DOCTOR ESHA Page 31 to 40 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / DOCTOR ESHA Page 31 to 40

DOCTOR ESHA Page 31 to 40

DOCTOR ESHA Page 31 to 40

Khalid yace” love mainamiki? Wani laifi na aikata Miki da kikeso ki hukutani haka? Baby love please talk to me, please forgive me Ina azabtuwa”
Essha naji muryashi ta rutse Idon ta na fitar da hawaye masu zafi, ita kadai tasan yadn takeji a zuciya ta, ta kalli bestie murya a hankali tace” ki ce mishi ya manta dani
Bestie ni……. Ta kasa karasawa kamar an rufe mata baki ta fashe da kuka  tace” kawai ki ce mishi ya fita daga rayuwa na, ya daina sona”
Khalid daji haka ya sarke da wani mugu tari, Basu Kara ji komai ba, sai hayaniya mutani, duk hankali su ya tashi,  bestie na kuka tace”  ki gani ko, kigani Zaki kashe yaro mutani a banza, ki manta alkawari daku ka ma juna ne, Essha Bata ba zato zakiyi haka na, ni zanje na sameshi” ta fice rai a bace.
Essha ta kife a gado tana kuka, bestie na fita mummy ta shigo, duk ta ji hirasu, ta dagata ta rugume Tana lalashita, sanda taga ta bar kuka tace” Essha ki cika Yar halak, ki na bi duk sharadi da daddy ki ya daura Miki, baki bi so zuciya ba,am proud of you, a kullum ki kasace Mai tawakali, in khalid mijiki ne, in Allah yaso Zaki aureshi, komai mai wucewa ne, watarana sai lbr, nasiha sosai ta mata Wanda ya rasata, yasa ta Kara saduda ta mayar ma Allah lamarita..
Bestie lkc dai Mai napep ya sauke ta a Bliss park, tun zurutu mutani tagani su taru a gefe daya, sai baza Ido take ko zata ga Khalid, banshi, wayashi take ta trying ama bai dauka ba, kawai ta yake taje inda aka taru ko Allah yasa tagashi, tana zuwa ta samu ta kusa ciki,  Tana shiga khalid tagani kwance numfashi sama sama yake fita, tana ganishi tasa ihu tana a taimaka mata,ba Wanda ya kulata karashe ma watsewa akariga yi daya baya daya, tana kuka ta rasa yanda zatayi , ta fara neman wayashi, ama ba waya, batasaniba, tun lkc da suke waya ya sarke da tari, waya ya fadi,daga ciki   masu zuwa kallo ne, wani ya dauke waya.
Khalid numfashi Dakar ya ke fita ga tari ga amai jini, da sauri ta dauki wayata ta Kira Bashir, ta gayamishi hali da Khalid ke ciki, da address din guri,  bada jimawa ba sai gasu su karaso, suka Parker motar a gabasu, su uku suka zo, da Bashir sai wani saurayi Mai Kama da Khalid din, ama Khalid ya fishi girma, sai mahaifi Khalid.cike da matsifa baba Khalid ya fito Yana babbali matsifa ya nufo khalid yace” wlh ko zaka mutu, bara ka auri yariya na ba, yariya da aka gayamin tagama talla kanta a titi,  shine kake neman kashe kashe ka ka akanta, toh wlh ba ka isaba, Kai ko Mai halaka da yariya bara na bar wani nawa ya aura ba, labari tas yazo kunne na, har hanata fita akayi, sbd abun kunya da ta aikata( ohh ni ya su🤦 mutani mutani, hmmm)..
 Toh bakai bar Yar iska yariya na  har abada nagayama kenan”
Bestie dake zungune ta kasa gasgata abunda kunnuwata suka jiyo mata, bestie ta ne ake mata Wana shairi , Wana abun da mamaki yake, abun daurai Kai ma Bashir(saurayita) tunda yazo guri yashareta Yana wani kauda fuska kamar bashi ba, bai ko kulataba, tun shekarajiya ta lura da chanzawashi, ga Kuma abunda baba khalid ke fada ya matukar girgiza ta, ta Soma tambaya kanta maiyasa yake aibanta bestie na haka? Yana kirata da Yar iska baya ba halita bane, toh maiyasa ma bestie ta canza? Tsikaro murya baba Khalid tayi Yana cewa” sa shi a motar , Kai Kuma Bashir na ji ance kana nema kawata ko? Toh ku rabu tun da wuri,kafi su shafa ma Kashi kaza”
Bashir ya dagaa hannu Alama baruwashi yace” ai daddy na dadane da cireta,sai dai ta nemi wani a gaba ba niba” ya baka ma sumaiya harara
Bestie ta sandare a guri daya ta kasa gasgata abunda takeji, Kuma take gani da idonta, tana hawaye tayi sauri goge idonta da Karfi ko za ta farka Killa mafarki takeyi , tana budewa dsame tagani , ta fashe da sabo kuka ta nufi guri motar ta rike Bashir tace” sweetheart ni ne fa, Wai maike faruwa ne? Kugayamin, wlh Essha na ba yar iska bace”
Bashir ya fisge rigashi da ta rike ya nuna ta da yatsa yace” kul Kar kisake kirana sweetheart, asiri ku ya tonu, a rayuwa na na tsani mace fasika, Kar ki sake nunawa ki sani , shima Khalid giyar so ne, ke dibarsa ba da daidawabs zai farfado, Allah ya hada kowa da rabonshi” ya shiga motar.
Sumy sandare wa tayi a guri ta saki baki da hanci ta na kallosu
Murya Khalid taji daker yake mgn taji yana cewa” sumaiya kiyi hakuri, ki ce ma Essha Kar ta Manta da alkawari da ke tsakanimu, baza taba daina sonta ba, sai Rana ……… Bata  Gama ji maizai fada ba Bashir ya ja motar ya bade ta da kura, suka fice daga park din.
Sumaiya tasa hannu akai tasa ihu kamar zarariya, yau Bashir sweetheart nata , shine ya barta, aka maganar da batasa dashi ba, kowa sai kallota akeyi a park din, zuciya yi yake kamar zai fashe, don tashi hankali, ta zube a kasa tayi kuka Mai isarta, sanan ta Mike Tana layi, yanzu haushi Essha ta ke ji, Taki gayama ta damuwata, ta tsaya shiru, tace kila gaskiya ne abunda baba khalid ya fada, Auzibillahi da sauri ta kori shaidan tace” I trust my bestie, bahaka take ba, ama zanyi fushi da’ita, bara Kara kulataba, har zaitazo gidamu taban hakuri, Bashir Allah na gani zai sakamin” ta share hawaye tace” i love you Essha , bestie Mai tauri kai, da zurfi ciki” ta fada Tana dariya tana kuka, tana tafiya tana magaganu har ta fita daga park , kowa kallo mahaukaciya akemata saboda yada tayi badau badau da kasa a jiki, Dakar ta samu Mai Nepep ya Kai ta gida , tana sallamarshi ta juyo ta kalli gate din gidasu Essha ta murguda baki tace” bestie nayi fushi dake, Kuma ko ki kirani bazan amsabs, har sai kizo gidamu kiban hakuri, gashi Bashir ya gujeni, wayyo Allah na” ta fashe da kuka abun tausayi ta bude gate ta shige “
*************************
Baya wata uku da faruwa haka, Aliyu ya canza gabadaya, yarage fara’a bakamar da ba, kullum bashi da Aiki sai na neman Essha, ba Rana da bai zuwa daji na, yasha zamashi, har TATARA ya je gari mallam Dagana waliyishi, Yan gari suka shaida mishi Bata mallam Dagana guri wata uku kenan dagashi har iyalashi ciki dare suka bar gari, a Rana yi yayi Kamar zaiyi hauka, sbd mallam Dagana ne only hope nashi gashi shima bashi, saura kwana uku bikishi, daddyshi ya tsanata mishi sai ya resume a office, baiyi musu ba , aka daura shi as director of Tycoon companies, Yana zuwa office ama fuskana a hade, duk ya fada, baya bacci kullum kwana yake sallah Allah ya bayanamishi Essha, bai son ci abinci sai Ammi tasashi a gaba, zaici ama baize wuci three spoon ba zai tashi yace ya koshi, Ammi duk tashiga damuwa hali da yaro na ke ciki, tayi fada har ta gaji, ta zuba ma saurauta Allah Ido, sai shirye shirye biki akeyi,, ama ango ko a kolashi,bikisu su hudu zasu ango ce,Aliyu , Idrees, haydar da Hafiz. Sai shirye shirye sukeyi ama Aliyu ko kulasu ma bayayi nema Essha yasa agaba birni da kauye na kd , ba’ ida baje nema ta ba, ama ba sa’a.
Ana gobe dauri aure, yadawo office a gajiya , fuskana ba walwala as usual, baya ya watsa ruwa , ya fito ya dauki waya ya Kira artist Mai zanen ya nasan ya zana mishi hoto Essha, zai Dora a media ko Allah yasa a yi dace, Kuma yanasa yariga kallota ko zaiji sanyi, bada jimawa ba dani liti yashigo yasanar mishi yayi bako,
Yace” ya jirani a garden Ina zuwa”
Dan liti ya amsa da” toh yallabai”
Dan liti Yama artist din iso zuwa wani beautiful and fresh garden na gida,  koina na guri nature ne, hata kujeru farare dake gurin sanda aka bisu da fresh flowers, gurin a zangaya yake, kasa gurin carpet grass ne, lafiyayu danwisu masu kyau suke yawo a gurin.
Aliyu ya Mike ya dauki wayashi da headphone kala kayashi, 3q ne da armless t-shirt light green ajikishi,ya hada fuska tam yanaji haushi kowa a gida, yanda ya ga anata hidima.
A kullum in ya rinse idon Essha yake gani, burishi a duniya shine ace yau ya wayi gari gashi ga Essha, headphone ya daura waka Aransh ft helena_ Broken angel yake sauraro, kullum sai yaji waka, Yana sauka a matakala waka na ratsashi yanaji kamar tare da Essha yake, hannu shi daya a aljihu Yana bin verse din waka a hankali”🎶🎶 am so  lonely broken angel, am so lonely listen to my heart, one and only broken angel come and save me before I fall apart🎶🎶” har ya sauka  daga stairs Idona a rufe, jishi kawai take a lovers and lonely mood,zai fita kenan yaji a zare headphone din, firgit ya juya da sauri ya bude idon dayasa aiki Ammi ne……..
Comment And share🥰🥰🙏🙏🙏 love you guys
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
     DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/10798094102? referrer=whatsa
_________________________
4️⃣3️⃣&4️⃣4️⃣
Yana juyawa yaga su haydar ne, tun a stairs na farko ya na saukowa suka shigo, suyi sallama baijiba , ya kure volume, idonshi a rufe, dukasu su zagayeshi, Suleiman ne ma ya cire headphones din,  suka zuba mishi Ido.
Fawaz ya yi ajiya zuciya yace” Buddy maiyasa kake haka? Duk ka canza, Wai agayama so hauka ne, come back senses, gobe ne fa daurin aureka, suhaima duk girma kanta, jiya tazo ta samai mu da kuka Wai baka kulata, u ignore her calls,  ka koma rayuwa kadaici da kunci akan yariya da bakasa mutum ce ko aljana ba…. Ya rage murya   yace” Buddy please kadawo kamar da, if this Essha mutum ce ko da jima ko ba dade, zata dawo gareka,  ka kwantar da hankali ka”
Haydar ya dafa Aliyu yace” Buddy, fawaz yay gaskiya, kaga duk amare suna kano, da tun safe mun wuce, dun yau akwai event a dare Kuma yakamata ka hallarci guri, gobe 10:00am ne fa za a daura, Ammi aciki damuwa take, maiyasa baza ka farata mata ba? Da Allah Don’t say No, kashirya mun wuce,  Kai mu ka zo dauka, munshirya flight 7:00pm za mu tashi, please Buddy”
Hafiz yasa baki yace” wlh buddy, duk tsanar da na ma suhaima jiya, San da na tausaya mata, ta na sonka, consider yourself in her shoe, kabar magana Essha Dina, ga luggage naka Ammi ta hadama, kaga ana daura aure gobe sai mu dawo, dubi a office yanda kasa workers a  gaba, haba, ka Manta da battun ta, Im ma aljana ce ta Dade da manta shafika”
Aliyu baicce uffan ba, ya juya ya fice yayi hanya garden, da saurisu suka bi bayashi, yana isa ya tarda artist din har ya gama shirya items na zane ready to work, artist na ganishi ya Mike ya gaisheshi cike da girmamawa, ya amsa, ya Sami guri ya zauna Yana ajiya numfashi, ya na dafa kirji, sanda ya natsu na Yan mintuna Sana ya Mike ya kalli artist din yace” are you ready? Artist din ya amsa da yes sir, su fawaz na tsaye suna kallo ikon Allah, Aliyu yana  lumshe Ido Essha ya gani, har wani murmushi ya sake, Ido a lumshe ya fara ma artist describing kamani Essha, her face, hair, lips, komai sanda ya zayyana ma artist, harda crying face nata tana haweye, har ya Kai Aya,  ya Kara rutse Ido Yana ajiya zuciya, kafi ya bude idon a hankali, Yana gama budewa idoshi ya sauka aka hoto Zane Essha, artist din na gefe Yana mishi murmushi, gaskiya artist din ya kware, don tamkar Essha ne aka daura, harda hawaye dake siyaya a gefe idota.
Aliyu ya tako a hankali Yana hawaye Yana murmushi ya karaso gaba zane, yasa hannu Yana zagaye hoto yace” yaushe zangaki naji sanyi, uhm please ki dawo gareni….. Yata zuba ma Zane Nan kalamai…  Haydar ne ya katseshi, gani kyau yariya dake ciki Zane is beyond their imagination, Aliyu da sauri yabar gurin, sai gashi yadawo hannushi rike da cheque da car key  sabuwa dal Mai tambari Lamborghini a ciki, ya Mika ma artist  cheque din yace” konawa ne ka rubuta nabaka” ya sake Mika mishi key din Lamborghini sabuwa dal.
 artist jiki na Bari murya na rawa na murna da mamaki yace” yallabai ayi haka? Aliyu ya karbi cheque din ya rubuta billions of naira da baisan adadi su ba, ya Mika mishi, artist sai murna kamar zai zube a kasa don godiya har da kukashi, yau ne happiest day na rayuwashi, yabar  gun da murna ko Kaya aiki bai kwasheba.
Suleiman yace” Buddy wace ce Wana dakayi kyauta billions of naira sbd ita? Badai aljana  na bace ko? Dun Wana kyauta ya wuce na mutum”
Aliyu yayi murmushi yake yace” Buddy Essha ce, zan iya bada dukiyana gabadaya ihar zan gata”
Hafiz da haydar su gama rudewa, Hafiz aranshi yace” in wana na hoto ne Essha ,toh tabbas ko wani iri hauka so mutum zai mata toh Ina bayashi”
Fawaz yace”  Buddy Essha ka kenan?  Ya gyada Kai, fawaz zaiyi mgn Aliyu ya daga mishi hannu ya dakata  yace”  tun baya haduwata da Essha, Bata ba natsuwa na baku labari haduwa mu ba, toh yau zan gayamuku, Essha da ku ke ta Kira aljana toh ba aljana bace, mutum ce kamar kowa, and she’s my wife….
Suleiman yace” dakata Buddy kana nufi ba aljana bace? Ur wife? Yaushe kuka hadu har aka daura muku aure bamusaniba? Duk ya jero tambaya a lkc daya..
Aliyu bai amsa ba, ya nufi guri board da akayi Zane yacire  Yana shafawa sanan yace” let’s have a sit, yau zanbaku lbr haduwa ta da Essha”
Baya su zauna duk suka zuba mishi ido, Aliyu ya fara Basu labari haduwashi da kungiya da hali dayashiga, the moment he fall in love with her, har aureshi da ita da aka hada , bai boye musu komai har yakai Aya. Their were shock, mamaki da rudewa ya hanasu furta ko da kalma daya, guri yayi tsit , Kara kuka dawisu Nan kawai ke tashi, sun fi minti na a haka, Suleiman ya kada Kai Yana sallati yace” lallai buddy kaga jarabawa, kana nufi kenan u had sexual intercourse with her?
Aliyu ya gyada Kai ya na haweye, haydar haweye sanda ya yi, ya sauke  ya Mike ya dafa Aliyu ya furza da iska baki yace” Buddy na matukar tausaya ma, maiyasa baka sanar da mu tun farko ba?  Aliyu bai bashi amsa ba ya zuba tagumi.
” Kace kaje  har TATARA ba malami? Fawaz ya jefa minshi tambaya   …. “Eh” Aliyu ya amsa..
Hafiz yace” ya tsorata ne Killa Kar yan kungiya su bi bayashi, when last ka koma daji ?
Aliyu ya amsa da ” tun last week, na tarda daji gabadaya a mayar dashi titi, Kuma nasa aiki daddy ne, don agayamai Ina zuwa daji”
“Aina za’aganta yanzu? Haydar ya tambaya..
“With the help of this za’a ganta inshallah” Hafiz yabashi amsa Yana nuna Zane Essha, ya dafa Aliyu da ya zuba tagumi yace” sai yanzu mu ka gane hali da kake ciki, we misunderstand you, kayafemana, we will stand by you mu taimakamaka har ka ganta inshallah, da Allah ka yafemana, we fail as friends” Aliyu ya janye hannushi ya Mike ya rugumeshi, saura ma suka rugumesu, fawaz har da kuka, Aliyu ya tabbing nashi yace”baku mu laifi ba, Rashi fahimtar juna ne shiyasa, ama ba komai, komai ya wuce” suka saki juna , fawaz yace” Buddy we promised you tare zamu nemonta Kuma zaka ganta, inshallah, duk suka Amince,suka shirya yanda za’a baza hoto Essha har Allah yasa aganta, baya su gama shirya plan nasu, su ka Mike..
“Buddy lokaci sallah yayi, 7:00pm yakusa,ya kalli time.. muna idar da sallah zamuwuce Kuma har da Kai” haydar yafada..
Aliyu ya Bata fuska yace” am not in the mood kawai kuje, da Allah in ku ga Ammi ko Mami kuce musu munatare, ni bazan jeba”
Fawaz yace” eyee ango  Essha karya kakeso muyi toh baka’isaba “
Yayi dariya yace” Allah am not in the mood for any partying tonight, I want to be alone”
” Hmmm kasa suhaima bara taji dadi ba ko” haydar ya fada
Aliyu ya daga kafada hali ko inkula ya fice a garden din rike da zane,suka binshi a baya,sai teasing nashi kawai suke Yana dariya…
ESSHA
*************************
Essha  ce zaune gaba mummy ta, sanye take da vex da  skinny jeans trouser ta yane kanta da white veil, ta canza ta murmure kamar ba itaba, yanzu hankali ta a kwance,  ko baki gate daddy ta ya Hana ta fita, gashi ta Kara ci sosai, Essha da da ko Rabin plate batayi yanzu sai ta cinye two plates a take, yanzu ma abinci take ci , hannu baka hannu kwarya, Kar ku zata wani abinci arziki a’a, zalla wake ne tayi mix da gari kwaki da zobo drinks a gefeta , tana ci har tana lumshe ido..
Mummy sai bin ta kawai takeyi da Ido ta na Nazari ta, ” ayya ba ciki Essha ke dauke dashi ba, tun last two months nake zargi haka ta fada aranta.( Last two months mummy har ta aiki pt strip, ta karbi fitsari Essha dun ta duba, da hankali ta bai kwanta ba tana son ta tabatar da zargi ta, baya ta aje Ptstrip a gefe toilet, kafi ya bada result, ta shiga kitchen ta duba girki, mufeedat ta shigo da scissors tana gani Ptstrip da yayakashi gunsir gunsir, gani hk ne yasa mummy ta fitar harka abun, tunda jikita bai wani nuna sign ba) mummy tayi ajiya zuciya , tana kallo Essha yada tacika gaba da baya , tace Allah yasa ba abun Dana ke zargi bane.. Essha na hada Kai  idota ya hadu da na mummy ta tura baki tace” Kai mummy tun dazun fa kike ta bi na da kallo” ta fada a shagwabe
Mummy tace” hmmm Essha ba komai”  Amir da Walid suka shigo..
” Mummy Wai yayshe daddy zai dawo ne? Amir ya tambayi mummy.
Walid yace” mummy sati daya kenan fa”
Mummy tace” yau zai dawo inshallah, ya na ma hanya”
Mufeedat tasa tsalle” ye daddy yau zai dawo”
Khairat tace” tafi can Mai bar na tsiya, mummy ta ja ta gefeta tace” zo zauna Kar su taba min ke”
Walid ya bi mufeedat da harara yace” Bari daddy ya dawo zaku biyani igiya PS4 na da ki ka tsinke”
Essha kam abinci ta takeci hankali kwance Bata kulasu ba, Amir ya leka plate ya ga Mai take ci, ya ga gari ne da wake, ya tabe baki ya janye plate din agabata yace” Allah sis kicika ci abinci kazata, Wana ai sai nayi amai”
Ta Mike ta kwace plate din tace” Ina ruwaka”
Yace” oho dai fake doctor kawai”  ta amsa da “eh din naji”
Walid sai dariya yake musu, khairat tace” sis Kuma yayi dadi ? Ta tambayeta tana yamutsa fuska
“Eh Mana ci ki ji” ta Deba ta Kai mata baki, tana samata da sauri tayi kitchen ta furza kamar zatayi amai..
Amir yace” Allah ya shi Kara Mai kwadayi”
“Sis Essha inji bestie Wai na gaisheki” Walid ya fada.
Essha na take ta bar ci abinci ta juya gun Walid tace” Allah Mai tace Kuma baya Wana ?
” Nothing ” ya Bata amsa..
Essha ta tsaya shiru ta kalli mummy murya tausayi tace” Da Allah mummy na je, please mummy ? Ta fada kamar zata yi kuka..
Mummy tace” a’a baruwana Essha, kibari daddy ki ya dawo, sai ki tambeyeshi”
“Uhm” ta Mike Tana buga kafa cike da shagwaba tace” uhm uhm mummy ki San bazai bar ni ba kina gani fa ko gate ya Hana ni lekawa, please mummy na”
“Aa Essha kiyi hakuri kinji” mummy ta fada murya lallashi
Essha ta tura baki tace”  mummy bestie fa,  fushi take da ni, Bata dauka kirana Wai sai na je gidasu, mummy almost three months ke nafa “
Mummy tace” hmmm Essha, in yadawo zsn Taya ki roko shi sai kije, yanzu shiga dakina aka mirror Zaki ga humra a kwalba, big mum ce ta aiko Miki dashi”
Tasa tsalle tace” wow mummy inaso humra” da gudu ta nufi daki ta shiga ta dauko, ta fito parlor tana bude murfi humra kamshi ya buga mata Kai na take ta Soma ji tashi zuciya taji tana gani jiri, kafi ace kwabo ta shiga kwararo amai, jiki tashi hankali mummy da saura suka Karasa gareta, dai dai lokaci daddysu ya shigo, Essha duk ta Bata guri da amai ba, mummy ta shiga shafa baya ta, daddy ya Karass gurisu da sauri ba su sa ma da shigowar shi ba , sanda suka ji muryashi yace,” maiyesameta? Ya tambaya babu Wanda ya bashi amsa, sai da ta gama amai, mummy ta Kira kharima ta gyara guri, da kanta Tak aita bathroom ta gyara ta, ta fito ta canza kaya, nanan ta ja blanket ta nanede a ciki ta na rawa sanyi da kerma, mummy na gani haka ta fice da sauri ta Kira daddy ya biyota, ta haye gado ta tallafo Essha.. daddy ya kalli mummy yace,” tun dama Bata da lafiya ne?
Mummy tace” kawai muje asibiti akawai abun da nake zargi ” ta fada kamar zatayi kuka..
Yacs,” okay jeki shirya ki fito mu kaita asibiti” mummy ta fice,  sai gata ta dawo sanye da hijab ta bude wardrobe din Essha ta dauko mata hijab ta sa, ta dagata tace” Essha Zaki iya takawa ?
Tace ” eh mummy ” ta fada har jiki ta na kerma
Suka fito a back sit t a zauna , daddy da mummy suna gaba , suna karasawa asibiti office din Dr Abbas Daddy yayi da ita, Daddy ya Mika mishi hannu ba yabo ba fallasa suka ya amsa..
Mummy tace” Da Allah ka duba ta”  Dr Abbas ya Soma dubata dakashi, ta fice zuwa lab,  baya waesu minti na, sakamako da ya gani ne yayi matsifa daga mishi hankali , fuska a hade ya fito daga ya bar lab din, yana shiga mummy ta Mike da sauri tare da tambaya maike damuta ? Bai amsa ba ya Mika ma daddy paper, daddy yashi dubawa , so roro daddy yayi batare da ya iya furta koda kalma daya ba , gani tashi hankali ya bayana baro baro a fuskar Daddy, tasa hannu ta amshi paper ciki tashi hankali tace” what!!! Kamar ciki na ke gani ko?  Ta fada a rude..” ciki har na wata uku ”  mummy ta sa kuka Tana wayyo Allah na munshiga uku” da sauri daddy ya rufe mata baki ….
More comment 😊more typing ❤️❤️❤️
Love you guys 🥰🥰🥰
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
      DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, BUrin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/10798094102? referrer=whatsa
__________________________
 4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣
Yace” ki daina fada haka, sai kace ba musulma ba”
 ya juya kalloshi ga Essha da tagama rudewa tace”  Daddy who is pregnant ? Me ? When?  Batakarasa tamboyoyi na ta ba ta fashe da kuka.
Ya zagaya gefeta ya dafata yace” Essha calm down, Kar kiyi kuka, zo muje gida ” ya mikar da ita , za su fice,
Dr  Abbas ya dakatar dasu  fuska na a hade yace” wait, tunda asirika ya tonu, har ya nuna yarka na da ciki, toh ba ta ba yanta , Kar ta Sha fa mata Kashi kaza, ko a waya ne ta Kira sumaiya  ta daga sai na tsine mata , sumaiya ma za ja mata kunne, kuje can da tsiyaku, banasa na Kara gani sumaiya da Essha”
Daddy ya juya ya kalleshi ya kada Kai Yana murmushi yace” nagode, bayi mamaki ba, inshallah Essha kam ta rabu da sumaiya kenan har abada, bisalam na barka lfy” ya ja hannu Essha da sai tsala ihu take, mummy na biye da su, Essha zafi rabuwa da bestie ne yasata kuka bama ciki ba, suna shiga motar daddy ya fara lallashi ta ya na Bata baki, ya hada har da mummy yace” Wana ciki fa ba na shege bane da aureta, gode ma zakiyi kirika kwantar mata da hankali ba ki riga tayata kuka ba”
Murya Essha na rawa tace”  daddy ni bestie na ke son gani, inson nagata please”
Ya girgiza Kai yace” Essha yaki keso nayi ne, ki fa ji  abunda daddy ta ya fada, kiyi hakuri watarana Zaki ganta”
Suna tafiya a hanya ya Kira hajiya uke yasanar da ita, duk ta rude tace”  tunda haka ne kawai ka kawo ta uke, ko tasamu kwanciya hankali ana, Kar magaganu mutani yasa mata wani ciwo daban”
Mummy ta amshi waya hannu na rawa tace” hajiya kawai a zubar da ciki zai fi alkhari “
Hajiya tasa salati tace” Kai fatimatu, kisan abunda kike fada kuwa, Anya kina ciki hayaciki , ciki yarki ki ke so a zubar , ciki halak”
Mummy ta fashe da kuka tace” hajiya kina ji fa, tun ba’aje koi’na ba anfara magana Kuma har……
 hajiya ta katse tace” Wai toh magana mutani Zaki bi ne, toshe kunuwaki zakiyi tunda kisan gaskiya, da aura ta, ciki halak ne baza a zubar ba, ku kawata gurina, ta cigaba da raino ciki har ta haihu, in Allah yasa anfa miji shikena”
Essha naji magaganu hajiya dake a loudspeaker yake tasa kuka tace” aa ni inason karatu, da Allah daddy Kar ku kaini, ka taimaka min ka barni ana iyi karatun please daddy “
Daddy ya amshi waya yace” hajiya duk yanda na take zan Kira na sanar miki “
Tace”  Kar  a zubar da ciki na fa?
Ya kalli mummy yace” hajiya karkidamu, rudewa ne yasa ta fadi haka, ba’ason ranta bane”
Har suka karaso gida Essha Bata bar kuka ba, daddy yayi parking suka fito jiki a sanyaye da gudu Essha ta nufi dakita ta fada gado tasa wani kuka Mai ci rai. Kukata da biyu, Kuka rabuwa da bestie Dana ciki da ta tsani uba, gashi dalili haka zai hanata karatu..
Su daddy su shigo duk suka Tara da yara su zuba tagumi, Amir na gani daddy ya Mike yace” Daddy maiyesameta? Naga ta wuce daki da gudu tana kuka”
Daddy yakikiri murmushi da bai shirya ba ya nemi guri ya zauna a tsakiyar su yace” yara yara? Duk suka zuba mishi Ido Basu bashi normal reply da suka  Saba bashi ba..
Yayi murmushi yace” ooooo… Yana ja musu kumatu hade da musu cakulkuli duk suka sa dariya da dolesu, ya sake maimata” yara yara? Suka bashi amsa da ” tsoho tsoho”  duk suka fashe da dariya..
Yace” abun daya nakeson kumi, inason kullum kuriga farata ma sis Essha, Kar kuriga barita ita kadai kujiko?
Amir yace” Daddy baka bani amsataba, maiyesameta?
Daddy yayi shiru ya kalli mummy da sai matse kwalla takeyi yace” sis Essha ai kwanaki baya, nagayamiki daddy karami ya mata aure ko? Suka amsa da”eh”.
Walid yace” yaushe ango ta zai zo?
 Yayi murmushi yace” very soon, kuzo kuji ….yayi magana kasa kasa, duk suka maso Dan suji , yace” sis Essha is pregnant” ya fada a hankali.. duk suka sa murna,na take musu ya barke a tsakani su, Amir da Walid suna namiji zata Haifa , khairat da mufeedat na mace zata haifa, Daddy ya kalamasa hannu Yana kallosu Yana murmushi, yaga abun zai zama fada yadakatar dasu Yana dariya harda rike ciki, mummy batayi niyya dariya ba sanda ta murmusa..
Daddy yace” ya’isa*2 , duk Rana da ta haihu zamu gani ko? Suka amsa da eh.
Yace” toh zaku sa ta fariciki ko? Suka ce dad” we promise”
Yace” yawwa good children, ku shirya yau a LACE restaurant zamuyi dinner” da murna suka mike..
Amir yace” daddy let me check her”
Daddy yace” no ka Bari sai anjima, dauko min jaka da na dawo dashi”  Amir ya je ya dauko yace”  bamu guri zanyi magana da mummy ka”
Yace” toh dad, Nima training zanje, mummy sai na dawo” hannu kawai ta daga mishi …
Daddy ya bude jaka ya ciro wansu papers ya Mika ma mummy tace” maiye aciki?
Yace” duba kigani?
Tafara dubawa batasn lkc da ta rugume Shiba,  ta sa murmushi tace” lallai kajika uba na gari,nagode ma Allah dayabani Kai a matsayi miji Kuma uba yayana,zakafitar da yarka daga ciki kunci na, gaskiya nagode sosai”
Yayi murmushi yace”  ki gode ma Allah, buri Essha zai cika, inshallah bazata ba Bari tayi rayuwa ciki kunci ba”
Mummy tace” hajiya  zata Amince kuwa?  Ga kuma ciki dake jikita” ta fada a sanyaye..
Yace” Kar kidamu zan mata bayani”
Tace”  toh aura fa?
Yace”   na tambayi malamai har biyu, su shaida  min cewa, a addinace idan mace tayi seven years batare da miji ta ba to babu aure,  waensu Kuma suce bai Kai seven years (Allah shine masani) duk yanda tayi yu dai zamugani, zo muje nagata, tana bukatar rarashi”
Suka shiga daki da sallamarsu,ta amsa a hankali murya kuka, ta hada Kai da gwiwar hannuta,ta rakube can karshe gado,ita kadai tasan yada takeji, mummy a hankali ta matsa wajenta ta daga mata Kai ta kwantar da ita a cinyarta,ta yaye mata kitso kalaba dasuka bin gefe fuskata  Tana share mata hawaye tace”  haba Yar Lele baba, kuka na bai isaba, ki kasace Mai tawakali da hakuri kibar ma Allah komai” ta fada Tana sake. Share mata kwala dake fama bin kumatu ta . Daddy ya gyara zama  akasa  ya mikar da ita, suka sata a tsakiya ta Soma magana murya kuka tace” shikena daddy  an rabani da bestie, Kai Kuma zaka komar da ni uke bani ba karatu”
Yace” a’ a Essha, kisan nagayamiki banason yawa kuka na da kikeyi, Essha kada ki manta fa, baki isa ki Hana kafara Allah ta faruba, Dan inhar an rubuta Abu zai faru toh, babu makawa sai yafaru… Yada saurara Yana kallota an hankali yacigaba da mata magana ” shawara ta agareki ki zama Mai yawa addu’a akan duk wani Abu data sameki  a maimako kuka da Zaki zauna kinayi, kada fa ki manta kuka baya magani matsala sai dai yakara ta
 Da haka ki Kama Allah shine zai yaye Miki gaba daya bakiciki da kike ciki, yawa rokoshi babu Rana zai sanyaye Miki damuwar daki ke ciki, Kuma ya amsa Miki dukani bukatuki”
Essha ta share hawaye cike da tawakali tace” nagode dad,  Kuma zaku kujeni ko, zaku komar da ni uke……. Mummy ta katse ta Tace” aa Essha kina tare da mu..
Daddy ya dagata da kyau tana kalloshi duk fuskata ya kumbura Saba kuka da Tasha, ya boye papers din a bayashi yana murmushi yace” albishiriki Yar Lele baba?
Ta tura baki a shagwabe kamar zatayi kuka tace” am not in the mood daddy ” tasa hannu tayi sauri  goge haweye dake shiri sauka.
Ya Bata fuska yace” okay since you are not in the mood, zatafi da Kaya na” ya Mike ya na folding papers din zai’ fita.
ta Mike Dakar jikita na Bari ta Sha gabanshi da sauri tace”   yi hakuri” ta yi kokari kikiro murmushi , yaja mata hanci yace”  toh na hakura, albishiriki?
Tace” goro
” Fari ko baki?
Tace” uhm uhm daddy fari”
Yana murmushi ya Mika mata papers din, Hannu ta na rawa ta amsa ta bude, mamaki yasa ta kasa gasgata abun dake ciki papers sanda ta Kara goge idonta da kyau tasake kallon.. Admission letter ne har ma tasamu, ga abunda paper ” Aisha Ahmed get admitted into University of Delhi, New Delhi India”  har su Bata gynocologist(likita mata ) she was surprised , ta sake Ware Ido da mamaki tana kallo daddy da mummy..
Mummy ta murmure tace” yes na ki ne” ta fada Tana mata dariya..
Tasake kallon Daddy yace” Eh is yours, very soon inshallah my dearly daughter za’a fara kirata da DOCTOR ESSHA, so buriki  yakusa cika ….
Essha ta rasa wani iri murna zatayi kawai ta sulale kasa tayi sujjada Tana ma Allah godiya , ta Mike ta rugume iyeyenata ta fashe da kuka, ko za a yankata ta aka tambeyeta kuka Mai takeyi ita kanta Bata Saniba, murya kuka tace” thanks dad, ur r d greatest of all time…….
Juma’at mufeedat readers ❤️❤️❤️
More comment more typing ❤️❤️❤️
Love you guys 🥰
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
     DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️ (M. W.A)
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/10798094102? referrer=whatsa
__________________________
4️⃣6️⃣&4️⃣7️⃣
Daddy yayi murmushi yace” gode ma Allah, zauna”  duk suka zauna, Essha na rike da papers, Kamar zata cinye.
Mummy tace” ya’akayi ka samo mata school din?
Yayi ajiya zuciya yace” hmmm it’s a long story,  abokina Ra’uf salis dake lecture ne a university din, toh kullum mukayi waya dashi sai ya tambayini Ina likitaka, dake hk yake Kira Essha, nagayamishi ta na lfy har ta samu jamb zan kaita A.B.U, shine yace Kar nakaiki A.B.U , shi zai samomiki makarata acan Delhi,  na ma manta da zance , sai last week yakirani, yaturamin admission letter,baya namiki online registration , sai na wuce Abuja,    saboda sai ambassador din India dake Nigeria yasa hannu a papers din, naje office nashi na tsare tun shekara jiya Ina zuwa sai yau Allah yabani sa’a ganishi, badi yau nagashi ba, da zai watarana kenan dun gobe Friday, babba yaro tycoon na aure kuga zama Bai gasuba…….. Essha naji daddy ta ya ambaci babba yaro tycoon nan take gabanta ya fadi, kawai sai ta bazar ta cigaba da saurara daddy ta..
Ya cigaba da cewa” nasamu na hadu Miki Visa, tun kafi na tafi na dauko passport naki, shiyasa yazo min da sauki, harda indigene foam na Nigeria duk amiki, duka suna ciki envelope dake hannuki,   kafi Nagama komai har su Bata admission, zuwa Nanda sati daya zata wuce, Nagama komai , Dr    Ra’uf har yasoma mata gida da zata zauna a can New Delhi, Nagama biya komai, yanzu shopping yarage zatayi, Saturday Mai zuwa ta wuce, Sunday ta huta, Monday zata fara attending lectures”
Essha ta rugume shi tace” nagode sosai dad, Allah yabar min Kai, yakara girma da budi”
Yayi murmushi suka amsa da ameen
Ciki sanyi murya tace” daddy cikifa?
Yace” Kar kidamu, nasan zaku’iya, school naku ma a Marital status nasa , kina da aure, Kar kiji komai kawai abunda nake son dake ki zake kiyi karatun, and Kuma zan samomiki zam zam da Zuma da dabino sune za su zama Abu sha ki kullum, har kitafi school, zai Kara Miki karfi da Kuma hanzaka, har da unborn child naki, kuma ko wani karshe wata mummy zata riga zuwa dubaki, so Kar kisamu da muwa, kirike mutuci inki tafi, kiga ke matar aure ce, Kuma musulma, Banda bi abokaina banza”
Tace” inshallah daddy zan kiyaye.
Suka mike suka fice, mummy ta juya tace” toh Yar India kishirya gobe zamu fita shopping kinjiko?
Ta gyada Kai Tana murmushi, sai taji duk zazzabi da takeji babu Kuma, toilet ta shiga ta Dora alwala ta fito, ta shimfidar danduma tayi sallah nafilah tana Kara gode ma Allah, Tana idarwa ana Kira magrib,ta hada gabadaya…
Gari kano ta dabo, kano ta dabo tubi giwa.ko da Mai kazo anfika..
*************************
 Gagarumi event aka hada aciki babba hotel dake ciki gari, angyara koi’na Royal decoration aka ma wuri, duka angoye da amaresu su hallara, ama bada goga oga Aliyu..
Suhaima na hango Tasha kwaliya harta gaji da haduwa, ama ba ango, Kuma gashi duka layi Kashi a kashe suke, Kuma ba hali tabar gun, koi’na cike yake makil da mutani, suhaima ji take kamar tasa hannu  akai ta kwala ihu sbd tuki Rashi gani Aliyu, tsorata ta daya Kar gobema yace yace bazai zo ba,  gashi duk yanda ta motsa sai masu hoto su Bata kat kat, haushisu ma takeji ama hk dole take murmusawa.
Su fawaz ta Basu tausayi , suka Sami Isa yayi shiri Kamar ango, ya  zauna a matsayi Aliyu duk Kar suhaima ta ji wani iri, suka shiryashi tsaf, dayake Kuma suna Kama da Aliyu, sai dai Aliyu yafishi budewa,Wanda bai San Aliyu ba zai zata shine, da farko daya zauna suhaima harta ajiya zuciya tazata shine, sanda taji murya ta gane cewa ba Aliyu bane, dun haushi Bata jira antashi ba ta fita daga hall din ta fige motarta sai gida, tana isa gida tasa hajiya binta agaba itama duk jikita yayi sanyi,
Hajiya binta ta ja kwafa tace”  lallai Wana yaro tatiri kansa ne, toh inyasa wata baisan wataba, Baby na karkidamu, akwai gobe,  kisan hajiya khadijah (Mami) ta hada muku dinner gobe acan Abuja, nasan doleshi yazo guri, kisan yanaji maganarta sosai”
Suhaima tace” mummy kiri kiri Aliyu ke nuna Bai Sona, wayyoshi fa a kashe suke, Kuma nasan saboda ni ya kashe waya”
“Hmmm” hajiya binta ta aje numfashi tace” suhaima Kar kitada hankaliki nace Miki akwai gobe, nasara namune, kudi Dana kashe bazu tafi a banza ba, je ki kwanta ki huta”
Ta Mike Tana tura baki ta cire Kaya jikita tayi wurgi da su ta kwanta.
ABUJA
Aliyu na kan daddurma ya idar da sallah nafilla, around 3:07pm, baya yagama adduoin shi ya Mike ya dauki Zane hoto Essha ya rugume, yanaji kamar ma yau za’a rabashi da hoto ne, da gangar ya kashe wayyoyisa yasan zan adameshi da Kira, side nashi ma yaja ma securities kunne kar su bar kowa yashiga, dauri aure ma ya ranya ma kanshi baza Shiba, sai da yayi sallah asuba Yana idarwa bacci barawo ya saceshi.
FRIDAY .
   Kano.
Yau dauri aure masu duniya inji wata kakana😀.. dauri aure uku za’a daura, daya ne a kaduna na haydar da Salmah.
Dauri aure yasamu hallita manya mutani , president na kasa, harda na waensu kasashe, dun Dana duba na kalla dakyau har da tonald Trump da president din Korea su Sami hallarta, governor’s har zuwa local officials, sarakuna kuwa na gari da gari,    kowa ya hallara guri ba mazuguni mutani ne cike kamar sallah.
Taro  ye taro, busa ake kamar yan Yan sarakuna, makada da mawaka kam ai sai abinda yayi gaba, su samu su baje kolinsu, karfe goma cib,ankafara sanarwa dauri aure Kamar yada al’ada ta tanadar a musuluci kowa ya shaida dauri aure UMAR ALIYU TYCOON da AMARYASA SUHAIMA RABI’U HUSSAIN. IDREES da AMARYASA WASEELAT, HAFIZ da amaryasa MARYAM. a lallai su kanawa su ka kwashe, an daura aure aka sadaki Mai ingaci,
 Baya Kamar minti biyar da dauri aure, Tycoon ne kenema Aliyu, shi azontashi tun jiya Aliyu na kano, Bai saniba Aliyu na na Yana shara barci shi rugume da hoto princess nashi, duk yawa taro na hk yasamu ya ya kunsa bodyguards na biyedashi ya’isa gurisu fawaz su Sha gezna farare farare kal kal sai walkiya suke, su Hafiz angoye baki yaksa rufuwa, sai shairri suke ma junasu suna dariya, suna gani Tycoon su ka sarara Kamar marasa gksky, suka fara wiki wiki da idon, su kansu ko ba a tambeyesu ba su San Aliyu yake nema..
Tycoon yakalli yanayisu Sam Basu da gsky yace” Ina Aliyu ?  Nan suka fara zanzare Ido,
“Ba tambayaku nakeba? Nace Ina Aliyu ?
Fawaz  yace”   am… .um dad…. Ya dakatar dashi yace” Kar ka min karya, gaskiya nakeso ji, Yana Ina kugayamin Aliyu yazo ko baizoba? Ya furta Rai a bace. Duk suka sukunyar da Kai na Rashi gaskiya.
Suleiman ya amsa”  kayi hakuri dad, baizo ba, baiji dadi jikishi ne”
Tycoon Rai a bace ya fidda waya ya dialing number Aliyu yaji switch off. Yace” Aliyu ya kyauta, zamu hadu” ya bar gun..
*************************Suhaima ne a daki, takasa zaune takasa tsaye, hankali ta duk a tashe yake, baya an sanar mata Aliyu Bai zo dauri aure ba, kwaliya fuskata duk ta kwabasu, hajiya binta ne ta shigo ta dafata, ta juya tana gani mummy ta ne tasa ihu, hajiya binta tayi sauri rufe mata baki,ta rage murya tace” ke natsu, Kar ki tona muna asiri, bamu kadai bane”
Suhaima ta cire hannu hajiya binta daga bakita tace” mummy har yanzu fa ba alamu nasara, nasan ba zuwa zaiyi ba, kawai ni kibar ni naje na saimaishi”
Hajiya binta Tace” Baby Ashe baki da wayo, ki kwantar da hankali ki, yanzu Nagama waya da Tycoon na shaida mishi komai harda Rashi kiraji da baiyi, harda kuka na, nasan kuwa Wana makircinawa ya zaunu, doleshi yazo dinner na yau, kiga kenan zamu cima buri mu ciki ruwa sanyi, bani mu kashe” ta Mike Hannu suka tafa taf.
“Iyye Baby na tazama surika tycoon,  kudi da dukiya Kuma sai dai angani agurimu, mun shantake yanda mukeso, Kai m soo happy” ta fashe da dariya shakiyi ci..
Suhaima ma ta Mike Tana rawasaya tana juya jiki da ko juyawa baiyi, hajiya binta na mata kirari tana Kara fasa mata Kai..
Karfe hudu nayi,aka kawo.amare gidajesu dake na abuja, mansion lafiyaye ana asokoro Tycoon ya Gina ma Aliyu, gefeshi kuwa na Idrees ne, gidaje ya gaji da tsaruwa, sai shirya amare akeyi saboda za’ayi bude Kai, karfe 9 na dare za’a wuce dinner.
Suhaima Sam Taki nutsuwa, Kai na rawa,sai firit firit take da artificial eyelashes daya cika mata Ido, Tasha alwashi yau zai tacima burita….
Kuyi manage da wana, sister na ba lafiya ni nake jinya. Na ga adduoiku na gode, Allah yabar kauna♥️♥️
More comment, more typing 😁😁😁😁
Love you guys 🥰🥰 🥰
“`👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
    DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️
     M.W.A
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari “`da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar
da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/10798094102? referrer=Whatsapp
_________________________
     Fans naji dadi adduoiku ☺️ nagode sosai, anatare 🥰 irin sosai na😜. Love you guys 🥰🥰 🥰🥰 🥰🥰
 4️⃣8️⃣&4️⃣9️⃣
Aliyu tunda yafara barci bai farka ba sai misali 2, shima sanda agogo daki ya buga two daidai sanan ya farka, ya ma manta yau ake biki dauri auresa, Yana tunawa yaja tsaki yace” WTF” ya Mike ya cire Kaya jikishi ya fada toilet ya _sakar_ ma kansa ruwa sanyi, kusan 15mins ya dauka, sanan ya daura alwala ya fito ya shimfida dadurma yagabata da sallah, baya ya idar sai tsaki yake ja. A fili yace”gaskiya Daddy bai min adalci ba, baigama rufe baki ba yaga inuwar mutum a tsaye gabashi, Yana daga Kai suka hada Ido da Tycoon, yayi sauri ya sukunyar da Kai dan yasa yayi laifi.
Tycoon rai a bace yace” Aliyu ka kyauta kenan, ban taba zato zakamin hakaba, ka watsa min kasa a idon, ace duk girma taro na,  Kuma dauri aure ka guda kaki hallarta guri ka kyauta, eh nace ka kyauta” Yana kaiwa na ya juya da nufi tafiya Aliyu yayi kasa da murya, sanan yashiga lalashi Tycoon Yana bashi hakuri, Dakar ya iya calming nashi, dun yasa daddy nashi komai ya mishi bai fushi dashi, Tycoon ya juya ya dafashi yace” son,Kar ka Kara kaji? Aliyu ya gyada kai.
  “Amarya ka na gidaka anjima, zakuje dinner da Allah Aliyu Kar kaki tafiya  ,dun nasaka, kaga yanzu hakkita ya rataya a wuyaka, u have to do anything that will pls her, imbaka je ba baza taji dadi ba” Tycoon ya fada a siga lalashi.
Aliyu yayi nisa a tunani Essha yace” Allah kadai yasan hali da ta ke ciki”
Tycoon ya girgiza shi yace” are you with me boy?  Aliyu ya amsa. Tom ka kunna wayoyika, Allah ya muku albarka” Aliyu ya amsa da ameen, Tycoon ya juya yabar side din.
Yana fita Aliyu yayi ajiya zuciya ya zauna ya kishigede da gado, idonshi na zuba da kwala, tausayi kanshi da hali da Essha takeciki yake ma kuka, yarasa inda zai da kanshi yaji sanyi, sai sambatu yake Yana yaushe zangaki naji sanyi a Rai na please come back to me… Ya dauki zane ya Bata kiss a daidai lips nata yakara rugume hoto.
Wurare 9:00pm, su angwaye su Sha wanka ready to party,Aliyu kadai ake jira , Aliyu kwance yake rugume da hoto Essha bai da ko niyya shiryawa, fawaz su rokeshi fir yaki tashi, karshe Ammi suka Kira.
 Ammi na zuwa, ta samu wace ta zauna a gefeshi tace” Aliyu yau  fa Ranar fariciki ne a gareka, kayi hakuri ka tashi ka shirya, kasa dai Mami ka ne ta hada ko, baza taji dadi ba , imbaka hallarci guri ba, ga suhaima tun jiya kuka takeyi , yanzu hk Tana na a motar Kai takejira. Aya zakaiya sauke mata hakkita kuwa?
Ya lumshe Ido, ko kadan baison ana mishi maganar suhaima bai sonta, haushi take bashi, Essha ya tuna yanda aka daura auresu cike da tsoro da firgici, he wish biki yau da ita ne, dazaiyi murna da fariciki da baitbayishiba, wasu haweye masu zafi suks zubo mishi a gefe fuska yayi sauri ya share Kar Ammi ta gani yace” Ammi inaje two minutes kawai zanyi na dawo”
“Ka dawo Ina? Kuna tashi gidaka zaka wuce da amarya ka” Ammi ta fada
Aliyu ya Kara hada fuska kamar suhaima ne a gabashi, ranshi kara baci yake  kamar ana fetir.
Ammi tace ” maza maza tashi ka shirya kaga dare nayi”
Kara gyara kwanciya yayi , ya lumshe Ido kamar Mai bacci, yadada damke hoto, jiyake inyatashi kamar ya rabu dashi kenan har abada.
Ammi ta Mike ta tsaya akanshi tace” iyye Aliyu kaga ma rainani fa, Ina magana kana Kara gyara kwanciya” tasa Hannu ta zare hoto da ya rugume Tana bin hoto da kallo mamaki, zai tayi magana kenan Tycoon ya shigo.
Yace”Aliyu Wai maikake jira ne,baka shiryaba?
Aliyu ya Mike jiki a sanyaye yace” Dad zan shirya bana ji dadi jikina ne”
” Daure ka ko kwakarta ka shirya, Kai kadai ake jira, kabar yariya mutani a motar sai kuka take, maiyasa kake haka ne?
Aliyu ya Mike yashiga toilet Yana ji zuciya shi Kamar zata fashe dun zafi , bai jima ba ya fito.
Amir  da wani hadade suits baki, sai kyali yake, da agogo da takalmi, suka bashi guri dun ya shirya.
Aliyu dan shuumaci suit din kawai ya zira a jiki,bai Dora belt ba bale yayi gyara gashi,da garga yayi haka dun haushi komai yake jin, ya sauko kasa , su haydar su zuba Ido suga saukawarshi su fara kashe minshi hotuna abun mamaki kawai suga Aliyu ya sauko barkatai , dukasu suka binshi da kallo mamaki.
Hafiz ya Mike ya na binshi da kallo baki a bude  yace”buddy kanka daya kuwa? wait tsaya kana nufi a haka zaka fita ciki taro na?
Ya amsa da”toh Mai ye fi Raina “
Suleiman ya tabashi yace” Buddy Aya Kaine kuwa? The you look at the mirror before coming down? Wlh  you look horrible”
Aliyu yace” ni fa muje,ku tsaya Kuna cika ni da surutu,toh ni Ina ruwana,imba Essha bane zanmata gayun,toh ba wata daban da zanmata gayun har na farata mata ehe”
Haydar yace” Buddy ita ma  suhaima matarkace fa?
Ya daga hannu yace” Kai kasani, let her go to hell” ya Kama hanya zai fice daga parlor…
Fawaz da sauri ya rikoshi yace” wlh baka isa ba, bara ka fita a hakaba, kalle ka fa kamar wani  Jehovah witness pastor, u look some how, da Allah ba don suhaima ba, saboda Mami zakayi kaji, ta Dade tana jira Wana rana”
Hafiz yace” muma fa, bakiciki yake muna, shi ya d’ana😜, shine mu yakeso ya Bata mana lokaci”
Aliyu daji haka yasaki murmushi har both side dimples nashi suka lotse, Yana kallo one side, yayi whispering a hankali da bai Mai iya jishi, Yana shafa Kai zuwa gemu yace” yea, she’s my sweet in the middle 😜”
Suleiman ya juyoshi yace” Mai kace?
Ya baka mishi harara kamar Ido zasu fado, tundama akwaisu tuburkallah yace” basaniba”
Suleiman yayi murmushi yace” a’a rike wukar bani na Kar zomo ba rataya aka bani”.
Kafi Aliyu ya akara har Hafiz ya gyara minshi Kai , fawaz Kuma na Dora minshi belt, haydar Kuma na fesheshi da waesu expensive perfumes masu shege kamshi, Suleiman sai aiki gets mishi collar yakeyi Yana Yana Kara gyara zama riga suit din na ciki.( I really love friends♥️🧡).
Suna gama mishi gyara Aliyu ya fito a asali Aliyu Umar tycoon, yafita a Jehovah witness inji fawaz😆,sai dauka Ido yakeyi, tsasa kyaushi ya Kara fitowa, suit din ya karbeshi sosai , balle black ya hade da light skin guy sai ya bada WOW, MashaAllah ango Essha ya fito, duk angwaye ya darasu.
Aliyu ya hada gira sama da kasa kamar bai taba dariya ba, ya dauki Bluetooth ya manna a kunne yanaji matsanaci faduwar gaba, Suleiman duk motsi da Aliyu zaiyi zai ya Kashe mishi hoto.
Idrees ya shigo yace” bros kufa ake jira” shima yasha suit yayi kyau shima, duka angwaye su fito kamar a sace su.
Fawaz yace” muje ku” har su fara tafiya sukai baki kofa, da sauri Aliyu ya juya ya haura dakishi, ya na zuwa ya dauki hoto Essha ya marairace murya kamar tanajishi yace” kiyi hakuri baby boo, sweet in the middle ya Kade mata Ido daya yacigaba”  I promise not to cheat on you, kiyefeni  biyaya nakeyi”  ya sumbaci hoto, sanda yaji daddyshi ya kwala mishi Kira sanan ya ije hoto yana waving mata bye ya sauko.
Suna fita gabadaya  aka fara kashe musu hotuna,ga motoci birjiki ana jira isorwasu, Aliyu ko yatsaya ayi hotuna dashi ya fuske ya shiga motar, front sit ya zauna dashi da driver Yana juya yaga suhaima haushi yakara kamashi yaja tsaki Ashe motar da yashi ga take ciki, kamar ya fita kawai yakara ja wani tsaki ya kauda Kai.
Suhaima ita kadai a back sit sai shara kwalla take , Tasha wani armless wedding gown da girma shi ya cika back sit din gabadaya, Tasha heaven makeup, ta tura baki taji dadi koba komai zaije Kuma zai zama nata.
Ana tada motoci suhaima da sauri ta fitar da tozali na ta murza a Ido, ta Kara mutuke Ido ta gari tozali sanda ta tabatar yakama radau radau ,tayi sauri ta komar da tozali ciki dan karami fashion  pulse da ta rike na amare a zuciya tace” sorry darling daga yau kazama nawa, bakai bawata, sai ni kadai.no more fuskar tsana dakake nuna min” tasaki murmushi.
Aliyu kam Yana gaba sai bin titi yake da kallo har aka karaso ciki gate din
 hall din da za’ayi biki,  guri cike yake dam da mutani, su kadai tundama ake jira afara biki gashi su karaso, guri yasha tsadade decoration,kafi Kashi ga hall dinma aiki ne, securities ne birjik, kala kala, ciki hall din sai wani kalloli wuta yake badawa,  guri zama brides da groom nasu shi kanshi abun kallone,  ciki hall ya Tara manya mutani.
Aliyu ana Parker mototoci, su amare da duk suka fito shi kadai ake jira, gashi tundaga kan photographers Yan media, duk su musu caa ana jira fitowar young Tycoon da amaryashi,shikama Kara shigedewa yayi ya kwantar da sit baya ya gyara kwanciya shi,ya lumshe, yarike kirji Yana furta inalilahi Dan gabashi faduwa yake sosai kamar zai fito. Hafiz ya saki Hannu nashi amarya ya nufi motar da Aliyu ke ciki,yayi knock driver ya zuge glass kasa yace” Buddy Sha daya yanzi sai Bata mana lokaci kakeyi , please ka sauko haka ga Mami fa a tsaye tana cira fitorwaka” ya bude mishi kofa , a hankali cike da kasaita ya sauke kafa daya, photographers da Yan media da suka nufishi, ai da sauri securities suka taresu, Aliyu ya fito Yana wani Sha kamshi Hafiz ya rage murya yace”  Buddy amarya fa?
Ya ja tsaki yace” intagaji ta fito”
Ashe Mami taji  abunda ya fada, ta matso taja hannushi ta rakwafar dashi dayake ya fi ta tsayi tace” Aliyu becareful, behave urself fa, ka fito da ita yanzu na,hata murmushi na yau sai kayi shi,  kabar hada fuskarna , muntara manya baki,so don’t disgrace us” ta murda mishi kunne.. Yan hoto kam a samu abinyi sai ket ket kakeji , ya zangayo ya bude mata kofa kanta a sukunye kamar wata Yar arziki ya kauda Kai gefe ya Mika mata Hannu, da sauri ta Kama hannu, taji laushi kamar hannu mace, sanda taji tsikar jikita sun tashi daji yanayi fatar Aliyu, da daga Kai ta kalleshi taga wani gefe yake kallo, ta furta” kash, dole nayi abun da zai jawo fuskar shi na yanzu,  Dan nasan muna shiga ciki kallo arziki bazai minba” ta furta, Nan take kawai sai tasa kuka munafurci , da sauri Aliyu ya juya Dan tabashi tausayi, dun yazu yasan so, kawai sai yadagar da fuskar ta ya fitar da hanky daka ciki aljihu Yana share mata hawaye, kawai idonusu suka sarke dana juna, Nan take yaji wani shock sanda yanda zabura,so yake ya furta Auzibillahi ama sai yaji kamar a rike mishi baki, kallota ya cigaba dayi Yana ji kamar ana sauke mishi wani azababe sonta, nantake yaji duk duniya bai Wanda yake so sai ita, nan kuwa ya manta da wata Wai ita Essha, ya sakar ma suhaima wani Wawa murmushi Yana Kara binta da kallo bai ko kiftawa yace” wow beautiful”
Suhaima murna yakamata a hankali tace” yes naji nasara , Aliyu welcome to my kingdom”
Suka cigaba da kallo juna   har yafito da’ita taga ciki motar , suhaima tagama rikecewa dagani yanayi kwaya Ido Aliyu yagama tafiya da ita, Ashe dama duk kallo data ke mishi na tsoro ne, suhaima har da hade yawu ..
Hafiz su tsaya kallo ikon Allah yau Aliyu ne, dazun yagama complaining baiso ta, yanxu Kuma kallota yake kamar zai cinyeta..
Fawaz yace” shareshi  buddy kila itama love at dinner sight ne dun bara’a ce first sight ” duk suka fashe da dariya suka wuce ciki.
Suhaima  sai Kara makele ma Aliyu take a jiki,   duk su makale ma juna Aliyu sai washe hakori yake.
Taro yayi kyau,Aliyu yaba kowa mamaki  aguri, yanda yake nuna ma suhaima so kamar zai cinyeta , sune baddest couples a guri, Dan guri yanka cake, suhaima ta yanka tasa a baki tasa Aliyu ya tsosi cake din tass a bakita, lokaci daya. Kawai yazage yanuna ma suhaima tsasa so, har feenat ta kawo Madara na, suhaima ta bashi yasha duk babu Wanda ya lura.
Mami tun abun nabata mamaki har Soma Bata haushi, abun mamaki ma suhaima Bata jira antashiba ta ja Aliyu suka bar hall din zuwa gidasu, Aliyu har wani tsorata yakeji, suna zuwa gida tun suna haurawa stairs zuwa dakisu tanuna mishi abunda take bukata ,  Aliyu yace” wait muyi sallah dear ” Taki amincewa zai sake magana ta hade bakisu guri daya, taja shi zuka fada aka sofa Dagana Kuma suka Lula duniya ma’aurata…………………….
 Bara  na gudu ko Mmr hikma ta zaneni🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️ 😜😜😜😜
More comment more typing ❤️❤️❤️❤️
“`👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
    DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
  J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️
            M.W.A
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta 🤙🏻.
https://www.facebook.com/10798094102? referrer= Whatsapp
_____________________________________
       Happy Juma’at Kareem 🥰 to you fans🥰🥰
   5️⃣0️⃣&5️⃣1️⃣
Baya sati daya, tafiya ya tasoma Essha a gagauce, Tana Gama shirye shirye tafiya , tabin dangi gabadaya suyi sallama, Dakar aksha daga da hajiya ta Amince, harda kukata Wai za’abar Essha taje uwa duniya ga ciki ga wahala karatu, Dakar dai daddy ya shawo kata ta amintace….
Yau Friday,  zata tafi, Essha tayi kuka sosai kamar ranta zai fita ,  Essha kuka rabuwa da family nata takeyi da na Rashi gani bestie har zata tafi, mummy da su khairat su ma kuka suke, daddy ne kawai Mai lallashi yadagota yace” Essha Kar kidamu, ai nagayamiki kowani karshe wata mummy ki zata riga zuwa dubaki, kiji?   Ya Kara mata nasiha Mai ratsa jiki”
Essha ta jijiga Kai Tana kuka nasiha ya ratsa ta Tace” inshallah daddy za’a kiyaye”
Yace” Kuna isa Dr ra’uf Yana airport, zai kaiki har gida da Zaki zauna kijiko? Ta gyada Kai..
Mummy bataiya cewa komai ba rugume ta kawai tayi tana kuka, da kuka suka rabu ta wuce ciki jirgi saboda an fara sanarwa jirgi zai tashi, tana shiga batafi mintina da zama ba, jirgisu ya daga zuwa India..
Essha na zaune gefe window ba abunda takeyi sai kuka har suka Kandi a India…
   INDIRA GANDHI INTERNATIONAL AIRPORT, New Delhi, India..
 Essha  da hamdala take saukowa duk step da ta taka sai ta Kira suna Allah har ta sauka, sai baza Ido kawai take , yau gata a new place da Bata taba mafarki zata so ba, batasan lokaci da da tasaki wani lalaulasa murmushi ba, tana bi airport din da kallo, yanda taga ana shiga ana fita , Bata ankaraba taji a dafata, an Kira cikeke suna ta, ciki sauri da  mamaki ta juya,  sai tasaki murmushi tana share hawaye gani aboki daddy ta ne Dr ra’uf rike da karamin signboard Mai dauke da sunata, shima yasaki mata murmushi  yace” welcome to New Delhi daughter”
Tace” nagode sir”
Ya amsa da Don’t mention sanan yace”   zo muje na kaiki inda Zaki zauna, sauri nake anjima zan wuce Nigeria”
Tace” okay sir”
Yafara tafiya tana biye dashi janye da manya manya trolley nata, har suka isa gaba motar ya taimaka mata suka sa Kaya a boat, suka shiga ya tada motar, suna tafiya , Essha ta har da sauke glass din motar tana bin Delhi da kallo, sai hayaniya kakeji, city ya burgeta, there busy roads , yanayi shigarsu ya burgeta ta saki murmushi.. Dr ra’uf na kallota shima yayi murmushi yace” The you like the city?  Bata waiga ba tana kallo wani babba temple na bauta ta kada Kai..
Shima ya fara mata nasiha dun yadda zata tafiyar da rayuwata..yace” Essha kiriga sai hakaliki a karatu , Kuma kisan condition daki ciki, you are pregnant you have to be careful”
Essha ta sukunyar da Kai   kasa nandana mood Nata ya canza, zatayi kuka a ranta tace” shikena daddy ya sanar dashi Ina da ciki”
Dr ra’uf yakalleta yayi murmushi yace” Essha Kar Wanan yadameki, daddy ki ya sanar Dani komai, you don’t have to be worried (kamar yasan abunda take ayanawa a zuciya kena).. Kuma albirshiki na Miki kawa, a gida daya ma zaku zauna, ba time yanzu muna zuwa Zaki ganta , itama student ne, school naku ma daya har course dima, itama this year ta fara, zata nuna Miki  komai na school kijiko?
Ta gyada Kai, Allah sarki harta tuna da bestie,  haweye zai sauko da sauri ta share, taji Dr ra’uf nacewa” sauko mun iso”
A hankali  ta sauka tana bin street din da kallo, quiet area ba wani hayaniya sosai, gefe guda kuwa fili cricket ne yara ke bugawa, sai bin street din take da kallo haryanzu Bata daina mamaki ba, yau itace a India, a hankali ta furta” Alhamdullila, thanks dad”
  Taji Dr ra’uf ya ja mata kumatu Yana dariya yace” hey Yar kauye, shiga ciki nariga da na shiga Miki da Kaya, Pooja zata nuna Miki room naki” ya nuni ga wani flat maidaidaici yace” shiga na ne gida naku, school naku bai da nisa Dana, ni zan wuce sai anjima”
Ta daga mishi hannu tace” nagode uncle”
Yace” you re welcome, shiga ciki, Pooja nanan” ya tada motar ya yi gaba..
Essha a hankali take nanata suna Pooja, ta Kama hanya ta shiga da sallamarta, ba amsaba sai bin gida take da kallo,   2 bedroom flat ne, da babba parlor, kitchen da dinning area,  gefe guda Kuma study room ne, gabadaya bedrooms din da furnitures iri na student Dan dai dai,  parlor ma yasha Ash sofa, sai da table a tsakiyar Mai kyau,  babu abunda babu a gida.
Ta nemi guri ta zauna tana share kwalla, tana daga Kai, tayi ido biyu da wata kyakyawa budurwa, da mamaki ta bude baki tana kallota don yariya Kama take da Alia Bhatt, babacisu kawai tafi Alia Bhatt girma jikine, ta fito daure da towel tana busar da gashi kanta da hand drying, tana gani Essha ta saki murmushi tazo ta rugume ta, ta Mike taba Essha hannu suyi musabaha, Essha kam takasa mgn sai binta take da kallo mamaki,
 ta shaking hannu Essha tace” Namaste!  Essha Ahmad right? Welcome to India, am your new friend, course mate, my name is Pooja Chandra am from pune, nice to meet you too”
Essha ta saki murmushi tace” nice to meet you too”
Pooja tafara zuba da turaci Tace”  ni Yar Hindi ce, ke Kuma musulma ko? ai zamuriga  zama tare ba matsala ko? Ki na da kyau sosai, Mr Ra’uf ya bani labariki, ki na da aure, Nima nakusa aure,Nanda wata biyu, mijina da zan aura  a Dubai yake aiki, sunashi saif Khan shima musulmi ne, ai zakizo ko? Kiga kena ki zama  babba kawana, tundama a kauye mu ba Wanda yakeso yayi kawa Dani saboda nayi kiba da yawa, kina so na a haka ko? Ta fada ta marairace ma Essha fuska…
Essha batasan lokaci dariya ya kubce mata ta Soma kyakatawa, gsky Pooja ta shiga ranta,  sanda ta natsu tabar dariya sanan ta gyada mata Kai Tana murmushi tace” ta Amince”
Pooja ta rugume ta, tana murna ta mikar da ita ta Soma zangaya da ita gida tana ta zuba tana Bata labari school, har waje ta kaita ta nuna nata gida su landlord nasu, Essha duk ta gaji, Pooja ta Bata hakuri, ta nuna nata dakita, Essha na shiga baya Pooja ta wuce ta fada gado ta fashe da kuka, ita kanta ta rasa dalili kuka, sanda tayi Mai isarta tukun ta Mike ta share hawaye ta fada bathroom tayi wanka, Tana Gama ta daura alwala ta fito tayi sallah, Tana idarwa ta fara jera kayata a ciki wardrobe, Pooja ta shigo ta taimaka mata suka jera foodstuffs a kitchen tana gamawa ta fito da dambu kaza da mummy ta hada mata taci sosai ta bin da ruwa ta kwanta da kewa gida…
Monday
 Tare suke tafiya school da pooja, su tashi Tare, tana fahimta karatun sosai… Tun safe in suka fitai lecture sai 7 wani lokaci har 9 suna kaiwa, su dawo duk a gajiya..a kullum sai tayi waya dasu daddy ta, harda su hajiya suna kirata su gaisa..
Baya three months
Essha ciki ta ya girma har ya Soma fitowa, tana samu kulawa sosai guri Pooja da mummy, Dan ko wani karshe wata mummy take zuwa  dubata, su Saba sosai da Pooja, da Pooja Bata da matsala,  inkagasu kamar amine juna da sukayi shekaru a tare,a bangare karatun kuwa, karatun take sosai ba Kama hannu yaro, ta mayar da hankali ta sosai ba wasa, har ayi biki Pooja two months dasuka wuce, suyi  shagali  biki sosai, baya biki miji ya dauketa sukaje honeymoon a Dubai, Essha tayi kewata sosai, sati daya Pooja ta yi ta dawo saboda school, ta koma gida mijita , tayi da Essha ta dawo, Essha taki amincewa, haka ta hakura itama ta park ta sake dawowa gidanasu suka cigaba da zama…
Duk abunda Essha ke bukatar Pooja ne kayi mata,ta hanata to komai sai dai taci ta sh tayi karatun, gashi tana samu kulawa sosai guri mummy da Daddy ta.
tun Pooja baiya girki naija ba har ta kwaya ta kwairai sanadiyar Essha, baza ta iya cewa ma Pooja komaiba dun ta mata abubuwa da ko yanuwata barasa su mata ba, shiyasa a kullum take kara shiga ranta..
Ciki na 6months sukaje scanning, scanning ya nuna namiji zata Haifa, Pooja tagaya ma mummy, su ka fara sayayar Kaya haihuwa,  kafi wani lokaci suga ma sayayar komai…
Baya wata tara da Yan kwanaki, Da safe, Essha na zaune , tana tsifa, takkadu ne birjik a gabata, mummy na gefe ta, tana bare ma ta gayda , Pooja na ka gado tana barci, Essha sai mutsu mutsu takeyi ta kasa sukuni, mummy ta kalleta tace” yadai ?
Ta yatsine fuska tace” bakomai mummy”
Mummy ta Mika ma ta gayda ta amsa zata Kai baki taji kamar wani Abu ya tsarga mata mara, ta dakata da sauri,  a hankali  ciwo ta takeji ya fara tsanata, Essha ta kasa Koda motsi sai cije lebe take,  can azaba ya ya tsanata tafara murkusawa,   Nan ta fashe da wani kuka Mai Kara, mummy da hankali ta baya kanta tanaji kukata da daga Kai da sauri ta Mike Tace” Essha lafiya?
 Tana kuka Tace” Wayoo mummy zan mutu marana”
Mummy tace” subhanallahi” na ta fara Kira suna Pooja.. Pooja na barci ji yanda mummy ke kira sunata tasan ba lafiya ta farka a zabure ta diro daga gado gani Essha a durkushe yasa ta karasawa gareta da sauri, daga ita har mummy dukasu a rude suke, Dan Essha ta Soma fita daga hayacita, azaba takeji sosai, gashi kanta duk ya mutse , duk ta jike gabadaya.
Pooja da sauri ta shiga bedroom nata ta zari car key da mijita ya Bata gift a lkc bikisu, ta koma daki da gudu, tana zuwa da turanci tayi magana tace” mummy dagata  mukaita asibiti”
Mummy ta dagata a rike suka fito da’ita, Pooja tayi sauri ta bude back sit ta aka Kwantar da Essha, mummy ta zauna a baya ta Dora kan Essha a ciyarta tana shafa Kai Tana tofa mata duk addu’a da yazo bakita.. Pooja ta figi motar sai asibiti …
A haraba hospital tayi parking ta sauri ta fito tashiga ta Kira doctor, sai gasu su fito da nurses da gado tura marasa lafiya su ka daura Essha akai, babu Bata lokaci suka shigar da ita labour room.
Pooja da mummy na tsaye gaba labour room suna ta safa da marwa, Pooja sabage rudewa ko takalmi bashi a kafarta, anfi awa hudu ana abun daya, Essha duk ta galaibata , tanaji kamar rayuwa ta ne yazo karshe, mummy duk su shiga tashi Hankali , addu’a kawai take Allah ya sauke ta lafiya….
Karfe hudu na bugawa cib Essha ta sauka, mummy ta dawo daga sallah  ita da Pooja su zauna jugum kamar ayi mutuwa,suka jiyo kuka baby daga ciki labour room ,  mummy ta Mike da hamdala , Pooja tasa ihu ta rugume mummy, can sai ga Doctor da ya amshi haihuwa ya fito da fara’a dauke da baby boy a hannushi da sauri suka nufeshi…shima Yana ganisu Kara saki murmushi yace” congrats ma, is a baby boy”
Mummy ta amshi baby daga hannu doctor Hadi da washe baki tace”Alhamdullilah! Alhamdullila! Allah muna gode maka binsa Wana kyauta ” ta rugume boy din a hankali so da kauna yaro na ratsa ta..
Pooja na gefe sai washe baki take, Saba fariciki har ta kasa magana.
Nurses suka fito da ga labour room suna tura gado da Essha ke kwance zuwa rest room, da sauri su suka bin baya nurses din zuwa daki, suka Tara Essha na bacci , nurse ta samata drip , Pooja ta tsaya a gefeta tana gyara mata gashi Kai dasuka barbaje.
Baya komai ya lafa, mummy ta tuna Bata sanar ma daddy ba, da sauri ta duba taga ma ta Manta da waya a gida saban rudewa..
Pooja Tace” mummy zanje na dauko” ta fita da saurita bada jimawa ba sai gata ta dawo, Wana Kara tasa slippers ta Mika ma mummy waya, ta na karba ta dialing number daddy, ringing na farko ya daga da sallamarsa ta amsa..
Tace ” albirshika ?
Yace” goro, goro ma fari tas tas”
Tayi murmushi Tace”. Toh diyaka ta haihu”
Daddy nazaune a office dama,yanaji ace Essha ta haihu da murna ya Mike har Yana haweye yace” MashaAllah Alhamdullilah, Mai aka samu?
Tayi dariya tace” sabon ango nayi”
Yayi murmushi yace”alhamdullila Allah ya Raya ya Bata lafiya, Ashe dai ankusa shayani gefe ” yayi magana cike da barkwaci
Tace” sosai ma kuwa, Sana tace” yaushe zakuzo “
Ya amsa da gobe inshallah, kila muzo dasu hajiya”
Tace” toh Allah yakaimu..ta katse Kira..
Bangare daddy kuwa, su hajiya yakira ya sanar musu , suyi fariciki sosai , daddy karami harda kukasa..
Washe gari sai misali uku na Rana su daddy suka iso, lokaci har àn sallamarsu Essha dun jikita na da kyau,harda hajiya da daddy karami,su zo da Kaya baby dayawa kamar za’a bude karami boutique.. cike da girmamawa mummy ta tarbesu, Daddy ya wuce ida Essha ke zaune gabata ruwa zafi ne ke turiri, cewa tayi tanaji kishi ruwa shine mummy ta,ta hadata da wanan sai fama tura baki  take, ta masu hajiya sannu da zuwa..
Daddy ya shafa mata Kai Yana murmushi yace” sannu Essha Allah baki lfy, ya Miki albarka ya Raya abunda aka Haifa”
Ta amsa da ameen da ameen nagode”
Ya juya ga Pooja da tasa tuwa da Miya kuka da mummy ta girka tanace sai ta koyi ci, hajiya na mata dariya..
Daddy  yasoma mata mgn ciki harshe turanci yace” Pooja mungode da kulawaki, Allah yamiki albarka ya sauke ki lafia(Kai Ashe ma tana da ciki ba lura ba 😛😅sai yanzu) “ta amsa da amen…
Daddy karami yace” sannu daughter Allah yamiki albarka” a shagwabe ta amsa ta fara complaining ruwa zafi da mummy ta Bata…
Daddy k yayi dariya yace”   yi hakuri daughter ,Kisha kiji a haka zai da Kara samu lafiya”
Hajiya tace” wanan ma kadan ne yariya, uke zan wuce dake dagana, imiki wanka jego, in cudiyaki da ganye dawa da ruwa tafasheshe habawa yariya Zaki samu lafiya” duk suka fashe da dariya Banda Essha..
A shagwabe tace” daddy ni dai banza bin hajiya uke ba, exams namu yakusa fa” ta fada kamar zatayi kuka………………
More comment more typing ❤️❤️❤️❤️
Jk to u guys 🥰🥰😍😍
Love you guys 🥰🥰
_👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
     DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
WRITING BY
J Hajara
🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️
    M.W.A
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
____________________________
    5️⃣2️⃣&5️⃣3️⃣
Daddy yayi murmushi yace” yi hakuri kwantar da hankali ki, hajiya wasa take Miki, ga mummy ki zata zauna dake na Dan wasu lokuta”
Mummy ta Mike ta dauko boy din da ta gama samishi Kaya ta Mika ma hajiya, hajiya ta kurawa yaro Ido tace” Adamu  kaga ikon Allah yarona wlh da ubanshi yake Kama” ta fada ta na Mika ma daddy karami baby boy din..
Shi da Daddy suka zuba ma yaro Ido batare da su furta koda kalma daya ba, dun daddy kasa magana yayi saboda faduwar da gabashi keyi, dun yaro na tsanani mishi Kama da family din Tycoon, ya sauke ajiya zuciya ya Bazar da zance aranshi yace” Kama ce kawai, imbahakaba ina Yan kungiyar zasu tare wani daga ciki yara Tycoon da suna da masu kuladasu sama da ashiri kullum  suna binsu a baya hmmmm”
Mummy ta kalleshi tace” yadai Abba walid?
Ya amsa da bakomai..
Baya su natsu, Daddy  k yace” yakamata ama yaro huduba”
Daddy ya kalli Essha da kanta na kasa yace” toh ke wani suna kike gani ya kamata a sawa yaro?
Essha tayi murmushi ta rufe Wai ita a dole kunya.. duk suka sa dariya, Pooja dake guri sai binsu take da kallo Bata ji abinda suke fada, da suyi dariya sai itama ta fashe da dariya.. duk sai ta ba su dariya suka ta kyakyawa…
Mummy tace” ka jita, common talk jare”
Tace” mummy duk suna da Daddy keso yasamai”
Daddy yace” toh naji, Allah yamiki albarka” ya dauki yaro ya mishi hudu ba yasa mishi suna ABUBAKAR SADIK , Yana son suna sosai , shiyasa yasa mai… Hajiya sukayi na’am da tana addu’a Allah yarayashi ciki tubar koyarwa addini musulici ,, duk suka amsa da ameen..
Baya sati daya, Essha da yarota suyi bulbul nonota da kyau,  Ranar suna kenan, Daddy a can gida nijeria yasa anka yaka raguna akayi sadaka, ya Hana su mummy suyi biki suna.. miji Pooja yazo shima da Kaya Niki Niki , abunda sai son barka ba acewa komai..
Bayan three months da Yan kwanaki baya ta Gama arba’insosai ta warke sumul , har su fara zana jerabawa na first semester , Pooja tasamo nanny  Wanda zata riga kula da sadik, Yar dattijuwa Mai Kamala Mai suna ummulkulsum, mata ta iya raino, Tana ba Sadik kulawa sosai..
Ciki ikon Allah suka Gama zana jarabawa aka Basu hutu sati daya, a lokaci Kuma big mum nata roko daddy yabar Essha ta zo tayi hutu a guri kafi hutu su ya cika sai ta koma, daddy yaki amincewa yace hutu bamai yawa bane…  A pune suka karasa hutu kauye su pooja, hutu na cika suka dawo school, dakaita har Pooja results nasu yayi kyau, bakaramin murna sukayiba..
Sadik yakara girma wata shi bakwai  da haihuwa yafara rurufe, lokaci ne Kuma Pooja ta sauka ta samu yarta mace suka sa mata suna Arundhati, Sadik tsasa kamanishi  na Kara bayana,  Essha haka tsoro yake bata, Essha har roko Allah take aka in ya girma Allah yasa kaminishi ya sauya,(batasan ikon Allah ba) .. sadik na Kara girma kamani daddyshi na Kara fitowa, haka ba karamin damuta yakeyi ba, ai kuwa Tasha alwashi bazata taba kaishi Nigeria ba komai rintsi..
Baya shekara bakwai da watani….
Masu iya magana  suce” sannu sannu  Bata Hana zuwa sai dai a Dade ba ajeba”
Toh Alhamdullila Essha ta Kamala karatuta cike da tari nasarori, she’s now a qualified Doctor, saboda Essha da first class ta fito, burita ya cika, Ranar da suka graduate Tasha kuka don murna kwana tayi tana sallah , fadi kyau da Doctor Essha ta Kara wani Bata lokaci ne, inkagata kamar ashawariya rai,  diri kuwa kamar Cardi B, inkagata kamar baitace ta haifi sadik ba, waesu da Basu sani ba , suna dauka ko kanita ne, tun zuwa ta India so daya ta koma nijeria shima service tajeyi, a LUTH tayi service nata ( Lagos University teaching hospital), tun kafi taje service a Nigeria a lokaci daya daga ciki manya hospital dake New Delhi suka dauke ta aiki saboda gani kokari ta, Tana Gama bautar kasa ta dawo ta cigaba da Aiki a BLK Super Speciality Hospital New Delhi, guri aiki su daya da pooja..Dakar mummy da hajiya suka Amince ta koma, Buri Essha ya cika tana taimako matar ya uwata da Kuma alumma yi haka na farata mata Rai sosai, tanason ta dawo Nigeria tayi aiki ama tsoro ya hanata, saboda batasa ta rasa danta  tanaji a jikita inhar ta koma nijeria kamar rasashi zatayi..
Saboda sadik kamanishi da maihafishi yayi yawa, kamar Aliyu yayi kaki ne ya aje, ba’abunda ya baro na uban haka na Bata tsoro, shiyasa Koda zataje service bataje dashi ba, tabarshi a hannu Pooja da mijita saif , dun Sai’f Yana matukar so yaro..
Zuwa yanzu sadik ya girma,ya neman shekara bakwai a duniya, kwana uku kacal yarage Mai ya cika seven years, yaro Mai wayyo da kyakyawa dabi’un, ga riko addini, tun Yana da three years ta enrolling nashi a mkrt  both Islamic da boko 6to6 ne ba zama, sosai yake kararun, inkukaji Sadik na qira’a zaku dauka murya sheik sudais ne…
Gata sosai sadik ke samu daga wajen family da Pooja da mijita, mummy shi ko sau daya bataba kaishi ziyara Nigeria ba, dayayi hutu Sai’f zai daukeshi su wuce Dubai, ama haka fa bai cire Mai tunani tambaya Ina Daddy Shiba, a kullum in yatambeyi mummy shi Ina Daddy shi, sai tace insu koma Nigeria zai ga daddyshi, yanzu haka baida wani buri iri yagashi a Nigeria, yeje yaga Daddyshi…
Zakusha mamaki inace muku Sadik baiji hausa ko kadan, ko zo inkashe ka da hausa bai saniba, hata gaisuwa ma hausa baiyaba, sai dai yaji mummy shi nagaisawa dasu daddy ta ta yare,  yare uku kadai yakeji, daga Hindi, turanci, sai larabci, yafi yi  biyu da Hindi da turanci, Essha batasamu time din mishi hausa,   asabar ne kadai freetime nata, dashi sadik din, dasu zauna Dan ta koya Mai hausa, kafi anfara hospital za’a Kira ta emergency, lesson da baza’ayi ba kenan, haka na damuta sosai na Rashi ji hausa da sadik baiyi, tasa fada zatasha in daddy ya gane cewa sadik baiji hausa…
        Thursday
Essha ce ta fito daga theatre, sanye take da Kaya light blue na surgery, ta Dora lapcoat akai, wuyata sakale da stethoscope da murna ta fito , saboda cs da tafito na was successful, Mai ciki Tama cs, tasamu quadruple (yara hudu)   tagama dinke mata a shirya ta ita da yara  kenan ta fito da murna  , doctor da nurses sai tayata murna sukeyi..
Pooja da gudu tazo ta rugume ta tace” congratulations Doctor”
Tayi murmushi tace” thanks dear”  ta nufi  hanya office nata Pooja na biye daita, da abaki kofar  office din ma suna ta nagani a mana “Dr. Essha Ahmad”
Suna shiga ta hangi sadik zaune aka chair data ke zama ya, Arundhati na gefe Kai yariya kyakyawa ta girma..
Sadik ya hada fuska na tam Sanya yake da school uniform da allamu ma daga school suke( ya illahi sai yanzu na Kara gani kamani sadik da Aliyu, a lalai akwai kura)
Essha ta zuba mishi Ido tana kalloshi , ta cire labcoat dake jikita ,  Sana ta zare stethoscope ta aje aka table Bata cemishi uffan ba..
Pooja da sauri ta karasa wajeshi ta na shafa Mai Kai ta kalli Arun(Arundhati) tace” Kya huwa?( Mai ye faru)
Arun tabafara Bata amsa da yare Hindi tace” yau ne end of the year party Kuma Father’s day , papi kowa zu zo gani haka ne yasa sadik kuka, yagayamin cewa wai shi baitaba gani daddy shi ba, Wai uncle Amir kadai yasani “
Arun nagama fada haka jiki Essha yayi Sanyi, Pooja ta jata gefe tace” Doctor  nasan kisan daddyshi Kuma kisan inda yake, maiyesa bazaki kaishi ba? Please and please doctor ki nuna mishi Daddy shi” ta hada hannuwata tana rokota..
Tabbas Essha tasa waye, information akanshi gabadaya tasani, dun tun lokaci da aka haskoshi a BBC ana hira dashi ta gashi , lokaci ta matukar tsorata dagani matsayi dayake, tashiga tashi hankali, tun daga wana lokaci ta dunga bibiya duk wani labari akashi, tasan komai ama Taki sanar ma iyeyeta  Dan Kar arabata da danta, tasa aranta cewa Aliyu yafi karfi ta nesan ba kusa ba,  shiyasa tunda sadik ya girma Taki tura masu da hoto shi da kamanisu ya baci, ba abunda zai hanasu zargi cewa sadik Dan Aliyu ne..
 Ta kife Kai a bango ta rasa yazatayi da ranta ,  ta  nufo Sadik jiki a sanyaye ta kuya chair suna fuskata juna , sadik ya sadda Kai kasa yaki kallo ta , tayi murmushi ta fara mishi cakulkuli na yafara kalkelewa da dariya duka dimples nashi sai aiki lotsawa sukeyi Yana washe hakori( wayyo Allah fa Aliyu photocopy)  sanda tabarshi yayi dariya Mai isarsa ta Mika mishi ruwa yasha tasoma magana da hausa  tace”  Albirshika?  Binta kawai yake binta da Ido baisan maitafada ba , ta dafa goshi tace” Kash sadik Rashi ji hausa na damuna, you have to learn ” ta Soma mishi speak da turanci tace”  tomorrow it’s ur birthday, Kuma uncle Amir zaizo gobe yatayaka celebrating na birthday jibi zamu wuce Nigeria, Kar kadamu kanka zanka ga Daddy very soon ”  ita kanta tasa fada kawai take yi ,  jibi zata koma Nigeria baduk taso ba, sai dai saboda daddy ta ya matsa mata da Kuma aiki da tasmu a Nigerian,  bayanda taiya ta sadakar    duk abunda zai faru ya faru…
Sadik ya Mike ya rugumeta ya bta peck a kumatu da murna shi yace” okay mummy thank you” ya Soma murna harda ma Arun  gwallo zaije Nigeria ya barta…
 Nigeria, Abuja…
Aliyu ya zama babba don, masu fada aji, Wanda kasa ke dama dasu a yanzu, yabar kasumba tsarsar kyaushi yakara fitar,  sai yayi kamar Bollywood actor na Gurmeet Chaudhary, Yana da jikai da tausayi na kasa dashi, ga taimako talakawa, koi’na asanshi, matane Kash baiyi sa’a nagariba.
 Aliyu tun baya bikisu da suhaima, sai yanda tayi dashi,  abinda tace, ya manta da batun Essha kwanta kwanta, tun abun na ba su fawaz mamaki har yadaina Basu mamaki karshe ma zubamishi Ido suke. Gani yanda suhaima ke juyashi son ranta.. yakeyi, dayake ba soyaya Allah bane har wani tsorata yakeji, suhaima duniya ta takeci da tsinke, ta taka duk Wanda taga dama, ba Mai tsawata mata,  yau itane a Wana kasar gobe a wacan..
Suna nema shekara bakwai kenan da aure , suhaima ko Bata wata batayiba,  haydar Idrees, Hafiz duk matasu su haihu, haydar na da biyu, Hafiz da Idrees na daya duka mata, fawaz da Suleiman su ma duk suyi aure da yayya..
Aliyu tun abun bai damusa, har ya Soma damushi na Rashi haihuwa, yanaso  shima
Yaga kwaishi a duniya ,ga dukiya ya Tara ama ba yara daza su Sanya shi nishadin, fawaz yabashi shawara suje asibiti a dubasu, yazo yasami suhaima da zance, ta daburce da Bata taba tunani Rashi haihuwa zai dameshiba, nandana ta Amince tasa abunda ta taka…
Suhaima duk hospital da sukaje kafi suga Doctor  sai ta zangaya ta bribing doctor na,dun yasa Aliyu ne da matsala, wani sirri suhaima da bakusaniba, lokaci da zata cire ciki na hudu maihafata ya lalalace aka cire ciki da mahaifar gabadaya, shiyasa batasan Aliyu yasani, har kasa waje suje don adubasu, dayake Yar duniyace tasan yadan zata shawo kan  doctors su amince, waesu inbasu karbi kudi ba har Basu kanta tanayi don su yarda..
Aliyu  gani duk inda sukaje abun daya yake nunanawa cewa he’s infertile” ba zai haihu ba, yasa  ya yarda yatara komai nashi yabar ma sarki Allah …
Yau ma hajiya binta ne tazo  har gida ta masu Ammi gori Rashi haihuwa da dansu baiyi , harda cewa ita tasan yarta ba juya bace, ita fa tanaso gani jikokita su San yanda zasuyi, sanda Tama su Ammi tas kafi tabar gida cike da matsifa har ta fita ba Wanda ya tanka mata..
Aliyu na gefe Ammi  zaune, Ammi kam ta zuba uban tagumi , Aliyu nata aiki lalashi yace” Ammi kuyi hakuri Kar ku Bari abunda ta fada ya dameku, haka Allah ya tsara min, ga yayya kanena su isheni rayuwa”
A hankali Ammi ta Dora hannuta sama na Aliyu tare da tsareshi da Ido , gani yadda damuwa ta fito karara a fuskarshi , a fili ya sauke ajiya zuciya yakalli Mami  Hadi da cewa ” please Mami kuyi hakuri da halisu, Mami komai Mai wucewa ne”
Mami taja tsaki tace ” tir da hali iri na waena mutani, ba uwa ba ba yarba, Sam Basu San kadaraba , badu Allah ya kadara aure ba, ai kafi karfi wanan mata taka, da Bata gaba Bata baya, mtchewew , Allah na na zai kawo maka sauki”

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements