GIDAN GADO Page 31 to 40 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / GIDAN GADO Page 31 to 40

GIDAN GADO Page 31 to 40

GIDAN GADO Page 31 to 40

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

“Kin kyauta ma rayuwar ki, yarinya ki tashi zamuje can gidan su Hajiya a nunnunaki  a dangin miji, “to aunty  juyawa tayi ta shiga daki ta dauko mayafi a zuciyarta kuwa zaginsu take tayi, naga Alama sai na tashi tsaye da wa’innan dangin Mijin zan kira Umma ince ta Kai mun so gurin Mai gobe da nisa, badai kunyi sake na shigo ba wlh sai na rabaku da danku, “wai ina Amaryan ne, gani nan zuwa aunty, bayan ta fito ne suka kama hanyar  Zuwa ainihin Family House din su Mubarak Talban fulani Family, don nunata a dangi,  kuma ayi budan kai,
Bayan an gama nunata a Family, sai aka wuce da ita Talba palace gurin Mai girma Talba, don yayi mata fada a matsayin shi na kakan Ango da Hajiya kilishin Talba Hamshakiyan Mata wanda ta Ansa sunanta, tana kishingide a kilisa, “Ran Talba ya dade ga Amaryar ka mun kawo maka kasa mata albrka, sai da yafi minti goma yana karemata kallo, duk Billy ta tsargu da kallon da yake mata kuma ta gaji da tsugunon, “Uhmmm Alhmdulillah Amarya barkan ki da shigowa Talba Family, Yanxu wai wannan jikan Muhammad Moddibo Yareema ne, Allah sarki Moddibo mutumin kirki, Allah yasa kin gado kakanki, in har kin gadoshi zamu zauna lafiya, sbda mu Talba Family bama bukatan wanda zatazo ta tarwatsa mana Zuri’a kinaji na kuwa? “Eh inshaallah, “To Allah ya muku Albrka, Ashe duk abun nan da, akeyi Yaya Mubarak na gefe, sai yanxu na lura dashi a gurin, to Hajia Kilishi ga Amaryar ki nan, naga iko da isa ranar Billy ta raina kanta a gurin Hajia Kilishi, don sunfi Awa suna zaune a gurin kafin ta tanka musu, kasancewar kowa yasan Halin isanta da ikonta ba wanda yayi magana, duk ita suke saurare, sai da ta nishadu sannan tace ma Billy ta taso tazo gurinta, tashi Billy tayi tana sassarfa ta isa gurin Matar datayi mata kwarjini, ta zauna, “keh!!!  Waya baki izinin Zama,?  Da sauri Billy  ta tashi ta tsugunna a gabanta, “ina Mubarak din?  “Gani Hajia sai na kiraka ne,?  “A,a Hajia tashi yayi ya isa kusa da ita, ya tsugunna kusa da matarshi yana fatan kar ta ce zata rabashi da matarshi don yasan inta zartar da hukunci ya zartu, “Mubarak me ka gani a jikin wannan yarinyar, iyeh?  “Ni badon ance mun jikan Muhammad Moddibo bane ita ba da a yanxu a nan sai ka saketa, ni yarinyar batamun ba, idon ta a soye,  daga ganinta batada tarbiya, Amma yanzu sassaucin dazan maka shine dole zaka kara Aure, Nanda shekara biyu, da sauri Mubarak ya dago, “Eh abunda kunnenka yaji haka na fada, ta gyara zaman glass dinta, “ku tashi ku bani guri na gama zance, Billy daskarewa tayi a gurin kawai kukane ya subuce mata, jiyakeyi kamar ya rungume matarshi ya rarrasheta, Amma ba dama,  shi wlh Matar nan ta fara isarsu kawai ta dunga musu mulkin mallaka,
Bayan an kaita su Daddy da su Momy sun mata Nasiha, aka wuce da ita gidanta ranar tasha kuka, sai taji duk auran ma ya fitamata a rai, wai a wannan Family zatayi rayuwa, dole Umma ta kara tashi mata tsaye, kuwa,
*************************
“Yauwa Abokina ya bayanin   filin mu, kasan mun zauna da Yaya Ameen na mai bayani kuma duk ya fahince ni, yacemun akwai wata plaza da ake neman masu siye a kasuwa kusa da shagon mu, shine yace mu siya kawai mu zuba kekunan dinki da kayan dinki, da manyan kaftanai da riguna dinkakku irin na sarauta, kun san Zaria sunyi suna a irin wannan fanni, to shine nace bari in sameka muyi mgnar,   gskya hakan yayi kuwa Abokina, gskya Yaya Ameen ya kawo shawara mai kyau.
Washe gari su Yaya Ameen sunje sun sayi plaza an gama komai a cikin kwana bakwai, saboda akwai kudi, a hannun su, plaza yayi kyau sosai su Baffa Yahaya da Baffa Jibrin da Baffa Habibu, sunje sun ga guri yayi kyau sosai, anyi musu sauka a gurin kuma, anyi musu addu, oi za,a fara Aiki a gurin ranar laraba, Maman Jafar tayi bin kwakwaf din dazataji plazan waye Amma ta kasa sani, tunda ance na Yaya Ameen ne, nan da nan Bakin ciki ya wanzu a cikin zuciyan yan gidan Fulani masu mai murna nayi masu Hassada nayi,
Note:wai ace yan uwa yau dan uwanka ne Abun alheri zai sameshi maimakon ka tayashi murna, a,a sai bakin ciki, taya zamuga cigaba a rayuwa don Allah mu gyara halin mu yan uwa sai muga cigaba, a rayuwar mu, Allah yasa mufi karfin zuciyan mu,
Su Yaya Ameen da Yaya Jafar da Yaya Umar komai ya tafi musu yanda suke so, MAMI SPECIAL SEWING MACHINE AND DESIGNERS PLAZA,  Yaya Jafar ya bada shawaran a sama plazan sunan Mami mutumiyarshi,  duk saboda kar mutane su gane plazan waye,
*************************
Sallama yayi ta Ansa mai shi Kadai ya shigo gidan, yana isa kusa da ita ya zauna “Amarya bakya laifi, “dakata Mallam dama ka daukoni ne danginka su wulakantani iyeeh?  Haba Baby na rungumeta yayi, kara fashewa da kuka tayi na kissa, nan da nan Ango ya rude, ya fara sakin layi nima dai na tattaro biro na da littafina, na gudo nace Allah yasa dai Wainnan Amarya da Angon nan ma su samu suyi dan sallah nafila da Addu’a, don naga Alama Angon a hannu yake, 🙈 nayi nan bani na fada ba🏃🏃
*************************
INDIA
Karatu yayi zafi don yanzu su Zarah basa wani samun zama, sosai,  “Yauwa Sittynerh wai wace na ganku tare jiya a Department kaman na Santa wlh, ya sunanta?  “Sunanta Raleeyat Ya’u kano, “kai wlh  nikuwa na taba jin sunan fa Sittynerh kuma tun da dadewa, Amma na manta inda na Santa, nocking akayi musu, “Bloodynerh ana nocking fa, “bari naje na duba, to, Hanyar fita tayi taje bakin kofa, sai taji gabanta ya fadi, tana bude kofar suka hada ido da wanda  take tsaye bakin kofar, kawai jiri taji ya debeta zata fadi da sauri Zahra ta tareta,
To kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU
Kowa Ummimi ta gani to nima dai ban saniba✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
    *GIDAN GADO*
💗💗💗💗💗💗
 *( THE BRIDE)*
*WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*
*🌹🌹EPISODE FOURTY FOUR&FIVE🌹🌹*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Aunty mu na kanmu (Aunty Hauwa) ina tayaki murnan fara sabon novel dinki mai suna BACIN TA Allah yasa kin fara a sa,a yasa zamu Anfana da, abunda littafin zai fadakar Ameen🙏🙏
Still Dedicated to you Aunty mu muna godiya da kulawa (Aunty Hauwa)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
whatpad
Zeeyterh Rahzeey yaree@
Sun isa Yola karfe ukun dare duk da ma sunyi gudu sosai, An sauki Amarya a gidan Momy su Yaya Amar, sai bayan an gama duk wani Event za, a kai Amarya gidan ta, bayan yan uwanta sunje sun gani Sai su wuce,
Kun san fulani akwai iya karrama baki musamman fulanin Yola, duk da dare suka isa An musu shatara na Arziki, kama daga Abinci ne Abun Shane gurin zama, don part guda aka bude musu a gidan Daddy Babba,
Tunda suka isa gidan suka rude saboda haduwan gidan, niko nace wani Haduwa ai sai gidan Amarya, wai don ma darene, ranar kasa barci sukayi, anata labarin gidan da santin gidan, “keko Billy kin more wlh kinji dadi kin sami mai kudin da kike mafarkin samu, Allah yasa mu a sanshi ki, da kyar Billy ta bude baki ta Amsa mata da cewa, “Ai na gaya muku iklymsi nifa bani ba talaka fa, kawai a haifeni cikin talauci in kara Aure cikin talauci tab ina bazai yuwu ba, “uhmm ke dai Billy ki gode ma Allah aiko family ku ba wasu talakawa bane sunada rufin Asiri, cewan wata kawar Billy, “kefa Halimsy komai kice zaki wani ma mutum nasiha, kawai ki rike kayanki, ni nasan mu akan su Mubarak talakawane, wayyo Allah ni har fa na hango event din dazamuyi gobe,  duniya zasuga Mijin dana Aura na nunama tsara, tashi tayi ta kama rawa duka dakin dariya suka samata, niko nace wannan Amarya ba kamun kai,
“Nifa gskya Abokina inaga Dinner kawai za, ayi  don na kosa a kawomun Amarya na “tofah Sadiq kanajin mutuminka koh, “uhmm ai naga Alama mutumina ya kosa fa, gaba daya ya zama mare kunya, “Uhmm a dai dage ayi Abun kunya Yaya Ameen dai yana jinka, 🙈🙈”Au ashe yayan mu na jina, “a,a ai banaji da dare Mutumina, gaba daya dariya suka kwashe dashi, Uhmm ni wlh Hankalina yana gurin su Baby tun jiya ban samu munyi waya dasu ba, bikin nan naka ya mana cikas, kai Abokina kanafa ji da kannin naka fa, inji Yaya Ameen, “Uhmm a dai gama gulman ni na dade da ganoka son wannan Figaggiyar kanwar taka kakeyi Allah ya kyauta, intayi wari maji, duka Amar ya Kaima Mubarak, Yaya Ameen ya tare, “haba man meye na dukan Ango daga fadar gskya, “Au har fa kai Yayan mu, na bar muku dakin bari inje in kira Baby na yafi, “hhhh oho dai Indai tayi wari maji,
*************************
“Sittynerh kin gane lecture din jiya kuwa?  Ke dai Bari Bloodynerh nifa Hankalina yana gida Ana can anata shagalin biki, mu munanan muna fama da karatu, “tab ni wlh har mancewa da wani biki nakeyi nifa da dai bikin Yaya Amar ne, “wai me Yayana ya miki kika tsaneshi tun ba yau ba ina lura dake ko Maganar yayana baki so in miki, har yau fa baku taba haduwa ba ko gaidashi baki tabayi ba Abun fa na batamun rai, kawai sharewa nakeyi Bloody, in wani Abu Yayana ya miki ki fadamun ina son inga kina shiri da Yayana kamar yadda kikeyi da Yaya Amar, ko kiran waya yayi nace gashi ku gaisa bakya karba, shima yayan sai yace a rabu dake ace yana gaidaki, kudin dukanku wai meke damunku,  iyee juya baya tayi tana share hawayen da suka zubo mata, rungumeta tayi ta Baya don Allah Sittynerh kiyi hkr, wlh nikai na ban san meke damuna,   ki tayani da addu,a kawai kar kiyi fushi dani, zan shiga cikin wani hali,  kuma kinga zai shafi karatun mu, juyowa tayi da sauri itama ta rungumeta suka cigaba da kukan su, sai da sukayi mai isan su, sannan sukayi shiru, kowa da abunda yake tunani a ranshi, Wayan   Baby ne yayi kara ta dauko da sauri, lah sitty Yayah Amar ne to dauka mana, picking tayi My sweet Baby na kuna lpy kuwa, lpy lau Yayana yasu Mamy da su Momy na, ya taron bikin Yaya Mubarak, Alhmdulillah Baby biki gashinan munata sha, ina Autan Mamy ne ina jinka Yaya Amar, ya kukaji da taro, haka dai suka sha hiransu ya musu alkawari gobe duk da Basu, dasu za, ayi Dinner zai kirasu Vedio call, yauwa my Yayan, sukayi sallama kasan cewan lokacin zuwa lecture nasu, yayi.
*************************
Biki yayi Biki can na hango su Iklimsy da Ikram anci Uban kwalliya har baka ganesu, sun fito Ana taku dai dai ga motoci nan birjuk, Anata diban mutane don zuwa gurin Dinner, su Momy ne da Mamy dasu Addah Adama ne suka fito cikin wata rantsatstsen materia, da ka gansu kaga kudi ya zauna,  Manyan Mata kenan da sauran kawayensu, can sai Gasu Maman su Iklimsy da sauran kannin Maman Billy sun fito dasuka ga su Mamy sai suka raina kansu, haka dai aka dunga diban mutane Ana tafiya dasu, Motar Amarya da Ango ne a karshe,
“Niko Maman Iklima kinga wata Mata dana ganta da uwar Mijin Bilki kuwa, sunyi bala, in kama da Aisha Maman su Ummimi fa, ashe bani kadai bane, kawai wannan ta danfi Aisha jiki ne, Da haske wannan kaman balarabiya take, to wai meme shirin faruwa ne wai, kudai cigaba da bin alkalamina.
*************************
Gurin biki ya hadu tsayawa lissafa muku haduwar gurin ma aikine,  kudi sunyi kuka a gurin, tunda Amarya ta iso hall kanta ya kara girma, ta san yes kudi ya zauna,
Yaya Amar ne keta aikin Hada su Baby da yan uwa Ana gaisawa gurin Dinner Amma Basu samu daman gaisawa da Ango da Amarya sabda taron jama, a sai dai sun hango su a nesa,  can na hango su Kawan aunty da aunty a tsakiyar fili, suna cashewa, can basai na hango sis Adama kusa da takwaranta tanata aswaki da kaji😜,  a,a can na hango yan kundin Arewa suna chasewa hardasu Asmeey, da sauran su,
Anci ansha an rakashe, Sai muce Allah ya bada zaman hkr,
*************************
Washe gari yan zaria sun fara haramar komawa gida, sbda daga gurin Dinner aka wuce da Amarya gidanta, ai ruwan kansu ya kare da suka ga irin gidan da aka kerama Billy, aljannar duniya kenan, da Asuba suka dauki Hanyar Zazzau Birnin Shehu, aka bar Amarya da Angon ta,
“Nifa ba wanda zai rakani anjima,  “to fah kunajin rashin kunya irin na wannan Ango, dariya suka sa musu,
“Amaryar fa munata sallama, shiru,  fitowa tayi ta tsaya musu gandakai tana musu wani kallon uku saura kwata, “lpy Kunzo kuna mana shouting a gida,  “To fah ni Adama irin wanda aka kwaso mana kenan, neman guri sukayi suka zauna ita kuma ta cigaba da tsayuwanta, “to ranki ya dade Amarya kidan rage tsawon mana koh, zaunawa tayi ta Dora Kafa daya kan daya ina jinku,  tab Addah Adama da yake tana da zafi, ta tashi ” ke shiga hankalinki duk cikin mu kinga sa, arki mare mutunci mare tarbiya muna kannin uwar mijinki mu shigo cikin gidan Dan mu ki mana diban albrka wlh ba, a haifeki ba, kul ki ajiye haukan da kika zo dashi, ko in gyara miki zamanki, don ki tanbaya kiji Adama bata daukan rai
a wulakanci, “da sauri ta zube a kasa don Allah aunty kuyi hkr wlh ban gane ku bane,,,
*************************
Kudai cigaba da bin YAR MUTAN Zazzau, kuji yanda zata kaya✍️✍️✍️✍️✍️
Vote
Share
Comment
Please 🙏🙏🙏
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(LIFE REMEMBER)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
🌹🌹EPISODE FOURTY EIGHT &NINE🌹🌹
Wannan page naku ne yan group din GIDAN GADO FANS ina godiya da kulawar ku, kuma inajin dadin comment dinku.
“Me kika ma yar uwata iyeeh!!  Wlh in wani Abu ya samu yar uwata sai kin sani, kimin magana mana kin tsaya kina kallona, kukane yaci karfin Raliyat, da gudu Zahra taje ta cakumeta kukan me kikeyi ne Iyeeh kimin magana mana kin Santa ne, a ina kuma kika Santa,?  Da gudu Raleeyat taje ta bude fridge din su ta dauko ruwa tazo ta yayyafa mata, tanayi tana kuka, “don Allah kawata karki mutu ki tashi, ina kika shiga tsawon shekaru ina nemanki gashi ban san gidanku ba, Uncle Mubarak ya nemeki har ya gaji, “nifa kin sani a duhu kimin bayani sai sunbatsihirine, “kamata mu kaita kan kujera ki dauko first Aid box mu bata temakon gaggawa tukun na sai muyi magana, kamata sukayi suka dorata kan three seater dake falo Zahra ta tafi Bedroom dauko Box din ita kuma ruwa ta samu a cup ta fara karanta Falaki da Nasi da Ayatul kursiyyu da karshen suratul Bakarah don wainnan Surori da Ayoyi suna karya sihiri sosai, kuma suna kare mutum daga kamuwa da sihiri Indai ka lazimci karantasu, Allah yasa mu dace, bayan ta gama mata Addu’a a cikin ruwanne ta fesamata a gaba daya jikinta, dai dai lokacin da Zahra ta fito, kawai gani sukayi tana jijjiga, da gudu Zahra ta kariso suka rirriketa, can ta fara jera Atishawa, “Alhmdulillah Allah sarki kawata tsawon shekaru nan Ashe sihirine a jikin ta,  Allah ya saka mana Allah ya isa tsakanin mu da wanda tayi miki wannan aikin, Raleeyat kuka Zahra kuka sun tasata a gaba, kasan cewan tunda ta gama Atishawa barci yayi gaba da ita, bayan sun gama kukan ne sun lallashi kansu, Shine Raleeyat ta kwashe duk labarin su ta fada ma Zahra  sai dai ita ta san Nusaibat yar Zaria ce, amma bata san gidansu ba sai dai tanada tabbacin Uncle Mubarak ya san gidan su, nifa ina zargin Yaya Mubarak shine Uncle Mubarak din da kike magana, Amma Bari kiga pic nashi, wayanta ta dauko ta nuna mata pic din Uncle Mubarak, “wlh kawata shine shiyasa tun farkon ganina dake naga kunamun kama, kawai dai banyi miki mgna bne, Amma suna tare da Uncle Mubarak tsawon nan Basu taba ganin juna ba, tab Allah mai hikima,
“To ni yanzu ya zamuyi da ita in ta frka tace bata sanni ba fa, “Haba kawata Zahra ai bazata ce bata sanki,  ki kwantar da hankali ki, “Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un Sittynerh kaman Raleeyat na gani dazu a bakin kofa, “nice Besty na da gudu taje ta rungumeta, Ina kika gudu kika barni, to yanzu bagani ba, bazan kara tafiya in barki ba, yanxu kin tuno wani Abu, Bloody eh na tuna Sittynerh ni yar Zaria ce Amma ban san gidan mu,  ba kaki damu, kin san wannan,? “Kai Sittynerh wannan ai Uncle Mubarak ne koh Besty, shine fa, “to ai shine Yaya Mubarak din mu wanda bakyason gani,, “to yanzu ya zamuyi, ina neman alfarma a gurin ku karku fadima kowa na warke har sai mun koma gida, ina so muba su Momy mamakine, “haka za, ayi kuwa, nifa Abunda yafi ban mamaki shine da sunanki ya tafi iri daya dana Nusaibat din mu banbancin kawai Yareema da fulani yanzu da Wanne zakiyi Anfani kowanne ma, “kunga ku tashi muje muyi sallah lokaci yayi,
*************************
NIGERIA
“Uhmmm baby ni bazan iya tashi ba, “yadai kamata ki daure muje kiyi wanka sai kiyi Sallah kinga lokaci nata tafiya bakiyi sallah ba, daukanta yayi ya kaita toilet, ya fito ya barta don tayi wanka, shikuma ya shiga kitchen don sama musu abunda zasu ci don Mamy tace suyi girkinsu ko nadan kwana biyu da, ake kawowa bazata kawo musu ba, niko nace Mami me mukayi da zafi haka,
Yana fita toilet din ta fito da wayanta data sakale a bra dinta, da sauri ta nemo number Umma Hello, Ummah, “Hello Amarya bakya laifi, “Umma ni ba wannan ba fa akwai Matsala wlh, “meya faru?  “Wlh Umma duk dangin shi basa sona fa ga wata shegiyan tsohuwa wai ita kaksnsu har da wani cewa ya karamin kishiya nan dai ta kwashe duk yanda sukayi ta fadamata, “yo ke mai zai dameki tunda mijinki na Hannunki Indai kinyi Anfani da maganin nan da nace kiyi matsi dashi, Indai komai ya wakana tsakaninku to angama zance, zuwa gidan su ma sai kin ga daman yaje, “eh Ummah nayi Anfani dashi, kinji inda yake sunbatu ne, 🙈dariya gaba daya suka kwashe dashi, “Shiyasa nake sonki Umma, “to ya za, ayi zan samu ko dubu Hamsin ne, “Eh Ummah karki damu zanma Yaya Jafar transfer sai ya baki, ke rabu da dan banzan yaron nan da yazama shanyayye, kimin a na Yayanku Sulemanu, to Ummah, sai anjima ji tayi an bude kofar Bedroom, da sauri ta saki shower tayi wanka ta gargasa jikinta, Amma batayi wankan tsarki ba, hakan duk yana cikin dokan Boka, niko nace waiyazubillahi,
Haka tayi wankanta ta fito abunta nanda nan ta shirya tasa hijab ta zauna a kan sallaya kaman tayi sallah,
**************
Lokaci na tafiya inda shekaru suka tafi, Abubuwa da yawa sun faru, Yanzu Billy tayi Nasarar raba Mubarak da Ahalinshi sai abunda tace mishi da sharadin duk randa suka hadu da Ummimi Asirin zai karye, yanzu Billy ta haifi yara biyu da Habibullah ana cemai Anwar,  sai Habiba wato sunan Umnanta Ana cemata Iman, yanxu saura wata uku su Zahra su dawo a matsayin cikakkun likitocin mata, sau uku su Momy na tsiyartan su, inda sun kara zama yan mata masu aji wanda in ba sanin su kayi sosai ba bazaka ganesu ba, karma Ummimi taji, don ta fisu cika da komai,
***********************
INDIA
karatu yayi tsafi suna gab da Exam din karshe basa da sukuni kwata kwata, duk da cewan suna daya daga cikin masu kokarin Daliban da, akeji dasu,  a department dinsu,
Sun fito sunata farin ciki yau sunyi final Exam dinsu.
Kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU
Share
Comment
Vote✍️✍️✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(MISSING OUR COUNTRY ZAHRA&NUSAIBAT&RALEEYAT)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
🌹🌹EPISODE FIFTY&ONE🌹🌹
Wannan page din kyautane ga duk sababin members din da muka samu a AREWA WRITERS ASSOCIATION ina muku fatan alheri.
Aunty mu na kan mu mai share kukan mu (Aunty Hauwa)  Allah ya kara daukaka ya raya zuri,a.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
***********************
INDIA
Da gudu Zahra tazo ta rungume Ummimi wayyo Bloodynerh yau burin mu ya cika, Mun kammala karatun mu lapiya tare da nasarori masu yawa, ji sukayi an kara rungume su, Ta bayansu juyawa gaba daya sukayi, “kai Besty kin bamu tsoro fa😂 “to sarauniyar matsorata, dariya duka sukayi, Motar su suka nufa wanda Daddy ya siya musu don zirga zirga, “Sittynerh yaufa ke zaki tukamu wlh na gaji, “ai dama na sani wlh nima bazan tuka ba, kullum ni nake tukawa, “kudai wlh kullum sai kun raba hali, gashi in mutum ya shiga fadanku ku bashi kunya, “Eh din kinji Sittynerh kawo key din zan tuka, haba mana Sittynerh kiyi dariya mana ko sai nace Autan Mamy ne kawar Hajia Kilishi, 😂kwashewa da dariya duka sukayi, ni kin san mene ke damuna ma  Bloodynerh muna komawa gidan wannan tsohuwan zata taso mu gaba, gunda ma kefa, naga tana daga miki Kafa, hhhhh”wlh na lura Sittynerh kina bala’in tsoron Kilishi ni kuma banji tsoronta har hira fa mukeyi in mukaje dake inkin fita kin barni dakinta, Uhmmm “ai ke din da banne Sittynerh kinada wani kwarjini da kikema mutane kamar yadda itama Kilishi ke dashi, kai har mun iso gida Ashe, suna shiga gida, Zahra ta kira Mamy ita kuma Ummimi ta kira Momy suka fara hira, suna Basu labarin Exam dinsu, haka suka sha hiransu, wai Mamy ina Yaya Mubarak ne?  Tunda fa mukazo kasar nan bai taba zuwa ya dubamu ba,  kuma har yanzu ko kalan Amaryan da yaranshi fa bamu sani ba, “Uhmmm Auta ke dai kawai ki Bari Yayan ku yana bukatar Addu’a don sai muyi wata bamu sashi a ido ba, “what!!? Mamy ko gaudaku bai zuwa kenan,?  “Sai ya dauro mai zaizo yayi ta bamu hkr yace bazai kara ba, shi kanshi bai san meke damunshi ba, “tab Mamy Amma wannan ba aikin sihiri bane kuwa, ya kamata ku tashi mai tsaye da Addu’a hakane Raleeyat sihiri ne kuma muna zargin matanshi ta mai, duk da ance zato zunubi, “Tab wlh Mamy muka dawo zamuje har gidan sai ta gane kuranta kuma ta karya sihiri data ma dan uwan mu, shegiya la,a nanniyan Allah kawai, to waima Mamy yar gidan uban waye ita, hala daga gidan marasu tarbiya ta fito karamin gida, duk Ummimi take wannan maganar, niko nace a,a Ummimi karki zafafa kanwarkice fa, sallama sukayi da Mami kowa ranshi a bace, musamman Ummimi da tun daga lokacin data dawo hayyacinta, taji ta tsani matar Yaya Mubarak kuma kullum sai tunanin shi takeyi, ga kuma soyayyanta da Yaya Amar jira kawai yake su dawo a Daura musu Aure, ya Allah ka kawomun mafita, bazan taba iya Auran Mubarak ba, dayana sona bazai taba Aure ba zai ta nemana ne, ya kuma jirani, Amma gashi yayi Auren shi Harda yara biyu, kuma yana sonane don sister Nusaibat data rasu, “Sitty wai tunanin me kikeyi ne tun dazu inata magana kinyi shiru, firgigit tayi ba komai Sitty na kosa mu koma gidane, karki damu jibi fa su Momy zasu zo, ranar Monday zamu yi celebrate Tuesday kuma muna gida inshaallah, muna komawa zamu sanar dasu Momy komai, daganan sai Yaya ya kaimu Zaria muga family ku mu dawo don bazasu kwace mana ke ba,  ehee,
*************************
NIGERIA
Momy ne ke ta shiri yayin da Affan ke tayata, “Momy I eager to see my Aunties fa, kai Affan ne ya zama saurayi haka, “aini Affan na fika kosawa inga Baby na kaman in jawo anjima in ganni a jirgi, “tab Momy aini duk nafi ku kosawa fa, Waigawa duka sukayi, “yaushe ka shigo gari Soja Mazan fama, murmushi yayi “wlh Momy yanzun nan, ok
“Abul khairi “yes Mamy wani dan gayun yaro ne ya fito yaci Ado Abunshi, sai da na kalla da kyau naga Ashe Abokin na Affan ne, ka dauko mun hand bag dina a daki, tom Mami
Gaba daya sun dunguma Harda yaran Mubarak kasancewar Kilishi taje har gida tama Bilki kaca kaca dataji Abunda ke faruwa kuma ta kwashe yaran ta dawo dasu gidan su Mami, sai Gasu a Airport kowa ka kalla kasan yana cikin farin ciki, nan da nan jirgin su ya daga sai india, niko nace su Mamy a dawo lpy nima ina nan zuwa da yan Indian gidan mu AREWA WRITERS ASSOCIATION, Meraahenat da lashyzmeyy😜.
************************
INDIA
“Ke lashmey ki sauri fa zamuje gyaran kaine fa, ok wanda aka kira da lashmey na kalla wata yar india ce datake musu aike aike a gidan nasu Yaya Amar ya daukan musu ita sbda Abubuwa sun musu yawa,
Su Momy sun iso lafiya, kawai dawowa sukayi sukaga Su Momy a gidan, ai da gudu sukaje suka rungume iyayen nasu, wayyo zaku karyamune baku ga inda kuka zama yan lukutaye bane, kai Mamy, “Uhmmm wato ni baku ganni ba ko su Momy kuka gani, ai da gudu sukaje gurinshi, Zahra ta rungume shi yayinda Ummimi tayi birki ta kasa karasowa, bude mata hannu yayi, sai ta kale mai kafada tana mai Murmushi, haka lashmey ta jera musu Abinci kowa ya hallara har su Daddy da sukaje Sallah sun dawo, an fara cin abinci kenan sai sukaji nocking izinin shiga aka Basu Ashe Raleeyat ne, da iyaeyenta itama da kanninta, biyu duka Maza, suna shiga Falon Alhaji Ahmad ya mike a,a Alhaji ya’u, “na, am Alhji Ahmad nan fa aka fara murnan ganin juna Ashe Abokai ne, gashi sanadiyan yaransu sun kara haduwa, nan hira ya barke tsakanin Family suna cikin farinciki,
Washe gari ranar celebrate din su Hall ne ya Amsa sunansa Hall inda kowa ka gani a gurin dan wanine, taro yayi taro inda aka fara gabatar da taron anyi presentation anyi debate kusan kowanne da Nusaibat inda ta samu manyan kyaututtuka ita da Zarah, Anan ma gwamnatin india ta daukeso aiki a babban Asibitin New Delhi in suna so saboda kwazon su, kyauta ko har sun rasa ina zasu sakashi, duk inda aka juya daukan su akeyi a pic ana watsama duniya, bayan angama komai Ummimi tayi kukan farin ciki bata taba tunanin zataje wani kasa karatu ba, Balle har ta samu irin wannan daukakan, ba, abun dazata cema su Momy sai dai Addu’a don bazata taba biyansu abunda suka mata ba,
Washe gari suka shirya sai Nigeria kasarmu ta gado kowa ya bar gida gida ya barsa, sun iso Nigeria karfe takwas na dare, Driver ban gidan Hajia Kilishi yazo ya daukesu sai gidan Hajia kilishi.
*************************
Tom kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU kuji yanda zata kaya..✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Please ✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
     *GIDAN GADO*
💗💗💗💗💗💗
 *(OUR COUNTRY)*
*WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*
*🌹🌹EPISODE FIFTY TWO&THREE🌹🌹*
*Wannan page din sadaukarwa ne ga duk wata mai suna (ZAINAB)  Ina matukar son sunana I love my Name😂🙈*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.*_
“Yahaya wannan ba Ummimi bane,?  Wai ina ma take ya akayi taje kasar India karatu, to wai ma ya, akayi duk muka manta da ita a Family din mu, da sauri suka fita don zuwa sashin Hajiya yayah, kadan ya rage suyi gware da Habibu lpy Na ganku haka?  “Ai kai zamu tanbaya lpy, “kunga Abunda na gani kuwa Ummimi ya’ta na gani a TV fa  ya akayi ta tafi meyasa muka manta da ita Wai, “nima tanbayar da nakeyi ma kaina kenan fa, mu karisa gurin Hajia Yaya suna shiga dakin Hajiya yayah suka tarar da ita tana zagaye dakinta, “lpy Hajia?  Da sauri ta waigo, “Yauwa Jibrin dama ina shirin nemanku ne da fatan kunga abunda na gani a TV?  Lokaci yayi da kowa zai san Abunda yake faruwa a gidan nan, Jikata mafi soyuwa a gidan nan aka ma Asiri ta shiga duniya, aka mantar da kowa a gidan nan game da ita, sai ni Kadai, da komai ake shiryawa a gidan nan akan idonane da kunnina, tunda Ummimi ta bar gida har yau ina bibiye da rayuwar datake ciki, na tabbatar ta fada hannu na gari, naki daukan matakin komai ne sbda na Bari Allah yayi ikonshi akan makiya, sannan su san cewa zakarar da Allah ya nufa da chara ko Ana mazuru Ana shaho sai yayi, Burin  Ummimi ya cika zata dawo gidan nan kwanan nan a Matsayin cikakkiyar likita, A lokacin Mahassada zasuyi kuka da idanunsu kuma su tona Asirin su kowa ya sansu, Abunda nakeso da ku yanzu kar wanda ya tada Maganar Ummimi a cikin ku, a cigaba da tafiya a haka, har Allah ya nuna mana ranar da Ummimi zata dawo gidan nan, “Insha Allah Hajia haka za, ayi  mun gde juyawar dazasuyi kawai ganin Mama sukayi a bakin kofa ta durkushe tana kuka a gurin da sauri Hajia Yaya ta karaso gurinta, ta dagota ta rungumeta, tana rarrashinta, Guggo tsohuwa a tsaye a bakin kofa ita ma ta hawaye, “Ashe Nusaibatu Halin da muke ciki kenan Allah mun gode maka, kiyi  hakuri Aishatu haka Allah ya tsaramuki naki rayuwar kin taso cikin Ahalin da ba naki ba har kin hayayyafa, har yanzu bamu samu wani lbr da zai bayyana Ahalinki ba, sai gashi tarihi ya maimaita kansa akan diyarki, Amma Alhmdulillah ita gashi zata dawo garemu cikin farin ciki, kukane yaci karfin Mama ta kara rungume Guggo tsohuwa “ni banda kowa da ya wucemun ku, kune Ahalina bandaku ban san kowa ba, kice Uwata Allah ya ji kan Babana Jibo ya nunamin gata na duniya, shiyasa kullum nake mai Addu’a Allah yaji kanshi, duka suka Ansa day Ameen gaba dayan su,
*************************
YOLA
“Kut Innalilahi wa Inna ilaihir raji’un wannan ai Ummimi ce kuma wa’innan mutanen ai yan gidan su Mubarak ne, meyake shirin faruwa damu ne dama bata mutu ba mun shiga uku, wayyo Allah na, da gudu tayi hanyar Bedroom dinta zata dauko phone nata, jitayi tayi karo da mutum, “kai Baby yaushe ka dawo, wani kallon tsana da yayi mata sai da hanjin cikinta ya kada…
*************
Tofa kodai kodai kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU ✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Please 🙏🙏🙏
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(OUR COUNTRY)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
🌹🌹EPISODE FIFTY TWO&THREE🌹🌹
Wannan page din sadaukarwa ne ga duk wata mai suna (ZAINAB)  Ina matukar son sunana I love my Name😂🙈
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
“Yahaya wannan ba Ummimi bane,?  Wai ina ma take ya akayi taje kasar India karatu, to wai ma ya, akayi duk muka manta da ita a Family din mu, da sauri suka fita don zuwa sashin Hajiya yayah, kadan ya rage suyi gware da Habibu lpy Na ganku haka?  “Ai kai zamu tanbaya lpy, “kunga Abunda na gani kuwa Ummimi ya’ta na gani a TV fa  ya akayi ta tafi meyasa muka manta da ita Wai, “nima tanbayar da nakeyi ma kaina kenan fa, mu karisa gurin Hajia Yaya suna shiga dakin Hajiya yayah suka tarar da ita tana zagaye dakinta, “lpy Hajia?  Da sauri ta waigo, “Yauwa Jibrin dama ina shirin nemanku ne da fatan kunga abunda na gani a TV?  Lokaci yayi da kowa zai san Abunda yake faruwa a gidan nan, Jikata mafi soyuwa a gidan nan aka ma Asiri ta shiga duniya, aka mantar da kowa a gidan nan game da ita, sai ni Kadai, da komai ake shiryawa a gidan nan akan idonane da kunnina, tunda Ummimi ta bar gida har yau ina bibiye da rayuwar datake ciki, na tabbatar ta fada hannu na gari, naki daukan matakin komai ne sbda na Bari Allah yayi ikonshi akan makiya, sannan su san cewa zakarar da Allah ya nufa da chara ko Ana mazuru Ana shaho sai yayi, Burin  Ummimi ya cika zata dawo gidan nan kwanan nan a Matsayin cikakkiyar likita, A lokacin Mahassada zasuyi kuka da idanunsu kuma su tona Asirin su kowa ya sansu, Abunda nakeso da ku yanzu kar wanda ya tada Maganar Ummimi a cikin ku, a cigaba da tafiya a haka, har Allah ya nuna mana ranar da Ummimi zata dawo gidan nan, “Insha Allah Hajia haka za, ayi  mun gde juyawar dazasuyi kawai ganin Mama sukayi a bakin kofa ta durkushe tana kuka a gurin da sauri Hajia Yaya ta karaso gurinta, ta dagota ta rungumeta, tana rarrashinta, Guggo tsohuwa a tsaye a bakin kofa ita ma ta hawaye, “Ashe Nusaibatu Halin da muke ciki kenan Allah mun gode maka, kiyi  hakuri Aishatu haka Allah ya tsaramuki naki rayuwar kin taso cikin Ahalin da ba naki ba har kin hayayyafa, har yanzu bamu samu wani lbr da zai bayyana Ahalinki ba, sai gashi tarihi ya maimaita kansa akan diyarki, Amma Alhmdulillah ita gashi zata dawo garemu cikin farin ciki, kukane yaci karfin Mama ta kara rungume Guggo tsohuwa “ni banda kowa da ya wucemun ku, kune Ahalina bandaku ban san kowa ba, kice Uwata Allah ya ji kan Babana Jibo ya nunamin gata na duniya, shiyasa kullum nake mai Addu’a Allah yaji kanshi, duka suka Ansa day Ameen gaba dayan su,
*************************
YOLA
“Kut Innalilahi wa Inna ilaihir raji’un wannan ai Ummimi ce kuma wa’innan mutanen ai yan gidan su Mubarak ne, meyake shirin faruwa damu ne dama bata mutu ba mun shiga uku, wayyo Allah na, da gudu tayi hanyar Bedroom dinta zata dauko phone nata, jitayi tayi karo da mutum, “kai Baby yaushe ka dawo, wani kallon tsana da yayi mata sai da hanjin cikinta ya kada…
*************
Tofa kodai kodai kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU ✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Please 🙏🙏🙏
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
( MY DECISION)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
🌹🌹EPISODE FIFTY SIX&SEVEN🌹🌹
Wannan page din na sadaukar dashi ga duk wani Masoyin Novel dina  GIDAN GADO,  Allah ya bar kauna.
Cakume Billy Zahra tayi “wlh Yayana ya mutu kema Sai kin mutu,  “dallah malama sakeni!! Kilishi ta ce a debo mata ruwa a cup, bayan an debo ta zauna tayi Addu, oi a cikin ruwan, ta mikama Momy datake ta Kuka, tace Amsa ki yayyafa mishi ku dago shi ku bashi ya sha ku tabbatar ya wuce mai cikin bakin shi, sbda tabbas jikin yaron nan akwai sihiri, kuma yarinyar can ita ce makarin sihirin shi, na sha gani a barcina, Billy komawa tayi gefe ta rabe ba, abun da take Sai aikin kuka, tasan Zamanta da Mubarak ya kare shikenan gashi bata san yanda zatayi ta samu Umma ba,
Bayan An yayyafa  mai ruwa ne, ya dunga jera Atishawa can kuma ya fara Wani bakin Amai, hade da wasu mulmula mulmulan Abu a cikin Aman, duk Hankalin su Momy gaba daya ya tashi, Kilishi tace musu kar ku damu sihirin dake jikinshi ne yake fita, ya kusa Awa daya yana Aikin Abu daya, ya wahala sosai daganan Sai wani barci mai nauyi ya daukeshi, su Daddy suka daukeshi aka gyaramai jikin shi, su kai shi daki, kowa ya kama gabanshi aka bar Billy a gurin ba wanda ya Kara bi ta kanta, ina shiga daki na fada gado na fara kuka sbda ganin Billy da Uncle Mubarak yau ya Kara tunamin komai na rayuwata, ina Mamana da Hajia Yaya wani hali suke ciki, dole zanzo in bar family nan don bazan taba iya Auren wanda ya Auri yar uwata ba, bawai zan butulce musu bane ko inki musu biyayya bisa hukuncin da suka zartar a kaina ba, yaya family na zasu dauki maganar Mijin Billy nake Aure da wani ido zasu kalleni, kai Ina bazan iya ba, Zahra ne ta shigo dakin, ta dafa ni, “don Allah Bloody kiyi hkr komai ya faru da bawa mukaddarine ga Ubangiji kiyi hakuri mu rungumi kaddaran mu, nasan bakyason dan uwana, Amma karkiga laifin dan uwana ba yin kanshi bane, wlh dan uwana na sonki sosai,
Karfe hudu dai dai, a lokacin ne kuma Yaya Mubarak ya farfado, da sauri Amar ya tashi ya rikeshi, yayin da Billy itama ta taso da saurinta, “dallah malama karki tabamun dan uwa muguwa kawai, wlh Sai Allah ya ma dan uwana sakayyah, sannu kaji besty, binshi da kallo yayi, da kyar ya bude baki, yace mai Besty taje na saketa saki biyu in ta sami miji tayi Aure, ban san ganinta ta cutar dani a rayuwa ta rabani da komai nawa, ta rabani da wanda nafi so a rayuwata, “wayyo Allah na shiga uku Baby kayimun rai wlh bazan iya rayuwa ba kai ba, don Allah kayi hkr kar muyi haka da kai ka taimakeni “dallah!! Malama ki fita daganan yace ya sakeki ko dolene Auren kudi ya jefo mata dauki kiyi na mota, “to yarana fa?  “Oh dama dasu kikazo iyeh bar nan gurin kafin in karyaki, da gudu ta fito, yayin da Ummimi ma ta juya da sauri ta shige kitchen ta Kara rushewa da kuka, wai yar uwanta ake ma kurar kare, tabbas tare zasu tafi, Indai ta tafi itama anjima zata kama hanyar Zaria,
Bayan fitowan Billy, can gidan su ta koma, Amma mai gadi kiri kiri ya hanata shiga, Sai dai Akwatin kayanta da ya miko mata, yace umarnine daga oga yace kar a barki ki shiga gidan, “hauka cemai tayi ta  dunga buga gidan wlh Sai ka budemun gidan Ubanka ne, dazaka hanani shiga iyeh?  Shidai mai gadi shigewa yayi ciki ya maida get ya rufe, ya barta anan da ta gaji taja akwatin ta tayi tasha tana tafe tana kuka, niko nace Billy Allah ya raka taki gona nima na dana inji su takwara bani ba😜, yau dai Billy Sai kwanan Zazzau, Umma yau zakiyi babban bakuwa ko ince baki don Ummimi ma tana hanya yau zaki girbi Abunda kika shuka.
*********************
“Maman Baby nifa yau gabana Sai faduwa yakeyi “to Maman jafar ni ina ruwana Allah yasa masifan da kike ta tarama kanki ne zaki girba, ehe ni da nake rakaki muke aikin nan tare Amma don kun samu duniya ne kika gujeni, ki ka maidani Banza, Au haka ma zakice lallai dan Adam butulu ne, duk hidiman danake miki baki gani, don kince in baki dubu Ashirin na hanaki shine kike cemun haka, “Ance din, danbe ne ya kaure tsakanin su, nan da nan Gida aka fara taruwa kasancewar gidan haka yake, da An fara fada zasu fara  taruwa kuma ba mai rabawa,  musamman fadan kawa da kawa, don kowa yayi mamaki, ga yar tone tone da suke tayi a tsakanin su.
***********************
Ummimi ne ta fito rike da akwatinta a hannu Sai data duba ba kowa a falon da harabar gidan sannan ta Ajiye musu letter a kan kujera ta tafi, niko nace Ummimi baki kyauta ba, bakiyi halarci ba, Ummimi ta dauki Hanyar zaria.
************************
Dambe yayi danbe har da jin ciwo har dare Ana Abu daya kwatsam Sai ga Billy ta shigo tana rusa kuka, gaba daya kallo ya koma kanta dama ga mutanen gida gaba daya a tsakar gida a na kallon danbe don Baffa Yahaya yace kar wanda ya rabasu a barsu su daku da kyau in sun gaji sa bari, Sai ga wani tashin hankali, da gudu ta yar da Akwatinta taje ta rungume Ummanta, da sauri Umma ta jata suka shige daki,  kowa ya watse Ana ta gulmace gulmace, wasu suna Allah Kara dama Auren bana Allah bane shiyasa baiyi lasting ba tunda gashi Maman Baby ta fara tona Asiri.
Ummimi ta sauka zaria karfe ukun dare,  da kyar ta samu Napep din datayi drop ya kaita har bakin titin Ungwan su kasancewar Abun hawa bai shiga ungwan, da kyar taja Akwatin ta har ta Kai kofar gidan su, Yaya Ameen ta tarar yana zaune yayi tagumi, ta isowa da sauri ya taso yaxo ya rungumeta “Well come to Home my sweet sister, I miss you too baby Hajiya, Congratulations Ashe kanwata ta zama likita, kawai kuka Ummimi ta fashe dashi, “Yaya ya akayi kasan duk wadan nan Abubuwan game dani, kinga mu shiga ciki Hajia yayah ta nan ta miki mutuminki, dan wake, 😜karfa kuce best food dina kenan, suna shiga Hajiya Yayah tazo da gudu ta rungume ta, “Sannu my jikalle na, Kara rungumeta Ummimi tayi tanata rera kuka da kyar Hajia Yaya ta rarrsheni, nayi shiru ranar kwana nayi banyi barci ba, muna hira da Masoyiyata, ranar duk wani labari Sai dana ba Hajia yayah, ranar tsohon shagwaba ya tashi, washe gari kuwa kowa yaxo gaida Hajia Sai ya ganni kuma kowa ya kasa mgna, nan da nan labari ya wade gidan fulani cewa Ummimi ta dawo, nan aka fara gulmace gulmace cewan taje gantalinta ta dawo tunda gashinan tayi kiba ga dan kunnin gold ne a kunninta, ta zama kamar baturiya kilama ciki gareta, inda tayi wannan kiban haka, magana dai ba dadin ji, bayan an natsa Hajia Yaya ta kira taron gaggawa inda ciki Harda Billy da Umman su, bayan kowa ya hallara ne Hajia Guggo ta bada umarnin Ummimi ta fito, ai tana fitowa Maman Jafar da Billy da Maman Baby, ita Billy tana mamakin yaushe Billy ta iso, ita kuma Ummanta Asirin da tayine ya dawo kanta, nan ta fara jifa da dankwalinta ta fara ihu Ummimi na cuceki, nan ta fara fadan duk abunda ta aikata, tun daga barin Ummimi gida har zuwa jiya da Billy ta dawo musu da mummunar labari, kowa salati ya fara sauran yaranta kuwa kuka suke tayi suna bama Mama da Baffa Habibu da Ummimi Hkri, kawai gani sukayi Umma ta falla da gudu don Allah ku rukota zata tafi, Billy ne take fadin haka, Yaya Jafar ne da Yaya Umar suka mike zasu rukota, Baffa Jibrin yace duk wanda ya bita bai yafe mai ba sunaji suna gani Umma ta tafi, ita kuma Maman Baby tunda ta fadi fralyse ya kamata, nan Ummimi taba kowa lbrn Abunda ya faru kowa ya tayata murna nan Baffah Jibrin yace ta zauna har Sai sunje sun musu godiya da irin rukon dasukamin sannan akwai Wani Asibiti a bayan layin nan ku fara zuwa kina voluntry har lokacin da komai zai dai daita, gashi su Baffa Jibrin sunje sun samesu Kilishi tai ta fada akan meyasa na gudu, sbda haka su tattaroni in dawo in ba haka ba zatazo da kanta, ita kuma Hajia Yaya tace ba inda za, a kaini in suna sona su zo da kansu, to kinji lbrn NUSAIBAT, “to Aunty ita Billy yanxu tana ina tana nan a gidan mu, tana fuskantar matsaloli Kala Kala, shi kuma Uncle Mubarak ance yana nan baida lpy kuma Kilishi ta hanashi zuwa, ita kuma Zahra tace bazatayi Aure ba Sai dani, “gskya Aunty na tausaya miki, Amma wlh in nine ke nafi karfin in zauna Asibitin nan, “in banda abunki ai taimakon garina nakeyi da Unguwta sbda watarana bazanyi ba, nidin ina da kishin garina, kuma Ina son inga garina ya cigaba sosai,  “hakane Aunty kinga har lokacin sallah yayi, wlh kuwa, duk ke kika ja mana.
*************************
Kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU don jin yanda ta kaya ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Please ✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(SUPRISE BIRTHDAY 🎂🎂)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
🌹🌹EPISODE FIFTY EIGHT &NINE🌹🌹
Sadaukarwa ga uwata mahaifiya ta Allah ya Kara miki lpy da Nisan kwana Ameen.
*************************
Sauri take tayi don yau Basu tashi da wuri ba gashi tana so taje Sabon gari tadan siyo wani Abu,
Tana dosowa kwanan layin su ta tarar da taron madinka hade da sa’ido, dauke kai tayi ko kallon su batayi ba, nan suka fara sababben nasu wato gulmanta, “kai Dan,Asabe ga karuwar gidan can ta dawo, “wai kuko meye matsalanku da yarinyar nan, duk kunbi kunsa ma yarinya ido ni wlh banjin dadin Abunda kuke fadi akanta, “an fadi din don kana tare da yayyinta sai kace karmu fadi gskya yarinyar da ta je yawon duniyanta har fa kasar waje taje wai karatu, bayan mun san komai, to ai sai kuyi na barku banzaye munafikai kawai,
Isanta gida kenan Mami ta fara gani taci kwalliya don yanzu Mami ta Kai shekara sha biyar ta fara zama yan mata don akwaita da daukan wanka ga yangan bala’i, “aunty Ummimi ai ina shirin biyoki Asibitin ne munjiki shiru, tana yi tana wani yatsine fuska da baki, “to uwar iyayi ni matsa kiban guri Mutum shikenan ya cika fuska da make up kaman mai aljanun kwalliya, “uhhhmm to wai ke Aunty don ke bakya son kwalliya sai kice kowa ma kar yayi don kinga kina da kyau ne kuma ke farace, ai wlh dani ke da kyanki da anga wulakanci, “ke dallah uwar surutu ban guri ai halinku daya da Yaya Jafar din shiyasa shirgin ku yaxo daya, wucewa tayi abunta tana masifan Surutun Mami, tana shiga taji falon tsit haka ma gidan duk hayaniya irin ta gidan su, to meya faru, bayan ta shiga daki, kayan ta Kawai ta cire ta shige toilet donyin wanka, tana fitowa taga Mami a Zaune a kan katifanta, “ke wai lapiyanki kin Kara zuwa ki damenin ne,? “Kai Aunty na kaya na kawo miki wai kisa inji Hajia ki kizo dakin baki ana jiranki, don Allah aunty ki tsaya in miki make up kin san ina fa make up din kudi nida Baby Yaya Jafar ya samu ita taki yi niko gashi na iya, don Allah kisa kayan in miki make up din ko light make up ne, “Naji din baki abun magana dallah miko min kayan, mikamata kayan tayi, tasa “Woww my sweet Aunty kin ganki kuwa, inaga nayi miki make up ai sai an kasa ganeki, “Oh ni Nusaibatu na shiga uku da yarinyar nan, dariya Mami tayi, “Sorry Aunty na zo in miki, Zama tayi tayi mata hadadden Make up shima anayi ana fada, Wowww readers ku hango mun Ummimi irin haduwan da tayi ya kamata Yayah Mubarak yaga wannan kwalliyan ya kuma biya kudin😂, jefota tayi da pillow din da ke kusa da ita, da gudu ta fita tana mata dariya, “sai Aunty na, “zaki dawo ki sameni, mare kunya, “Aunty kiyi sauri dai ana jiranki a Fallon baki na Alhaji Mallam, “Naji baki Abun magana, tashi tayi ta kalli kanta a mirror ita kanta tasan ta hadu, don wani hadadden gown na material kaman an gwadata dai dai jikinta ga shape din nan ya fito sosai a cikin kayan, ta kalli mayafin shima kanshi abun kallone da gown din da mayafin pitch colour ne mayafin takalmin ma haka sai dan golden a jikin takalmin kasancewar dan kunne datasa da sarka golden ne, kai tsayawa baku lbrn ma bata lkcne ku kiyasta ma kanku irin haduwan da Ummimi tayi, ita kanta ta yaba tasan tayi kyau ina ma Yaya Amar yaga kwalliyan nan, niko nace fadi gskya dai Ummimi kice dai Yaya Mubarak, to wai duk wannan kwalliyan na menene, ita tanaji a jikin ta kaman Sittyneerh tana gidan nan kuwa, haka dai ta gama tunane tunanenta ta fito ta Kama hanyar falon baki, tana zuwa taga Mami a tsaye a kofa,  “yauwa aunty kin fito dan tsaya minti biyu, da sauri tazo dayake tsawon su daya da Ummimi tana zuwa ta rufe mata ido da wani farin handkichef “wai Mami me kikeyi hakane sorry aunty me dai ki tsaya ki ga ikon Allah, rike mata hannu tayi, suka shiga fallon tana shiga taji kanshin turarukan da bazata manta dashi ba, ji tayi sun tsaya, “yauwa aunty tsaya Anan, Oh ni yau naga ta kaina,  Da sauri aka kunna wutan falon haske ya gauraye ko ina a falon wasu Kala suke bada hasken wazan hango Zahra, Yaya Amar, Yaya Mubarak, Yaya Umar Yaya Jafar sai Yaya Ameen, Sai sis Raleeyat, da gudu Zahra ta taso ta rungumeta, tana rada mata, a kunne, “HAPPY BIRTHDAY SWEET BLOODY WISH U MANY YEAR GOOD HEALTH BLEESING MORE  CIGABA MAI YAWA, YA RABAKI DA SHARRIN MAKIYA MAHASSADA, YA BAKI ABUNDA KI KESO DUNIYA DA LAHIRA, I MISS YOU BLOODY,,,,,,,,,!!! sai da falon gaba daya ya Amsa da sauri Ummimi ta cire kyallen da aka kulle mata ido ta rungumeta I miss u too Bloodynerh sai hawaye da dariya sukeyi na murnan ganin juna gaba daya falon aka fara musu dariya, “Happy Birthday to you,,!! Happy birthday to u dear da sauri suka waiga gaba dayan su, suna murmushi, Yaya Ameen ne ya iso kusa dasu to cewgum kun wani manne da juna kaman zaku hadiye kanku, dariya duka aka kwashe dashi, “to yayan mu baka ga mu ko a nuna ma an san da zuwan mu ba, ko farin cikin ganin mu ba, ayi ba, sunkuyar da kai Ummimi tayi, “sorry yaya Amar wlh nayi farin cikin zuwanku mana ina su Momy gaba daya,? Shiko Yaya Mubarak gaba daya ya kasa yin magana gaba daya kallonta yakeyi duk inda tayi yana jin wani soyayyanta na Kara ratsashi, sai data tsargu da kallon da yake mata, sai taga gaba daya shi Yaya Amar hankalin shi na kan Zahra, hakan data gani ba karamin dadi yayi mata ba, shiyasa ta nesanta kanta dasu don su daidaita junan su, zata rungumi Mubarak dinta duk tana tunanin yar uwanta ya ku mutane zasu kalli Abun, “ke wai Bloody tunanin me kike tayine iye, inata magana kinyi shiru, muje a yanka Cake, “sorry Sittynerh banji bane, “ai dama ina zakiji kun shige lanbun Soyayya keda Yayana, duka ta kaimata,  “aini wlh ma dukan ku na fasa kulaku duk kun wani shareni kaman baku ganni ba, “Lahh Besty dama dake akazo wlh ban ganki ba dama ina zaki ganni, Zuwa tayi ta rungumeta Sorry my Besty, “kasan meye Umar? “A, a Sai ka fada, “wlh tun dazu Yaya Ameen keta Satan kallon Baby can “wai wancan yar black din, “eh ita fa, “ai wlh ta hadune fa, kai baka ga inda Yaya Mubarak yake kallon Ummimin Hajia bane, kai dukan su Soyayyan su fa sukeyi mu mun zama yan kallo, “tab kai kazama dan kallo, ni ga Mami na nan a gefe 😂, Dallah matsa mare kunya kawai, “to magulmata in kun gama gulman ku taso a yanka cake, 😂dariya suka yi, “kai Yayah Ameen mune magulmatan sun iso gurin yanka cake, Zahra da Raleeyat ne suka rike mata hannu ta yanka,  Amma ba haka Yaya Mubarak yaso ba, su Zahra sukayi mai shishshigi😂, nan aka hau tafi Suna mata Happy birthday kowa yaxo mika gift din shi sai ta bashi cake din a baki, Zahra ta fara vata gift din wani hadadden writch, ta debo cake ta cusa mata, duk ta vata mata fuska, aka samu  dariya, haka kowa ya vada gift dinshi sai da sukayi da Yaya Jafar, kaima dai kasan da kadan kuka gurmeni kai da Yaya Umar din, oho dai mun girmekin dai, to ai yanzu na zama aunty ka, tunda kanwata kake so, dallah matsa, sai da kowa ya gama bada gift dinshi sai ga Anwar da Iman da Abban su sunzo bada nasu gift din yaraTakwaralle girma da bul bul, sun iso gabanta gaba daya sun tsaya suna kallonta fuskan tausayi sukayi, sai ta samu kanta da dukawa a gabansu, taji wani tausayin yaran har cikin ranta, hada baki sukayi suka hada hannu biyu Alaman roko, “Aunty did u marry our Father please our Father luv u too,! Da sauri ta dago tana kallon shi shima da sauri ya duka a gabanta, “NUSAIBAT please did u marry me ya mika mata wani hadadden ring na Diamond, da sauri Zahra ma ta kariso ta duka kusa da yayan nata, “please Bloody did u marry my Brother, Yaya Amar ne ma ya iso gurin ya duka a gabanta, “please Baby I beg  u to marry my Sweet brother, gaba daya suka Hada baki gurin cemata pleaseeeeee!!!! Da sauri ta juya baya, tace musu sai nayi shawara, wani farin ciki ne ya lullubeta please suka Kara cemata juyowa tayi ta gansu gaba daya har yanxu suna tsugunne, bata san lokacin da tace na Amince ba, ai da sauri Zahra ta rungumeta shiko yaya Mubarak rungume Amar yayi, “ta Amince dan uwa Besty ngd sosai, ture Zahra tayi ta fita da gudu, tana fitowa sukaci karo da Billy data make bakin kofa tana kallon su da sauri ta juya tayi sashin su, tana kuka, Umma ta cuceta, gashi tana kallon yaranta Amma Sunki kulata, sai dai ta kalle su a nesa, Ummimi tana shiga daki sai ganin su Momy tayi, Ai da gudu ta nufii Momy zata rungumeta, sai taga tana kuka, ga Mamanta a gefen ta, ta jin gina kanta a kafadar Momy, Momy ne ta bude ma Ummimi hannu zo Baby na dama ni Naji a jikina ke jinina ne, don wannan kamar tayi yawa, da gudu Ummimi ta karasa ta rungume Momy, kowa a fallon yayi shiru, suna kallon ikon Allah, Su Amar ne suma suka shigo, nima nace bari in shiga in juyo muku meke faruwa, Yaya Jafar yayi sauri ya tare kofan, “to uwar jin kwakwaf bazaki shiga, to readers yaya Jafar ya jamuku nayi zuciya na fasa shiga.
*************************
Kudai ku cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU don jin yanda zata kaya✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
. vote
More Comment more typing ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
,😂😂😂😂😂😂😂 sister Adama, Maman Ahmad sister Nafisat, sister saratu, my sweet Takwaralle, da sauran Wanda ban Anbata ba kuyi hkr More Comment more typing 😂😂😂😂🏃🏃🏃
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
( NUSAIBAT &ZAHRA)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
🌹🌹EPISODE FIFTY FOUR&FIVE🌹🌹
Wannan page din na sadaukar dashi wa kannina dasuka rasu Allah ya ji kansu ya kai Rahma kabarin su Ameen👏
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Sun isa gidan Hajiya Kilishi da yake saukan dare sukayi suna zuwa, bayan driver sun sauke su, su Momy duk suka shige cikin gida Zahra ta dauki Hand bag dinta zata wuce, Ummimi ta jawota, “Haba Sittynerh ki jirani mana duk saurin ganin kawan naki ne haka, bige mata hannu tayi,  “kefa Bloody kin Faye neman tsokana wata zubin, juyawa tayi ta shige gida da sauri sbda kar hawayen da take boyewa ya zubo mata, tana zuwa bakin Kofan falon ta jin gina tana kuka, Allah ka yayemun son Yaya Amar, ya zanyi, tun tuni ya kasa fahimtar soyayyata a gareshi gashi yar uwata kuma Aminiyata wanda nafi so a duniya ita yake so, niko nace too Zahra kina ko son maso wani, don Yaya Amar yayi nisa baijin kira,
“Wai sai yaushe Babyn Momy zaki fahinci irin son da nake miki ne,?  “Yaya Amar Kaima sai yaushe zaka Fahinci irin son da Sittynerh ta ke makane, Yaya Amar kai ne Mutum na farko dana fara so a duniya, Sai daga baya na fahinci Sittynerh ta fini sonka tun bata san meye so ba take sonka, shiyasa na sadaukar da Soyayyata a gareta in dai da gske kana sona, to kaso Sittynerh na rokeka please 🙏😭kukane yaci karfin ta ta juya da sauri tayi cikin gida, kawai ji tayi tai karo da mutum tana daga kai sai taga Zahra ne, kawai rungumeta tayi suka ci gaba da kukan su, da kyar suka lallashi kansu, sukayi shiru suka karasa cikin gida,
Kowa ya hallara a falon Kilishi an zauna ana ta cin abinci, Anwar ne ya taso yazo kusa da Ummimi Aunty ni ke zaki ban Abincin “to Daddy na ai yanda kace haka za, ayi, dariya gaba daya akayi ban Kilishi da take harde a kujera, bayan An kammala cin abinci ne aka zauna zaman hira da irin nasarorin da suka samu, Hajia Kilishi ne tace, “gobe in Allah ya kaimu ina bukatan ganinku dukan ku kuda ya’ya’ ku karfe Tara na safe, Harshi wancan Hadaddan wanda matarshi ta shanye,  a kirashi a waya kuce ni Kilishi ina nemanshi, “to Hajia Insha Allah za, a fadamai, kowa yaje ya kwanta,
“Eh na dawo sai akayi yaya kuma, ina yarana iyeh, dayake yar duniya ce sai cewa tayi “Haba Baby ka Bari kadan huta mana kayi wanka kuma, “ke dakata ban son surutu, dai dai lokacin wayan shi tayi Kara Alaman Ana kira yana dubawa yaga Daddy ne, ya dauka “Hello Daddy  ina ji kun dawo ne, to Harda Bilkisu to insha Allah  muna nan zuwa, to Allah ya bamu Alheri ngd, waigowa yayi yana kallon ta inkin ga dama gobe ki shirya da wuri Hajia Kilishi na neman mu, “what wlh bazan je ba don kiran wannan tsohuwan ba alheri bane, kawai a dunga takura ma mutum a barshi yaji da Abunda ke damun sa mana, “ke ni kike fadama haka!!?  “Eh an fada ma din me zakayi, bata gama rufe vaki ba ya bata lafiyayyun Mari guda biyu, an fada miki ni sa, anki ne iyeeh shegiya Mare tarbiya, kuma zuwa ya zama miki dole, juyawa yayi fuuu ya  shige Bedroom din su yana zuwa ya dauke wayoyinta gaba daya guda biyu ya cire layin ya wurga shi cikin toilet yayi ploshing din shi, inga uban da zaki kira, ni ban san ma mena gani jikin shegiyan yarinyar nan ba,  in ban da kaddara me zanyi da ita ma, niko nace kai dai Mubarak fadi gskya, Anci moriyan ganga wato za,a yada koranta koh, “wlh sai dai ka kasheni kuwa don bazan je gidan mqsifaffiyan tsohuwan nan ba da ba kaunata takeyi ba, yara dai ta kwashe dama ni ba damuwana ba an ragemun aiki ne, juyawa tayi ta shiga Bedroom din ta don daukan wayanta, waya yace daukeni mu gani, “tab wlh yau sai ka ban wayata kuwa, da gudu ta fito ta karisa bakin kofar shi ta fara bugawa ni ka ban wayoyina Mallam tunda ba kai ka siyamun ba, banza da ita yayi ta gama haukanta taje ta kwanta, haka ta dunga hargitsa dakinta tana sunbatu, ta shiga uku Indai Ummimi ne ta gani a TV ai ko sun shiga uku ita da Ummanta don Boka yace duk randa ta dawo suka Hadu da Mubarak Asirin zai karye kuma sai ya sake ta, Indai ya saketa ai ta shiga uku, kuma Boka yace Indai Asiri ya karye Umma Hauka zatayi kuma ta bar gida bazasu Kara ganinta ba, a haka har barci yayi gaba da ita, bata sani ba, sai ince kawata Asuba ta gari.
************************
Kwana sallah Mama tayi tana gode ma Allah mai yadda yaso itama tanaji a jikin ta ta kusa ganin dangin ta ta sanadin yarta.
************************
Washe gari  kowa ya hallara a falon Kilishi ita kawai ake jira, sai su Mubarak da Basu iso ba, Sallama sukaji na Mubarak da Matarshi, Zahra ne ta kura ma Yayan nata ido ganin inda ta lalace Abun tausayi ita ko matar gaba daya tayi wata katuwa, shegiya kawai, koda ya shigo Ummimi bata dago kai ta kallesu ba, kawai dai taji gaban ta yanata faduwa,  yayin da Yaya Amar shima ya kurama Abokin nashi Ido rabon da ya ganshi tun Haihuwar Anwar, gaba daya Falon Sai da suka tausaya mai halin da ya shiga, bayan ya gaida Iyayen nashi ne ya nemi guri gefe daya shida matar shi suka zauna, sai kallan yaranshi yakeyi da suka zauna, a jikin wata balarabiyan yarinya wanda tun da ya shigo yake kalonta Amma ita taki dago kai yaga ko Wacece kodai wanda suke tare da Zahra ne, shifa dama bai taba ganin yarinyar ba, tunanin shi ya yanke ne lokacin da su Kilishi ta shigo Falon tare da Mai gidanta, bayan sun zauna Aka umarce a bude taro da Addu’a, bayan Daddy ya gama Addu’an ne Kilishi ta fara magana kamar haka, “to Alhmdulillah kunje karatu kun dawo lpy, yau zan cika burina dana dade ina fatan cikawa, Ni Hajia Kilishi kun san Inna yanke hukunci ba wanda ya isa yamun musu, sbda  kai AMAR na yanke hukunci zan hadaka Aure da yar uwar ka Zahra da sauri duka suka dago suna kallonta, ke kuma Nusaibatu zan hadaki Aure da Mubarak wannan shine burina tun Marigayiya, to Sai Allah ya dauketa ya kuma bamu madadinta, na gama magana ranka ya dade ko kana da Magana ne, “Ai kin riga kin gama magana, Abunda zance kawai shine nanda sati daya biki, ku tashi kuje Allah ya muku Albrka, “tab wlh ba, a isa ba, da sauri Ummimi ta mike tana kallonta Bakin ta na rawa ta fara ja da baya “dama kece Matar Yaya Mubarak din Billy dama kece, “Na shiga uku Abun da na gani a TV ya tabbata wlh baki isa ki auran min miji ba, saboda maita duk nesanta kin da Umma tayi damu kina nace kukan kura tayi taje zata shaki wuyan Ummimi Zahra ta tare ta kina tabata ina miki dukan mutuwa a falon nan, kunki Allah yaso to Sai mene, mugaye Azzalumai, wayyo Allah Mubarak kar ka mutu ka barni da dangin ka da basa kaunata, Ashe tun farkon da yaga Ummimi ya sume,  gaba daya suka yo kanshi, garin gudu kawai suka bige mun wayata ta fadi, kunga va dama in karishe dauko muku rahoto😜😜😜 in ga comment anjima Sai in koma in kariso muku jin ya zata kaya.
*****************
Kudai cigaba da bin YAR mutan ZAZZAU 😜😜✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Please ✍️✍️✍️✍️

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements