DOCTOR ESHA Page 21 to 30 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / DOCTOR ESHA Page 21 to 30

DOCTOR ESHA Page 21 to 30

DOCTOR ESHA Page 21 to 30

Mami tace” Isa kiramin Joseph ”

 

Isa yadana wani Abu kamar waya..

A jiki an rubuta security alert, ko minti daya baiyi da danawa ba sai ga chief security ya shigo da sauri shi..

Mami ta kalleshi tace” Kai da yaraka kuje kune nemi yarona, imbahakaba…..bata karasa ta kada yatsa sanan tace” and you guys should be fast”..

Advertisements

Jiki ladabi chief security yace” okay ma”..

Haydar ya Mike yace” Ammi zanbinsu ?”..

Tace” toh Haydar sai kun dawo , Allah ya bayanashi” suka amsa da ameen” ..

saura ma suka Mike suka ce zasuje..

Ammi ta kada Kai tace” Hafiz da Allah Kar ku Bari  maihafishi ya yaji Wana magana ku jiko? “..

Yace” inshallah Ammi Kar kidamu”..

Suka bi baya chief security..

 

Suna fita chief security na fita ya shaida ma yaranshi su shirya zasu fita, Suma duk jikisu yayi sanyi su San suna ciki tashi in har tycoon yaji labari na .

Wani Babba gate dake gefe haraba mansion din chief security ya nufa, security gate ne , sanda ya Dana wasu lambobi kafi gate din ya wangale kanshi..

ciki babba fili da aka gyarashi sumul sumul , helicopter ne masu ji da kansu dal har uku , ruwa navy blue  , jiki helicopter suna TYCOON ne baro baro aciki..

 

Advertisements

Chief security da wani daga ciki matuki helicopter din Mai suna mike.. chief security ya karbo keys din helicopter din daga guri Mai kula da guri .. ya Mika ma Mike daya , suna shiga ya daga masu Suleiman hannu da saura yarashi , su Suleiman na shiga suka gyara zama sit belts , helicopter biyu su ka dauka, Suleiman da haydar na tare da Mike, Hafiz da fawaz suna ciki na chief security .. motoci ana waje ana jira sutashi.. suna dagawa zuwa sarari samaniya suka dauki hanya kaduna, tafiya suke kasa kasa kamar za su sauka ma mutum akai, ba’a abunda kakeji sai Kara helicopter a hanya kaduna, ba inda Basu duba ba, lungu da sako ,ama ba Aliyu ba labarishi jiki a mance sukasake juyawa,  su fawaz su matukar shiga tashi hankali aranshi gani aboki nasu, har su fi security dima ..  su Ammi naji dawuwarsu suka fito da sauri da zima ko angashi ..

Mami ta nufi haydar da kanshi a kasa ta tasa hannu ta daga shi Yana kallota murya kuka tace” haydar ina yake ? Ina boy Dina ? Tana magana tana jijigashi

Yace” Mami hakuri zakiyi inshallah za’agashi ya fada murya na rawa”

” Haydar boy ya fita gidana tun 8:00am gashi ganshi  uku tayi har da minti na,ba’asan inda yashigaba iyye Wai Wana wani iri duniya ne muke ciki”ta durkusa a kasa tana kuka…

Ammi ta dagata da sauri tace” ki daina kuka za’a ganshi inshallah, kuzo mu shiga ciki”

Mami ta juya ga chief security tace” ku bance min dagani baga amfani ku ba” …

Da sauri suka bar gun don Suma  sunfisu ciga tashi hankali

*******************
Suhaima ne zaune da hajiya binta, sanye take da wani half gown a jiki, wata maid nata na kasa tana gyara mata kumba kafa, a hankali ta dubi hajiya binta ta shagwabe fuska… Hajiya binta tace” yadai Baby na?

” Mummy tun jiya nake trying number Hubby yana shiga ama bai dauka, yau Kuma switch off ne gabadaya, kila ma da gangan ya kashe waya “ta fada murya a shagwabe

Hajiya binta tace” yo Baby na Mai kike ci na baka na zuba, nasha fada Miki cewa Kar kisami damuwa, shi Aliyu guda nawa yake, kawai ki Kira Daddyshi ki gaya Mai”

“A’a  Mummy wallahi  tsoro Daddy shi nakeyi, Allah Mummy shakkashi nakeji  bazan iya ba” ta girgiza Kai

Hajiya binta ta tafa hannu tace” iyye baby duk fadi duniya na Ashe akawai Wanda kike shakka da tsoro , haba dai*2 Kar ki badani mana , kamar ba baki Kisha ba , ta nuna kirjita.. kwantar da hankali ki ai na Gama da uba , yaro muke jira yanzo hannu,kisan nawa na kashe da wuya danasha kafi tycoon ya Amince da aure, Dan kutumar burar uba danya Kai ne dasu, sai ayi dagaske, kawai ki kirashi ki gayamai”

Suhaima ta daka tsale tace” hoho sai mummy na” ta tura Mai gyaramata kumba tace” ke banza tashi ki bar na, kice ma lami akwai pant da brazier na Dana cire tasa yanda zatayi dasu Kuma ta gyarami daki”…

Da sauri jiki na Bari Yar
aiki ta Mike tace” toh hajiya ” ta fice. Suhaima ta binta da kallo tana yamutsa fuska..

Tace”Mmmy nakirashi yanzu ba matsala?”
.

” Ai baby na ki kwatar da hankali ki kamar kiyi filo da gawa, kirashi kawai ai mugama dashi”

Suhaima har da gyara murya za’ayi waya da siriki, ta dauki wayata ta dialing hot line din Tycoon da bakowa ke dashi ba sai family nashi..

 

CAPETOWN, SOUTH AFRICA..

Tycoon ne zaune a baki beach na babba birni Capetown na kasa south Africa, gaba da bayashi duk bodyguards ne, zaune yake aka kujera beach , da Dan karami table agabashi, samashi kuwa umbrella ne babba Mai fadi Yana Kare minshi rana, sai danne danne kawai yakeyi a laptop dake gabanshi Yana sipping Liptop…

Bodyguards dake rike da wayoyyisa ya karaso da sauri yace”  Sir ur phone is ringing Kuma hot line ne” ya fada cike da girmamawa..

Fuskashi na kan laptop din yace” okay answer it, kila Aliyu be, basa matsala shi ba tun jiya bai kiraniba ”

” A’a  Sir bashi bane ” bodyguard din ya fada Yana Mika mishi waya..

Ya karba yasa a kunne, suhaima ko sallama tace” hi Dad”

Tycoon yayi murmushi yace” ohh siyama Daddy yakike?

Suhaima ta Bata fuska tace” Suhaima ne sir”

Yace” ohh Suhaima yakike?

 

Ko amsawa batayiba murya tsoro tace” uhm uhm da..da ma..dama ….

Yayi murmushi yace” saki jiki kiyi magana kinji suhaima am ur dad”

” Uhm Aliyu ne, tun jiya Ina Kira shi bai daukaba, yau Kuma a kashe, shine na Kira naji ko lafiya ” ta fada murya a shagwabe….

Dam yaji gabashi ta fadi yace” shi Aliyu ne number shi a kashe?

Ta amsa da eh Daddy”

Yace” hold on, kashe bara nakirashi”

 

 

 

 

 

 

Comment & share

 

 

 

*DOCTOR ESSHA*

_WRITING BY_
_J Hajara_

*MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION*

“`Kungiya d’aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoyan ta.“`
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________

&

 

Nan take ya dialing number Aliyu, number akashe, yanaa trying ba adadi, yace bara na mishi video call” ..ya jayo laptop nashi, daya Dana number Aliyu ko ringing baiyi sai yanuna disconnect, inyakara trying abun daya yake nunanawa.. .. ” bara nakira ammishi dai naji ko lafiya” yakirasu duka bawanda ya dauki waya..lokaci kam su Ammi sufita dukasu suduba ko aganshi ,Basu fita da wayaba… Ranshi ya Soma baci kawai yace bara yamusu video call direct da number gida yaga ko lafiya…layi ya Soma ringing ba’a dauka har Kira ya dauke, yasake dialing …

Rahma da shigowanta falon kenan taga Kira Daddysu, wana abun dai kamar tv ya bayana sai surutu yake Yana cewa” alert alert Daddy  is calling” da gudu tafita sukaci karo dasu Ammi a hanya..

Jiki a sanyaye tace” Ammi daddy ne ke Kira Kuma video call ne”

” Inalilahi waina ilaihi raju’un” shine abunda Ammi ke ta nanatawa. ..

“Ammi kawai muje mu amsa Kar anunamishi komai nafaruwa” Suleiman ya fada…

Siyama tace” eh haka za’ayi Ammi ”

Suna shiga wani Kira nasake shigowa, duk suka zauna suka natsu kamar ba komai..Haydar ya picking kira… Tycoon ne ya bayana a screen, dun dole duka suka sa murmushi dole,ya bin ya parlor da kallon daya baya daya, suka gaisheshi ciki girmamawa, ya amsa..

Ya Kai dubanshi ga Haydar ya jefa minshi tambaya” Haydar ina takwaraka?”..

Haydar yaji tambaya a bazata ya kasa motsi in ya kalli Ammi sai ya kalli mami… Ammi ta mishi Alama yayi shiru…

” Haydar nace Ina abokika? Yasake tambaya

Haydar ya tsure ya rasa wani amsa zai bashi …

Sofia ta amsa charaf idota da haweye ta Soma magana tace” Mami , Ammi kuyi hakuri, ta juya ta kalli tycoon tace”  Daddy Yaya tun safe yatafi kaduna, kuma Ummi ta Kira tace baizoba, ba Ina ba’a duba ba’a ganshi ba” ta fashe da kuka …

Isa yasa hannu akai yace ” shikena yau munshiga uku”

A fusace Tycoon ya Mike cike da kidima da razana har jikishi na Bari yace” Aliyu nawa ne ba’agani ba tun safe” kit ya kashe Kira….

Mami da Siyama suka fashe da sabon kuka… Ammi tayi lalashi har ta gaji ita kanta daurewa takeyi.. su Fawaz ba motsi sanda aka Kira sallah la’asar tukun suka Mike zuwa masalaci …

 

Tycoon na katse Kira jikishi sai rawa yakeyi, yakasa natsuwa … Yace” ismail maza maza kiramin pilot ” ba da jimawa sai ga pilot ya karaso…

Yace” muje ku Nigeria zamu koma yanzu na”  Yana jikishi na bari…

Ko yajira a bude minshi motar dankashi ya bude yashiga, aka tada motoci sai airport, private jet dayazo dashi ya wuce direct ya shiga , da sauri guards suka bi bayashi suna shiga jirgi na tashi.. bada jimawa su ka sauka Nigeria, kaduna airport , da sauri guards suka sauke motoci dake ciki jirgi.. saboda emergency iri haka suke ajewa..

A ciki motar kuwa sai ma driver matsifa yake Wai bai sauri, gudu kawai suke akan hanya kamar zasu tashi a sama , har suka karaso anguwar su Ummi , sai horn kawai suke zubawa , da sauri gate man ya bude gate din suka shigo…

Ummi dake sama balcony tana sauraro redio taga shigowar motoci tace” wato shakiyi yarona sai yanzu ya karaso, zanyi maganika ka ai” ta dauki walking stick nata ta fara saukowa tana zuba matsifa…  Tana sauka taga Tycoon ne.

” Wato ma Kai ka rakoshi kenan ? Ummi ta fada cike da matsifa tana ta leleka ko zantaganshi..

Tycoon ya nufo Ummi yace” Ummi ba’aganshi ba, Wai yazo na kaduna ” ya fada jikishi na Bari”…

Ciki tashi hankali da razana tasake tace” Aliyu din, inalilahi wayyyooo nashi ga uku na Ina gada gana yashiga ” ta fashe da kuka ta sake walking stick din Kamar zata fadi, Tycoon da sauri shi ya rike ta..

Yace” Ummi Kar ki tada hankali ki za’agashi insha Allah nayi waya da commissioner yansanda, ya tura yarashi a bazama nemeshi, Kar kidamu Ummi” Yana magana muryashi na rawa”..

Ummi ta share hawaye tace” toh naji, Umaru nasa kawai dauriya kake yi , wuce ciki kasamu ka huta”.

Ya girgiza Kai yace” Ummi bazataba samu wani kwanciya hankali ba har sai Naga Aliyu, kiyi hakuri Ummi”..

Ummi tace” Aya Umaru Kar kadaga hankali da yawa fa, Ina zuwa”… Sai gata ta fito,Yan aiki maza ne biyeda ita suna rike da babba daddurma da plastic chair,  Uncle Bello  nabinsu a baya hannushi rike da bottle water…

Ummi tace” Kai ku shimfida a gabanshi”… Suka shimfida, taje kusa da je kusa da Tycoon da sai safa da marwa yake, wayoyyishi sai Kira akeyi yahanasu amsawa.. jikishi sai Bari yake…

Ummi tace” Umaru zauna ka huta “..

Yace” Ummi kiyi hakuri, baza iya zama ko samu sukuni ba har sai Naga Aliyu “..

Ta kada Kai Tana hawaye tace” haba Umaru da wane zamuji , dubi fa Bari kakeyi a tsaye, Dana shiga ciki maihaifiyarshi ta Kiran, tana kuka Wai kaki daga wayoyisu, Alama dai kenan kana fushi dasu, haba dawane zamuji” ta fada Tana share hawaye…

Yace” ya’isa Ummi daina kuka, bayi fushi dasuba, gashi zan zauna… Ya zauna.. ” Abba Salma mu zauna”..

Ummi ta gyara zama tace” inba fushi kakeyi dasu ba, gayamun Maiye dalilika na ki daga musu waya, Aliyu ko da masu Kama da gunki na(guards ) ya fita in Allah ya rubuta wani abun zai samaishi toh fa bazai tsalake ba saiya faru, saboda haka ka kwantar da hankali ka insha Allah za’agashi ciki koshi lafiya kuwa, ba abunda zai samaishi, Kuma ai Aliyu ba yaro bane”..

Uncle Bello   yace” gaskiya ne Ummi, insha Allah za’agashi”.

Yace” Allah yasa” ya Mike tsaye

” Ina zakaje? Ummi ta tambayeshi

Yace” masalaci zanje Ummi, ankira sallah la’asar”..

Baigama rufe baki ba bodyguards Mai rike da wayoyyisa yazo da sauri yace”Sir,  commissioner ne ke kira”..

Ya amsa da sauri yasa a kunne yace” hello kungashi?”..

Daya bangare commissioner yace” Sir  lungu da sako, ciki gari da baya ta, hanyoyi titituna ba inda bamu duba ba, yallabai ka Kara hakuri, dakaina nayi jagora , ama Kar kadamu yallabai zamu Kara himma, sai aganshi yau Dina ba gobe ba”..

Tycoon duk ya firgita baiya magana sai bin waya yake da kallo… Karshe ma katse Kira yayi …Ummi sai kuka..

Yasa hannu a baya yaje ya dawo*2 iyayi sai furza da iska..

Can yace” Abban  Salma kashiga da Ummi ciki ni zanje sallah “..

Ummi tace” Umaru zaka iya fita jiki ja fa yannuna bakada lafiya ?”..

Yace” Kar kidamu Ummi sallah zanyi”..

Ya wuce bodyguards na binshi a baya hagu da dama, fuskar na ya hadashi tam kamar baitaba dariya ba,  har yakarasa baki  masalaci, dakanshi ya dura ruwa a tap yayi zauna yayi alwala hannushi na rawa saboda baci rai, mutani masalaci kam sai mamaki sukeyi yau tycoon ne a gabasu, mutumi da suke gani a tv yau ganshi su ganshi a zahiri…. Yana idar da alwala ya wuce zuwa ciki masalaci guards zasu bimshi ya dakatar dasu da hannu, baya an tada jam’i suyi sallah su idar, ya zauna yadade a zauna Yana roko Allah yabayana mishi Aliyu shi …sai misali karfe biyar ya fiti, jiki shi duk yayi lagwas, guards ne a baki kofa masalaci suna jira fitowa shi, da Uncle Bello hardasu commissioner, hannu kawai ya daga musu bai yi maganaba, ya tsaya shiru sai bi anguwa kawai yake da kallo….

 

Shiru shiru bakaji motsi, yakai dubanshi  ga gate dinsu Ummi.. kawai idonshi ya   sauka a wata motar kirar range Rover, can Parker  nisa da gate din,  ya tsaya shiru Yana kallon motar.

sai ga commissioner ya karaso gefe shi” Sir munkarasa ciki ko, yamma nayi Sir,Naga alamu sunu na kamar bakaji dadi”..

bai amsaba,shidai hankalishi kawai na kan motar na.. ” Abba  Salmah waye da motar na a anguwar na daya Parker shi a gefe gidaka? Ya jefa ma uncle bello tambaya..

Uncle bello yace” yallabai wata motar kenan ni bagantaba?”..

Yayi nuni da motar dake can a Parker a gefe gate… Inbaka lura ba bara kasan da wani motar aguriba..

Uncle Bello yace” Kai gaskiya babu, ama basan dai ko wani bako bane mukayi..”

 

Dai dai lokaci da suke magana aka motar, iska ya kada, kofa ya bude dayake ba rufewa akayiba, an jigina ne, Tycoon yaji gabanshi ya fadi, dun kamar ya hangi mutum a ciki, ama baigani sosai saboda akwai Dan tazara a tsakani su…

Ya Soma tafiya yanu fi guri motar….

Commissioner yace” sir Ina zakaje kuma?”..

Hannu kawai yadaga minshi(Ashe Aliyu yayi gadone)…. Yayi Tata ki har guri motar ama baikaba yaga ko waye ba..

 

 

 

 

Comment &share

 

DOCTOR ESSHA

Writing by J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

 

Kungiya d’aya tamkar da dubu.masu Nazari da Aiki da ilmi, burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

 

 

&

 

Har zai juya kawai ya hangi hannu mutum ya fito, da sauri yakarasa guri motar, gabanshi na faduwa , Yana karasawa wa zai gani Aliyu ne, kwance shabe*2 kamar baya numfashi, ya yake salati da Karfi sanda su commissioner suka firgita, da sauri su su ka karasa wajan, Tycoon yakara bude kofar backsit din yashiga ya talafoshi, abunda yakara razana shi gani jini da ke jikishi yasa yakara rikecewa, ya talafo fuska Aliyu yace” Aliyu bude idoka nine Aliyu, nace ka bude idonka daddy ne”

Su commissioner da karaswasu kenan suka taimaka mishi aka fitar da Aliyu daka ciki motar,, Tycoon duk ya rikece dagani hali da Aliyu keciki..

Commissioner yace” yallabai ka kwantar da hankali ka tun da aganshi….

Tycoon ya katse shi da cewa” maza ku Kira min ambulance “…… Ciki hanzari uncle bello ya Dana kira number ambulance din hospital dayake zuwa, bada jimawa ba suka karaso….. tycoon dakashi ya sukuce Aliyu yasashi a motar ambulance.

Dai dai Ammi na Kira waya uncle bello, ya amsa, yaji duk murya yaji duk murya a shake Alama Tasha kuka tace” Yaya haryanzu fa bw Aliyu ba labarishi gashi har magriba ta gabatoh”

Uncle Bello yace” Hajara, alhamdullila Zaki ce don aganshi, yanzu haka asibiti za’ayi dashi, ki kwantar da hankali ki”

Ammi ta rude da taji cewa” za’akaishi asibiti tace” subhanallahi, maiyesameshi? Aina aka gashi? Aciki wani hali? Ta jero tamboyoyi duk lokaci daya….

Uncle Bello yace” hajara wa na tamboyoyi haka nace ki kwantar da hankali ki”

Ciki tashi hankali tace” a’a Yaya gamuna zuwa” ta kashe..

Aliyu kam tuni aka wuce dashi wani babba private hospital dake ciki gari kaduna, likitoci ciki gagawa  suka karbeshi, ana bashi taimako gagawa .. .

Tycoon ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai ziriya kawai yake a baki daki, addu’a kawai Allah yasa Aliyu ya farka, ya fi hour daya, haka ma guards duk inda yabi sai su binshi da sorry sir”.. commissioner da uncle Bello su na  ta rokeshi ya zauna ya huta, ko kulasu baiyiba, harsu Ammi suka karaso, duka family din, hardasu Suleiman..

Likitan ya fito daga daki, da sauri Tycoon ya nufeshi, Ammi da Mami ma haka, don dagani alamu shine likitan

Tycoon yace” Doctor how  is my son doing ?… Kowa ya tsaya cirko cirko Ana jira amsa likita..

Likitan yayi ajiya zuciya yace” sir ka kwantar da hankali ka, ba wani Abu bane Mai tsanani dogo Suma ne yayi sakamako kwaya dayasha,  bincike mu ya nuna, kwayoyine suka so suyi mishi illa har yakaishi da Suma”

Kwaya?!!! Harsu na hada baki guri Kira….

Mami ta rude ta cakumo likita a gaba riga tace” what the you by that, Dana baya shaye shaye”… Likita duk ya tsorata sai zaro idon kawai yake,..

Suleiman ya zo ya janyeta yace” Mami kiyi hakuri munji bayani likita, Nima nan zan shaidin Aliyu akan baya shaya shaya ” yakali doctor yace” doctor yajikishi yazun?

Doctor kam ya gama tsorata balle yaga family din tycoon dashi tycoon baison yayi kuskure da saurishi ya amsa yace” yes jikishi da sauki inshallah Nanda few minutes ma zai iya farfadowa inshallah”

Tycoon yace” doctor jini dake kayashi  fa?!

” Sir muyi iya bincikemu, ba wani ciwo da yaji kila shafaminshi akayi bamudai sani ba” doctor ya fada…

Ammi tace” zamu ‘iya ganishi?

“Eh hajiya zaku’iya shiga”.. doctor bai Gama rufe baki ba Tycoon ya shiga, saura suka bin bayashi ciki hanzari…kwance yake, hannushi da Kari drip, idonshi a lumshe haryanzu bai farka ba, bawanda bai tausaya mishi dagani hali da Aliyu ke ciki. Tycoon ya zauna a gefeshi yarike hannushi, daki ayi shiru kamar ba mutani aciki , har aka Kira sallah magariba, Aliyu bai farka ba, jikisu a mace suka je sallah, har akayi isha’i , suna idarwa suka sake komawa daki. Daki dal yake  da wutar lantarki koina kamar Rana, Ammi,Mami  da su rahma suna zaune ne akan katuwar daddumar da akan shimfida a daki, kowa da carbi a hannusu suna casbaha,duk suyi shiru kamar a musu mutuwa, rabonsu da abinci tun breakfast na safe, ba karami tashi hankali suka shigaba,  da sallama suka shiga, suka amsa.. Tycoon ya nemi guri a daya Dana ciki kujera dake kusa da gado Aliyu , ya zauna shiru, ya kalli gefeshi yaga su fawaz ne duk su zuba tagumi Suma idonsu na kan Aliyu harsu bashi tausayi, uwa uba Idrees da tun zuwashi yakasa sukuni..

Tycoon ya girgiza Kai yace” haydar kuje gida ku huta, inshallah abokiku zai farka, ai abun yazo da sauki tunda aganshi ko?Isa ka dauki ummi dakai”

“a’a daddy kayi hakuri mu zamu zauna, Kai kaje gida ka huta, dasu Ammi , Kuma ma am a doctor zan iya kuladashi” fawaz ya fada..

Idrees yace” gaskiya ne daddy, yakamta kaje ka huta , kusa wani abun a ciki ko, kaga su rahma yarane Kar yamusu illa”

Tycoon yayi ajiya zuciya yarike hannu Aliyu tam kamar za’akauce mishi, baice uffan ba,can yaji kamar Alama hannu na motsi, kafi yayi wani abun ya sake hi Aliyu ya Kara rike hannu shi gam, da sauri ya daga Kai ya kalli fuska yaga kamar ya farka,bakishi na motsi kamar abun yakeso furtawa, same time idonshi a rufe. Tycoon ya Mike da murna yace” Alhamdullila, Aliyu bude Idonka  daddy ne” ai su Mami daji haka duk suka yo kansu..

Aliyu kam ya farka ama dishi dishi yakai gani mutani da ke kanshi, kafi ya bude idon gabadaya a hankali, Yan bi Yan daki da kallo daya baya daya, yayi mamaki ganishi ana,jikishi gabadaya ya mance, ya sake binsu da kallo har Yana Kara Ware Ido.. Essha yake so gani ama batanan, a razana ne ya Mike yana dube dube..

Tycoon ya rikeshi yace” Aliyu Alhamdullila ka farfado”

Yakalli daddyshi , bakishi na rawa yace” daddy Ina Essha? Daddy Ina ku kaita? Duk ya birkece yakasa natsuwa sai tambaya su Essha yake…

Mamaki yahana Tycoon amsawa shima maimatar suna yakeyi “Essha Kuma? Ya juya gasu Ammi yace” wacece Essha kuma?ai’na take ?

Ammi ta girgiza Kai tace” mufa bamusan wata Essha ba, kila dai su Hafiz za su santa”

Hafiz yadaga hannu Alama basusan da wata Essha ba..

Haydar yace” Ammi bamu taba ji yakira maisuna na Nan baa”

Tycoon ya kalli Aliyu da duk ya birkece suna Essha kawai yake furtawa , ya dafashi yace” Aliyu mune fa, ur family, here is ur mom’s ur siblings, ur friends and ur granny  no one is bearing essha here, first of all wacece Essha?

Aliyu ya tsume fuska ya tsay ya yana kallasu shiru ya rasa wani amsa zai basu, a ranshi yace” waton kenan daddyshi a daji na yabar mishi Essha, No she’s hurt,dad u can do that….yayi yikuri zai sauka,da sauri fawaz ya rikeshi yace” buddy kayi hakuri kayi a hankali fa, u re sick”

Ya kalli fawaz dake magana ya Soma hawaye yace” Essha fa, badai aguri ku ka bar min ita ba,ya daka tsawa sanda daki ya amsa da amo muryashi yace” Ina Essha na ,she’s hurt, tana bukatar taimokona ”

Tycoon yace” calm down son, Essha Kuma? Ai’na take Wai gayamin?

Aliyu ya fara sambatu Yana nuna both side nashi yace” dad she was here with me, tana bukatar taimokona daddy, maiyasa baku daukotaba ? Daddy ni zanje ,I will go and bring her,she’s my wife ” ya Mike ya balle drip dake hannushi, carnular kadai yabari,  jini sai rushing yake daga hannushi Yana diga  a kasa, zai balle sauran carnular dake lilo a hannushi, tycoon da uncle bello suka rikeshi suka zaunar dashi ama tirjewa yakeyi Yana kokari mikewa, ga Kuma jini nata zuba a hannushi.. fawaz da sauri ya dauko plasta da cotton wool yarike hannu  Aliyu dake zubar da jini ya dressing  hannu.. ya kalleshi gaskiya ya tausaya mishi, dun tunda suke da Aliyu baitaba shiga ciki wanan haliba..aranshi yace” ayya ba wani Abu aka bashi yasha dagaske ba, har Yana Kira masu suna  da Basu taba Koda mu’amalane da Mai iritaba..

Aliyu ya kalli fawaz da daddy shi duk yazama abun tausayi yace” please daddy ku sakeni na je na dauko matata, tana bukatar taimakon, Kar su cutar da ita please daddy ka taimakeni ..

 

 

 

 

Comment & share

 

 

DOCTOR ESSHA

WRITING BY
J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta  fad’akar ta Kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_______________________

 

&

Kowa sai bin Aliyu suke da kallo mamaki, yadda yake Kira Essha na dai a matsayi matashi, Ammi abun ya fara Bata tsoro da mamaki” ayya Aliyu kwaya na da akace yasha bai taba minshi kwakwalwa ba ko, dun ta sa yarota, tun tasowarshi soyaya bai dameshi ba, balle wata mace daban da har ya damin kanshi haka”

 

Mami ta Mike ta shafa kanshi tace” boy Kaine kuwa,  u r hurting yourself ka kasa natsuwa, da Kira wata daban da mu bamu Santanba… talk to me mana boy,  boy Dina jarumi ne baya ragonta, Mai yasa ka….Bata karasaba ta fashe da kuka…

Aliyu da sauri ya rugume ta shima haweye yakeyi yace” Mami no, please don’t cry, sshs karkiyi kuka, Essha ta ba wata daban bane Zaki santa Mami, she’s my preety, my destiny, my wife”

Yasaketa Yana ta musu describing yanayi Essha Yana sambatu , ya rike hannu tycoon ” daddy let’s go zo muje mu dauko ta, Kar wani abun ya samaita, kaji dad zo muje”

Duk suka tsaya suna kalloshi cike da mamaki don aik aika Aliyu yafara Basu tsoro, yi yake kamar ya zare, kowa da yanda yake aiyana abun a zuciya, su Suleiman sufi kowa mamaki” yau Aliyu ne ke sambatu akan mace, Wanda su Basu santaba..

Ummi tace”   eya lamari yarona, ba accident yayi a hanya ya boye suka shafeshi bako, sai Kira suna da kwantace mace yakeyi, duk kwantace na fa Mai suffar aljanu ce, gashi har baya, fara da ita, idonta kaza Wana kaza, Kuma Yana kirata  a matsayi matashi, eya ba aureshi tayi ba ta shanye manashi?!!

Duk suka Amince da maganar ummi…. Aliyu yasa ihu kamar ba shi ba yarike hannu Ammi yace” No*3 Essha na ba aljana bace, mutum ce, Ammi ki yardadani… Ya rike Idrees Yana girgiza shi yace” Bro kaima ka yarda kenan cewa Essha na aljanace, a’a ya kadan kai” Bro please Kar ka yarda da batu ummi please…. Idrees rasa baki magana yayi Yana binshi kawai da ido yaje…

Yaje gaban tycoon yace” Daddy zo na kaika ka ganta, kaji dad don’t say no please ka biyoni, please dad my heart is burning, in bagantaba  zuciya na  tarwasewa zaiyi , please dad ka ceceni” ya kife Kai a kirji tycoon yana kuka Mai cike da kunci,

Tycoon  yace” calm down  nayarda zan bika kanuna mi ita, if dat is d solution”
Yadaga da sauri Yana murmushi yace”  dagaske dad” Tycoon ya lumshe minshi idon sanan yace” amafa zaka Bari sai gobe, kaga yanzu baka da lafiya”

ya Bata fuska yace” no daddy  dat place it’s not safe, za ta cutu aguri, Kuma dad na warke muje kawai”

Ya jijiga Kai yace” son yanzu dare fa yasomayi”

Ya shagwabe fuska” daddy muje yanzu if not za’a cutar da ita”

” Toh Aliyu muje”

ya rugumeshi yace” nagode dad”

Tycoon yace” u r welcome boy, can do anything for you….

Ummi matsifa takeyi wai anki yarda da zanceta, gashi yanzu ya biye mishi har da wani zuwa a dubata tace” wlh Nima sai na binsu Naga wanan  ya Mai suffar aljanar na inhar dagaske ke ne”

Tycoon yasa aka Kira doctor yamishi bayani komai, doctor yace” ba matsala sir sai ku dawo”

Duk family su yake za su bisu, fawaz, Hafiz haydar Allah Allah suke suga yariya da ta ruda musu da aboki haka.. ajere motoci kuda takwas, manya manya Jeep ne, Aliyu dakanshi yake driving ,ayi ayi driver ya yi driving yaki, yafadi suna anguwar yace” baisaniba”

Shidai kawai abinda yasani zai kaisu guri Essha, su hudu ne  a ciki motar daya, tycoon, mami, Ammi da oga boss din dake driving, saura Kuma su fawaz, su ummi siyama da su Idrees sai guda biyu Kuma bodyguards ne ke biye dasu..

Aliyu sai sharara gudu kawai yake , Mami suyi shiru suna kallo iko Allah, har su fara fita gari, da’a Ammi ta tambeya shi” Aliyu ba’akai bane?

sai yace ” mun kusa”

Su matukar tsorata dasu ka ga Aliyu yayi corner ta hanya daji, ama duk suka zuba mishi na mujuya ba Wanda ya’ iya cemishi ko da ka’ala.. har sanda ya tsayar da motar a ciki tsakiyar daji, ya Parker ya fito yace” dad, Ammi Mami kifito nane , duk suka bude suka fito..

Sofia da rahma su tsorata daji yanda daji yake motsi, don ba alamu wani Dan Adam na rayuwa a ciki, Kara tsutsaye ne kawai da macizai da abubuwa da baza arasaba ke tashi, gashi yayi dulum dulum..

Ai da gudu suka rugume Ammi, su ka kakemeta..

Ummi da siyama sai Bari..

Ammi tace” Auzibillahi, Aliyu Ina ka kawo mu Kuma?

Tycoon sai bin daji yake da kallo, Yana mamaki yanda Aliyu yasan daji, don daji Mai hatsari ne ba kowa bane keshiga, sai ka shirya kanka…

Aliyu yayi murmushi” yace Ammi Essha na ana take, tana can a bukka kuzo muje”

Wa?!!! Hafiz da Isa har suna hada baki.. Hafiz yace” gaskiya badaniba” da gudu suka shiga motar suka rufe ..don daji ya matukar Basu tsoro..

Isa yace ” gaskiya batun hajiya gaskiya ne da tace Yaya da aljana yayi gamo”

Suleiman don tu fitowar daga motar jikishi ke Bari saban tsorata yace” buddy kana nufi kenan ana ku ka hadu? Yayi tambaya har muryashi na rawa.. Aliyu ya gada Kai alama eh Yana murmushi…

Suleiman yace” lallai da sake, Kai badaniba” ya make a baya Aliyu yace” Buddy su San ka baza su cutar da mu ba”

Aliyu ya Bata fuska yace” Mai kake nufi??

Yace” su suke gani mu ba mu muke gani su ba, shiyasa na boye a baya ka Koda wani abun zai faru, kaga su Saba da Kai , Kuma na ga baka tsorata ba”     ya Kara noke fuska a baya Aliyu..

Siyama tace” gaskiya shi ne Yaya, tsoro na keji da Allah kuzo mu bar na guri tunkafi dare yayi ko ummi?

” Eh mana, da Allah umaru kuzo mubar daji na tunda wuri, gashi ma ba ko haske… Mami kam kasa magana tayi..

 

Tycoon yace” ku natsu mana aduba, Bari a kunna haske”.    Ya umarci driver’s da su Kuna fitilu motoci.. duka Jeep takwas a kunna fitilolusu, farare kal kal, ya  haske guri gabadaya, ya kalli Aliyu da duk jikishi yagama sanyi yace” son Ina take?

“Daddy a can ne, zo mu karasa ” ya furta murya a sanyaye… Ya jasu suka Kara sa dai dai spot din da abun ya faru, ama ba Alama wata bukka a guri, kamar ba abunda aka taba ginawa a gun..

Aliyu ya rikice ya daburce sai zangaya wuri yake Yana” wlh daddy ana ne, daddy bataa, su dauke ta, daddy ka taimakeni ummi Mami Ammi wlh ana Essha take, ana aka daura Mana aure, my heart is bleeding ya rike sai tin zuciya shi, ya saki ya da fe kansa da hannu bibibbiyu Yana gani komai da ke daji Yana juya Masa, numfashi sama sama ya ke fita, a hankali ganishi yayi rauni , idanuwansa suka rufe ruf ruf Nan ya sulale ya fadi kasa….

Da sauri wani guard ya sukeceshi , tycoon dakeciki tashi hankali da gani hali da Aliyu yake ciki murya na rawa yace” sanshi a motar Abuja zamu koma, da sauri suka tada motoci, Idrees ya zauna a mazauni driver Yana driving dinsu Ammi, hankali su duk a tashe yake, Airport suka wuce,  ambulance aka kira da sauri akasa ma Aliyu abun numfashi akasan Masa don ceto rayuwarshi……….

 

 

 

 

Love ur comments guys

 

 

Comment share

 

 

DOCTOR ESSHA

WRITING BY
J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

 

Kungiya d’aya tamkar da dubu.masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
_______________________

 

 

 

&

 

Baya jirgi ya daga, suka sauka a Abuja, motar asibiti fawaz yakira suka duguma sai asibiti, family din tycoon suga tashi hankali dun Dakar aka ceton Rai Aliyu, kwana shi nagaba, a ICU ROOM aka ijeshi, bamai shiga sai dai su hangoshi ta window glass din kofar daki, duk ya rame a lokaci daya, yakara haske fayau sai hanci…

Fawaz ya fito Yana sharce gumi duk jikishi yayi sanyi yace” daddy kuje gida mu zamu kuladashi inshallah, kusamu ku huta kodan lafiya ka”

Idrees yadafashi yace” daddy  you always encourage us da muriga juriya baikamata ace kanuna kasawaka ba, Yaya zai samu sauki inshallah,.kayi hakuri muje gida ka huta, kaga yadda Yan news suka taru a baki gate, nasan damuka zasuyi”

Tycoon ya gyada Kai Yana haweye yace” muje ku”

Mami tace zata  kwana ita..

Siyama tace” haba Mami kiyi hakuri Yaya ba’abunda. Zai sameishi , gasu yaya haydar zasu kuladashi”

Mami Taki fiti fiti, Dakar siyama da Isa suka convienceing nata tabisu, su Rahman har su fara bacci.. suna kaiwa gida acikisu babu Wanda ya iya bacci, Tycoon kwana sallah yayi Yana roko ubangiji ya fitar da danshi daga ciki Wana hali, hk ma Ammi da Mami

*********************
Daddy karami karfe 6:00pm cib suka isa  gari lafia duk da gudu da yaketa sharewa, tun a hanya hajiya ke tayi dashi ya tsaya a kaita wani asibiti ama yaki..

Suna isa direct DASH(Dalhatu specialist Hospital) babba asibiti gari , Yana karasawa ya Parker motar  aciki haraba asibiti , ya daukota, hajiya ta fito tayi office din likita, Babba likita asibiti Dr. Abass ne mahaifi bestie (sumaiya) da gagawa yasa nurses suka fito da gado  tura Mara aka kaita ciki … Dr Abbas sai tambaya daddy karami yake maiyasa maita?

Daddy karami da sai sharce gumi yake ya girgiza Kai yace” likita ka ceto rayuwa ta da Allah, Kar wani abun yasameta, zanje na sanar ma iyeyeta da Allah likita”

Dr Abbas ya girgiza Kai ciki tausayi  ya shige daki da aka kaita, tashi hankali sosai ya ziryace shi gani hali da take ciki, ya Raya aranshi Aya ba fyade aka mataba… Ya Kira nurses Nan suka dafa masa, suna kokari tsayar da jini dake fita ta kasanta” ya Allah!! Wani Rashi Imani ne haka? Ya fada ciki tsoro gani hali da yariya ta ke ciki…

Fitowa yayi baya suyi nasara tsayar da jini dake zuba a kasata, Allah yasa ma tana da isashe jini imbahakaba har Kari jini sai amata(Aliyu yayi babba aiki) su sa mata leda ruwa da allurori ya Kuma Basu umarni da suyi mata dinki a jikita…

A can gidasu Essha kuwa, family din su shiga tashi hankali, na Rashi zuwa su Essha,  tayi, Dan tun two suke  expecting dawuwarsu, ama gashi har magriba tayi Basu karasoba…

Daddy Essha sai ziriya yakeyi a ciki parlour rike da waya a hannushi, mummy ne gefeshi zaune kan dogo sofa din parlor ita da anty zainab , ta zuba tagumi ita Sam hankali ta bai kwanta ba tafi kowa daga hankali, su amir su na islamiya.

Daddy Yana ta trying duka lambobisu baya shiga, ya Kira Big mum can k.d ta shaida mishi cewa tun safe suka tashi, Killa hold up ne ya rikesu a hanya…

Anty zainab tace” Alhaji ka kwantar da hankali ka za su karaso, kila haka dine, kasa yanayi hanya”

Mummy ta yarfa hannu kamar Mai shiri kuka tace” haba mana, go slow tun safe ace har yanzu Kuma ana trying lambobisu baya shiga, Wana wani iri go slow tun safe haryanzu, Kai ni gaskiya hankali na bai kwanta ba”

Aina’u tace” mummy sha’ani network ne Kar ki daga hankali ki inshallah zasu karaso ciki koshi lafiya” Tana rufe baki suka  ji  horn din motar , an bude gate, da sauri suka fito har suna rige rige.. Daddy da ya rigesu fita yaga Ashe motar su amir ne sun dawo daga islamiya, suna fitowa daga motar, mufeedat ta nufi daddysu tace” daddy sis Essha ta dawo?

Ya girgiza Kai yace” autar mama don’t worry kinji sis Essha suna zuwa ” ya fada Yana shafa mata kai…

Amir yace” daddy datzu da muka fita break na Kira layi sis Essha Yana ringing Bata daukaba”

mummy ta zabura ta nufeshi  tace” layi ya shiga? Kara trying amir”.   Ya fida waya daga ciki aljihu ya dialing number Yana ringing ama  ba’adaukaba..

Tace” Kara trying na daddy karami ko na hajiya”       duka layi in yakira Yana ringing ama ba’adauka..

Anty zainab tace” hmm Allah yasa dai lafiya suke… Bata Gama rufe baki ba sukaji horn din motar, atare duksukayi ajiya zuciya… Daddy yace” gasunna ma su karaso”

Gate man na bude gate, daddy karami ya shigo da motar ko Gama parking baiyiba ya sauko a firgice Yana haweye ya nufi Daddy..  suka binshi da kallo mamaki gabasu na faduwa…

Daddy yace” lafiya ya na gaka a haka Ina saurane? Jini Maine Kuma a jikika?

Daddy karami duk ya firgice sai sharce haweye yakeyi yace” Essha, Essha …. Mummy da Daddy dam sukaji gabasu ya fadi..

Daddy yace” Ina Essha din, maiye samaita? Accident kukayi komai ya jera mishi tamboyoyi a take har jikishi na rawa..

Daddy k. Yace” tana asibiti, ku zomuje, ku yafeni nakasa rike amana, kunyafe nakasa Kare Essha””

Mummy taji kanta na juyawa tace” Wai Mai kake nufi ne? Wani asibiti ? Maiyesameta? Ta fada Tana haweye…

Yace” ku zomuje ku zomuje” mummy ko hijab Bata dauka ba, dogo rigane a jikita sai mayafishi ciki tashi hankali suka dunguma sai asibiti… Hajiya suka samu a baki kofa ba’abunda takeyi sai kuka, har da shesheka da sauri mummy ta nufeta tana hawaye ta dafata murya  na rawa tace” Essha na ta mutu ko? Hajiya ta girgiza Kai.. mummy tasa kuwa kamar ta zare tace”  ki gayamin gaskiya Kar ki boyemin da Allah hajiya, ta mutu ko? Kamar zautaciya takeyi…

Daddy ya janyeta yace” ya’isa ”

” No ka kalleni Ina Essha , Ina take?

Hajiya bataiya cewa komai ba tayi daki da aka kwantar da Essha da hanzari suka bi bayata, suna shiga suka tarda Essha kwance hannu da drip, da mugu sauri mummy ta karasa wajenta tana girgiza ta da dukkani karfita, ama Essha ko gezau, Kara tasaki Mai karfi Wanda amonsa yacika daki da suke.. “ESSHA” ta fada Tana Kara girgiza ta, ciki tashi hankali idon ta ya sauka aka kafata , taga layi jini nabin kafata, ta Kara kallo da kyau, na kafa damata har yasoma bushewa, tasa Kara a karo na biyu, ta Mike ta nufi saiti kafa ta daga dogo riga ta leka,Nan take ta runtse ido, kirjita ne ya shiga bugawa da Karfi gaske, saitin zuciyarta na fat-fat Kamar zata yi tsalle ta fito , ta Soma furta ” inalilahi waina ilaihi raju’un, inalilahi waina ilaihi raju’un” a hankali ta sulale a wajen ta zauna ta rike kai.. tana kallo Essha tana hawaye…

Daki yayi tsit bakiji komai sai sautin kuka mummy da hajiya.. Daddy yagamy rudewa yakasan fahimtar komai dake faruwa,.

Ya kalli daddy karami bakishi na rawa yace” Wai mai ke faruwa ne? Ku gayamin ku barni a duhu. Maiyesameta?

Mummy Dakar ta ‘ iya bude baki tace” Abba Essha, Essha was raped, fyade aka mata ” ta sake fashewa da kuka…

Daddy kansa ya dafa, ji yake kamar zai balle daga madaukarsa, bugun zuciyarsa ya tsanata wajan bugawa.. ya nufi hajiya da kanta na kasa sai shesheka takeyi yace” hajiya ki gayamin zance na Dana keji karya ne, ki gayamin gaskiya ”

Hajiya na kuka ta kwashe duk abunda ya faru tundaga  farko haduwarsu da kungiya har zuwa su asibiti …
Daddy  da mummy su matukar firgita daji wanan labari … Haweye ke sauka a idon daddy kamar an balle famfo yace” inalilahi waina ilaihi raju’un Allahum arjini fi musibati*2….

Tunda hajiya ke bada labari anty zainab ke haweye take haweye, Bata taba jin labari iri haka Mai firgirtawa da abun al’ajabi ya taba faruwa ba ko da a film ne ko littafi ….

Daddy ya rike saitin zuciyarshi Yana girgiza Kai yace ” Essha Dina ne aka aurar da ita, ga yaro da ba’asanshiba , ba’asan asalinsa ba, Allah Mai iko ya share haweye ” alhamdullila tun da har aka daura aure, ba fasikaci suka aikata ba, haka ma yazo da sauki, aure alkhari ne, toh maiyasa kuka bar shi a can baku daukoshi ba?

Daddy karami yace” mun rikece ne da gani hali da Essha take ciki, shiyasa na Manta da batun yaro” dai dai lokaci Doctor Abbas ya shigo daki ya tardasu fuskokisu cike yake da haweye…ya Mika ma daddy Essha hannu sukayi musabaha..

Doctor Abbas yace” kuyi hakuri zata farka, firgice da tsoro ne ya hadasa mata Suma,ya kalli daddy” inason gani ka a office na..

Daddy yakasa magana ya bin baya Doctor Abbas zuwa office nashi , baya su zauna .. Dr .Abbas ya kalli daddy ynda ya shiga damuwa, ya kadan kai” Yaya ku ka Bari haka ya faru da ita? Dr. Abbas ya Mike a fusace yanuna daddy da yatsa yace” ga abunda na ke fadama kenan akullum inmu hadu, kadaina sake ma yaraka da yawa, kullum Kai burika ka, ka farata musu ne baka tsawata musu ba, baya kuma kasa hali yaran zamani na, Wana ya’isa ya zama ishara a gareka, yawa bama yaraka freedom shi ya janyo aka ma Essha fyade . A matsayi na na makwabcika nake gayama gaskiya ” Daddy ya bude baki sheke Yana kallosa har yagama magana , mamaki zance sa ya hanashi bashi amsa.. bai San asali magana shine har ya ke hukuci yake Daura minshi laifi.. toh Wai ma shin maiye aibu  wanan duk ka sake ma yaraka, wanan ai sunnah ne na Ma’aiki (S.A.W.) ka riga farata ma iyalaka, ka Dora musu da tarbiya nagari, takura, matsi ko iyaye suriga hade ma yarasu gira shine zai sa yaro ya natsu no  yawaici ma shine ke cefa yara ciki wani hali( kaluballe agaremu iyaye).

Daddy aranshi yace” wani amsa yaka mata ya ba bawa Allah na? Kai na ma fasa gayamishi abunda yafaru” baice uffan ba ya Mike yabar office din fuska cike da damuwa..
Yana fita Dr Abbas ya tabe baki yace” tundama iriku bakusan gaskiya, kullum Kuna tsakiyar yaraku Kuna washe musu hakora Wai shi so, Kaya sai Wanda suka sa, Tayays bara’aji sha’awa yi musu fyade ba, toh kawace da yanta ma na kusan rabasu very soon “ya kada hannu..

Daddy na fita magaganu Dr Abbas ne ke masa yawo akai, sai tambayar kansa yake” ayya Dr Abbas ne kuwa amintace makwabcishi, shine yake gayaminshi haka, bai tayashi jaje ba, bai Kuma San kan magana ba shine ya yake hukuci, hmmm yayi ajiya zuciya, Yana gode ma Allah a yanda kaddara nashi yariya yanzo a haka , da aure akanta komai ya faru.. yama kanshi alkawari baya family shi bawanda zai gayama ko da kuwa abokaina shi ne, dun yasa tabas bawanda zai yarda da zanceshi, ya bar ma Allah komai, ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi……

 

 

 

 

Ur comment is my strength

 

 

 

 

 

Comment &share

 

DOCTOR ESSHA

WRITING BY
J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

Kungiya d’aya tamkar da dubu. masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
____________________

 

 

&

Ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi, ya nufi daki da aka kwantar da Essha,Yana kaiwa baki kofar suka ci karo da daddy karami da haryanzu kuka yake, daddy ya kalleshi duk ya hargizai yajashi gefe suka zauna a kujeru da aka jera agefe dakuna.  Baya su zauna. Daddy ya kalleshi yayi ajiya zuciya yace” yakamata ka daina kuka na haka duk abunda yasamu bawa mukadarine daga Allah, yanzu kawai munjira farkawata”

“Yaya kunya hada Id……

Daddy ya daga mishi hannu yace” ya’isa haka, Kar ka Manta fa duk abunda yasamu bawa haka Allah ya rubuta mishi, ni musulmi ne kaima haka, Kuma duk muyi Imani da kaddara, Ina Kara godema Allah ba keta mata haddi sukayi ba, aure suka hada rokona ana shine Allah yasa ya zamto alkhari, idan da rabo za su hadu tom, dun ace matar mutum kabarisa, fatana Allah yaba Essha lafiya da juriya”

Daddy k ya amsa da ameen yaji dadi kalamai daddy, sukara kwantar mishi da hankali, suna zaune suyi jungum sanda aka Kira sallah magarib suka Mike zuwa masalaci dake ciki asibiti.

Har akayi isha’i, Essha Bata farka ba, mummy na makale a gefeta , wata likita daban tazo takara dubata ta tabatar musu cewa suyi na bada jimawa ba zata farka.Dare ya tsala dukasu ba bu Wanda ya runtsa mummy da Daddy,  hajiya da daddy k tun baya isha’i, Bala driver ya wuce dasu gida dun su huta.. Essha kuwa can tsarka dare ta farka batama gane kosu wa ye akanta sai kuka take tana fisge fisge tana magaganu” hajiya kuce mishi ya sakeni wlh basan aure, na tsaneshi, mugu ne, hajiya ki taimakeni”

Daddy da gudu yaje yakira likita dake da duty a daren yana zuwa ya mata allura bacci, mummy kam tayi kuka da Bata tabayishiba..

Washe gari sai misali 1:30pm na Rana Essha ta farka.” Alhamdullila ta farka” maganar nurse din data zo dubanta ta ratsa dodo kunnuwansu haka yasasu juyowa a hautsune Dan gani zahiri abun da kunnuwasu suka jiye musu” Tabbas ta farka” mummy ta fada lokaci da idanuwansu suka hade waje daya, da sauri ta karasa wajenta tana ” Essha daddy” ta fada Tana kokari ruko hannu ta, Essha ta Mike da ga kwance da sauri  ta rugume mummy ta, ta fashe da wani kuka Mai kashe jiki Mai sauraro, mummy ma haweye takeyi tana shafa kwantace gashi ta da ya gaji da hargitsewa.

“Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life” ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi ” Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa …. Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka” daddy why me? Why? Why?

Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace” ya’isa haka Essha daddy, ki daina ai’bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma’aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA” yaja mata kumatu yayi murmushi ” ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke”
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya,  Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura  take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace” Essha zanje sallah ankira zuhur”

” Ni ma zanyi sallah daddy” ta fada Tana share hawaye , tun jiya banyi sallah ba”

” Toh mummy ki da antyki zasu tamaika miki” ya fice da sauri baison ya rasa jam’i.
Nurse din ta kalli mummy tace” hajiya bara na taimaka mata dun ba’ason tayi kwakara motsi saboda dinki dake jikita”

Essha ta makale kafada ta tura baki tace” uhm uhm mummy nane zata taimakamin”

Nurse tayi murmushi ta shafa kanta tace” okay beauty badamuwa Bari na baku waje” ta fice..

Mummy ta Mike ta dauki flask din da hajiya suka kawo da safe, tafasheshe ruwa ne dam , tashiga toilet ta juye a baho wanka, da taimako anty zainab ta kaita toilet, ta zuba gishiri kadan ta Kara surka ruwa, sanda suka Kai ruwa Rana Essha ta Amince ta shiga ruwa zafi,  ihuta yagama cika asibiti, kuka tasaki da Karfi tana Kira hajiya da daddy ta su zo su taimaketa, Wai balle Essha iyaye raki.. sanda mummy ta tabbatar ta gasu sosai sanan ta cire ta tasata tayi wanka janaba ta Dora alwala tafito, tan Dan ji dama dama, Dakar take takawa mummy na rike da ita, har su ka Kai baki gado, haweye kawai take sharewa ta hura baki, ita kadai tasan yanda takeji a zuciya ta, sai tsine Aliyu takeyi, yasha Allah yaisa ba adadi.

Mummy ta shimfidar mata daddurma tabata riga da skirt na atamfa tasa da hijab , a zaune duk ta Rama sallolita tana hawaye..

ABUJA
************************
Gari na wayewa ummi tasa su a gaba sai fada take musu” tun jiya nagaya muku cewa su shafi Aliyu ama kuka ki yarda da batuna, gashi har su na nema sumishi illa, Allah sarki bawa , Yana ban tausayi , ke Kuma aljana Essha, Allah yama jikana kataga karfe dake” Mami ta amsa da ameen sanan tace” ummi maiye mafita?

Ummi ta rike haiba tace” mafita kenan ana sallamorshi atara malamai Yan ruqiya kawai suriga mishi tofi har tasakeshi”

Tycoon ya Mike yace” ummi ni zan wuce asibiti”

Tace” bamugama magana ba”

Yace” duk abunda kika ga yadace shi za a yi, sai na dawo”

Mami ta Mike tace” jirani na dauko mayafi na muje”

Yace” sai ki fitoh”

Suna isa asibiti Tycoon ko yaji ra a bude minshi kofa ya bude kofar da kanshi, guards na gani hk da sauri suka bi bayashi ya dakatar dasu.. I C U ya wuce Mami na biye dashi, suka Tara a canza ma Aliyu room an cireshi a I C U. Mami tayi ajiya zuciya tace” Alhamdullila  son yasamu sauki tunda acireshi a ICU” tana magana saiga haydar yamusu iso zuwa harzuwa daki da Aliyu yake , Allah sarki, Hafiz suna na a zaune su zuba uba tagumi harsu dan fada kamar a jikisu ciwo yake, Tycoon ya binsu daya baya suka yi musabaha cike da girmamawa suka gaida mummy ta amsa .

Tace” Allah ya muku albarka” suka amsa da ameen Mami

Tycoon ya nufi gado Aliyu ya ke kwance kamar gawa, baya ko motsi, fuska na tayi fayau, lips nashi duk su bushe, ya shafa ganshi kan Aliyu yayi ajiya zuciya sanan yace” boy Allah yabaka lafiya suka amsa da ameen, ya nemi guri ya zauna a gefeshi ya kalli fawaz yace” Doctor yajiki nashi?

Fawaz ya su sa Kai yace” da sauki dad.gani sauki ne shiyasa aka canza mishi room.

” Ya farka dai ko ? Mami ta tambaya

Yace” eh mami ya farka around two na dare, sai sambatu yakeyi Yana Kira suna dai Essha, shine kawai mikamishi allura bacci, inshallah na bada jimawa ba zai farka”

” Inalilahi waina ilaihi raju’un, Essha Essha haba haba, wanan Essha mutum ce ko aljan da zata adabi rayuwa dana” Mami ta fada ta rike Kai ta fashe da kuka..

Suleiman dake gefe ta ya Mike ya dafata yace” Mami ba kuka zakiyiba, addu’a zakimishi, Allah yabashi lafiya, yanzu Yana farkawa yaji kina Kira suna Essha Dina Kara rikecewa zaiyi”

Mami ta hada hannu ta na addu’a Tana haweye tace” Allah ga Dana na, ka. Fitar da shi daga ciki wanan hali dayake ciki, Allah na rokeka” suka amsa da ameen, suna amasawa sukaji an bake kofa anshigo bako sallama, suna daga Kai sukaga suhaima ne, dogo riga ne a jikita na atamfa ta cugale dauri dankwali bako mayafi s jikita, car key ne da waya  a hannu ta kirar iPhone 11 pro max, Suleiman na gani itace ya baka mata harara, ya Mike ya fice, saura ma suka bi bayashi, don bakarami haushi ta sukeji ba, toh su San hali, ita kam ko ajikita kallo sama da kasa ta binsu dashi taja tsaki.

Suleiman suna yaja tsaki yanemi guri ya zauna yace” wlh I hate this girl, gsky an cuce Buddy, yariya batasan daraja mutani ba, Mai karanci addini” ya Kara ja wani dogo tsaki..

Hafiz yace” Nima ko kallo ta basanyi Mai Kama da sisiya, wlh ko a office ko kallo Bata isheniba, Allah ancuceshi , dubeta ma Kama kara, Allah yasa ma aljanana Essha Dina , aljana ce dagaske, Allah zan iya biyata tayimin maganita yariya ba tarbiya kawai (lolz kuji Hafiz fa).

Haydar yace” Kuna ma da lokaci ta kenan bara kuga hoto da ta daura a page nata na Instagram guri misali karfe 3 na dare fa” ya ciro wayar shi  daga aljihu Yana nunamusu hoto suhaima, suhaima ne zaune a club, su hudu itace kawai mace a ciki su, tasa dogo riga ne a cikita ya matse ta sosai ko rabi cinyar ta baiyi ba, fixing da tayi na attach duk ya barbaje tukunyar shisha ne a gabansu, tana tsakiyar maza, hayaki take fesowa cike da korewa a fuska yan samarin.

Fawaz ya ja tsaki yace” tir da hali iri nata, ni narasa dalili da yasa for the first place daddy ya Amince da aure na, wlh da abani irita guda goma goda aban Yar karkara wancan batasa komai ba” duk suka fashe mishi da dariya..

Hafiz yace” ahaf Kar kudamu nasan buddy zaiyi maganita, zanta gane kureta, Allah sarki buddy yaro kirki Allah yabaka lafiya” suka amsa da ameen..

Ciki daki kuwa, suhaima Chewgum take fasawa fas fas kas kas batama San da su Tycoon a daki ba, hankali ta na waya tana chatting, yantsu zaro zaro yasha pink artificial nails, Mami sai binta take da kallo mamaki, Bata cemata uffan ba, ita akullum tir takeyi da Wana Hadi aure batasan maiyasha kan maigida nata ba da ya nace sai ya aura ma Aliyu Wana gataleliyar, kwanaki baya har batawa sukayi akan magana aura Ammi ne tabata hakuri tace su zubamishi idon Allah yasa haka shine mafi alkhari..

Mami ta tabe baki ta bita da kallo.. Tycoon yace” a’a daughter welcome ga guri ki zauna”

Suhaima har ta Dan firgita da taji magana ta daga Kai suka hada Ido da tycoon ta saki murmushi tace” good morning Dad ” a tsaye ko ta Dan ragwafa.

Yace” morning daughter ga Mami ki ” ta juya ga kallota ga inda yanuna mata, Mami sai binta take da harara kamar idon zai fadi.. na take taji shakku Mami ta sukunyar da Kai tace” good morning ma”

Mami ta amsa fuska a hade ta kauda Kai..

Suhaima Sumi Sumi taja jiki zuwa gefe Aliyu tace” dad ya Mai jiki?

Ya amsa da sauki Yana shafa kafa Aliyu, yana shafa kafa kuwa, kamar ace ma Aliyu ya farka, ai da sauri Mami da Tycoon suka Mike , Tycoon ya rike hannu shi Yana murzawa yace” Aliyu bude Idonka kaji ”

Aliyu dayayi kamar zai bude sai yakara lumshe dasu, har yazo yabudesu gabadaya..

“Aliyu, Aliyu ” yaji daddy shi na Kira, bai iya amsawa ba, ya yinqura zai tashi Tycoon yayi sauri taimaka mishi ya zauna yace” son sannu yajiki? Bai amsaba ya binshi da kallo yasoma motsa baki yanasa yayi magana ama yakasa. Mami ta rike mishi hannu tace” boy badai jiki bane ko?

Kamar ansashi magana dole yasoma magana a rarabe yace” da…ddy m..ami, kun..gan..ta, kug…amin Essha na”

Tycoon yace” subhanallahi, Aliyu ba  kabar magana Essha Dina ba?

Ya dafa saiti zuciya shi yana cewa” daddy zuciya na zata buga da Allah ka taimakeni kanemo mi Essha, daddy imbahakaba wlh zaku iya rasani” da sauri Mami ta rugumeshi tana shafa bayashi Alama rarashi tace”  boy kadaina fada haka, kaji ko, take it easy, ba abunda zai saimeka, this Essha you are talking about , we don’t even know whether ita mutum ce ko aljan, I probably guess ita jinnu ce, don inba jinnu ba, babu mahaluki da zai’iya rayuwa a ciki wanan daji, ka Manta da ita kaji ko”

Ya girgiza Kai yana haweye yace” no Mami bazaniya mantawa da itaba, she’s my wife, my happiness” Mami kalloshi ta tsaya Yi ta mamaki dan nata, daga jiya zuwa yau duk ya canza ya birkece aka mace, har da kirata matashi, Kai gaskiya na yarda Wana aiki jinnu ne…

Suhaima dake tsaye taji duk kalamai Aliyu kefada ai sai ta tsandare a guri, zuciya ta yayi baki,tasoma fitar dawani haweye Mai zafi , ranta yakai kololuwar baci, tanuna kanta” wato ma Aliyu wata yakeso baniba , dun su Raina min hankali shine sukece aljana ce,har dawani kirata my wife my happiness,kan burar ubancan, wlh ko waye ita saita gane kurata” ta fice a daki a fusace..
Su Tycoon ma hankali su baya kata, basumasan ta fice ba,

Aliyu ya rike hannu daddy shi yace” please dad ka taimakeni”

Yawun Mai daci Tycoon y hadiye ya dora hannushi a sama gashi kan Aliyu yana shafawa har sanda ya daina kuka sanan yace” Aliyu kayi hakuri, dakai fa mukaje nemamta bamuganta,mu nemata murasa,  Kai bana tunani ma akwai wani dan Adam dake zama aguri, inason ka dauka cewa faruwa haka daga Allah ne, yayi hakne don ya jarraba Imani ka, na tabbatar idan kayi hakuri wata Rana zai zama labari”

Yajijiga Kai yace” no no daddy bazai iya jurewa ba, daddy she’s hurt, tana bukatar taimokona, nasan duk inda take hankalita yafi nawa tashi, daddy help me please ”

Tycoon yaja numfashi yace” kayi hakuri mana Aliyu be strong”

” a’a daddy bazaiyab, Ina ratsa ta, na ratsa fariciki na, she’s my first love, daddy bazakara samu wani fariciki ba, inhar Essha Bata tare dani”

Tycoon yace” haba son , zaka samu fariciki inshallah fiye da kake zato, nasani wanan duk abunda kake na dan lokaci ne da an daura aureka da suhaima shikena zata mantar da Kai so called Essha”

” a’a daddy I can stop loving Essha, sonta a jinina take, Kuma bazata ba so wata baya ta ba, zan auri suhaima ne kawai saboda ……..

Mami ta katseshi tace” ya’isa boy don’t talk again, bakada isheshe lafiya ”

Yace” daddy promise me Ina warke zaka barni naje nemanta, da Allah daddy promise me that, daddy dun girma Allah kada kace aa ”

Tycoon ya sauke nannauyar ajiya zuciya yace” na Amince maka, ama da sharadin…

Ya zabura yace” daddy shara din daka gindayamin zanbi ”

Tycoon yace” akodayaushe in zaka fita, zaka Riga fita da masu tsaro lafiya, sama da ashiri, ka Amince?

Ya sukunyar da Kai kasa gsky baiji dadi wanan sharadin ba, ama ya zainyi, dole zai Amince sbd ya nemi sanyi idanuwanshi, yadaga Kai yace” na Amince dad”

Tycoon yasake cewa” kuma duk abunda ummi zata daura ka akai, Kar kamata musu”  Aliyu ya kalli mami yasake kallo daddy shi, fuska shi da alamu tambaya ama sai Bazar dun haushi ummi yake ji, ita tafara Kira Essha da aljana..

Murya ciki sanyi yace” na Amince”

Tycoon yace” yawwa good boy, yanzu Bara na Kira Hafiz su zo su taimaka ma , kayi wanka ka Rama salloli dake kanka ”

Yace” zaniya daddy”

Mami tace” a’a boy Karka yi musu, jiki ja ba karfi..

Baya Akira Hafiz, ya taimaka mishi yashiga dashi toilet din ya fito yaja mishi kofa, Baya Hafiz ya fita, ta Dade a tsaye, Essha yake tunawa da iri hali daya barta a ciki, waensu zirori haweye masu zafi suka zubo mishi , ya sa hannu a gashi kanshi ya cakudasu, ji yake kamar yasa ihu ko zaiji sauki yanda zuciyashi ke mishi, ya kunna shower ya Soma wanka, yana gama yayi na tsarki ya dora alwala yafito , Yana dafa bango da sauri ya taimakamishi , yasa jalabiya, Mami ta shimfidar mishi daddurma, ya hau ya tada sallah,  duka ya Rama salloli daake binshi, bayan ya idar yadade a zaune ya na roko Allah ya bayyana mishi matarshi, Yana haweye…

Mami ta dagashi tace” boy ya’isa hka, hakuri zakayi, tashi kasa wani abun a cikika, kasha magani, kaji?

” Mami bazaniya ba ” ya girgiza Kai

” A’a boy zaka’iya, daddy shi kasa baki mana”

Tycoon yayi ajiya zuciya yazo ya dafashi yace” haba gadagaa na, nasaka fa da jarumta da juriya, maiyasa bazakayi hakuriba, uhm aliyu, yihakuri please ko kadan ne kaci kaji boy, sai kasha magani… ya dauki fruit salad dake hannu Mami ya deba ya kaimishi baki .. Aliyu ya girgiza Kai Yana yamutsa fuska yasa hannu ya janye spoon din fruit suka zuba  yace” daddy kayi hakuri bazaiya ci komai ba, daddy zuciya na zugi takemin.. ya rike saitin zuciyarshi yacigaba”daddy inhar basa Essha idona ba, tona tabbatar muku bazantaba rayuwa ciki walwala ba, daddy rashita zai sa nasha wuya, nazama kullum aciki kunci”

Haydar ya tareshi yace” haba buddy yakake magana iri wana, so kake ka jefa su daddy da ka ka ciki tashi hankali, Essha Essha Essha bamusantaba, wani halaka bai taba hadaka da maisuna ba, tabbas sai yanzu na gasgata magana ummi, Essha Dina aljana ce ta aureka, ta shanye ma zuciya… Ya dafashi yace” look at me, Aliyu yakamata ka farka, mu yaketa, da adduo’i, addu’a makami mummini, kaga mata kala kala ma su kyau, aji dukiya , su so ka ka kisu, shine daga jiya zuwa yau zaka fada so haba buddy impossible……….

 

 

 

 

 

 

 

Comment &share

 

 

DOCTOR ESSHA

WRITING BY
J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
______________________

&

Aliyu ya sauke hannu haydar daga dafashi da yayi yace” haydar, Essha ba aljana bace mutum ce kamar kowa.  Tabbas da basan so ba, na kasa yarda da wata kalama Wai ita so tsakani ya mace da namiji, in aka cire na iyaye,  duk Mai soyaya Ina daukar shine kamar Mara aiki yi, gashi yanzu na fada tarko so. Wlh aka Essha zan iya sadaukar da komai nawa inhar zan ganta” ya rufe fuskashi da taffuka hannuwashi Yana kuka yace” basan a wani hali take ciki ba, tana matukar bukatar a tare da ita, Wai Maiyasa ma ku dauko ni ba tare da ita ba why? Yadaka tsawa ya Mike ya na buga kanshi a bango, da sauri haydar da Suleiman suka rikeshi duk yabasu tausayi. Ya kwace kanshi daga rukosu ya zo gaban tycoon Yana tangadi, tycoon da saurishi ya tallafoshi ya rugumeshi Yana rarrashi shi. Ya kalli mami da duk fuskata ya baci da hawaye, Abu mamaki ya ke Bata, Wai yau  Aliyu ne ke kuka, kuka ma aka mace. Taji murya Aliyu nacewa” Daddy maiyasa kuka barta acan,  why why ?

” Aliyu kuka ya’isa haka, tun jiya da safe ake ta nemanka lungu da sako ama ba inda bamu duba ba, karshe a gefe gate din gidasu ummi muga, bamusan waye ya ajekaba” Tycoon ya fada Yana share mishi hawaye.

Mami ta share hawaye tace” sai yanzu na Kara yarda da maganar ummi gaskiya ne, aljannace ta shafi boy”

Aliyu ya rike Kai da Karfi kamar zai cire Yana girgizawa yace” no Mami Essha mutum ce, ba aljana bace, Mami kubar kirata da aljana.. ya rike hannu daddyshi yace” daddy Kar yardadani, da Allah ka taimakeni wlh zuciya ta zata iya feshewa”

Tycoon yace” Aliyu take it easy mana, be strong, in har kanaci abinci, kana Sha maguguna ka, har ka warke toh zamu nementa  Kar kadamu”

“No daddy baza taba warkewa daga ciwo danakeji a zuciya ta ba inhar bagantaba” Aliyu ya fada kamar zai zauce.

” Hmmmmm” Mami ta ja dogo numfashi… Tace” Hafiz, haydar ku tatara mubar asibiti na mukoma gida Naga kamar Kara rudewa yakeyi”

“Toh mami” suka amsa..

Fawaz ya ya Hado mishi maguguna aka Kira babba likita suka bashi sallama, Aciki motar ya ki kulla kowa titi kawai yakebin da kallo, harsuka isa gida, suna isa parking lot , kafi angama parking yasa hannu ya bude motar ya fito, ya wuce side nashi Yana tangadi, fawaz da Suleiman da gudu suka bi bayashi, suka taimaka mishi ya karasa ciki.

Suna bude kofar parlour sukaci karo da manya manya malamai su takwas ga Al’qurani a gebasu, su zagaye parlour suna karatu, ummi da Ammi suna zaune akan couch gabasu kasko ne ga Kaya hayaki lodi Lodi a gabasu, Aliyu ya binsu da kallo al’ajabi, sukayi sallama, suka amsa.

Ummi tace” yawwa malamai ku dagata gashi ma ya dawo, Suleiman ku kawoshi tana ya zauna a tsakiyar su”

Aliyu ya Bata fuska Yana hararata yace” Ammi ki gayamata ba’abunda zanyi”

Tycoon da Mami da shigowar su kenan yace” kamata sharadin da mukayi da Kai a asibiti ko?

Yace” Daddy wlh mutum ce, ku fahimce ni”

” Ssshh bansaji komai kayi yadan tace, je ka zauna”

Ya nufosu jiki a sanyaye ya zauna a tsakiyar malamai.

Fawaz ya kalli Ammi yace” Ammi abanshi wani, Abu yasa acikishi yasha magani Naga kamar za’a jima”

Ummi tace”  eh ku kawomishi abinci yaci yasha magani kafi a fara”

Ya Galla mata harara yace” ni na koshi banzaiya ci komai ba”

Ammi tace” baka isa ba, Hafiz  jeka kawo magani, ni baza naje na hadomai wani abun da zai ci”

Yace” Ammi ni na koshi banzaiya ci komai ba”

Ta harareshi tace” mun shiru, banasan nakara ji murya ka ana, abinci sai ka ci shi, sana afara” tayi hanya kitchen dake side din,  sharp sharp ta hada mishi pototo with kidney sauce, da coffee, tasa mutumishi ne. Ta fito ta jera a dinning table, takira su fawaz, zu zo suyi breakfast tasan tun jiya rabuwasu da abinci ga idanusu yanuna, baya su zauna tayi serving nasu,  ta debo na Aliyu ta dire mishi agabashi ya kauda fuska, ta tsuguna agabashi tace” Aliyu Allah ka ci abinci na, ko na sabba ma”

Ya marairace murya yace” Allah Ammi bazan iya ci komai ba”

Ummi tace” iyye ku shagwaba Wana Kato da yawa, kamar shi haka ace ana wani lalashi shi, irishi a kauye su aje hudu biyar, ku gashi ku sagarta dashi, sai abunda yafada, irishi tsumagiya (bulala )za ku neman ku chala mishi, ama ku……..

Mami ta katse ta Tace” yihakuri ummi, yaro ne, Yana bukata lalashi”

Ummi tace” iyye Wana kato ne, yaro, Mai aure wata gobe”

Aliyu ya hada fuska tam jiyake kamar ya wulata a waje.

Ammi ta zauna daf dashi ta rike mishi haiba tayi maganar kasa kasa Wanda daga ita sai shi sukeji tace” haba mana dan lalle Mami da daddyshi, yihakuri kaci wani abun ko, ummi kishi take shiyasa, inshallah zakaga ta, ama fa sai kaci abinci” yayi murmushi Wanda har dimples nashi suka lotse gabadaya.. Tycoon ya zuba musu Ido Yana kallo su gwani sha’awa uwa da Dan kenan, rabuwashi dagani murmushi Aliyu tun shekara jiya ama gashi Ammishi, ko minti bai bugaba, tasashi murmushi..

Aliyu yace”Allah Ammi” ta gyada mishi Kai… Ai da sauri ya dauki coffee, ya shanye tas ya aje cup, tayi dashi yaci abinci, yakici ta hakura ta bashi magani, sanan aka fara ruqiya, bin malamai yake da kallo, suna qira’a ya na ratsashi, yanaji wani sanyi aranshi,( Aya Allah rahma), tun Yana bin har bacci ya bige dashi agun.

Ummi tasa kabara tace” ai sutafi shikena sauki yazo.. Tycoon dakashi ya daukeshi ya haura dashi dakishi har ka gado, ya gyara  Mai kwanciya, Yana fata Allah yasa komai yazo karshe.

 

*************************

Suhaima tuki take Rai a bace, speed tasa ma motar tana gudu Kamar zata tashi a sama, sai dai a kauce mata a hanya badai ita ta masa ba, har ta karasa gida, wani mahaukaci horn take dannawa kamar zata ballashi, Kara ya cika ko’ina . Baba maigadi har yafara bacci, Yana ji Kara horn a firgice ya farka, ya fara Bari dun yasa Mai horn din dako Alhaji ma baya haka, da sauri ya Mike don yaje ya bude mata gate, suka ci karo a hanya har ta shigo, tabar motar a waje, suhaima ta dauki hannu ta zuba ma tsoho na lafiyayu Marika har biyu, ta hankadashi da kafa, Allah sarki tsoho na zaiyi jika da ita.tana ya mutsa fuska tace” Kai tsoho na koreka a aiki”

Ya durkusa Yana kuka yace” da Allah hajiya ki tausayamin, wanane kadai hanya samu ci na da iyalaina, ki taimakeni” Yan aiki gida duk suka zuba musu idon tsoho yabasu tausayi, suhaima takama hanya. Baba maigadi yabin ta Yana kuka yace” hajiya inshallah bara na Kara kuskureba, ki ceci rayuwa na” ya tsuguna a kasa Yana rokota.

Ta juya ta dakamishi tsawa Rai a bace tace” Kai talaka banza, talaka wofi, bakasan aiki ka ba, sbd haka ka bacemin dagani , Kar na huce fushi na akanka, na koreka na koreka” ta Kara hankadashi da kafa, ta wurga ma wani Ma’akaci car key nata da sauri ya cafke ta wuce ciki. Baba maigadi durkushe yake Yana ta rusa kuka, ya Mike yashiga daki tatara kayashi yabar gida ya na kuka.

Suhaima na shiga ciki Rai a bace, feenat zaune Tana latsa waya, taji shigowarta ta Mike da fara’a tace” ke Wai Ina kika shigane, ki dawo Rai a bace, to nvm, tun dama accessories Dana muna order ne a Jumia nazo na nunamiki , koyayi” ta Mika mata waya , suhaima na amsa ta buga waya a bango, ya bada  Kara Tass, ta daka  tsawa dayasa feenat ta firgita tace” banza inanana Ina fama da zuciya ta, Ina fama da Aliyu ya Soni, ama ke ta accessories kike, Yana na can wata yake Kira bani ba, wata yakeson daban, baimasan Dani a lissafishi ba” ta dauki glass cup dake gaban feenat ta hadashi da center table dake tsakiyar parlour, ta fisge dogo  home theater, takama duka babba plasma da aka kawatar da parlour dashi. Feenat zata riketa ta daga mata hannu tace” hey u stupid don’t touch me, soyayar Aliyu zai kasheni” ta cigaba da rutsa Kaya Mai amfani dake parlour, yan aiki da feenat Dan suyi yukiri riketa sai tamusu rauni, duk taji musu Rauni a jiki, Bata sadudaba sanda ta ta tabbatar ta runguza komai Mai amfani dake parlour, ta durkusa a kasa ta fashe da kuka , duk ta hargizai, ta dago Kai ta nuna kata tace” ni Aliyu zai cimi mutuci yace bai sona wata yakeson, ni ” ta Kara fashe da kuka,

Feenat a tsorace tazo gefeta, tana dar dar, tana tsoro Kar tasake hi mata wani Rauni ta dafata tace” haba mana nawa, maiyesan kike haka, Aliyu fa naki ne ke kadai, ba wata sai ke, ki daina fada kalma baya sonki bai….  Bata barta   ta karasa ta dago da idanuta da suka rine ta katse ta dacewa”wlh, wlh talahi , sai na sa Aliyu ya Soni, Dan doleshi, ko da kuwa duniya zata tsaneni sai nasa yasoni , ko ta hali ka’ka, Kuma na ratse da Allah zan iya kisa akan Aliyu ” tayi murmushi muguta tacigaba” wlh feenat koda kuwa kece, zan kasheki, har lahira , duk Wanda na kashe na kashe banza”

Feenat ta tsorata da kalamanta tayi murmushi kamar ansa ta dole tace” haba nawa, Mai zai kaini, ai Aliyu naki ne, ke kadai , ki kwantar da hankali” Tana rufe baki hajiya binta ta shigo, wata Mai aikisu na janye mata da trolley,  ta tsaya kallo yanda parlour ya hargizai, duk anfasa komai , takai dubata ga su suhaima dake zaune ciki fasasu glass, ga ya aiki su yi cirko cirko, suna jira hukuci su San dole abunda zai biyo baya kenan.

Hajiya binta ta wangale baki tace” what babyna Mai zagani haka? Waya Bata Miki Rai? Ta nufota zata tabata,

suhaima ta Mike ta buga  mata tsawa tace” Kar kitabani , baki Sona ”

Hajiya binta tace” haba babyna, Mai nayi Kuma? Yihakuri zoki gayamin maiyasa maiki? Kodai kina fushi akan nayi tafiya basanar Miki ba?

Tace” Ina ruwana da tafiyaki” cike da matsifa tace” mummy sau nawa Kisha gayamin na kwantar da hankali na,Aliyu zai Soni, maganar ki duk yatafi a iska, bai Sona ko kada, wata mayake Kira daban a matsayi matashi, Kuma wlh mummy ko waye sai na rabashi da ita, sai nasa ta daina numfashi a doro kasa, dun su Raina mi hankali , Wai ita ba mutum bace”

Hajiya binta tasa wani uban shewa tace”  dat is my baby, zo ki ji, maganar da na Miki akan Aliyu bai tafi a iska ba, dun ya kusa tabata, Aliyu sai dai yaji Mai sunashi na zance soyaya da wata ama badai Shiba, har abada abada kuwa” ta kada Ido iri na goggu mata tacigaba”  baby na ,yanzu daga nijer nake, kuma sbd ke naje, naje guri babba malami, sunashi malami kan dutse ama afi sani shi da Aiki da cikawa. Baby na bukatiki sukusa cika, taja a jiki tace”zo muje daki, ba yarda da waena masu Ido kamar munzuru ba” ta nuna yan aiki da sauri suka sukarya da Kai kasa  tace” ku tabbatar ku gyara parlour na, tsaf darling na zai dawo yau, zan sa akawo sababi Kaya ku jera , waena Basu da amfani Kuma, ta kalli suhaima tace” baby badai ki sake hali naki ba ko?

Ciki da gatse tace” Mai nayi kuma?

Hajiya binta tace” baby na dawo, driver na ta horn babu Wanda yazo ya bude gate, sai jamilu driver yazo ya bude, Mai ki ma baba maigadi?

Tace” mummy na koreshi , Kuma basan kikara cewa komai akai, kawai ni munkarasa ki gayamin abunda yakamata naji” ta fda cike da Rashi kunya…

Hajiya binta ko ya yadamaita tayi murmushi tace” toh baby na, naji Allah ya huce zuciyarki, muje”

Suna isowa dki feenat da suhaima suka zauna a baki gado, hajiya binta ta nufi mirror tasa hannu ta cire sarka gold din dake wuyata.

Suhaima tace” mummy ke fa mukeji ra”

Tace” Kai baby matsala dakai Rashi hakuri” ta dauki baki handbag nata baki ta zazage musu agbsu da wani gora cike yake da madara shanu, suhaima sai bin kaya take da kallo tana yamutsa fuska..

Feenat tace” mummy what is dis ? Ta nuna Kaya

Hajiya binta tayi dariya , ta dauki kuli dayayi kamar tozali tana juyashi a hannuta tayi wani shu’ummi murmushi tace” wanan sunashi MANTA MASOYI”

Suhaima da feenat suka hada baki ” MANTA MASOYI Kuma?

Hajiya binta ta sake saki wani shu’ummi murmushi tace” tabbas ku fada dai dai, sunashi kenan, ba karami kunne nakshe akn wanan magani na ba, nakashe sama da 2.5million akan wanan”

Suhaima ta karbi tozali tana kara kalloshi da kyau tace ” mummy toh maiye amfani shi?

” Hhhhh, baby Wana dakike gani shi zai sa Aliyu ya Manta da masoyiyarsa, ya Kuma tsuduma ciki kogi sonki

 

DOCTOR ESSHA

WRITING BY
J Hajara

MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION

Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.
https://www.facebook.com/107980946102? referrer= whatsa
_________________________

 

&

Hajiya binta ta sake dariya shakiyi ci tace” baby inhar kikasa wana,toh Aliyu zai Miki son da ke ma bara kima kanki ba,ita Kuma masoyiyar tashi, ko da suyi nisa a son, su Kai Layla da majnu ne, toh ya manta ta kenan na har abada, ama fa yace duk Rana da sukayi Ido biyu da masoyiyar, asiri zai washe, zai dawo hayacishi”

Suhaima ta tsume fuska zatayi magana, hajiya binta ta katse tana murmushi tace” baby nasan Mai za ki fada, ki kwantar da hankali ki, nasa boko ya kadata tayi nisa, bara su Kara haduwa ba”

Suhaima tayi ihu murna ta rugume hajiya binta tace” gaskiya mummy na ki na so na, ki ceci rayuwa na, masoyi da na ke so zai so ni, mummy ko yanzu ma zan sa na koma asibiti ya gani, wow zaga soyaya” tayi fari da Ido.

Hajiya binta tace” Kai babyna, sauri Mai kike, ai yanzu Aliyu a hannumu yake, sai yanda muka juyashi, boko yace ba yanzu Zaki Sa ba, sai Rana da aka ranar aureku zakisa, zakiga aiki da cikawa, dun na trusting boko”

Feenat tace” ama mummy ki ce sai Rana dauri aure, what if tasa wani daban yayi tozali da ita fa?

” Haba yanmata, ya Ina baku Kuna roko, wanan tozali Mai suna MANTA MASOYI saboda Aliyu kadai akayi shi, da sunashi da nata aka hada magani, ku ga kenan akan Aliyu ne kadai zaiyi aiki, ku chill mana ” hajiya binta ta fada Tana kade musu Ido daya.

Suhaima tasa dariya tace” Bani mu kashe mummy na” hajiya binta ta daga hannu suka tafa taff..

” Wanan kuma” ta nuna gora tace” baby na Wana Madara da kike gani, magani ne shima, Madara ne da surki magani Zaki tatse shi da pant dinki”

Suhaima cike da mamaki tace” what!!! Mummy da pant  fa kikace?

” Eh” ta Bata amsa ta cigaba” in kika tatse da pant naki, baby na da sharadi fa, pant din daki ke amfani dashi ba sabo ba, Wanda kikesawa, if possible ma ki tatse shi da Wanda ke jiki ki”

Suhaima ta Bata fuska tana bin hajiya binta da kallo tana kara yatsine fuska..
Hajiya binta Bata kulataba tacigaba” ki na tatsewa za’a sa a fridge, a preserving nashi har sai ranar aureku, baya yayi tozali da ke, toh Zaki bashi Wana madara yasha, Yana Sha, shikena ki kulle mishi zuciya da soyayarki ba wata baya ke”

Suhaima tace” mummy ba wani hanya ne daban dole ne, sai na yi amfani da pant dina? Ni dai gaskiya bazan iya ba” ta fada ta yatsine fuska kamr taga kashi..

Feenat tace” haba nawa, Wana ai karami aikinne, so ki ke ki rasa Aliyu, inhar kina sonshi dole nefa kiyi yanda boka na fa kibi Sharadi boka”

 

” Yawwa fada ma ta dai yariya kirki” hajiya binta ta fada Tana kada Kai.

Suhaima tayi shiru for a moment, can tace”  mummy duk abunda zai sa Aliyu ya soni, zanyishi”

Hajiya binta Tace” yawa Yar gari”

Suhaima ta Soma haweye.feenat ta dafata tace maiyefaru kuma?

Ta rage murya tace” mummy jiya Jace ya kira ni, haryanzu dai akan magana zubar mishi da ciki danayi”

Hajiya binta ta fashe da wani dariya mugunta tace” Jace , Jace hhhhh Wana karami kwaro, shima tun jiya nasa boka ya mantar da shi komai inhar aka ki ne, kai yanzu haka in aka tambeyeshi waye suhaima zaice baisantaba, balle ma wani magana ciki mtchewew a zubar din”

Suhaima ta rugume hajiya binta Tace” shiyasa nake kara sonki mummy”

Hajiya binta tayi murmushi tace” Kar ki damu wanan angama dashi, Jace din banza”

(Wanene Jace, Jace Steve dan kasar amurka ne, course mate din suhaima, school ya hadasu , har suka kula soyaya Mai karfi a tsakani su, ba tsiya da ba sa aikatawa, tare ma suke kwana. Har sau uku suhaima na ciki tana zubarwa , bada sani Jace ba, ana hudu ne asiri ta ya tonu, lokaci Kuma daddy ta ya dawo  da’ita kasar Russian ta karasa  karatu ta, baya ta koma Russian ta ga Aliyu , ta Soma sonshi, ta Manta batun Jace, kuma lokaci da Jace yaji cewa ta taba  zubar mishi ciki har four times, shine yasa ta a gaba, yace mata kotu ne zai rabasu, tsora haka ne yasa ta dawo Nigeria , dun tasa hali Jace bai da mutunci tabbas zai iya. Babba dalili da ya ta na dawowa Nigeria kenan ta buya, sai aura na da zantayi, uwar take daure mata gindi duk wani shuumaci, gashi yanzu su shafar da Jace.)

” Toh mummy ya ake tatsa? Suhaima ta tambaya.

Hajiya binta ta Mike ta dauko fari kyalle da ruwa da cup, ta nuna mata yanda zatayi..

” Yawwa mummy zan’ iya” ta fada Tana murmushi , ta dauki goro Madara hajiya binta ta Mika mata wani Dan karami bowl tace” kije daki ki kiyi baby na Kar wani ya ganki, sai ki kawo min nasa a fridge, Kar kiba wata tayi Miki fa da nasaki”

Tace” okay mummy” ta fice daga daki zuwa nata, ta zuwa ta dire gora akan gado ta na yatsine yatsine fuska tace” Allah ya kiyaye na tatse Madara na da pant din dake jiki na, sabo zan duba, ko ni Ina kyakyamin jikina balle abunda hubby ne zai Sha inaa” ta nufi wardrobe ta bude, tana duba sayaya da tayi jiya, im Bata mantaba ta sayi inner wears na Gucci masu shege tsada, ta fito da sabo pant na Gucci  Mai tambari  din Gucci, fari Kal, dal yake, ta aje akan Dan karami table dake daki, ta dauko gora  Madara da bowl ta aje ta fara tatsa tana ya mutsa fuska, ba abunda yaiya sai shirme, Tana Gama  ta cilla da pant din,ta kaima hajiya binta Madara ta bude fridge tasa,  harda samata albarka.

ESSHA
*************************
Anty zainab ta zuba mata abinci ta zauna agaba ta, Essha ta kaudai Kai , dai*2 doctor da nurse din dake kula da ita sun ka shigo, da magaguna da allurai. Dr Abbas tun jiya daya ma Daddy mgn bai Kara lekasu ba, kuma Yana ciki asibiti.

Juyi duniya na Essha taci abinci Taki ci komai, sanda aka Sha daga sanan ta yarda mummy ta kada mata hot tea, tana Sha tana hawaye, rabi cup Tasha tace ta koshi, doctor ya mata allura , Tasha magani, tana gama sha, daddy ta ya shigo shi da daddy karami, Yana rike da wayata a hannu ya Mika mata, ta amsa, haryanzu batabar kuka ba, tayi fayau kamar ba’ itaba, tana haweye ta bude waya, missed calls din Khalid da bestie ne ba’adadi , harda hunaisat,  tana kan dubawa Kira Khalid nasake shigowa bata amsaba takara feshewa da sabon kuka, jikita har Yana karkawa, har Kira ya tsinke Bata daukaba, mummy ta matso ta rugume ta tana hawaye , daki tsit kuka Essha ne kawai ke tashi.

Daddy karami yayi gyara murya yace” Essha hakuy zakiyi kibar yawa kuka na, kuka na wani ciwo zai Kara Miki, karki sama kanki damuwa, Essha ke Kuma iri Taki kadaran kenan, haka Allah ya tsara mana, nasan Allah baya taba yi abun babu dalili,  duk abunda kaga Allah yayi akwai dalili dayasa shi, haka Allah baya dorawa bawashi abunda bazai iya ba, ki rugumi kadaraki da hannu bibibbiyu watara na sai labari”

Ciki sanyi da tausayawa hajiya tace” toh maganar aure da ke kanta fa, tun da ba miji kusa, Kuma ba’asan asalishi ba, balle a Nemo shi”

Daddy yace” Kar kudamu zamu tambeyi malamai akai”

 

Baya Kwana biyu, an sallamorta daga asibiti, dun ta da warware, Essha duk ta chanza, Bata da wani aikiyi sai kuka, gaba daya ta chanza, gashi yanzu daddy ta ko na da can ya Hana ta fita, ya chanza mata layi wayata cewa yanzu ita matar aure ce, abun na bala’in Kona mata Rai , mummy ne kullum Mai lallashi..Sam yanzu Bata da wuya kuka, mummy mamaki take a kullum , Essha ce ta dawo haka, yariya da batasan Mai ye damuwa ba, ko yaushe murmushi shi ne shimfide akan fuskar ta, yanzu Sam Bata da wuya kuka.

Yau ma zaune take a parlor, ita da siblings na ta suna kallo , mufeedat ne a cinyata, ta zuba uban tagumi tayi zurfi a tunani. Sumaiya(bestie) ta shigo da sallama ta, su amir suka amsa, ta nemi guri a gefe Essha ta zauna, ta kalleta shiru, Essha ba ta masa ta shigo ba sbd tayi nisa, Bestie ta Mike ta zungure ta a kai,  a zabure ta juyo tana kallo bestie idon ta har ya fara Tara ruwa, ta marairace fuska kamar zatayi kuka, zatayi magana bestie ta rufe mata baki tace” zo muje” ta sauke mufeedat, sukayi hanya daki Essha ,  suna karasowa..

Bestie ta kalleta  tace” Wai Essha what’s wrong with you? Ki canza gabadaya, tun Ranar da daddy na yagayamin kina asibiti na shiga tashi hankali na tambeyeshi ko accident kukayi bai bani amsaba, Kuma ya Hana ni fita, Kuma Ina trying number ki a kashe”

Essha ta share hawaye da ya zuba mata ta zauna a baki gado , Tana share hawaye wani na sake zubowa, tanason tayi magana ama kuka yaci karfita da Kuma yada kirji kemata yasa baza tai iya ba, kawai ta rugume bestie ta fashe da kuka.. Mai tsuma Rai.

“Subhanallahi, Essha Wai maike damuki ne” bestie ta fada Tana share mata hawaye,

” Bestie ki fada min mana daga wuri Khalid fa nake Yana ciki tashi hankali, Yana Kira ki, number ki a kashe, Kuma yace min first day da ku ka dawo ya Kira ba ki dauka ba maiyasa?

Essha ta kalleta shiru tana hawaye, itama bestie kuka takeyi.

Tace” please bestie kimin magana ko zaji sanyi, Khalid na Bliss park Yana jiramu , na mishi alkawari zan mu zo tare,  tashi muje kibar kuka na, nasan bai wuce menstrual pain, shi ne yake bata min bestie, don’t worry zai wuce tashi muje, Kar kice a’a please,  khalid na ciki tashi hankali”

Essha zuciya ta zafi yake mata, na ji hali da masoyita ke ciki, gashi ba hali zuwa gareshi ta rike bestie murya kuka tace” bestie kiyi hakuri, ki je kawai, ki bashi hakuri, ki ce mishi ya cire ni a zuciyarsa, ya yafe min in da rabon zamu sake haduwa……

“What!! Kisa Mai kike fada kuwa, Anya ma kina ciki hayaciki, Khalid ne fa  ” bestie ta katse ta fada a fusace… Ta sausauta murya tace” wlh bazai iya  wa ba, Essha ki tausaya minshi, yace fa bazai taba iya wata ya mace ba , Im bakeba, Kar kimishi haka bestie, ki tausaya ma rayuwa  bawa Allah na, Wai Maiyasa ma ki ka canza haka? Wani abun ne ya hadaku? Tunda ki ka dawo ki  ka canza why?

Essha bataiya Bata amsa ba ta girgiza Kai Tana kuka sosai..
Bestie tace” toh gayamin reason dayasa bake dauka kirashi, har kina cewa ya cireki a zuciya sa ki gayamin” tasa kuka

Essha tasa hannu a baki ta na girgiza Kai, haweye ne kawai ke ambaliya a fuskata, sumaiya ma kuka take.. dai lokaci waya bestie ya Soma Kara, kira ne , ta duba taga Khalid ne da sauri ta pick ta sa a loudspeaker tace” Essha fa Wai bazata zo ba” ta fada har muryata na rawa….

 

 

More comment, more typing

 

 

 

 

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements