Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / DUNIYAR FATALE

DUNIYAR FATALE

DUNIYAR FATALE

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 1&2

Gari ya yi shiru sai kukan tsuntsaye da namun dawa kake ji ta kowane sako da lungu, ya zame musu al’ada tunda fad’uwar rana kowa ke ‘kokarin shigewa gidansa ya gar’kame ‘kofarsa badan komai ba sai dan taraddadin abin da zai faru.

‘Kwance nake ina baccin karya saboda ina jiran Kakata tayi bacci na samu kafar da zan samu hanyar silalewa na fita, a kullum zuciyata na ‘kwad’aitamin fita domin na ganewa idanuwana ko wane abu ne ke addabar birninmu, kuma yau na sha ahurin ko sama da ‘kasa za ta had’e sai naga ko me ne ne?.

‘Kakkarfan iska ne ya taso, ba a san asalin ta ko’ina ne yake fitowa, kullum a dai-dai wannan lokaci ne yake tasowa kuma abin ban al’ajabi idan ya gama abin da yake cikin wata tsohuwar majami’a wadda a kiyasin da akayi tayi shekara d’ari ba a shigarta saboda miyagun abubuwan dake zaune a ciki.

in ka dubi sararin samaniya wasai take ko girgije d’aya babu balantana a sa ran cewa ruwan sama ne za su sauko,bishiyoyi sai rausaya suke kamar zasu tashi sama, daga nan kuma sai ga hasken wal’kiya ya game ko’ina, zuwa da’ki’ka biyar komai sai ya tsaya cak! tamkar abin da aka daidaita tare da bugawar agogo.

Bargo na jawo domin rufe jikina sam na kasa ko wani’kwakkwaran motsi ina tsoron kada ta iskeni, a yanda rufin d’akinmu ke jijjiga tamkar zai rufto mana, kai a tunani ma girgiza ‘kasa ce, iskan da ya taso da hasken walkiya ya taimaka matukar gaya gurin, kashemin idanu aci bal-bal din dake haskaka d’akinmu ta mutu marus duhu ya maye gurbin hasken.

Duk wannan bidirin Kakata ko motsi sai ka rantse da Allah matattace.Nikam firgici, tsoro, rudewa babu wanda banyi ba,kwakwalwata ta gaza daukar wannan al’amarin domin ya zarta tunani na tsoro ya ziyarceni ai kuwa sai maganar fita waje ta zamo tashin zance.

Baccin dole nayi wanda sam babu shi a lisafina, amma kan azaba da bala’in dana gani sai gashi ya tafi dani kyaftawa da bisimillah wanda ban shiryawa yi ba, a cikin baccin nawa ne naji an danne min lumfashi idanuwana suka firfito, dole tasa na bude idanuwana wadanda na rufe su ruf!.

Ina tsaye sai Hannun mutum na dinga gani babu alamun gangar jiki a tare da shi, yana tunkaro ni tun daga nesa na dinga kwakwalo idanu,Hakan ya k’ara min firgitar da nake ciki ta ninku fiye da tsammani lisafina ya hargitse min kwakwalwa, har ina k’ok’arin sakin fitsari ba tare da na shirya ba, gumi sosai nake kamar wadda ta had’iye kunama.

Tun ina ja da baya har nakai ma’kura wato karshen bango babu gurin guduwa bakina sai kakkarwa yake inason nayi kuwwar neman ceto ba hali.

Dole na tsaya, bai daina tunkaro ni ba, sannu a hankali har ya zo kusa dani yana fad’ar”Shameeena ki taimakeni zasu kasheni ki agazamun”.’Kara gyara kwanciyata nai bayan na takure jikina guri d’aya tare da rufe idanuwana, gadon da nake ‘kwance akai kuwa babu abin da yake sai jijjiga kai gabaki daya d’akin juyawa ya dingayi sama ta koma ‘kasa, komai ya juye, sai ‘karar kwanika kake ji.

A tsorace na farka wai ashe mafarki ne nake, sanyi naji ta ‘kasana ruwa na ‘bul’buluwa kamar ‘korama koda na duba ashe fitsari ne nayi, na sauke ajiyar zuciya “Wai! duk wanda ke kiran bala’i bai gan shi a zahiri bane.”

Na hau tada Kakata daga nauyayyen baccin da take wanda na yiwa la’kabi da suna baccin mutuwa. Duk abin da ake kai na takaita zance na ko a saman kanta zaka d’ora gangar kid’anka a saitin kunnenta ba za ta farka ba,wai a banza an tsikari kakkausa, Sai in karan kanta ta farka ita kadaice hanyar da zaka samu kafar mu’amala da ita.

Mi’ka tai sannan ta juya wani ‘barin ,tagumin na saka dan ta zame min kamar wata majigi sai minshari take babu kakkautawa can kuma baiyi aune aci bal-bal d’in dake haskaka d’akinmu haskenta ya dawo, har ga Allah daga inda nake ko hannu na bana iya d’agawa balantana ace ni ce na kunna Fitilar “to waya kunna ta?”ga shi kuma idan an kunna haske ya gauraye d’aki can kuma sai a kashe, na shiga tambayar kaina.

Da karfi na shiga dukan Kaka Shamna ina fadan”Ki tashi tsoro nake ji sosai, ki tashi dan Alla….h”kafin na rufe bakina na hango ta cikin wani karamin madubi da ya fad’o na mike da sauri Kaka Shamna ce take kyalkyala min dariya da wad’ansu fararen idanuwanta sun firfito sannan gasu a farare tas ko farin wata albarka.’Kirar jikinta ma ta sauya komai nata ya koma fari tasssss! ko farar takarda sai sam barka.

Hakoranta babu kyan gani gasu da kaifi kamar reza ta zazzagosu zuwa waje, da sauri na kashe hasken fitilar nasa hannuna ina lalaben makwancin Kaka Shamna dan in tabbatar da abin da idanuna ke min gizau amma tana nan inda take ko gizau sai sharar baccinta take..

Tun daga nesa tasa shind’imemen hannunta tana jawoni zuwa gurinta ni kuma ina turjewa, da yake ‘karfi ba d’aya ba, zuwa d’aya tai min sai gani durkushe a gabanta.

Dole ne dangana na dukar da kaina’kasa dan bani iya had’a ido da ita, ta dinga tafiya dani sai wata tsohuwar masarautar garinmu mai dad’a’ddan tarihi muna zuwa kofar ta bud’e muka sa kai.

Iya yanzu sam nadaina jin tsoro girgijewa nayi na mike ina kallon tsarin masarautar lallai an kashe dukiya a cikinta to amma mi ne ne dalilin rufeta har na tsawon shekara d’ari?dole akwai ‘kwakkwaran dalili.Zanen wata kyakkyawar mata na gani wacce ba tada maraba dani tana sanye da sulken ya’ki, murmushi zanen ya fara yi min ba shiri na juya.

‘Kiiiiiiiiiiiii! ‘kofa ta rufe babu hanyar fita sannan wadda ta kawoni tayi ‘batan dabo.

“Kada ki ji tsoro na, ni ce mahaifiyarki ta asali ki zo gareni” matar cikin zanen ta ware hannuwanta alamun na zo.

Ma’ke kafad’ata nayi ko hauka nayi ta ya za ayi naga zanen hoton mutum yana min magana na tsaya? wannan ai ba zai yuwu ba….

“Idan baki zo ba zan kasheki da hannu na”matar dake cikin zanen ta fadi haka.

Hanyar fita na dinga nema ido rufe har wani jiri ke d’ibana, gabana sai faduwa yake, yau nakai karshen ‘kwakkwafi, sannu-sannu naga ‘kofa ta fara bud’ewa Kakata Shamna ce ta shigo da gudu na rungumeta ina kuka jikina na rawa, ta ce”tashi muje wallahi Shameena kunnen kashi ne dake kullum ina tunatar dake cewa ki tsaya matsayinki wannan fad’an ba naki ba ne, amma kina kokarin sa kanki muje”.Ta rika hannuna kamar yar jagora……..Kallonta hakaice nake mata sau tari zantukan da mutane ke fad’a akan Kakata nakan d’aukesa a matsayin ‘kanzon kurege ko kuma ‘kiren ‘karya amma tabbas yau akwai amsoshin da nake bukatar sani….

“Shamna”na kira sunanta dan wani lokaci idan muna wasan jika da Kaka takance na dinga fadan sunanta.

Ta juyo kallon da tayi min sai da na ji y’an hanjina sun kad’a kuma an rufemin baki, dole zancen da zanyi ya ma’kale ya a ciki.

Tsakanin Masarautar da gidanmu tafiyace mai tazara amma sai gashi wai rufe idanunta kawai tayi sai gamu a gidanmu.

Ban koma kan shimfida ta ba dole kan ta Shamna na koma cukuikuyeta nayi in ka ganni zaka rantse da Allah a cikinta zan koma.

Duk na rufe ido sai hoton Shamna ke min gizo a mummunar siffa amma kuma banida halin magana da bakina.

Can kusan kimanin ‘Karfe ukun dare…..

Sharhinku shi ne zai bani lasisin yi muku Typing kan lokaci, in ba haka ku ji kid’an Ganeral a sama🙄 zan koma gefe, a radu nayi kallo.
11/8/20, 10:06 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎✞︎ DUNIYAR FATALE ✞︎☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

1st Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 3&4

Can kusan kimanin ‘Karfe ukun dare zuwa sallar asuba ‘Kwaramniyar mutanen gari itace tasa na samu natsuwa a raina baccin gaba d’aya sai na fasa.

Lokacin fitowar mutane ya yi, sannan ne za kiga kowa yana hada-hadarsa komai namu yana tafiya kan iyaka daga wannan lokacin idan har baka samu damar yin duk abin da za kayi ba sai dai ka dangana wannan dokar sarkin garin ce, in kayi gigin shallaketa sai dai uwarka ta haifi wani, da safe ba muda halin fita. kamar masu zaman kaso.

Amma fa duk wannan dokar Kaka Shamna ba ta shayin fita lokacin da take so, kuma ta dawo lokacin da take so ba wanda zai tunkareta da zancen banza saboda haiba da ke gareta kallo d’aya mutum bai sanin sanda yake sakin fitsari.

Na miƙe makai na d’auko na zuba ruwan alwalla sannan na shiga tada Shamna lokacin fitarta ya yi wanda bansan gidan da take zuwa ba, yau dai nace sai na bi bayanta dan naga inda take zuwa.

Na d’an kai hannuna kan jikinta ina fad’in”Kaka Shamna lokacin fitarki ya yi fa ko yau ba zaki fita bane?”.

Ta bud’e idanuwanta tana kallona nikam da naga abin ya wuce makad’i da rawa sai na dukar da kaina.

Tayi zurum tana karantar yanayi na can na ji ta kira sunana”Shameena shirin bibiyata ne ki kayi ko?”.

Ina cikin d’aura takalmin fatana bansan lokacin dana zabura da ‘karfi ba wannan wacce irin tsohuwace mai gani har hanji?jikina na rawa har hakora na suna had’ewa da juna na ce”wallahi ni gurin farauta nayi ba bayanki zanbi ba”.

Ta ce, “ko da wasa kada kiyi gangancin bibiyata dan zaki ganewa kanki abin da idanunki basa iya gani kunnuwanki basa iya d’auka”.

Na girgiza kaina alamun” to” ba zanje ba alwallata na cigaba da yi.Can kuma me na gani nace mata”Kaka Shamna ba za yi sallah bane”.

“Na yi sallata tun shekara d’ari da suka shud’e saboda haka yanzu ke ce ta zama wajibi a gareki”Daga haka ta gifta ta gabana zauren gidanmu ta nufa.

Yayin da na fara sallah ta,cike da d’okin yau zan ga ko miye ta ke aikatawa a d’akin Allah ya sani sallar ma bansani ba ko raka’a nawa ce nayi, na taƙaita ,zancena duk garinmu ni kad’aice mai yin sallah, nima dai na tashi da son yinta ne, sanda wani maƙwafcinmu na raye ina zuwa gurinsa na zauna ta hanyarsa ne nasan wani abu kafin mutuwarsa, amma fa badan na iya komai ba.

Yau ma hakance ta kasance birin-birin na yi ta saboda hankalina ya karkata da son ganin ‘kwakwaf , tana shiga d’akinta na gado wanda kullum tsakiyar talatainin dare ya zame mata wajibi sai ta le’kasa, kuma tana zuwa ‘kofar ke bud’ewa sannan idan har ba ita, ta bud’esa ba sai dai mutum ya ‘karasa dambarwar shi idan jikin mutum ya gaji da ba’kar wahala ya bar shi.

Sai da na bari ta dad’e da shiga sannan na afka a lokacin wani gurnani ya bayyana, sannan kuma wani hayaki ya soma bayyana, take na kutsa kaina ko tsoro ba na ji.

Ina haki duk na fusata, idanuwana jajur tamkar garwashin wuta, na nufi Kaka Shamna a sannan ne kuma gurin ya soma girgiza, lokaci guda wata dariya ta biyo baya, na ci karo da wata mummunar fatalwa zaune akan kujera, yayin da kuma daga gabanta wata ‘katuwar tukunya ce take tafarfasa, wani tururi yana tashi sama.

Kaka Shamna ta kwashe da dariya mai tsanani , wani yawu na dalala daga bakinta.

“Barka da zuwa Duniyar fatale yake wannan nama nawa, ha’ki’ka ubangijina ya bani umurnin yau nasha lagwada dake, ki sani yau kusan shekarata d’ari ina neman wannan damar domin na kawar da duk wani sauran dangi da ya rage muku a doron ‘kasa”.Kaka Shamna ta fad’a.

Cikin ‘karaji na dube ta”bana tunanin cewa ni kasonki ce domin na wuce ‘karfin ci sai dai ke na halakaki daga ke har shugaban naki kinyi matukar bani mamaki Kaka Shamna ta ya kika zama fatalwa ban sani ba, na zare takobina wanda tsohon makwafcinmu ya bani tun ina yarinya ya ce na ‘boye kada na bari kowa yasan dashi domin zai zame min wata garkuwa a gaba.”

Kaka Shamna ta kuma fashewa da dariya tana mai tand’ar baki. “Ki sani an kawo bil’adama wadanda suka fiki taurin kai na gama da su, balantana kuma ke macce ‘karamar alhaki, na so a ce kin zo lokacin mahaifiyarki da kinga yanda na azabtar da ita”.Ta mike tsaye sai ga fatalwar ta koma ainahin siffarsa ta Sadauki Marhan.

Duk na rud’e gabana ya fad’i har bakina na rawa gurin furta sunansa”Sadauki Mar……ha…n”….da..ma kana raye?”….
11/8/20, 10:07 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎✞︎ DUNIYAR FATALE ✞︎☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

2st Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 5&6

Sadauki Marhan ya fashe da dariya”kina mamakin ganina ko?to ki sani yana daga cikin gadon gidanmu koda mun mutu sai mun dawo cikin duniya mun cigaba da rayuwarmu A duniyar Fatale, burikan da muke son cimma a rayuwa sai mun cika su.

Nayi masa duban ‘kas’kanci sannan na ce”kayi kad’an, kuma ina ka ‘boyemin da Kakata? wallahi duk inda ka ‘boyeta na sha alwashin sai na nemota.”.

“Ki gama bulayinki a banza yanzu zan lakumeki muje mu cigaba da rayuwa a duniyarmu”. Ya fad’a.

Sannan ya zaro dogon harshensa yana barazanar lakumeni, cikin sauri Na kauce sannan na kai masa wawan cafka , daga nan muka fara ba’kin artabu.

Yana son ya kamani, yayin da ni kuma nake ‘kokarin kauce masa.

Ran Marhan ya yi mummunan ‘baci, ya ‘kwalla ‘kara mai tsanani sannan ya daki ‘kasa ya shige ciki.

Na soma ja da baya, ina dube-duben ta inda za ya ‘bullo.

Ban ankara ba sai tsintar kaina nayi cikin wani rame, gangar jikina duk ya shige, kaina ne kawai ya rage a waje hankalina ya yi mummunan tashi.

A lokacin kuma Sadauki Marhan ya tunkareni da azar’babi rufe idanuwana nayi tuni na bada kai bori ya hau.

Matar nan dake cikin zane ce ta bayyana a gabanmu ta samu a tsakiya tana dubana ta ce,”Shameena ina addu’oin da aka koya miki kina nufin a matsayinki na cikakkiyar musulma amma kina yiwa addininki ri’kon sakakanci tir! dake albasa ba tayi halin ruwa ba”.

Jin haka yasa na fara nazari to me zanyi ne tunda ba wani zurfi nayi a addini ba?.

Can na tuna lokacin da nake zuwa gurin ma’kwafcinmu kullum akwai wasu addu’o’i da nake yawaita jin yana yinsu ko da yaushe amma sam bakina ya kasa na furta su.

Cikin iyawar ubangiji na tuna wata gajeriya daga ciki babu ‘bata lokaci na soma karantawa”Bismillahi lazhi laa ya dhurru ma’aa ismuhu shai’aan fil ardhi wa laaa fi samaa’i wa khuwal aliyul azeeem”.

Wani ‘karfi ya zo min ko da na ankara tuni Sadauki Marhan ya yi ‘batan dabo matar nan da na had’u da ita a tsohuwar masarautar garinmu dake cikin zane na gani a tsaye tana dubana.

Daga nesa ta dinga d’aga hannuwanta duka biyu tana jinjina min fuskarta sai murmushi take fitarwa.

Ta ce, “kinyi bajinta y’ata da har na fara tunanin yanda zan kasheki da kaina domin har duniya ta nad’e ba zan iya yafe miki wannan babban zunubin ba.”

Kalamanta ban san a wane mizani zan d’auke su na d’ora ba, wa ce ce wannan fatalwar dake ikirarin itace mahaifiyata?, wadda a kalla za tayi shekara d’ari tsofa duk ya bayyana a tare da ita.Sa’banin ni da nake y’ar shekara Ashirin wannan ai ko a mizani hankali ba zai ta’ba d’auka ba.

Na runtse idanuwana a halin yanzu ba abin da nake mararin son sani da zumud’i fiye da nasan ko wacece ni sannan ya dangantaka ta da Shamna take ko makaho ya lalaba kai tsaye zai fayyace biri har wutsiya.

Da ‘kyar na samu kuzarin magana na ce,” a ina kika sanni kuma ina ne asalina?”.

Hakan yasa matar ta kwashe da dariya, sannan ita ma ta girgiza ta zama wata halitta mai muni, ta ce, “ki zo muje Duniyarmu ta fatale zan nuna muki inda Kaka Shamna take rufe idanuwanki”.

Na rufe kyaftawa da bisimillah sai na samu kaina cikin wata duniya”inalillahi wa’inna ilaihin raji’un”na dinga furtawa duk na firgice addu’ar da nayi a d’azun ko yanzu ma ita ce nake.

Ta juyo gareni”yau ce ranar da wannan takobin dake hannunki zai miki rana kiyi amfani dashi domin ki samu hanyar tsira da rayuwarki, in har ki ka tsaya sanya ina mai tabbatar miki da cewa sai buzunki, domin wannan duniyar babu wani bil’adama dake rayuwa a doron ‘kasa wanda ya ta’ba zuwa a nan”.

“Duniyar Fatale?”na maimaita ina tambayar kaina”Dankari wai kuka gidan mutuwa”.

Matar ta kalleni ta ce” Ki sani yake Y’ata kada ki ji tsoro ko kuma ki razana domun ‘kaddarata tana had’e da taki sannan wannan takobin dake hannunki ina mai sanar miki da cewa kakarki ta yanke sa’ka domin duk wani ya’ki da zaki fuskanta zuwa gaba matukar kika ri’ke addu’a da kuma wannan takobin za ki samu duk abin da ki ke so a duniya sannan babu wanda ya isa ya samu nasara a kanki”.

Nace”Na shiga uku ni Shameena ina zaman zamana na ‘ban’baruwa kaina ya’ki?tukunna ma da wa Zanyi ya’ki ni da ko cinnaka bana iya kashewa”.

Da kyar na samu kuzarin tambayarta na ce”Ya’ki ni da wa kuma dan Allah ki rufamin asiri wallahi ba zan iya rayuwa cikin fatale ba!”.

Ta ce” za ki iya tunda ko yanzu ma duk mutanen garinku da suke rayuwa fatale ne kad’an ne daga cikinsu a bil’adama”.

“Fatale?” cikina ya murd’a ai bansan lokacin da na saki zawo ba.

Ta ce min”kada ki ji tsoro zan taimakeki Y’ata domin ki cikamin wannan burin nawa sannan zan baki labarin duk abin da ya faru dani har na kasance ina rayuwa a duniyar fatale sannan Zamanki a wannan birni hatsari ne ga rayuwarki dole sai kinyi da gaske, kin yaye dukkan wani Hijab…….”

Baki d’ayansu suka mi’ke a razane had’i da zare takubbansu, yayin da haya’ki ya mamaye gurin a lokacin wata Fatalwa ta bayyana mai manyan kawuna jiki d’aya amma kawuna ba adadi nikam na zura da gudu, a lokacin ne ta soma ‘kokarin ganin ta halakani.

Da na ga babu wurin gudu dole na zare takobina nakai mata wawan sara babu ‘bata lokaci tayi sama ko kasa.

Kaka Shamna na hango duk ta galabaita na warware sar’kar dake d’aure da ita ‘ka’ka! ‘kara,!! ‘ka’ka!!! yau ake yinta ta ina zan iya tallabarta.

Sai ga Matar ta fito ina bud’e idanuwana sai a cikin masarautarnan da na ta’ba zuwa a nan ta ajemu ta dube ni sannan ta ce “nan ne kawai zaku iya fakewa ba tare da kowacce fatalwa ta kawo muku ziyara ba.”

Na d’aga mata kaina, nan ta ‘bace muna na dubi Kaka Shamna na ce”Dan Allah ki fad’amin asalina?”.

Ta ce “ba sai kin rokeni ba yau zan fad’a miki ko wa ce ce ke?”.
11/8/20, 10:07 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎✞︎ DUNIYAR FATALE ✞︎☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

2st Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

❀❀❀
༆𝐀𝐥𝐡𝐚𝐦𝐝𝐮𝐥𝐢𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐦𝐚𝐬𝐨𝐲𝐚𝐧 𝐃𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚𝐫 𝐅𝐚𝐭𝐚𝐥𝐞 𝐧𝐚𝐠𝐨𝐝𝐞 𝐬𝐨𝐬𝐚𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐮𝐧𝐚 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐛𝐚𝐫 𝐳𝐮𝐦𝐮𝐧𝐜𝐢 𝐤𝐮 𝐜𝐢 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚 𝐲𝐢𝐧 𝐬𝐡𝐚𝐫𝐡𝐢 𝐤𝐚𝐧 𝐤𝐚𝐫𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐧𝐚 𝐣𝐢 𝐤𝐮𝐳𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐲𝐢 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐭𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠 𝐤𝐚𝐧 𝐥𝐨𝐤𝐚𝐜𝐢 𝐬𝐨𝐧 𝐬𝐨 𝐝𝐞𝐚𝐫𝐢𝐞𝐬.༆
❁❁❁❁

Page 7&8

Cikin dakewa Kaka Shamna ta fara bani labari inda ta soma da cewa”Shekara d’ari da suka shud’e abubuwa da yawa sun faru marassa dad’i , Garin Bardam Allah ya yi masa tarin albarka da kuma Ni’imomi iri daban-daban, Addinin wannan gari namu shi ne musulunci, idan da ace zan tsaya fayyace miki zare da a bawa sai garin ya yi matukar shiga ranki fiye da zatonki.

A kusa da wannan garin namu muna makwaftaka da wasu manyan birane da suke d’auke da wasu azzaluman masarautu har biyu, Ta birinin Gawaisha da kuma arewa maso yamma wato masarautar birnin Gamshan zaluncinsu ya fi gaban a misalta shi.

A tarihin manyan azzaluman masarautu da suka wanzu a doron ‘kasa in har za a lisafa to ina mai tabbatar miki da cewa sai an lissafa da su. Ko da yaushe cikin ya’ke -ya’ke da junansu suke duk dan kowa burinsa bai wuce ya hallakar da d’ayansa,

Daga ‘karshe dai sai da Sarki Shandam ya samu nasarar d’an uwansa wato Sarki Barnabash ‘karfin mulkinsa da isarsa ya ‘karo ninkin ba ninki.

Masarautar garinmu ta Bardam a wancen zamani a lokacin macce ce ke mulkarmu waton Mahaifiyarki mai suna Sarauniya Gunaiza macce mai kamar maza.Sannan shahararriyar maya’kiya ce, na takaita miki zance ita ga baki d’aya jan ragamar mulkin da take tamkar dole ne ya zame mata, ga ta’karama amma sai tarin hikima da hangen nesa da tunani, ba ta cika tsawaita zance ba, sai dai duk ranar da ta bud’e bakinta dole sai an jinjina mata mata. saboda kalmomin da za tayi amfani dasu a tsare kamar wadda aka tsarawa zance.

Ita d’in kaifi d’aya ce sannan duk abin da ta sa himmar yinsa komai wuya da wahala za ta jure, bu’katun talakawanta sune gaba da komai. Ba ta goyon bayan Azzalumi sau tari lokutta ba adadi Sarkin Shandam ya sha ta da d’an aike da wasi’ka ya kawowa Sarainiya Gunaiza wasi’ka, kan ta zo su had’a ‘karfi da ‘karfe su cure guri d’aya domin su kasance tsintsiya mad’aurinki d’aya.

Wai ashe duk cikin makirci ne son yake ya ga bayan masarautarmu daga nan ya had’a gangamin ya’ki. Babu sanarwa sai da abin ya zo gab-da gab! wanka ya zo gaban goshi a sannan ne ya turu mana sanarwar cewa” kodai Sarauniya tayi mubaya’a ta saduda gamida janye kudirinta na ‘kin amincewa da bu’katarsa, ko kuma mu fuskanci matsin Rayuwa”. da kanta ta rubuta masa martanin koda zaiyi dugu-dugu da naman jikinta ya yi masa filla-filla har abada ba za ta ta’ba lamunta da bukatar sa ba.Ta ‘kara da rubuta masa cewa na sha bugu tamkar ganga saboda haka ‘karamin ‘bera bai isa ya tayarmin da hankali ba”.

Bayan Wata d’aya ranar ya’ki ta zagayo Sarki Shandam ya fito yana d’agawa yana furta wasu kalamai na isa da ta’kama yana mai cewa”yau rana ce ta juyin mulki
adadin sakanni da mintunan dake juyawa to sune iya adadin da zan baku”.

Ita dai Gimbiya Gunaiza ko kallo bai isheta ba tayi shahararren gagarumin shiri na fitar hankali”.Kaka Shamna na kawowa nan ta dakata Na dubeta na ce” ya kika dakata kuma?”.

Ta ce”abin da za kiji sai kin matukar tsorata gara ki bari har zuwa lokacin da zuciyarki za ta iya jurewa.”

Wani kallo na yiwa Kaka Shamna”me me ki ka ce?ai wallahi ko wani irin mugun labari ne zuciyata za ta iya jurarsa kawai ki cigaba.”

Ta ce, “to”.

Ta cigaba da bani labari”ranar anyi gumurzu wanda a tarihin ya’ke-ya’ke ba a ta’ba zubar da jini kamar yadda aka zuba a wannan karawar ba.

A lokacin da Sarauniya Gunaiza da kuma Shandam suka fito filin daga, kowannensu ya yi shiga ta musamman ta ya’ki, take aka buga tambura suka zabura kan juna, ‘kura ta tashi sama kallo ya koma sama.

Yayin da gumu ya yi gumu, sai ran Sarauniya Gunaiza ya ‘baci, ta cewa sauran dakarunta”kowa ya mayar da hankali sannan kuyi juyi kamar yadda kuke juya dawakanku.ina maya’kan cikin ‘kasa duk ku fito?”.

Ta koma ‘barin hagunta ta koma cewa”ina maharba?”suka amsa mata da “gasu”ta ce”kowa ya fara ‘barin ruwan kibiyoyi?”.

Sarki Shandam sai murmushin mugunta yake ganin yakai shi ne zaiyi nasara ganin yanda Sarauniya Gunaiza ta firgice, bai san lam’bo ne take masa saboda ya’ki d’an zamba ne.

Daga can ta hangi Baraden Sarki Shandam suma sun fara ‘barin kibiyoyi da ‘karfi ta ce”ga kibau nan zuwa kowa da kowa ya sanya garkuwarsa”.

Sannan ta juyu suka cigaba da gabzawa
A wannan gumurzu Sarauniya Gunaiza ta nuna ‘kwarewarta, cikin azama ta daka tsalle ta kaiwa sarki Shandam sara, shima da yake tsohon ‘kwaro ne da sauri ya kauce , babu ‘karar dake tashi sai na takubba.Nan ta kaiwa Sarki Shandam sara da takobin da ke hannunta, ya hantsila taga-taga zai zuwa ‘kasa ya fad’i matacce.

Ta doka Kabbara tana dukan ‘kirji”ina mayakan suke?bana fada maka ba cewa ba zaka iya dani ba, nasarar wa ce ce?’Karamar alhaki ba za ta iya aikata wannan aikin ba, na fad’a maka cewa sai na karar da mulkinka na zalunci a doron ‘kasa.

Sadauki Marhan yana d’aya daga cikin tawagar maya’kan da sauri ya zo gaban Sarauniya Guzaina ya fad’i ‘kasa”gaisheki dai sarauniyar matan wannan nahiya tamu takawarki lafiya hakika kinyi namijin kokari na kawar da wannan azzalumin mahaifin nawa dole na jinjinawa matantakarki macce mai kamar maza”.

Kowa ya zuba ido yana kallonsa tayi masa wani kallon shu’umanci na kar tasan kar sannan ta ce…..
11/8/20, 10:08 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎✞︎ DUNIYAR FATALE ✞︎☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

3rd Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

༄߷༄
𝐌𝐫𝐬 𝐍𝐚𝐬𝐞𝐞𝐫 𝐢𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐧𝐢𝐧 𝐬𝐚’𝐤𝐨𝐧 𝐝𝐚𝐝’𝐚𝐝’𝐚𝐧 𝐬𝐡𝐚𝐫𝐡𝐢𝐧 𝐝𝐚 𝐤𝐢𝐤𝐞 𝐦𝐚𝐢 𝐫𝐚𝐭𝐬𝐚 𝐳𝐮𝐜𝐢𝐲𝐚 𝐧𝐚𝐠𝐨𝐝𝐞 𝐬𝐨𝐬𝐚𝐢 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐛𝐚𝐫 ‘𝐤𝐚𝐮𝐧𝐚, 𝐡𝐚𝐫 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚𝐫 𝐫𝐚𝐢 𝐒𝐨𝐧 𝐬𝐨.

𝐌𝐚𝐬𝐮 𝐲𝐢 𝐦𝐢𝐧 𝐬𝐡𝐚𝐫𝐢𝐧𝐠 𝐛𝐨𝐨𝐤 𝐚𝐥𝐤𝐡𝐚𝐢𝐫𝐢𝐧 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐫𝐢𝐬𝐤𝐚𝐫 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐤𝐞, 𝐟𝐚𝐭𝐚𝐧𝐚 ‘𝐤𝐨 𝐝𝐚 𝐲𝐚𝐮𝐬𝐡𝐞 𝐤𝐮 𝐤𝐚𝐬𝐚𝐧𝐜𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐚𝐦𝐢𝐧𝐜𝐢𝐧 𝐔𝐛𝐚𝐧𝐠𝐢𝐣𝐢.

 

Page 9&10

Ta ce, “Addininmu sauki garesa sannan ya shar’anta mana ta yanda duk za mu gudanar da tsarin rayuwarmu, ba matsafiya ba ce amma Allah ya horemin tarin baiwa da zan iya gane mai cutar dani farat d’aya saboda haka wannan durkusawar da ka yi min, suna daga cikin muguwar aniyarku ta son ganin bayanmu”.

Sadauki Marhan ya ‘kara kaskantar da kanshi ya ce”ya ke Sarauniyar kyawawan matan nahiyarmu ki sani ina d’aya daga cikin mutanen dake kyamatar halayen mahaifina na zuluntar talakawansa kada ki manta a kowane hali Allah yana fitar da nagari cikin Munana”.

Sai da ya tabbatar da ya saye zuciyar Sarauniya Guzaina nan take ta ce”zan y’anta ka amma ka sani dole ne ka dawo da rayuwa a masarautarmu domin matukar kana zaune a masarautarku zuciyata na bani za ka iya komawa ruwa wato ka koma kan addininku da kuka gada tun Kaka da Kakanni”.

Ya ce”Zancenki dutse dole nasan sai sun yi ta kawomin farmaki a rayuwa dan haka na aminta da wannan shawara taki d’ari bisa d’ari”.

Babban dalilin da yasa Sarauniya Gunaiza ta Aminta da shi cikin sauri sai dan domin cikin sauki ta samu damar da za ta jefi tsuntsu d’aya da dutsi d’aya na farko ta samu ladar jahadi wanda a koda yaushe burinta ta ga Al’ummar musulmi na ta ‘karuwa a doron ‘kasa, romon rahamar Ubangiji da kwadayin tarin ladar da za ta samu ta sanadiyyar gayyatar wani zuwa cikin addinin musulunci lada ce wadda ba za’a iya ‘kirga ta ba.

Y’an tawagarta ganin da su kayi za ta janyo musu ala’ka’kai wanda zai yi sanadiyyar tarwatsa jama’ar birninsu yasa babbar hadimarta ta ce”yake shugabata wannan al’amari akwai bukatar a dubesa ta manhaga mai d’orewa wannan da kike ganin inada tabbacin da wata a ‘kasa, ladabin da yake miki duk na banza ne”.

Guzaina ta dakawa hadimar tsawa”rufemin baki?kina tunanin kan banza zan amince da zamansa cikin birnina dole zai kasance akwai ‘kwakkwaran dalili.”

“Allah ya baki hakuri ya shugabata duk hukuncin da kika yanke za muyi farin ciki sosai sannan mu sanya hannu biyu mu d’auka”.Hadimar ta fad’i haka.

Wani Sadauki shima yace” wannan hukuncin bai cancanta, a matsayinmu na musulmai kada ki manta kafirai ne suka ya’ke mu, wanda suke son ganin bayanmu amma bisa jagorancin ubangiji yasa muka rinjayesu, In har kinyi mini izini yanzu zan d’auke kansa zuwa kasa”.

Ta ce”Dakata indai har ni nake da ikon fad’a aji to wannan maganar na riga na yanke hukunci”.

Da jin haka sai Sadauki Marhan ya fashe da kuka harda turjiya yana mai halin tir da rayuwar Mahaifinsa Sarauniya ta kallesa

“Ka daina zubar da hawayenka duk da bansan abin da ka ‘boye a zuciyarka ba, amma ina son kasa wannan a ranka tunda dai har ka aminta da musulunci shi ne tafarki na gari ko bakada kowa idan kanada ni ba za ka yi kuka ba da izinin ubangijin ‘kaba”.

A lokacin ashe Sarauniya Gunaiza hankalinta ya yi mummunan tashi, yayin da ta ji wani matsanancin son Marhan ya kamata, dan haka ba za ta bari a halaka shi ba tana ji tana gani.

Kaka Shamna ta dubeni fuskarta cike da juyayi tace”A zahiri idan kaga hannu ana cewa baiwa ne, amma wani sa’ilin rashinsa shi ne zai zama mafi alkhairi Sarauniya Gunaiza, abin da ta yi zato sai ya kasance a bai-bai kamar dai azancin maganar nan da ake cewa anyi gudun gara amma an farma zago.”

Aka tusa ‘keyar sauran sadaukai a matsayin bayi daga nan kowa ya watse.Sosai ganima ta samu.

Dama muna da wata al’ada in har akayi ya’ki to duk wanda Allah yaba nasara za a had’e birane su cure guru d’aya sannan a fitar da masarauta d’aya shi ne dalilin da yasa sarki Shandam ya ‘kir’kiri ya’ki dan ta wannan hanyar ce kawai zai samu damar cikar muradinsu.

Masarautar Bardam ta Fad’ad’a sosai a wannan zamani tayi ‘karfin da ba a ta’ba tunanin za ta yi ba.

A ‘bangaren Sadauki Marhan sosai ya kwantar da kansa ganin haka zuciyar Gunaiza ta samu salama har ta sakankance da cewa ya bada kai ne bori ya hau.

Guri na musamman ta tanadar masa sannan ga ababen more rayuwa sai wanda yake muradi.

Ta wanzu tana kula da shi har tsawon sama da wata uku, daga nan kuma soyayya mai ‘karfi ta shiga tsakaninsu Yayin da sauran al’umma suke tunanin ta tabka babban kuskure a rayuwarta saboda ma’kiyi ba abin amincewa bane.

Lokaci yana tafiya aka yi musu baiko ba a dauki lokaci ba mai tsawo ba, ranar Aure ta zagayo anyi buki na ji da gani ranar da Amarya za ta tare wani bakon al’amari ya faru Babbar wata majami’a ta fara girgiza wani sinadarin guba yana fitowa yana shiga cikin jikin mutane haya’ki ya fara tashi sama, ai babu ‘bata lokaci mutanen gari suka fara rubgudun zuwa layi-layi suna wa’kar coci ke hatta manya-manyan shahararrun malamman birnin Bardam wad’anda duniya tayi musu kyakkyawar shaidar tilawar alkur’ani sai gasu suna rawa da waka.”

Cikin al’ajabin zancen Kaka Shamna nace”rawa da wa’ka kuma?to mi ne ne musabbabin haka?.”

Kaka Shamna ta ce,” bakin tsafi ne Marhan ya yi burinsa ya tarwatsa birninmu shi ne ya tayar da fatalwar Mahaifinsa da nufin d’aukar fansa”.

Zufa ya karyomin a jiki nace “fatalwar mahaifinsa?to sai me ya faru? domin na ‘kagu na ji taya haka ya faru..”
11/8/20, 10:09 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

3rd Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*IDAN HAR WANI ƘORAFI KE GA MUTUM AKAN LITTAFINA PLEASE IN A PEACEFUL WAY YA KAMATA YA YI MIN MAGANA, BA WAI ANY HOW BA 08130359515*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 11&12

Kaka Shamna tayi murmushi wanda inada ya’kinin yafi kuka ciwo sannan na ‘kunci ne, ta ce”Marhan ya yi amfani da soyayyar Guzaina da take nuna masa ta rai da numfashi ya cinma muradinsa, shi ke aikata laifi amma kuma a tare da shi ake neman wanda ya aikata d’in.

Washe gari mun samu kanmu cikin wani iftila’i da ya farmana dare d’aya masallatanyenmu sun koma a can ne ake rawar y’an coci da wa’ke-wa’ke kowa na garin ya daina Addinin musulunci sannan anyi da ‘karya anyi da gaskiya wurin gano inda matsalar take a banza sai kara fitowa suke da sabuwar fitina.

Zaki ga mutum na zaune kawai fatalwa za ka fito masa ba wuya idan gungun mutane ne sai kiga duk an watse kafin nan ma d’aya bayan d’aya fatalwar Sarki Shandam ta fara kashe hadimmai idan dare ya yi ko da safiya za ta waye iyaka a tsinci gawar mutum sannan shima in ya mutun fa bawai ya mutu bane shi ma zai fara d’auki d’ai-d’ai ne.
Daga nan fatale suka zame mana annoba a gari.

Kusan tasamma shekara ana abu d’aya babu wani cigaba Sarauniya Gunaiza ita kad’aice musulma saboda kariyar da ubangiji ya ba ta kuma a sannan ne aka haifeki, ko fuskarki ba ta gani ba ta miko min ke a lokacin ta fad’amin wasu maganganu masu kama da wasiyya ta ce min”na kula mata dake na baki kariya” ta ‘kara da cewa “na tsaya miki a al’amurranki tamkar yadda nake tsaya mata yanzu tayi mummunan mafarkin daya canza mata ‘kaddarar rayuwarta babu tantama akwa yiyuwar iftila’in daya farmata zai iya farma y’arta”ta mi’ko min ke kina cikin jini na fita har na kai kofa kuma sai na dawo sam na kasa barin tilon y’ata cikin wannan halin da kyar na dakewa zuciyata, dan kada ayi haihuwar guzuma uwa kwance y’a kwance.

Na fita waje gari ina neman mafaka can na samu wani babban kogo a
cikinsa ne na samu mafaka na cigaba da rainonki.

Ban koma birnin Bardam ba sai da kika shekara goma ko da naje na samu labarin abin da ya faru a wata ranar lahadi”.

Cike da shaukin son jin labarin na ce”sai ma ya faru koma?”.

Kaka Shamna ta girgiza kanta, tana son furta wani abu amma ta kasa sai kuka ta fashe dashi.

Lallaminta na dinga yi har na samu zuciyarta ta sanyaya nace”Kaka ba sai kin cigaba ba tunda wannan labarin tamkar yana tayar miki da tsohon ciwonki ne ki barni nasan abin da zanyi kawai”.

“A’a Shameena kinada bu’katan sanin ko wacece Sadauki Marhan shi ne mahaifinki sannan Sarki Shandam shi kuma yana ansa sunan kakanki”.

Haka kawai na tsinci kaina da furta”ke kuma fa ya alakarmu take?”.

“Ni uwar mahaifiyarki ce ina matsayin ‘Kuyangar kakanki sarki Lamnad na goma sha tara, Sarauniya Gunaiza ita kad’ace tilo a garesa bayan dad’ewar da yai Allah bai bashi haihuwa ba sai a kaina.”

Na dubeta”Allah sarki wai ma na tambayeki?”.

Ta gyad’a kanta na ce”ya akayi baki mutu ba har yanzu bayan naga duk fad’in birnin nan ke kad’aice tsohuwa mai yawan shekaru kusan zancen ‘karni d’aya ake fa?”.

Kaka Shamna ta ce”Har yanzu da sauran kurciya a tare dake dan ban karasa miki sauran labarin ba ne”.

Na tunzuru baki irin wasan jika da Kaka nace”to ba kece naga kina shirin fashemin da kuka ba”.Na karashe fad’ar haka ina mai tur’bune fuskata.

Dakuwa tai min a kai tace,”Shameena badai wayo ba haka itama mahaifiyarki take”.

Na kai dubana ta sosa min inda kemin kaikayi nace”ni dai to ki karasamun labarin”.

Kaka Shamna zamanta ta ce, “To kamar yadda na fara baki labari ba wai kuma nasan ha’ki’kanin gaskiya bane sai dai nasan Arwan bazai ta’ba bani labarin daba haka yake ba”.

Nace”Arwan wani tsoho fari mai haiba, yana da jiki, kuma gajere, mai yawan ibada shine ya fara koyar dani addinin musulunci kuma ya bani wani takobi mai kyau lokacin har da cemin ya yi zai bani wani labari washe gari ko da naje gida gawarsa na rataye a kofar gidansa?”

Kai tsaye Kaka Shamna tace min “A ina kika san shi Shameena?babu makawa Sadauki Marhan ne ya kashesa”

Nace “lah! kin manta wannan makwafcinmu da nake zuwa wajensa”.

Kaka Shamna tace”Allah sarki ban gane shi ba”.

Na dinga kallonta “to wai tsaya har tsawon wane lokaci na d’auka ina rayuwa da fatalwa a matsayin Kaka Shamna?”Akwai babban ‘kalubane a tare dani kenan.

Bayan tafiyata dake a ranar wata kora ce ta mamaye birnin ko tafin hannu mutum ba zai iya gani ba duhu yace salamu alaikum a ranar masifa da kata’i ba wanda ba a gani ba Yayin da Ko’ina ya fara girgiza ashe fatalwar Sarki Shandam ce ta shiga cikin Sadauki Marhan ya tunkari Sarauniya Gunaiza babban burinsa ya shafe labarinta kan doron kasa daga nan suka fara gabza ya’ki kamar ba gobe.

Can jini ya fara zubuwa da kuma wasu sassan jikin Sadauki Marhan ko da’ki’ku basu yi a ‘kasa su kayi ‘batan dabo wata tsawa kawai da harguwar mutane, daga nan kuma sai komai ya yi d’if.

Gari ya yi shiru sai kukan namun dawa mutane kuwa sunyi sama ko ‘kasa babu labarinsu har zuwa yanzu da nake baki wannan dad’addan tarihin”.

Na fiddo idanuwana waje”to suna ina?”

Tace”wannan amsar tambayar har zuwa yanzu ba wanda zai iya baki ita danginmu gaba d’aya daga ni sai ke muka rayuwa, ko shi nasan saboda lokacin bama cikin birnin ne, sai bayan wasu shekaro aka tsinci wasu gawarwakin mutane sai kuma wad’anda keda sauran ‘kwana a gaba, sun dawo suka koma kafa wata daular zalunci tamkar dai ta Sarki Shandam”

Na mike tsaye jikina har wani girgiza yake Kaka Shamna sai kallona take dan gaba d’aya halittar jikina sauyawa tayi gashina ya barbaje sai huci nake nace “sai me ya faru kuma?”…
11/8/20, 10:09 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

4, Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*IDAN HAR WANI ƘORAFI KE GA MUTUM AKAN LITTAFINA PLEASE IN A PEACEFUL WAY YA KAMATA YA YI MIN MAGANA, BA WAI ANY HOW BA, DAN BA AJENI YA YI BA DA ZAI BANI ORDER 08130359515*

Mom Afnan da kuma Maman jidda mai neman d’an rakiya idan za ta shiga Band’aki sannunku matsorata ina jinjina. Au! na manta ke Maman Jiddda&Bilkis yanzu kin zama jaruma dake zamu kafta a filin daga. Maman Oummi kema fa ki shirya dan ke ce zan wakilta a madadina.😛

Dole nayi godiya Preety Umma nagode sosai da ‘kauna.

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 13&14

“Ni fa ba na son kina wannan abun shi kenan babu damar ayi miki zance sai ki tashi zuwa tayar da hankali”.Kaka Shamna ta katseni, ina! nikam tuni nayi nisan kiwo bana ganin komai har na fara hango kaina a filin daga. Ina kad’awa y’an maza gumba.

Ta ce”ki natsu za muyi magana ta fahimta ai ba zan hanaki d’aukarwa mahaifiyarki fansa ba to amma abin tambayana a nan da ga wa za ki d’auki fansa yanzu?Fatale ko miye?”

Sai a lokacin na dawo cikin hankalin kaina nace” lallai na tabka babbar wauta kuma ai kamata ya yi na bari har naji ‘karashin labarin”.duk wannan zancen cikin ,zuciyata ne nake yin sa..

“Ki natsu nayi alkawarin ko da zan rasa rayuwata ne zan tsaya miki ke kad’aice wadda ta ragemin da idan na kalla zanji sanyi a rayuwata amma fa..”

“Amma me?”

“Bakomai kawai dai ina tsoron abin da zai biyo baya ne kada kema su kassaraki”.

Nace”Haba dai Kakata ta kaina idan kika karaya ai na shiga uku kece fa fitilata”.

Ta kaimin duka”wacce fitila shekara d’ari da d’oriya ai na kusa tafiya ‘kabari”.

Dariya ta kumeni wai ashe da gaske ne ko cikin manya wani lokaci idan su ka fad’i wata magana ko yaro d’an shekara goma yakan tsaya shayin furta irinta.

Nace”Lallai ma Kaka Shamna!”na fad’a a tsigar mamaki”kina ina yaron da yake cikin mahaifiyarsa ajali ke riskarsa kawai dai a cigaba da lalla’bawa har a cimma adadi”

“Na ji to”.

Mikewa nayi na fara zazzagaya masarautar kusurwa da lungu ina ganin abubuwan al’ajabi dama gani da son ganin ‘kwa’kwaf ai sai na ‘kara bubbud’esu ina cire ‘keyar idanu.Na furta kai na zaune bai ga gari ba yanzu wannan makekiyar Masarautar amma a rasa wanda zai iya mulkarta amma dai anyi Y’ay’an iska”.

Garin yawace-yawace na can na tsinto kaina cikin wani tafkeken d’aki mai ado inata mamakin ance shekara d’ari tana rufe to ya akayi komai yake sabo dal tamkar yanzu aka sanya shi hmmm! da wata a ‘kasa dai.

Na ji ina sha’awar ‘kwantawa kan makeken gadon dake da’kin Aljannan duniya kenan, masu kud’i na haskawa.

Mafarkin Sadauki Marhan nayi yana min gargad’i kada nasa kaina a cikin wannan bada’kalar domin ba zan ci riba ba, na mayar masa da martanin cewa” Wallahi fad’a da kai yanzu na soma sannan dole sai ya nuna min inda ya kaimin mahaifiyata”.

Ban gama maganar da nake ba ya ‘bace min da gani, a rud’e na farka daga baccin wanda mafarkin Sadauki Marhan tun ina ‘kan’kanuwata na soma yinsa amma ban ta’ba ganin fuskarsa ba sai a wata rana ya fitomin cikin siffar tsoro da d’imaucewa.

Gumi na min tsiyaya nasa hannuna ina shafewa a raina na kudurta tunda fa har na fara mafarkinsa yanzu lallai yana gab! da zuwa, dole Kaka Shamna ta ‘karasamin labarin nan domin na fuskanci madafa”.

Na mi’ke ina layi dan sam kafafuwana sun gaza d’aukata inda Kaka Shanma na nufa tana nan a zaune inda na barta na dube ta

“Kinyi sallah kuwa?”

“A’a” Ta fad’a kai tsaye..

Na koma tambayarta

“Me ne ne dalilinki na ‘kin yin sallar?”.

“Na manta yanda ake yi ne”.

Na dafe ‘kirjina shin kin yi me? ko dai ba Kaka Shamna ba ce?”

Ta ce, “Wannan ba abin mamaki ne idan har ki ka ji dalilin da yasa”.

“To gayamin yanzu ina sauraro?”.

Gyara zamanta tayi har za ta fara bani labarin na ce dakata bari har nayi tawa sallar domin daga yau ba zan koma wasa da addinina hasken rayuwata ba”.

Da nayi neman ruwa ban samu ba dole sai taimama nayi ko da na gama sallar tawa bacci ya shureta abin da nake nema kenan Majami’ar nan nake da burin zuwa da Kaka Shamna ta bani labari, wanda dama ba tun yau nake da kwad’ayin le’kata ba.Sai yau dama ta samu.

Nan na tsaya ina tunanin ta wacce hanya zan samu na fita, dan kam aiki ya sameni, ai kuwa na dinga le’ka ‘kusurwa-‘kusurwa har Allah yasa na dace da wata kofa mai azabar nauyi a yanda na ‘kiyasta ‘katta majiya ‘karfi mutum goma suka d’ai ne zasu iya wangaleta sai ga shi cikin da’ki’kun da basu kasa biyar ba na bud’e haske ya shigo tass! har yana kashemin idanu.

Babu wani tsoro ko fargaba na tunkari gurin tsit! ka ke ji kowa yana ma’boya duk da yana safiya nace “kai wannan wace irin rayuwa ce wadda mutum baya da Y’ancin kansa.”

Ina tunkarar gurin na ji ‘kasa ta fara girgiza wasu halittu na kaida kawo a sararin samaniya.

Haka na cigaba da cusa kai har na isa gurin take ‘kofa ta bud’e tsoro naji har zan juya daga bayana na ji wani sauti wanda sai da hantata ta kad’a ana fad’in lale Marhabun! a *DUNIYAR FATALE* sannu da ‘karasowa Sarauniyar bin diddigi da tone abin da ya shuɗe”.

Jikina ya fara mazari na d’aga kafata da niyar komawa aka hankad’a keyata cikin Majami’ar ‘kofa ta koma tamkar ba a ta’ba bud’eta ba.

Na mike ina kakka’be korar da ta rufemin idanu.

Da kyar na bud’e idona “me zan gani?”Wai ashe kan ‘kabari ne nake
Zaune ta ‘karkashina naji sanyi yana fitowa ‘kabarin ya soma jijjiga bishiyar dake kusa da shi ta rabe gida biyu nan wasu fatale suka fara fitowa tamkar yanda kudan zuma ke rufe mutum haka suka yi min dafifi a kai.

Cross d’in dake kan ‘kabarin ya fara fad’uwa kasa daga nan kasa ta buɗe…
11/8/20, 10:11 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*@AYSHART647*
4, Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*IDAN HAR WANI ƘORAFI KE GA MUTUM AKAN LITTAFINA PLEASE IN A PEACEFUL WAY YA KAMATA YA YI MIN MAGANA, BA WAI ANY HOW BA, DAN BA AJENI YA YI BA DA ZAI BANI ORDER 08130359515*

*FANS KU FARA SHIRI TUN YANZU DAN ZAN FARA NA’DA WA’DANDA ZAMU JE FILIN DAGA YA’KI A DUNIYAR FATALE DUK WADDA KEDA TSORO TUN YANZU NAYI BARAM-BARAM DA ITA JARUMAI NAKE SO IRIN MAMAN JIDDA MACCE MAI KAMAR MAZA😉*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 15&16

Wani ‘katon mutum ya bayyana tsirara sumar kansa tana ja har ‘kasa akaifunsa zaram-zaram.

Su ha’kora ba a ma maganar su domin ba su da maraba da gyaturra duk sun zazzago, ko zago sai sam barka.

Da fari har na dumfaresa cikin dakakkiyar zuciya, sai kuma tsoro ya ziyarceni.

Ya tunkaro ni gadan-gadan fitsari bansan iya adadin da nayi ba yau kata’i, masifa, bala’i duk babu wanda ban gani ba.

Suna zuwa dab! dani kowanensu ya ja tunga ashe babban na tafe bayan wancen da ‘kasa ta tsage ya fito.

Wannan kam lokacin da zai fito tuni na fita hayyacina nayi suman wucin gadi.

Sanda na farfad’o sunyi min da’ira babu ‘bata lokaci na ji kaina ya fara juyawa ina tangad’i tangal-tangal na zube a ‘kasa.

Gabad’aya suka fara dariya mai
Mugun sauti.

Sai sunyi kamar su kamoni sai kuma su kuma ja da baya.

Ta bayana na ji gurnani ya karad’e ko’ina wai ashe Sadauki Marhan ne sai murmushin mugunta yake min.
ya d’aga ni sama sannan ya dire timmm! a ‘kasa.

Kan rudewar da nayi bansan lokacin dana tunkaresa ba, ina ‘kokarin cimmasa yana ‘kara yi min nisa daga karshe ya tsaya cak! yana min wani shu’umin kallon mai cike da tsana wutar fansa na dad’a ruruwa a zuciyarsa ba zai ta’ba manta kisan walakancin da Gunaiza ta yiwa mahaifinsa ba.

Abubuwan dana shud’e suka dinga dawo masa tamkar a sannan ne abin ya auku, duk fa wannan bidirin da ake halittar nan da ‘kasa ta tsage banga fuskarsa ba dan sumar kansa gaba da baya duk ta rufe fuskarsa.Ya dakawa Marhan tsaya” ka dakata wannan ya’ki na ne domin ni aka tozarta aka rushemin martabata.

Ya bud’e fuskarsa”innalillahi wa’inna ilaihin raji’un! ya subhanallah!”na dinga fad’a

Kamar kada na furta haka sai suka dinga ja da baya wasu har suna komawa inda suka fito.

A sannan ne na samu natsuwa na tuna cewa wad’annan fa basa iya yimin komai tunda ina tare da ubangiji, in nace kuma zanyi fad’a dasu wuya kawai zan fuskanta ko kuma na jigata ne tunda su ba aljannu ba kuma su ba bil’adama ba,kamanceceniya ne su kayi da aljannu ta wata manhagar.

Na tuna da wata addu’a da na ji Arwan yana yawan karantawa koda yaushe na tambayesa ko ta mi ce?nan ya fara warwaremin zare da abawa muhimmancinta da kuma tasirin da take a rayuwar wanda ya lazimceta.

Yake cemin”ita wannan addu’ar idan mutum ya karanta ta ko da acikin makabarta ne zaka iya zuwa ka ‘kwanta abinka da izinin ubangiji har ka farka Babu abinda zai same ka, na cutarwa sannan kaida ma’kiyinka zai gina maka ‘katangar ‘karfe matukar kayi imani da shi.

Na fara karantawa” *A’UUZU BIKALIMATILLAHI TAMMATI MIN-SHARRI MAA-KHALA’KA*”.

Fatalwar Sarki Shandam ta dubi Sadauki Marhan a fusace ya fara sauke masa ruwan bala’i kai me yasa karamin aiki zai wahalar da kai me na fad’a maka game da zancen Ahalin Sarauniya Gunaiza?”

Ya nuna ni da hannu ya ce”kana d’aukar wannan yarinyar a matsayin ‘karamar alhaki ko?tabbas sai ta zame maka turmin tsakar gida sha lugude, wannan tafi karfinmu, tukunnan ma ba cewa nayi ka karkatar da hankullansu su daina bautar ubangijinsu ba”.

Sadauki Marhan ya karkatar da kansa a d’aya gefen ya ce”Duk wata hanya da zanbi domin ganin na ‘batar da tunaninsu nabi ‘karshe ma Ita Shamna da na kasa samun damarta daga ita har wannan yarinya mayar dasu duwatsu nayi shekararsu kusan d’ari a haka bansan ta yanda akayi suka dawo siffarsu ta mutane ba”.

Cikin zuciyata nace”ohho! shi yasa kenan Kaka Shamna nake mamakin ya akayi kowa ya mutu amma banda mu?hakan na nufin kenan tsafacemu ne ya yi, amma dai anyi ba’kin mugun ne ai kuwa allah ya hutar da Kaka Shamna yanzu na samu salamar cewa da mutum nake rayuwa.”

Sarki Shandam ya ce”to ai kaga babbar wautar da kayi na barinsu a doron ‘kasa tunda an samu wanda ya ‘kwance su, yanzu sai ka saurari abin da zai biyo baya, sannan zan gargad’eka kada ka koma damun ruhina tunda na mutu ka barni na sarara”.

Yana gama fad’ar haka ya juya da nufin komawa cikin ‘kabarinsa da gudu Sadauki Marhan ya riko, Sarki Shandam ya ‘kwalla ‘kara mai tsanani sannan ya daka tsalle da gashin kansa ya d’aure Sarki Shandam lokaci guda ya fara aman wasu ruwa masu tsananin d’oyi daga bakinsa wuta na tashi sama

Nikam duk ilahirin halittar jikina kad’awa take na kira ruwa da kaina kai wani bin diddigi bai yi ba a rayuwa kana zamanka ka jawowa kanka jangwam.

Gefe na koma dan yanzu y’ar kallo na zama tunda Allah ya ceceni reshe ya juye da mujiya mugun nufinsu ya koma kansu.

Kana nufin me? duk ahurin da nayi ina jiran zuwan wannan ranar zaka tarwatsamin lisafi to bari kaji rayuwa a *DUNIYAR FATALE* yanzu muka soma ta, kai bama abin jin dad’inka ne ba ace ka mutu amma kana rayuwa a duniya, kada manta ni keda alhalin duk wani motsin da kake a *DUNIYAR FATALE* har duniya ta nad’e ba zan ta’ba bari Birnin Bardam ya samu zaman lafiya ba dole sai na wargaza duk wani jin dad’insu”.

Nace”karya kake duk wani mugun nufinka da sannu zai koma kanka”.

Ya saki Sarki Shandam ya nufu ni ko d’ar banji ba na tunkaresa gaba da gaba.

Ya fincikoni tara da sha’keni na dinga kakarin mutuwa amma fa duk bai kashe bakin tsanya ba na dinga sakar masa maganganu masu zafi da ‘kona.

‘Kirjina na duka sannan nace masa
koda zaka rika guntsirar namanka ba fa zaka tsira ba zaka dawwama cikin takaicin Sarauniya Gunaiza a tunaninka ka kawar da ita ko? bari ka ji ni shameena, Saina zame maka bakin kumarci takamarka tsafi ni kuma da Addu’a na dogara sannan tunda ka bari mahaifiyata ta samin suna tun kafin a haifeni ka jira fansa…
11/8/20, 10:12 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
* AYSHART647*
5 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*IDAN HAR WANI ƘORAFI KE GA MUTUM AKAN LITTAFINA PLEASE IN A PEACEFUL WAY YA KAMATA YA YI MIN MAGANA, BA WAI ANY HOW BA, DAN BA AJENI YA YI BA DA ZAI BANI ORDER 08130359515*

*ASIYA SARKIN TSIYA FANS SOSAI NAKE SONKU, YASEEN A KANKU ZAN IYA CINYE KAZA ‘DAYA SHARHINKU NA MATU’KAR BURGENI. KU CIGABA DA GASHI SUYA SAI RAN SALLAH. Y’AN TEAM ‘DIN MARHAN KU MATSU KUSA ZAMU FARA KOYON SABABBIN DUBARUN YA’KI.KO DA YAKE AI NASARA TAMU CE WAKE IYA JA DA FATALE.?😜*🤣

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 17&18

“Fansa?”Sadauki Marhan ya komai maimaitawa ba yabo babu fallasa ya zuba mata idanuwansa masu kama da na mujiya dama Allah ya hore masa idanuwa sannan ga cikar zati da moruwa da wannan dama ya ja hankalin Sarauniya Guzaina har ta afka tarkonsa.

Na fara mutsu-mutsun kwance kaina daga garesa amma na kasa in banda ni da abina taya ma za ayi ‘karfina ya kasance d’aya dashi wannan mai siffar samudawa ga tsawa sannan kaurin jiki ma ba a barshi a baya ba.

“Ka sake ta nace”

Sarki Shandam ya fad’a da ‘karfi yana mai lalabar wuyansa gurin da Sadauki Marhan ya sha’kesa.

Marhan ya juyo ya ce “idan na’ki fa?”

“Za ka ga abinda zai biyo baya kasan ni, Na sanka karewa ma ni ne mahaifinka duk wani rauninka na sani duk kanwar ja ce kar tasan kar”.

Da naga wankin hula na iya kaini dare na ce”bari na gwada hilarmu ta mata dan na samu hanyar fita kada Kaka Shamna jarababbiya ta tisani a gaba”.

Na fashe da kuka na nufi Sarki Shandam ina zuwa saura tako d’aya na isa gurin sai na dakata” ah to ina zan iya kai kaina a wahala”na ayyana a zuciyata.

Marairaice murya nayi ina kuka nace”Kaka Shandam kayi masa magana ya fita a rayuwata ko banza shi mahaifina ne bana son yin wani abu da zai tozartar da shi”.

Yasa shantamemin hannunsa nufinsa wai ya tayar dani ai kuwa nikam baya na dinga komawa yo! ina zan bari ya ta’bani ina ganin wannan halitta ace fatalwa ta ta’bani da an sha kallo dan ban sanin sanda nake fecewa.

Ya ce”zo jikanyata kinsan ni ne Mahaifin babanki ba zan cutar dake ba, ina kaunarki sosai kuma zan taimaka miki ki gano inda mahaifiyarki take”.

Na dubesa daga baya kenan kar nake kallonsa da harda kyaftawar da ya yiwa Sadauki Marhan na ankara son suke su ruftani na ce”akwai kitimirmira fa kofar fita kawai nake nema kafin su ‘kaddamarmin”.

Marhan a fusace ya cewa Sarki Shandam”karka wahalar da kanka ba wanda ya isa ya canza min abin da na tsara”.

Sai kuma ya kwashe da dariya mai tsanani”daga yau kada ka koma yunkurin wannan tunani domin yin hakan kawai zai ku’butar da kai daga sharrina”.

Sanin da nayi tabarmar hauka da hauka ane nad’eta nima sai na zame musu y’ar tanyon shanu ciri dariya na dinga yi babu sassauci.

Sarki Shandam har yanzu bai daina mi’komin hannunsa ba yana fad’ar”Ki zo mana bazan cutar dake ba zan baki wani sirri wanda za ki iya amfanin dashi gurin ya’kar Marhan”.

Ai ina jin ya furta haka bansan lokacin dana fara tafiya ba, sauri-sauri gudu-gudu saboda hauka da kurciya irin nawa da kuma kurciya wai ni dole zan samu lagon karya ma’kiyina.

Har na kusa kai garesa ina masa murmushi shima a ransa ashe murmushi samun nasara ne yake.

Cikin kudirar ubangiji sai ga wani haske ya bayyana ko’ina ya haskaka ai sai naga suna ja da baya suna ‘kokarin guduwa mamaki na dinga yi lallal falalar ubangiji da yawa ta ke.

Sautin Muryar Sarauniya Gunaiza ya karad’e gurin har tsoro ya kamani a zuciyata sai addu’a nake ina fad’in” *YA GHALIBU*”har babu iyaka fatana Allah ya bani galaba a kan wad’annan makiya Allah da har yanzu basu san Annabi ya Fako ba.

Ta fara magana da gautsi dodon kunnena tamkar zai fashe sosai na ji dad’in ganinta a raina nace “to bari na kauce fad’an na manya ne ina dariyar ‘keta banza ta samu.

Da hannu d’aya ta yafito ni lokacin da na jera kusa da ita sai na koma wata gajeriya muka jera.

Ta soma magana ba yabo ba fallasa dama Sarauniya Gunaiza ita bata cika dariya ba saboda kada a rainata duk wani halin Mahaifinta Sarki Lamnad shi ta ‘kwaso dubarun ya’ki ba wanda zai nuna mata su, ta wannan ‘bangaren ta d’aga tuta a zamaninta sosai ake shayinta bata d’aukar wasa, sannan duk abin da tasa a gabanta da kyar kaga Allah bai bata nasara ba.

Ko yanzu da take fatalwa duk wani wani zalunci bada ita ake ba, musamman y’an tawagarta har had’a ‘karfi suke domin ya’kar Sadauki Marhan suke, amma abin ya ci tura,dan Marhan ya d’aureta da sar’kar ta tsafi ta yanda bata iya wani ‘kata’bus domin d’aukar fansa.

“Har abada musulunci shi ne mad’auki ko ka’ki ko ka so, kafirci kuwa makaskanci, ka daina ganin yanzu Allah ya lamunce maka kana tsula tsiyarka yanda kake so akwai ranar kin dillanci, ranar d’aukar fansa, sannan kai a tunaninka wannan ‘ikon ka ne da kake cutar da bayin Allah ba laifin zaune balantana na tsaye?lallai ka sauya tunani domin duk musulmin kwarai dole sai Allah ya jarrabesa a rayuwa dan ya gwada karfin imaninsa, ina son kasan da cewa”Ta dakata nikam tunda ta fara jawabinta nake la’be a bayanta ta jawoni a tsakiyarsu ta direni….

“Wannan yarinyar sai ta shayar da kai ruwan mamaki kuma na godewa Allah da yasa albasa ba tayi halin ruwa ba”.

Sadauki Marhan ya yunkuru yana son kawo mana farmaki amma tufafin da take sanye dasu haskensu ya kashe masa idanu baya iya ganin komai sai lalabe yake.Nan ya fara lailayo ashar yana ‘kunduma mana

“Shameena!” ta kira sunana da karfi na d’ago fuskata tace…
11/8/20, 10:12 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
5 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*IDAN HAR WANI ƘORAFI KE GA MUTUM AKAN LITTAFINA PLEASE IN A PEACEFUL WAY YA KAMATA YA YI MIN MAGANA, BA WAI ANY HOW BA, DAN BA AJENI YA YI BA DA ZAI BANI ORDER 08130359515*

*JET RECOVERY MY PINKY.😭 CONGRATULATION HABIBTY MRS BASAKKWACE ALLAH YASA KIN FARA SABON BOOK ‘DINKI A SA A.*

Bismillahi Rahmani Rahim

 

Page 19&20

Ta ce, “Zo muje”.

Daga haka sai ta rufe idanuwanta bayan ta rungumeni tsintar kaina kawai nayi kan wani tsibiri mai ban sha’awa da burgewa tsirrai sunyi kore shar! na ji tamkar ta barni nan na cigaba da rayuwata inda ba tsana balantana tsangwama.

Kukan namun dawa kad’ai ke tashi sai tsuntsayen dake shawagi a sararin samaniya can na hango wasu tantabara suna sumbatar junansu bansan lokacin da nayi murmushi ba.

Sarauniya Guzaina ta tisa ni a gaba tana kallona tana mamakin tsananin kamanceceniyarta da ni, tabbas jini baya ‘boya.

Ta katseni min tunani ta hanyar cewa”Ki bani aron hankalinki ta hanyar amfani da kunnuwan basirarki domin ki ji zancen da zan gaya miki”.

Nace “to ina saurarenki”

Ta matsu kusa da inda nake zaune ta har jikina na gugar na ta, gaba d’aya yanzu na daina tsoronta duk da nasan cewa fatalwa ce.

Ta ce, “Duk yanda za kiyi kada ki yarda wani ya koma hawa kan karagar mulki idan bake ba, sannan daga yau in har kika koma za ki bud’e dad’addiyar masarautarmu da wannan azzulumin ya yi sanadiyyar rufewarta”.

Nace “kamata ya yi ayimin takaitaccen bayanin dalilin da yasa aka rufeta”.

Ta dubeni” zan baki labari da duk wani ‘karin bayanin da kike bu’kata saboda na baro Birnin Gamsha suna shirin zuwa domin su haye karagar mulkin nan sannan suma azzaluman gaske sunfi Tsatson Sarki Shandam waba’i”

Na kwalalo idanuna ana murna an rabu da bukar sai gashi an haifi abu .

“Bangane inda kika dosa ba? taya wad’annan mutanen suke aikata haka? rashin imani ya yi ‘karanci a zuciyarsu kowa kwad’ayin ya samu ‘karfin ikon da zai iya cutar da masu rauni?”

Na fad’i haka muryata na mugun rawa.

“Za ki gane zuwa gaba amma dai yanzu haka na baro su kan hanya a kiyasin da nayi tunda akan dawakai ne suke saura Awa goma sha biyar ya rage musu da su ‘karaso Birnin Bardam kiyi duk yanda za kiyi domin ki kwato mana masarautarmu wadda tun bayan mutuwata aka rasa wanda zai maye gurbina”.

“Ya akayi kika mutu? kuma Saboda me?na samu kaina da tambayarta.

“A ya’kin da muka yi ni da Marhan mu kayi mutuwar kasko sai tsintar kaina nayi ina rayuwa a *DUNIYAR FATALE*”

Ta nisa sannan ta, ce”Amsar tambayarki ta biyu duk wanda ya hau kujerata Fatale ne ke addabarsa, masarautar ta zama sansanin zubar da jini Marhan ya riga ya tsafeta babu wanda ya isa ya hau karagar mulkin ba tare daya kassarashi ba, shine dalilin da yasa aka rufeta baki d’aya da nufin sai bayan shekara d’ari sannan za a koma bud’eta duk wanda ya samu nasarar shigarta kafin zuwan lokacin shi ne zai kasance mallakin wannan kujerar. Farkon zuwanki a wannan masarautar nice na jawo ki, Shameena kada ki watsamin ‘kasa a ido ki tallafi masarautarmu da kuma addininmu birnin Bardam ya dawo tamkar yadda yake a farko daular musulunci cibiyar addini “.

Nace”akwai matsala kuwa”.

“Shameena! dole ke ce zaki yi wannan ya’kin, dole ke ce zaki zama garkuwarsu ki fitar da su a tsananin duhun da suke ciki”Sarauniya Guzaina ta fad’i haka zuciyarta cike da rauni har tana ‘kwalla.

A yanzu kam duk na gama fahimtar dawar garin Nace “Wallahi! Wallahi!! sai na yanka musu kazar wahala kuma sai sun figeta.”

“Yawwa! haka nake son ji Y’ata muje na tayaki gyaran masarautar”.

Nace”To”.

Kamar yadda muka zo haka muka koma sai tsakiyar masarautar ta direni Har yanzu Kaka Shamna Bacci take.

Na ‘kwa’be mayafin da na rufawa kaina nan take kyaftawa da Bissimillah har mun gama gyara komai tsab-tsab.

Ta umurceni dana je na wangale babbar ‘kofar masarautar kai tsaye nace mata”taya zan iya bud’e wannan ‘katuwar ‘kofa?”.

“Ai kuwa dole sai ke zaki bud’eta sabuwar sarauniyarmu ta wannan lokacin”.Ta ‘karashe fad’ar fuskarta na d’auke da murmushi samun nasara.

“Kofar na nufa ina cike da alhinin yanda za ayi na iya bud’e shin wai halan ta zaci nima fatalwarce.?

Zuwa d’aya nayi mata aikam sai gata na bud’eta, haske ya mamaye min idanu birnin da yake kullum safiya tamkar dare ya haske duk ya ‘bace.

***
A can cikin gari mutane fad’uwa ‘kasa suka dinga yi wani haske na fita a jikinsu kowa tamkayar kansa yake me ke faruwa haka gari ya yi haske? kafin mutum ya kai ga samun amsa shima ya zube ‘kasa.

 

*Comment ya fara ‘kasa dan haka zan dawo shafi d’aya a rana idan baku gyara ba, Kid’an genaral a sama, ko na aje al’kalamina na zama y’ar kallo za’bi ya rage gareku.*
11/8/20, 10:12 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
6 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*Thank So much My Nimcy luv sharhinki ya matu’kar ‘kayatar dani , godiya da jinjina Allah ya ‘kara rufa mana asiri.*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 21&22

***
Gabas ga birnin Bardam wasu matafiya ne ke tafiya kan dawakai cikin sahara da sai yanzu suke danasanin zuwa da dawakai tunda sahara ce rakumma sune suka fi cancanta.

Bayi na d’auke da wata y’ar rumfa kamar d’aki wadda akayi mata adon gaske ko’ina sai walwali take.

Sautin zantuka ke tashi daga ciki alamun akwai mutane da yawa a ciki hatsaniya kawai suke kowa fuskarsa tamke rayukka duk sun ‘bace manya sadaukai ne masu ingirman jikunkuna mutum biyu farare tas! sai ka rantse sun had’a jinsi da larabawa ko kuma turawa.

Sadauki Zamnad yana zaune ya d’auki kafarsa d’aya ya d’ora kan d’aya ya dubi abokin hatsaniyar ta shi fuskarsa a d’inke ya ce”ta ya kake ganin zamu nemo Shameena idan har mun isa Birnin Bardam”.

Barde Hamnad Ya kara gyara zamansa ya fuskanci Sadauki Zamnad ya ce”a iya yanda boka ya siffanta mana ita yanada matukar wuya mu iya ganeta to amma akwai wani abu da zanyi matukar ita tsatson Sarauniya Guzaina ce zata bayyana kanta.”

Zamnad ya furzar da iskan bakinsa” amma dai har yanzu na fuskanci ‘kurciya ke damunka Hamnad ta ya za ka tsaya wani tsohon daya kusa mutuwa har dan ya fad’a maka zance za ka yarda? ”

Barde Hamnad Ya maida hankalinsa kacokan a kan Sadauki Zamnad yace”ban gane ba! kana nufin ka ji lokacin da muke maganar?”

“Eh!”ya ba shi amsa kai tsaye.
Sannan ya ce”awanni nawa suka ragemana mu ‘karasa?”.

“Ba zai wuce minti ashirin ba” .
Barde Hamnad ya fad’a.

Mamakin duniya ya ishi Barde Hamnad taya akayi har ya yi sakacin da Sadauki Zamnad ya ji wannan sirrin? gaskiya akwai ‘kamshin gaskiya ga zancen da mahaifiyarsu ta fad’a masa dole sai ya tashi tsaye kan Sadauki Zamnad kada jan ragamar birnin Bardam ya koma hannunsa, sanin
sanin kan shi ne duk hilar Zamnad ba zai iya yi masa wayo ba. Amma ta yanda ya fitar da sautin zancensa kuma gaskiyace zallarta.

Dama haka suke tun suna yara kowa yana ganin damar wani. Abin ban al’ajabi kuma mahaifiyarsu d’aya.

Zamnad ya dubi Hamnad wanda ya fad’a ‘kogon tunani ya katsesa ta hanyar cewa “kar nake kallonku daga kai har matar da take amsa sunan mahaifiyarmu wannan ma babbar shaida ce, da ta nuna min kowa yafi son d’an da ya haifa a cikinsa. Ko da yaushe zuciyata na bani ba ita ce mahaifiyata ba. sannan bari ka ji, ni ba kwad’ayin mulki nake ba, yaudar da kuka yi min ce yasa na ji ina kwad’ayin mulkin a yanzu.

A gadarance Hamnad ya ce”Wani sa’ilin yakan zamu gaske idan kayi mafarki kadaina cika baki marar ‘karfi sai kuri sannan lokaci ne kawai zai raba mana gardama”.

Daga nan kowa ya d’inke bakinsa a daidai sannan ne kuma suka ‘karaso babbar ‘kofar da zata sada su a cikin birin, tunda babu mai tsaron kofa shigewa kawai su kayi ciki, Yayin da suka yad’a zango a masaukin da suka tanada Barde Hamnad Da kuma Sadauki Zamnad kowa ya ja y’an tawagarsa zuwa gefensa yana shawarar ta yanda zai nemo Shameena wadda za ta bud’e musu ‘kofar masarautar bokayinsu sun riga da sun siffanta musu yanda yarinyar take sannan sun basu tabbacin wanda duk ya yi nasarar ha’duwa da ita shi ne zai haye karagar mulki.

***
Sai bayan wasu da’ki’ku suka fara farfad’uwa amma fa kowanensu halittarsa ta juye. A bakin Masarautar sa’ka ta yanke gindin kaba, dan kuwa jerawa su kayi tamkar yadda ake jera kibau a cikin gidanta dan’kari.

Bayan na bud’e ‘kofar masarautar hankalina duk bai kai gurinsu ba na sake komawa a inda nabar Kaka Shamna har yanzu dai ko motsawa ta kasa yi na zuba mata manya idanuwana ina nazarinta “babu makawa wannan baccin bana lafiya bane”na furta a sanyaye.

Rangadi na shiga yi kowacce kusurwa ina lekawa har nakai wani shashe mai matukar kyau, kofar shiga a bud’e, cusa kaina nayi ciki yayin da na ci karo da wasu kayan tsafi masu muni,’kiiiiiiiii! ‘kofa ta fara tafiya a hankali har ta rufe hankalina na wani guri sautin rufewa kawai naji gagab! da gudu na dawo gurin ‘kofar ina kiciniyar bud’eta.

k’wak’walwata kwancewa tayi, na zurfafa tunani na ko da zan iya samun wata dabarar bud’e kofar.
Duk basirata dana kore na rasa mafita d’aya wadda nake ganin zata fiye min sau’ki, don haka na zage har da shan d’amara a ‘kuguna nasa iya k’arfina ina son na bud’e k’ofar ta kowane hali.

Aikin banza harara a duhu dan jin nayi tamkar an dasa wani kwad’o ne an datse kofar ta waje ne.

A sukwane na kurma ihu na soma yi mai sauti wai ko za’a kawo min d’auki amma shiru kake ji kamar maye ya ci shirwa.Inbanda hauka irin tawa wa nake tunanin zai ji sautin nawa tunda mu biyu ne kad’ai a duk fad’in wannan masarautar kuma Nayi imani da har yanzu Kaka Shamna Bata farka daga baccin mutuwarta ba.

Juyawata keda wuya da nufin na koma tunda na rasa mafita ai kuwa sai bakin gani nayi.

Akan kujera nayi arba da wata mummunar halitta dogon mutun ‘kakkarfa bak’i wuluk zaune akan kujera tsirara bayada maraba da fatalwa ga wasu hi’ka’k’kun ha’kora guda biyu jal acikin wangalelen bakinsa bakinsa yana murmushi yace min,

“Dakata kada kiji tsorona mutun ne d’an adam tamkarki,kada kiyi ‘ko’karin guduwa domin duk inda kika tafi kafata kafarki.”

Ina rawar jiki nace masa”to”.

Ya nuna min gefen gadon dake d’akin umurni ya bani kan na zauna.

Na dinga waige-waige can idanuwana suka kai kan madubin ba shiri na mike tsaye saboda banga fuskata ba, wata halitta ce ta daban…
11/8/20, 10:13 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
6 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*HI! FANS SARKI AND ‘BOYAYYEN SIRRI IS STILL TRENDING, TRY TO SUSCRIBES, KUN SAN DAI YANDA MSS FLOWER DA KUMA CHAMSIYA LOUALI RABO SUKA KWARE WURIN BAJE KOLIN BASIRAR DA ALLAH YA BASU.DAN HAKA SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA.😜*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 23&24

“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un kada dai ace nima na zama fatalwa?a iya sanina fatale ne kawai, ko da sun duba madubi basa iya ganin kawunansu”har na fara kidayar kaina a cikin fatale shi kenan nima tawa ta ‘kare.

“Kada ki razana ni mai taimakon ki ne, amma bisa ga wani sharad’i”

“Wane irin sharad’i kenan?”Na fad’a a zafafe.

Ya karkatar da kansa”sharad’in shi ne” Me zai hana ki yarda ki aureni, na rantse da rayuwar mahaifiyata ni kuma sai na mallaka miki wannan birnin da dukkan ‘karfina da kuma sihirina”.

Nace masa”Bana bukatar haka ya kai wannan mutumin ba kwadayin mulki nake ba babban burina bai wuce ace wannan birnin ya kasance tamkar yadda yake a farko ba”.

Yace”Haka kika ce?”

“Eh! Sannan ba gudu ba ja da baya saboda ni bana zance biyu”.

Ya kalleni cike da kallon so da ‘kauna, sannan ya soma magana.

“Yake masoyiyata ki sani na dad’e ina tsimayin jiran wannan ranar da zanyi ido hud’u dake”.

“Masoyiya!? so da ‘kauna!?”na maimaita ina tambayar kaina”oh! ni Shameena na zama rabon fatale da matsafa kuma”.

Ni wallahi sam yanzu abubuwan ma sun daina bani tsoro ko fargaba yanzu dariya suke bani, dan haka ko yanzu ma d’in dariyar ce nayi ina nuna sa da babban yatsana.

Da yaga na maida shi d’an bushin leda hakan yasa zuciyarsa ta harzu’ka, ya nufu ni gadan-gadan sai jin kaina nayi ya rungumeni tsam! a jikinsa a lokacin kuwa zuciyata tamkar ta fashe nake ji, kan tsananin d’oyi da hamamin da yake tashi a jikinsa.

Nasa hannuna da nufin na rufe hancina ashe ya ankara ya kwa’beni da sauri.

Da naga yana ‘ko’karin ya sumbace ni da mugun bakinsa mai kama kashi a sannan ne na harzu’ko masa da ‘karfi na kifar dashi.

Ba shiri nace “na amince”.
Ina gama fad’ar haka yana sakina.

Ajiyar zuciya na dinga saukewa babu sassauci zuciyata sai tashi take.Na gyara tsaiwana.

Ya katseni”Me ki ka ce?”

“Yanda kunnanka ya jiyo”.

Cikin zuciyata nace” Tab! da kamar wuya”.

Yau jin yake tamkar an dam’ka masa makullin aljana a hannunsa ance masa ya je ya shiga, duk tsawon shekarun da ya d’auka yana jiranta kamar a mafarki sai gashi ta amince masa ba tare da wani turjiya ba, Lallai dole ya ‘kara godewa Sadauki Marhan domin ya iya haihuwa.

Wannan zankad’ed’iyar kyakkyawar budurwa yau itace matsayin mallakinsa?.

Ai daga nan sai bakinsa ya bud’e ya dinga zuba fad’i ba a tambayeka ba,
shi kan dole ya samu tsuntsu daga sama gasashshe

“Wato kin gane lokacin da na yiwa mahaifinki wani aiki nace masa”tunda babban aiki ne to dole ya bani tukuici mai tsoka sai yace min “duk ranar da matarsa ta haihu kin zama mallakina tun daga lokacin nake tsimayin zuwan wannan ranar”

“Aikin me?”na tambayesa.

Shiru ya yi dan sai alokacin ya gano ya tabka babban shirme aikam sai ya sha mur! sannan ya ce”wannan ba huruminki bane.”

Nace masa” to na ji”

“Ko kefa! bana son yawan tambaya dama ko ‘yan Adam kun cika bin diddigi ki tsaya matsayinki”.

Mutumen ya kwashe da dariya, ya ‘bace daga shi har kayan tsafinsa.

Da naga ya ‘bace sai na dinga jan kafafuwana, inka ganni tsab! za ka rantse ni gurguwa ce, sam gaba d’aya na kasa d’aga su da rarrafe nakai gurin ‘kofar ina ta’bawa abu kamar tsafi sai gata ta bude.

Na fito wai ashe tuni har dare ya tsala take na kiyasta awowin da Sarauniya Guzaina ta fad’amin kenan ba’kin sun iso.

Bakina ba abin da yake furtawa sai addu’a ina fad’ar

“*WALLAHU GHALIBUN ALA AMRIHI*”.

Sosai hankalina ya koma tashi, da har na samu karfin gwiwa farat! d’aya wannan mutumen ya dagulamin lisafi.

Maganarsa na dinga maimaitawa tamkar wadda ya fad’awa karatu aka bawa umurnin sai ta haddace ta .

“Mu ‘Yan Adam?kenan karya ce ya min daga farko sanda ya ce min shi mutum ne? Lallai na ‘kara zurma kaina Aure da wannan halitta wannan ai da ganinsa ya fito ne acikin tsatson aljannu ne?”.

Kaka Shanma tunda ta farka bata ga Shameena ba ta shiga muguwar damuwa a fili ta furta”Wannan yarinyar ta cika neman fitina”.Gyara kwanciyarta kawai tayi tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwan kan duka, yarinya sai tone-tonen masifa.

Jikina a sanyaye na koma inda na bar Kaka Shamna d’akin dana shiga har bacci ya tafi dani ko yanzu can na nufa.Sallolin da ake biyata na rama.

Ranar na ci kuka mai isata, ga kuma tunani cankas a raina har zuwa lokacin da bacci ya yi awon gaba dani, shi maganar abinci ko maganarsa ba ayi dan ba wani damuwata ya yi ba.

Tun da na idar da sallar Asuba nake zaune zugum, komai na duniya ba ya min dad’i sam!.

Muryar Kaka Shamna naji daga bakin ‘kofa tana fad’in

“Ke Shameena”.

Da sauri na mike ina fad’in “Na’am.”

Ta ce, “Amma dai daga yau ba zaki koma zuwa farauta ba ko?”.

“Tir’kashi”na fad’a ina murmushi”Kaka Shamna kin ta’ba ganin wanda ya kai kansa ma’kabarta?”

Ta, ce”A’a!”

“In kuwa haka ne kinga nida zuwa farauta mutu kan raba ki jirani yanzu zanje na dawo”.A dawo lafiya tayi min.Nasa kai zuwa fita daga masarautar.

Har yanzu jama’ar gari suna nan bakin masarautar tun jiya bambanci d’aya yanzu sun farka halittarsu ta dawo daidai.

Da ganin na fito duk suka duka ‘kasa”an gaisheki sabuwar sarauniyar birnin Bardam takawarki lafiya Allah ya kauda idon makiya”.

Banbarakwai namiji da suna Hajara hannu kawai na d’aga musu, na d’aure fuskata dan kada su ga damata tare da cewa” nagode kowa ya wuce na sallamesa”.

A tare da juna suka furta”Mun gode ranki ya dad’e” daga nan kowa ya sani inda dare ya yi masa.

Nikam a nan suka barni ina al’ajabi da tunani can naji kuwwar mutane suna fad’in”Ku gudu! Ku gudu!!”.

Kafin na ankara tuni tsikar jikina ta fara tashi halittata ta fara sauyawa jikina ya dinga kwayewa sai……
11/8/20, 10:13 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
7 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*Alhamdulillah today am plus 1 ya Rabbi Allah ya ‘karawa rayuwarmu albarka,ka bamu lafiya da zama lafiya. Sannan kasa mu shiga aljannar firdausi badan halinmu ba.*

*Jinjina da ban gajiya ga duk wad’anda suka hanawa idanuwansu bacci domin kawai su tayani farin ciki da murnar zagayowar wannan rana Nagode sosai Allah ya bar ƙauna.*

*MEERAN MAMA SON SO NAGODE DA SHARING.*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 25&26

Jikina ya cigaba da ‘kwayewa na tabbata da wani zai ganni babu shakka guduwa zai yi saboda sauyawar halittata.

Ban gushe a nan ba sai da na samu kusan minti talatin ina tsaye na kasa d’aga kafata ina kallon ikon Allah.

Kuwwar da mutane keyi har yanzu itace ta cigaba da karad’e kunnuwana,ina nazarin me zai sanya su wannan kuwwar ana zaune kurum?.

Ga biki ya tashi amma babu zanen d’aurawa yau duk diddigina sai dai na zubawa sarautar Allah ido.

A masaukinsu Sadauki Zamnad firgicewa su kayi abinka da d’an baka sababa nan aka shiga aikin kallon kallo akuya kallon kura, matsorata ne na’kin karawa dan acikinsu idan ka cire Zamnad sauran ba suda maraba da mata maza.

A rud’e Barde Hamnad ya kai kallonsa ga d’an uwansa yana fad’in “ya ya za muyi kenan d’an uwa?”.

Me Zamnad zai yi idan ba dariya ba yau uban alfahari da cika baki shi ne ke tambayar shi yadda za su yi?abin mamaki bai ta’ba ‘karewa duniya.

Da ya fahimci kan gaskiyarsa yake dole ya daidaita kansa, ya ‘kome dariyar a ciki, sannan ya ri’ko hannunsa yana mai dadda’bar bayansa, aikuwa take ya ji natsuwa na sauko masa.

Da ya dawo hankalinsa, ‘Kwace jikinsa Barde Hamnad ya yi daga jikin Zamnad d’in yana wani cin magani, shi dai bai koma bi takansa ba, ah to! kur’bi ya riga ya ‘bata sha babu wani sauran girma.

Ya shirya domin fita zuwa cikin gari, sosai yake son sanin duk wani sirrin birnin da kuma ta yanda za ayi ya mallaki Shameena a yadda boka ya siffanta masa ita ya ce masa”Gaggausar macce ce doguwa sannan tanada idanuwa matsakaita komai nata cif-cif tamkar ita ta halicci kanta.

Ta ‘bangaren kasuwa ya fara zuwa komai shiru babu kowa ya dinga mamaki to ina jama’ar garin suka shiga ko ana nufin basu tashi daga bacci bane?.

Gurin yawonsa har hanya ta biyo dashi a masarautar garin tun daga gininta har zuwa yanda tsarinta yake sosai tayi matuƙar kayatar dashi masarautar ta gargajiya ce amma fa komai ya ji a fili ya furta “wajen masarautar kenan ina ga cikinta”kwarai ya zaku ya samu kafar da zai shiga wannan masarautar mai abubuwan ban al’ajabi.

Wannan yana d’aya daga cikin babban dalilin da yasa ya amince da zuwa birnin arayuwarsa yana matu’kar son ganin ire-iren abubuwan tarihi.

Hankalinsa duk ya tafi wani guri karo ya ji ya yi da wani abu, sai ya d’ago ai da gudu-gudu sauri-sauri ya fara ja da baya..

Yarinyar tayi matu’kar razanar da shi sosai halittarta keda ban tsoro.

Daga inda nake yanzu na daina jin abin da nake ji d’azun fuskata ce kad’ai nake jin tana min zafi da kuma zugi tamkar wadda ta fad’a a ruwan zafi.

Na bishi da kallo ina tunanin” to me ya razanar dashi har haka?

Cikin tausayawa Sadauki Zamnad ya dubi Shameena ya ce”Sannu baiwar Allah?”

Nace masa”Banida lafiya ne aka gayama?”

Dariya ma ta bashi wlh ga rabin fuskarta a ca’be wai amma shi take tambaya halan ba tada lafiya ne.

Na fusata ganin ya ma raina min da wayo ya dubi gudar Sarauniya amma ya dinga yimin dariya lallai sai ya fuskanci horo mai tsanani.

Tsawa naji an dakamin wadda na rasa daga ko ina ne, na juya da nufin komawa cikin masarautar farautar ma na fasa zuwa zuwa Sarauniya Guzaina ta rufe min hanya dole na tsaya.

Ba kida hankali ne da zaki shiga masarauta a gabansa yana d’aya daga cikin ba’kin dana gaya miki zasu iso”.

Na zaro idanuwana waje harda dafe ‘kirjina alamun na razana Sarauniya Guzaina ta ce “ki koma gurinsa kada ki yadda ya fahimci ko ke wacece saboda ya’ki d’an zamba ne, koda wasa kada ki bashi wata kafar da zata nuna masa cewa ke ce Shameena”.

Na amsa mata da “to”.

Ta sake cewa” d’azu rabi mutane rabi kuma fatale ne suka zo gaidaki ba ainahin mutanen garin bane”

Nace “fatale kuma?”

“Eh! sune mutanen garin Sadauki Marhan ya ‘boyesu a wani guri amma kada ki damu ina iyakan ‘ko’karina zan san yanda za ayi domin na gano ainahin inda ya ‘boyesu.”

Ta ce “ki koma gurinsa a yanzu”.

Na gyad’a kaina sannan na koma
juyawa zuwa gurinsa tamkar yadda ta umurceni wanda har yanzu yake a tsaye inda na barshi.

Shi dai mamakin duniya ya ishe shi wato bayan lalacewarc’barin fuskarta harda ciwon hauka ke damunta? kwarai ta bashi tausayi.

Ina kai gurinsa na zube kukan kissa na soma ina fad’ar dan Allah ya taimakamin banida kowa a garin nan bakuwa ce ni”.

Ya kalleni”to nima fa ba d’an gari bane zuwa nayi amma wane taimako kike bu’kata ne?”.

Bakina na rawa nace masa”masauki nake nema daga nan zuwa kwana biyu kafin na samu nawa”.

“Bakomai muje”.

“To” nace masa da sassarfa nabi bayansa dan yana shirin ‘bacemin saboda saurin tafiya ne dashi.

Cikin Masarautar Sarauniya Guzaina ta koma da zama a matsayin Shameena saboda kada hankalin Kaka Shamna ya tashi.

Da muka isa masaukin idona kuri! akan komai na bazasu,ba laifin gurin ya yi bala’in ‘kayatuwa na musamman bayi da hadimma sai kallonmu suke haka muka ratsa ta cikinsu, wani da’ki na mussamman ya kaini an kawatashi da gadon bono na al’adar garinmu.

“Ga masaukin nan sai kiyi hakuri da yanda kika samesa nima ba d’an gari bane”.

Na marairaice fuska”ai bakomai nagode sosai Allah ya biyaka da gidan aljannah”.

Ya ce”Aljannah kuma ina ne haka?”

Rausayar da kaina nayi na ce”Affuwan na zaci kai musulmine”.
ban k’arasa fad’an haka ba sai juyawa naga ya yi, ya fita.

Na koma d’akin ina fad’in “Allah yakai damo ga harawa ko bai ci ba ya yi birgima da sannu zan bankad’u duk wani shiri naku…”
11/8/20, 10:14 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
8 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*Dan Allah Fans a dinga yi mana uzuri, wani lokaci ba a son ranmu ne muke ‘kin yin typing ba, beside nayi muku update d’in safe na marece ne bai samu ba, Fisabilillahi amma sai ku zageni.Duk da haka nagode da ‘kauna domon ita ce silar haka, son so na ke muku .😭*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 27&28

Sai da na bari dare ya tsala sannan na fito rangadi tun kafin na afka cikin wannan cakwakiyar sana’ata kenan burina a ko da yaushe ba zai wuce naga abin da ban saba gani ba.

Diddigi da jawa rai wahala lambata ce.

‘Kus!’kus!! na ji, zance na tashi sama, na ce”abin nema ya samu Y’ar gidan Malammai da cikin shege”.

Da sand’a na dinga tafiya dan kada a ji takuna.

“Me ka ke nufi boka? duk yanda za ayi ka bincikomin ainahin yadda siffar wannan yarinyar take na yi al’kawarin ko da za a zubar da jini ne masarautarmu dole sai ta zama mallakina”Zamnad ya fad’a cikin ‘konar zuciya har jiyojinsa sun nuna shati.

Boka ya ce, “Ka ga matsalarka kenan saurin fushi da nuna hasala kamata ya yi ka kwantar da hankali nka “.

Na kwantar da hankalina fa ka ce?
ba ka ganin yadda Hamnad ke raba ido kullin burinsa ya samu kafar da zai kifar da taurarona”.

Dakata min wannan ba abin tada jijiyoyin wuya bane kada ka manta
taurarinka sunada matukar haske da wahala a samu mahalun’kin da zai sha gabanka”.

Wani munafikin murmushi Sadauki Zamnad ya yi.

Sai da Boka ya tabbatar da hankalin Zamnad ya dawo jikinsa sannan ya ce,”Maganar yarinyar nan tabbas inaji a jikina tana a kusa da kai saboda haka kada kayi sake wani ya yi maka sakiyar da ba ruwa”.

‘Dan ‘kara siffantamin yanayinta?”Sadauki Zamnad ya fad’a da sauri.

Boka ya koma zayyana masa Zamnad ya girgiza kansa” ba ita ba ce”.

“Wa kenan?”

Ya ce, “Ka manta kawai wata nakasasshiyar yarinya ce na had’u da ita kuma ko hanya basu had’a ba”.

“Kada fa garin kallon ruwa kwad’a ya maka ‘kwafa ina jiye maka abin da zai je ya dawo”.

Zamnad ya ba boka amsa”Wannan ‘kwad’on ko kallo ba zai isheni ba balantana ya min kwafa”.

“To shi kenan amma fa ka kula da duk wani motsin wannan yarinyar banganta ba, amma zuciyata tana bani cewa akwai wani ‘boyayyen sirri dake tare da ita, shawarata anan ka tsaurara matakai sannan duk wani motsinta ya kasance kanada wata masaniya a kan shi.”

Ya ce, “Zan kiyaye”.

‘Kara baje kunnuwana nayi ina kwasar rahotu Allah ya yiwa Sarauniya Guzaina albarka da tayi wannan dubarar kenan duk lalabe ne take cikin duhu yanzu ne za a buga wasan mai rabo shi ne wanda zai kai labari.

Nayi haka na juya sai na ‘barar da wani abu da bansan ko mi ne ne ba?da gudun tsiya na soma gashi akwai tazara mai yawa kafin na kai d’akin da ya sauke ni”.

Cafkeni kawai naji anyi,
“Haba yarinya gudunki ai ba zai amfanar dake ba, duk inda kika shiga sai na ganoki duk la’ben da ki ke mana ina hankalce dake dan gani nake har hanji”Boka ya fad’a yana mai yi min murmushin ‘keta.

Na zube ‘kasa wallahi ranka ya dad’e fitsari ne naji kuma gashi bansan inda ba d’aki yake shi ne na fito ko zan samu wanda zai nuna min”.

“Karya ki ke la’be dai ne kika zo yi mana , baki san hanyar band’aki ba amma kinsan ta d’akinsa ko?”

Zamnad shikam tsareta ya yi da ido yana mata kallon tausayi, shi indai mutum yanada wata nakasa nan take zai shiga zuciyarsa, yanzun ma ba ‘bata masa rai tayi ba.

Da ‘kyar ya bud’e bakinsa tamkar wanda aka tilastawa dole sai ya yi magana na yarda da ita ba za tayi mana abin da kake rayawa aranka ba boka.”

“Ka fa yarda da ita?”.

“Eh!”

“Shi kenan na tafi nidai”.

Ya ce, “Sauka lafiya.”

A tara muka je ya nuna min ‘band’aki na shiga wanda dama karya ce na zabga saboda ina neman mafita.

Bayan na gama na fito ina zancen zuci ashe ya fito fili, a tunanina wallahi har ga Allah cikin zuciyata ta ne.

Bai fita ba samun guri ya yi, ya zauna abinsa dan akwai tambayoyin da yake so ya yi mata game da birnin a matsayinsa na bako.

Bai fahimci zantukan da nayi ba Kalmata ta ‘karshe kawai kunnensa ya jiye masa.

“Me ki ka ce?”

Ina walainiya da idanu yau ‘karya ta ‘karewa d’an kada.

Na ce” Bakomai wallahi”.

“Ban yadda dake ba
kin yi min ‘karya, irin wannan ‘karya har haka? akwai sirrin da ki ke ‘boyo?”

Na ce”Ba abin da nake ‘boyo wallahi kunnuwanka dai ne suka jiye ma haka”.

Ganin za ta raina masa da hankali ne yasa ya mike tsaye tare da zare takobinsa daga cikin gidansa”Ko ki fad’amin ala’karki da masarautar Bardam ko kuma na fille miki kai yanzu za’bi ya rage gareki na baki minti biyar kiyi shawara da zuciyarki idan ba haka kima yau cikin daren nan za ki ba’kunci lahira?”….
11/8/20, 10:14 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
8 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*’Yan Wattpad son so, Dejerleen Nagode da ƙauna, wai ashe dama ke marubuciya ce? jinjina a gareki.*

*My taƙwara a cigaba da voting ko a ji kiɗan Genaral a sama lol.*😂

*SARKI AND ‘BOYAYYEN SIRRI HAR YANZU ANA TURURUWAR SIYA, KU HANZARTA DOMIN KU SAMU NA KU RABO.*😝

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 29&30

 

“Sarauniya Guzaina fa kika ce kin santa ne?”

Na girgiza kaina”A’a a fili ban santa ba sai dai a labari kuma wallahi ko kasheni za kayi wallahi babu abin da zaka samu dan bansan komai akai ba”.

“Fita daga d’akin nan”

Na kallesa” ina zanje a wannan talatainin dare ka tausayamin badan halina ba”…

Na rantse da ruhin mahaifina dole sai kin fita bana zama da munafiki ko waye dole yau sai kin bar nan. tun farko tausayinki ne yasa na zo dake”.

“Yanzu ina tausayin nawa ya je da har za ka kore ni kan abin da zuciyarka ke raya maka?kamata ya yi sai ka tabbatar da samun natsuwa sannan za ka yi min wannan tambayar”.

“Korafinki bai ‘kar’bu ba?”Ya fad’a ba wani shayi.

Na yi murmushi har kumatuna suka motsa na ce “In kaga belbelu sun zauna cikin ‘yan uwansu belbelu dole akwai ‘kwakkwaran dalili kada ka kore ni watakila akwai amfanin da zanyi maka zuwa gaba.”

Ya ce,”Idan ba zindi’kanci da da’ki’kanci ba ta ya za ki had’a kaina dake?

Alfahari da isa ba zai amfanar da kai komai ba, dama za ka sanyawa rayuwarka salama kujerar Sarauniya Guzaina duk cewa ta fi ‘karfin dubunnan sadaukai wanda har ya yi sanadiyyar rasa rayukansu, ba a ja da ita, mafad’aciya ce ko rina albarka zakanya ce sannan kunama ce dafinta yafi wuta ‘kona. Ka lalla’bani zan nemo maka mafita kasancewar sirrin wannan birnin a tafin hannuna yake”.

“Keee!!!” ya dakamin tsawa wanda ya zagi jaki dole ne ya fuskanci fushin jakkai.”.

Dariya ya bani sosai abin tsoro kura a rumbu Macce ‘kwara ɗaya tal! kuma matacciya sai ita ce za ta gagaresu?Allah ya wadaran naka ya lalace.

Na kallesa sosai ya tsora min ido “Kai! kus, kus! wannan irin kallon mayu fa, in maye kake ka ci kanka, ka sha ruwa da bakin tulu”.

Na mazaya ina rangwad’a kwanciyata nayi a kan gado.

Na karashe zance na da fad’an” duk wanda ya kona rumbu yasan da cewa inda toka za ta kwana”

Ya ce, “Tsab! zan iya salwantar da rayuwarki na zauna da bokaye na ji irin maganganunsu matsafan duniya babu wanda bai sannni ba.Amma na zamu musu kangaran gwani” .

“Shawarar da zan baka kada kayi wasa da damarka domin sau d’aya take zuwa a rayuwa, da za kayi hakuri ka barni watakila zan zame maka jigo kan abin da ka ke nema”.

“Me nake nema?”

“Ohon! maka wannan kuma ai kafi shege sanin hanyar tasha”.

Sosai na zaburar dashi har abada ba zai ta’ba yarda ya mutu da fushin Barde Hamnad ba

Na ce masa”Ka jira har ka ga yanda al’amari zai kasance yanzu na ‘kara lura ba kwad’ayin mulki ne ke d’awainiya da ku ba, addinin musulunci ne kuke fito na fito da shi”

Ya nufu ni gadan gadan hannunsa d’auke da takobinsa ko gizau banyi ba sai ma ‘kara gyara ‘kwanciyata da nayi.

Na ce “Haba! dallah shashasha wanda bai san banbancin duhu da haske ba sai ba’kar gadara, inda a ce ka bada kai bori ya hau Na rantse da Ubangijina da tuni bukatar ka ta biya”.

Ya ce”Ni wankakke ne garau tas!”

Assha! illar jahilci kenan wankakke gogagge sai fiyayyen halitta ba wani mahaluki ba Annabi Muhammad (SAW)shi kad’aine keda wannan martabar, bayan shi duk wani mai ikirarin haka dolo ne gaula ne sannnan makaskanci. Hasken ilimi da hasken addini yana sa mutum ya samu galaba a rayuwarsa.

Yana ‘yar dariyar ya ce “Da alamu dai kema za a dama dake dan haka zan so mu kulla har’kalla nayi miki alkawarin za ki samu kaso mai tsoka indai na kasance sarkin garin nan, duk irin abin da kike so zan yi miki”.

Nayi dariya”idan muka kulla harkallar Anya iya cika alkawarin nan kuwa?”.

“Sosai matukar kika bani had’in kai sannan kika bani sirrin wannan birnin”.

“Ka d’auka tamkar wannan birnin ya zama naka tun yanzu kawai ka fara shirin nad’a dagatai da hakimmai”.

Sarauniya Guzaina wadda tun farkon fara maganarmu tana a tsaye sai dai ni kad’ai ce ke iya ganinta.

Na Kyakyaci idon Sadauki Zamnad nayi mata murmushi tayi min nuni da d’an yatsanta a wuya alamar kada na yi wasa na yanka shi.
Yana murmushi ya fita.

Barde Hamnad na zaune sakon bokansa ya iso zuwa garesa na cewa”Yarinyar da yake nema ido rufe tana nan cikin gidan nan dan haka kada ya tsaya sanya yanzu-yanzu ya bincike kaf! fad’in gidan nan ya fito da ita…..”

Team Duniyar Fatale
Team Shameena
Team Sadauki Zamnad
Team Sadauki Marhan
Team Sarauniya Guzaina
Team Sarki Shandam
Team Kaka Shamna
Team Barde Hamnad

Get ready yanzu wasa ta fara yaseen sharhi yana ‘kasa nima shed’ara biyar zuwa goma zan dinga yi.
11/8/20, 10:14 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
8 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 31&32

Hankalin Barde Hamdan ya yi masifar tashi kai tsaye har ya ce” aje lungu da sa’ko na gidan a nemo masa ita”, wani tunani ya zo masa.

Ya kira babban hadiminsa kuma abokin shawararsa suka shiga d’akin sirri ana tattauna yadda za a ‘bulluwa lamarin.

Hadiminsa ya ce”ranka ya dad’e kasan dai a komai ana bu’katar sirri ko”.

“Eh nasani”.Ya bashi amsa.

“Yawwa abin da nake tunani kada ka fito da maitarka a fili ta bayan gida zamu biyo.”

“Kamar ya kenan?”.

Hadimin ya taso daga gurin zamansa” Kawo kunnenka ka ji”.
Cikin rad’a ya gaya masa yanda za ayi.

Barde Hamdan ya d’ago fuskarsa
kunshe da farin ciki ya ce”gobe ranar laraba ta bawa ranar samu, burina dana dad’e ina son ya cika sai gobe komai ta fanjama fanjam! akwai bidiri.

” ‘Kwarai kuwa ranka ya dad’e Allah dai ya kaimu.”

Tun kafin safiya ta ida wayewa Barde Hamdan ya fito ya ci ado sosai da irin kayansu na sarauta cikin tafiyar ‘kasaita ‘yan lasar miya sun dafe masa a baya.

Tafiya ce mai nisa tsakaninsa da gefen Sadauki Zamnad dan haka ya hau dokinsa. Saura suka take masa baya.

Hayaniyar mutanen Barde Hamnad ce tayi sanadiyyar farkawar Sadauki Zamnad wanda yake ta sharar baccinsa hankali kwance zuciya zaune tun da Shameena tayi masa alkawarin mulkar birnin Bardam

Da tsaki ya farka lallai Hamnad ya rainasa da yawa taya tun da safe zai takurawa rayuwarsa ya mike da niyyar zuwa ya ci wa Hamnad mutunci, ya rabu da shi kowa ya yi rayuwarsa shi kad’ai babu tsangwama.

“Janam! Janam!! ” Ya dinga kwalawa baiwarsa kira.

Ta ‘karaso da sauri”Ga ni Ranka ya dad’e”.

“Ruwan wanka nake so”

Ta sunkuyar da kanta alamar girmamawa sannnan ta ce”Angama ranka ya dad’e”.

Bayan ta je duk ta had’a masa komai yanda yake so.

Ta dawo “An kammala komai ya shugabana”.

Da hannu ya amsa mata sannan ya fito waje dan a nan band’akin yake nesa da mutane kwatankwacin yadda mutanen da suke band’akinsu komai a sirrance wani yaro sai ya girma ne yake iya tantance manya suna zagayawa band’aki. Sa’banin wanda muke a yanzu karshen tonon silili cikin da’ki sauyawar zamani ya canza mana d’abi’ummu da muka gada tun kaka da kakanni.

Barde Hamnad bai tsaya neman iso ba kutsa kansa kad’ai ya yi cikin d’akin Sadauki Zamnad ya samu guri ya zauna yau tamkar ya zuba ruwa a fa’ko ya sha yake ji.

Yau na tashi a makare nayi bacci har da minshari sallah asuba ma dakyar barci ya bar idanuna nayi a fili na furta “gadon bono dad’in kwanciya ne da shi”.Kaka Shamna tayo min sak! a rai gaskiya ba zan iya ‘kara wasu mintoci anan ba tare dana je na ganta ba.

Tsam na mike ina amfanin bad’i ba rai na takurawa kaina kan banza ba zai yu ba wallahi dole sai na tafi.

Aljanin da na yiwa alkawarin Aure ya bayyana a gabana “ina za ki je? Kuma me ki ke yi anan ba tare da izinina ba?” Ya tambayeni.

Muryata na rawa nace “ko’ina?”

Ya ce”muje gida?”

Na daki ‘kirjina dan Allah ka rufamin asiri ka barni nayi rayuwa cikin ‘yan uwana mutane”.

Ya ‘kwashe min da dariya”yarinya bakin al’kalami ya riga ya bushe tun ran gini tun ran zane kuma har abada wannan kyauta ba za ta ta’ba tashi ba.”

“Ka taimaki rayuwata kasan komai fa , me yasa za ka ‘kara min ba’kin ciki a kan wanda nike ciki?”

Ya ce, kada ki yi jayayya da burin mahafinki aure na fa dake babu makawa ke ko mutuwa ki kayi sai na tafi da gawarki a gidana”.

Na fasa kuwwa da niyyar a kawomin d’auki amma babu wanda ya zo ina kuka nace”na ci wa bakina albasa yau na shiga uku ga addu’a inason nayi amma an danne min ‘kirji lumfashinma sai da kyar yake fita.

Wasu hawaye suka zubo min, na soma kuka”Dama nufinka kenan?”.

Ya dam’ki hanunna ina tirjewa guguwa ta sure mu zuwa sama bata ajiye mu ko’ina ba sai a wani daji mai yawan duwatsu cikin wata fada mai tsananin girma, da kuma fad’i na tsinci kaina dubban manyan zaratan halittu masu kawunan aladdu na gani kowa ne yana ri’ke da almaduddinsa tsaro na musamman ake bawa fadar.

Daya kammala wankansa ya nufi masaukinsa takalma ya gani a ransa ya ce”to wane ishassheni zai masa dirar mikiya a d’aki ba tare da izininsa ba”.

Aikuwa sai ya yi turus ganin Barde Hamnad hakince a gadonsa.

Kayan da zai sanya ya d’auka fitowa waje ya yi, wani wawan tsaki ya buga babu inda zai shiga domin ya sauya kayansa tun da d’ayan d’akin nasa shi ne ya ba Shameena ta zauna.

Dole d’akin ya koma ya shirya cikin tamfatsetsiyar alkyabba ko’ina ya bi jikinsa ya feshi shi da madarar turare .

Suka kalli juna suka yi murmushi Zamnad ya ce, sai ka fad’amin dalilinka na son gani na dan nasan ruwa basa tsami banza.Amma kafin nan bara na zo”.

“To shi kenan”Barde Hamnad ya fad’a.

Da sassarfa Sadauki Zamnad ya nufi d’akin da ya sauke Shameena ya yi nemanta ‘kaura wambai bai ganta ba.

Har zai fita ya hango wata mata dun’kule da mayafi ya ce”amma yarinyar nan bakida mutunci shi ne ina miki magana ki kayi banza dani?”.

Shiru babu amsa ya fusata gamida zare takobinsa wanda ko da yaushe yake cikin jikinsa bai ankara ba matar ta tashi tayi kan Sadauki Zamnad tana ‘karaji.

A guri guda wata ‘kura ta tashi sama a lokacin da ya yi arba da matar tuni…..

*’KARSHEN KASHI NA FARKO*

*BA A SON RAINA HAKAN YA KASANCE BA LAIFINKU NE, YANZU KUMA NA GAJI DA RO’KON SHARHINKU DUK MAI BU’KATAR KASHI NA BIYU TA NEMENI A WANNAN LAYI .08130359515 DOMIN TA BIYA KU’DINTA.MASU SHARHI DAN ALLAH KUYI HAKURI LAIFIN WASU NE YA JA MUKU.*
11/13/20, 7:43 AM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
10 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

*Ammin Najwa Nagode sosai wallahi Allah ya bar ‘Kauna kin ceto Duniyar Fatale fans😜.*

Bismillahi Rahmani Rahim

Page 33&34

A gaban sarauniya Guzaina aka tafi da Shameena tana kallo sai tsiyayar hawaye take, domin ba tada yanda za tayi dole haka ta kyale tana ji tana gani.Wai an yiwa mai dame d’aya sata.

Sauya kamaninta tayi ta dawo sak! Shameena ta fuskanci Sadauki Marhan daya sha’ke Zamnad iyakar gaskiyarsa tun da bai mulki Birnin Bardam ba ya yi al’kawarin ba wanda zai mulkesa.

Ta bayansa ta cakumesa” ka sakesa nace”ya ‘bagarar da Sarauniya Guzaina a can gefe.A lokacin ta mike tsaye da sassarfa Sadauki Marhan da ya ji wuya cikin mazantaka shima ya hantsilata ta fad’i gefe guda, ya kai mata wawan duka da kafafuwansa.

Ta ja da baya da ‘karfi tamkar wadda ke a filin daga sai akan Sadauki Marhan ba shiri ya saki Sadauki Zamnad wanda idanuwansa suka yi jajur da su, sai kace wanda ya leka barzahu.

Ganin haka Sadauki Zamnad da azama ya cilla mata takobinsa ba ta samu damar amsa ba, sai shi ne ya da’bawa Sadauki Marhan takobin a kafarsa sannan ya daka tsalle ya daki fuskar Marhan gumurzu ya kaure da kyar suka samu galaba a kansa ya ‘bace.

Suka zube a ‘kasa suna ajiyar zuciya yau sunyi gumurzu sai kallon mamaki Zamnad ke bin ta
da shi tabbas sai a yau ya tabbatar da cewa bai yi za’ben tumun dare ba da taimakon Shameena zai cika muradinsa.

Tambayoyi birjik yake dasu wadanda yake da bu’katar sanin amsarsu daga bakin wannan yarinyar gata da siffar nakkasssu amma fa sai azababben taurin kai da ‘taurin zuciya.

Sarauniya Guzaina ta kifar da kanta kasa dan gani take kamar zai fahimci da fatalwa ne yake tare.

Ya kalleta”Na tambayeki mana?”

“Eh “ta ba shi amsa a gajarce.

“Amma dai ke maya’kiya ce ko?”.

Ta d’ago” me ka gani kenan?”

“Ah! mazantakarki da kuma jarumtarki sune suka taka muhimniyar rawa gurin jefani a duniyar mamaki, duk fad’in nahiyarmu a yanzu ban ta’ba ganin macce mai kamar maza ba, sai a ‘karnin da ya gabata da wata shahararriyar maya’kiya mai masifar dakakkiyar zuciya da kowa tana iya karawa abin mamaki rana tsaka tayi ‘batan dabo”.

Tayi murmushi”ba mamaki watakila ya kasance ni ce”.

Ya ce”da kuwa an tabka gumurzu saboda kujerar mulkinta babu wanda ya cancanci zama a kanta sai ni”.

Sarauniya Guzaina ta zuba masa idanu cikin wani irin bala’n takaici jin take kamar ta kama Sadauki Zamnad da duka saboda tsabar tsana.
Ba ta ce komai ba ya ga kaɗa kanta ta mike tsaye zuwa fita har za ta wuce ya taro ta “ki tsaya mana akwai zancen da za muyi” nemi ya yi kamar zai kamota ta fisge gamida ‘komawa wani gefe tace,

“Ka kula! ba kowane kare da doki zai nemi ta’bamin jiki ba sosai nake martaba kaina”.

“Na ji amma ki tsaya dan Allah?”

Sarauniya Guzaina ta tsaya d’if “Me ka ce ?dan Allah?dama kasan shi kuke fakewa kuna zaluntar bayin Allah?”.

Ya ce,”dakata ni dai yanzu ba wannan ne a gabana ba ki taimakamin tamkar yadda kika fad’a a baya”.

Ta kwashe da dariyarsu ta Fatale sannan ta ce”kasan ko dawa kake magana kuwa?”.

“A’a sai dai ina son na sani”.

“Lokacin sanin naka bai yi ba, maganarmu kuwa tana nan ba gudu ba ja da baya badai masarautar Bardam ka ke so ba?”.

Ya gyad’a kansa ta ce”kada kasa damuwa a ranka yanzu kaje duk bukatar da d’an uwanka ya gabatar maka ka amince masa”

Ya ce ,”to!” har ya kai kofa me ta gani kuma?sai ta ce”tsaya muje a tare”.

Barde Hamnad da ya gaji da zaman jira kwanciyarsa ya yi inda a da ne take zai fusata.Idanuwansa na lunshe ya ji motsin shigowa ba shiri ya tashi a zaune.

‘Kuri ya yiwa Sarauniya Guzaina yana kallonta a zuciyarsa ya ce”babu makawa wannan yarinyar ita ce boka ya siffanta masa”.

Bai bi takan Zamnad ba, ya nufi Sarauniya Guzaina data canza siffarta zuwa ta shameena.

Bakinsa na kakkarwa ya ce”Yaya ka Auramin yarinyar nan inasonta sosai”.

Zamnad ya yi murmushi”haba kanena wannan ai tayi maka yawa sai ni dai ka yafewa yayanka dai”.

Bud’ar bakin Sarauniya Guzaina sai cewa tayi” Ai wannan ba abin tada jijiyoyin wuya bane duk zan iya aurenku a lokaci d’aya……”

 

Share pls😒

 

*Shaid’an kawai ake ba hakuri amma ya yi biris saboda haka na kar’bi ‘korafinku, da fatan hakan ba zai sake faruwa ba, cox gaskiya idan kuka sake i swear…….🙄Ba sai na ‘karasa ba kunsan sauran kid’an genaral a sama. Ku tambayi Ma’ule fans ya muka karke da juna.🤣 Duk da haka kuma zan gajarta labarin.🙄*
11/13/20, 7:44 AM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
11 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

35&36

A tare suka had’a baki da juna cike da tsananin mamaki”Aurenmu lokaci d’aya kinada hankali kuwa?”

“Ras! nake ba abin da ke damuna kuma ni gaskiya duk kunyi min babu na yadawa a cikinku musamman Wannan”ta nuna Hamnad ina ganin shi bansan lokacin da soyayyarsa ta shiga zuciyata ba”.

Zamnad ya sassauta muryarsa ya ce “Dan’kari ashe akwai lukutin masifa”.

Zuciyarsa sai tu’ku’kin bakin ciki take masa wato yarinyar nan tana son tayi masa wasa da hankali, abin da matukar yana raye ba zai ta’ba faruwa ba har abada.

Fuskar Hamnad tamkar gonar auduga ya kai kallonsa gurin Zamnad wanda ya yi kicin-kicin da fuska dan kawai ya tula masa takaici yasa ya ce,”Yaya ka ji ita da kanta ta furta tana so na ko?”

“Na ji tana sonka sai dai hakan ba zai hana faruwar aurena da ita ba, duk da cewa kana a matsayin sha’ki’kina”.

Gefe Sarauniya Guzaina ta koma dariya kamar ta kasheta tanada ya’kinin da sun san da fatalwa suke magana da tuni kowa ya sani inda dare ya yi masa.

Gaddama ta kaure tsakaninsu wannan ya ce”ta shi ce” wannan ya ce”da shi ta dace”.

Abin da take nema kenan ta rikitar da tunaninsu komai ya dagule musu, tayi imanin cewa akan macce babu abin da ba za a iya aikatawa ba shi yasa tayi amfani da wannan damar.

Ta katse musu gaddama ta hanyar cewa”zan tafi duk lokacin da kuka gama musun naku kuna iya nemana”.

Hamnad ya sassautar da muryarsa ya ce,”Ki tsaya mana bamu gama magana ba kuma shi ne za ki tafi”.

“Ba ku tashi zancen bane tun da naga sai takaddama kuke bayan na riga na gama magana duk ku biyun zan aureku sai dai fa inada sharad’i”.

“Sharad’in me?”suka tambayeta.

“Ba wani abu mai wahalar da kai bane kawai son nake ku ceto mutanen birnin nan daga Azzalumi ko nace Fatalwar Sadauki Marhan”.

Hamnad ya dinga ma’kyar,kyata fatalwa kuma wallahi duk ‘kwad’ayin mulkina haka kawai ba zan jefa kaina a mahalaka ba.”

Ta, ce”kenan ka saduda da mulkin wannan birinin?”.

Bai tsaya shayin komai ba ya ce,”Eh Allah ya raba rai da wahala”.

“Lallai ka kawo kanka a mahalaka domin mafi yawan mutanen birnin nan duk fatale ne kai na takaita maka zancena yanzu haka *A DUNIYAR FATALE* ne kake zaune”.

Ai nan take cikinsu ya d’ori ruwa amma fa Sadauki Zamnad bai wani karaya ba, tsoron shi ma bada yawa bane Hamnad dai ne ya tsorata.

“Ke wace ce?”

Tayi murmushi”Ni mutum da rabin mutun ce nasan za kuyi mamaki amma mu ku aje duk wani ‘korafi ko tambayarku ba sai na tambaye ku ba ga alamu ku manya sadaukai ne, shi yasa zanyi amfani daku domin cikar burina saboda nasan ‘Yata ba za ta iya da wad’annan azzaluman ba.”

“Dama kinada ‘Ya ne kada ki rainamin da hankali kamarki a ce wai kin haifi yarinya duk shekararki nawa”

Ta ce, “Ban cika maimata zance ba, dan haka ka kiyaye ni, tun farko shi yasa nace muku ni mutum da rabin mutumce, babu mamaki kuma idan ka zurfafa bincike ka taras da cewa ni fatalwa ce,

“Amma fa al’amurranki da d’aure kai suke sai dai bazan karaya ba, masu iya magana na cewa” mai nema yana tare da samu”.A cewar Zamnad.

Bajintar ka saura kad’an ka burgeni amma fa ba yabon kai ba ‘Yata duk da kasancewarta macce mai rauni hakan bai hanata kasancewa zama jaruma ba, yanzu dai mu aje wannan zance, na yanke ranar Auremu a gobe da ‘karfe biyun dare badan komai na za’bi wannan lokacin ba sai a sannan ne Fatale ke addabarmu baya ga haka da wannan damar nake son nayi amfani domin cikar sharad’ina”.

“Mun ji kuma mun amince gobe ki zo sai kiyi mana jagora”Zamnad ya fad’a.A zafafe Hamnad ya cakumi wuyar rigar Zamnad kanada hankali kuwa? ta ya za ka ce wai muyi ya’ki da fatale bari ka ji abin da baka sani ba, babu wani ‘boye-‘boye wannan matar da ka gani itace yarinyar da muka zo nema jiya boka ya sanar dani komai sannan ya ce tanada matukar hatsari na rantse da gawar mahaifina bazan je ba, kai kaje tunda ka gaji da zama duniya duk takadaranci na ina son rayuwata”.

Bayan da Sarauniya Guzaina ta tabbatar da ta had’a gurmi tana murmushi ta ce”na tafi kada ku manta da lokaci karfe biyu ne”.

“Kada dai ya manta dan nikam ba zan je ba”.

Sarauniya Guzaina ta ce”Ka kula in har kana son rayuwarka babu makawa sai ka je tun da ka kawo kanka gidan mutuwa, kuma idan kana shakku ka tambayi Yayanka me ya faru da shi a yanzu?”.

***
Cikin dare na ware idanuna, a lokaci guda wata yunwa ta yunƙuro min, babu ‘bata lokaci na tashi a zaune ina mitsittsike idanuwana.

A daidai lokacin ne boka ya shigo cikin d’akin da ya ajeni nace”ka taimaki rayuwata ka fad’amin manufarka ta sace ni bayan na riga dana yi maka alkawarin auren da kace?”.Ficewarsa kawai ya yi.

Abinci na gani an ajiye A natse na bud’e na fara ci. Sai da na ji na ‘koshi dam! sannan nasha ruwa. A sannan ne kuma komai ya dawo min cikin kai. Zumbur na miƙe da nufin dosar hanyar da naga yabi, sai dai kuma wani tunani da ya dawo min ban yi Sallolina ba.Balantana nayi wata addu’ar samun nasara dan nayi alkawarin yau sai na bar gidan nan….

 

*SAURA ‘KIRIS* 🙄

*SHARE PLEASE NA FITA GROUPS DA YAWA.*
11/13/20, 7:45 AM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
12 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

37&38

“Ina zan samu ruwan alwallah ga shi ko ‘kasa ban gani a nan ba?” Wasikar jakin da na dinga karantawa kenan.

Sanin da nayi sallah ta wuce wasa kuma a halin da nake ciki babu wani uzuri da zai kauda sharad’in cewa ba zanyi ta ba.

Hakan yasa na mi’ke can na tuna da sauran ruwan da nasha bayan na gama cin abinci.

Zaune nayi hankalina kwance a tsakiyar d’akin nayi alwallata to miye matsalata ai wallahi kazanta sai wadda na manta tun da ya rufeni ba gaira ba dalili.

Da na gama haka na shimfid’a d’an ‘kwalina na tada harama sannan na ninkaya cikin sallah ta da addu’an neman mafita gurin Ubangiji.

Ban kai ga kammalawa ba gurin da nake zaune ya soma girgiza jikina sai ya dinga rawa take na soma kiran sunan ubangiji ina fad’ar,

“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un, Allaahumma’-jurni fee musibatin wa ‘akhliflni khairan minkhaa.”

Kamar kada na fara sai na ji abin da nake ji ya rage.

‘Dakin da boka yake ashe tun lokacin da Shameena ta fara sallah yanayinsa ya fara sauyawa
Tsoro ‘karara ya bayyana a fuskarsa kada dai ace labarin da Sarauniya Guzaina ta fad’a masa shi ne zai tabbata. Haya’ki ya fara fita a bakinsa babu ‘kakkautawa tare da yin wani tari mai had’e da gyaran murya, ‘kat! ‘Kat!! ‘Karrrrrrr! tuf!.

Wannan lamarin ya zame masa abin ban kunya da takaici, ba ‘karamin zubar da mutuncinsa ba ne a tarihin kafuwar matsafarsa hakan bai ta’ba faruwa ba. Dan haka zai d’auki mataki mai tsanani tare da hukuntar da ita domin duk a silar ta ne.

Ran maza ya ‘bace duk soyayyar da yake mata zuwa yanzu ta kau ya nemeta ya rasa, afujajan ya fito ya tunkari d’akin daya kulle Shameena.

Da ‘karfi ya bankad’ata sai gashi a tsakiyar d’aki jikinsa har ‘bari yake. ya daka mata gigitacciyar tsawa mai razanarwa”Keee! ki dakata da abin da kike domin kina lalatamin aiki”.

Ko kallo bai isheni ba, idan na tanka masa d’akin da nake ciki shima zai maganta masa.

Na cigaba da yin addu’ar kariya daga ma’kiya, daga nan ma sai na ‘kara sautin muryata da acikin zuciyata nake saboda ina son na kulesa na dinga yi a sarari

Ina ta fad’ar “*Wallahu ghalibun Alaa Amrihi” ba iyaka*.

Ya cira sandar tsafinsa sama yana nuna ni da ita, ‘kara ma’ke jikina nayi inata addu’a.

Ya dinga yi min kallon ‘kaskanci yana magana cikin alfahari da izza ya ce min,”Ki gama duk wani iskancinki yau sai naga bayanki Sadauki Marhan ya yi gaskiya daya fad’amin kada na raina allura domin kuwa itama ‘karfe ce jinin Sarauniya Guzaina guba ne mai wuyar sha’ani dole sai da taka tsantsan”ya dakata yana jiran ya ji amsar da zan ba shi.

Ganin da ya yi nayi biris da shi yasa ya ce,”duba nan”.

Na d’an d’ago da kaina”Innnalillahi wa’inna ilahin raji’un! Subhanalla me nake shirin gani yau ni Shameena na shiga uku! wata ‘karamar ‘kwalba ce mai d’auke da allururi sunfi dubu ko’ina an zagayeta da sunan Sarauniya Guzaina sai nawa da kuma Kaka Shamna daga ‘kasanta an rubuta Sadauki Marhan sunan na shi sai fitar da wuta yake. “.

“Kin firgita ko?wannan yana d’aya daga cikin ‘karamin aikina rayuwarku a halin yanzu duk tana a hannuna saboda haka za’bi ya rage ga mai hawan rijiya da baya ko dai ki daina abin da ki ke ko kuma na tagayyaraku.
Wannan kwalbar duk duniya ba wanda ya isa ya bud’eta”.

Tunani ya d’arsu a zuciyata ina sa’ke-sa’ke tsoro ko nuna karaya ba nawa ba ne, madadin na firgita sai wata natsuwa ta zo min na ji da kowaye zan iya karaya kuma na samu nasara har abada Allah ba zai ta’ba tozartar da addininsa ba sannan duk wanda ya dogara ga Allah kada ya ji tsoron mahassada bale ‘keta.

Na katsesa ta hanyar furta”Sai ni ‘Ya a gurin Sarauniya Guzaina shalelen Kaka Shamna”.

Ya kece da dariya” yaro bai san wuta ba sai ya taka kada kice za ki ja dani, dan ina mai baki tabbacin kece za ki wahala shawarata a gareki ki “kwashi tsumman rayuwarki ki rufawa kanki asiri kafin Azabata ta tabbata akanki”.

Na ce”Bari ka ji “Wai ita gaskiya dad’a dai ko an ‘ki ta sai an dawo mata idan za ka kiyasta a tarihin rayuwarka ka ta’ba ji ko ganin ance gaskiyar mutum ta ‘kare?ai sai dai ace ‘karyarsa kuma ramenta kurarre ne.”
duk girman zamani ko kuma ‘karni babu yanda za’ayi ace a rayu babu wani musulmi ko d’aya me kuke tunani?kun asirce mutanen gari sun bijirewar addininin Musulunci sannan ku yi rayuwarku yadda kuke so akan kwad’ayin mulki?”.

“Yimin shiru” ya ce a fusace.

“Na’ki tun da Allah ya sahalemin bakin magana babu wani tsohon najadu da zai d’auremin shi”.

Ya ce,”ba za ki rufe bakin ba kena””.

“Eh! idan kai ka haliccesa ai sai ka rufe nagani”.

Da hannunsa ya zira ya dinga ‘kwallo da ni har bakina ya fashe yana min dariyar mugunta nan na fara karanta wata addu’a na bud’e sautin muryata ya game ko’ina d’akin ya dinga amsawa ina fad’ar,
“*Allaahumma munzilal-kitaabi, saree’al-hisaabi, ihzimil-‘ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum.*”

Aikuwa sai Allah ya saukar min da ijaba gashi tsaye yana son ya yi min wata illah ba hali sai rawar da jikinsa ke yi harshensa ya kare yana son ya furta wata magana amma ba hali da shi da wani makyararren hannunsa da ya d’aga a sama da niyyar ya tsaface ni Allah ya nuna masa shi ne *Ahadu-Samadu*.

Na nuna sa da babban farcena”ina maka albishir da cewa yau itace ranar da za ka bar duniya badan ka gaji da ita, sai dan ‘karshen zaluncinka ya zo da kuma kawar da makiyin Addinin Allah. A doron ‘kasa.”

Cikin tafiyar ta’kama na dinga taku har na je daidai inda yake tsaye ina murmushin farjn ciki na warce kwalbar dake hannunsa na fita a nan na iske duk magoya bayansa sun suma d’akin tsafinsa na je na taradda ‘katuwar tukunya ya rufeta da bakin ‘kyalle ko d’ar banji ba, na sanya kafata da karfi na duketa timmm! ta tarwatse wasu fararen ruwa masu ba’kin d’oyi ba kyan gani suka zube a d’akin…

Share pls🙄
11/13/20, 8:11 PM – 𝑂𝑢𝑚𝑚𝑜𝑢 𝐴𝑟𝑜𝑢𝑛: ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

*☠︎︎ DUNIYAR FATALE ☠︎︎*

☠︎︎ ☠︎︎☠︎︎☠︎︎☠︎︎

NA
*༆PRINCESS AYSHATOU༆*
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

*༆WATTPAD༆*
*AYSHART647*
13 Nov 2020
*Sadaukarwa ga:Leamart Pinky*

*Jan kunne*
Yawwa kada ki ji suna ya miki dad’i ki sanyawa d’anki ko Y’arki, ba ruwan Indo garuruwa da sunayen Mutane duk na ‘kir’kira ne.

Bismillahi Rahmani Rahim

39&40

Rufe hancina nayi dan d’oyin ya wuce misali can sai ga wani dodon tsafi ba’ki ‘kirin ba kyan gani yana bud’ar baki kamar wanda ya samu nama ya nufu ni.

Na dinga ja da baya ina ta kiran sunayen Allah duk addu’ar da ta zo min a baki ita nake karantawa.
Rufe idanuwana nayi dan na yanke tsammani.

A lokacin wani gurnani ya bayyana tare da haya’ki daya rufe ko’ina hannuna nasa ina kakka’bewa saboda naga hanyar fita.

Dodon ya bayyana yana haki na fusata, idanuwansu sun yi jajur tamkar garwashin wuta, ya tunkaru ni a fusace.

Takobina na zaro wanda ke cikin jikina rai da addini tun da aka bani shi, nayi kansa ina zuwa na sari cikin dodon ya fasa ‘kara da ‘karfi take cikin ya dare gida biyu ya sulale ‘kasa baya ko wani motsi.

Wata jarumta na ji ta shigeni ina ‘karaji na kwalla ‘kara mai tsanani, sannan na hau dodon tsafin da sara ta ko’ina har ya ‘kwalla ‘kara ya zube ‘kasa a lokacin ne kuma ya kama ci da wuta, ya ‘kone ‘kurmus.

Hamdala na yiwa Allah” komai nisan jifa ‘kasa za ta dawo.Da izinin Allah zamu ci nasara a wannan ya’kin”na furta haka ina murmushi.

Hargitse d’akin nayi ko’ina ina dube-dube ko da zan koma samu wani abu.

Gefen gadonsa naga wata duruwa can na nufa na bud’e takardu ne birjik sai wasu dad’ad’d’un layu masu yawa daga ‘kasa naga wani ‘katon littafi ban tsaya sanya ba na fito da shi, ina jujjuyasa”da gani wannan tsohon littafi ne to ko mi ne ne ya ‘kunsa? Allah masani”nayi tambaya kuma na bawa kaina amsa nace ina murmushi.Ina d’aukar littafin na fito, tsaye nayi dan bansan hanyar da zan fita ba

Ana wata ga wata, ‘barawo a hannun mata.

Wai tsuru-tsuru kenan?na dinga ‘kwasar dariya kamar sabuwar mahaukaciya.

Rufin d’akin naga zai ruftumin duk inda na saka kafata zan ji gurin na girgizawa kofa ta wangale haske ya shigo fayauuu!
da hanzari na fita. Ginin ya fara rushewa take ya kama ci da wuta.

Gefe na ja tunga sai mazari jikina ke yi ina sauke ajiyar zuciya da d’aid’ai.

Nayi fitar kutsu ikon Allah! ashe wai gidan bokan tsakiyar Birninmu yake?na dinga mamakin to ya akayi d’azu naga tamkar wata duniya ce?ko da yake wannan ba abin mamaki ba ne mai yuwa tsaface gurin ya yi.

Zama bai ganni ba masarautarmu na tunkara har yanzu dai kamar kullum bakowa a gari ni kad’aice ke tafiya kamar mayya har na isa bayan na waiwaya dan kada wani ya ga shigata.

“Sannu da zuwa ‘Yata hakika dama nasan ban haifi lusara ba wannan ya’kin da taimakon ubangijin ‘Ka’aba sai mun yi nasara”Sarauniya Guzaina ta tarbeni cike da annashuwa.

“Ina Kaka Shamna?”na tambayeta sosai nayi kewarta muyi fad’a mu shirya haka nake kullum da ita.

Ta kalleni”Allah sarki har yanzu bacci take ba ta farka ba”.

Na kwalalo idanuwa”Baccin lafiya kuwa?”.

Ta ce,”Bana lafiya ba ne amma kada ki damu komai ya zo ‘karshe da taimakon Ubangiji Sadauki Marhan ne.”

Na d’an rausayar da kaina ina alhini na furzar da iskan bakina sannan nace”Wannan mutumen mugun gaske ne wai me yasa wasu mutane ke rud’e akan neman mulki? bayan Annabi Muhammad SWA a cikin wani hadisi yana cewa”Hakika kuna ‘kwad’ayi akan mulki, sannan za ku yi nadama ranar Al’kiyama”.

Ta dafa kaina dama Sarauniya Guzaina macce ce har macce gwargwado Allah ya azurtata da komai, duk da ance mutum d’an tara ne bai cika goma ba, ita dai kam Alhamdulillah shi yasa wani sa’in ake shakkarta ta d’an share min hawayen da suka wanke min fuska, har ga Allah ina tausayin duk wanda Allah ya d’orawa alhakin mulkar mutane saboda babban nauyi ne wanda takai ko da mutum d’aya ya ‘kwanta a gidansa bai sawa cikinsa komai ba, sai Allah ya tambayeka.Wanda ke cikin wannan bala’in amma wai a hakan sai rububinsa tir! da masu ‘kwad’ayi.

Ta kira sunana cikin tattausan lafazi

“Shameena?”.

Na amsa da “Naam”.

“Allah ya dafa miki ro’kona a gareki ko bayan babu ni Dan girman Allah kada ki sauya halinki na tausayin mutane kada ki damu da tun kina ‘karamarki nauyi ya hau kanki, Abin da za kiyi tunani shi ne mulki Allah ke bada shi ga wanda ya so kuma a lokacin da yaso. Kiyi amfani da wannan damar ki nemo lahirarki, sannan ba ma wannan ba da komai Allah ya azurtaki za ki iya neman lahirarki, ki kasance mai (‘kana’a )ma’ana wadatar zuci komai Allah ya baki ki kar’ba da hannu bibbiyu saboda Allah SWA ya ce”Idan kuka godemin to zan kara muku kan wanda na azurtaku da shi, haka kuma idan kuka kafircemin ha’ki’ka azabata mai tsanani ce”.

Tana fad’amin haka jikina ya sanyaye na ji duk banda wani kata’bus sai nake ganin tamkar wasiyyar bankwana ne take min za ta tafi ta barni ai kuwa sai na fashe da kuka.

“Insha Allah zanyi ‘ko’kari nayi amfani da wannan nasihar taki”

Ta ce”Allah ya yi miki albarka sannan ya haskaka miki rayuwarki bani littafin naga abin da ke ciki?”.

Na dam’ka mata a hannunta sai da tayi bisimillah sannan ta bud’e littafin.

“Subhanallahi! wannan bala’in har ina mutane basa tsoron Allah”A cewar Sarauniya Guzaina.

“Me ya faru ne?me kika gani halan?”.

Ta dunguno min littafin “duba ki gani da idonki”.Na kar’ba cikin tsoro.

Wasu halittu ne ke yawo cikin littafi gasu a hoto amma tamkar su fito a fili kawunansu tamkar na jakkai kafafuwan dokuna.

Rubutun dake a kai na fara karantawa ashe yadda ya had’a surkullen a rubuce Sadauki Marhan ya Sadaukar da rayuwarsa ga wad’annan halittun domin biyar bukatarsa na idan ya mutu Boka zai tayar da shi ya cigaba da rayuwa a fatalwa. Kuma ta wannan hanyar ne yabi bayan mutuwar Mahaifinsa shima aka tayar da shi daga nan suka yad’a Zango a majami’ar birnin suka addabi mutan da d’auki d’aid’ai, ya dinga d’inga satar mutane.Kai karshe ma aka had’a masa wani asiri ya sace mutanen garin sai ya kasance babu kowa daga baya wasu mutane suka bud’e birnin daga ciki harda Kaka Shamna wadda ya tsafacesu ita da Shameena saboda boka ya fad’a masa kashe su tamkar karya alkadarinsa ne.Bayan tsohon nan daya bawa Shameena takobi ya karya asirin duk da haka ita Kaka Shamna d’in Har yanzu asirin yana cikin jikinta.shi yasa ko da yaushe cikin bacci take ibada kuma ba a maganarta.

Haka na dinga bincikar littafin kakaf sai da naga komai dake cikinsa ‘Kwalbar dake hannuna na d’aga sama ina murmushi”Karshenka yanzu Sadauki Marhan badai a duniyarmu ba yanzu kam sai dai ka koma rayuwar barzahu kaida Ubanka.”

“Karfe biyun dare ki shirya zamu fita”Sarauniya Guzaina ta furta. fuskarta naga ta sauya nace”me ya faru kuma yanzu bayan mun samu dukkanin amsoshin da muke so?”.

Bata amsa min tambayata ba illa kawai ta ce min “ki je ana nemanki”.

“Wa kenan?”

“In kika shiga ciki za ki gani”.

Ban koma tankawa ba na cusa kaina Kaka Shamna ce ta farka, da sassarfa na nufeta rungumeta nayi “ina kika shiga ‘kwana biyu ban ganki ba?”

Na ‘kwa’be fuskata”Ni fa ko’ina banje ba amma dai anjima zan fita”.

“Ki je ina?”

Ba wani rufa-rufa nace mata”Ya’ki zan je”.

Hankad’ani gefe tayi sannan a fusace ta ce”kinada hankali ya’ki a gidan wa?kuma ke da wa?”.

“Ni da Fatale zanyi”.Na ba ta amsa ai kuwa lafiyyayen mari ta sakarmi tana huci”ko da wasa kada na sake jin kin furta haka”.

“Na mike tsaye”gaskiya fa sai dai kiyi hakuri amma ya’ki kam kamar na je na dawo ne”.

Kaka Shamna ta ce, “wallahi babu inda za ki tafi”.

A lokacin zuciyata ta kawo iya wuya na ce”wallahi sai na je dan
Mahaifiyata bata haifi lusara ba.
Ki hutar ranki Kaka Shamna ba amincewarki nake nema ba, matukar Mahaifiyata tasa min albarka nakan gudanar da abubuwana cikin salama.”

Daga haka ban dad’a ba kuma ban ‘kara ba fitowata nayi ina ji sanda take kwalamin kira nayi biris da ita.

Inda na barSarauniya Guzaina na dawo ta miko min sulke da kanta ta shiga dani wani d’aki ta shiryani na fito sak a maya’kiya.

Ta zaunar dani a kusa da ita tana ‘kara bani haske gamida dubarun ya’ki musamman addu’ar tunkaran makiya ta ce na riketa sosai da munje gurin ita a gefe za ta koma domin fad’ana ne , dan haka ba za ta saka min hannun ba da sunan taimako.

***

“Da alamu Zamnad ka haukace ta ya za ka ce wai tunkarar fatale za ka yi ?”A cewar Barde Hamnad wanda tun lokacin da Sarauniya Guzaina ta fad’a musu zancen ya’ki da fatale ya karaya.

Zamnad da ke ta shirye-shirye duk kayan ya’kinsa ya tattara a gefe d’aya lokaci kad’ai yake jira.

“Kana fa jin zancen da nake maka”.

Ya muskuta fuskarsa a d’inke ya ce”Wai na tambayeka Hamnad yaushe ka fara ‘kaunata ne, naga dai a gida ba mu ga maciji da juna amma yanzu dare d’aya ka dinga nuna zallar ‘kaunata anya ba wani mugun abu ne kake kullawa ba?”.

“Babu abin da nake kullawa kai da naga kana tunanin sa kanka a tsaka mai wuya nikam ba zanje ba”.

“Kada Allah yasa ka je”.

Ya fito yana auna inuwarsa tun da ba agogo ne da su ba komai ‘kwatantawa ne sukai.

“Lokaci ya yi”.Ya furta ciki ya koma duk abin da zai bukata na ya’ki mashi ne, kibiya ce, da takobinsa kai harda ‘kwari da baka ya fito.

“Ka shirya kenan?” Sarauniya Guzaina ta furta.

“Eh! Mu je.”Hankalinsa na a filin daga sam! Bai lura da Shameena ba wadda ta kure shirinta cikin kayan ya’kin mahaifiyarta.

Kamar kullum Birnin ya yi shiru sai rud’unniyar Fatale ka keji Majami’a ta d’au sauti ai sai Zamnad ya fara ja da baya ganin da ya yi kofa ta bud’e da kanta .

Shameena dake ankare da shi ta daka masa tsawa”Lusari kawai”.

Sosai kalmar ta daki zuciyarsa shi da ke ganin kansa jarumi kuma sadauki sannan a jefe shi da wannan ‘kazamar kalma.

Na cusa kaina ban taka burki ba sai a tsakiya na daki ‘kirjina “Sadauki Marhan kai da tsohonka idan kun cika ku fito gani yau mai kan uwa da babi za ayi ko ni ko ku”.Na ‘boye hannuwana ta baya kwalbar dana d’auko gidan boka ce son nake yana fitowa na kifa masa ita a fuska.

‘Kabarin Shandam ya fara girgiza tamkar sanda na ta’ba zuwa wannan karon kam tsaye nake ‘kyam Sadauki Zamnad rabon idanu ya dingayi har da zawo ya kufce masa ya ga zaren da ya fi na shi.

Ta bayana suka fito dariya suka kwashe da ita dan ganin ‘Yar tsako suke min wai ni ‘yar firit dani zance nayi fad’a da Fatale wannan ai sai ‘karar ‘kwana.

Addu’a na diga yi ina musu kallon
Karshe da su har tawagar tasu ta fatale nakai idanuna gurin Sadauki Zamnad tuni hanyar guduwa kawai yake nema bale da ya ji ‘kasar gurin na tangal-tangal.

“Zamu kasheki yau kema za ki dawo duniyar fatale da zama.”A cewar Marhan.

“Kaiii! yau sai naga karshenka sannan kai dai karyarka ta kare dan yau za ku koma rayuwa ta dindindin.

Takobina na zare suna tunkaroni nima ina tunkararsu ba gudu ba ja da baya.

Na d’aga takobina sama ina”Allahu Akhbar! Allahu Akhbar!!”Wani haske ya mamaye gurin kwalbar dake ‘boye a bayana na fiddo ta fad’i ‘kasa ta fashe take suka fara konewa kamar darma suna darerewa kafin su kai ‘kasa na shiga girbar kawunansu, ruguntsumin artabu sai sadaukai taurin zuciya sai maya’kiya.

Suna fad’uwa kasa shi da Sarki Shandam kaburburan dake gefe suka fara motsi.

Na dakata ina jiran naga ko miye?ashe turuwar mutanen gari ne daya binne suke fitowa kowa kan shi furfura ta fito masa shekara d’ari wasa ne, Sadauki Marhan ya dad’e yana tsula tsiyarsa yau dai ta kare masa ‘karshen azzulamai makiyan Allah sun zo.

Bayan sun gama fitowa kallo suna dinga yi wani daga ciki ya fara cewa”Allah ya ja da ran Sarauniya Guzaina”aikam sai guri ya dau kuwwa nace ku dakata”wannan fa ba ita bace ‘Yarta ce “.

“Mi ye marabar dambe da fad’a ai jiki da fata duk mallakar wuya ne.”

Sosai na ji dad’in yadda suka bani girma da alamun ba zan sha wahala yayin gudanar da mulkina ba.

Kowa ya watse aka barni daga ni sai Sadauki Zamnad na dinga raba idanu can na hangi Sarauniya Guzaina tana min murmushi na taka har na isa gurinta na rungumeta ina sumbatarta.

“Kinyi kokari ‘Yata Nagode! Nagode sosai Allah ya miki albarka zan koma inda na fito”.

“Dan Allah kada ki tafi ki dawo muyi rayuwarmu a tare”.

Ta ce,”Bakin al’kalami ya riga da ya bushe yanzu ruhina zai samu salama dama Marhan ne ya tayar da fatalwata”.

Muna kuka muka rabo” shi kenan kuma sai a lahira idan Allah yasa munada rabon ganin juna”. Na furta hakan fuskata jage-jage da hawaye.

Daga inda Sadauki Zamnad yake ya saki kayan ya’kinsa da ya zo da su, gabana ya tsaya yana kallona yace”tun da nake a duniya ban ta’ba ganin abin mamaki wanda kwakwalwata ta gaza d’auka ba sai a yau tabbas addininku shi ne tafarkin gaskiya ina neman alfarma da ki gaggauta musuluntar dani”.

Wo! ho! ho!! dad’i kan dad’i take na musuluntar da shi na ja shi sai a Masarauta ashe tun kafin naje mutanen gari har sun gyara min komai ni kad’ai ake jira.

Cikin daren Aka nad’ani a matsayin Sarauniyar Birnin Bardam burin mahaifiyata ya cika yanzu kuma sai me ya rage?”na tambaye kaina.

“Sai kuma Aure” .Kaka Shamna ta furta nayi fari da ido sannan nace “indai haka ne to na za”bi Sadauki Zamnad a matsayin mijina”.

“Alhamdulillah yau Allah ya nufa ashe inada rabon ganin Auren ‘Yar gaban goshina.”.

Na rufe fuskata dan muguwar kunya na ji.

Nace”indai Aure ne ko yanzu ana iya d’auramin Wannan”na nuna Zamnad take ya washe hakoransa bai mulki birnin ba amma sai ga shi zai Auri Sarauniyar Gaba daya.

*YASEEN BA ZAN WAHALAR DA KAINA GURIN ZAYYANA SHAGALIN BUKI BA🤣CAN KU KIYASATA DA KANKU.*

***
*BAYAN SHEKARA ‘DAYA*

Birnin Bardam ya dawo yanda yake muna zaune cikin amincin Allah dan har Aurena da Zamnad Allah ya azurtani da samun ‘Ya macce tamkar nayi kaki na zubar ko kad’an ba ta yiwa mahaifinta kara ba.Mulkina kuwa sosai nake kwatantan adalci saboda gyaran gobe na.

A cikin shekarar ne kuma Kaka Shamna ta amsa kiran ubangiji wanda kafin ta rasu d’in ta dawo cikin hankalin kanta ibada babu wadda ke wuceta sai fatan Allah ya yi mata rahama.

Labarin Barde Hamnad kam tun sanda Zamnad ya tafi ya’ki da fatale cikin daren ya nad’a ‘yan komatsansa ya koma birninmu na Gawaisha. Maganar kwadayin mulki ta mutu sai dai fa har yanzu shi da sauran ‘Yan uwansa ba su san Annabi ya fako ba.

Zaune Sarauniya Shameena take cikin fadarta anata zuba mulki wani bafade ya shigo hankalinsa a tashe jama’a na tambayarsa “kai lafiya?”bai saurari kowa ba har sai da yakai kan karagar mulki ya dur’kusa yana ta faman haki.

Da hannunta tayi masa alamar ya kwantar da hankalinsa sannan ta tambayasa”Me ke faruwa ne?”.

Ranki ya dad’e *” ‘KORAMAR AJAL….I”*

“Ta yi me? Me ya faru? ina ne can d’in?”.Ta dinga tambayarsa duk a jere da juna.

Ba ta samu amsar tambayarta ba Bafaden ransa ya aje.

“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un kada dai wani ibtila’in ne zai koma afko mana”.

Hadimarta cikin sigar lallashi ta ce”Yake uwargijiyata kada zancen wannan bafaden ya tayar miki da hankali yana yuwa shaci fad’i ne”.

Sarauniya Shameena ta dubi Hadimar a kufule”ba ki ji abin da ya ce bane* ‘KORAMAR AJALI FAHH…*

*TAMMAT BI HAMMDULLAH*

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da ƙasaita take saukowa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.