuwa na?
a’a big bro mami ne Bata so na da yariya, basan maiyasa ba idriss yafada a murya tausayi”
Aliyu yace Kar kadamu zan shawo maka kansu”
Ohh that’s my lovely bro idriss ya fada” ya rugume Aliyu , ya fice da sauri, Aliyu ya jijiga Kai kawai Yana murmushi.
Ya haura dakishi, ya wuce toilet, ya watsa  ruwa, yayi alwala, bai jimaba saboda yasa baiyi sallah zuhr ba.
Yana fitowa yasamu Dan liti a baki kofa(dan liti amintace Mai aikishi ne, tundaga kan gyara wuri, sako, sometimes har girki Yana mishi sbd ya aminta dashi, Kuma ya na saka shi nishadin, dun Dan liti iri mutanina ne masu son barkwaci dasa mutum dariya, shiyasa Aliyu ke ji dashi).
Dan liti yace” yalabai sannu da zuwa, ya zuguna har kasa.
Aliyu ya amsa da musa maiku lafiya?
Lafiya rankashi dade, ai yallabai nayi matukar kewa ka, dun tun tafiya ka bani sukuni a gida nan , a guri waeina yara su biyu na , walahi yalabai su adabi rayuwana, nasa suna tsoraka, ka ga Sofia har sani wani rawa da waka takeyi , rahma na kwasheni a waya su, wassh wlh yalabai har nayi ciwo baya😅, nasa suna tsoraka, yanzu sa sayaya min.
Wai Dan liti kana ta zuba, Bari inyi sallah tukun Wana Kara na ka babba ne Aliyu ya fada”
Dan liti yace “yihakuri yalabai Kuma fa hajiya tace” Kar na damaika , Ina jera maka abinci in fito, ya dungusar da Kai Alama amishi afuwa.
Aliyu yace tashi katafi saina fitoh” toh yallabai.
Ya nufi wardrobe nashi Kaya ne, a ninike dayawa kamar wani boutique, tun daga kan English wears zuwa su shadodi. Ya cire wani armless t_shirt, baki da jeans trouser shima baki, yasa bakarami kyau yayi ba.
Ya shimfida dadurma yayi Sallah, yana idarwa, ya nufi wani jaka dayazo dashi, ya fitar da wayashi, da laptop. Yana kuna waya, Kira na shigowa, fawaz ne, ya dauka da sallama?
Fawaz yace”rike sallamarka tun 2:00 kana garina shine ko ka nimamu toh ka kyauta,
Haba likita boka tura kamin uzuri mana ya fada”
Fawaz ya katseshi da cewa” mudai gamuna zuwa, musa Kai ba zuwa zakayi ba, ya kashe waya.
Ya kishigede shiru a gefe gado,ya lumshe idon kamar Mai bacci. Ya rasa dalili dayasa tun da ya sauko Nigeria yake ji gabashi na faduwar gaba, ama yabar ma Allah komai,
Ya naji wayarshi na ringing ama ko yace zai tashi yaduba, dun yasa ba daddy shi bane, ko Ammi ko Mami, shiyasa ya share Kira, waya nata ringing har tsawo tw o minutes ama ko yadaga , har aka hakura abar Kira.
Waya na tsinkewa ana sallama a daki, bakowa bace ila Salma cousin sister shi, yariya uncle bello.
Salma yariyace Mai jida kanta. Tunda ta tashi da soyaya Aliyu yatashi.yanzu hk Tana 300l a KASU(kaduna state University)Tana karata computer science, ga kyau , turbakallah,tana bala’ in son Aliyu , ama shi baima San tanayi ba.
Lokaci da aka sanar mata da cewa zaiyi aure , taci kuka har ciwo sanda tayi, tan binciki yariya da zai aura wato suhaima, tagama Bata fita da komai ba, Kuma abun da yayi mata dadi ta taji cewa ai aure dole za’amishi shiyasa ta saki ranta. Mummy ta ta Sha fadamata tabar zance aure Aliyu ama taki, shiyasa tu Ranar da siyama tagaya mata Aliyu zai dawo ta tatara ta dawo Abuja da zama, dun Tasha aniyar cewa zata gayama Aliyu abunda ke ciki ranta, tasa ko ba komai zai so ta,
Shiyasa yau Tasha gayun ta nufo part dinshi, ta duba parlor Bata ganshi ba shiyasa ta haura har daki shi.
Tana ta sallama ba amsaba, Kuma Yana kwance Yana jita , baiso a damaishi.
Ta shigo a hankali, sanye take da riga da wando na Pakistan. Ta nufoshi a hankali, ta zauna ta zuba mishi Ido, akansa zuciya ta tace Kai ya Aliyu ya hadu, ya Allah kasa ya zama mijina, ta cigaba da kalloshi tun daga kan eyelashes har zuwa dan madaici light pink lips kamar ta taba. Shi Kuma kallo ya Soma bashi haushi,
Ya ce” yayya da kallo? Har ta firgita dun yayi kamar bashine yayi maganarba.
Tace” Yaya magana nazo muyi, ya Mike zaune, ya dauki wayashi Yana latsawa, can yatuna anata kirashi bai amsa ba, ya duba missed call yaga Ashe ma suhaima ne, ta mishi har 12missed call, wani dogo tsaki yaja, ya cigaba da Danna wayarshi,
Salma na zaune bai ko kalleta ba, saitaji jiki ta yayi sanyi
Can yadago yace” Ina ji jiki Mai ke tafe dake.
Murya na rawa ta Soma magana” da da -dam dama
Yace ” keki natsu kimin magana basan bata lokaci.
Ta sukunyar da Kai tace” Yaya Ina sonka!
Ya dago Kai da sauri yace”What!! Salma yakira sunata da karfi ya Mike tsaye.
Ta cigaba da mgn tana kuka tace” walahi Yaya Ina sonka, banaji son kowa a zuciya inba Kai ba, da Allah yaya ka taimaka ka soni,
Mamaki ma ya Hana Aliyu magana, Wai yau shi Salma tazo tace ta na so.wai Wana wani iri duniya ne,
Salma ta sauko ta rike kafarshi tace” da Allah yaya please please, ka tausayi min, ya wani iri ball da ita, yada ka mata tsawa.
Yace” Wai ni saran wasaki ne, da Rashi kunya da fitsara shine har Zaki iya bin namiji ki ce kinasonshi, ya rike Kai Wai Mai yasa yanmata yanzu Basu da kamu Kai me, ya Dade Yana ji haushi suhaima da saura yanmata da sukecewa suna sonshi,  Yana gani wanan kamar subar da aji ne da Kuma karaci tarbiya.
Salma tace” Yaya walahi Yaya inbaka soni walahi zan iya mutuwa, ya wani Kai mata Mari a baki
Yace” bara kinji nagayamiki bana sonki, Wai kwata kwata guda nawa kike Dan har kisan wani so😳, dube kifa da ko Isa ban za ce ya sonki ba, shine Zaki kwaso wani stupid jiki ki, kixo kice kina sona Koh
Toh bara nagayamiki this should be the first and last da zanji iri magana abaki, rubbish , tashi kibar min daki, kafi nabalaki a guri.
Da gudu ta fice  da ta matukar tsorata da Yaya nata, dun bai taba ko canza ma ta fuska, shine yau kawai dun tace tana sonshi, har da Marita.
Wayyo ni Salma na shiga uku, Tana fita taji karo da Ammi a baki kofa, ta fado jikita takara fashe da sabo kuka.
Ammi Ashe taji komai, dun tu dazu take Shashi tazo taduba ko Aliyu yaci abinci dun tasashi da ranshi so ci abinci (uwa kenan♥️).
Tace” keki room Dina Ina zuwa, Salma ta fice da sauri da Kar ya Aliyu yaxo ya samaita.
Ammi na shiga daki tasamaishi rike da Kai, sai kwafa yake tayi, tanufi fridge ta dauka bottle water Mai sanyi ta Mika mishi, batayi magana ba shima haka, ya amsa,ya kafa Kai ya shanye duka yayi wurgi da gora.
Ammi ta zauna a gefeshi, tana tapping nashi a hankali.
Tace” Allah ya huci zuciya gadagaa, gadagaa gutsa yaki, takawa ka lafiya da gaban goshi tycoon da mamishi.  Sai yaji hankali shi ya kwanta da Wana kirari.
Ya kife Kai a kafada Ammi .tace” Aliyu da Allah ka rage zuciya na kaji ko?
Yace” Ammi kidubi yariyana Dan tsaba Rashi kunya…… Ammi ta tareshi da ssshh bansaji komai, naji abunda ya hadaku, ama Aliyu bai kamata ka mareta ba, kaga ita mace ne.
Comment & share😍😍🙏
Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by J hajara.
1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Ammi tace”Amma Aliyu bai kamata ka mareta ba kaga ita mace ne,dakata tazo tace ta na sonka ai batayi laifi ko Rashi kunya ba,kamata tarihi Ma’aiki (S.A.W) lokaci da Nana khadijah (A.S) tazo tasamaishi tace tana sonshi ai hannu bibibbiyu ya karbeta”
Yace”Ammi a gsky bana son Salmah”
Ammi tace”ok naji, ai sai ka mata magana na fahimta Wanda baizai daga mata hankali ba,har ya Kai da Mari, kasan zuciya ba Kashi ko?
Yace” Ammi are you supporting her”
Tayi murmushi tace” Aliyu har yanzu bakasan so bane shiyasa kake Wana maganar”
Yace” toh Ammi naji u r just supporting ur daughter shiyasa”
Ta jijiga Kai tace”a’a Aliyu bahakabane”
Yace” naji Ammi yanzu ya kikeso ayi”
Tace” inaso kasame ta ka Bata hakuri”
Yadaga kanshi daga kafadata yace”Ammi hakuri fa!
Tace” eh hakuri mana, kace mata ka dauke ta ne a matsayi su siyama tayi hakuri baza kaiya aureta ba, ka lalasheta nasan cewa batasa da maganar aure ka ba,ka fahimtar da ita har tagane ama ba duka ko zagi bane zakayi, abun yadace kayi kenan”
Yayi shiru Yana tunani sai a lokaci da Ammi tace aureshi yarage wata uku sanan ya tuna da wani zance aure yayi ajiya zuciya.
Ammi tace”Aliyu are you with me? Ya daga Kai Alama eh.
Tace” yawa Dan mamishi tashi muje kaci abinci ga la’asar ya gabato tundama abunda yakawoni kenan”
Suna sauka sukaji sallamar su fawaz dukasu hudu sukazo fawaz, haydar, Suleiman da Hafiz suka gaida Ammi tace” Hafiz tundama Kuna gari shine ko ku laikamu sai yau duku ga aboki ku yazo ko?
Dukasu kowa sai soshe soshe Rashi gaskiya sukayi.
Ammi tace” ku kyauta”
Suleiman yace”Ammi aiki ne ke taremu shiyasa da Allah kiyi hakuri”
Haydar yace” wlh hakane Ammi ba time”
Tace” ai gashi kuzo duba abokiku ko?Wai ma na tambeyeku tun yaushe ku ka dawo?
Aliyu na gefe Yana musu dariya, suna ta mishi signal yacecesu, ya daga musu hannu Alama Babu ruwashi,
Aliyu yace”Ammi ai yau Friday satisu daya kenan da da dawowa,
Tayi murmushi tace” ohh Allah ya taimakeku,toh ku taso kuci abinci saura naji wani yace min ya koshi”
Ai da sauri suka hau kujera dining.
Fawaz yace” Ammi tundama yunwa mukeji”
Ammi tace”gwaraye kawai”
Dukasu sukayi tsit, dun suna amsa wani jamb question ne zai biyo baya 😅
Tayi serving nasu fried rice da farfesu kaza, sai fruit juice da salad, tace kawo ya cinye yabani empty plates”
Ta fice daga part din, Tana fita suka sauke ajiya zuciya .
Fawaz yace” Kai buddy yau kayi amfani ka cecemu daga jamb question din Ammi😅duka suka fashe da dariya.
Hafiz yace” gobe fa Alhaji na zai tura manya gidasu my queen”
Haydar yace” shege Kaya kace kashirya kenan”
Yace” eh mana”
Suna hira sunaci abinci, Aliyu kam ba wani ci yake ba, kwata kwata hankalishi ma bashi aguri, sai juya cokali yake tayi, Suleiman ne ya lura dashi, ya dafashi yace” buddy are you okay? Mai ke damuka? Duka sukayi shiru hankalisu ya dawo kansu. Bai amsa ba ya Mike daga dining ya wuce parlour, ya kwanta shiru, Suma kowa jiki a sanyaye suka bi bayashi,  fawaz ne ya katse shiru dacewa” Wai buddy Mai ke damuka ne? Aliyu yamike ya zauna, ya Soma Basu lbr abunda Salma tamishi, sai jimami kawai suke,  haydar  ma abun yafi damushi, don tunda yaga Salma yake ji Sonta a ranshi, Ashe ita ga inda ta dosa, yace” Aliyu bai kamata ka hk ba, abunda Ammi ta fada tayi gaskiya ka sameta kuyi magana ta fahimta, zataji dadi a ranta”  duk suka goyi baya magana da haydar ya fada,  yaja wani dogo tsaki, sbd ya tuna da batu suhaima.
Hafiz yace” kazo kenan zaka samu agaba, Kai bazaka tsaya ayi magana  ta fahimta ba, sai dai kata hada fuska,ni wlh abinci na zanje nakarasa ci” ya Mike yaje ya cigaba da ci abinci, ba Wanda ya tanka mishi don su sanshi baya wasa da cikishi.
Aliyu yace” kunsa Nanda 3months ne fa aurena” ai nandana Hafiz dake ci abinci ya shake, dukasu suka hada baki guri cewa” what!!! Dagaske kakeyi? Ya daga musu Kai Alama eh”
Fawaz yace” kwal ubancan, tabdi jam, Wai yaushe aka sa Rana ne baka gayamana ba”
Aliyu yace” Nima basani ba, Ranar Thursday ne dad yaki rani yake gayamin, Nima na Manta sai yau da Ammi take mgn na tuna” ai sai duka suka fashe da dariya shakiyaci, Aliyu ya tsaya yana kallosu yarasa dalili dayasa suke mishi dariya.
Suleiman yace”ango ango kasha kamshi, ango na suhaima”
Aliyu yace” da Allah u guys should stop”
Fawaz yace” toh ango ya magana Salma?
Yace” ni gaskiya bani da niyyar yi mata biyu daya ya isa, Kuma Salma na dauke ta a matsayi kanwa na ne, baza iyaba”
Haydar yace” hmm toh nikamin hanya wlh ni Ina sonta”
Suleiman yace” wayo ku kaisan kumana kenan ko, toh baku isaba”
Haydar ya kalleshi yace” buddy stop Allah am serious wlh ni inasonta , zan aureta”
Aliyu yace” karkadamu zan mata magana”
Aka Kira sallah la’asar duk suka Mike zuwa masalaci dake ciki gida gida.
A daki Kuma Salma be keta rusa kuka kamar nufashita  zai dauke, Ammi da siyama suyi lallashi har su gaji, takikiyi shiru.
Ammi tace” Wai Salma yaki keso ayi ne, ki cika gida da kuka, har ki ja makaki ciwo a banza, kema kisan Aliyu inyace bayayi to ya zaunu, sbd hk kiyi hakuri kijiko, Allah zai zaba maki Wanda yafi  alkhari, Kuma kisan Koda a fada ma daddy su ra’ayi shi yakebin, kiga bahali a jegunda kenan, kiyi shiru kibar wanan kuka”. Ta share hawayeta, sai ajiya zuciya take tayi da shesheka kuka.
Ammi tace” siyama kaita side naku, ta huta, siyama ta mikar da ita suka fice daga daki. Ammi ta jijiga Kai Tana mamaki yara yanzu.
Su Aliyu na idarwa suka fice a gida gabadaya don ko daddy shi baikara lekashi ba.
*************************
Suhaima sai haushi takeji, Aliyu ya dawo kasa na, shine bai naimaita ba, abun takaici ma ta kirashi yaki daga waya, wanna wani iri Abu ne, sai wurgi da Kaya dakita ta keyi, sbd haushi da matsifa.
Ma’aikata gida sai hakuri suke Bata ama kota kullasu, daya daga cikisu taje takira mommy  ta tagayamata hali da suhaima ke ciki,  da sauri mummy ta nufi dakita ta sameta rike da kwalba turare ta farfasa mirror hannuta nata jini,
Hajiya binta(suna mummy ta kenan) tace” baby na maiyasameki haka? Wayata ba min ke?     Mummy ta Kira suna ta da Karfi” hajiya binta ta matso kusa da ita tayi sauri ta karbe kwalba fasashe dake hannuta tace”  Wai suhaima so like ki illata kanki a banza, nace kigayamin waya tabaki ne a garinan? Bata amsaba  tasake durgusa a guri da ta fasa kwalba da sauri hajiya binta ta riketa. Tace” zo muje dakina kigayamin kiga Ina barki ana zakiji  makaki ciwo” tana magana Tana gyara mata kitso attachment nata da ya barbazo yayi kamar wata aljana 😅.ta jata suka fita daga daki, takira daya daga ciki maid nata, da tazo ta share mess din da suhaima tayi, ai da sauri ta karaso, dun suna bala’in tsoro hajiya binta Bata da kirki ko kadan daga ita har suhaima din, sam Basu San mutunci dan Adam ba.
Suna Isa daki ta kaita toilets,ta watsa ruwa ta da towel, Kaya da ta cire aguri tabarsu , don a rayuwa ta batasan wani aiki ba, hata pants da bra Yan aikisu ne ke wanke mata.
Tana fitowa hajiya binta ta tareta tace” zo ingyara maki guri da kikaji ciwo da first aid kafi daddy ki ya dawo, yaga wanan ciwo”
Wace ce suhaima?
 Suhaima yariya ce sagartaciya  na buga  a jarida, Wanda tun tasowata  iyayeta suka Bata ta da kudi, sbd ita kadai Allah ya azurtasu da ita. Mahaifita Ambassador ne na Nigeria dake kasar Russian🇷🇺 .
 Suna mahaifita Alhaji rabi’u Hussain Dan asali jahar kano, matashi daya hajiya binta, family nasu daya da Ambs rabi’ u Hussain aure zumuci ne aka musu, tun da sukayi aure har tsawo shekara biyu Basu samu haihuwa ba, sai a shekara na uku ne, Allah yabasu suhaima , Kuma tsanadiyar haihuwata ne, mahaifar hajiya binta ya lalace, aka cire mata gabadaya, shiyasa ita da Ambassador suka daura mata son duniya, duk abunda takeso Bata taba rasawaba, rayuwa ta rabi  a kasa waje tayi shi, tarbiya da al’adu mu na hausa suhaima Bata sanshiba, duk shiga da taka dama tanayi tafita, kaweyenta kalla kalla, Yan club goggu mata masu ji da kansu,  Ama Tana da best friend maisuna nafisat ama suna kirata da feenat, itama yariya babba Dan siyasa ne a kasa namu.
Suhaima tun lokaci da ta hadu da Aliyu a Russian, yakawo ma daddy ta ziyara, taji dun duniya ba Wanda takeso kamar shi, shiyasa ta nace ma daddy ta har ya ma tycoon magana, har aka kai ga muzali aure.
Suhaima manager ne a daya daga ciki company tycoon, ita tasa daddy ta ya naima mata aiki a company sbd ta saba da Aliyu da Kuma ahalishi.
Cigaba lbr
Hajiya binta tace”yawwa baby zona kigayamin maiye samaiki har da taba lafiya jiki?
Suhaima tace” Mommy ba Aliyu bane, yadawo ko ya naimeni, ko ma yagayamin yau zaidawo”
Hajiya binta tace” toh ke baby waya gayaminki yadawo?
Tace” daddy shi mana, yau yazo office da safe ya sanar cewa Aliyu na zuwa yau, Kuma na Kira number shi na Nan har 12 missed calls bai dauka ba”
Hajiya binta tace” ho babyna Kisha kuruminki, ai yakusan zuwa hannumu, mujuyashi son ranmu, bandai aure saura wata uku ba , toh ki kwatar da hankali kawai babyna”
Suhaima tace” Allah ko mummy na?
Tace” eh mana Kar damu”
Suhaima tayi murmushi tace ” yawwa dats my best mum” ta rugumeta ,ta gyara kwanciya a gado mommy nata, taja bargo ta rufe jiki .
Hajiya binta tace” babyna badai bacci bako? Yanzu fa 4:00 ne dots, Kuma nasa bakiyi sallah azahar ba balle la’asar”
Tace” uhm uhm ni mummy ki kyalleni inatashi zanyi, ni na gaji”
Hajiya binta tace” toh baby na, na kyaleki sleep well” ta gyara mata bargo(waiyazubillahi🤦).
Su Aliyu suta zagaya gari har misali 6:30pm ,sanan suka tsaya a central mosque, sukayi sallah magarib, suka jira Isha , sanan sukama hanya gida, dun daddy shi nata kira, ya dawo gida hakama Wai yafita bada security ba, ya sallemi su haydar yace musu sai suyi waya.
Yana shiga , ya wuce parking lots direct, ya ije mota a hankali dun bayasa su hada Ido da daddyshi, dun yasan fada zai Sha, Kuma yasa tabas daddy shi ya dawo gida yau da wuri,
A hankali ya kashe mota ya cire key, ya sauka tuna nishi yabi kofa baya ya shiga side nashi, Kar daddy shi yaganshi, bai sani ba tun shigowar shi da motar , tycoon ke kallonshi , Yana tsaye agefe garden, dayake guri da ya tsaya ba haske Sosai sai yayi kamar wani security ne a gun, yafi minti goma a guri Yana jira yaga shigowar shi.
Aliyu na sauka zai bi ta ida  zai sadashi da kofar baya, har ya Soma tafiya yaji anakirashi ,Aliyu?  Ya tsaya cak  tabbas murya daddy shi ne
Yace” shikena yagani”  ya juya a  hankali kamar Mara gaskiya ya sunkuyar da Kai yace” Ina wuni dad?
Tycoon bai amsa ba yace” zonan” ya nufoshi a hankali kamar wandakwai ya fashe minshi a ciki.
Tycoon yace”  Aliyu saunawa zagayama inkazo Nigeria, kariga fita da masu tsoro lafiya ka iye?  Yau ma daga zuwaka shine ka fita ko ka sanar ma Ammi ko Mami ka zaka fita ko ?
Comment and share 😍😍
Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by J Hajara
1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣
Dad kayi hakuri ban zan sakeba mu Dan zagaya garine da su Suleiman” Aliyu ya fada.
Tycoon yace” ok naji, wuce muje kaci abinci Kai kadai ake jira”
Yace” no dad ni ba yanzu zan ci ba, Allah dad zafi ya dameni baza iya zama na Kai three minutes banyi wanka ba, daddy zufa”. (Aliyu Sam bayason  zafi,bale ma weather naija)
Tycoon yace” haba mana Aliyu kowa yayi missing big bro, yau suna murna zasuyi dinner dashi shine kace bazakayibs, yi hakuri muje ko two minutes kayi”
Yace” Allah daddy inakara one minute banyi wanka ba ihu zan saka don Kai kayi nake ji”😅
” Eh daurai son zakaiya nasan son dinna jarumi ne” yaja hannushi suka taho gwani sha’awa, duk lungu da suka bi sai security su Sara musu, tycoon kadai ke amsawa ama Aliyu kam hankalishi ma baya wajan.
Suna karaso wa ciki babba falo gida wow😮 ya hadu, ba’ amagana, hotuna yagidane dukasu gabadaya suyi family picture a bango falo, suyi kyau kamar larabawa, family din tycoon MashaAllah ba dai kyauba,  kowa ya hallarci babba dining area din, tycoon kawai da Aliyu ake jira,  sukayi sallama aka amsa, ya gaidasu su Ammi.
Mami tace” wato son kaki zuwa mun gaisa ko?
Yace” a’a mamina yi hakuri mu dan fita ne dasu Suleiman”
Sofia da rahma suka tambayeshi tsaraba, yace” oops  sorry yanmata Ammi imu gama dinner kuzo ku karba kujiko?
Sofia ta amsa da ohk Yaya”
Suka fara ci abinci, tuwo🍛da Miya taushe yasha nama gaja gaja, har nama yaso yafi Miya yawa.
Aliyu ba wani ci arziki yakeyi ba, yanaci Yana yamutsa fuska Alama zufa na damushi, sai zufa yaketayi duk AC daya cika lungu da sako parlor, amashi zufa yakeyi.
Siyama dake gefeshi ta leka plates taga bai wani ci ba, ta mishi rada da cewa” Allah imbaka ci abinci ba zangaya ma Mami”
Yace” yi hakuri sis, zanci ama wlh am not comfortable zafi ke damuna can’t you see?
Tace” ama wlh big bro Kai ajebone, toh bara nasa akara ma karfi AC”
Yace”godiya  nakeYar kanwa”
Tace u r welcome bro”
dakanta ta Mike don ta Kara karfi AC.
Tycoon yace” siyama Ina Zaki baya ba’agama ci abinci ba?
“Daddy ba ko’ Ina Yaya zankara ma karfi AC sbd Yana ji zafi sosai ” ta amsa.
Ammi tace” ni dai basan iri jiki Aliyu ba, Wai mutum duk sanyi na sai yasa akara”
Mami tace” karkidamaimu haka Allah ya halicemu”
” Toh nayi shiru” Ammi ta fada Tana Kama baki.
Siyama tana karawa ta dawo ta zauna, Aliyu ko minti uku baiyi da zama ba yamike, Isa yatambayeshi yace” Yaya inazakaje Kuma?
Yace” na koshi young corper”
Isa yace” Yaya bakaci komai bafa?
Yace” kaikayi nakeji bro bazan iya zama ba”
” Ok Yaya goodnight” cewa siyama da Isa.
Yace” Allah yatashemu, Ammi mamina sai da safe?
Dukasu suka amsa mishi da sweet t boy”
Tycoon yace” kafi ka kwanta inaso gani ka”
Ya amsa da ” toh dad”
Da sauri ya wuce part nashi, direct toilet ya wuce ko koya jikishi bai cire ba, ya kunna ma kanshi  shower, sanda ya Soma ji iska sanyi tukun yacire Kaya ya Soma wanka, Yana Gama wanka ya dora alwala ya fito, ya ciro white boxer da singlet, sai jalabiya Mai guntu hannu,shima fari, Yana sawa yaje gaba, yashafa wani tsadade body lotion, ya fesa turaruka masu sanyi kamshi, Yana gama ya shimfida dadurma yagabata da sallah nafilah(Aliyu akwai son ibada) Yana idarwa yaji sallamarsu su Sofia, ya amsa”
Sofia tace” Yaya Wai zakayi aure da gaske?
Eh ya amsa”
 Rahma tace” Yaya mu bamu taba gani amarya kaba”
Sofia tace” eh hakane yaya, Kuma Kai baka taba kaimu mu ganta ba”
Rahma tace” no no Yaya show us her picture first, munga ko ta Kai yayamu kyau”
Aliyu yace ” toh iyaye surutu, kuzo ku amshi tsaraba ku ne ko kuzo ne ku cikani da surutu?
Dukasu suka hada baki guri cewa” a’a  Yaya yihakuri, but please show us our bride picture please Yaya”
Aliyu ya koma zance zuci yace” yara na su nema kureni aya ma Ina da hoto suhaima kuwa?
Rahma ta katse mishi zance zuci da yakeyi da cewa” Yaya please” harda buga kafa.
Yayi murmushi yace” yanmata Ammi , no kudawo gobe ,zanuna muku , kuga yanzu daddy na Kira na Kuma bansa na Bata lokaci, Yana magana Yana shafa musu Kai, toh ga tsarabaku”  ya Mika musu wani jaka Mai kyau cike da kaya , suka mishi godiya suka fice.
Suna fita yayi ajiya zuciya, yace” Allah na godema” can ya Mike ya nufi side din Tycoon, da sallama ya shiga, ya amsa, zaune yake rike da jarida daily trust a hannushi ya Mike kafafuwashi,  Aliyu da sauri ya Isa gareshi yariga ma kafa tausa.
Tycoon ya kalleshi ya murmusa yace” thanks son” yaciga da cewa” tundama nakira Kane na tuna ma maganar aure ka, Kuma na shaida ma cewa next week zaka fara zuwa office, ka ga kenan sai ni na huta da zirgazirga, Kai ka cigaba, I surely know my boy can do it, kaga kenan zaka zama junior tycoon, ya murmusa, yacigaba , toh nabaka hutu one week kenan, Hafiz tun last week ya fara zuwa office zai nunama komai so don’t worry”
Aliyu bai amsa kanshi a kasa Yana ta ma kafa daddy tausa.
Tycoon yace” son baka jinane?
Yace” dad naji ama please maganar aure da Allah a dafashi please ? Ya marairace fuska,
Tycoon yace” ama Aliyu maiyasa kakeso a daga?
Yace” haka kawai dad”
Tycoon yace” toh kayi hakuri son gaskiya bazaniya sa a daga biki ka ba, just have patients komai zaiyi dadai inshallah kajiko?
Yace” toh dad nagode sai da safe”
Tycoon ya amsa da Allah yabamu alkhari sa”
Ya Mike jiki a sanyaye zuwa dakishi, jalabiya kawai yacire ya kwanta.
   KADUNA
Su Essha sai wurare 3:30pm su ka Isa kaduna duk sugaji, anguwar dosa straight baba driver ya wuce dasu, a kofar gate dinsu big mom, baba driver yayi horn gate man yabude musu, ciki gida makil da Yan biki , tun daga yanuwa miji  big mom da nata, da abokaina arziki.
Baba driver ya Parker motar duk suka fitoh, hanan ta hangi Essha da gudu taje ta rugumeta, tace” Oyoyo sis Essha”
Essha tace” ohh baby hanan yaushe kukazo?
Hanan tace” shekaran jiya, Ina khairat da su Yaya amir? Ta tambaya
Essha tace” suna gida suce a gaisheku ” taja mata hanci.
Tace” toh maiyasa basu zo ba?
Essha tace” baby hanan makarata ne ya sayardasu”
Su daddy karami suka wuce masalaci dake kofar gida domin suyi sallah la’asar.
Essha Kuma na kwashe Kaya dake boat, hanan na Taya ta. Taji a rufe mata Ido ta rasa wayane .
Tace” baby hanan da Allah waye rufemin idon ” batasaniba hanan tun lokaci da tafitar da trolley nasu ita da hajiya suka wuce ciki.
Ta Kara tambaya ta marairace murya tace” da Allah waye? Akaki magana, tayi tayi ta bude ta gagara a rike Ido tam, sai can taji a koyi murya ta da Allah waye?
Tayi murmushi tace ” Aina’u  bude min idona, ai tundama  nasa kece”  ta cire hannuta da sauri tana dariya tace” Oyoyo sis”
Essha tace” bazan amsa ba, baya ki tsoratar Dani”
Aina’u tace” yi hakuri zomuje ciki, kiga hajiya ta Dade da wucewa Wai bazata tsaya kallo shirmemu ba, Wai kafafuwata suyi tsami” dukasu suka fashe da dariya.
Gefe guda ta hangi su Yaya Usman, Yaya Abba , Yaya salis , sai hira suke akar Kashi bishiya mangoro dake ciki gida.
Aina’u tace” ni bazan Kai Kaya ciki, kije ku gaisa ko?
Tace” toh sis ngd” ta nufisu, dayake Bata guri suke kallo ba shiyasa Basu gantaba, ta cigaba ta nufisu ciki tafiya ta Mai dauke hankali Mai kallo, tana zuwa daf dasu
Tace” hi yan samari”  duka sukayi sauri juyawa don suga mallaki murya, kawai sai sukaga Essha, kawai dukasu suka sake mata murmushi, Usman ne kawai ya hada fuska.
Salis yace” sis sauka yaushe mutani lafiya ne(ya koyi hausa lafia😆)
Ta harareshi sanan ta amsa da” yanzu na tare dasu hajiya da daddy karami muke”
“Eya sannu da zuwa Yar kauye ” cewar Yaya Abba
Tace” ni ka daina cemin Yar kauye”
Sameer yace” ke Yar
kauye ne mana, da wani hausar ku tsamama Wai ku Kuna hausa😆( mutani lafia kumun afuwa😅🙏)
Tace” Allah Sameer ka kiyayeni” ta juya ga kallota zuwa bangare Usman ya wani hada fuska kamar baitaba murmushi ba, hkl shi na waya.
Tace “babba yaya Ina gaisuwa”  bai amsa ba ya Mike kamar zai wuce ta, ya dawo ya tsaya daidai inda take ya kama mata kunne.
Tace” wassh ni Mai na maka?
Yace” laifi ki da yawa, na daya bakison san da zumuta, Kuma sau nawa zagaya maki, ki daina sa iri Wana gyale ki ki ji, Kuma daddy Yana kalloki”
Tace” ni ka kyalleni” Tana tura baki.
Salis ya Mike ya kwace ta daga hannushi,
Yace” bros kyaleta yi hakuri, ka ga tayi tafiya Mai nisa ko, ta gaji”
Usman yace” ai Allah yasoki”
Tace” eh din” ta mishi gwalo , da gudu ta wuce ciki.  Tana shiga ta Sami big mom zaune a parlor tana waya, da gudu ta fado jikita,
Big mom tace” eh zankiraki anjima, ta kalli Essha tace” Wai Wai daughter so kike ki karya ni, wow daughter na ta Kara kyau da girma, ki gaki kuwa”
Tace” Kai big mom” ta rufe fuska. Yan parlor sai dariya suke musu.
Tace” big mom Ina hunaisat?
Big mom ta amsa da tana dakita”
” Ok mom” da gudu ta wuce daki hunaisat, big mom tace” daughter kiyi a hankali fa?
Ta amsa da ” toh big mom”
Ta shiga,ta Tara da humai zaune a tsakiya gado, ta Sha lalle a kafa da hannu sai walkiya kawai take na amare, sai waensu yanmata su uku, agefe ta, suna kallo Abu a waya, a zuciya ta tace Killa ma hotuna biki suke kallo.
Tayi sallama suka amsa, hunaisat ta daga Kai taga Mai sallama taga Essha ne, tayi Kara, ai da gudu ta rugumeta, sai murna takeyi.
Essha tace” Kai amarya na Zaki karya ni”
Hunaisat tayi murmushi tace” sis kigaki kuwa, ki hadu fa”
Tace” ni wa , ai duk haduwa da nayi ai ban Kai ki ba amarya”
Hunaisat tace” sis Allah wlh dagaske nake”
Tace” toh nagode amarsu”
Hunaisat ta juya ga friends dinta tace” Maryam, asma’ u, dija Meet my special cute sis, itace Essha Dana ke baku labarita”
Maryam tace” ai Naga Alama , sannu da zuwa”
Essha Tamika musu hannu sukayi musabaha,da fara’a  a fuskata tace” nagode”
Dija tace” Kai walahi ki hadu da inada Yaya namiji Dana mishi hanya”
Essha tayi murmushi tace” Kai bar fasamin Kai”
Asmau race” Allah da gaske ne”
Tace” nagode tom sosai, sis bara nayi sallah ko”
Ok ” ta wuce toilet tayi alwala, ta fito ta gabatar da sallah la’asar, Tana idarwa suka Soma hira.
Tace ” sis Naga hotuna bridal shower din?
Hunaisat tace” a’a ni bazan nuna miki ba”
Tace” haba mana amarya Anas”
Hunaisat tace” har kisan naji sanyi gashi ki ganni”
Tana kallo hotuna tace” gaskiya sis ku fito, I really miss” taga hotuna har Dana KAMU tace” sis Wai yaushe akayi wanan?
Hunaisat tace” yau man”
Tace” eya sis maiyasa bakusa 4:00pm a tashi seven ba?
Hunaisat tace” a’a ba ruwana, Yaya Usman ne ya Sara komai”
Essha ta hada fuska kamar zatayi kuka tace” shi Kuma Yaya Usman Nashi kenan ra’ayi tsiya kamar shine ango, ace nazo biki sis, events ko daya bani aciki”
Maryam tace” Essha karkidamu ai ba’ariga a daura  ba, Kuma ai gobe akwai walima sai reception bayan daura aure”
Tace” Kai har naji sanyi”
Yan daki sai tsokanar hunaisat suketayi Wai tacika surutu da rawar kai kamar ba amarya ba”
Essha tace ” Kar kudamu gobe ne Ido zai Raina fata ” duk suka fashe da dariya
Hunaisat tace ” eh din ku kyalleni”
Hafsat ta shigo tace” sis Essha big mom nakiraki, Wai kizo kici abinci”
Tace” toh hafsy muje”
Ta Mike tabi bayata, ta samu big mom tana shirya abinci akan dining, Yan taro sai safa da marwa sukeyi.
Essha ta lagwabar da Kai tace” big mom ni gsky baza iya ci abinci anan ba zan Kai daki”
Big mom tace”  toh badamuwa , zo ki Kai ma hajiya da daddy ku nasu”
Ta kwashe nasu hajiya takaimusu, taxo ta dauki nata sai daki, tana zuwa ta jima wayata na ta ringing ta dauja, taga bestie ne.
Tace” hello”
” Hi har ku sauka”cewar bestie”
Essha tace” eh dear tun misali 3:30″
Bestie tace” tom ya hanya?
Tace ” hanya lafiya lau, ya lecture din?
Bestie tace” ai kibari kawai Essha lecturer dina yaso yasamana zafi, daga zuwa aji fa, Wai tests, ai student nata complain shi ne ya hakura Wai gobe Saturday mun dawo 4:00pm”
Essha tace” toh bestie iya complain Allah yabaki sa’a”
Bestie tace” ameen bestie mie, ni gsky nayi missing naki, ki dawo Sunday kijiko”
Essha tace” Nima hk, Kar kidamu, Sunday zamu dawo inshallah, ga amarya ku gaisa” ta Mika ma hunaisat waya suka gaisa sanan ta mata bye ta kashe waya.  Ta Kira mum da dad dinta suka gaisa, sanan ta Kira Khalid su Dade suna waya kamar baza su rabu ba, shima ta ba hunaisat waya suka gaisa, suna Gama gaisawa ta kashe, ta Soma ci abinci, sanda aka fara Kira sallah mahgrib sanan ta handa plates takai kitchen.
Su maryam suka musu sallama zasu wuce sai gobe da safe zasu dawo , har baki gate suka rakasu, sanan suka juyo ciki , sai kiraye kiraye sallah kakeji, suna dawo suka Dora alwala , sukayi sallah magarib, suna idarwa suka fara tilawa alqur’ani maigirma har akayi Isha, suna idar da sallah Isha.
Essha ta shiga ta watsa ruwa, ta fito daure da da towel Dakar ya wuce cinyar ta.
Hunaisat tace” sis kigaki kuwa, kigama haduwa tuburkallah dama ni ne”
Tace” Kai hunaisat basan shairri “
Hunaisat tace” Allah ba sharri bane , dubeki fa kamar Nicky Minaj ” tayi dariya
Essha taja pillow dake baki gado ta harbe ta dashi tace” ke yariyana Allah yashiryamin ke”
Hunaisat ta cabke pillow tana dariya tace” ameen”
Tana rufe baki sukaji sallamar , big mom, anty zainab da Aina’u, dukasu rike da Kaya a hannusu, big mom kula ne a hannuta, guda biyu , ita Kuma anty zainab robar ne kamar na talla, cike yake dam da turare  wuta, daya Kuma da lalle na Hadi na wanka amare, Aina’u Kuma gora ne maidaidaici a hannuta sai leda fari baiya gani abunda keci.
Big mom ta a aje kulla a gaban hunaisat, ta amshi  roba da ke hannu anty zainab shima ta aje a gabanta , har da Kaya hannu Aina’u duk ta hada ta aje.
Big mom tace” hunaisat? Ta amsa da na’am momy”
Big mom tace” kiga Wana kula ta bude kaza amare ne ya shs Hadi sai kamshi kawai ke tashi, tace” toh inason ki cinye kiban kula , zan aiko a daukamin, da wanan ma ta nuna gora tace ” tsumi ne duk ki shanye su, kinaji na ko, na roba na Kuma ta nuna na lalle Hadi tace” yanzu nakeso kishiga ki watsa a jiki kizo anty ki zata turareki”
Hunaisat tace” toh momy” ta fada Tana tura baki, ta dauka ta wuce ciki toilet dashi.
Big mom tace” Essha ki tabatar da ta shanye komai kinjiko, intaki kizo kigayamin, kijiko daughter?
Essha tace” toh mum zan yi yada kikace”
Big mom ta fice daga daki taja Aina’u saboda zata tayata hada kayayaki, Aina’u ba haka taso ba, taso ayi agabatane😆.
Essha sai a sanane taga anty zainab tace” la aunty zainab tundama kene a tsaye”
Anty zainab tace” eh Essha nine , Ina waya zai barki ki gani”
Tace” la aunty yihakuri, Ina wuni?
Lafiya klau ta amsa”
Tace” mummy na Wai na gaisheki”
Anty zainab tace” Allah sarki Ina amsawa, gobe zamu wuce zamu bi tagari naku ai “
Essha tace” eya anty zaku wuce gobe?
Anty zainab tace” inshallah”
Hunaisat ta fito daga toilet rike da robar , sai tura baki kawai takeyi, anty zainab ta ja ta tace” zona yata yihakuri ke fa amaryace, zo na turareki , kawuki na jirana”
Essha tace” anty Nima nazo?
Ta amsa da toh Essha zo ba matsala”
Duka ta hadasu ta turaresu ciki da bai, agama sai tashi kamshi kawai suke Mai dauka hankaki .
Anty zainab tace” ni na wuce saura Kar kici, Essha ki kula da itafa?
Tace” zanyi anty”
Anty zainab na fita hunaisat ta Soma guna guni tace” ni wlh na gaji da ci abubuwa na, waensu fa kamar zanyi amai”
Essha tayi dariya tace” yariya gwamnati ki a ke taimaka “
Hunaisat tace” ni banso”
Essha tace” wlh Allah inbaki ciba zana je nagayama big mom cewa kice baza kici ba” ta Mike tsaye.
Hunaisat ta tare ta tace ” haba mana lovely sis zauna Allah zan ci ama zakitayani ko?
Essha tace”  ayah? Na amare ne fa?
Hunaisat tace” Allah sis bazai Miki komai ba”
Tace” dagaske kikeyi?
Hunaisat tace” Allah sis believe me”
Tace” tom nayarda” su biyu suka cinye kaza , Essha ma tafi ta ci har da tsumi  suka Sha tare, ballema hunaisat batasha sosai  ba, Wai zai sata amai, Essha baki. Kwadayi duka ta shanye harda na leda duka suka hada suka cinye.
Suna Gama ci Aina’u ta shigo taga duk su cinye sai kashi🦴 ya rage.
Tace” wlh yanmata na baku kyauta min ba, Ina ta sauri nazo ashema ku cinye”
Essha tace” yi hakuri sis da Allah Kar ki fada ma mom tare mukaci “
 Bata amsaba ta sharesu ta haye gado ta kwanta , Essha ta matso kusa da ita ta yaye bargo tana mata cakulkuli ,
Aina’u tace” ya’isa ya’isa tafada Tana dariya, ya wuce bazan fada ba, wlh ke Kuma Allah yasoki “ta nuna hunaisat.
Eh din” hunaisat ta fada Tana mata gwalo.
Aina’u tace” habawa ai Allah yakaimu gobe muga baki Rashi kunya yanda zaiyi”
Hunaisat ta amsa da ameen” ta murguda mata  baki.
Essha ta Mike ta tatara kuloli takaima big mom, ta wuce  guri hajiya ta mata sai da safe.
Tana dawowa ta cire hijab din da tasa, tayi shiri kwanciya , zata kwanta hunaisat tace” sis zokiga anko ki, kigashi ta daga atamfa da lace duka dogaye rigunane  diki”
Tace” sis wlh nagaji da safe na gani , ta koma tayi addu’a bacci, tace ” sis ainan , amarya sai da safeku , suka amsa da Allah ya tashemu”
Hunaisat ma tabar chatting da take yi da Anas ta mishi good night , ta kashe wutar daki ta kwanta.
Comment & share 🥰😘🙏🙏
Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by-j-hajara
1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣
Washe gari
Da misali karfe  goma ne za’a daura aure, su Essha tunda suka farka da asuba Basu samu su koma ba, gida cike tam da baki nisa Dana kusa, sai shirye shirye daura aure kawai sukeyi.
Amarya hunaisat a shiryata ba karami kyau tayi ba, Mai makeup Anas ya turata ta tsantsara ma amaryashi  makeup da yanmata amare, har su maryam suzo, su ma susha ankosu ba karami kyau sukayi ba.
Can na hango Essha da Aina’u wow yanmata sufita, inbaka kalli Essha sosai bane baza ka gane taba, ta hadu karshe haduwa, duk inda suka wuce sai a kallesu akara.
Suna kan tafiya suka hannu dasu Yaya Usman, a hanya sufito daga part nasu dukasu Sha shadda farare kal kal Suma su fito.
Salis ne yace” wow sis kifito daker na ganeki, na zanta kowata bakuwa ne mukayi daga Makkah”
Tace” Kai Yaya salis Banda shairri fa”
Allah sis ya fada”
Usman yace” ko kyau, Bata ma iya kwaliya ba, Aina’u ne kawai tayi kyau”
Tace” oho dai jealousy, don nafi budurwa ka kyau”
Yaja mata hanci yace” Allah yakiyaye kifi budurwa na kyau, gata a kusa dake “yanuna Aina’u , Aina’u ba karami kunya taji ba, ai da gudu tabar wajan.
Abba yace” Yaya gashi kasa inlaw na ta gudu Wai ita kunya” ai duka suka fashe da dariya
Suka sata a tsakiya Wai adole sai suyi hoto, ai kuwa dole ta tsaya, suka kashe hotuna kalakala, salis ya aiki Sameer yace ma Aina’u ta fito da hunaisat za suyi hoto, aikuwa nandana yaje, ya dawo yace” gasu zuwa Yaya”
Suna zuwa aka sake Dora selfie kalakala ba adadi.
Salis yace” dole na tura ma Yaya Abdul Wana yayi missing (Abdulhamid Yana service a imo shiyasa bai zoba).
Khasim yazo yakira Essha yace mata ga daddy ta a guest room Yana neimata, ai da sauri ta je ta samaishi, tare dasu hajiya yake, ta gaishesu.
Tace” lah daddy yaushe kazo?
Yace” tun 7:00am Ina garina”
Ta shagwabe fuska tace” dad jiya fa munyi waya baka cemin zakazo ba”
Yace” yi hakuri Essha mantawa nayi”
Tace” ya mum da su autar mum?
Kowa lfy su ce na gaisheki, ama fa mufeedat batasan nazo ba”
Tace” eya daddy daka kawo ta”
Yace” no guri da nisa, Bata Saba ba”
Tace” toh dad bara na wuce”
Yace” okay inza wuce zankiraki”
Karfe goma dai dai aka daura aure hunaisat da Anas.

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements