GIDAN GANDU Page 1 to 10 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / GIDAN GANDU Page 1 to 10

GIDAN GANDU Page 1 to 10

GIDAN GANDU Page 1 to 10

Page 1
GIDAN GANDU by Biebee Isa
Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu, yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti? Bilqeesu tace Aifah, inda sabo ai ya ci ace mun saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu Tsoho mu gaya mishi, Islahulkhair da ke gefen su ba ta tanka musu ba, cikin damuwa Fadila tace Mallam Audi donAllah ka qara mata horn, kafin Mallam Audi ya qara Horn suka hangota tana sauri cikin yanayinta na sayih ta fada cikin mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja mota ya bar haraban wakeken gidan da ke qunshe sashe sashe..
Kusa da Islahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce riqe da keypoint tana karatu, Ta ce hey Sisters, sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta, cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da zamu daina jiran Maysah, kin cika nawa, tace wlh banga safata bane ta kalli Islah tace yadai sisi? Murmushi ta mata tace lafya u will never change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe tace duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki tare da hararta, ba ta damu ba don idan da sabo ta saba. Mazan da ke zaune su hudu a chan baya tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na’imah da bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din, sa’idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau suke fara NECO exams…
Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu rubuta Jarabbawar qarshe ta makarantar Sakwandire na TopOnwards Science College Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana…
***************
Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon da ke zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne, kadan ya rage ya cika shekaru chasa’in cif a duniya, tsufansa me kyau ne, gyara zaman gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune, amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace ja’ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi, duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun kasa magana, ku fada matsalarku a magance maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu tace daman Tsoho qara muka kawo ma, Haneefa tayi charaf tace tsoho mu dai mun gaji, wao kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun fara jarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba wata rana sai an hana mu zana harabawa saboda latti, Mu gaskia da sakel, a san yadda zaayi damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri, kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma maganar raba tafiya duk bata taso ba, tun lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu makaranta kunga lokaci guda ba za a bar wannan qaidar ba, Hmm ai daman munsan baka san laifinta ka fi sonta cikin jikoki, da sauri yace haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku, ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni kunji? Sukayi godia suka mai Sallama.
*******
Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA’U Meyasa kike sa ‘yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da fuska tace, kayi haquri InshaAllah zan daina, yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da bansamu latti ba, yacr donAllah ki daina kinji? Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta miqe ta fita, a ranta tace InshaAllah sai na riga kowa shirin makaranta jibi, ba za a qara jirana ba sai dai na jira…Tayi Sassan Matan tsoho domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa) a dakin, suna ganinta sun ka bata fuska, ta gaida su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho na kiranki, ba ta jira ta ce komai ba, ta fice don bata son jin zagin da za a jefi kakar ta dashi ba. Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai. Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho.
*******
Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne, me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna Rabi’u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan Shuwa Arab, Shekara 2 kachal ya ba qanenshi. İyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin Maiduguri inda suke sana’ar sirfani da dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu İlimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka zama matasan Attajirai.
A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata yarinya Karime da ke kawo musu tallan fura fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin qanenshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya wannan yarinyan ta man, bansan ko babanta ze ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta daman gwara kayi auten kaima, ko da baban ya dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa, Mallam yayi shiru yace baqi taku ba, amma Hajjo bata da kowa sai Allaj sai ni, Hajjo tasha wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati 2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan su…
*******
Da daddare Mallam ke gayama maman karime yadda sukayi da meson Karime, murna fal ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take Annurin fuskarta ya dauje dif, tace bangane ba, yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na bashi ita, maman karime ta daka tsalle ta re da riqe qugu tace Kam babban balaeen chan….
Page 2
GIDAN GANDU by Biebee Isa
Sai kuma ta fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asiri ba, dan ka ga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi aure wazai na kai mun talla? Ko ni kakeso na fita tallan da kaina? Takaici ya hana mallam magana sai kawai ya fice ya bar dakin…
*****
Tadihn su sukeyi irin ta masoyan da, Hajjo ta shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan karime ta hada gabas da yamma, tace wato Rabiu ba xai janye ba koh? Me zaayi da wanda ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata rai yace haba karime me yasa kike haka neh? Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban, Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola ce, kuma da ta rasu, shine babana ya riqeta, ni kadai ral mahaifana suka haifa, Musbahu yace najih dai, be kamata kina nuna qyamarki gareta a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiko kyau, wani mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe zasu je Chadi don sanar da kawunninsu auren su, ta mai Allah ya kiyaye
******
Ko da Su Musbahu suka isa qasar Chadi suka tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi da su Mudassir da labaran Nigeria, yara ne ba su fi shekaru 10 ba su da kowa yanzu sai mu, yace Yaya duk yanda kace hakan zaayi…
Haka kuwa akayi Washegari suka kama hanyar Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo. Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru, Musbahu yace Karime ta riqe su, fir taqi ita bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo su, ta amshe su hannu bibiyu.
*****
Bayan Shekara daya.
A daddafe ta szuwa ta kai kanta bangaren Karime, kuka takeyi tana kiran Yaya ki taimakeni, bayana zai balle, Karime da ke zaune tana tamnar cingam ko kallo bata isheta ba, nan Hajjo ta xube tana murqususu, amma karime bata ce mata ci kanki ba, Tunda Hajjo ta samu ciki Karime ta ji wani tsanarta ya shigeta, jin haushinta daya ya zaayi hajjo ta samu ciki? Ita bata samu ba? Ta sha kai ma cikin hari tun yana qarami amma bata samu nasara ba, Kishinta takeyi Sai kace kishiyoyi, ta dinga juyi a qasa amma ko kallo bata samu ba daga karime, maqociyarsu ce Umm Afeef ta shigo gidan da Sallama, ganin hajjo a qasa yasa ta qarasa gunta tana sallami, me ya sameki haka? Ko naqudar ce? Sannu, ta kalli karime tace kedai bakiji dadin rayuwarki ba, wai shin mini daya kuke aure da zaki nuna mata wannan halin ko in kula? Karime tace Maman Afeef wlh ki fita idona zamu kwashi yan kallo dake. Cikin wahalaliyar muryan hajjo tace umm afeef marata, bayana, ta fita da gudu tana fadin ina zuwa Bata tsaya ko ina ba sai gidan Unguwan zoman garin Ummu Anisa, ta ce ki temaka haihuwa tazo ma hajjo, ai ko da gudu suka fito suka nufa gidan, har ynx hajjo na qasa ta na mutsu mutsu, maman Anisa tace kamata mukaita ciki, Karime tace Waaa? Ai wlh ba zaa shiha da najasa dakina ba, ummu Afeef ta buga tsaki tace in fitsari banza ne, kaza ma tayi, Ummu anisa tace rabu da marar tausayin nan kamata mu kaita bangarenta, nan suka bar karime na ta zazaga masifa. Suna ko shiga daki Hajjo tayi wani yunkuri ta santalo danta, Kai Masha.. Maman afeef ba ta rufe baki ba sai ga wani dan ya fito, cikin murna tace Yan biyu– sai ga wani dan ya kuma fitowa, Guda maman afeef ta sake da qarfih, ummu aneesa sai sannu take ma hajjo, kafin aka gyara hajjo. Da yaranta maza kyawawa kamar babansu. Ummu Afeef ta fita waje da sauri taga karime na labe tana leqe, ummu afeef tayi shewa tace samun Yan uku sai ‘yar baiwa, Karime ta dafe qirji tace na shiga uku, Yan uku? Maman afeef na fita ta samu almajiri kayi maza kaje kasuwa kace ma malam Rabiu hajjo ta haihu ta samu yan uku. Da gudu almajiri ya ruga.
Karime kuwa kamar tayi hauka, sai sambatu take tayi, Hajjo ta haihu? Ta samu yan uku? Kuma maza? Jar ubanchan, wlh bazata sabu ba. Da balaee nima sai na haihu cikin watan nan hka ta dinga haukanta…
Da gudu Rabiu da Musbahu suka shigo gidan, kallo daya zaka musu zaka san suna dauke da tsantsar farin ciki, Hajjo har tayi wanka tayi kyau abunta, Rabiu ya kwaso yayan ya rungume, ya miqa ma yayanshi, Musbahu ya amshesu tare da musu addua, Allah shi rayaku.. Nan ummu aneesa tace a bar hajjo ta samu bacci, Yan gidan kuwa Labaran da mudassiru sai murna suke tayi Nene Hajjo ta haihu.
Musbahu ya shiga cikin Gidanshi jiki na rawa yake ta qwalawa Karime kira yana Karime karime, Hajjo ta haihu har daki ya bita yana gaya mata, Yan uku ta samu, kuma duka maza, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, shi be ma lura da yanayinta ba, yace wai baki san hajjo ta haihu bane ba? Cikin tsawa da masifa tace Tou Sai Me? Ya dan kallota, karime lafiya? Ta miqe tace ita ta kawo hakan, ta sabi zaninta ta bar gidan, shiko Musbahu tunani yake me yayi zafi haka?
***Rannan suna Yara sukaci suna Hassan Hussaini da Gambo, Yaran nan abun so ne gurin Jamaa, har yau Karime bata leqo ta gansu ba, Rabiu wani kuka ta musamman yake ba matarshi, Hajjo na shan wahaln yan ukun nan, ba wanda ke tayata da rainonsu, sai Mudassiru da Labaran, ganin hakan ne Karime ta sami Rabiu da kuka wai ita dai a bata mudassir da labaran, ita tana cikin kadaici, waye waye, Rabiu be ce komi ba yace su koma gun karimen, Musbahu ya so tambayar ba a si kawai sai ya share. Karime ta cigaba da riqonsu don kawai kar Hajjo ta moresu, a hankali a hankali ta dinga chusa masu tsanar Hajjo.
*******
Abu na Allah cikin Shekaru yaran hajjo 6 har da yanuku kasancewar duk shekara take haihuwa wani abun Allah yaranta duka maxa, Bayan Yan uku ta samu Ahmad da Ibrahim, sai auta Hafiz har yau Karime ko batan wata ba ta taba yi ba, an bi Malaman anbi yan tsibbu da bokaye amma a banza. Musbahu na san Yaran Yanuwansa sosai, ya sa yan uku da Amad makaranta Islamiya..
***
A bakin kogi me kallon boader ya hango er yarinya na kuka gashin kanta ya rufe mata fuskarta da sauri ya qarasa yace ke me akayi maki? Dago kanta tayi Ya Salam!! Aljana ce ko mutun? Cikin hausarta da be fita tace wlh mutun ce ni, ya sunanki? Sunana Aishalle daga ina kike? Masu kamen bayih ne suka kamo mu shine ni na gudo nayo nan, ke er wace qasa ce? Tace kamaru, yace ina iyayenki? Ta matse qwallah tace sun rasu da dadewa, yace ta shi na siya miki abinci, na saki kwalekwalen da zai kaiki har kamaru, da sauri ta girgiza mai kai,Tace wlh ba zanje ba, banda kowa a chan, bauta mukeyi a gidan sarki, kuma na gudu da na koma zaa fille mun kai. Ka barni a nan kawai, Musbahu ya tausaya mata qwarai, yace zakije gidana? Da sauri ta daga mai kai, yace toh biyo ni, ba gaddama ta bishi, sunyi tafiya kadan kafin suka isa gida, tun daga soro yake qwala ma karime kira, ta fito, kai mallam ya kake kwala man kira kamar wani watan ramadana– turus ta tsaya ganin Alajana da gudu tayi daki ta na fadin bayanka Musbahu bayanka Aljana, yayi daria yace keee mutum ce, ta dan leqo tace daga ina? Ya kwashe komai ya gaya mata, shine nace ta zo ta xauna a gidan nan, Ashar ta saki, Wannan Alajanar zata zauna dani? Wannan Mayyar? A gidan nan? Wlh ba dai gidan nan ba, Musbahu ya fusata yace Gidan ki ne ko nawa? Toh sai ki hanata xama gidan nan idan kin isa.. Zuciya ta ci karime ta daka tsalle ta damqo gashin Aishalle
Page 3
GIDAN GANDU Biebee Isa
Aishalle ta sake ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya hadata da bango, ya ja hannun Aishalle yayi waje da ita, karime na kwance kasa amma bakinta be daina furta zagih da batanci ga Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi sauri fa lullube jikinta da zanih, yace hajjo ga yarinya nan danAllah aba ta abinci kuma tayi wanka a bata kaya, Hjjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga qanwata na zata kula da ke kinji? Aishalle ta gyada fuska,usbahu ya sakai ya fice,Hajjo tace zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincin nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka.
Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta, ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo ya ga ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gidan, don ba shiga sassan hajjo takeyi ba balle ta ganta. Kuma ta hana su mudassir shiga balle su kawo mata rahoton gulma.
Wasa wasa har Aishalle ta samu wata 2 a gidan Rabiu, tayi clean ta qara wani irin kyau me firgitarwa. Kuma tana son yaran Hajjo har ranta, da taimakon Hajjo Aishalle ta iya abinci da wasu gyaran da ya kamata ace mace ta iya. Haka suke zaman su cikin aminci da yarda da juna..
******
Yaya kana ganin karime baza ta bamu matsala ba? Musbahu yace Rabiu ni ba raggon maza bane, na isa da gidana, Kuma bawai zan auri Aisha bane don na ci mutuncin karime sbd bata haihuwa ko wani abu, aa zan auri Aishalle ne don ina matuqar sonta kuma dan raya sunnan manzo. Rabiu yace toh shkn Allah shi sa a dace..
Hajjo ce ta ma Aishalle bayani, tace Mamman Hassan ba wai zan muku musu bane, amma wallahi ina tsoron matarshi, hajjo itama cikin damuwa tace kar ki damu kowa da halinsa zai zauna. Allah dai ya sa mu dace..
Yau ana sallahn jumaa aka daura auren Musbahu Zailani da Aishalle, bisa sadakin silallan zinari 5, Hajjo ta gyara Aishalle, da daddare Musbahu ya shigo Sashen qaninshi yace ma Hajjo ta shigo da Aishalle sashen karime zai hada su, sai da gaban hajjo ya fadi kafin tace toh Yaya ga mu nan zuwa. Wuce wa yayi sashen karime, tana xaune ta na shan rake ko Isha’i ba tayi ba. Mallam sannu da zuwa, tace yauwa karime rake ake sha, e wlh zaqin tsiya kana sha? Yace aa, yo daga ina kake haka sai uban qamshi kake zubawa, rabon da na ganka tun safe? Kafin yace komai su hajjo suka shigo da sallama ya amsa, karime tace wai meye? Da daddaren ma ba za a barka ka zanta da mijinka ba? Hajjo dai bata ce komi ba, Aishalle kuwa gabanta ya tsanta bugu, hajjo wace ce wnnan sai noqe noqe take kamar manahuka? Musbahu yace Karime, tace naam mallam, zaki tuna fuskar nan? Hajjo bude mata fuska, Hajjo ta bude mata fuska, karime tayi zumbur ta miqe, oh Allah Musbahu wai kai ina kake samo aljanai masu tsigar mayu! Haka kwanaki ka kawo wata mayyar, ai gwara wanchan akan wannan! Wannan ai kynta ya shahara, danAllah kiyi haquri baiwarAllah, ai kuma Allah ya hallice ku Duk da bansan me mijin nawa ya miki ba amma kiyi haquri, ta ba musbahu daria sai da ya dan dara, yace Karime wannan ce na kawo miki ita kwanaki sunanta Aishalle, kuma a yau ta zama matana saboda na aureta, Karime ta daka tsalle ta chakumo wuyanshi,/Ni zaka munafurta ni zaka ci ma amana? Idan ka isa Allah ya tsinen, babban balaeen chan, sai ta sakeshi ta wawuro sandan rake ta maula wa hajjo a baya, hajjo ta gantsare baya, ta yo kan Aishalle, yau sai na daddaki kashin babba buraubaki, Cikin zafin nama musbahu ya damqota ya jefar ya nuna ta da yatsa, karime ki kiyayeni karime ki fita idona, ta yo kanshi ta chakume shi, na rantse yau sai ka sakeni idan baka sake niba ba ka haifu ba, wlh sai ka saken, yace karime na sake ki saki daya, ihu ta sake da qarfih tace na shiga uku, daman basona kqke ba? Shege tsinanne laananne, ta figi zanenta ta bar gidan da gudu ko tsoron dare bata yi.
Ya kalli Hajjo tace Hajars kiyi haquri ni na jamaki ko? Tace bakomai Yaya, yace nagode ki jeki wanke fuskanki kar ki sa su hassan damuwa tace to yaya nagode sai da safe, Aishalle Allah ya tashe mu lafiya.
Like · 1 · Reply · Report · Aug 3
Phatee Lamin
****
Bayan Wata Biyar
Zama suke cikin so da qaunar juna, abu na Allah Aisha na dauke da cikin Wata 4, Hajjo na kula da ita sosai, su Hassan na sonta Goggo Amarya suke ce mata, Hafiz na ce mata Goggo Ama sbd shi yana da tsamin baki, haka kuwa kowa ke ce mata Goggo Ama, su Mudassir kullum suna gidansu karime suna kai mata rahoton abun da ke wakana cikin gidan, ta dau alwashin raba Aishalle da gidan nan amma bokanta ya shaida mata Aishalle ba zata taba barin gidan nan ba, kuma ya hango yaranta da jikokinta cikin wannan gidan, kuma duk wanda Musbahu zai aura a bayan Aishalle yake don sonta a cikin jininshi yake, Hankalin ta ya tashi ainun, babban baqin cikinta be wuce yanda Musbahu yayi watsi da ita, a tunanin ta zaizo yace a maida aurensu amma shiru, gashi uwarta ta rasu, abinci ma gagaranta yakeyi, haka ta samu babanta tana kuka tace sai dai yaje ya ba Musbahu haquri a maidota, yace shifa ba inda zaije, ba zata maidashi tsohon banza ba Nan ta fashe da kuka tana tirje tirje, don yaga uwarta ta rasu shisa be damu da ita ba, ya fi son hajjo, duk da Hajjon ba diyarsa bace, tsakanin da da mahaifi sai Allah, zuciyarsa ta karaya, yace zai ma Musbahu magana. Da kanshi yaje kasuwa gurin Musbahu, Musbahu yace haba baba ai da ka aika an kirani yace bkmi, nan ya gaya mai abunda ke tafe dashi, ya danyi jimm baba yace idan baka so dole ta haqura bawai ina maka dole bane, yace lahh bakomi wlh ni ko ynx a shirye nake a maida auren mu.
Haka kuwa akayi ba a jima ba aka maida auren, bayan ya samu Aishalle ya mata bayani ta nuna mai bakomi, amma ta shige dakih ta ci kukanta hajjo na lallashi,. Daga bangare a ka fidda ma Karime dakih ciki da parlo, rananr da tare su Mudassir dadi kamar ya kashe su uwar dakinsu ta dawo, nan ta rada musu wanih abu kunne suka hau shewa…
******
A yau Aishalle ta suntulo danta kyakyawa me kama da babanshi da taimakon hajjo da na umm aneesa, ko kallo basu ishe karime ba, amma hauka ne kadai batayi ba, takaicinta ya akayi Ama ta riga ta haihuwa kuma namiji? Musbahu baki har wuya yau ya gudan jininshi, Rannan suna da yaci suna Aliyu. A rannan ne karime ta tashi da wani kitifi wai ita ba ta san qanshin ragon da ake soyawa, maqota basu bi kanta ba don sun san halinta sai da suka ga tana amai suka temaka mata, a ka kira ummu aneesa don ta dubata, gwajin farko ta gane karime na da juna biyu. Aifah tun lokacin karime aka fara salon iyayi da kankamba, ba ta san wannan ba ta san wanchan. Har Allah ya sauketa lafiya, amma tayi baqin cikin ganin mace ta haifa, Musbahu ya nuna farincikin shi ranar suna diya ta ci suna Abida. To daga nan Aishalle da karime suka fara gasan haihuwa, duk shekara sai sun haihu, sai da Karime tayi mata 2 Sadiya da Zainab kafin tayi namiji daya Usman, ita kuwa Aishalle bayan Aliyu ta haifi Umar da Abubuakar sai mace daya Maryam tun daga maryam Ba su sake haihuwa ba. Maryam din Ama na da shekara 7 Hajjo ta qara haifan Yan biyu mata, Hassana da Hussaina, Aishalle kam kamar ita aka ma haihuwan nan murna kamar mene, tace wlh Yaya Hajjo ke er baiwa ce, daga yan uku sai yan biyu dama ni, tace kema Allah xai baki….
*****
Hannun hajjo saqale da nashi, kuka take tayi jin abun da ke fita daga bakin mijinta, Hajjo na so na zame miki Gata har qarshen rayuwarki, amma da alamu kwanana yana gab da qarewa, tace wai rabiu me kake cewa haka? Cuta ba mutuwa ba fa? Hajjo kenan sati biyu kenan ina fama da ciwon cikin nan, nidai dan Allah kayi shiru, Hassan ne da qanenshi suka shigo dakin ganin mahaifansu na kuka yasa suma suka fara kuka, Da qyar rabiu yace hassan Allah muku Albarka, jeka kira mun babanka, da gudu ya fita sai gashi ya dawo da Musbahu da Aishalle a rude, Asha Rabiu ciwon ne haka? Sannu yace yaya ka yafe man idan na taba bata maka, Yaya ga Amanar iyalai na, na san zaka kula mun dasu, Kafin Musbahu yace wani abu rabiu ya cika yace ga garin ku nan, Tashin hankali.
4. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, shi ne abunda Musbahu ke maimaitawa, Hajjo kuwa don rudu kasa kuka tayi, Musbahu yayi qrfin halin fita kiran maqota don a suturceshi cikin awa da be wuce daya aka kai Rabiu gidanshi na gaskia, kafin aka zo zaman makoki, Karime ta dan rude da farko amma daga baya sai ta gyagije wai Allah ke kama maqiyanta ta hanyar kashesu.
******
Bayan Arbain; Musbahu ya rungumi iyalan marigayi qaninshi, dukkansu ba wanda be zuwa makaranta banda Hassana da Hussaina.
********
Bayan wata 5
Aishalle kince kina son muyi wata magana? Tace eh Mallam, daman wani abu na hango, yace me ke nan? Tace Me zai hana tunda Yaya Hajjo tagama Takaba me zai hana ka aureta? Ina ganin ta hakan ne zaka fi kula da ita kuma ka riqe amanar da qaninka ya bar ma, ya tsura mata ido, dama chan yayi wannan tunanin amma yana tsoron abun da zaije ya dawo shisa ve gaya ma kowa ba, kaii amma Allah yayi ma Aishalle albarka Akwai da kaifin tunani, yace Aishalle kin tabbata wannan shawarar taki har ranki? Don ni bana so nayi abunda zai bata ranki, tayi murmushi Maigidana kenan, kamanta hallacin Hajjo a gareni? Ko kirkinta da kular da ta bani ka mance wlh wannan abu har raina, don a qasar nan banda kamarku. Yace toh shkn, na amince, tace ka taso muje mu kai qoqon barar mu, yayi daria yace Aishalle baki da dama.
Karime dake labe bakin kofa ta na jinsu idonta ya rufe tsabagen tashin hankali, kishi da Hajjo? Aiko zaayi yaqin basasa na biyu a gidan nan, keji wannan hegiyar mayyar, dan taga na barta ta zauna shine har da gayyato hajjo, ganin sun kusa fitowa ne yasa ta shige dakinta da gudu.
******
Hajjo jin maganar tayi bambamraqwai, ya zaayi ta auri yayan mijinta? Kuma Mijin Yaya karime? Aishalle tayi sauri tace donAllah yaya hajjo kar ki baza mun qasa a ido, kinsan duk wnda zaki aura a bayan mijina yake, kuma so kike kiyi aure wani gurin ya rabaki da yaranki? Auren mijina ne mafita gareki, hajjo ta harareta, hussain da ya shigo yace Umma danAllah ki auri babanmu, shiru tayi sai chan tace Allah ya hada kawunnan mu. Suka amsa da Amin. Ji sukayi ance idan ka isa Allah ya tsinen, ni zaka ci wa mutumci? Hajjon zaka aura? Qanwata? Yayi murmushin takaici, yace ynzun kika san cewa qanwarki ce? Ai aure be haramta tsakaninmu ba, kuma kamar anyi angama, ta chakumo wuyanshi, tace kuran sai ka saken, ya ce so kike na sakeki? Wani dan guntun tunani tayi tace da sauri aa kar ka saken danAllah, amma yasin da sake ba zata sabu ba. Daria yayi ya ja hannu Aishalle sukayi qofa ta juyo ta fara zagin Hajjo, Musbahu ya leqo yace qara ce mata uffan a bakin Aurenki wlh kuna kika tafi kin tafi kenan. Dif kakeji kamar an dauke wuta, sai murgude murgude da harare hararen da takeyi, ba halin magana. Oh su karime ashe ana san auren… Ana idar da Sallahn jummaa aka daure Auren Hajjo da Musbahu…..
******
Bayan Shekara 15.
A halin yanzu
Hajia Babba(karime) Haihuwan ta 10 Shida sun rasu saura Abida, Sadiya, Zainab, sai Usman haushinta daya yaranta maza duk sun rasu daya kawai ya rage mata. Hajiya Ama(Aishalle) yaranta Aliyu, Umar Abubakar, Maryam, Rabi’u sai Auta Nuratu. Tun Da aka yi Auren Hajjo da Musbahu ko batan wata bata taba yi ba, Yaranta da Rabiu basu da bambanci da yaran Musbahu a cikin Gidan.
******
Dalilin da ya sa na tara ku anan shine; Na yanke hukuncin hada aurenku duka, kasancewar ku Maza duk kun gama makaranta ga Sanaar ku kunayi, ya kalle Mudassiru da Labaran yace matsayin qannai na kuke, amma aure be haramta tsakanin ku da ‘yayana ba, saboda haka kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai Labaran Sadiya ce matarka, karime sai faraa take tayi, don tasan sai yanda tayi dasu mudassir din Musbahu Zailani ya cigaba da cewa, Hassan Maryam ce taka Hussaini kuma Nuratu, Gambo kuma na baka Zainab. Aliyu kuma zaka auri Hassana, Umar kuma Hussaina, Abubakar kuma akwai diyar Alhaji Mai dala’ilu Hafsat, yace ya baka ita charaf Karime tace Wa?? Ai kuran baku isa ba, Hafsatun da ke son Usman? Kuma mun gama magana da mahaifiyar yarinya tace ta ba usman Hafsatu, Wlh ba wani Habuvakar, karime sanin dukian Alhj me dalailu ne yasa ta ke son hada danta da diyarshi, Shi dama Abubakar ya fita daban cikin gidan, yace Baba a bar ma Usman din, duk daya ne, don be son Auren yanzu musamman na zumunci, ya cigaba da cewa ni dama ina son na qaro ilimi, , yace toh shkn da kai da Usman din duk daya ne, Allah ya ba da xaman lahya. Suka amsa da Amin gabaki daya, Karime tace yauwa Alhaji maganan Zainab da Gambo, ya xaayi ka hadata da gambo? Bayan kasan hajjo bata qawnar jinina? Wani kallo da ya watsa mata ya sata nustuwa lokaci guda..
*****
Sunyi qoqarin fahimtar junansu, kowa yayi naam da hadin da aka mai, Zainab kuwa tana son Gambo qwarai da gaske amma Karime tana laantar wannan hadin, Gambo ma yana danne zuciyar sa, don duk dakin Hajia babba ita kadai ce ta fita daban, Hajia Hajjo(mama hajja)da Goggo Ama suka lallasheshi kan yayi haquri yama babansu biyayya, Haka dai yayi haquri ya chusa ma kanshi son Zainab don ya lura tana sonshi.
A haka akayi aurensu, nan cikin gidan aka fidda ma kowa gidansa ciki da parlo, aka aje amare anan. Abubakar har ya tafi qasar Rasha(Russia) don karatu.
A qasar Russia ya hadu da Yarinya me suna Raijana, course mate dinshi ce, yau da gobe suka shaqu, har suka qullah soyayyah tsakankinsu, har Abakar ya yanke hukuncin aurenta, Raijana ta gabatar da Abbakar ga mahaifinta, dayake mamanta ta dade da rasuwa, fir babanta yaqi wai bazai aura ma dan Africa diya ba, ta dage ta nace tace wlh sai ta aureshi, yace shiko idan ta nace sai ta aureshi, to ba ruwanshi da ita, ya yafeta, da yake sun yan chan sun dauki soyayyah da mahimmanci ta tsallake mahaifinta ta ja hannun Abbakar, Haka sukaje wani massalaci aka daura aurensu.Haka suka gama karatunsu, sukayi shirin dawowa NIGERIA, yace su zo suyi ma babanta sallama, suka nufa gidanshi amma yana ganin su ya musu korar kare, yace beson qara ganin Raijana, haka suka wuto Nigeria guiwa a sage.
*******
Zaune suke a parlorn M.Zailani gabaki daya ana cin Abincin Gandu, yayi sallama hannunshi riqe dana Raijana, duka suka zubo musu idanu, Umma Hajja ta fara ganeshi da sauri ta miqe tana tafa hannu ga Abbakar ga Abbakar, gunta ya nufa don tun kafin ya girma ita yafi sani don tana sonshi kamar ita ta haifeshi, ya rungumeta ta shafa sumar kanshi, ya nufa M.Zailani ya zube ya na kwasar gaisuwa, kafin ya nufi Hajia Ama yana gaidata farinciki ya mamayeta amma kawaici ya hana ta nuna, ta amsa, sannnn ya Gaida Hajia Babba ta amsa cikin yatsina. Ya gaida yanuwanshi, Idon M.Zailani kan Raijana da take tsaye bakin qofa, yace Abbakar wacece wanchan, yayi murmushi ya kamo hannunta ya kawo ta gab da baban nashi, cikin turancinta tace Good Afternoon Papa, cikin turancin yan da yace hawwayu? Tace fine papa, Yace Abubakar wacece wannan? Abbakar ya murmusa yace Matata ce, Duka dakin suka hada bikin wurin cewa MATARKA?
5. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Hjia babba ta fara tafe hannayenta biyu tana salati, Abbakar kafira ka auro ka kawo ta cikin gidan nan?wani mugun harara ya jefeta dashi, Hajia Ama tace yanzu daman baka da wayau, Abbakar ya dafe kanshi, Umma hajja tayi saurin miqewa ta ja hannun Raijana tayi waje da ita, sassan ta ta kaita ta shigar da ita dakih, ta debo mata abinci ta mata alamun ta ci sbd ba ta iya turanci ba, Raijana tayi murmushi tace thank u, Umma hajja ta komo cikin babban parlo, Abbakar xube gaban babanshi, yace Baba ka yafe mun, bana son aikata sabo ne yasa na aureta, kuma musulma ce, ta rabu da mahaufanta saboda ni, baba idan na rabu da ita ban mata hallaci ba, na kuma ci amana, shiru ya gifta na wasu yan lokkuta M. Zailani yace shikenan Allah ya maka Albarka, na yafe maka, amma daga yau ba wanda zai qara auren bare, kuma ni zan zaba ma kowannenku mataye da mazaje, yace nagode baba, Abbakar ya matsa gun mahaifiyansa Hajia Ama, yace Ama danAllah ki yafe mun, tace bakomi Abbakar Allah ya bada saman lfy. Yace Umma hajja ina raijana? Tace tana chan daka, ya nufe dakin tana ganinshi ta fashe da kuka, Abbakar ur family is against our marriage ryt? Ya rungumeta yace dont cry, dy are not like dat, i explained evrything to dem, and dy understood me, u have nothin to worry abt.
*****
30 years later..
Baba Mudassir da Aunty Abida(first daughtern karime) na da yara 7, Tahir, Fatima, Noorayne, Zayd, Farida, Haneefa sai auta Ahmad, Baba Labaran da Aunty Sadiya na da yara 5, Yusuf, Khamis, Mu’ammar, Yusra , Bilkisu. Yaran Aunty zainab(diyar karime) da baba Gambo(dan Hajjo) 2, Samir, Samar. Baba Usman kuwa da Aunty hafsat diyarsu daya Ni’ima sai da suka shekara 15 da aure suka haifeta. Baba Hassan (dan Hajjo)da Aunty Maryam(diyar Aishalle) na da yara 4, Imran, Faisal, Munira, sai auta Nasir, Baba Hussaini da Aunty Nur yaransu 3,Irfaan, Zayyad da Raffiyah, Baba Aliyu(dan Aishalle) da Aunty Hassana (diyar hajjo) nada Yara 3, Aisha, Nabila sai fadila, Baba Umar da Aunty Hussaina na da yara 2 daga Suraj sai Islahulkhair. Uncle Abbakar da Aunty Raijana(er mutanen Russia) diyarsu daya tilo Rumaysa’u….*********
Yawancin jikokin M.Zailani sunyi aure, shike hada auren jikokinsa, Be hada auren jikan dakin Hajjo da jikan karime ko jikan karime da na Aishalle, hada yan daki yakeyi (misali dan baba hassan da diyar baba Hussaini) ko kuma diyar (Baba labaran da dan baba mudassir) shi a ganinshi hada auren jikokin Karime da jikokin hajjo ko na Aishalle matsala zai haifar don yana sane da gaban dake qulle tun kafin a haifi yaransu, amma ya kan hada jikokin Aishalle da Jikokin hajjo aure don su yasan Akwai yarda da amincin junansu. A qaidar gidan M.Zailani namiji daya gama karatun degree dinshi zaa mai aure, sai ya dauki matarshi ya tafi da ita duk inda zai kaita, mace kuwa da ta gama sakandire ake mata aure ta qarasa gidan mijinta. Jikokin gidan kama sukeyi don da wuya ka tsame wannan kace yana da kyau wannan be dashi, duk kakansu su ka dauko wurin kyau da haske, Sai dai kowa da halinsa, suna gaban da suka ga kakkaninsu sunayi, yan dakin Umma hajja da hajia Ama kadai ke zaman lafiya, Amma baka ra’ban yan dakin hajia babba, don da kun wuce sai ta zagi kakarku.
Maza 7 zasu kammala degree dinsu ko wa da fannin karatunshi, gabaki dayansu suna Oxford University, Mata 6 kuma ke jarabawar qarshe, kuma da sun gama za a hadasu Aure, matsalar gidan baka soyayyah don baka san da wa zaa hadaka ba, amma ba zaa rasa wanda kake burin a hadaku dashi ba.. Wannan kenan.
Kowa da halinsa, Islahulkhair ba ruwanta da kowa, maganaa be dameta ba, Yan dakin Hajia babba ke mata laqabi da er jiji da kai, Fadila kuwa ba ta da haquri ko kadan, idan ka mata laifi nan zata wanke ka tas, shisa Haneefa da bilkis ke shakkunta, Ni’ima kuma gata nan dai lafiyarta lao amma idan ta maka abu sai ka zata me ciwon hauka ce, abunta dai kamar sakarya, kuma Qalaw take, Rumaysah kuwa haqurinta yayi yawa, matsalarta daya Nawa, bata abu cikin hanzari, ko abinci su keci kowa sai ya tashi ya barta, yan dakin Hajia babba ba irin zagin da ba sa ma mahaifiyarta kasancewar mahaifiyar ta er wata qasace, kyanta dai ya fi tada musu hankali, suce mata mayya Aljanna, ko su zage kakarta Ama, tafi duka jikokn gidan kusanci da Tsoho(M.Zailani) saboda yanda take kuka dashi, tayi mis tausa, da fita, har yaqi cin abincin GANDU yace Na ta zaici..
A halin yanzu suna ta fama da Jarabawa ta NECO…
*******
Gida ya kachame, yau baqin turai zasuzo, shiri ake tayi ba babba ba yaro, shekara 5 kenan rabon su da gida, Har masu aure ‘yan nesa da kusa sunzo, misalin Qarfe 2 daidai suka shigo gidan, Waiyo Allah, Akwai maza Hurul Ayn dama? Ko wannensu najin kanshi, sai dai su basa yar tsama da junansu, ba ruwansu da beef din iyayensu ko kakaninsu, son junan su suke kasancewar sunyi shekara kusan 6 guri daya inda ba su da uwa ba uba… Sallama sukayi a parlorn Tsoho, Murna ya lullube iyaye da kakaninsu, zube wa sukayi gaban tsoho suna kwasar gaisuwa, kafin kowa ya nufi iyayensu, a ka gaigaisa.. Tsoho yace Sarkin Gida ka kaisu cikin Sashensu kowa ya zabi daki, yace ku biyoni suka ja Akwatinnansu suka nufa sashensu, ko wannensu ya dauki daki suka shige don huta gajia..Wurin 5 yanmatan Gidan suka shigo don yau evening paper sukayi, Babban parlo suka shige suka ga yayyinsu suna fira da tsoho, kowacce ta nufi yayanta ta rungume, Tsoho yace oh Allah, ko Sallama babu? Ku tashi kuje kuyi wanka kuci abinci kafin ku zo a gaisa ko? Suka ce toh, suka fice, har ta kusa bakin qofa yace Rumah, ta juyo tace naam tsoho, idan ba ki gaji zuwa anjima ki min wannan hadin shayi tace angama tsoho bari nayi laasar, yace yauwa er albarka. Zayyad ya bita da ido, wacece wannan tsoho? tsoho yace duk ba ku san juna ba, zumuncin ku ya tabarbare, kowa nashi kawai ya sani, dan wannan daki be san dan wannan dakin ba, Zayyad yace ayi haquri tsoho, ayi mana uzuri shekara 5 rabon mu da gida, mun san juna matsalar baza mu sheda juna ba, Tsoho yace Allah shi kyauta. A ranshi kuwa ya ce dole zan chanza wannan rashin zumunci, na san abun da zanyi, ko kun qi ko kunso sai kun zama TSINTSIYA MADAURINKI DAYA, Ya kalli Mu’ammar yace yaushe Zaidu din zai dawo? Muammar Ya tabe bakih chan yace nan da wata 3, tsoho yace wai saboda mene baku dawo tare ba? Inace duk tare kuka fara karatun? Samir yace kwantar da hankalinka nan ba da jimawa ba zai dawo cikin yanuwanshi. Tsoho yace akwai abunda ba kwa so na sani, Suraj yace kasan ko sun boye ma ni me fada ma ne, yace toh Allah sa dagaske ne, suka ce hakan ne ma. Yauwa da kunyi bautan qasa sai Aure ko? Muamaar yace Aifa maganar kenan Aure Aure mundawo GIDAN GANDU kenan, duk suka sa daria….
6. GIDAN GANDUby Biebie Isa
Yau basu da paper, suna gida, Fadila ta shigo Sashen Uncle Abbakar, Aunty Raijana na zaune na kallon wani Fim, Aunty Maisah fa? Cikin hausarta da har yau be fita tace ki dubata dakih, ta shiga, tsakih ta buga da qarfi, Oh Allah haka zaki qare dai, don fa kiyi sauri ki shirya ya sa na kiraku tun dazu, amma ji beki shafa ki keyi, Maysah tace sorry riga kawai zansa tace wlh ki same mu sassan Baba Hussaini, bari naga Islah ta shirya, ta iske Islah ta shirya suka dai ta ke jira, Islah tace lemmie guess maysah bata shirya ba, Fadila ta yi dan guntun tsaki tace ke da kika san komi, yaya Suraj ya shigo dakin yana Sisi bani earpiece dina, islah tace bro donAllah bari mu dawo zan baka, yace kinga dai ki– shiru yayi da idonsa ya kalli fadila, murmushi ta mai tace Yasuraj ina wuni, ya mayar mata da murmushin yace wacece wannan? Tace fadila ce, lalala haka kika qara girma, kai murmushi ta mai, Yace ina zaku ne? Islah tace walimar Quranin qawarmu, ya kalli fadila yace tohm muje na kaiku koh? Ta dago kai suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta, Islah tace wai sarkin Nawa muke jira, wacece sarkin nawa kuma? Maysah ta shigo dakin tace iyayen mita gani nan, Yasuraj ina wuni? Ya sakar mata murmushi ya ganeta don fuskar aunty Raijana gareta, yace Rumaysah wai duk kun zanqale banda su o’eh Islah ta turo bakih tace kai koh yaya? Ban ma yi missing dinka ba, yace liar, ku tashi muje, suka nufa parking lot motar da Tsoho ya ba kowannensu bayan dawowarsu, ya bude ya shiga Islah ta bude gaba zata shiga yace ke zaki shigo ki isheni da surutu koh? Ko ma baya jareh, Eeelerh dawo gaba kinji suka tsaya kallon kallo waye kuma eelerh anan? Ganin Fadila yake kallo yasa ta gane da ita yake, ba musu ta shiga gaba, Maysah da Islah suka shige baya, Ya kalleta eeelerh ina zamu ma? Jikin ta yayi sanyih ta gaya mai, bini bini yake jan ta da fira, Islah cikin rada tace maysah kin ga abunda na gani? Ita ma cikin murya qasa qasa, ngani, Yasuraj ya fole, suraj ya kallo su ta mirror yace gulmanmu, me kuke cewa? Sukayi daria, suka iso gidansu Fatima Bobboi wace ake ma sauka din, fita su Islah sukayi, fadila zata fita taji Yasuraj ya riqe mata hannu juyowa tayi cikin tsiwa taga yana kallonta ba shiri ta kai kanta qasa, a hankali yace I love you fadila, Kallonshi tayi da sauri yace Fadila will u marry me? Murya na rawa tace, Yasuraj kasan dai we are not allowed to fall in love koh? Kayi sauri ka cire wannan tunanin don baka san wacce tsoho zai baka ba, yace fadila, yanzu ba a auren dole, all m asking is for u to let me love u, nd i promise u, u wont regret it, ya qare matse hannunta, yace pleaseee, a hankali tace i love u yasuraj, ya sake ajiyar zuciya. Islah ce ta durquso ta window, hey are u coming on not? Suraj yace shes not byebye, Fadila tayi mata gwalo, Rumaysah tace ke ma dai ina ruwanki ki zo mu shiga ciki, in yaso sai muce ma bobboi tana love cikin mota. Sai da Suraj ya tabbatar ya gina sonsa a ziciyar fadila kafin yace ta shiga ta mata Allah sanya Alheri ta kira su Islah su zo su wuce.
******
Nikam Mu’ammar ka gaya ma hanifan? Ya dan tabe fuska yace kasan bana son raini, but zan aika Bilkis, Jawad yace kana bani mamaki wlh, kana son abu amma girman kai dinka ba zai barka ka furta ba, kuma idan gudu kake kar tsoho ya hadaka da wata, dama ka bar tunanin nan, dan a kanmu Culture dinnan na auren hadi zai tsaya, fine ba xa mu aura bare ba, but a bar mu mu xabi na cikin gidan da kanmu, amma idan kaga zaka tauye ma kanka haqqi ka auri wacce baka so den goodluck wit dat, Guy, ya ka dauki zafi ne haka, yace Allah bana son bacin rai, wai hadin Aure kawai sai a hadani da wacce banaso, yace wlh akwai matsala don ba yarda zanyi ba, yanzu ma Bilkis zanje nayi approaching, Muamar ya kaimai duka, kaii carefull dats my lil sis, Jawad yace na ga nima hanifan sista tace, hurt my sis nd i will hurt urs, sukayi daria daga nesa suka hango haneefa ta fito daga sassan su tana yauqi, Jawad ya miqe tare da cewa man up and tell her wat u feel, yaqwala mata kira Hanee, ta qariso tana wannan yauqi, Yajawad yadai? Yace Yayan ki ke kira, wane yayan? Ya nuna mata mu’ammar tace ok, ina Bilkisu ne? Tana sassan hajia babba, yace ok yayi gaba ita kuma ta nufa Yamu’ammar how far, yace hanee m in love, jin maganar tayi wani bambaraqwai, tace with who? With you ta zaro kyakyawan idonta tace what? Shima ya zaro mata nashi yace Yes i love haneefan Baba Mudassir tayi rau rau da fuska, Yamu’ammar namiji ne da ko wacce mace zata so, haneefa tace amma Yamua’ammar kasan tsoho–shh ya dakatar da ita, i dont care abt tsoho’s decision ol i know Is dat i lob u, unless ban miki bane ba, tace Aa fa ba haka bane, yace nasan me kike tsoro, but its high time su bar wannan Culture din, munji ba zamu aure bare ba, amma a bar mu mu xabi na gidan da kanmu. Bazan tava iya auren yarinyar da bana so ba gaskia, Tace toh shkn, Allah ya bamu saa, ya dan kallota is dat a yes? Ta kashe mai ido daya nan suka zauna suna firar soyayyah..
*****
Hajia Babba tace Ahh yau Jawad a sashe na? Tunda kuka dawo so daya ka shigo dakin nan da ba ni na haifi uwarka ba kuma na riqi ubanka ba da na ce kai ba jikana bane ban san ko Aishalle ta shiga tsakani da kai ba, yayi daria, kin cika mita wlh, wai ni meye matsalarki da Hajia Ama ne? Ko don ta aure miki miji?Tsohon ma ya tsufa amma kina kishinsa har yau, ko don ta fiki kyau ne? Da yarinta? ai fa ya zunguro ma kanshi, nan ta fara zagezage da tsinuwa, yo indai kyau irin na mayu ne wlh na yarda na fi duwawu muni, Allah ya tsareni da kyaun Mayyu da Aljannu, nan ya shige dakih yana daria zaune ya ga bilkis tana ninke kayan Hajia Babba, yace Sis ya dai? Ta fadada murmushin ta, duk cikin causins dinta Yajawad ya fi burgeta, ta na mugun sonsa Yajawad ina wuni, yace me kikeyi? Hajia ta sani ninkin kaya, Ya ce duk cikin yaran gidan nan Hajia ta rasa wanda zata sa aiki sai matata? Dadi kamar ya kashe bilkisu amma ta wayance tace matarka kuma? Wace matarka? Yace ke mana, ko ba zaki aureni ba? Tayi mai far da ido, tace Dan tsoho zai baka mata, Yajawad yace ke ni rabani da wannan hadin zumuncin, ni ke nagani nakeso inaso sai dai in kece ba kyasona, da sauri tace ina sonka fa Yajawad, yace lets stick togeda, ba me rabani dake kinji? Ta gyada Kai tana murmushi.
********
Sanye yake da 3quarter hannunshi riqe da basketball ball, leqawa dakin Jawad yayi ya ga bayanan, ya leqa dakin mu’amar beyanan, tsaki yayi ya ga suraj kwance yace guy muje muyi basketball, Suraj yace uhm uhm not in d mood, Zayyad muje muyi, zayyad yace No thanks tsaki yayi yace Kar Allah ya sa kuyi, haka ya isa field din da ke bayan Sashen Hajia Ama yana bouncing ball din. Da ya hango basketball court dn ya wurga ball din, daga chan nesa Islahulkhair ce ke skipping, ji tayi saukan Qwallo a kanta, qara ta sake na shagwaba ta dafe kanta tana kallon wanda ya jefeta da ball cikin tsiwa tace ba ka gani ne? Ya kalleta yace da kika ga ball me sa baki matsa ba, Miskilancin Islah ya tashi, ta ga idan har ta tsaya tanka mishi tana iya sake kuka ta duqa ta dauki rope dinta ta wuce warta, har ta kusa barin field din ya daga murya yace Islahulkhair tsaya wa tayi bata juyo ba, yace kin iya B.Ball? Juyowa tayi tace wat if na iya? Yace i want u to play wit me pls, kamar ba zata tanka ba sai kawai ta qaraso tace lets do dis, ya fara bata ball din suka hau bugawa, sai da yayi mata 12-0 wai ita ojoro yayi haka zatace ba ta yarda ba sai a sake, haka suka dinga yi ko daya bata ci ba, tace a qara one last time, yace Nooo nan ta yi wayon kwace ball din taje ta sa a ragar sa, yabita ya qawace ball din ta yi tangar tangar zata fadi ya tallabota suka zube a qasa suna daria sosai, yace Islahulkhair I need smeone da zan dinga games da ita bayan nayi aure, i love games, nd u fit wat i like, so u want to be my game partner nd my life partner? Ta tsureshi da ido, yace zan fahimceki idan kika ce aa coz nasan beef din da ke tsakanin Grandma dina and ur grandma, but kar fa ki manta mun hada kaka da ke da babana da mamanki Uwasu daya ubansu daya nima ina da jinin Umma hajja tatare dani so ban ga dalilin da zaisa ki qi ni ba, oh maybe ban miki ba, ya miqe ya barta kwance har ya juya, Islah tayi saurin cewa Yasamir ya juyo ta miqa mai hannu da ga kwance, ya sa hannu ya dago ta, cikin sanyin muryarta tace Yasamir m scared, yace i knw wat u are afraid of, dis Culture has to stop now, ba Zamanin daaa mu ke ba, trust me pls, ta daga mai kai tace ok. Yace I love u Islahulkhair, cikin kunya tace i love u Yasamir..
7. GIDAN GANDUby Biebee Isa
Sun gama exams qarfe 12 suka dawo gida, Maysah ta shiga wanka, ta ci abinci, ta fito da sauri tana yana gyalenta na afta dress, ta kalli mamarta tace Amma na je gurin tsoho, cikin hausarta, akwai dambun nama a kitchen ki kai mishi, da sauri ta shiga kichin ta dauko, ta nufa Sassan tsoho.Ta shiga dakin da Sallama, aka amsa ta, ba shi kadai ke dakin ba su biyu ne, ta ce tsohona ina wuni ya ce cikin sake fuska, Ruma kina lfy? Ya exams? Lahya Alhamdulilahi, ta kalli wanda suke tsaye tare dace Yazayyad ina wuni yace lfy lau Ruma tayi murmushi, Tsoho yace ki diba bedside na nan tun da safe babanki ya kawo man newspaper nace sai kin dawo zaki karanta man, ta miqe cikin yanayinta ta nufi dakin Tsoho, Zayyad ya bita da ido, ta dauko jaridar ta matso da sofa ta zauna ta shiga karanta mai newspapern nan cikin qwarewa da muryar ta mai dadi. Lumshe ido zayyad keyi sakamakkon jin muryar ta dake ratsa jinin jikinshi cikin kwanyar kansa.Nan take zuciyarsa ta kamu da son Rumaysah, duniyar tunani ya fada, ba tare da sanin ta gama har ta shiga dakin Tsoho don dauko mashi magungunanshi, Tsoho sai magana yake mai amma inaa hankalinshi baya gareshi, Tsoho yace Kaii Zayyadu, firgigit ya dawo hankalinsa, Naam tsoho, lafyan ka? Yace wlh tsoho Rumaysah ce, me tayi? Yace ba tayi komai ba, Amma wlh na kamu da sonta farat daya, Tsoho ya danyi jimm kafin yace amma kasan dai ba a soyayyah a gidan nan ko? Nike da ikon zabar ma kowannen ku mata, Zayyad yace Tsoho, Ba wai nace ka bani Rumaysah a matsayin mata ba, nidai ina gaya maka ne na kamu da sonta, duk wacce ka zaba mun zan maka biyayya don na san kai Adali ne, ba zaka zabar mana abunda zai cutar da mu ba, jikin Tsoho yayi Sanyi, Zayyad ya daure shi da jijiyoyin jikinshi. Ya daure yace Allah ya sa mu dace, Zayyad yace Amin, Maysah ta gama jin zancen Tsoho da Zayyad jikinta ya fara rawa. Kanta a qasa ta shigo parlorn tace tsoho bari na koma Sassan mu, yace Rumah daga zuwanki? Ko don kin ganni da wani ne kike kishi? Tayi murmushi tace Aa zan daije na dan duba karatu ne, muna da exams gobe. Yace toh Rumahna Sai da safe. Ta wuce da sauri, Zayyad ya bi bayanta shiko tsoho ido ya rakasu dashi. . ji tayi ana Maysah Maysah, ta tsaya tare da juyowa, Zayyad ne nan jikinta ya soma rawa, Yace Rumaysah bansan yadda zaki dauki maganar nan ba, tunda nake a rayuwata bata son wata mace da sunan soyayyah, burina na samu na kaina, najira tsoho ya zaba mun mata, nikuma zan sota, muyi zaman aure, amma kuma sai na kamu da sonki tun ranar da muka dawo, na bar abun a raina don kar na zurfafa a sonki kuma a zaba mun matar da bake ba, a yau kuma na ga bazan iya jurewa ba har sai da na fada ma tsoho sirrin dake raina, kuma a ganina ya bani damar sonki don be ce kar na soki ba, Maysah ina soki ki bani damar nuna miki son da nake miki, i love u rumaysa’u, jikinta yai sanyi qalaw ta rasa wane yanayi take ciki, bata taba soyayyah ba, amma haka kawai taji Yazayyad ya mata kuma da alamu Tsoho ya amince musu, Bakyasona Ko Maysah? Ta gyada kai Alamar Aa, yace kina sona? Ta daga kai cikin kunya, ya sake ihun murna yace i prmis u wont regret dis…
*****
Cikin Kwana 14 Soyayyah me qarfih ya shiga tsakanin Mu’ammar da Haneefa, Jawad da Bilkisu, Suraj da Fadila, Samir da Islahulkhair, Rumay’sah da Zayyad. Tsoho na sane da su duka, ya dai zuba musu ido ne, ni ko biebee nace tunda sun daidaita kansu ai sai ayi..
******
Sun gama Jarabawa Lafiya, Tsoho ya hada musu gagarumin Walimar kammalla karatun Sakandire, ko waccensu taci kwalliya, aka gabatar da Walima cikin murna tsoho ya ba ko waccensu Kyautar Mota, tare da check din dubu 50, Daga baya kuma a ka ci aka sha… Suna zazzaune tun daga matan Tsoho zuwa yaranshi da jikoki, Naima(Amira)tace Tsoho yaushe zaka zaba mana mazajen aurene? Ni fa na qagara nayi auren nan naji abin da akeji, Dukansu suka ji maganar bambaraqwai kunya ta lulube su duka, barin ma babanta baba usman da ya daburce dan kunya, haka Amira take, wani lokacin idan tayi magana ji yake kamar ya nitse, ya rasa me ke damun Amira, gashi ita kadai ce diyarshi, tsoho ya rasa me zaice mata? Haneefa tace kefa banza ce jaka kawai mara hankali, Suraj ya kasa hqr cikin bacin rai yace ke meye haka kike zaginta? Amira ba ta girmeki ba? Hajia babba ta chafe tace ai naga girmanta kawai tayi ba haihuwarta ba, kuma kai meye naka? Ka bari yanuwanta na jini su yi mata fada ba kai ba jikan mayyu da aljannu, zai yi magana Umma hajja tace Surajj ya isa, duk jikan umma hajja da Hajia Ama sunji wannan zagin, iyayensu sun saba da jin zagin da ake ma mahaifansu shisa abun ya dena damunsu. Amira ta buga tsaki tace Haneefa kinsan ina tausayinki, don wlh na fara jibgarki garada 10 ba za su iya qwatarki ba, dan kinsan qarfi ne da ni kamar shari’ah… Bilkis ta ma hanifa rada tace kinsan dai bata da hankali ko? Ta fara jibgarki wlh ba me iya qwatanki. Tsoho shine kayi shiru ko? Yaushe zaka zaba mana mijin aure? Tsoho ya daure yace Amira aure kike so? Tace Eh tsoho, duk aka juyo ana kallonta ita ko ko a jikinta. Yace kar ki damu da Zaidu ya dawo za a sanar da kowa madafarshi, ta yi shewa yauwa tsoho ni Yazayd din ma nakeso.. ZAYD kuma??
8. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Tsoho yace ku tashi zan ne meku, Duk suka tattashi, Tsoho yace Hassan da Hussaini da Gambo ku tsaya akwai magana, Su suka koma suka zauna, Tashin hankali, in akwai abunda Hajia babba ta tsana be wuce yanda M.Zailani ke nuna wariya ga yaranta ba, tayi mitar tayi masifan amma shirun, A cewarshi sune manyan yara maza a gidan, duk da bashi ya haifesu ba amma jinin qaninsa nashi ne kuma yana auran Uwarsu, Yo su Mudassir da Labaran fa? Ai in akwai Manya be wuce su ba ko? Yace toh bana buqatar shawararsu, idan ina da buqatar hakan zan nemesu, haka zata zauna ta tare yaranta ta chusa musu tsanar Qanwarta ta Hajia Ama. yaran Umma hajja ne abokan shawarar Tsoho, ko yaransa na cikinsa(‘yan dakin Hajia Ama) be neman shawararsu, da yake su masu fahimta ne basu taba damuwa da hakan ba. Tsoho baya yanke hukunci sai ya nemi shawarar Baba Hassan, Hussaini da Baba Gambo. Yace Ya kamata yaran nan a aurar dasu don naga har wasu daga cikin su sun fara magana, Baba Hassan Yace Tsoho ina ga kamar a bar yan samarin su gama bautar qasarsu su kuma matan ko Dan Computer skul a sasu na shekara 1, Tsoho yace amma ka san da sun gama ba a jiran komai sai a aurar dasu, in yaso su tafi dasu chan wurin bautar qasar tasu. Baba Hussaini yace Ehtoh Baba haka ake yi a da. Amma ynz ina ga a dan qara musu shekara 1, lokacin sun gama bautar qasan har sun fara aiki ko wq ya samu na kanshi, sai ayi auren su dauki matansu su tafi dasu chan. Tsoho yace toh Shikenan Allah ya shige mana gaba suka amsa da amin.
9. GIDAN GANDU by Biebie Isa
A hanya Samir ya samu Ameerah, yace Amira meyasa kikayi rashin kunya gaban tsoho? Ta kalleshi da niyyar mai masifa taga ya tsureta da ido, tace kaga dai ina jin kunyar ka ko? Meye rashin kunya a ciki? Son Yazayd ko ce musu su mana aure? Ai nasan kowa nason auren nan, don na ari bakinku nayi magana sai ace nayi rashin kunya, da yake yana da sanyih yace Ba haka nake nufi lil sis meerah, waiyoAllahna wannan sunan yayi dadi yasamir, dan qara fadih muji, yayi smile yace Lil sis meerah, ta saki ihun da ya tsoratar dashi, ta ja hannunshi kamar wani soko ya bita suka zauna, DanAllah Yasamir ina son sunan nan ka dinga kirana dashi kajih? Yace toh ynz kinsan me nakeso da ke? Ta girgiza kai, yace inaso ki zama me kunya, kinga dai da babanki da mamana ya da qanwa ne ko? Ta daga kai, to inaso ki zama me kunya da kawaici, idan kina da prblm ki fada mun kinji? We’ll solve it togeda, nd if u nid someone to talk to, i’ll b ryt here, tace ba zaka gujeni ba? Don mutanen gidan nan na cewa na cika damu nd ina da saurin ginsa yace bazan tava gajia da maganganun lilsismeerah ba ko da kuwa zamu kwana tana mun labari ne, tayi murmushi tace tohm bigbrosamir, yayi smiling zaiyi magana wayar shi tayi qara, Islah ce ya dauka hey babe gani nan zuwa, Amira ta kalleshi tace waye Babe? Yace Islahulkhair, tare da miqewa yace bari naje, tace bigbrosamir ya juyo yace naam lilsismeerah? Tace u think Yazayd will like me? Jaruba yace a ranshi a fili kuwa ce mata yayi he will love u. Tsalle ta daka tana tafi yace i gotta go, oryt bye, ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da kallo, dabadan Yazayd ba da tace tanason yasamir…
****
Yanzu ku haka xaku tsaya wasu barehn da basu fiku da komai ba su mallake muku mahaifi? Kune yaranshi gudan jininsa, Aunty Zainab(matar B.Gambo) tace haba Hajia wai kullum sai an nanata maganan nan, wannan magana an dade anayinta fiya da shekaru 30. Ni banga laifin baba, Keee Zaynaba, yi man shiru mutuniyar banza da wofi inji hajia babba, kaii Allah ya isa tsakanina da Hajjo, ynz sai da ta shanyeki? Ta gama dake, takai sunanki gaban boka da yan tsibbu, tashi ki ban guri banza sususu wanda bata kishin kanta da yanuwanta. A. Zaynab ta miqe sumsum ta bar dakin yanuwanta suka rakata da ido, ita ko Addua take musu Allah ya sa Ta gane. duk dakin karime ita kadai ta fita daban. Amira ta shigo sasan taji Muryan Babanta (Baba Usman) yace Yanzu Hajia meye abinyi? Yauwa mafita dayace, hankalin Musbahu ya karkato kanmu, ni da ‘yayana da jikoki na kadai, yayi watsi da lamuran ‘yan dakin Aishalle da Hajjo, ya zamana muka dai ke gabansa, Aunty Abida tace taya zamu sa hakan ta kasance? Hajia babba tayi murmushi tace ku bar komai a hannuna… Zan shayar dasu Mamaki, da nayi sanya amma yanzu ko ni ko su. Ku tashi ku tafi. Duk suka miqe Amira najin haka tayi saurin barin gurin, da niyyarta tashiga tace Allah ya tona Asirinku, sai kuma ta tuna da mgnr Bigbrosamir na dazu. Tayi sassan su Islahulkhair da gudu, zaune ta iske su suna shan lov, ta zuve gabansu tana haqi, Islah ta miqe da sauri lafia Amira? Samir cikin damuwa yace lil sis meerah wats wrng? Ta fara zuba zance, ba wanda ke gane me take cewa, Samir ya dagota yace kallenih, ta kalleshi yace fada mun me ya faru a hankali, a hankali kuwa ta dinga zaryo duk abunda tajih, hankalin Islahulkhair ya mugun tashi Tace yanzu me zamuyi? Muje mu sanar da Tsoho, Samir yace wait, Islah na, no one must know abt dis? Tace heyy we are tokin abt my parents nd grandparents i cant jus stnd here and do nthn, wel yea my father too is involved my grandma olso, meye amfanin gaya musu? Suyi ta tashin hankali? Su rarrabu? We are going to stop dis frm happening, mu 3 dinnan! I dont trust Amira, kasan bata– Amirah ta chakumo islah tace banida me? Samir ya shiga qwatar Islah data qi cewa komai, don ita ko chachan baki ake da ita bata daga kai ta kalleka balle ta tanka maka. Amira ta saketa ta ce U dnt trust me? Yo trust dinki nakeso dama? I am telling on my dad nd his siblings, yet u dnt trust me, ke a tunaninki ban san abun da nake ba, Bani da hankali? Toh da uwarrrr– samir yayi saurin rufe mata baki tare da cewa ya isa lilsismeerah. Idan har kuna so plan din mu yayi aiki we will have to work togeda, ku ajiye differnces dinku aside. Amira tace Ni bro banda matsala itace dai ke da ciwon qwaqwalwa shisa bata san who’s on her side ba, Islah tayi murmushi tace kiyi haquri Amirah i dnt mean to, tayi murmushi tace toh shkn ya wucei, bigbrosamir me zamuyi??? Yace Yauwa sisters abinda zamuyi shine mu samu su ido sosai, duk moves din da zasuyi muna sane, Islah tace How? Yace yauwa we’ll kip a close watch on dem, ni da Amirah mune ‘yan ciki zamu san me su keciki, barin ma ke Amirah ke macece, zaki fi kutsawa ko ina kingane me nake nufi? Tace nagane i’ll prove to u m not crazy as dey think i am, yayi smile yace i know, My lilsismeerah is’nt crazy. Tace yauwa Yayana ka ma wannan budurwar taka warning ta qara ce mun mahaukacyi sai na zaune mata ruwan Hanji, suka fashe da daria duka, islah tace Oh Ai fa na bani da mita, ba kince kin haqura ba? Ameerah tace wai misali nake baki, Samir yace Amirah kar ki manta, kar ki gaya ma kowa kinji? Tace ba wanda zai sani, Okay i will leave u too ku dan sha soyayyah ta fada tana kakkashe musu ido tare da tafia duk suka sa daria. Ni nace Ooo Amira halinki sai ke.
10. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Ko da Amira ta koma sassan hajia babba bata ce komai ba, zama tayi kusa da ita tace hajia babba fita zakiyi? Tace eh Amira, muje na kaiki a Mota na, Waaaa? Allah ya sawwaqa na shiga tuqin ki, kinga ma tafia ta, Sai kin dawo, Hajia karime ta lullube fuskarta ynda ba zaa shaedeta ba tayi waje, taci saar fita daga babban gate ba tare da an ganeta ba, Adaidaita ta tsaida tashiga tare da cewa marrabar konduga zaka kaini, yace dari 500 tace yi sauri zan baka dari 8. Da sauri me napep ya ja er qurqurarsa. Suka bar layin. Sameer da Amira ne suka fito daga gidan, suka bi bayansu Hajia Babba, tafia me nisa sukayi kafin suka iso malilo, unguwa ce me kama da qauye, jan qasa ce sai bukkoki, bukar gun basu wuce 10 ba, da alamun mutane basu fiye yawa ba. Daga nesa samir yayi parking, hajia babba ta fito daga keke napep ta biyashi ta nufa wani bukar da yafi sauran kyau. Daga nesa tace bigbrosamir muje yace A’a ba musan me ke ciki ba, kamar daga sama suka ga wani mutum daga shi kamfan ganye, Samir yace baba ina wuni? Yace lhfy yaro? Eh baba daman wanchan bukar na ke tambaya, ya nunu bukar da hajia karime ta shiga, tsohom yace eh nan ne, ko ba bukkar er madiyo qashi ba tsoka ba? Ai yaro kar kaji komi, tun da kazo nan buqatarka ta biya(Waiyazubillah.) tsoho yayi gaba, Samir yace Wato wurin Bokanya Hajia Babba tazo? Bari kaga naje, yace kee so kike ta ganki? Dabara zanyi, uace lilsismeerah be careful pls, ta fita ta nufa bukkar, daga nesa ta fara jin muryar Hajia babba samasama inda take cewa, ina so ki musu yankan qawna ya zaman ba kowa gabansa ba hajjon ba, ba Aishallen ba, daga ni sai ‘yayana, sai jikoki, da sauri Amirah ta qarasa jikin bukkar ta kasa kunne, ‘yar madiyo tayi daria tace wannan shi yafi komi sauqi, abu daya kawai zakiyi, tayi dan buga buganta ta dauko wani garin maganin da tayi mai sidabbaru, tace amsa wannan, yaushe kike da miji? Ina nufin yaushe ne kwananki ranar girkin ki, tace gobe ne, kuma ai girkin ba.mu keyi ba akwai masu yi, Er madiyo tace toh gobe ki tafasa wannan maganin, kiyi tsarki dashi, ki kwanta dashi maigidan naki, toh daga wannan rannan ba macen da zai qara gani da gashin ido sai ke, Hajia Babba tace Er madiyo banan gizo ke saqar ba. Dan Zailani ya kusa shekara 100, ta ya zan kwana dashi? Ai an kwan biyu er madiyo a dai chanxa wata hanyar, Er madiyo tace Keeee hakan na zaba miki, idan be miki ba bani garin maganin da na baki. Da sauri karime ta fara zuba haquri, Ameerah da daria ta ci qarfinta ta zura a guje tayi hanyar mota, samir na ganinta yayi saurin bude mata qofa. Ya fincika motar yayi reverse, ita ko Ameera sai daria take tayi Samir ya dinga tambayarta ta kasa magana sai dariar mugunta da take tayi, sai da tayi me isarta kafin tayi shiru, yace Lilsismeerah kinji yanda sukayi?ko sunganki kina leqemsu? Sai ta kuma fashewa da daria Samir yace ke nifa bansan daria me ya faru? Nan ta kwashe komai ta gaya mai, shi Samir kunyar maganar yaji ita kuwa ko a jikinta. Haka suka kama hanyar Gari…
*******
Ya Samir yanzu ya zamu hana wannan abun ya kasance kasan yau Girkin sassanta ne ko?cewar Islah Ameerah tace me zamu hana? Tsarki da maganin ko kwana da tsohon? Waiyo Allah da Islah da Samir kamar su rufeta da duka da kunya, Samir yayi dauriyan cewa muyi dozing dinta, maganin baccin da ba zata tashi ba for d whole nyt. Kinga ba za ta samu damar shiga dakin nasa ba, Islah tace hakane yasamir. Ya fita da sauri ya nufa chemist, magungunan bacci ya hado kafin ya dawo don samun dabarar da za a samu hajia babba ta sha magungunnan nan..
Ameerah amsa wannan maganin ki hada mata dan juice ki watsa mata guda 14 a ciki, yo ni na san juice din da zan hada mata, Islah tayi saurin cewa bari ni zan hada sobo ynz shine ba zai chanza kala ba, sai ki mata dabara ta sha. Duk suka amince da hakan, Islah ta shiga kicin dinsu ta hado sobo, Harda sa qanqara, ta iske Yasamir da Amira ana labari, ta miqa mata tace gashi tym to do ur part. Suka balle magungunan nan suka watsa cikin sobo, Samir yace Lilsismeerah i trust u on dis, ds our only hope make sure it works, are u doubting me or wat, da sauri yace nooo ta miqe ta nufa sassan su, Qarfe 8:30 Hajia babba ta yi wanka, su karime harda wanke baki zaa je gurin darling Tsoho (lol) Ameerah ta shigo da Sallama da Jug a hannu da kofi. Karime ta tabe bakih, Sanabe, daga ina haka, meye a hannunki? Tace sobo na hado maki, tace waa zai sha qazantarki? Ameerah tayi rau rau da fiska, Anya ke kika haifi uba na? Kina nuna min tsana qiriqiri, ko kasheki xanyi? Ko na samaki guba ne a ciki?toh kalla Amira ta tsiyaya sobo a cup ta shanye, to kinga ban mutu ba( nikam nace Anya kuwa Amira?), Karime tace toh uban wa yace kasheni zakiyi? Baki ga nayi shiri ba? Tsoho na jirana, ko so kike naje gun Tsoho da warin baki? Amira tace Uban wa yace maki sobo na sa warin baki? Toh qamshi zai qara miki Allah ko Amirah? Eh wlh, to tsiyayo man, ta bata copi daya karime ta kafa sai da ta shanye cup daya tass, Amirah tace kakus bari kiga na gyaraki kiyi kyau don tsoho ya rude da ya ganki, bazai dinga kula da Hajia Ama ba ko Umma hajja, cikin maye Hajia babba tace Allah Amira? Yi man Me guduma irin na zaman– rigijib ta zube kan gado, Amira ta fashe daria, wooo hajia babba ta bugu, heheh tana darian mugunta itama ta zuve kan gadon. ni dai biebee nace swtdrms Hajia Babba nd d Amazing Ameerah

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements