Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / LAMARIN KADDARAR AURE NA

LAMARIN KADDARAR AURE NA

LAMARIN KADDARAR AURE NA

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️ EPISODE 1& 2

Gidane d’an madai daici , baza’a kira masu gidan da talakawa ba ,amma sunada rufin asiri , d’akuna biyar ne , a cikin gidan , da kitchen da d’akin matar gidan dakuma bayin waje sai d’akin bak’i daga gefe kuma a cikin d’akin matar gidan d’akin mai gidan ne a ciki ,wato mu had’u a parlor sai toilet a gefe , malale gidan yake da fasasun tails ,gefe ga pampo ,wata matashiyar mata na hango tana fitowa daga d’akinta , fara amma ba sol ba sanye take da doguwar riga ta atamfa mai ruwan ganye da kwaliyar flawoyi a jiki , rigar ta zauna a jikinta sosai , ta fito da asalin kyaun ta dakuma kyan diri na cikinta , hannayenta sanye suke a awar waro wuyanta kuwa wata sark’a ce y’ar k’arama , bakinnan yasha pink d’in jan baki , a k’ala zatayi shekara ashirin da biyar 25yrs , kitchen ta nufa , tukunyar dake kan risho ta sauke ta dawo ta koma d’akinta , ta fito da jug da food flaks , kitchen ta nufa , bud’e tukunyar da ta sauke yanzu tayi , jollof d’in shinkafa ce yaji salad da carrot da albasa , sai k’amshi take zubawa , bud’e kular tayi ta zuba abincin ta rufe , ruwa ta d’ibo a randa ta zuba a cikin jug d’in , ta maida murfin ta rufe , tirai ta d’auko a kwando mai adon falawoyi a jiki ta jera abincin da cokali da plet da kula a ciki , ta nufi parlorn ta dashi , wani d’an madai daicin tebur ta ajiyeshi , kana ta koma bedroom d’inta , ta zauna a gaban stool tana kallon dressing mirror , k’ara shafawa fuskarta powder tayi tare da k’ara feshe jikinta da humra masu k’amshi .”

Daga kanta tayi ta kalli agogon dake manne a jikin bango , k’arfe tara na dare , mik’ewa tayi ta k’arawa d’akin turaren wuta ta ciro wayarta dake , chaji wata number ta danna cikin sa sanyar murya tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina , daga cikin wayar wanda takira yace ”Afnan sarauniyar mata afuwan yau nayi dare ,yanayin aiki ne amma insha Allah ganinan , zuwa mekikeso ?”k’ara rage muryarta tayi tace ”banason komai Allah ya dawo dakai lafiya ,amen yace ”daganan suka kashe wayar , bacci ne yake k’ok’arin surarta tana k’in kwanciya , jiyo bugun k’ofa tasata ficewa da gudu , bud’e k’ofar tayi , tana ganinsa ta rungumesa tana dariyar farinciki , d’agata sama yayi yace ”ammata ba kya girma ko da alamu bakici abinci sosai ba ?” naci Afnan tace tana dariya , rik’o mata hannu yayi sukayi bedroom d’inshi , temaka masa tayi da cire kayan jikinsa ,ta rakashi toilet nanma ta temaka masa yayi wanka , wanan ta zamo al’adarsu tun tana amarya yanzu gashi shekararta biyu ,amma babu wanda zai ce tayi wanan shekarun komai nata kamar na budurwa , tare suke wanka sai dai inbabu mutum d’aya hakama cin abinci tare sukeyi abincin rana ko sbda babu organ nata sai lokacin da tayi ra’ayin cinsa .”

Temaka masa tayi da shafa mai , ta dubo masa kayansa a drowa , wando gajere da farar singlet , gado ya hau zai bud’e laptop d’insa , cikin Maria raicewar murya tafara bubuga k’afa tana cewa uhm uhm my Hubby kazo muje kaci abinci , Hankalinshi ya tafi ga laptop d’in da ya bud’e , yace ”jeki ganinan , no bazan wuce ba harsai ka taso ,mik’ewa yayi tana gaba yana biye da ita , teburin data jera masa abincin sa ta nufa , bayan ya zauna ne , ta zubo masa tare da sa nata cokalin tana bashi a baki , shima hakan yake himata , har sai da suka k’oshi sanan kowa yai brush , Afnan na ganin Haisam zai wuce ,bedroom d’inshi ta rik’o masa hannu cikin shagwa6a tace ”yanzu lokacin bacci ne kadinga hutawa rayuwarka , badan Haisam yaso ba ta dawo suka wuce nata bedroom d’in .”

Washe gari ta tashi da shirin zuwa anguwa , bayan Haisam ya fita tagama komai na gidan da yazame mata farillah , misalin sha biyu na rana ,tajiyo ana bubuga k’ofa , mik’ewa tayi ta je gurin mai buga k’ofar , tana bud’ewa gabanta ya fad’i , mama ce sanye da hijabi , tasan lokacin kukanta yazo , cike da masifa mama , ta shige ciki batare da tayi sallama ba ,Afnan ce ta bi yanta ,a parlor maman ta tsaye tana k’arewa gidan kallo , mtsw taja tsaki ,tafara sababi , ga gida har gida ,amma babu y’a y’a nikam Haisamu ya kwaso mana juya , ta fashe da kuka ,

Afnan data mik’e daga durk’uson da tayi tace ”mama itafa aihuwa rabo ce , kee rufemin baki banason kinibibi , wayasani ma ko kafin auran naku kinje kinsha abinan na hana d’aukar ciki , shiru Afnan tayi ta sunkuyar da kai k’asa , inda sabo ta saba da gorin mama , amma ba’a sabo da wulak’anci , yasata fashewa da kuka mai ban tausayi, kitchen mama ta shiga hango gwan gwanin madara yasata Ciro ledar da ta sak’ale a Mara tasa cikali ta d’ibi madarar ta fito , itadai Afnan ta koma d’akinta .”

Mama na fitowa tayi waje ko rufo k’ofar batayi ba , Afnan ce ta mik’e ta fito waje , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata , tanata zancen zuci ,ace tunda nayi aure banida kwanciyar hankali uwar miji tasani gaba , akan maganar aihuwa , ta kuma fashewa da kuka , tana cikin haka mak’ociyarta ta shigo suna mutunci sosai sunanta Fatima , mamaki ne ya kamata ganin k’ofar gidan a bud’e , shigowa tayi da sallama tace ”Afnan har yanzu baki shirya bane ,ni gashi harna gama komai , kan Afnan a sunkuye bata d’ago ba , Fatima ce ta rik’o hanunta tare da shigewa da ita d’aki suka zauna , Fatima ce tace ”ko baki gayamin ba nasan mama ta shigo amma dan Allah kiyi hak’uri ki cire wanan surutun nata a zuciyarki , Allah ne me bawa kowa aihuwa kemafa bawai baya sanki bane ya hanaki , kuma ko asibiti da kikaje kince likitar tace ”lokacine beyi ba amma zaki biye mata hankalinki yadinga tashi ?”.

Afnan ce a share hawayenta tace ”Fatima kinfi kowa San in halin da nake ciki kuma kinfi kowa na anguwar nan sanin halin mama , takuma share hawayen da suka sake zubo mata race ”aurena da Haisam yin Allah bana mutum ba ,cikin tausayawa Fatima tace ”nasani amma kirage sawa kanki damuwa , tashi ki shirya muyi mu tafi , cikin fushi Afnan tace ”Fatima bazan iya zuwa ba wlh kwai kije zanje wata rana , babu rarrashin da Fatima batayiwa Afnan ba ‘amma furr tak’i , haka Fatima ta wuce gida zuciyarta babu dad’i ko kad’an, bedroom d’inta ta koma ta kifa kanta akan fillo tana kuka , tana cewa ya Allah ka kawomin aihuwa cikin satinan Allah ka duba irin gorin da nakesha a gurin dangin mijina .”

Tana cikin kuka taji wayarta tana ring dubs mai kiran tayi , ganin my husband ,yasata dai daita muryata ,tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina ya aikin , dafatan babu wata matsala ko ?”dariya Haisam yayi yace ”wato ni zaki yiwa wayo ko ?”waya saminke kuka ? dariyar yak’e tayi kamar yana ganinta tace ”ba kuka nakeyi ba, kwai kai na ke ciwo , hmm Haisam yace ”badan ya yarda ba yace ”to ki kularmin da kanki , daganan sukayi sallama jiki a sanyaye , sallama taji na muryoyi da dama tasan ko suwaye , hakan yasata mik’ewa ta fito parlor su biyu ne y’ammata ,da Khadija da Aisha , taunar cingom sukeyi cikin isa da wulak’anci , Afnan ce ta k’araso da fara’arta tace ”ah sanunku da zuwa , ko kallo bata ishesu ba bare tasa ran zasu amsa mata , neman guri tayi ta zauna a gefen kujera , Khadija mai shekara goma sha biyar ta mik’e tana yarfe hannu tayi kitchen , Afnan ce ta taso cikin zafin rai tace ”gaskiya yau bazan yarda ba ,kunason wulak’anta min gida , Aisha ce ta mik’e tare da gallawa Afnan harara tace ”gidan yayan mu ne dole muyi abinda ranmu yakeso .”

Zuciya ce ta d’ibi Afnan ta wankawa Aisha mari ,da gudu Khadija ta shigo jin k’arar kukan Aishe ta cakumi wuyan Afnan , Afnan ce ta kaimata mari , dayake k’arfi ba d’aya ba , Afnan ta nad’a musu duka , girkin da basuyi ba kenan suka , wuce gida rai a 6ace , zama Afnan tayi tana girgiza k’afa , tana jiran abinda zai biyo baya, indomie ta dafa dan yunwa ce ta addabeta , tana gama dafawa ta kwashe a plet ta fito kenan ta jiyo tafiyar da bata tunanin ta kowace face ta mama , mama na shigowa ta ka6ar da abincin kana ta murjeshi a k’asa , bala’i tafara yo gidan ubanki ne kokuwa , dan sunzo ziyara gidan yayansu shine zakiyi musu duka , matsiyaciya juya kawai , Afnan ce ta dubi mama ido cike da hawaye tace ”mama menayi dahar kike jifana da wanan mugun kalamin ?”marine ya biyo bayan k’arshen maganar ta , juyawa mama tayi tana dura mata zagi.”

Afnan ce ta koma d’aki rik’e da kumatu tana kuka , janyo akwatin ta dake saman durowa tayi tafara loda kaya , sai da ta cikashi tabb sanan ta d’auki hijab d’inta ta fito waje , kulle gidan , ta mik’awa Fatima mukulli Fatima da ganinta tace ”ina zuwa kuma yau , Afnan na kuka tace ”zani gidan iyayena , bazan zauna ba , Fatima cikin tausayawa tace ”karkitafi bada izinin mijinki ba ,girgiza kai Afnan tayi tace ”karkiyimin haka ,iya hak’uri nayi to yau nagaji da zagarmin iyaye da akeyi wlh , babu inda Fatima ta iya ,sabda tasan iya hak’uri Afnan tanayi , an k’ureta ne , haka ta k’ar6i mukullin ta janyo hijab a igiyar shanya tabi bayan Afnan , mashin ta tara ,sai da ta d’ora akwatin sanan ta hau tana d’agawa Fatima hannu .”

Mislin k’arfe goma na dare Haisam ne ya keta bubuga k’ofa amma shiru , cikin mamaki ya nemi guri a kan mashin d’insa yana jira Afnan tazo ta bud’e masa , yasan dai bata bacci sai ya dawo , sallamar da yaji ne ta katse masa tunaninsa , mijin Fatima ne ya mik’a masa hannu .”

Bayan sun gaisa ya mik’a masa mukulli , cikin rashin fahimta Haisam yace ”wanan mukullin kamar na gidana ?”mijin Fatima ne yace ”eh shine mai d’akin naka ce tabawa Fatima tabaka , ran Haisam babu dad’i ya kar6i mukullin ya bud’e gidan , shi ko lura ma baiyi ba gidan da kwad’o sai yanzu .”

Shiga da mashin d’in yayi ya ciro wayarsa a aljihu , ya danno lambar Afnan , jiyayi ance a kashe take , cikin tashin hankali ya bud’e parlorn ya shige bedroom d’insa , zama yayi a bakin katifar tasa cike da tunani , tun zamansu da Afnan bata ta6a tafiya anguwa bata sanar masa ba , to anya yau lafiya kuwa?” sai sak’e sak’e yakeyi a zuciyar sa , tun a hanya yakejin yunwa ,amma da yashigo yaga gidan babu gimbiyarshi yasashi ,jin komai ya ishe shi , ya had’e kai da gwuwai wa .”

*FARKON LABARI*
Afnan yarinya ce ga Alhaji Nasir , Alhaji Nasir yanada arzik’i dai dai gwar gwado , zuwa makkan shi sau biyu , yanada mata biyu , da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila , Hajiya Zainab tanada yara biyu ,da Afnan da Salma ,Hajiya wasila nada yaro d’aya babba mai suna Usman ,duka yaran nasu sun girma kuma suna gidan aure , Alhaji Nasir yanada zafin rai sosai kuma ba kasafai yakeson ana kawo complain d’in yaransa ba , inhar kunason zaman lafiya dole kaso yaransa koda sunyi abin rashin kyautawa, kowace a cikinsu na k’ok’arin ganin sun kyautatawa y’ay’ansu ,amma baya gani , yanada wata yaya mai suna Anty Aisha , bata k’aunar matanshi ko kad’an ita kuma Allah bai ta6a bata aihuwa ba , ta tsani taga y’ay’an mutane , kuma a hakan tasami shiga , a gurin Alhaji Nasir .”

Kuma shawarar ta tana aiki sosai , acikin y’a y’anshi Afnan ce bata auri mai kud’i ba , kasancewar batada hangen nesa , kuma Allah ne ya had’ata da Haisam , a gurin wani biki da sukaje , shekaru uku da suka wuce , na k’awarta , yanayin kamun kanta yasa Haisam jin yana sonta , sun dad’e suna soyayya , kuma a soyayyarsu sunci karo da mahassada da makusa , kaf cikin dangin ,dadynta da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila babu mai son auran , hakan yasa duk wuyar da takesha bata magana ,saboda tasan babu mai temaka mata , wata k’awar mahaifiyarta mai suna anty Ummi ‘itace mai zuwa gidanta ta kawo mata abubuwan da zasu amfaneta ,kuma take tambayarta matsalar ta ,itama Rana kai mata ziyara sosai bata d’aukar lokaci mai tsayi bataje ba, Suna shiri da y’ay’an ta sosai kuma ziyartar junansu , wanan kenan .”

Suna zuwa anguwar su Anty Umma ta sauka , Ciro kud’i a jakarta tayi ta mik’awa mai mashin ,tafara bubuga k’ofar , mai gadi ne ya fito yana washe baki , gaisawa sukayi Afnan ta shige ciki , direct parlorn da zai sadata da , Anty Ummi tayi ,parlor ne tsarare yasha kayan alatu komai na gidan a in burgewa ne , inka shiga parlorn kamar karka fito saboda wani k’amshi da keyiwa mutane sallama , Afnan ganin bataga Anty a parlor ba yasata wucewa bedroom d’inta ,samunta tayi tana waya, janyo akwatin nata tayi ta zauna a bakin gado, saboda bata ban banta Anty Ummi da mahaifiyarta ba , kasancewar bata nuna mata wani abu dazai 6ata mata rai , Anty na gama waya ta zauna a bakin gadon kusada Afnan , idanun Afnan sun ciciko da hawaye ta kifa kanta a cinyar Anty , mamaki ne ya kama anty ganin akwati a gefe kuma ga Afnan na kuka .”

Anty ce ta d’agowa Afnan kai tare da jero mata tambayoyi , meyafaru mai Haisam d’in yayi miki ?kodai mahaifiyar tasa ce? “babu tambayar da Afnan ta amsa sabida kuka yaci k’arfinta ,cikin tausayawa anty ke kallonta tana girgiza kai , Anty ce ta shiga toilet ta had’a mata ruwan zafi ,ta bud’e mata sabon brush da man goge baki , ta tara mata ruwa a bahon wanka ….✍️.

Idan naga comments zan cigaba ,saboda kune na maidashi free , rashin sharhi zaisa ya zamo na kud’i🤙.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*MARUBUCIYAR👇*
*ZAINABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*
*NANCY YAR KARYA*
*AND NOW*👇
*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA*

*DOMIN KU YASA NA MAIDA WANNAN LITTAFIN KYAUTA👌RASHIN SHARHI ZAI SA NA MAI DASHI NA KU’DI*

WATTPAD momislam2020
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

 

🅿️EPISODE 3 & 4

Taji dad’in wankan , ta fito d’aure da tawul dakuma wani a kanta, Anty data ciro mata kaya a ‘akwati masu kyau tace ”kshafa mai kiyi kwaliya inkin gama ga abinci can a dining sai muyi magana , to tace ” ta je gaban dress mirror ta shafa mai da powder , ta sanya janbaki da kwali , ta d’auko kayan da Anty ta za6a mata , riga da skirt na atamfa ,dinkin ba k’aramin kyau yayi mata ba , dama itan mai kyauce ,kowane kaya tasa sai ya amshi jikinta , mik’ewa tayi ta fito daga bedroom d’in tabar Anty da sak’a da warwara , dining ta nufa ta bud’e food flaks d’in wani tashin k’amshi tayi a duka kulolin macaroni ,ce da taji kayan lambu sai farfesu a gefe rufe na farfesun tayi ,tafara cin abincin sai da ta k’oshi sanan ta bud’e farfesun tafara ci , tana gamawa tasha lemun kwakwa ta mik’e ta koma parlor , y’ar aiki ce tazo ta kwashe kayan tayi dasu kitchen , anty na bedroom tana zaman jiran Afnan ,batasan Afnan ta koma gaban TV ba , MBC 2 take kallo film d’in yasata nishad’i sosai , hakan yasata mancewa da wata damuwa da take ciki.”

Fuskarta yalwace da murmishi ta gyara zamanta tare da maida hankalinta ga TV , Anty ce ta fito da wayarta daga hand bag d’inta ,ganin a kashe yasata kunnawa , tace ”oh ko menene yasa Afnan fushi harta kashe waya oho , Anty na cikin tunani taji Ring d’in wayar , ganin sunan my Husband ,na yawo a screen d’in wayar yasata mik’ewa da sauri , ta nufi parlor , ganin Afnan na kallo yasata kuma harda dariya ,yasata tsayawa ,tana kalonta , wayarce ta kuma ruri a karo na biyu , hankalin Afnan ne ya juya ga gurin da tajiyo k’arar wayar ta , kalon kalo sukayi da Anty ta sunkuyar da kanta k’asa , k’arasowa Anty tayi kana ta mik’a mata wayar ,tace ”ki amsa man , d’agawa tayi cikin sanyin murya tace ”Aslamu Alaikum , wa’alaikissalm ,yakike ina kika shiga nazo gida bakya nan ?”shiru Afnan tayi can kuma tace ”gobe zan dawo , ran Haisam in yayi dubu ya 6aci ,Afnan ba k’aramin 6ata masa rai tayi ba , ajiye wayar yayi batare da yakuma magana ba ya fad’a gado zuciyarshi na k’una , da tunani iri iri .”

K’arasowa Anty tayi ta zauna a kujera mai kallon ta Afnan ta d’auki remote ta kashe TV , Afnan maiyasa zaki bar gidan mijinki ba tare da izinin shi ba , kuma ba tare da kinyimin waya ba¿”eh tambayarki nakeyi , Afnan idanunta zun ciko da k’wallah tabawa Anty labarin dalilin tahowarta , Anty ta tausaya mata sosai ,musamman ma akan gorin rashin aihuwa , amma Allah maji rok’on bawansa sekaga Allah ya kawo , Anty ce tace ”to yanzu dai tunda dare yayi mubari zuwa gobe ,in Allah ya kaimu sai in maidaki ,to Afnan tace ”tare da mik’ewa ta nufi wani d’aki da ban na y’ammatan gidan kasancewar sunyi aure, juyi takeyi a gadon rungume da pillow ,da rasa abinda ke yimata dad’i , hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata , tace ”ko ya Haisam zaiji inyazo yasamu bananan sai Allah , tuno Fatima mak’ociyarta tayi , da tace ”Afnan karki tafi batare da sanin mijinki ba , ina idanunta sun rufe, lokacin tana cikin tsananin 6acin rai ,kuma juyawa tayi taji sam kwanciyar babu dad’i ,tasaba dajin d’umin mijinta yanzu kam komai komai ya kwance mata , tarasa washe shawara zataba zuciyarta , tsananta kukan tayi amma ba’a jiyo sautin sa sosai .”

Washe gari tun misalin k’arfe hud’u na asbha ta tashi ,tayi wanka tayi alwalah ,tafara jero nafil fili ,tanata kai kukanta gurin Allah , tana idarwa ,ta koma gaban dress mirror ta janyo stool d’in ta zauna tare da cire d’an kwalin kanta tafara tsara kwaliya , dama gwanace , tana gamawa ta feshe jikinta da turare kasancewar ba bu inda zataje daga nan sai gidanta , batajin ma zata iya yin breakfast ,a gidan Anty saboda kewar mijinta takeyi ,jiyo kiraye kirayen sallah tayi daga masallatai da dama , hakan yasata sanya hijab tabi wani masallaci sallah , suna idarwa ta yi adu’a ta shafa ta cire hijab d’in ta d’aura d’ankwalinta , ta yafa gyale ta fito parlor ,gidan shiru kamar ba mutane , dake Anty ce da y’ar aiki ,kawai a gidan mijinta yatafi k’asar waje , sai kuma drivers da masu bawa flawoyi ruwa , zama tayi a parlor rik’e da hand bag d’inta da wayarta a hannu , jiran fitowar Anty takeyi amma shiru , daurewa tayi ta nufi kitchen ,ta tsiyayo ruwan zafi a flaks tasa lipton ,da madara da da sugar ta dauki biscuit ,tadawo parlor ,tana sha , harta gama sha Anty shiru , kuma mik’ewa tayi ta nufi bedroom d’in anty tafara nocking , tare da sallama , Anty da tayi sallah yanzu take shirin komawa bacci tace ”daughter lafiya kuwa?”.

Lafiya Anty ceawar Afnan , inason komawa gida ne ,murmishi Anty tayi mai cike da maganganu sai kuma naji tace ”to babu damuwa jekiyi breakfast ,yanzu zanyi wanka , nayi cewar Afnan ,to ki jirani ganinan fitowa , to kawai tace ”ba haka taso ji daga bakin Anty ba ta koma parlor tacigaba da zaman jira ,tana kwance a parlor har k’arfe takwas kuma tasan k’arfe goma Haisam yake fita, tana shawarar tashi sai ga Anty nan ta fito sanye da doguwar riga pink color mai adon fararen stone a jiki , kanta tayi rolling d’in d’ankwalin , tayi kyau babu lefi , kasancewarta fara , zama tayi kusada Afnan tace ”daughter ,na d’auka zaki yimin kuwana uku ne , gimtse fuska Afnan tayi batare da tak’ara magana ba , Anty ce tace ”to mik’e mutafi tunda sammako zamuyi , amma biyoni d’aki daganan saiki d’auki akwatinki, rufawa Anty baya tayi suka zauna a bakin gado , Anty ta rik’o hanunta tace “daughter jeki bud’e bed site ki d’aukomin wata leda , mik’ewa Afnan tayi ta bud’e ta ciro ledar ta mik’awa Anty , kar6a Anty tayi ta bud’e ledar , ciro wata gorar Zuma tayi tace ”wanan ke naketa ajiyewa su sauran sun kar6i nasu so wanan karki wasa dashi , cokali biyu zaki dingasha ,safe rana dare , ta ciro wata roba mai dabino da kwakwa da Zuma a manne, tace ”wanan gumba ce karkiyi wasa , nasan ta 6angaren mijinki bakida matsala to karkiyi wasa gurin kyautata masa kuma kirik’e shan magani akan jari gadiya Afnan tayiwa ,Anty suka mik’e suka fice , direct gurin motocin gidan suka nufa , da gudu driver yazo ya durk’usa ya gaida Anty Ummi , da Afnan , Anty ummi ce ta nuna masa motar dazasu hau ,cikin azama ya fito da motar tare da bud’e musu back side, suka shiga.”

Sunyi tafiya sanan suka iso gidan , Anty a duk lokacin da tazo unguwarsu , Afnan sai ta jinjina kai , to yauma kamar kulum girgiza kai tayi ,saboda anguwar talakawa ce sosai , banda so gamon jini mezai kawo Afnan anguwar nan da gatanta ,ga mahaifinta shahararen mai kud’i, kasancewar drivern yasan gidan Afnan d’in yasashi parking ,a k’ofar gidan, farinciki fal zuciyar Afnan zataga rabin ranta , harta mance wulak’ancin da ya sanyata fushi , jin Anty ta bud’e murfin motar yasata yunk’urowa ,Anty na fita itama ta fito suka kulle , motar da isarsu k’ofar gidan suka fara nocking , sbda ko da Afnan take nan bata barin k’ofarta a bud’e , jin ana zare sak’ata ,yasasu gyara tsayuwar su , Haisam ne yafito da fara’arsa , yana musu sannu da zuwa ,Anty ce ta amsa Afnan ta kasa koda had’a ido dashi , kai tsaye cikin gidan suka wuce , ko ina fess babu datti , Haisam ne ya d’auko key ya bud’e k’ofar d’akin Afnan su Anty suka shiga , d’akin natama babu datti ko kad’an sai tashin k’amshi yakeyi , da sallama ya shigo ya durk’usa ya gaida Anty Afnan cikin jin kunya ta gaisheshi , ,ya mik’e ya fita, anty ce ta k’ara yimata tuni akan ladabi da biyayya dakuma iya kalami mai sanyaya zuciya , dakuma iya sarafa miji a lokacin da yake cikin 6acin rai , kowace nasiha ta Anty ta zauna daram a kwakwal war Afnan , anty ce tace ”to inaso yau kisha wanan abin dana baki karkiyi wasa dan Allah , to Afnan tace ”Anty ta ciro kud’i zasuyi 20k tabawa Afnan , sosai Afnan taji dad’i , daganan Anty ta fito , tana shirin sa takalmi saiga Haisam ya shigo da alamu fita yayi da k’atuwar leda bak’a a hanunsa , yana ganin Anty yace ”dan Allah Anty ki koma Ante na dariya ta koma ciki ,ta zauna a parlor , Afnan ce ta fito da hijab tana shirin raka Anty mota , ganin Haisam ya ajiye leda ya fita ,yasata bud’e ledar ta lek’a ,dariya Anty tayi tace ”to sarkin kwad’ayi abin nema ya samu ,Afnan tasa dariya , dawowa yayi da plet a hanunsa ya bud’e ledar ya fitoda kaji manya gasasu da ,lemun gora maltina da viju milk da fanta , kasancewar a ya yanke suke yasashi zubawa a babban plet yace ”anty dan Allah kici , Anty na murmishi ta d’auki yanka d’aya ta jefa a bakinta ta mik’e tace ”Allah yayi muku albarka , Haisam dan Allah aci gaba da hak’uri , Afnan tabi bayanta .”

Sai da motar ,Anty ta 6ace Afnan ta dawo gida da kuka , fad’awa jikin Haisam tayi tana kuka ,Haisam da yana fushi da Afnan ,ganin tana kuka yasashi rungumota , tafara share mata hawaye , ganin tak’i dena kukan ya sa6ata a baya yana yimata wak’a yana cewa “wanene ya ta6amin y’ar baby na ,inkamashi , Afnan ta tuntsire da dariya , tafara yimasa cakul kuli yana zulewa , sauketa yayi , yana dariya , filon kujera ta wurga masa aikuwa suka fara karad’e gidan da dariyaku suna gudu , wanan ya jefi wanan haka dai suka dingayi, suna haka har k’arfe , 11 pm tayi basu sani ba ,jin shugowar mutum sukaji babu sallama , cikin masifa tafara zazzaga ruwan bala’i ,tana cewa ” yanzu Haisam asirin da sukayi maka harya fara tasiri a kanka? ” to bazan yarda ba , tsabar rashin aikinyi shine ka biye mata kuke wasan banza kamar awakai ?to wlh ko kazo ka tafi aiki ko kaci gidanku , parlor mama ta shiga , ganin gasasun kaji baje a faranti yasata zare ido tace ”kai Haisam abinda kukeci kenan?”nashiga uku ni Lauratu , tadama abinda kuka koma ci kena?tabb hmm lallai ashe mallakar tafi haka ?” yana shirin magana ta wanka masa mari , tace ”maza kazo gida ina nemanka , munafuka tun kafin yasami mai gadonsa shine kikeson tatseshi ko dan kinga ke juya ce bakya aihuwa, ko wata tazo kartasami ragowa , kuce ma kundena cin hatsi saimu talakawa , Afnan ce ta rufe baki ta shige bedroom d’inta da gudu tasa key .”

Haisam zai bita mama ta dakatar dashi tare da cewa kana binta walhi sai kayi nadama , lashe maka zuciya tayi ?”kokuwa tsoronta kakeji ?niban isa inyimata fad’aba kenan ? ta jero masa wa’inan tambayoyin , tabbas dayasan ,mama zata shigo a dai _dai wanan lokacin da bai tsaya a gidaba dayayi sammakon fita , mama ce tace ”tattaro min naman da lemon duka ka k’ullemin su a leda , cikin rawar jiki Haisam ya tatara ya k’ulle ya mik’awa mama ,tana k’ar6a ta fice tana kaiwa tsakar gida tace ”saura karka taho mutafi wlh zakaga abinda zai biyo baya, tana tafiya ,Haisam yayi hanyar d’akin Afnan yana bubugawa , yana cewa “dan Allah ki bud’e ki saurareni Afnan , kuka yaci k’arfinta tace ”kaje kiran mama kaje kawai , Haisam tun yana tsaye harya gaji da tsayuwa ya fice, daga gidan zuciyarshi babu dad’i, mashin d’inshi ya tayar ya nufi gidan su , gidane k’ato daga ganin gidan zakasan gidan yawa ne mutane ne a ciki zasuyi biyar kowa da d’akinsa , d’akin mama shine farko sai d’akin kishiyarta da tarasu tabar yara sune y’ammatan da sukayiwa Afnan rashin kunya , mama iya Haisam ne yaronta ,ta d’auki son duniya ta d’ora masa sai dai ba kasafai takeson wani yaci arzikinsa ba , aciki kuwa harda mahaifinsa da matarsa , hakan yasa take taka tsan tsan da komai nashi kuma koda ya kawo yace ”tabawa mahaifinshi zatace to ,yana fita ta 6oye , yanzu kam harya zame mata jiki ,kuma dole mahaifinshi yake hak’uri da Halinshi , kowa na gidan yasan masifarta bata barin kowa , sallama Haisam yayi a k’ofar d’akin maman nashi , ko amsawa batayi ba tace ”inka gama munafurcin naka kashigo , shigowa yayi jiki babu k’wari ya zauna a tsakiyar d’akin da aka shimfid’a tabarma kasancewar babu leda a d’akin , yai shiru , kagama bata hak’urin ?”nace kagama bata hak’urin ?”eyee ? kan Haisam na k’asa bai d’ago ba yace ”kiyi hak’uri mama , dakata cewar mama , banason ban hak’urinka banason duk wata kalma dazata karyamin zuciya tunda kai bakasan zuru ba ,wlh Haisam ka kiyayeni , kokuma nayima!!!, Haisam ne ya matso ya katse mata maganar ta hanyar shafa hanunta a fuskarshi , kawar da kai mama tayi , sbda inta fara sababin fad’anta to batajin gari.”

To kiyi hak’uri mama dan Allah ,shiru tayi tana girgiza k’afa tace ”ai na hak’ura tunda har gashi zanyima albishir da sabuwar matar danayi ma , ehee?” waro ido mama tayi tace ”kajimun wulak’anci ni sa’ar wasanka ce ?to aure zakayi budurwa mai aihuwa Allah yasama aihuwar fari ta haifo mana y’an biyu , mama na maganar tana dariya , Haisam da zuciyarshi ke bugawa hankalinshi ya tashi ,ya dubi mama tare da had’e hanuwanshi biyu yace ”dan Allah dan girman Allah mama kiyi hak’uri ki janye maganar nan, shek’ewa da dariya mama tayi tace ”walahi sai kayi aure kaji na rantse ,bazaka zauna da juya ba kana cefane tanaci tana zuwa kashi , yanzu ma iskancin da kuka d’aukarwa kanku ,kundena cin abinci sai naman kaza ,ni gani a nan a bushe kukwa kunyi dumur mur , Haisam zaiyi magana mama ta dakatar dashi da cewa , nasan mezakace ,dan haka inason ayi bikin nanda wata biyu ai nasan jarin shagon yanzu ya bunk’asa da wacan juyar na aihuwa ai da yanzu ka kaini makka….✍️.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*Rashin sharhi zaisa ya komai na kud’i👌.
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 5 & 6

Sunkuyar da kai k’asa Haisam yayi yace ”ki k’ara hak’uri mama ,insha Allah Afnan zata haihu , banzan kallo ta watsa masa ,kana tace ”ubanwa kafi sanin tin tini ?”aure babu fashi na rantse da Allah kamar kayishi , cikin sanyin jiki Haisam ya mik’e tare da gyra hular kansa yace ”mama nabarki lafiya , ko kalonsa batayi ba , ya fice ,mashin d’insa ya hau kana ya nufi gidansa , samun k’ofar gidan a bud’e yasashi sanin , Afnan bata fito ba , to har yanzu 6acin ran ne , ya tambayi kansa , kulle k’ofar yayi yasa sak’ata kana ya nufi cikin gidan , yana shiga direct ya wuce parlorn da zai sadashi da ita , yana shiga parlorn ya ganta ,a kwance a kan 3 sitter idanunta , na kallon sama , d’ago mata kai yayi yace ”my sweetheart , inata sallama amma baki kulani ba ?”maida kalonta tai zuwa gareshi , da fararen idanunta masu rikitashi , batace komai ba , Haisam , daya shiga damuwa ganin 6acin rai k’arara a fuskar ,Afnan ya kuma janyota jikinta ya zauna a gefen ta ya d’orata a kan cinyarsa yace ”dan Allah kiyi hak’uri , tabbas abinda mama tafad’a bai dace , ba kinsan kuma mahaifiya dole nayi mata biyayya , Afnan ce ta shafo gefen kumatun Haisam ,tace ” abin alfahari na karka damu , nice nace ina sonka kuma har gobe bazan dena sonka ba , cikin farinciki ya had’e hannayensa biyu alamar godiya , ya rik’o hanunta ya mik’ar da ita , kana yace ”zo mushiga kitchen inkuma bazaki iya ba , ni barinje ko ruwan zafi in dafa miki.”

Hanunta ta rataya a kafa d’arshi suka nufi kitchen , indomie suka dafa da suka soya k’wai , kana suka juye a plet suka nufi parlor , zama tayi a kan kafet d’in da ya mamaye tsakiyar d’akin ,shima ya zauna kusa da ita , sai da suka gama ciyar da junansu , hira sukeyi ,cikin nishad’i kamar ba ita ta gama kuka ba , saboda faranta mata yasashi k’in fita aiki sunata gwada wa junansu soyayya , sauya salonsa yayi zuwa had’e bakinsu guri d’aya ganin hakan yasa nabasu guri , a duk lokacin da Haisam ya sami nutsuwa da Afnan , yana sanya mata albarka fiyeda tunani dan jinta yakeyi kamar sabuwar amarya , wanka sukayi a tare suna fitowa suka shafa mai mai k’amshi , Afnan ta sauya kaya zuwa doguwar riga milk color mai adon flawoyi , Haisam da yayi shigar k’ananun kaya shima yai kyau sosai , turare Afnan ta d’auko a gaban dress mirror ta fesa masa turare ,tace ”gaskiya my man kayi kyau sosai ,karfa y’an mata su kallemin kai , dariya Haisam yayi tare da rungumo Afnan yace ” tabb babu mai kallo na kedai ki kularmin da kanki , kiss ya manna mata a goshi tayi masa Allah ya tsare , yana fita ta sakawa k’ofar sak’ata ,ta koma bedroom d’inta tafara gyara gado , ta goge ledar d’akin tare da goge gadonta , kasancewar ta mace mara son k’azanta , komawa parlor tayi tafara sharewa ta goge ta goge TV , ta koma tsakar gida ta share takuma wankeshi fess , ta sa turaren wuta mai k’amshi , cikin k’an k’anin lokaci gidan yad’au k’amshi , tana shirin wanke _wanke , taji k’arar buga k’ofa , k’in tashi tayi dan tasan bazai wuce mama ba , kuma yau batada niyar k’unsar bak’in ciki , dan haka tacigaba da aikinta , cikin d’agun murya akace , Fatima ce fa ,da gudu Afnan taje ta bud’ewa Fatima k’ofa tareda k’yal k’yalewa da dariya suka shige parlor , zama sukayi ,Fatima tace ”matsoraciya ,kindawo ko magana babu ?”Afnan ce tace ”ke my man ne yabani tausayi , kuma nayi kewarshi so kinga dole in damu , cikin mamaki na soyayyar su Afnan Fatima tasa dariya kana tace ”masoyan asali , nima da Umar zai yarda da mundinga soyewa , suka kwashe da dariya , Afnan ce tace ”ban gane ba kina nufin ko irin shagwa6ar nan bakya yimasa ?”.

Fatima ce tace ”mutum sai kiga ya shigo gida babu fara’a ,to yazan yi masa?, gyara zama Afnan tayi kana tace” to yanzu dai ya kamata kisani ,kwaliya da tsafta itace ginshik’in komai , musamman in kika had’a da k’amshi , kuma sai abin yafi bada kala, agogo Afnan ta duba k’arfe hud’u na yamma , hakan yayi dai dai da shigowar ,wata budurwa mai jiki bak’a , kai tsaye ,d’akin dasu Afnan suke ta zarce, samunsu tayi itada Fatima suna hira,wani irin kallo tayi musu , budurwar tace ”wacece Afnan?” Afnan da gabanta yake fad’uwa ta kalli Fatima , Fatima ma ta kalle ta , tace ”to malama babu sallama babu gaisuwa ,sai nema?”girgiza budurwar tayi tace ”to ai ba ita ta kawoni ba dan haka matar gidan nakeson gani, Fatima da Afnan suka mik’e ,Afnan tace ”nice mai gidan ,mai kikeso ?”budurwar ce tace ”tunda naga mai gidan ai magana ,ta k’are , ta juya ta fice, mamaki ne ya kama su Fatima suna bak’in cikin dalilin da yasa basu nakad’a mata duka ba , amma babu komai ,Afnan tace ”idanunta cike da hawaye , Fatima da tsoron kar a yimusu duka yasata ,raku6ewa gefe , tana shan majina kamar wacce taci abinci mai yaji ,tace ”Afnan sai hak’uri.”

Haushi Fatima taba Afnan, wani mugun kallo tayi mata kana tace ”dama kamaki tayi ta sambad’eki , kekam anyi ma tsoraciya , tsoro yayi miki yawa , neman Fatima tayi ta rasa , komawa parlor tayi ta zauna a gefen hanun kujera , ta fara tunanin wanan budur war , to daga ina take ?” mik’ewa tayi dan tasan inta tsaya tunani ,har Haisam ya dawo batayi komai ba ,tsin tsiya ta d’auka ta kuma sharo ko ina na d’akin , dukda dai ba datti yayi ba , tasa turaren wuta , takuma fesa room freshner ad’akin , komawa toilet tayi ta wanke nata ,kana ta wanke na d’akin ,Haisam tana gamawa ta shige wanka, lokacin k’arfe 7pm tayi alwalah ,ta fito ,tanayin sallah ta zauna tsara kwaliya , dama tayi girkinta , mayukanta masu k’amshi ta shafa ,kana ta shafa powder ,tasa janbaki da gazal ta sanya kwali , tayi kyau sosai, mini skirt d’inta da ya tsaya mata iya gwuiwa tasa ,mai kalar pink sai farar riga , fara mai yan kaken hannu iya cibiya , ta kama kanta da yake a tsefe da abin kama gashi ,ta sanya pink d’in hula ,a gaban hular an rubuta my baby .”

K’ara feshe jikinta tayi da had’a d’un humra masu tada hankali ,ta zauna jiran , kiran sallahr isha’i , bayan wasu mintuna ,tajiyo kiran sallah ,hakan yasa ta mik’ewa , ta fara gabatar da sallaha , tana idarwa ta fara salatin annabi tare da kwararo adu’oi na bud’i dakuma k’arin soyayya a gurin mijinta , bayan ta kammalah ,ta nad’e abin sallar, ta d’auko wayarta dake jone a charge ,ta fara duba number Haisam ,cikin sa’a ta shiga , yana d’auka kafin tayi magana carab ,yace ”gimbiya yakk ya gida ?dafatan dai babu wata matsala ko ?”rage sautin muryarta ,tayi kana tace ”uhm ni ka barni sai kewar kallon fuskarka nakeyi ,yasan dole sai an lalla6a ta ,dan haka yace ”to ayimin hak’uri gani nan insha Allah yanzu .”
Dariya tayi ,tace ”fatan alkairi mijina Allah ya dawo min dakai lafiya , amen yace ”ki kulamin da kanki, I love you , kashe ido d’aya tayi kamar yana ganin ta tace ”love yau 2, kallo ta kuna ,a tashar MBC 2 wani film da suka sa ne a ja hankalinta , har k’arfe ,tara a rabi, jin k’arar mashin d’in Haisam ya sata mik’ewa, ta 6oye a jikin labule , sallama yakeyi shiru , baiji anyi magana ba ,my baby ina kika shigane ?”da gudu ta rungume shi tana ,oyoyo mijina , d’a gata sama yayi ya mai data bayan sa ,yana juyi da ita kamar yarinya, rad’a masa tayi a kunne “zomuje muyi wanka, shima cikin rad’a yace ”ba yanzu ba , sauka tayi a bayan nasa, taje bayi ta d’auko bucket ,ta zuba masa ruwan tare da sirkawa, tana shiga ta ganshi zaune da alamun damuwa , zama tayi kusa dashi tace ”mijina lafiya kuwa naganka haka?” babu komai yace ”ya kalle ta ,komai nata birgeshi yakeyi ,amma mama zatace ya k’aro aure ,gaskiya shikam ba ‘ayi masa adalci ba ,Afnan ta lura akwai abinda ke damun mijinta dan haka ,ta mik’ar dashi ,tare da cire masa ma6allin rigarsa , jikinshi yayi sanyi matuk’a ,tunda ya tuno da hukuncin da mama ta keson yankewa.”

Haka dai jikin nasa babu k’wari ta temaka masa yayi wanka, yana fitowa ta fito masa da kayansa , ya Sanya , marasa nauyi , zubo masa macaroni tayi a plet , wace taji kayan k’amshi da albasa, sanin baya cikin han kalinshi ya sata d’aukan cokali tafara bashi a baki , ci yakeyi kamar mara lafiya , hakan sam bai yiwa , Afnan dad’i ba, cikin zuciyar ta tace ”zan bishi a hankali insha Allah zai fad’amin koma menene ,ganin har yanzu yak’i sakin jikinsa yasata ,fashewa da kuka , kasancewar ta mai saurin kuka , kallonta yayi cikin tashin hankali ,yace ”mai kuma ya faru”mik’ewa tayi ta shige bedroom ,ko kulasa batayi ba , damuyoyi biyu kenan , Haisam ya ce lokacin da ya mik’e zuwa bawa Afnan hak’uri , ranta ya 6aci matuk’a saboda a rayuwarta bata son tayiwa mutum magana ya shareta , shikam Haisam oga ne ,bakin gado ya zauna tare da janyota jikinsa yana shafa gashin kanta , k’arfin hali kawai, ya keyi, amma ba dan zuciyarsa na yimasa dad’i ba, shuru tayi kamar ba ita keyin kukan ba , ta d’ago ido tana kallon sa ,murmishin dole ya k’ir k’iro , hakan yasa ta maida masa da murmishin , haka dai ya samu ya lalla6a ta har bacci mai nauyi yayi nasarar d’aukarta, gyara mata kwanciya yayi tare da lulu6eta kasancewar ,garin ana sanyi , ya mik’e a hankali ya ,koma bedroom d’insa , zagaye d’akin ya shiga yi yana mai k’ara tuno kudirin maman nashi , tausayawa Afnan yakeyi ,ya koma ya kwanta ,bacci 6arawo ya kwashe shi ,k’arfe kiran sallahr farko a kunnen sa , hakan yasa shi yin adu’ar tashi daga bacci ya shiga toilet ya d’auro alwalah , sai da yayi nafil fili sanan ya ,tafi d’akin Afnan , ya kwanta gefenta yana shafa fuskarta ,tare da hura mata iska ,bud’e ido tayi ta sakar masa murmishi ,shima hakan yayi mata ,yace ”lokaci yayi nisa kitashi kiyi sallah.”

To tace ”masa ganin zai tafi ne tace ”Allah ya dawo min dakai lafiya mijina , amen ya Allah my honey, cewar Haisam lokacin da yake shirin sa takalmi,kasancewar yana dad’ewa a masallaci , yasata kunna risho ta d’ora ruwan zafi ta dawo tayi alwala ,tayi sallah tana idarwa ,bayan tayi adu’oin ta , da ta saba , ta mik’e ta fara da gyra gado ta tsaftace ko ina tasa turaren wuta mai k’amshi , juye ruwan wankan tayi , ta shige toilet tayi wanka, tana fitowa ta koma kitchen ,ta juye wanda ta mayar , jin shigowar Haisam , tayi yana shigowa parlor ta durk’usa tace ”barka da safiya my man , da fara’arsa yace ”gimbiya ta kintashi lpy , lafiya Lou tace ”ruwan wanka ya kammalu yana toilet , okay Haisam yace ”please zamuje ki tayani cire kaya, mik’ewa sukayi rik’e da hanun juna , suna gama cire kayan, ya shiga wanka ita kuma ta fara kwaliya bayan ta d’ora shayi a kitchen, riga da zani ta sa na atamfa mai ratsin green da fari sai d’ingon bak’i a gefe , tayi kyau sosai ,d’akinsa ya wuce sai da ya gama shiryawa , sanan ya fito sanye da k’ananun kaya , sun amshi jikinsa kasan cewa shi fari dogo kya kyawa ,wow mijina wanan kyau haka?” dariya yayi yace ”kai matar Haisam wanan kashe kala haka , kamar zamuje , rufe masa baki tayi tace ”na gama tea madara da sauran su zan sa ,so me za’a dafa indomie ko doya da k’wai , kawai kiyi indomie and egg zai fi sauri , ficewa Afnan tayi ta fara hidimar girki , misalin k’arfe 9am ta kammala komai ta jerasu a tebur da cokula da cup , suna karyawa suna hira , Haisam ne ya mik’e tare da cewa ni zan tafi , ki kularmin da kanki , Allah ya tsare Allah ya bada sa’a , amen Haisam yace bayan ya bata kud’in cefane ya fice , kwashe kwanukan da suka gama breakfast tayi ,kana ta wanke su ta dawo ,ta kunna kallo ,misalin k’arfe uku na rana , taji alamar bugun k’ofa , mik’e wa tayi ,dan bacci ma takeyi sbda tana fashin sallah , k’arasawa tayi , bakin k’ofar , ganin k’anwarta Salma yasata fad’ad’a fara’ar ta .”

“Tace my sis barka da zuwa , d’aukan yaron tayi mai suna Sudais suka k’arasa parlor, suna zama Salma ta ,yamutsa fuska, kana tace ”yanzu sis wanan rayuwar da kika za6awa kanki yayi kenan, kin zauna gidan talaka yana baki wuya , jibi inda kika rame , murmishi Afnan tayi , lokacin da ta mik’e ,zatayi kitchen batace komai ba, ruwa ta d’ibo wa Salma a jug kana ta had’o mata da abinci da tagama yanzu , taliya ce ,mai da yaji , kuma ke6e baki tayi tace ”ta6 Allah ya kyauta sis yanzu abinda kikeci kenan?” juyowa Afnan tayi tace ”mai yasa kika biyoni ,kitchen ?”kinzo ki kuma 6atamin rai ko just ki forgetting komai ,but ya wuce ,komai Allah ne mai yi kuma komai kikaga bawansa dashi , bawai baya sonsa bane .✍️.

Kuyi hakuri nayi tafiya ne wlh ba lallai gobe kusami update ba , ku fahimceni biki mukeyi, masu sharhi naga sharhinku Allah nagode🙏.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*zai koma na kud’i tunda kuna karantawa amma bakwa sharhi*

*karku manta wlh zan dena post a Watsapp zan koma wattpad yafimin* 👌👌

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 7 & 8

Fad’in haka yasa Salma shiru da bakinta , tana gama shan ruwan ta mik’e tace ”sis mukam zamu wuce ,ga wanan kya rage wani abu, no bana so , Afnan tace ”lokacin da ta kamo hanun Sudais tana shirin yin hnyar waje , tsaki Salma taja kana tace ”wlh tunda kikace auran talaka ,hmm ina tausaya miki ko dady , yanzu baya ambaton sunanki , Afnan ce tayi dariyar yak’e wace tafi kuka ciwo ,tace ”ina da Allah tunda kowa na gudu na please in wucewa zakiyi ki fice, karki k’aramin ciwon kai , okay don’t worry , nice ma nazo inda kike ,tunda ke ba neman mu kikeyi ba ,wani wawan mari ,Afnan ta wanka wa Salma , Kana tace ”ficemin a gida ,bana neman temakon ku bance kowa ya temaka min ba , rik’e da kumatu , Salma ta fizge hanun Sudais a na Afnan suka wuce a zuciye , komawa kan kujera Afnan tayi ,rik’e da kanta , cikin damuwa da 6acin rai ta sa kuka mai tsuma zuciya , innalilahi wa inna’ilaihir raji’un ta ambata cikin muryar kuka , ya Allah kayimin magananin matsala ta , tun farkon aure na banida kwanciyar hankali , oh Allah ka duba lamurana, ta kwanta tana kuka ,Fatima ce ta shigo ,hanunta rik’e da wani abu a gora kamar zuma , da sallama ta shiga gidan Afnan tace ”matar Haisam na kawo miki wani sirri na musamman , da jajanyen idanunta Afnan ta dubi Salma, tace ”wa’alaikumus salam , tsoro ne ya kama Fatima tace ”yau kuma maiya faru ?”Afnan ce tace ”dan Allah ki tayani da adu’a Fatima ,insha Allah barinje gida cewar Fatima , Afnan ce tace ”mai kika kawo , a’a kibari zuwa gobe mayi magana ,to Afnan tace Fatima ta wuce gida.”

Dare nayi ta yi abubuwan da tasaba , shigowar Haisam misalin k’arfe 8pm yau ya dawo da wuri , jiki a sanyaye ta mik’e tayi masa oyoyo , ganin yau babu fara’a dakuma barkwancin da tasaba yi masa yasa shi ,k’are mata kallo ,rungumo ta yayi yana murza hanunta da ya rik’e gam , rurin da wayar sa keyi ne yasa shi sakinta , d’aga wayar yayi tare da sallama , jin muryar mama yasa shi k’ara matsawa nesa da Afnan dan yasan labarin gizo baya wuce na k’ok’i , jiyo muryar mama yayi tana cewa ,wlh inhar baka zo yanzu ba to wlh sai nayi mumunan 6ata maka rai , juyawa yayi yaga Afnan bata gurin ,ya rage muryarsa yace ”mama ganinan zuwa, karma kazo wlh zaka gane ta kashe wayar , k’ara sawa bedroom d’in Afnan yayi ,gajinta a zaune tana gyara powder fuskarta yasa shi , sakin fara’a yace ”my lovely barinje in dawo mekikeso ,in taho miki dashi¿” dariya tasa wace kamar ta dole ce tace ”dabino da kwakwa , to karki damu , cikin rawar jiki ya fice, ƙofar gida ya fita ya tada mashin ɗinsa ,kai tsaye gidansu ya nufa ,sallama yayi kana ya shige ɗakin mamanshi ,samunta yayi a zaune tana jijiga ƙafa, yana shiga ta miƙe ,cike da ɓacin rai tace “wato Haisam ban isa in gaya maka magana ba?” yanzu ƙarfe nawa? duba agogo ka gani ,Haisam ne ya kalli agogon hanunsa yace “ƙarfe goma ,to mekake nufi da maganar da muka yi dakai?” Haisam ne yace “kiyi haƙuri mama zanbi umarninki amma kibari zanyi shawara, shawarar banza cewar mama ,to wlh tun wuri kabi umarni na kokuwa na tsi…. innalilahi ya ALLAH mama ki gafarceni karkiyimin baki ,na yarda zanyi auran ,ywwa Allah yai maka albarka , nariga na gama magana hira zaka fara zuwa , kuma daga yau , a kid’ime ta kalli mama da keta washe hak’ora , dubu d’aya ya mik’a mata kana yasa Kai zai fice , dakatar dashi mama tayi , tace ”to yanzu bari a kirata a waya inyaso sai kaje ko?” shiru yayi bai ce komai ba , mama ce ta ciro wayarta a lalita ta mik’awa ,Haisam kana tace ”lalubo min lambar , Maimuna ,yana dubawa yaga number danna kira yayi ya mik’awa mama, hararar shi mama tayi tace ”nice mai zuwa zancen?” zaka fara nunamin halin naka ko?”cikin ladabi ya k’ar6i wayar , sallama tayi ,jiyayi ance “baby takake yakuma gajiyar aiki ?” muryar Haisam babu alamun fara’a yace ”zankira ki gobe , okay I love you , yana kashe wayar ya mik’awa mama.”

Cikin fara’a mama tace ”to d’an albarka baka d’auki number ,Maimunatun ba , sbda gudun fad’an mama yasashi , kar6ar wayar ,ya d’auki number ya fice , 6angaren maimunatu kuwa murna cike da zuciyarta ta buga tsalle kana tace ”wanan gayen da alamu kyakyawa ne , zanso ganinsa , tayiwa wayar kiss ,sai k’arfe 11pm Haisam ya koma gida ,Afnan mai saurin kuka , taci kukanta ta gaji hartayi bacci , yana shigowa tare da mashin d’ainsa ya kulle gidan , ya jingine mashin d’in ,k’arasawa yayi ,bedroom d’in Afnan , samunta yayi tayi bacci ,haska fuskarta yai da fitilar wayarsa kasan cewar babu wutar nepa , ganin hawaye bushe a fuskarta , yasashi cewa Allah sarki baiwar Allah , ya koma d’akinsa yai alwalah ya kwanta, tunnin yarinyar ne keyi masa yawo a brain d’insa , tabbas yasan inhar Afnan tasan labarin nan to kashinsa ya bushe , dan wlh zata iya barinsa , yasan Afnan ba ajinsa bace , mahaifinta nada dukiya taban mamaki amma ta za6e shi, to wai shin ita haihuwar nan ba ta Allah bace ?” ganin yana shirin yin sa6o ne ya sashi yin shiru , yayi adu’a bacci mai nauyi ya kwashesa , washe gari antashi da sanyi sosai ,bayan sunyi sallahr asbha Afnan ta koma d’akin Haisam baccin safe , bacci mai nauyi yai awon gaba dasu ba su suka farka ba sai misalin k’arfe goma Na safe , Afnan ce ta fara bud’e ido ta zare jikinta a na Haisam , gyara gidan tayi ta koma d’ora abin karyawa , tana gamawa ta shige wanka , jera kayan shayin tayi a kan tebur , kana ta nufi d’akin Haisam , tana shirin tashin sa raji ya fara salati , kwantowa tayi kan cinyarsa tace ”barka da safiya , ruwan wanka ya kammala , okay to tayani cire kayan.”

Tayashi tayi suka shige toilet yai wanka , yana fitowa ta taimaka masa ya shafa mai ,ta ciro masa kaya ya sanya shadda ce green taji aiki ,inka ganshi kamar sabon ango sai wani shek’i yake zubawa , bayan sungama breakfast ,ya dubeta cikin tausayawa zai yimata magana ya fasa , Afnan ta lura da yanayin sa , tace ”akwai magana a bakinka ko ?”gayamin mai ya faru? Haisam ne ya marai raice ,fuskar kamar mai shirin kuka yace ” lovely mama ce …mama tace me ?”inajinka , shiru Haisam yayi kana yace ”aure takeson in k’ara , a razane Afnan ta mik’e lokaci d’aya hawaye suka cika mata ido ,ta dubi Haisam da kansa yake k’asa , yak’i had’a ido da ita , hmm kawai Afnan tace ”ta shige bedroom , ta janyo akwatinta , wanda ta d’ibi kayanta na kwanaki da tayi yaji, shirin sa hijab takeyi Haisam ya sha gabanta , yace ”dan Allah ki saurare ni kiyi hak’uri , a fad’ace ta dubeshi tace ”a halin yanzu bana k’aunar jin sautin muryar ka kabani guri intafi gidan iyayena , ada bana tunanin tafiya gidan mu yau kam wlh bazan kwana anan gidan ba , kuka takeyi mai ban tausayi , ta juyo da jajayen idanunta tace ”ada in ana yimin gori nakanji haushi , wai yau bakinka ne ke gayamin maganar aure,? kai da kanka kamar a mafarki.”

Haisam yayi magiyar duniya Afnan tak’i yarda ta zauna , komawa bakin k’ofa yayi da gudu ya tare yana kallonta , amma nace dai karki fita ko?”idanunta da suka rufe tace ”koma me zakace kace dan wlh nikam nagaji da gorin da ake yimin , ta k’arashe maganar da share hawayen da suka kwaranyo mata , kasancewar ta doguwa kuma mai k’arfin jiki , ta shammaci Haisam ta turashi gefe , taja akwatinta ta fice , tsabar 6acin rai hartazo bakin titi bata lura ba , sbda tsakaninsu da d’an tafiya ,mai mashin ta tare tace ”ya kaita unguwar su , d’ora akwatin tayi itama ta hau suka d’auki hanya , suna isa gidan ta bud’e jakar hanunta ta mik’a masa kud’insa , kasa shiga gidan tayi dan rabonta da gidanan zatakai wata shida , tunda ta ta6a kawo k’ara mutanen gidan suka koreta kamar ba gidan su ba , cikin sanyin jiki taja akwatinta , ta bud’e get d’in ta shige , jikinta ne yakuma sanyi sbda tana tunanin abinda zata je ta tarar, bud’e k’ofar da zata sadata da d’akin mahaifiyar tata tayi , ganin babu ,yasata samun guri ta zauna ,jin alamun shigowar mutum yasata dai daita nutsuwar ta , mezan gani? nace mezan gani? uban me kikazo yimin da akwati?” cikin kuka Afnan ta gangaro daga kan kujerar da take zaune tace “mama ki yafemin dan Allah ,Haisam ne zai ƙara aure…aure?!!cewar momy ,da kyau kinga irin abinda muke jiye miki ko? dady ne ya shigo yana cewa”menakeji kamar hayaniya , hango Afnan yayi durƙushe a ƙasa yace “mekikazo yi ?bakin canza iyaye bane ? dady wlh ba haka bane kuyi hak’uri , momy ce tace ”wai aure mijin zai k’ara shine tazo , dady ne yace ” to ta tattara ta koma ai mijin ta za6a akan mu to taje ta rik’e mijin , suna tsaye a kanta suna zazzaga mata masifa .”

Dama tasan za’ayi haka , amma zata jure koma menene da zai faru , ficewa dady yayi ba tare da yace ”komai ba , momy ce ta zauna a gefen kujera tace ”in har kinason farinciki na to wlh sai dai kibar auran wanan munafikin dan bamu gaji tsiya ba , har meyaci dazai wulak’antaki , cikin sha shek’ar kuka tace ”momy bazan iya rayuwa babu Haisam ba , mari momy ta wanka mata tace ”uwar wa kike gayawa haka , to keda Haisam kunyi hanun riga ,inhar inada rai da lafiya to babu ke babu d’an talakawa ,momy ta k’arashe maganar ,tana nunata da yatsa , kuka Afnan ta saki tare da kwantar da kanta a kujerar dake gefenta , mom na fita direct d’akin Anty tayi anty na ninke kaya ta zauna gefen gadonta , cikin 6acin rai tace ”yarinyar ki ta dawo wai mijin zai k’ara aure , ehee aure kuma? cewar anty me ya tara dahar yake tunanin k’aro aure? ” mu dama ba son auranan mukeyi ba ,kawai ta zauna Allah ya fito mata da wani dan wlh wanan yaron ba kalar Afnan bane, momy ce tace ”ganemin dai ,ana haka suka jiyo sallamar Anty ummi ta shigo , nanfa hira ta kaure , suka fara bata labarin Afnan ta dawo gida , cikin rashin jin dad’in maganar tasu tace ”wai maiyasa kuke haka ne ? bakwa tunanin mai kud’i da talaka duka Allah ne ya yisu ? kuma akwai lokacin da Allah zai azurta talakan , momy ce ta dubi Anty ummi tace ”duk da haka dai , girgiza kai Anty ummi tayi dan tasan basajin kira sunyi nisa , anty dake gefe tana yiwa Anty ummi kallon wulak’anci ta juya kai gefe..✍️.

Nayi tafiya ne bazaku dinga samun update kullum ba so yanzu dai sharhi da comments nake so .👌

Vote and follow me on wattpad👍.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_

EPISODE 9 & 10

Washe gari , mama tayi sammako da sassafe lokacin k’arfe bakwai 7am bubuga k’ofar gidan su Haisam tafara cikin gaggawa , Haisam daya farka daga baccin asbha ya mik’e yana mik’a ya isa bakin k’ofar ya bud’e , ganin mama yasashi d’an durk’usawa yace ”barka mama sannu da zuwa ,yawwa kawai tace ”ta ra6a ta gefensa ta wuce ,ganin gidan ba inda tasaba gani ba ,yasata cewa “ina matar gidan?” sosa kansa yayi kana yace ”ta tafi anguwa , bud’ar bakin mama tace ”Allah yasa intaje karta dawo , shidai Haisam burinsa yaga fitar mama lafiya , ganin ba shirin fita takeyi ba yasashi ,jingina da bango , mama ce ta dubeshi tace ”insha Allah nanda sati biyar ka zamo ango da yardar Allah zaku shekare da jariri , Allah yasa kawai Haisam yace ”dan bashida amsar da zai bata , juyawa tayi zata fice ta juyo tace ”to yakamata kaje gurin yarinyar ku fahimci juna ko ?”to Haisam yace ”da alamun k’aguwa a fuskarsa , mancewa tayi da sallamar ma ta fice , Alhmdulh Haisam yace ”ya koma d’aki yana cewa “dame zanji ga Afnan bata gida ga mama tazo min da wani batu , gaskiya bansan ina zan sa rayuwata ba.”

Yau kwananta biyu a gidan su hakan ya yiwa dady dad’i kasancewar yafi son yaga duk zuri’arsa sun auri mai kud’i , zaune suke da rana kowa da farfesu a gabanshi , Afnan wayace a hanunta , ta gwada number Haisam shiru tak’i shiga , hakan yasata shiga damuwa tace ”wayo Allah , hankalin kowa na parlorn ya dawo kanta , momy ce tace ”to mai yafaru kuma?”sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”babu komai , dady ne yace ”yanzu so nakeyi wanan yaron yazo ya baki takardar ki kinga zaki fara sabuwar rayuwa ko , uhm kawai Afnan tace ”kana ta maida hankali ga abinda take ci ta ajiye wayar a gefe , suna kammala ciye ciyensu mai aiki ta kwashe kayan ta kai kitchen , Afnan ce ta mik’e ta nufi d’akinta na da lokacin tana budurwa , fad’awa makeken gadonta tayi wanda fentin jikinsa pink ne ,kifa kanta tayi a fillo tafara rera kuka , tana dana sanin fitowa daga gidan mijinta mai yasa tayi haka ?”anya tayiwa rayuwarta adlaci kuwa? kodai zata gudu ne ?”wata zuciyar ce tace ”inhar kika gudu to zaki janyowa kanki mumunan hukunci gurin dady da Anty Bilki.”

Mama na komawa gida ta fasa asusunta ,kud’i ta k’irga sunkai dubu ashirin ,kuma duk a kud’in da Haisam yake bata ne take tarawa , gud’a ta rangad’a wanda hakan yai sanadiyar juyo da hankalin mata gidan , tanajin alamun tafiya ta danne kud’in a k’asan cinyarta tace ”kowa ya watse ba komai nake ciba , duniyar ce ta yimin dad’i , komawa sukayi dan suna ,tunanin fad’a irinna mama , suna komawa ta janyo kud’in ,ta gyarasu tasa a lalita , ficewa tayi gidan wata dilaliya dake kusa dasu , tana sai da kayan d’aki da bokitaye da sauransu na amfani , sababbi da tsofafi , da sallama mama ta shiga , gidan samun dillaliya tayi a zaune tana k’arga kud’i , cikin fara’a d’ajin sallamar mama yasata , gyara zama tace ”barka da zuwa , ywwa mama tace ”inason kayan sa lalle bokiti ta kofin silba da kwano shima na silba , magajiya ce tace ”angama kud’inki dubu biyar , cikin rawar jiki mama ta mik’awa dilaliya kud’in aka had’a mata , cewa tayi sai zuwa dare zatazo ta d’aika dan munafukai sunyi yawa .”
Tafawa sukayi kana mama ta fice , bayan isha’i mama ta yafo gyale tayi ,hanyar gidan su magajiya , samun kayan tayi a gefe a baranda ta ajiye mata , dajin sallamar mama yasa magajiya fitowa ta nunawa mama kayan , d’auka tayi ta fice kai tsaye gidan su ta nufa , sai da ta lek’a babu kowa a tsakar gidan sanan ta wuce , washe gari ta shiga kasuwa ta siyo kayan buk’ata , tana dawowa baba yake tambayarta ina taje. ”

Maganar auran Haisam tayi masa , dayake shima kamar ta gama dashi yasashi yin shiru, wata k’anwarta ta kirawo suka shirya kayansu , number Haisam ta kira , cikin sa’a ya d’aga maza maza kazo mama tace ”masa cikin sauri yace ”ganinan zuwa , ba a d’au lokaci mai tsayi ba Haisam ya k’araso gidan , da sallama ya shiga ganin mahaifiyarsa da k’anwarta yasashi durk’usawa ya gaishe su , amsawa sukayi cikin fara’a , k’anwar mama ce ta dubi Haisam tace ”ya maganar kai sadaki , zaiyi magana mama tace ”wlh mudin kaimin wata maganar da bata shafi na Maimunatu ba sai na sa6a maka , cikin sanyin jiki Haisam yace ”sati mai zuwa zan bada akai nawa sukace ?”mama ce tace ”basu yanke ba amma zan kuma tura manya , okay kawai Haisam yace ”kana ya mik’e ya fita.”

Bayan ya mik’a musu d’ari biyar biyar yayi gaba, albarka suka shiga sanya masa , shiko yayi gaba , tundaga wanan rana Haisam ya zamo bashida walwala , yana tunanin zuwa gidansu Afnan yana tsoro saboda ra’ayinsu ta rik’a k’a , da komawarsa gida yai wanka ya janyo filon Afnan ya rungume yanajin kewar matarshi , cikin sanyin jiki ya janyo wayarsa , yafara lalubar number Afnan , cikin rashin sa’a yaji a kashe , tsaki yayi ya maida kansa ya kwanta yana tunani da ban daban , oh god wai maiyasa Afnan zatayimin haka ?”in anyi magana tace tana sona to wai shin haka so yake?” mik’ewa yayi ya nufi toilet d’in d’akin Afnan d’in , cikin sanyin jiki , alwalah yayi ya tada sallah lokacin anayin isha’i , nafila yayi ya kai kukansa ga rabil izati, ya dawo yakuma gwada number Afnan , cikin sa’a ta shiga , wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarsa lokacin da yaji sautin muryar ta ta doki dodon kunensa , lumshe ido yayi , yana saurarar sallamar ta , hak’ik’a yayi kewar matarsa sai dai a halin yanzu yana ganin kamar bazata dawo gareshi ba, jin shiru yasa Afnan cewa my honey kayi shiru kuma lpy ? Haisam ne yace ”inafa lafiya kina gani tunaninki yana neman sani cikin uquba wlh karki d’auki hak’k’ina , kinsan dai ban baki izinin tafiya ba ko?”

A halin yanzu bazan iya jure rashinki ba a kusa dani, walh kin horani , wane laifi nayi miki dahar kike k’ok’arin azbtar dani , kalaman mijinta suna shigarta a hankali , k’ara rungumo filon da take zaune a kujera tayi kana tai rau rau da idanu tace ”zan dawo mijina dan Allah karka yi fushi dani zan dawo, k’ara sa sauta murya Haisam yayi yace ”to yaushe zaki dawo inyi miki tanadi na musamman , murmishin yak’e tayi tace ”zan dawo surprise zan yimaka , okay to Allah ya dawomin dake lafiya , suka ajiye wayar , momy dake tsaye a kanta tace ”keda mara zuciyar nan kuke waya ko ?”to babu maganar komawarki gidansa ,karma in k’araji , wlh zan sa6a miki , sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”momy kiyi hak’uri dan Allah bazan sake ba , wucewa momy tayi batare da tabi ta kanta ba , washe gari Haisam ya gyara gida ya wanke ya sa turaren wuta ya gyara gado ya wanke toilet yanata farinciki, komai cikin zumid’i yakeyi , yana gama gyare gyaren , ya shige wanka yana fitowa ya shafe jikinshi da turaruka masu k’amshi ya ciro dakakkiyar shaddar sa mai kalar ruwan toka yasa yakuma feshe jikisa da turaruka, d’aga kansa yayi k’arfe sha d’aya na rana 11am k’ara gwada number Afnan yayi , jin shiru tak’i shiga yasa shi doka tagumi .”

********************
Bayan sati d’aya , Afnan ta rame sosai momy da dady sun kuma matsa mata akan bazata koma gidan Haisam ba , Haisam tayi kira a waya shiru , tun tana shiga ba’a d’agawa har yazo a kashe ,damuwa sosai ya shiga gashi safiyar yau mama ta matsa masa akan kud’in auran da yayi alk’awari, ba shiri ya tattara ragowar kud’insa na bank ya nufi gidan su mama , tana ganinshi tahau washe baki Haisam kansa na sunkuye ya wuce d’akin maman itama shigowa tayi tare da janyo bokiti ta mik’a gabansa ta zauna , Haisam ne yace ”mama wanan kayan fa?”washe hak’ora mama tayi tace ”wato da tsumun mu muke tare , jingina kai Haisam yayi batare da yakuma magana ba , ciro kud’i yayi yana juyasu ya ajiyesu a gaban mama , wani irin farinciki ne ya lulu6e mama , tace ”d’an albarka Allah yasa wanan auran kayi a sa’a , abin mamaki da ya dami Haisam shine mama bata ta6a kiran sunan Afnan kokuma cigiyarta , sai ta batun sabon aure take, maganar da mama tayi ne ya sashi dawowa daga duniyar tunani Haisamu kud’in nawa ne , kansa a sunkuye yace ”dubu d’ari ne farinciki fal zuciyarta tace ”Allah yai maka albarka ,amen Haisam yace ”kana ya mik’e yace ”to mama zan tafi , zaro ido tayi tace ”wato ni yanzu nazamo abokiyar jin kunyarka ko ?”
Ran Haisam babu dad’i yasa kai ya fice .

Anty Aishe ce keta doka sallama a parlorn Alhaji, amsawa yayi tare da cewa “Anty kishigo mana , shigowa tayi tana dad’a k’arewa Alhajin kallo , murmushin mugunta tayi dan tanada labarin Afnan ta dawo gida , shine tazo tayi ziga , Alhaji barka da hutawa ,yawwa Anty kinzo lafiya , lafiya lau Anty tace ” sai kuma naji wai wanan yarinya ta dawo gida?” uhm kedai bari Anty wlh abin yayimin ciwo dan rainin wayo ma aure zai k’ara , to bama batun auran ba ,mai yaci bare ya basu da har zai tattago wa kansa aure ?”nisawa Anty tayi kana tace ”to albishirinka yanzu daga kusada gidansu nake dan in tambayi halin da Afnan d’in take ciki , ashe kusan kullum sai uwar mijin tazo tayi mata duka , kuma tace ”sai ta wanke mata kaya🤭anty ta shararo k’arya …. cikin tunzura Alhaji yace ”dama wanan wahalar takesha shine ta zauna ?so takeyi ya kasheta ya huta ko.”
Gyara zama Anty tayi tace ”koni ba son auranan nakeyi ba kai ka biyewa dangin uwarta dahar sukaci galaba akanka , ran Alhaji ya 6aci sosai ,yanzu kam ya yards da maganar Anty Aisha tabbas laifin momy ne aikuwa babu ita babu auran Haisam, dama ni ba son yarana sudinga shan wahala nakeyi ba , jeki kiramin Wasila 🤔dan k’ari tau babu batun cewa momy , Anty Aisha ce ta dubi Alhaji tace ”gaskiya bazanje ba karma ka kirata yanzu dan wlh zataga kamar nice na zugaka ka cimata mutunci , eh hakane .✍️

Follow me and vote on wattpad.

Dalilin k’inyin post d’ina shine kuna karantawa bakwa sharhi👌

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

My Facebook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 11 & 12

Anty na shirin mik’ewa tace ” yanzu ma anguwa zan zarce daga nan , ganin Alhaji na laluba aljihunsa yasata murmusawa , dubu uku ya mik’a mata tare da fatan Allah ya tsare , godiya tashiga kwararo masa ta mik’e ta fice , batason su had’u da kowa hakan yasata ficewa a ankare batare da sunyi ido biyu da matan gidan ba , fitarta keda wuya sai ga Anty ta shigo da sallama ,amsa sallamar yayi yana k’are mata kallo , to yau kuma yarintar ce ta motsa ?”matsowa kusa da Alhaji tayi tana mai kai cinyarta kan k’afarsa , tofa 🤨 Alhaji da zancen yafara sakin layi yace ”tashi muje ciki kinsan gidan baya rabo da bak’i , mik’ewa sukayi tare da turani waje suka rufo k’ofar , dare nayi yau Alhaji zai koma d’akin momyn Afnan , tun k’arfe hud’u na yamma tasa ake yimata gyare gyare , duba agogo tayi k’arfe biyar , toilet ta shige ta had’a ruwan wanka wanda yaji turaruka na musamman , tana fitowa tasa turaren wuta dana tsuguno ,kasancewar ta y’ar mai duguri bata wasa da gyaran jikinta bare ma matan gidan kowace tana k’ok’arin gyara kanta ,tana gamawa ta mulke jikinta da mayuka masu d’aukar hankali , wani mai ta tsiyayo ta shafe gashinta dashi ta zauna kan stool d’in dake gaban dress mirror tafara tsara kwaliya kasancewar lokacin ana kiran magrib tariga tayi alwalah , Afnan ce ta shigo da sanyin jiki ta dubi momy ,ta kawar da kai momy ko kallonta batayi ba ,ta mik’e ta d’auko cup da spoon ta dawo ta zauna magani ta d’auko a leda ta bud’e fridge ta d’auko nono mai sanyi ta dama , ganin zata sha yasa Afnan cewa “momy ina nawa , momy kallonta takeyi cikin tuhuma can kuma tace ”a lokacin da kika auri wanda zuciyata da hankali na sukeso to lokacinne zaki dinga ganin gata iri iri so yanzu kibi umarni na kiji dad’i a rayuwarki, sunkuyar da kai Afnan tayi tace ” momy yanzu duk akan auran Haisam ne dukanku kuka tsaneni ?” no Afnan ba tsanarki mukayi ba somukeyi ki gane ban bancin dake tsakanin talaka dakuma mai kud’i , Allah ya horewa mahaifinki company da dama ga dukiya mai yawa amma ace kin k’are ke y’ata ta cikina kin k’are a talaka futuk wanda in yayi kwana d’aya tak bai fita ba zakushiga damuwa.”

Afnan dai tasaba da irin wanan fad’an yasata jan bakinta tayi shiru ,ta zubawa momy ido wani fitinanen leshi ta ciro a drowa mai kalar pink da adon black stone anyi mata d’inkin riga da zani rigar iya guwaiwa mai breastcot tai kyau sosai kasancewar ta mace mai dirin jiki sbda irin jikinta Afnan tayi , war waro ta sa kana taciro tsadajiyar sark’arta ta sanya ni dai gani nayi momy ta koma kamar yarinya , kamar ba ita ta haifi Salma da Afnan ba ,momy na gama kintsawa takuma feshe jikinta da humra ,itadai Afnan a halin yanzu kewar mijinta takeyi sosai ,sallamar dady ce tasasu kai duban su gareshi da alamun fad’a yashigo amma ganin momy tasha kwaliya yasashi sa sauta murya ya kalli Afnan ganin bashi take kalli ba yas shi kashewa momy ido kana yace ”in kin kammala ina jiranki a d’akina zamuyi magana Afnan ta lura da kallon da dady ya ke aikawa momy hakan yasata mik’ewa tayi bedroom d’in ta ta fad’a gado, tana tuno soyayyarsu da Haisam tabbas ta tafka uban kuskure dahar ta biyewa son zuciyarta yanzu gashinan daga dadyn har momy babu mai damuwa da damuwarta yau satinta biyu , tinda tacewa Haisam washe gari zatazo har yanzu shiru ko shine ya sashi yin fushi oho , miƙewa tayi dan gabatar da sallahar isha’i tana idarwa ta jerowa kanta adu’oi dakuma Haisam ɗinta.”

Mama tasa ankai kuɗin aure , iyayen Maimunatu sun yanke lokaci kasancewar su mama sun roƙa kar asa bikin da nisa ,cikin sa’a kasancewar a shirye suke suka amince yau saura sati biyu biki , Haisam na burin zuwa gidansu Afnan yana tsoro yasan dole zai fuskanci cin mutunci da cin zarafi daga duka ɓan garorin guda biyu , wanan shike sage masa gwaiwa ya kasa zuwa ,ga matsa masa da mama tashiga yi yanzu bashida saƙat kasancewar biki ya kusa tasashi siyo akwati ya kawo ɗakinta ,aikuwa haka akayi dan gudun tashin hankali , akwatuna ukune biyu manya ɗaya ƙarami cikin fara’a mama tadinga sanya masa albarka , yanzu kam Haisam yafara cire rai da samun Afnan saboda dalilai da dama hakan yasa ya haƙura da auran da ake shirin liƙa masa amma badan yana soba ,kwanci tashi asarar mai rai yau biki saura kwana uku sbda Haisam yagama haɗa kayan akwati yasa Mama kwantar da hanlinta ,hidima akeyi sosai baba kam baya kula lamuranta dan zata iya tsigesa ba tsoro bare fargaba , ƴan uwa kowa sai yayi tsegumin wanan aure ,kowa tambayarsa itace to ina matarsa , kaf cikinsu ba suda mai basu amsa yasasu jan baki sukayi shiru.”

Biki yayi biki Haisam bai gaiyyaci kowa ba sai dai ya gayyaci abokansa na anguwa , suma gudun kar suyita yi dashi ne amma da babu wanda zai bawa labarin auran da yazamo tamkar auran dole , bayan an ɗaura aure Maimunatu ta kira Haisam ko akwai wani events da za’ayi ?”cikin baƙar magana Haisam yace “to ni babu wani shirme da za’a kawomin ,
“kuma kidena rawar kai ba sonki nakeyi ba liƙamin ke akayi dan haka karki ƙara koda marmarin kirana kinaji ko?” Maimunatu da jikinta yai sanyi duk azabar masifarta amma takasa mayarwa Haisam martani lallai ko zata rama koba yanzu ba katse wayar yayi tare da jan dogon tsaki, ɗakin Afnan ya shiga ganin komai kamar tana nan Allah sarki masoyoyiyar gaskiya Haisam ya faɗa lokacin da ya kwanta a gadon Afnan ya luluɓe jikinsa da blanket ƙamshin turarenta ne yake masa yawo ,gani yake kamar zai ganta kwance kusa dashi , tabbas Afnan da Allah ya bata aihuwa da babu abinda zai hana ƴa ƴanta su taso cikin irin halinta , duk da Allah yayiwa mahaifinta arziƙi hakan baisa ta ɗauki talaka da ƙyama ba , kwance yake duk wannan tunanin da yakeyi , wasu hawaye ne masu zafi zuka kwaranyo masa agefe idansa ,tunowa yayi ashefa wai shine ango ko ?”kuma yau za’a kawo amarya ,tabb to ni mema zanyi? miƙewa yayi ya fice a ɗakin , yasa takalmi yana shirin fita yaji sallamar Fatima ɗago kai yayi tare da amsa sallamar Fatima ce tace “ina yini Haisam lpy lou y gida bata amsa ba tace “har yanzu Afnan bata dawo ba ?eh Haisam ya bata amsa bata dawo ba nima jiranta nakeyi , ficewa tayi batare da ta ƙara bi ta kansa ba , tana faɗawa gida ta saki kuka mai cin rai , shikenan Afnan ko shawara babu yanzu gashinan ya tafi ta barta takuma sakin kuka.”

Tuno ɗaurin auran Afnan yayi da ya kashe kuɗi sosai wanan kam tamkar za’a sashi a kurkuku yakeji tunda babu mai sa ssauta maganar auran ,ganin Fatima ta fice ya sashi koma wa bedroom ɗinshi ya kwanta , jin kwanciyar babu daɗi yasashi juyi a gadon , jin an rangaɗa sallama yasashi miƙewa jiki babu ƙwari , ganin mata da yawa ga motar kaya a waje ya matsa gefe ba tare da ya kallesu ba kanshi a ƙasa yace “ina yininku sama sama suka amsa ,ganin gidan babu lefi yasa su washe baki suna sanya alkairi , a wane ɗakin za’ayi jeren?” Haisam ne yace”ga ɗaki can ,ɗakin baƙi ne zaku iya yin jeren a ciki , wata daga ciki da alama ƴar uwar Maimunatu ce ta turo ɗaurin ɗankwali gaba tace ” aikuwa sai dai in a fito da kayan ɗakin kishiyarta a jera na Maimunatu , danƙari Haisam yac” lokacin da yake shirin ciro kwaɗon ƙofa a aljihunsa ya kulle ɗakin Afnan sa kai yayi ya fice ,kan uba to wlh Maimunatu zatasha wuya a gidan wanan shu’umin sai ta tashi tsaye ,wata daga gefe da tun shigowarsu batayi magana ba tace “wayasani ko kishiyar tata azabarshi ce ta korata gidansu , haka dai suka dinga tsegumi , ganin hakan bazai fishesu ba yasasu komawa bakin aikin nasu , dole a ɗakin baƙin suka yimata jere ɗakin bawani mai girma bane amma dai kayan sun zauna sunyi kyau amma ko ƙafar na Afnan basu kamo ba, kasancewar iyayen Maimunatu talakawa, suna gamawa suka kullo ƙofar suka fito kowa na tofa albarkacin bakinsa akan Haisam shiko ya fice ya barsu.”

Ƴan kai amarya ne keta shiri dan mama ta kira Haisam a waya akan ya kawo motoci , dole yakebon umarnin ta haka yaje ya taho da motoci aka rakasu gidan su Maimunatu ,kowa sai kururuwar shiga mota yakeyi ƙanwar maman Maimunatu da basu fito da Amarya ba sunanan suna yimata uɗubar tsiya akan ta koyi tattali mijinta mai yawan cefane , tadinga ɓoye wani abin tana kawowa gidan su komai da aka gaya mata ya shigeta sosai musamman ma maganar tara kuɗi, haka acikin abokan Haisam wai ya shiga gidan su amarya yace “ita suke jira tayi ta fito , luluɓo mata fuska sukayi aka nufi ɓota da ita sunyinyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan ,jin guɗa yayi yawa ya sanya Fatima leƙowa taga ko suwaye , ganin mata nata shiga gidan Afnan yasata riƙe baki tace “angama Haisam ma yayi aure ta sa kuka shikenan Haisam ya saki Afnan wane laifi tayi masa dahar yayi mata haka ?”kasa zaman gidan tayi ta kulle ƙofa ta nufi maƙotansu.”

Maimaicin abinda Haisam yayi musu suka fara Maimunatu buɗe ido tayi tana ƙarewa ɗakin kallo babu laifi yayi kyau sosai ta maida mayafinta ta rufe , faɗa aka shiga yi mata har ƙarfe tara na dare , kowa ya cire ran Haisam bazai kawo mota ba , sunata dai zaune wata a cikinsu ma batada kuɗin komawa horn sukaji lokacin ƙarfe tara da rabi hamdala sukayi ✍️.

Follow me and vote on wattpad
Nayi tafiya ne shiyasa kuka jini shiru

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

Zainabhabibu713 gmail.com

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

My facbook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

Zainabhabibu713 gmail.com

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

*💦{AREWA WRITER’S ASSOCIATION}💦*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

 

EPISODE 13 & 14

Kufito mu tafi suka ji ana cewa , da sauri suka miƙe suna yiwa amarya sallama , tun tana saka ran shigowar ango harta fara cire rai agogonta dake manne a jikin bango ta ɗaga kai ta kalla ƙarfe shabiyu na dare to ko bazai zo bane ?”ta faɗa cikin ranta gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta cire kayan jikinta ba , ɓangaren Haisam harya shigo ya kwanta a ɗakinsa duk bata sani ba , da asbha ya miƙe cikin salati yayi alwala ya fito da shirin tafiya masallaci tunowa yayi da ace Afnan ce a gidannan da tuni komai ya gyaru amma amarya guda ta saki baki tana bacci , ficewa yayi yabar gidan ya nufi masallacin kusa dasu ko nafilar ma yau baiyi ba ,ƙarfe takwas Maimunatu tayi miƙa tare da salati ta kalli agogo ganin ƙarfe takwas yasata cewa “kan uba wai na makara ne shiyasa na tashi inajin wata azababiyar yunwa , toilet ta nufa ta yi alwala tazo ta tada sallah ko cikakiyar adu’a batayi ba ta shige kitchen, ganin indomie guda uku manya a jere ya sanyata murna to ina zanga ƙwai?” to me hawa sama ya taka leda ai sai tafiya barin dafa indomin ina gamawa na haɗa shayi mai kauri nasha ko zanji sanyi a raina tunda rabona da abinci tun jiya da yamma , ɗaya da rabi ta dafa ta cika kofi da ruwan lifton kasancewar ta nemi madara ta rasa ,Haisam ne ya fito palo kasancewar dole zasu haɗu tunda a palorn take zaune , ganinta yayi ta mimiƙe ƙafafuwanta tanata loda abinci , Maimunatu ce ta ɗago kai ta ƙarewa Haisam kallo cikin zuciyarta tace “nayi sa’ar gwarzon miji mai jini a jika , ta miƙe tana suɗe hannu tace “barka mijina wai a ina ka kwana ?”a gidan ku , nace “a gidanku meyasa bakice nemana ba ?aida kinsan inda na kwana.”

Bata damu da maganganun da ya faɗa mata ba ta ruƙo hanunsa tana shinshina ,to sabon salo sai kace maiyya ? Maimunatu ce ta zaro ido tace “kowane miji yana alfahari da daren farkonsa shida matarsa amma kai kamar bakayi , gyara tsayuwa Haisam yayi yace “daren baƙinciki ko ?”to kishirya zaman ƙunci a gidannan dan walah keda jin daɗi muddin kina gidanan kunyi sallama ,oho dai nariga na sameka mekuma yarage kawai kazo mu buɗe soyayyar mu , wani kallon banza Haisam yai mata kana ya fice , Maimunatu ce tayiwa mamanta waya akan taje gurin malamin da suke zuwa dan sunji daɗinsa tun akan maganar auran gashi yanzu ta sami Haisam sunso ya mance da Afnan amma abin ya gagara ,maman ce tace “to ina magun gunan da na ƙulle miki a baƙar leda , Maimuna ce tace “nayi amfani dasu amma shiru , to ki kwantar da hankalinki insha Allah anjima zani ,duk iskancin sa zai sakko yanzu dai babbar damuwar shine inda za’ayi ya kwanta dake har kisami ciki , daganan kinga sabon gata zai rashi da gurinshi da gurin uwarshi , Maimunatu ce ta nisa kana tace “hmm yaushe ma ya shigo ɗakin nawa to jiyama ban san a gidan ta kwana ba , ɓama ce tace”ke wawiya ce bakida tunani meyasa bazaki san inda zakiyi ba sai kace ba mace ba ?”nifa duk iskancin namiji sai na juyashi naga kamar ke bazakiyi gado naba ko ?mama zan gwada karki damu cewar Maimunatu sukayi sallama , tana gama cin abincin ta miƙe ta nufi bedroom ɗunta ta kawanta , tanata tunanin maganar mahaifiyar tata.”

Tabbas inhar Haisam bai kwanta dani ba bazan sami gata ba dan nasan kaf danginmu babu wacce bata aihuwa , to yazanyi ?” kemis zani in siyo ƙwaya , janyo dogon hijabinta tayi ta sanya ta ciro ɗari biyar acikin jakarta ta fice tare da janyo ƙofar gidan , ganin kemis a kusa da su ba sai tasha wutaba yasa ta shiga ,Allah yasa babu layi , ta ce abata maganin tada sha’awa , ƙare mata kallo likitan yayi yace “baiwar Allah wa zaki bawa wanan maganin?”mijina tabashi amsa a taƙaice , mijinki kuma ba auran soyayya kukayi ba ?” Maimunatu ce ta dakatar dashi tare da cewa “kaga malam idan baka dashi kokuma bazaka bani ba in wuce ,wanan tambayar banga amfaninta ba , mai kemis ne yayi murmishi yace “karki damu indai magani ne zan baki , cikin zuciyarsa yace “wlh sai na shirya miki gadar mugunta da zaki sha wuya , sachet ɗaya ya miƙa mata yace ” kibashi biyu kekuma gobe kisha biyu ,to nawa ne ɗari biyar ,ya bata amsa cikin zumuɗi tace “inkasan wata bakasan wata ba wlh sai kazo da ƙafafuwanka kana haɗani da Allah , zanga ƙarshen taurin kai ,tana tafiya tana maganar shiko mai kemis tana fita ya tuntsure da dariya tana tafa hannu.”

Da fara’a ta shiga gidan kai tsaye ɗakin Haisam ta shige , ganin ruwan gora a gefe ga kuma fanta ta gora ansha ragowar zaiyi rabi yasata dan daƙa maganin ta juye a ciki ta girgiza ta ajiye ta fice , wanka tayi ta wanke kwanukan da taci abinci , shara ce dai Allah bai bata ikon yi ba,

Labari ya isarwa Afnan maganar bikin Haisam , tasawa kanta damuwa sosai momy ta sata a gaba da faɗa akan ta damu da Haisam shiko bai damu da ita ba , tun tana damuwa har tazo ta fara ragewa sbda dena tunanin Haisam zaiyi wuya ,taci kuka har ta haƙura , dady yanzu yafara kula Afnan ya canza mata waya ya bata kuɗi mai yawa tayi siyayya hakan tafara rage mata damuwa , Anty ummi rabonta da gidansu an daɗe , kasancewar tunda anty ta cimata mutunci ta tafi ranta a ɓace , yau tana son zuwa gidan su anty ummi tana tsoron tambaya dan dady ya hanata fita , harta fito da gyle ta maida tama haƙura da fita kwata kwata gashi yanzu batada number kowa ,

Salma ce ta shigo da sallama riƙe da Sudais a hanunta , da sauri Afnan ta fito tana cewa”oyoyo my sister cikin fara’a suka rungumi juna ,Salma ce ta ɗauki Sudais tana yimasa wasa , ƙarasawa Palorn momy sukayi , momy na zaune a kan kujera ta fara yimusu oyoyo , ganin yaran nata reras yasata sakin fara’a , Salma ce tace “momy yaushe Anty Afnan tazo ?”momy ce tace “ai ta kwan biyu takardar ta muke jira yazo ya bata , ashe ma har yayi sabon aure , riƙe haɓa Salma tayi tace “tun farko abinda nake faɗa muku kenan yanzu gashi ya maida anty bazawara , momy ce taja ƙwafa tace “ai yanzu komai ya wuce , baban farinciki na ma shine , batada ciki kina bazatayi wuyar samun miji ba ,✍️.

My fans banfa dawo ba kuyi haƙuri

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 15 & 16

Haka dai suka dinga hirarsu Anty ce ta shigo ta samesu a palo cewa tayi” aa saukar yaushe ?”Salma ce tace”Anty ban jima ba , gaisawa sukayi hira ta ɓarke tsakaninsu , wanda duk rabin hurar ta Anty Afnan ce , hakan ya sata ƙin kulasu dan inda abinda ta tsana bai wuce hirar Haisam ba ,sai yamma Salma ta fara shirin tafiya , momy ta bata turaruka da su zuma , kirane ya shigo wayarta , ganin number mijin yasata cewa “to drivern mu ya ƙaraso ,bata samu haɗuwa da dady ba hakan yasata tafiya tace “a gaishe shi, momy ce ta ƙwalawa Afnan kira kasancewar ta koma ɗakinta , amsawa tayi ta fito , momy ce tace “zo kiyi wanka kiyi kwaliya dan Allah ji tsara kwaliyar maiya faru momy ?” sai kin tambayeni ko kina ganin zan cutar dake ne ? a’a Afnan tace ” ta shige toilet tafara wanka da sabulun da momy ta bata mai ƙamshi , tana fitowa ta tarar da momy a ɗakinta da kaya a hannu tana gama kwaliya tace “momy wanan kayan zan sa?”cikin fara’a momy tace “eh man ƴar albarka karɓa Afnan tayi tasa momy ta miƙo mata sarƙa da ɗankunne da war waro , kana ta miƙa mata turare mai ƙamshi , feshe ko ina na jikinta tayi ta juyo tace “momy nayi kyau?”.

“Sosai ma my daughter kinyi kyau , yanzu kinsan abinda nakeso dake? a’a Afnan tace “to baƙo zakiyi daga Kano zai zo nan Abuja so ina san ki tarbeshi da mutunci yaron abokin dadynku ne insha Allah Afnan tace “in ya iso zai kiraki a waya oky momy , jekisa a gyara ɗakin saukar baƙi , ficewa Afnan tayi dan isarda saƙon momy ,turare mai ƙamshi aka sanya a ɗakin , ƙarar wayar Afnan ce ta dawo da ita daga duniyar tunani sbda tana tunanin to shi waye kuma mezai kawoshi , inko soyayya ce hmm , amsa kiran tayi tare da sallama a bakinta , wa/alaikis salam barka taji ance daga ɗayan ɓangaren gimbiyar mata kuma sarauniya , gani gurin parking ɗin mota oky Afnan tace “tana shirin miƙewa , da fitarta ta hango wani kya kyawan saurayi lol to koma dai bazawari ne ,nidai ya yimin kama da saurayi , yana hangota ya haɗiyi wani miyau tare da magana a zuciyarsa , shin wanan bazawara ce ?”anya nifa naga kamar budurwa , ga tsayi ga kyau komai na jikinta mai ɗaukar hankali kai masha Allah ,kona aureta bazan haɗata da matata ba 🤭wai dama yanada mata ?”fans kuzo muji , sallamar da Afnan tayi ne yasashi daɗa ƙare mata kallo ,yana amsa sallamar yace “gimbiya sarautar mata kuma mata a gurin Abdallah , waro ido Afnan tayi tace “wanan kirari haka ?.

To zomu shiga gida ƙin jerawa yayi da ita tana gaba yana baya ,yana kallon yanayin takunta , jinjinawa yakeyi a zuciyarsa inhar yasami Afnan to yasami farinciki gashi ya riƙe sunanta gam , suna shiga ya zauna a ƙayataciyar kujerar da ta ƙarawa ɗakin kyau , nesa dashi Afnan ta zauna tunani ne ya faɗo mata ashefa tanada aure zata tsaya hira innalilahi to yanzu yazanyi ?”momy fa na sane wlh , Abdallah ne yace “gimbiya bamu gaisa ba lokacinne ta ƙare masa kallo ba wani yaro bane dan zai kai shekara talatin da biyar ko fima amma kasancewar nera ta zauna sai ta ɓoye shekarun nasa , murmishi tayi tace “ina yini lpy dafatan nasami mazauni a zuciyarki , tsintar kanta tayi da cewa insha Allah, ganin abin takeyi kamar almara wai itace a gaban wani harda tsara kwaliya ba mijinta ba kai ina!!, Abdallah ya lura hankalinta baya gurinshi dan tun ɗazu yake magana batasan yana yiba amma hakan bai ɓata masa rai ba ,sbda tunda ya ganta yaji zuciyarsa ta amince da auren ta kuma dukiya ko nawa take buƙata zai kashe dan yaga ya sameta.”

To Afnan barin shiga mu gaisa da dady yacemin yana hanya ɗazu da alama yama ƙaraso , to kawai Afnan tace “ta miƙe jiki babu ƙwari tayi bedroom ɗin momy , momy na ganinta ta faɗaɗa fara’arta tana cewa my daughter ya kukayi , zama gefen gadon momy Afnan tayi tace “mun gaisa yace “bari yaje gurin dady su gaisa , oh amma babu wata matsala ko ?”eh Afnan tace ” momy kinsan fa da aure na nake kula wani , haɗe rai momy tayi tace “to ai Haisam ya sakeki yau kwana biyar kenan gama takardar , cikin ƙaguwa da ganin takardar , sbda gani takeyi momy kamar wasa take yimata , miƙa mata takardar momy tayi , Afnan ce ta nutsu ta fara karantawa .

ASLAMU ALAIKUM
NI HAISAM NA SAKI AFNAN SAKI BIYU,

Maimai tawa tadin gayi a zuciyar ta ya sakeni ?” Haisam ya iya sakina ? kalonta momy tayi tace “Afnan inason ki kwantar da hankalinki yanzu kina fita idda zaki yi auranki , namiji ba ɗan goyo bane ,yakamata kisani daga lokacin da yayi sabon aure shikenan kin zamo abin wula ƙantawa ,yanzu kinga aya a auranki da Haisam ko , fashewa da kuka Afnan tayi tana juya takardar tana kuka , yayi kyau zan cireka a zuciyata in huta tunda ba sona kakeyi ba , taɓe baki momy tayi tace” “dama menene abin so a gurin talaka kina soyayya ai , no momy inason sa maiyasa yayimin haka ?” shigowar dady ne yasata tsagaita maganar tare da kukan , kallon fuskar Afnan yayi cikin tuhuma yace “mai yasami Afnan nakejin maganarta tun daga ƙofar ɗaki , momy ce tace “wai dan na miƙa mata takardar sakin da Haisam yayi mata shine take kuka , samun kujera dady yayi a can gefe ya zauna , yace “wato Afnan har yanzu bakisan talaka ba ko ?” idan zaki yarda da zaɓi na na zaɓa miki Abdallah a matsayin miji , ɗago kai Afnan tayi saboda tariga ta yanke shawarar bin umarnin iyayenta , tunda Haisam yayi mata haka bazata ƙara yimusu gardama ba.”

Momy ce ta karɓe da amma yanada mata ɗago kai Afnan takuma yi a karo na biyu mata kuma!!eh cewar dady hakan bazai sa Abdallah ya wukaƙan taki ba , momy ce tace ” karki watsa mana ƙasa a ido daughter,to Afnan tace “na karɓi zaɓinku momy insha Allah bazakuyi kuka dani ba , cikin farin ciki dady ya miƙe yana cewa”Allah yayi miki albarka yanzu mai kike buƙata wanda bakida shi ?babu komai dady ,to kitashi ki raka Abdallah zai tafi ,Afanan ce tace “to dady, mayafinta ta ɗauka ta fice samunsa tayi a gaban motarsa a tsaye da alamu ita yake jira , ganinta yasashi faɗaɗa fara’arsa yace “gimbiya barka da fitowa , mumishi Afnan tayi tace “sannu ba wata hira sukayi mai tsayi ba yace “zai tafi aiyuka sunyi masa yawa amma zuwa gobe zai dawo , buɗe mota yayi ya ciro kuɗi masu yawa ƴan ɗari biyar biyar ya miƙa mata , ƙin karɓa tayi tace ..✍️.

KUYI HAƘURI PAGE ƊIN BABU YAWA

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 17 & 18

Tace nagode fatana shine Allah ya maidaka gida lafiya , to amen gimbiya ta tunda kinƙi karɓar kuɗi ga wanan , dan Allah karkice bazaki karɓa ba , a kunyace Afnan ta karɓi ledar da alama turmin zani ne , batadai buɗe ba sukayi sallama ya tafi , dawowa ɗakin momy tayi wanan karon tasamu momy na sallah hakan yasata ajiye kayan a gefen gado ta shige toilet ɗin momy , tana fitowa daga bayin ta sanya hijab tafara sallah , bayan ta idar lokacin ma momy ta idar ,Afnan ta janyo ledar da tashigo dashi tace “momy gashi , to mekika samu? cewar momy wlh ko buɗewa banyi ba momy barin duba wani tsadajen leshi dakuma atamfa mai tsadar gaske sai gyale kowanne kalar kayan , wow Afnan tace “amma sunyi kyau momy washe baki momy tayi tace “kinsan kuɗin les ɗinnan kuwa 30k ne wanan atamfar kuma 20k ce to gyalukukan zasuyi 5k kowane ɗaya ,Afnan ce ta buɗe baki tare da cewa yanzu momy duk wanan hidimar ni ya yiwa?” to bagashi ba , ai na gaya miki auran mai kuɗi akwai daɗi , ke ki mora ƴan uwanki suma su mora , dariya suka sa.”

Haisam ne ya shigo ɗaki ransa a ɓace ,haƙiƙa yayi baƙin cikin rabuwarsa da Afnan yama akayi ya rubuta takardar ?”tabbas yasan shine ya rubuta to amma mai yasa , rasa abinda yake damunsa yayi a wanan lokacin gorar lemun da ya rage jiya ya ɗauka ya shanye ,ya kwanta wani kasala yaji yana dabai bayeshi , a halin yanzu Afnan yake buƙata , subhanallah Afnan maiyasa na rabu dake ?” juyi yakeyi a gadonsa gashi yanzu yana buƙatar Afnan a kusa dashi sallama Maimunatu tayi dama tasan yasha maganin sbda da ɓacin rai ya shigo duk tana lura dashi lallai boka ya cika alƙawari na raba Haisam da matarsa yanzu zasu buɗe sabuwar rayuwa kai wayo daɗi , Maimunatu sai wani rangwaɗa takeyi ta isa gaban Haisam tace ” sweety me kakeso ? jin muryar tayi iri ɗaya data Afnan yasashi miƙewa da ƙyar cikin ƙarfin hali ya janyota yana cewa nayi kewarki matata meyasa kika gujeni alhali kinsan kece farinciki na Afnan , Maimunatu ce ta juya kai tare da galla masa harara tace “uhm ai gani , Maimunatu kamar jira takeyi ta cire komai nata , nifa fitowa nayi dan wanan soyayyar tasu Haisam sai a slow .”

A wahale tace “Haisam ka ƙyaleni walhi na gaji , wani irin gurnani yakeyi kamar mahaukacin zaki , bayajin duk wata kuwwa tata sai ma daɗa shigarta da yakeyi , tayi cizon tayi yaƙushin duk a banza , sai ƙarfe ɗaya na dare ya sarara mata , shima kansa wahalalen nunfashi yakeyi , Maimunatu kuwa Haisam na ɗagata ta ta ruga ɗaki da gudu har tana cin karo da ƙofa , jikinsa duk ya mutu babu ƙwari ko kaɗan ,sai yanzu abubuwa suka fara dawo masa yafara tunanin dawaye yayi sxx ɗazu ?”karfa ace da Maimunatu ne ?”inko haka ne wlh ya jawa kansa raini kuma duk jiji da kansa da ƙin sake mata fuska ya tashi a banza kenan? taɓɓ amma maiyasa ma harna ji sauyin jikina ɗazu ,sanin bashida mai basa amsa yasashi mirginawa gefe ya fara tuno abubuwa da dama, faɗawa gado tayi tare da sakin wahalalen kuka mai tare da dana sani wai dama haka ma’aurata sukeji ?”kokuma ita batada lafiya ne ?”kukan nata ne ya tsananta tafara tuno abubuwan da Haisam yake yimata , yanzu jinya zatayi kenan , dan takawa ma bata iyawa sosai , nashiga uku ni Maimunatu na janyowa kaina bala’i to da ace banyi hakaba da inanan lafiya , tunowa da ai yanzu haka ta ɗauki ciki yasata murmusawa tama rage jin raɗaɗin sosai , ɗingisawa tayi ta shige toilet wankan sabulu tafara , kana tayi na tsarki ta gasa jikinta , Maimunatu ce tac”nadai ji daɗi amma walah har yanzu inajin ciwo to kodai sai anyimin ɗinki ne🤣🤭fans kuzo muyi jinya lol.”

Gyara jikinta tayi ta shafa mai ta kwanta dan wani gajiya takeji , adu’ar bacci ma ta gagareta ,haka ta kwanta , Haisam ma wanka yayi ya sauya kaya , yayi alwalah yayi nafila , ya kwanta asbha tagari… Afanan duk huɗubar momy yanzu tana tasiri a ƙwaƙwal warta , kwaliya take tsarawa sabda Abdallah yace “yana hanya momy ce ta zaɓo mata kayan sawa masu kyau ,doguwar riga ce pink mai adon farin stone ba ƙaramin kyau tayi mata ba , momy ce tayi mata make up Afnan ce tace” momy kinga kyan danayi kuwa ?”ai inhar kika kwantar da hankalinki zakiyi abinda yafi kyau ma , ring ɗin wayarta ne ya katseta ,zata ɗauka momy tace “no ɗan ja aji kaɗan aikuwa hakan akayi saida yakira su biyu sanan ta zo ɗagawa shima momy tace “ki kashe masa murya , ok mom , kana ta ɗauki wayar , Abdallah ne yace “ranki shi daɗe , yau jan ajinne ya motsa , uhm baby nayi missing ɗin muryarka , waro ido Abdallah yayi cikin zuciyarsa yace “yau kuma , yarinyar da kunyata takeji , ƙara duba sunan wace yakira yayi ita ɗince Afnan ,to jin shiru yasa Afnan cewa” my honey naji kayi shiru ne , am ina driving ne so zan kiraki inna iso.”

please kayi driving a hankali kaji , insha Allah gimbiya matata kiss Afnan tayiwa wayar kana ta katse , 🤨fans karkuji mamakin huɗubar da momy take yiwa Afnan , to dama ita ba baya ba gurin iya soyayya to bare ma yanzu ana yimata tini hmmm.

mama ce zaune da redio a hannu jin ana sanarwa wata mata ta haifi yara uku kuma duk rayayu yasata jin , nishaɗi dajin itama takusa kama jikokinta a hannu , kai jikoki fa da daɗi mama tace ” niko nace “sunan tafe , yau Haisam ya tashi da ƙarfi a jikinsa ya yi wanka ya gyara ɗakinsa , ya fe sheshi da turare palo ya fito riƙe da waya a hanunsa , ya sunkuya yana goge takalmi yaji mutum ya hau masa baya , cikin masifa yace “waye wanan ban san iskanci , Maimunatu ce ta lafe a bayansa jin yana ƙoƙarin timata da ƙasa yasata saukowa ,ta ƙura masa ido wanan wane irin rainin wayo ne ?”dan iskanci dakuma raini shine zaki haumin jiki da ƙazamin jikinki , Maimunatu ce tace “dan nahau jikinka shine kake gayamin magana ,an faɗa miki keɗin waye , Maimunatu ce tace “niba kowa bace “a haka kagani kuma ka hau…..wani wawan mari ya wanketa dashi hakan yasata yin shiru batare da takuma cewa komai ba.”

In taƙamarki raini ne to sai na gyara miki zama a gidannan wlh kika ƙara shiga harkata sai kinyi nadama ,to inyin mana wake tsoron a mutu kai bafa tsoronka nakeji ba wlh duk wulaƙancin da zakayi ka daɗe bakayi ba , ni jira ma nakeyi kayi ganin zata manna masa hauka yasa shi ficewa bai kuma bi ta kanata ba.✍️.

Naji daɗin sharhinku ana tare masoya 👍
Vote me on wattpad

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 19 &20

Kwanan su biyu basuga juna ba dama shi ba memanta yakeyi ba , a ranar na ukun ne ya shigo da safe yayi wanka yasha bugagiyar shadda sai sheƙi takeyi , Maimunatu najin alamun tafiyar mutum ta miƙe da gudu daga kwanciyar da tayi , to sai kuma ina ?”ta tambayeshi tana girgiza kwan kwaso , sai gidanku ko kinada ja ne ? a’a tace “to ai naga gidan namun ma bakaje ba da kake gayamin baƙar magana , shidai Haisam gani yakeyi yanzu kam kamar an maƙala masa jaraba ne dan yarinyar bata neman kwanciyar hankali kwata kwata , bai ƙarasa shiga ɗakin ba ya yi ficewarsa waje , kan uba inama tsaye har ya wuce ya barni kan uba wlh wanan ɗan taurin kan zanyi magzninsa , barin zo in kira umma taje min gurin boka ko da akwai maganin da zai ragemin wanan rainin haba fitina har ina ?”.

Yau ne Afnan ta gama idda ,Abdallah yayi maganar aure , dady ne yace “ka tambayi Afnan ɗin inhar ta ‘amince to babu matsala ,kwana biyu tsakani momy tasa aka shiga yiwa Afnan dilka saboda ta ƙara kyau inda zata gigita samari , yanzu idon Afnan yafi dz buɗewa nesa ba kusa ba , ƙarar wayarta ce tasata duba mai kiran , Abdallah ne ,dama yama sani anshafe labarin ɗaukar wayarshi intai ring sai ɗaya ,dole sai tayi sau biyu, aslm mijina katseta yayi da gani a palo dan Allah ki fito yanzu , gyalenta ta ɗaukz tare da ƙara feshe jikinta da humra , isa gurinshi tayi da sallama tace “ranka shida ɗe barka da isowa , ywa gimbiya komai naki birgeni yakeyi dariya tayi masa mai haɗe da fari da ido tace “kaima ai hakanne ,gyara zamanshi yayi yace “kinsan me ? a’a Afnan tace sai ka faɗa , inason a kawo sadaki ne kin amince manya su shiga tsakani ? murmishi tayi tace “haba honey nama ɗauka wata maganar ce nikam tun yaushe na amince karka damu , kai amma godiya nake sosai cewar Abdallah inason komai kar ya ɗauki lokaci nafison in ga amaryata a gidana , dariya Afnan tayi tace “ai ka sameni ma tun yaushe.”

Yau duk rabi hirar tasu ta lamari auran ne , Afnan ji takeyi kamar yanzu ne zatayi sabon aure , wani nishaɗi takeji , momy ma sai daɗa zugata takeyi, ana kuma gyarata tun ba’a kawo sadakin ba ma bare ayi maganar aure , yau kwanan Abdallah uku bai zo ba kasancewar ya gayawa Afnan cewar zaiyi tafiya , a yau iyayensa sukazo nema masa auran Afnan tare da dukiyar aure , dubu ɗari da hamsin suka zube gaban su dady , dan su biyu ne shida abokinsa , fatan alkairi sukayi kana sukayi musu sallama , Abdallah na Ibadan yaje gurin wani kaya nashi da aka kawo , sana’ar kayan sawa yakeyi kama daga takalma na mata harma na maza shaddoji da atamfofi da sarƙa da ɗan kunne duk dai , kuɗi a gurinshi ba’a magana , duk kuɗin dadyn Afnan to Abdallah yasha gabansa .”

BAYAN SATI UKU .

Yau kwanan sa ɗaya rabonsa da gidan dan yanzu sai yayi ra’ayi yake shigowa , Maimunatu na kwance zazzaɓi ya rufeta ta koma abin tausayi , jin alamun shigowar mutum yasata daddafa bango ta fito , ganin Haisam zaune da ƴar laptop ɗinsa a gabansa yana sarafata yasata zama gefen shi , ɗago kai yayi ya galla mata harara yace “wane irin iskanci ne zakizo ki zauna min dalla tashi jiki duk tsami , dariyar yaƙe tayi kana tace “ka temaka ka kaini asibiti , kallon kinma rainani yayi mata ya maida hankalinsa ga abinda ke gabansa , kuka tafara shaɓe shaɓe ta miƙe jiri na ɗibarta ta tsuguna a fabansa tace “dan darajar iyayenka dan Allah ka temakeni zan mutu , shi dariya ma tabashi , gani yakeyi kamar langwai take yimasa yace “inna fice naga wanda zaki laƙewa kauce dallah ,haka ya fice ya barta a gurin wani gagarumin amai ne ya taso mata ba shiri tadinga kwarara shi kamar zata amayar da hanjin cikinta , nunfashinta sama sama ta ɗauki ruwan dake kusa da ita a tebur ta sha ai kamar ta kuma kiran aman tacigaba , tashin zuciya ya takura mata wanan wace irin rayuwace ?” cewar Maimunatu jiri na ɗibarta ta ɗauko tsumman rigarta ta naɗe aman ta koma ɗaki bawai dan gurin ya gogu ba sbda wari ma gurin ya ɗauka amma haka ta koma ɗaki ,

TA ɗauki wayarta ta danna lambar mahaifiyarta , cikin sa’a ta ɗaga tare da cewa”Maimuna lafiyarki kuwa ?”naji muryarki wata iri kamar mara lafiya ,cikin ƙarfin hali Maimunatu tace “umma banida lafiya kamar zan mutu ga Haisam ɗin yaƙi kulani , to meye yake damunki cewar umma?”wlh amai ne da zazzaɓi gakuma tashin zuciya ,Alhmdulilah ƴar albarka kinyi ƙoƙari kin haifu Allah ya inganta shiɗin waye da zaiƙi kulaki lallai ma , bari yanzu zan fita gidan barka daganan zan wuce gurin wani malami da aka yimin kwatancensa jiya kwantar da hankalinki zakisha gata shiɗin banza ma , kashe wayar umma tayi zuciyarta fal farinciki yo aisu kakarsu ta yanke saƙa.”

Anty Aisha ce ta zauka a gidan misalin ƙarfe huɗu na yamma kai tsaye ɗakin yayan nata ta wuce, yana ganinta ya washe haƙora tare da cewa dama so nakeyi in kiraki a waya yanzu to sai gaki kin iso , sassuta murya Anty tayi kamar munafuka tace “ai gani dama zmfanin ɗan uwa kenan yanzu mai yafaru Alhaji ?”dady ne yace “akan maganar auran Afnan ne, riƙe baki anty tayi tace “yanzu gidan matsiyacin zaka maidata?”a haba ni na isa ai wani sabo Allah ya kawo mata shi wancan ai harya bata takardar ta tun yaushe hidindimun bikinne dai ankawo sadaki ankuma sa rana wata biyu me dame kike ganin ya kamata a siyo banason wancan kayan ɗakin nata so nakeyi a canza mata masu tsadar gaske , cikin fara’a anty tace “dama abinda zance kenan to suɗin wa za’a bawa naga basuyi komai ba , dady ne yace “wa nakeda shi bayan ke kece zaki kwashe ,ai da sauri anty ta sunkuyar da kai tana zubowa Alhaji godiya.”

Alhaji ne yace “ai ba komai yanzu nawa ne kike ganin zai isa kokuma tare zamuje kasuwar , ai kam dayafi Alhaji ita kuma uwar tata sai ka bata kuɗin siyan kayayyakin abinci kuttt hmmm…

Kumafa kin kawo shawara barinje banki in dawo zuwa gobe sai mu tafi , yana ficewa anty ta wuce saɗaf saɗaf ta fice dan batason su haɗa ido da kowa, tana fita bakin get tayi hamdala da tari abin hawa ta fice , kai tsaye dady ɗakin momy ya wuce , samunta yayi ita da Afnan suna duba wasu turaruka da aka kawo musu daga saudiya, zama dady yayi yace “biki nata ƙaratowa harkun fara shirye shirye ne ?momy ce ta kashewa dady ido ɗaya tace “turarukan Afnan ne ƙawata da zata dawo daga saudiya nabata sautu to shine ta kawomin , kuɗinsu dubu ɗari uku , ok babh matsala amma sai naje bank dan yanzu babu kuɗi a hanuna masu yawwa….✍️.

Follow me and vote on wattpad

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 21 & 22

Tun safe Abdallah ya sanarwa Afnan yana hanya abinci iri iri momy ta sata yi masa farinciki kuwa kowa na gidan ya gane tana cikin nishaɗi.

Ƙarfe biyu na rana sai ga kiransa , ya sauka a airport tsabar farinciki Afnan tace “ko inzo ɗaukarka ne?” no my Afy cikin kasalakiyar murya yace “.

Oky to me kakeso inyima yaufa da kaina nashiga kitchen “wow”my Afy sabon sunan da ya laƙaba mata kenan inanan zuwa insha Allah nanda 5:pm ɓata rai tayi kamar yana ganinta tace ” yayi yawa namatsu in ganka ,ƴan kwana kinnan da kayi ji nakeyi kamar kayi shekara.”

Oh sorry my Afy zanzo amma surprise zanyi miki ,barin shiga mota oky Afnan tace ” sanin ba ita kaɗaice dashi ba ,dole sai yaje gurin matar sa ya huta ,wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata a fili tace “LAMARIN ƘADDARAR AURENA… Allah sarki rayuwa ,

Kai tsaye wanka takuma shiga ta daɗe tana ƙalƙale jikinta daga bisani ta fito ɗaure da tawul a ƙirjinta dakuma kanta , wasu humra masu masifafen ƙamshi ta shafa ,kana ta kawo mai shima mai ƙamshi ta mulke ko ina na jikinta.

Momy ce ta shigo ɗauke da murmishi a fuskarta tazo gaban Afnan dake kan kujerar dake gaban mirror daughter ki tsara kwaliyar da kyau fa oky mom zanyi nama gama ,

simple makeup tayi wanda ya kuma ƙawata kyakyawar fuskarta , kana ta ɗauko atamfa ɗinkin riga da skirt wanda ya matse ta sosai hakama rigar ta fito da kowace sura ta jikinta .

Ƙarfe biyar dai dai sai ga kiran Abdallah ya shigo , a yangace ta ɗaga tare da rage sautin muryarta , ganinan a parking spice ,oh baby yau kazamo baƙo kenan ?kashe murya yayi kamar mai shirin yin barci yace “.

Nafison ganin kwaliyar da aka yimin kafin in shigo in bada tukwaici , murmishi Afnan tayi ta janyo ƙaramin mayafinta tayo waje , taku takeyi kamar bazata taka ba ga wani fitina nnen ƙamshi dake tashi ,
Tun daga nesa ya hangota wani kasalalen murmishi yayi kana ya shafa sajen fuskarshi , gyara tsayuwarsa yakuma yi yana juyu da keys ɗin nake hanunsa.
tun daga nesa take sakar masa tsadajen murmishi , shima maida mata yakeyi cikin ƙwarewa ,da sako irin nasa, gimbiya Afy sarautar mata takawarki lafiya ,
Uhm to barka yarima zomushiga man ka huta , biyota yayi wanan karon ma itace a gaba shiko yana baya sai rawa yakeyi yana kallon kowane irin taku nata , da isarsu palo ya zube kan luntsumemiyar kujerar da ta ƙarawa ɗakin kyau drinks iri iri Afnan ta zuba masa da tsararen abinci mai rai da lafiya tuwon shinkafa yaji kifi da nama gakuma farfesu na kaza a gefe , kalar abincin da Abdallah yake so ne shiyasa ya zage yaci sosai .
Kallon gefensa da Afnan ke zaune yayi lumshe ido ya sake yi a karo na biyu tare da kamo hanunta yasanya cikin nasa , wani irin tafiyar tsutsa yake yimata da yai sanadiyar saukar mata da kasala , lumshe ido tayi kuma ta kasa hanashi yin hakan.
Afy ya faɗa cikin sasanyar murya,a kasalance ta amsa tare da kai kalonta gareshi .
Nayi missing ɗin kyakyawar fuskarki da komai ma , tunani Afnan ta fara gaskiya da Abdallah ba haka yake ba dan meyasa zai dinga yimata haka alhali iya sadaki kawai ya kawo ba’a ɗaura aure ba ?” tayi nisa cikin tunani ta tsinkayo muryarsa yana cewa “Afy tashi muje ki rakani gurin mota ,to kawai tace “tana miƙewa ta yafa gyaleta , shigo Abdallah bai matsa ba yananan a tsayen , to muje ,Afnan tace tana mai kallonsa , ƙin kulata yayi ya janye gyalen dake jikinta tare da ƙare mata kallo cikin zuciyarsa yana cewa”wanan yarinyar kamar aljana , ga tsayi ga ƙiba ga bobs ga hips komai normal ina na aureta na huta wlh,
Hura masa iska tayi a fuskarsa tare da cewa “baby kazo muje yamma tayi , bangaji da ganin matata ba ,cewar Abdalla h rasa ta cewa Afnan tayi ta zuba masa fararen idanuwanta , to zomuyi sallama ,cewar Abdallah hannayensa yasa duka biyu tare da …..

ciki ya baiyana muraran Maimunatu laulayi sai abinda yayi gaba , mama ta ziyarci wani malami akan ya dawo da ƙwaƙwalwar Haisam kamar ta yara sai abinda ƴar tata tace shi zaiyi , malm ne yace “nayi iya ƙoƙari na wanan yaro mutanen dake kansa ba ƙaramin bashi kariya sukeyi ba Allah na kareshi suma sunayi , haka mama ta kaso kuɗi ta dawo gida da ɓacin rai.

👏zaku dinga ganin page ɗin guntu wlh har yanzu ban dawo ba kuyi haƙuri insha Allah ina dawowa komai zai zama dai dai .

FOLLOW ME ON WATTPAD

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 23 & 24
Tare da rungumo ta sun dad’e a haka , Afnan ta tattaro k’arfinta ta turashi gefe tare da galla masa harara , kai Abdallah wanan wace irin rayuwa ce? ” kasan fa shed’an neman abokai yakeyi .

Wata shu’umar dariya Abdallah yayi kana yace “nikam bazai galaba a kaina ba saboda komai kikaga inayi Afy kece sanadi , kina tunanin irin wanan shigar da kwaliyar bazai sa kowane d’a namiji jin sha’awarki ba ?” kisani niba dutse bane dazan dinga zuwa ina ganinki alhali inada tabbacin nine mijinki ,oya zokiji , wasu zafafan hawaye ne sukayi nasarar zubo mata tace “babu komai banyi dan kayi sha’awata kamar hakan ba nayi ne dan na burgeka , k’ara matsowa Abdallah yayi tare da had’e hannayensa biyu yace ” afuwan my Afy am sorry nasan nayi laifi kuma kar hakan dana fad’a yasaki dena yimin kwaliya ,uhm kawai tace “ta mik’e ta fice Abdallah ya rasa me yake yimasa dad’i gaskiya daya sani bai fad’awa Afnan wanan kalmar ba kash ya had’e hannayensa biyu , gwada lambar wayarta tafara dan yana son suyi maganar hidimomin da za’ayi a biki to gashi a kashe ranshi ne yakuma 6aci sai ya fara duba lambar momy , cikin sa’a ta shiga.”

Ring d’aya aka d’aga muryar momy ce dan haka ya sa ssaura muryasa tare da d’an risinawa barka da yamma momy , ywwa “barka dan Allah Afnan na kusa?” a ‘a batanan , shiru yayi can kuma yace “to ya kashe wayar , momy ce ta fito parlor dubata amma batanan komawa bedroom d’inta tayi ,ta hangota a nannad’e a gado fuskarta sharkaf da hawaye , da sauri momy ta k’arasa kusa da ita tace ” daughter meyafaru?babu komai momy ,to maiya faru naji kiran Abdallah yana nemanki fad’a kukayi ? a’a momy , momy ce ta had’e rai babu alamun wasa tace “ni mahaifiyarki zaki 6oyewa damuwarki ko ?mik’ewa Afnan tayi inda abinda ta tsana bai wuce fushin momy ba dan haka batason fushinta , momy kwanannan Abdallah ya tsiromin da abubuwa marasa kyautawa ,shine da rungumata ,sai kuma tayi shiru murmishi momy tayi a ganinta tana ganin y’arta zatayiwa matarsa zarra ,karki damu daughter , momy tace ” cike da nishad’i , yau saura kwana nawa ne bikin ?saura kwana goma fa kwantar da hankalinki , daganan momy ta mik’e ta fice , Afnan ta kasa fassara maganar da momy tayi mata …✍️.

Kardai Ku manta karku jini shiru ne yasa nayi muku wanan , kunsan dai haryanzu ban dawo ba , dukda yanzu andena comments ina tunanin zanbarshi sai zuwa bayan sallah kawai 👌tunda Baku nuna damuwa ba⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 25 & 26

Ganin cikin Maimunatu yafara girma yasa Haisam fara kula da Maimunatu , hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba , tana ganin yanzu ya dawo sonta ne sosai , yau juma’a Haisam na zaune a kasuwa yaji wayarshi na ring cikin azama ya ɗauka ,jiyayi ance “kai ne Haisam ? eh nine Haisam yace “cikin rawar jiki duk da bai san mai kiransa ba ,amma yana tunanin alkairi ne ,malm Haisam muna nemanka a shagon mu na sai da turaruka muna odar su daga Dubai abokina ne ya bani lambarka , gaskiyarka da riƙon amana yasa nayi maka magana , cikin rawar jiki Haisam yace “to nagode ya waiga ya kalli ƴan tsirarun kayan dake jere a shagonsa kayan kwaliya ne basuda wani yawa amma Allah ya sanya masa albarka a cikin sana’ar .”

Ya naji kayi shiru ?babu komai Haisam yace sukayi sallama , Haisam na ajiye waya yafara saƙa da warwara anya zai yarda da ƙudirin mutumin nan ? baisan ko waye ba hmm , ya zurfafa cikin tunani yaji sallamar Abubakar babban abokinsa yanada shago a nan kasuwar jos ɗin wato ƴan tifa yana sana’ar sai da atamfofi ,shima yanada katafaren shago babba kuma suna bada sarin atamfofi , gefe kuma takalma ne masu kyau da tsada , Haisam abokina ya kiraka ?” Haisam ne yace “eh ya kira “to ka amince zaku fara kasuwanci tare ? uhm Haisam yace ” bawai naƙi bane amma inason kasani wanan ɗan akurkin shagon da nake rainawa yana rufamin asiri ina tunanin ranar da Allah zai yi ikonsa ya zamo bana wancan shagon kaga akwai damuwa ,

Abubakar ne ya taɓi kafaɗar Haisam kana yace “karka fara wanan tunanin abokina insha Allah bazakayi kuka da Alhaji Jamilu ba ,mutum ne na mutane kuma bashida ƙeta , to Haisam yace “Allah ya zaɓa mana abinda zai zamo alkairi , amma bazan bar shago naba dole zan nemi mai zama a ciki , daganan sukayi sallama kowa ya kama gabansa .”

Haisam ne ya tada mashin ɗinsa bayan ya rufe shago duba agogon hanunsa yayi ƙarfe biyar na yamma , hakan yasa shi ɗaukar titin da zai sadashi da gidan sa , yana isa ya kashe mashin ɗin tare da tura ƙofar kasancewar Maimunatu ba rufewa takeyi ba ,ya shiga da mashin ɗinsa ya kullo ƙofar , da bayan ya jingine mashin ɗin ya nufi ɗakinsa ya kwanta batare da ya doshi ɗakin Maimunatu ba , da shigowarsa da komai Maimunatu na gani ta windo.”

Yunƙurowa tayi da ƙaton cikinta a ƙalla zaiyi wata biyar ta gyara ɗaurin zaninta , saukowa tayi daga gadonta kana ta fito palo , ganin yamma tayi bata ɗora komai ba yasata jan dogon tsaki tace “wanan wace irin rayuwa ce ga ciki ga aiki ni wlhi bazan iya ba sai kace wata baiwa , haka dai ta ƙarasa ɗakin Haisam ta tura ƙofar babu sallama, hangoshi tayi kwance dagashi sai gajeran wando ,sosa kai tayi tare da yatsina fuska tace “sannu da dawowa , juyowa yayi ya ɗan kalleta yace “yawwa ya jikin ? da sauƙi tace kana ta zauna gefensa ,yanzu dai yaɗan rage tsanar da yayi mata albarkacin wanan ciki na jikinta , shima a halin yanzu yana son ganin jininsa , shiyasa yake ɗan sakin jiki da ita , janyota yayi tare da rungumeta yafara haɗe bakinsu guri guda tare da shafa bayanta , tuno azabar da tasha a daren su na farko tayi kuma tunda Haisam ya yi sex da ita bai ƙara yiba sai yau , zaro ido tayi kuma gashi tanason ta cima burinta na wani shu’umin magani da mamanta ta kawo mata hakan yasata daurewa ta fara maida masa da martani , ganin cikin zafin nama yake komai yasata fahimtar yana buƙatar ta , cikin zuciyarta tace “Allah ka bani ikon daurewa a wanan karon , fitowa nayi domin leƙa gidansu momy.”

Yau alhamis ,asabar ɗaurin aure gida yafara cika da baƙi su Anty Aisha itace a sahun gaba su momy da Anty ba ƙaramin haushi sukeji ba akan rashin yawan shawarar da Alhaji bayayi dasu , amma a hakan hausawa sukace komai wayon amarya ….. yau takama juma’a akayi sa lalle kasancewar Abdallah ya cikawa Afnan account batada matsala da kuɗi, komai tsadar tsadar abu inhar momy tagani to bata ƙyashin siya saboda kyansa , babu wani wasanni da sukayi , washe gari asabar dubban al’umma suka sheda ɗaurin auran ABDALLAH DA AFNAN akan sadaki mafi albarka dubu ɗari lakan ba ajalan ba , kowa ka gani fuskarsa cike take da annuri anci ansha amarya na hango sanye da wani haɗaɗen less mai ruwan pink da flawoyi baƙake a jiki ba ƙaramin kyau tayi ba fuskarnan tasha makeup sai sheƙi takeyi , ƴan uwan momy ne suka riƙe hanunta suka shiga da ita sashen Alhaji kasancewar babu kowa duk suna ɗakin baƙi , Alhaji munkawo Afnan ne ka sanya mata albarka , cikin farinciki dakuma nishaɗi dan Afnan ta auri wanda dady yakeso yasashi cewa , Allah ya albarkaci auranki Afnan Allah yayi miki albarka , kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga fuskarta.”

Tunowa tayi da lokacin auranta da Haisam dady ko kulata bayayi da aka kawota gabansa lokacin da za’a kaita gidan mijinta cewa yayi bashida abin cewa , amma yau itace yake cewa haka , tashi kuje Allah yayi miki albarka yar albarka , wani sanyi taji ko ba komai zata aurin zaɓin iyayenta a gurinta babu abinda yakai farincikin su a gurinta.”

Ɗakin Anty suka wuce da ita itama fuskarta cike da fara’a tace “madallah naji daɗin ganin wanan rana , anty Ummi dake gefe ta ja Afnan wani ɗaki banji mai sukace ba suka fito suka koma ɗakin momy.

Misalin ƙarfe takwasa kowa yayi sallah ya idar motoci suka fara hallara a harabar gidan , daga ganin motocin ma kasan kaf cikinsu babu na haya duk na ma’aikatane , Allah sarki rabuwa da iyaye sai dole Afnan ta ƙanƙame momy sai kuka takeyi momyn ma sai da ta zubar da hawaye sosai ganin Afnan tanata gursheƙen kuka, kasancewar ba wasu ƙawaye ta ɗiba masu yawa ba suka shige mota Afnan ma da ƙyar suka sanyata tanata kuka , ganin babu kowa a motar daga ita sai Abdallah a gefe , sai ma yanzu ta lura dashi , a gefenta sai direba , da ya maida hankalinshi ga wayar dake hanunshi , waro ido Afnan tayi shima Abdallah maida mata da martanin waro idon yayi ya sanya hanunshi cikin nata suka fice , kasancewar kowa ya fice daga gidan iya motarsu ce kawai, Afnan dai bata yi magana ba kasancewar jinta takeyi kamar zazzaɓi ne zai kamata , tafara haɗe hannayenta biyu tare da rintse idonta dataji yana yimata zafi …..✍️.

Ga masu buƙatar littafin daga farko zaku iya duba wattpad momislam 2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 27 & 28

Ganin idanunta sunyi ja tana ta rawar sanyi yasa Abdallah cewa dreba muje asibiti a dubata kar ka wuce damu gida , to yace “ya juya motarsa basuyi wata tafiya mai tsayi ba sai gasu sun iso asibitin kulawa likita yafara bata , cewa “Abdallah yayi muje office muyi magana , ok Abdallah yace kana ya rufawa likita baya da isarsu kowa ya zauna likita yace “wanan matarka ce ?eh Abdallah yace “to tana buƙatar kulawa , Abdallah ne yace ” menene ainihin abinda ke damunta ?”rashin bacci ne amma bayan shi babu wata matsala shine ya haifar mata da zazzaɓi amma zan haɗa mata magani insha Allah zata war ware , godiya Abdallah yayi masa bayan sun karɓi magani suka ɗauki hanyar da zata sadasu da katafaren gidan amarya , kasancewar hospital ɗin a kan titi yake suna isowa dreba yayi horn mai gadi ya buɗe get ɗin sa kai sukayi cikin gidan , samun mutane sukayi cirko cirko a tsaye kowa da mamaki a fuskarshi , ina ango yakai amarya.”

Buɗe murfin motar kowannen su yayi ,Abdallah ya rungumo Afnan suka fito Anty Aisha ce ta taho zuwa gurinsu tace “me yafaru munata jajanta rashin ganinku , murmishi Abdallah yayi yace “batajin daɗi ne shine muka wuce , asibiti to Allah yabada lafiya , amen Abdallah yace “anty ummi na tsaye tana kallon ikon Allah , haka kowa keta ɗan taɓe baki ko mai yasa oho .”

wata mata dake gefe da alamu itama ƴar uwar momy ce ta karɓi Afnan ta shige da ita ciki , gaskiya faɗin tsaruwar gidan ma ɓata lokaci ne maƙudan kuɗin da Abdallah ya kashe bazasu faɗu ba , part ɗin Afnan ɗin na can nesa sana uwar gida amma da tafiya a tsakaninsu dan kowanne da nisa gidan babba ne , zaunar da ita tayi a tsararen ɗakinta dayaji flawoyi ga wani ƙamshi dake tashi , gaskiya komai na ɗakin abin birgewa ne kasancewar dady ma ya kashe nera,

Iya mutum uku ne ragowa dare yayi sauran sun tafi suma suna gama gyara ta kasancewar batada kafiya ta kwanta sukayi mata sallama suka wuce , misalin ƙarfe sha ɗaya na dare shugaba ya shigo bayan yasa dreba yakai su anty gida , sanye yake da wata baƙar doguwar riga mai hula , sai tashin ƙamshi yakeyi saboda shi ma abocin tsafta ne dakuma son ƙamshi ,

Kasancewar zazzaɓin nata ya sauka yasata yin ƙarfi da jikinta tace “barka da zuwa , ajiye ledar hanunsa yayi ya cire agogon dake manne a tsin tsiyar hannunsa yakai dubansa gareta suka sakarwa junansu murmushi ywwa Afy ya jikin “da sauƙi tace “tare da rage idanunta ta maidasu ƙanana ,to masha Allah , yanzu dai dare yayi ki tashi mu nuna godiyarmu ga Allah ta hanyar yin sallah , sunkuyar da kai Afnan tayi tace “banayi whattt….!!! mekikace ? mai maita masa tayi da cewar banayi , alamun ɓacin rai sun baiyyana a fuskarsa ƙarara sai taji yace “to zokici abinci karki zauna da yunwa , tunowa tayi rabonta da abinci tun na safe gakuma wata masifafiyar yunwa na addabar ta .”

saukowa tayi ta cire mayafinta ta ajiyeshi a kan gado ,Abdallah ne ya haɗiyi wani yawu kai kace “wanda yaga mai siyarda awara , lol fitowa tsararen falon sukayi a jere tana gaba yana baya yana kallon abinda yake ɗauke masa hankali , zama tayi a ɗaya daga cikin jerun kujerun tare da janyo ledar da ya ajiye a gefe , miƙewa Abdallah yayi ya nufi kitchen, ya wanko plet ya kawo mata da cup, kasancewar a ya yanke take yasata ɗiba ta zuba a plet ɗin tafara ci shiko a haka dai wayarsa yake dannawa amma inka lura da satar kallon da yake yimata ba wayarce ta ɗauke masa hankali ba , tana gama ci ta tatara sauran takai kitchen bayan ta kora lemu mai sanyi dawowa tayi ta zauna tare da duba wayarta ganin ƙarfe ɗaya saura yasata , zaro ido ta kalli Abdallah da ya kawar da kai,

Dare yayi zan kwanta , Afnan tace “ba tare da ta dubeshi ba ok muje niba baccin nakeji , har tafara gaba Abdallah yace “to jirani takowa yayi zuwa gabanta ya riƙe hanunta suka wuce bedroom , kasa cire kayan jikinta tayi ta maida na bacci abin ya gagara irin kallon da Abdallah yake yimata yasata kwanciya tare da juya baya , shima bin gadon yayi ya kwanta tare da rungumeta ya juyo da fuskarta tana kallon tasa , nunfashin su na cuɗanya dana juna , uhm bacci nakeji Afnan tace “lokacin da taji hanun Abdallah a rigarta , cirin sanyin murya yace “to ai yanzu lokacin hutawa ne , bana sallah , cewar Afnan no karki damu ki yarda dani na matsu pls , cikin tashin hankali Afnan ta dubeshi tace “kadai sani ba ƙarya zanyima ba amma mai yasa zaka saɓawa faɗar Allah , nifa ba komai zan yimiki ba to ai ke mallakina ce , eh nasani amma ka barni nayi bacci , Abdallah ne yayi wani irin murmishi tareda ƙara matseta yace “gurinda Allah ya haramta min ƙasanki ne amma daga saman cibiyarki har komai ma zan iya amfani dashi , wanka ya shiga yayi kana ya dawo ya kwanta , Afnan batasan lokacin da baccci mai nauyi ya yi nasarar ɗaukarta ba , shiko ya daɗe baiyi bacci ba yanata juyi shi kaɗai yasan halin da yake ciki .”

Haisam ya kama sana’arshi baji ba gani kasancewar ya roƙi zaɓin Allah akan wanan Alhajin da yakeson ya zauna masa a shago yaƙi yarda , Abubakar yayi yayi amma yaƙi yarda ,

Mama ce keta rangaɗa sallama lokacin ƙarfe goma na safe Haisam na bacci kasancewar bai fiya fita ranar asabar ba yana hutawa.

Mama ce tace “inata kwaɗa sallama ko babu kowa ne a gidan ? cikin ɗaga murya take maganar , walaikis salam gani waye mai dako min tsawa , Maimunatu ta faɗa.

Mama dake ƙarasowa tace “baiwar Allah kice rabo aka samu ? yatsine fuska Maimunatu tayi kana tace “rabo dai muka samu, mama dake murna tana tafa hannu tace “to masha Allah to mushiga daga ciki man , wa ? wlh babu mai shigarmin ɗaki na gyarashi sai dai in ɗauko miki tabarma mijina yana ciki yana bacci , mama ce ta riƙe baki tana kallon Maimunatu da cikinta ya fito sosai dan ga dukkan alamu zai kai wata takwas dan daƙyar take duƙawa , abinka da mai ciki mama ta tausaya mata ƙwarai da gaske ta yunƙura tare da cewa ƴar albarka mai za’a tayaki dashi ? kai kaice baki maimunatu tayi tace ” nifa ba gaiyyar kowa nakeyi ba dan haka a ƙyaleni✍️.

DOMIN SAMUN LITTAFIN NAN TUNDAGA FARKO ZAKU IYA ZIYARTAR wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K’ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

 

EPISODE 29 & 30

Zama mama tayi a tabarmar niko nace Allah sarki Afnan wargi ma guri yake samu , Maimunatu datasha ɗaurin ƙirji ta dubi mama daketa ƙare mata kallo ta galla mata harara , abinku da ƴar lelen mata mama ta sakar mata murmishi, Haisam ne ya fito da alamun hayaniyar su ce ta tayar dashi , faɗaɗa fara’arsa yayi kana yace ” ah mama kece a gidan namu ?fuskar mama ɗauke da murmishi tace “wlh nazo duba Maimunatu ne , Hausam ne ya durƙusa tare da gaishe da mama, amsawa tayi amma isanta na kan maimunatu dan cikin jikinta yayi girma da yawa sosai kamar mai aihuwar ƴan uku , itako sai aikawa mama da harara takeyi dan ta tsani mama tunda taga take takenta na bibiyar gidan .

“uhm Haisam dama cewa nayi naga kamar Maimunatu bata iya aiki sosai to inba damuwa mezai hana in dawo gidannan indinga temakon ta tunda yanzu naga Allah ya buɗa maka sosai kuma ba ƴar aiki ka ɗauko mata ba ?, Haisam ne yace “to ai mama gara a ɗauko ƴar aikin kamarki ki zo gidannan kina aiki , mama ce tayiwa Haisam daƙuwa tace “kaci gidanku Maimunatu ai ƴata ce inda zan riƙeka haka zan riƙeta dan haka ka ƙyaleni in zauna kawai zan kwaso kayana zuwa su wanki da shara ai kaga su sunfiya sa tsuguno taji da wanke wanke da gyaran ɗaki , Maimunatu dake gefe ta taɓe baki tace “taɓɓ wlh nikam anaso a takuramin ne yo banda takura meye nawani zuwa ace za’adinga yimin aiki dacan wa yake yimin?cikin zafin nama Haisam ya miƙe zai wanka mata mari dakatar dashi mama tayi da cewa kull ba’a taɓa mai ciki koda gaba karkayi kuskuren sake kwatanta hakan , sunkuyar da kansa yayi yace “to mama , kidawo da kayanki kawai tunda ankwashe kayan ɗakin can , cikin murna mama tadinga sa musu albarka , miƙewa tayi tana duban Maimunatu tace “to barin tafi sai nadawo ko kallonta Maimunatu batayi ba ta ɗauke kai gefe .”

Washe gari tun da safe Afnan ta samu tayi wankan tsarki tayi sallahr asbah , dawowar Abdallah daga masallaci kenan ya tarar da ita tana sallah , farinciki fal zuciyarshi zama yayi gefe gado yana ƙarewa kyakyawar fuskarta kallo tare da lumshe ido , ƙarar wayarsa ce ta fargar dashi aga kalon Afnan , aslm yace “cikin firgici naji yace “ganinan zuwa kuyi dashi asibiti , Afnan dake gefe gabanta na faɗuwa tunda taji ance asibiti tasan ba lafiya ba, juyawa tayi bayan ta shafa adu’ar tace “barka da safiya mijina , ywwa barka Abdallah yace dan hankalinshi na gurin masu zuwa asibiti ƙara kai dubanta tayi gareshi tace “waye babu lafiya ?”Sadiq ne Abdallah yabata amsa a taƙaice , waye Sadiq ? yarona ne Abdallah yace ,nizan fita zan dubasu , in da wata matsalar ki kirani a waya ,to Afnan tace jikinta a sanyaye taƙara da cewa”Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa.

Da isarshi asibitin ya samu anba Sadiq gado , Sadiq yaro ne da a ƙalla zai kai shekara goma sha takwas mahaifiyarshi wato mata agun Abdallah sunanta Shamsiya ,gaishe da Abdallahn tayi yace “mata ya mai jikin da sauƙi tace “to ya amarya washe baki Abdallah yayi tare da cewa amarya tana lafiya tana gaisheki idanun sa na kan Sadiq dake bacci ta galla masa harara tace “ina amsawa , duba agogon dake ɗaure a hanunsa yayi yace “yanzu ƙarfe ɗaya saura zanje zuwa anjima zan dawo , miƙewa tsaye tayi tasha gabansa tace “ciwo ya kori komai maiyasa bazaka bawa ɗanka kulawa ba ? Abdallah ne yace ” kiyi haƙuri zan dawo anjima, ƙwafa tayi batare da ta ko lallesa ba ta koma ta zauna zuciyarta babu daɗi, kai tsaye motarsa ya nufa tuƙi yakeyi hankalinsa na gurin Afnan cikin zuciyarsa yana cewa “inda nayiwa wanan rana buri bazan bari yauma nakuma rasa farinciki ba , gudu yake yi a titi ikon Allah ne ya kaishi gida , ƙarar horn ɗin da mai gadi yaji ne yasashi tashi buɗe ƙofar da azama , Abdallah ya shige dan baima lura da gaisuwar da baba mai gadi yake yimasa ba.

Zaune take a katafaren falonta mai sanye da kayan more rayuwa faɗin tsaruwar falon ma ɓata lokaci ne dan koni tsayawa nayi ina ƙare masa kallo , hangota nayi kwance a ɗaya daga cikin kujerun da alama waya takeyi ,

Jinayi tace ” momy nasami tsarki kuma nayi amfani da magun gunan tun ɗazu , daga can ɓangaren momy tace “yawwa ƴar albarka dan haka nake sonki kinsan su masu matan nan wlh sai da gyara jiki kuma insha Allah nasa a tahomin da wani haɗaɗen magani da turare insha Allah zakisha mamaki .”

Dariya Afnan tayi tace “momy na kenan Allah ya barmu tare gaskiya sai yanzu na tabbatar aurena da Haisam ba alkairi bane , kinga breakfast ɗina na yau dakuma ranar danazo hmm momy ba’a magana , kwashewa da dariya momy tayi kana tace “ai ba tun yanzu nake nusar dake dai dai ba kinƙi fahimta kice yanzu kin dawo hanya ?gaskiya kam momy ,daganan sukayi sallama ,

Jin sallamar Abdallah yasata miƙewa tare da kashe masa ido , kallon shugar jikinta yayi , can kuma ya faɗaɗa fara’arsa ya buɗe hannayensa duka da sauri ta faɗa jikinsa tare da rungumeshi ta zaunar dashi a palo , oh Allah na gaji , Abdallah yace “lokacin da yake shafo dogon gashin kan Afnan da yasha gyara.”

Ƙara narkewa Afnan tayi tace “baby ka gaji ko ? uhm Abdallah yace” dan wanan shagwaɓar tata tana rikitashi wani lokacin , Afnan ce tace “tashi muje inyima tausa , abin nema ya samu aikuwa cikin azama gogan ya miƙe tare da ɗaukar Afnan kamar jaririya ya kaita bedroom ɗin ɗakinsa …

Cire mata ɗankune yayi da warwaro ya kwanta gefe tare da rungumota sunajin nunfashin juna , am sorry baby kiyi haƙuri dani pls ni mabuƙaci ne !!!…wata azababiyar faɗuwar gaba ne ya ɗarsu a zuciyar Afnan , kasancewarta wayayiyar mace ƴar boko yasa bata nuna masa alamun damuwa ba amma gaskiya a ƙarƙashin zuciyarta tsorone ya dirar mata , idanunsa a lumshe yafara hura mata iska ta kunne yana shafa gashin kanta hakan yasa ta mance da komai tafara maida masa , daganan salo ya sauya zuwa cire …..am sorry nafito kasancewar naga gidan Haisam ana drama .

Da sallama mama ta shigo kasancewar Haisam bai fita ba shine ya amsa sallamar , kayane ta ɗibosu zasuyi kala ashirin ta ajiyesu a tsakar gida , Haisam ne yace “mama zo in nuna miki ɗakin da zaki zauna cikin rawar jiki mama ta miƙe ta bi bayan Haisam , Maimunatu na ɗaki baƙin ciki ya isheta….✍️.

Uzururuka sunyimin yawa bawai ina yimuku wula ƙanci bane kuyi haƙuri kunkusa samun post kullum afuwan my fans .

Ga mai buƙatar karanta littafinnan tundaga na ɗaya zai iya samunsa ta wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 31 & 32

Ganin rana tayi kuma Maimunatu bata fito ba yasa mama miƙewa ta nufi kitchen ta kunna risho kasancewar bata iya kunna gas ba , ruwa ta dora da wake a haɗe dan da alama shinkafa da wake zata girka , fitowar Maimunatu daga ɗaki kenan ta leƙa ɗakin Haisam taga babu kowa ya fita , kitchen ta nufa hango mama tana gyaran shinkafa yasata cewa sannu , washe baki mama tayi cikin rawar jiki tace “sannu ƴar albarka.”

sai da Abdallah ya sami nutsuwa da Afnan sanan ya shafo fuskarta tare da manna mata kiss a goshi , Allah yayi miki albarka duk da wani ya rigani amma dole nayi alfahari da wanan rana gaskiya Afy kin shayar dani zuma , Afnan dake kwance tana kallonshi yana sumbatu ta rungumeshi tare da raɗa masa a kunne tace “karka damu mijina koda wane lokaci ina tare dakai , wanan maganar ta Afnan tasa shi jin daɗi sosai ya miƙe ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa , wankan tsarki ta fara kana yayi na sabulu ,Afnan miƙewa tayi ta ciro masa boyel mai laushi baƙi da farar hula da farin takalmi kasamcewar akwai wasu kayan nasa a ɗakinta ..

Yana fitowa ta shige itama wanka tayi tare da na tsarki ta fito kanta ɗaure da towel na tsane ruwa ,

Samunsa tayi har ya shirya sai zuba ƙamshi yakeyi ga wani sihirtaccen kyau da yayi mata ..

Kamo hanunta yayi tare da ɗorata kan cinyarsa yace “gaskiya zanje in dawo ki kularmin da kanki ,

Ƙara marai rai cewa tayi ta ce “gaskiya nagaji da fitarnan inace hutun two weeks ka ɗauka ,

Buɗe baki Abdallah yayi yace “wane ni yazanyi da jama’ar da suke jirana in dawo ?”

Uhm to yanzu ina zaka ?”zanje duba Sadiq ne wai sun dawo gida ..

Kishi ne ya tasowa Afnan amma dole ta danne dan tanason samun fada a zuciyar Abdallah ,ka gaishe shi shida momyn ‘nashi oky Abdallah yace “yana ɗaura agogo a hanunsa,

Shafa fuskarta ya ƙarayi kana yace “natafi Allah ya tsare Afnan tace “fuskarta ɗauke da murmishi .”

da isarshi gidan takalma ya gani a ƙofar ɗakin zasukai na mutum huɗu ,nazari ya kamayi dan lokacin magrib ta farayi , jiyo surutun su yayi suna cewa ai wlh hajiya ki kaɗa ƴar banza …

Kina zaune da mijin zata fara kawo miki cikas nifa dama bason aurannan da yayi nakeba duk da bani ke zama dashi ba …

Momyn Sadiq ce tace “uhm ni yanzu ma kullum sai nayi kuka sbda ya sabarmin da komai nasa , wata daga gefe tace “uhm nidai banida ta cewa tunda tun farko baki ɗauki shawarar mu ba ….

Akwai wani hatsabibin malami wanda yataɓa yimiki aiki har kika samu cikin Sadiq .

Tagumi ta zuba alamar tunani , momyn Sadiq ce tace “wlh wanan karon bazan aikata zina ba inaji ina gani ,

Nice ban jira lokaci ba ai likitoci sunce akwai lokaci dagani har mijina muna aihuwa ,

taɓe baki sukayi tare da miƙewa sukace to kizauna ta kasheki karkuma ki neme mu , fashewa tayi da matsanancin kuka ta miƙe tsaye tana takowa gabansu tace …

To ni mezan sa boka yayi mata ?” sallamar da sukaji ne yai sanadiya faɗuwar gaban momyn Sadiq ta dafe ƙirji suko sauran ko a jikinsu sukayi waje kowacce na kallon Abdallah .”

Zama tayi jugub a kujera tana share gumin da yake karyo mata tare da mai maita innalilahi a zuciyarta .

Abdallah wayarsa ya ciro yafara danne danne amma inka lura dashi sosai hankalinsa a tashe yake ,

Ko kaɗan bata ƙaunar taji yayi mata magana hakan yasata miƙewa ta nufi hanyar da zata sadata da bedroom ɗinta keee!!! taji Abdallah yace ” cikin tsawa juyowa tayi batare da tace “komai ba ,

Kuma maida hankalinsa kan wayar dake hanunsa yayi a zahiri kukan zuci yakeyi dan nafili yaƙi fitowa .

Takai wasu mintuna a tsaye a gurin dan yanzu tsoransa ma takeji kar tayi ƙwaƙwaran motsi ya yanke mata mumunan hukunci,

Tashin hankali gami da rashin ƙaunar maman sadiq ya darsu a zuciyar Abdallah ,mai maicin da zuciyarsa take yimasa shine zina ?zina tayi kenam ba ɗana bane ?” ya ilahi ya riƙe kansa da yake sara masa.”

Ya ɗago kansa ya dubi maman Sadiq yace “naji duk abinda kuke ta taunawa akai dame na rageki ci ko sha ko tufafi kokuma haƙinki ne bana saukewa kiji tsoron Allah ,

Yaci gaba da cewa kin cuceni kin cuci ɗanki dan bazance ɗana ba ,

Momyn Sadiq jira take taji kalamin Abdallah na ƙarshe yace ya yafe mata sai taji akasin hakan yace ” na sakeki saki biyu inkin sami miji kiyi aure kuma ki tafi da ɗanki banida alaƙa dashi…..✍️.

Fans kuyi haƙuri kwana biyu kunjini shiru nayi tafiya ne amma na dawo ganin sharhinku shine zai sa kusami pagin gaba amma in bangani ba sai bayan sallah gaskiya 🤗.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*

 

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

 

EPISODE 33 & 34

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kasa tsayuwa tayi a gurin saboda wani jiri dake ɗibarta ta durƙusa kan guwaiwar ta tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu oh ni ƴa su ina zansa kai na ,rarrafowa gabansa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace “dan darajar iyayenka ka yafemin wlh ba ‘ason…!!! wani wawan mari ya wanketa dashi kana ya miƙe tsaye yace “kar in dawo in samu kina gidannan wlh sai kinyi dana sani , ya fice zuciyarsa na suya , driving yakeyi amma hankalinsa a tashe yake ,ikon Allah ne ya kaishi gida , ko horn baiyi ba ya buɗe murfin motar ya fice tare da buɗe get ɗin , mai gadi dake zaune a wata farar kujera ta roba ganin Abdallah ya shigo a fusace ya miƙe yana cewa Alhji barka dai ywwa kawai yace .”

Bai jira ƙara jin wata maganar ba ya shige ciki , mai gadi ne ya jinjina kai ya ƙwalawa driver kira da sauri ya taho sabda shima ya lura da yanayin Alhajin .”

Wangale get ɗin yayi ya shigo da motar, sukazo suka zauna kafa hirar shigowar uban gidan nasu ,

Bai sameta a palo ba ya nemi guri ya zauna , kashe tv da yaketa ƙararsa shi kaɗai yayi , ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya abubuwan da suka faru tsakaninsa da momyn Sadiq suka fara dawo masa ..

Cikin zuciyarsa yace ” ko kaɗan banyi dana sanin rabuwa dake ba dan bansan ko bada ni kaɗai kike taraiyya ba .

Shigowar Afnan ce ta sanyashi katse tunanin tare da faɗaɗa fara’arsa irin karta gane yana cikin wani hali , takowa takeyi cikin isa da ƙasaita ,
kai kace ƴar wani sarkin ce .”

Zama tayi gefensa tare da ratayo hanunta a kafaɗarsa tace “lafiya mijina ? naga kamar kana cikin damuwa ” a’a Afy kaina ke ciwo yanzu ma so nakeyi na ɗan kwanta ..

Badan ta yarda ba ta ƙyaleshi amma ta fuskanci akwai abinda yake damunsa jikinta a sanyaye tayi bedroom ɗinta ta fashe da kuka ,

jiyo kukan yayi lokacin da zaiyi hanyar bedroom ɗinsa ya dawo zuwa ɗakin nata , dole ya jata gado ya rungume ta yana jijiga ta kamar baby har bacci yai gaba da ita .

Ajiyar zuciya ya sauke can kuma sai wasu zafafan hawaye suka sauko daga idonsa , kallon sa ya kai ga Afnan dake ta bacci hankalinta kwance amma fuskarta duk alamun hawaye gasunan ..

In ya tuna Sadiq ba ɗansa bane sai ya saki wani mahaukacin kuka mai ban tausayi , yana cikin hakan ne yaji ring ɗin wayarsa ..

Kasancewar ya bar wayoyinsa a palo ya miƙe a hankali ya isa gurin wayar da ɗaga warsa, my son yagani sai da yakuma zubar da hawaye sanan ya ɗaga wayar, kafin yayi magana yaji Sadiq yace “dady na koma school fa gashi yanzu banida wasu kuɗi a hanuna , jimm Abdallah yayu can kuma yace “zan tura maka zuwa anjima inna fita , nagode dady Sadiq yace ” lokacin da Abdallah ya jiyo ƙarar tafi da dariyaku ya kashe wayar , kirane yakuma shigowa a karo na biyu Abdallah ya ɗaga a fusace yace “wai lafiya ?am dady wayar momy ce tun jiya a kashe dan Allah in kuna kusa ka bata , bana kusa Abdallah ya bashi amsa a taƙaice ya kashe wayar duka ma.”

Lefin momynsa yana neman shafarsa ko da yake yanata shawara da zuciyarsa akan ya fito ya faɗawa Sadiq ba shine ubansa ba sai kuma ya kawar da tunanin , ya shafe mimtuna a gurin yanata tunani iri iri amma babu wata mafita da yaga ta dace , kwanciya yayi a doguwar kujerar tare da ɗaga kansa sama , yau ɗinnan a tunani ya ƙare , bayan Afnan ta tashi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga baƙa mai adon faraten dutsina ba ƙaramin kyau tayi ba , samun Abdallah tayi kwance a palo bacci ya ɗaukesa gashi lokacin ƙarfe shida na yamma , kasa tashinsa tayi kwai ta miƙe tayi hanyar kitchen,

Abinci mai sauƙi ta yi doya da miyar ƙwai dan yau tunda taga mai gidan babu walwala take jinta babu daɗi , tana gamawa ta dawo palo ta zauna gefensa tana shafa fuskarsa a hankali , buɗe ido yayi yana salati “ana kiran sallah fa , oky yace “tare da miƙewa ya nufi hanyar toilet , bin bayansa da kallo tayi tana mamakin sayawarsa daga fitarsa zuwa yanzu , kodai wani ya ɓata masa rai ne ? ta tambayi kanta , dawowarsa ce yasata ɗago kai tare da cewa Allah ya tsare amen yace “yasa kai ya fice….✍️.

Babu sharhi 🤨?.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*

 

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 35 & 36

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Washe gari safiyar litinin (monday) Maimunatu ta tashi da wani matsanancin ciwon mara da baya , jin shiru har ƙarfe takwas bata fito ba yasa mama nufar ɗakin , jiyo nishin Maimunatu yasa hankalinta mugun tashi ta shigo a guje , ganinta tayi durƙushe tanata juyi idanunta sunyi ja , subhannallah mama tace ” tare da kamo mai munatu ta gyara mata tsuguno , yau kam babu magana kuma bata yiwa mama musu , ganin abin ya wuce tunani gashi dai alamun aihuwar ce amma har yanzu shiru , sake Maimunatu tayi ta wuce ɗakin Haisam dake bacci ..

Bugun ƙofar takeyi tana ƙwala masa kira , a tsorace ya taso ya buɗe ƙofar yace “lafiya mama?” inafa lafiya maza fito kazo ka ɗauko mashin ɗinka muje asibiti wanan yarinyar inaga aihuwa ce , ai dajin tace aihuwa ce yasashi azamar sauya kaya ya fito da sauri mama ta kwaso kayan yaro , kasancewar ba zaman daɗi sukeyi dashi ba amma yana siyo kayan jarirai , kai tsaye suka nufi asibiti ,da isarsu aka wuce ,da Maimunatu ɗakin aihuwa ..

Mama da Haisam sun zuba tagumi kawai jira suke suji ance ta aihu ,

Ɓangaren Maimunatu likitoci ne zagaye a kanta sunata aiki ,itako batasan inda kanta yake ba ,adu’a sukeyi duk wacce ta faɗo musu amma kaf ɗinsu hankalinsu ya fara tashi , tun ƙarfe tara na safe gashi yanzu ƙarfe biyar na yamma , wata likita ce ta fito fuska babu walwala ganin hakan yasa mama miƙewa da sauri Haisam da bai san ko mai ke faruwa shima ya miƙe , hango likitar yayi ta doso gurin su …

Tun a zuciyarsa yafara mai maita innalilahi haka mama itama , likitar ce tace “waye mijin Maimunatu a nan ko kai ne ? ta nuna Haisam ,cikin tashin hankali yace ” nine ok “kazo office munason ganinka , to Haisam yace “jin ba abinda yake tunani bane yasashi sakin fuskarsa ,

Da sallama ya shiga ya nemi guri ya zauna likitar da tazo ta kirashi ne takuma cewa malam muna mai baka haƙuri akan rashin matarka , a razane Haisam ya miƙe daga zaman da yayi yace ” ban gane ba ?”.

Kina nufin Maimunatu ce ta rasu ? wani doctor dake gefe tunda Haisam ya shigo bai ce komai ba yace ” abokina kayi haƙuri kulli nafsin za’ikatull maut kayi haƙuri adu’arka take buƙata ..

Da zamuyi maka magana kasa hannu ayi mata aiki to muna tunanin aihuwar da saura amma Allah da kansa ya ƙarɓi abarsa .”

Mama jin Haisam shiru bai dawo ba yasata neman gurin zama amma tanajin yawan faɗuwar gaba , hangoshi tayi yana share hawaye kamar ƙaramin yaro , a saninta Haisam bai cika zubar da hawaye ba inba babban abu ne ya faru ba , lallai akwai abinda ya faru mama ta faɗa a fili “.

Yana isowa gurinta yace ” mama ta mutu !!zaro ido mama tayi tanajin abin kamar a mafarki ƙarya kakeyi Haisam ,waye ya mutu ?Maimunatu ya bata amsa innalilahi ta bazama cikin asibitin da gudu , binta Haisam yayi yana ƙwala mata kira amma ina sai da tayi ɗakin da gawar Maimunatu take ta bude gawar da aka lulluɓeta da farin mayafi , salati ta dinga rafkawa tana surutai marasa amfani ..

Ashe tafiya zakiyi kintafi da ciki , tsayawa Haisam yayi a bakin ƙofa idanunsa cike da hawaye yana share wa wani na biyo baya , haka likitocin suka shigo suka samesu suma sun tausaya musu amma dayake lamarin na Allah ne da yafi kowa so ya karɓi abinsa suka cigaba da yiwa su Haisam nasih.

Haka ‘asibitin suka bada mota aka sa gawar Maimunatu suka nufi gida , tun a hanya Haisam yafara sanar da ƴan uwansu dana Maimunatu , mahaifiyarta ko kuka tasa tana ihu ,

Kafin su ƙaraso an ɓalle ƙofar gidan mutanen kusa sunata shigowa , da shigarsu aka wuce ta gawar ɗakinta aka ɗibi ruwan ɗumi aka yimata wanka aka karɓo likafani a masallaci , aka suturce ta, kasancewar iyayenta duk sunzo ana fito da gawar ta mahaifiyarta ta miƙe tana ihu wani malami ne ya fara yimata wa’azi da ban haƙuri , kuka kam ansha haka aka kaita makwancin ta rai kenan baƙon duniya.

Gida ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi mama kam hauka ne batayi ba amma tadingi kuka sosai ga cikin babu tadinga mai maitawa a cikinzuciyarta…✍️.

Follow me on wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*

 

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

 

EPISODE 37 & 38

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Duk abinda Sadiq ya nema Abdallah ya tura masa harda kuɗi masu yawa , washe gari yayi sammakon zuwa gidan su momyn Sadiq ,samu yayi ta kwashe duk wani kaya nata durƙusawa yayi a gurin ya saki wani kuka mai cin rai a fili yace ” ina sonki wlh ina sonki amma soyayyar da nake yimiki bazai sa inkasa yanke hukunci dai dai da abinda kika aikata ba , fuskarsa tayi shaɓe shaɓe da hawaye kamar ƙaramin yaro , miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗinsa ya kwanta zuciyarsa fall baƙin ciki da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarsa , ya daɗe yana baccin tare da mafarkai iri iri na ban tsoro rin ɗin wayarsa ce ta tashe sa daga bacci salati yayi kana ya janyo wayar ya danna ya kara a kunne ,wlkslm naji yace ” daga ɗayan ɓangaren akace ango hutun ya isa haka ma’aikata nada buƙatar ka kuma kasan gobe za’ayi taron cika shekara biyar da buɗe ma’aikatar mu bamuyi wasu shirye shirye ba? innalilahi Abdallah yace “.

garin ya hakan ta faru kash mutumin da yakira ne yace “bye zai zuwa goben , tom kawai Abdallah yace ” kana ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa ya cigaba da tunane tunanen sa , da sauri ya saka kaya ya fice daga gidan yaukam kowa ya gansa yasan babu lafiya kasancewar ko mai bai shafa ba , abubuwa sun taru sun yi masa yawa ga matsalarshi da momyn Sadiq ga gurin aiki .

Washe gari tunda ya dawo daga masallaci da asbha bai koma bacci ba ,shirye shirye yaketa yi na inda lamarin taron zai kasance , dan ma abinka da mai kuɗi kira yakeyi a waya a gudanar da komai , bayan Afnan tayi sallah asbha ta nufi ɗakinsa da sanyin jiki , samunsa tayi a zaune da wasu takardu a gabansa da alama na aikin ne , zama tayi dab dashi can kuma ta durƙusa tare da cewa ina kwana “lpy Abdallah yace “ya kike ina lpy sai dai tunanin ka , riƙe kai yayi yasan ko kusa bai kyautawa Afnan ba , naƙin kulata kwana biyu janyota yayi kusa dashi tare da rungumeta , hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba , dan tana tunanin ko tayi masa laifi ne ? amma yanzu ta gane uzuru ruka ne sukayi masa yawa .”

“Afy zoki shirya , Abdallah yace “lokacin da yake fitowa yana sanye da shadda ruwan toka sai ɗaukar ido takeyi , ganinan zuwa sweety Afnan tace ” kasancewar tun ɗazu ya gaya mata sunada taro , itama shaddar tasa kalar tashi ta ɗauko mayafi da takalmi marar tudu da jakarta fara kalar takalmin da wani glass baƙi ta sanya a idonta , wow gaskiya Afnan tayi kyau dayake ɗinkin doguwar riga ce ba ƙaramin fito da ƙyan dirinta tayi ba kallonta ya tsaya yi sbda shima tayi masa kyau , turare ya ɗauko ya fesa mata yana sakar mata murmishi , suna gamawa suka rufo ƙofar suka nufi gurinda aka tanadar domin ajiye motoci , da ganinsu driver ya taso da sauri ya buɗe mota suka shiga back side ya rufe , shikuma ya shiga gaba , hira sukeyi jefi jefi a motar , amma fuskar Afnan da alamun damuwa , Abdallah sam bai lura da yanayin ta ba kasancewar yanata amsa wayoyi na mutane , faɗuwar gaba takeji a kamar akwai wani abu dazai faru a gurin taronnan , wata zuciyar tace “ki koma gida kawai ‘ ina babu halin yin hakan yasa ta daure zuciyata tare da mai maita innalilahi.”

Sunyi tafiya mai nisa sannan suka iso tsararren gurin taron , misalta tsaruwar gurin ma ɓata lokaci ne gurin yashe gyara kasancewar hidimar ta manyan mutane ce abin ya birge , bayan angama bada kyau tutuka Abdallah ya tashi yayi jawabi akan cigaban kamfaninsu dakuma inda zasu dinga tafiyar da al’amura cikin sauƙi , Afnan dake gefe sai murmishi takeyi , hango wata farar budurwa nayi tana sanye da riga da sikel ɗan kanti ta yafa wani tsdadden mayafi mai kyau fuskarta dauke da kwaliya tanada manyan idanu farare ga gashin kanta dogo , dan anyi mata kitson gaba , cikin yanga take takun hanunta ɗauke da farar takarda dakuma flawoyi ta isa gaban Abdallah , ganin haka yasa Afnan jin wani mugun faɗuwar gaba kamar an caka mata kibiya , lokaci ɗaya murmishin ya ɗauke daga fuskarta hango wanan budurwa suna gaisawa da mijinta kuma hannu da hannu har tana lumshe masa idanu , kuma duk da haka bata bar gurin ba , baƙin ciki ne ya cika zuciyar Afnan ta miƙe tabar gurin , gurin da sukayi parking motarsu ta isa ta buɗe motar ta shige ciki , kuka ta fashe dashi kamar wacce aka aikowa da mutuwa,

Maiyasa maza suke haka ne ? .

wayarta ta ciro tafara dannawa amma hankalinta yana gurin wanan budurwa to wacece ita ?” babu mai bata amsar tambayarta a halin yanzu yasata yin shiru tare da ƙara fashewa da kuka.

Leƙenta Abdallah yakeyi amma sam bai ganta ba , budurwar dake gefensa ta lura da akwai abinda yake nema tace ” maiya faru big boy ?” murmishin yaƙe yayi kana yace ” nup bkm ina duba wani friend ɗina ne naga ma kamar ya tashi , oh budurwar tace ” ina matarka ne ? batanan amsar data fito daga bakinsa kenan , hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa budurwar ba , tace “zamuje shan is cream ?sai da yayi jim kafin yace ”to babu matsala yarasa mai yasa baya iya yimata musu ko kad’an , fad’ad’a murmishinta tayi tace ”big boy har yanzu kak’i bani amsar tambayar da nayi maka shekara d’aya data wuce ko ?”.

Jiyo alamun tashin taro sukayi hakan yasa hankalin Abdallah komawa gurin Afnan ya ilahi , yace ” lokacin da ya tuna da ta dad’e da tashi a gurin gashi ko kiranta a waya baiyi ba , dafe da goshi ya yi hanyar fitowa ganin baiga motar tasu ba yasashi jin tsoro kardai Afnan ta tuk’a motar nan ne tayi gida ? yana tsaye yanata tunani kala kala har mutane suka fara fitowa suna mik’o masa hannu suna gaisawa annan ma sai da ya k’ara bata lokaci , janye jikinsa yati ya koma gefe guda ya danna number driver ✍️.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

 

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 39 & 40

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Ring d’aya driver ya d’auka tare da sallama yace ”ranka shi dad’e na dawo d’aukarku nasamu babu mota ? dafe kai yayi tare da cewa “innalilahi yanzu ina Afnan ta shiga oh Allah driver ne ya k’ara magana a karo na biyu yace ” mai gida wani gurin tayi ? shut up your mouth wlh zan sa6a maka , kana yaja wayar ya kashe , budurwar nan mai suna Husna ce ta tako har kusa dashi tace ” hi my man mutafi ko ? juyowa yayi a fusace zai yimata masifa ya kasa , shafa k’eyarsa yayi yace ”mutafi , wani irin murmishi tayi wanda ita kanta tasan ma’anar hakan , motarta suka shiga tana driving shikuma yana gefenta , Afnan na zaune a cikin mota a can gefen titi kasancewar gabas sukayi ba lallai su ganta ba amma ita ta gansu musamman lokacin da Husna ta rik’o hanun Abdallah , runtse ido tayi tare da ambaton Allah.”

Yau watan Maimunatu daya da rasuwa duk da bawani shiri sukeyi da ita ba amma rasuwarta ta dakeshi sosai , haka yakejin gidan shiru babu hayaniyar kowa , wanka ya shiga bai jima ba ya fito daure da towel a k’ugunsa ya wuce d’aki ya shafa mai ya sanya riga da wando na jeans , yayi kyau ba laifi amma ramarsa ta fito , kulle k’ofar yayi da key kana ya nufi gurin mashin d’insa fita dashi yayi waje ya kulle k’ofar wajen ya tada mashin d’in ya nufi gidansu ,da sallama ya shiga babu kowa a tsakar gidan hakan ya sashi nufar d’akin mahaifiyarsa , samunta yayi a zaune da wata yarinya a gaba a k’alla zatakai shekara goma sha biyar suna hira zama yayi a kujera y’ar tsugunno ya gaida mama ‘ amsawa tayi cikin fara’a tare da cewa ya kasuwa Alhmdulilha Haisam yace ” yana duban yarinyar , wacece wannan mama ?” Uwale ce mama ta bashi amsa , Uwale kuma eh man yarinyar yaya Halilu a k’auyen kano suke zaune ba lallai ka santa ba raboka da garin tun kana yaro , jin jinawa Haisam yayi , mama ce tace ” baki iya gaisuwa ba ko ?washe hak’ora tayi tace ” ina wuni “lpy Haisam yace ” ya mik’e tare da ajiyewa mama dubu d’aya ya fice Allah yayi albarka tace , to inason yin magana dakai zuwa anjima to mama , Haisam yace ” ya fice .”

Kasancewar ta iya mota yasata tuk’awa a hankali kamar mara jini a jika , ikon Allah ne ya kaita gida , mai gadi najin horn ya mik’e a guje yaje ya wangale get d’in a fusace ta shigo da motar ko gurin parking bata wuce da ita ba tayi cikin gida , tana shiga parlor ta zauna dabas a kan kujera tare da cewa maza !! maza!! daga auranmu harya fara bibiyar wata shegiya , matarshi ma bai taho da ita ba saboda yasan abinda ya shirya dama yaso wulak’anta ni ne , ta saki kuka mai tsuma zuciya , Haisam ne ya fad’o mata ,saurin kawar da tunaninsa tayi gudun fad’awa wata damuwar , dafe kanta daya fara sara mata tayi tana cigaba da kuka ,

tana kunna wayarta da niyar kiran k’awarta sai ga kiran Abdallah nan ya shiga k’in d’agawa tayi saboda a halin yanzu haushinsa kawai takeji batason jin muryarsa a wanan lokacin , miss call biyar yayi mata amma ko a jikinta sai ma k’ara fashewa da kuka da tayi,

Zaune suke a gurin shak’atawa Husna na zuba masa shagwa6a san ranta , tunda ta lura da Abdallah damuwarsa yaji muryar Afnan , tafara amfani da salon jan hankali tana kasheshi da zantuka masu sanya farinciki , aikwa nanda nan Abdallah ya ajiye waya sunata zuba soyayya , sunyi hotuna da yawa a gurin, wani ta dafashi wani kuma suna rik’e hannun juna suna dariya, daga nan suka shiga motar , a k’ofar gidansa ta saukeshi ita kuma ta wuce , da sauri ya fara nocking mai gadi ne yai azamar bud’e masa , yana shiga yace “Afnan ta shigo ?” eh baba mai gadi ne yace tun rana ta dawo amma …shutt, mai gadi ne yaja baki yayi shiru , Abdallah ya k’arasa ciki zuciyarshi a karye , yana shiga ya tura k’ofar parlor n ganin bai ganta a nan ba yasashi nufar bedroom d’inta bubuga k’ofar yafara amma shiru tak’i bud’ewa, Afy ya fara k’wala mata kira , Afnan na kwance a kan gado tana duba sak’onni a whtsapp tana kuka kamar dole , wani massage ne yaja hankalinta , bud’ewa tayi tana dubawa , hotuna ne sunkai kala biyar , bata tsaya karasa kalonsu ba takuma sakin azababben kuka .”

Jiya sautin kukan Abdallah yakeyi har cikin dodon kunnensa amma babu inda ya iya ,d’akinsa naga ya nufa ya dawo hanunshi rik’e da extra key ,bud’e k’ofar yayi jikinsa na rawa ya nufeta ganin tana rawar sanyi kuma tana kuka , d’aukarta yayi ya fice da sauri tayi k’ok’arin hanasa amma ta kasa kasancewar jikinta babu k’arfi ko kad’an , bai tsaya kiran driver ba ya nufi motar da ita ko hijab bai d’aukar mata ba sbda a rud’e yake ya nufi hospital , da isarsu doctor ya nuna musu d’aki anan aka kwantar da Afnan , har yanzu hawaye bai dena zarya akan fuskarta ba , Abdallah da yakejin zuciyarsa babu dad’i ya dubi Afnan yace ” ya jikin?”.

“Cikin k’arfin hali tace ” na warke , cikin zuciyarta kuwa cewa tayi kaci darajar doctor dake zaune da badan haka ba babu abinda zai sa na kulaka ta runtse ido , tana buk’atar hutu doctor yace ”tare da duban Abdallah , to mungode doctor bayan an saka mata k’arin ruwa bacci mai nauyi ya d’auketa , tunda tayi bacci ya sauke ajiyar zuciya , wayarsa ce tafara ring sai da ya kalli Afnan sannan ya mik’e dan a tunaninsa yanzu baccin takeyi , yana fita ta bud’e ido dama k’arar wayarsa ce ta tashe ta , hawayen da sukak’i dena zubowa ne suka kuma zubo mata sharewa tayi tana tunanin halin rayuwa, shiko da fitarsa ya kuma bin kiran suka fara magana shida budurwar , banji me yake cewa ba ya katse wayar , komawa ciki yayi ya nemi kujerar daya rashi ya zauna tare da kallon fuskar Afnan ko ta tashi , ganin tanata bacci ya koma ya zauna lolz

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*

 

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 41 & 42

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

Da yamma bayan sallahar isha Haisam ya shigo gidansu mama samun Uwale tana rera wak’a yayi mai kamada ta y’an k’auye , dariya yasa kana ya shige d’akin , kasancewar mama na sallah yasashi neman guri ya zauna yana k’arewa Uwani kalo , fara ce doguwa tanada dogon hanci sai dai idanunta jajaye ne sbda tana fama da ciwon ido kyakyawa ce amma ba kowa zai gane ba sai wanda ya lura da hakan .”

Mama na idar da sallah ta kalli Haisam tace ” harka dawo to barka , Uwani mik’a masa tuwo yaci , nak’oshi Haisam yace” naci shinkafa gidan abokina Abubakar , to masha Allah mama tace ”tana gyara zama ” dama maganar da nakeson muyi itace wanan yarinya Uwani nakeson a had’a auranku !!!zaro ido Haisam yayi tare da kuma k’are mata kallo tabb ya fad’a a cikin ransa to ni mezanyi da wanan? bashida mai bashi amsa yasashi yin shiru , mama ta fuskanci zabin bai yi masa ba ,tace ” bawai inason cutar dakai bane sonakeyi ka sami nutsuwa aure na k’ara nutsuwa , Uwani na gefe sai boye fuska takeyi a cikin labulen gado kasancewar gadon mai rumfa ne.”

Haisam ne ya dubi mama yace ” ko watnni ba’ayi da rasuwar Maimunatu ba kice nayi aure yanzu ?” sakin bani tayi tana kallonsa kuma tayi mamakin maganar baya yimata gardama akan cikar burinta amma yanzu ya fara kai , nasani mama tace ” tare da wayancewa wanan da kake gani zata maye maka gurbin Maimunatu inkuma kanada wacce kakeso to ka kawota , babu Haisam yace ” a tak’aice , nizantafi to Allah ya bamu alheri mama tace ” tana rik’e baki.

Yau aka sallami Afnan daga hospital labari ya isa gurinsu momy da Antynta batada lpy hankalinsu ya tashi sosai , wace suke kira da Anty wato k’anwar dadynsu itace ta kira su momy ta sheda musu cewar Afnan tana asibiti laulayi ya sata gaba , kowanensu na murna sosai haka suka nufi gidan , basu dad’e da dawowa daga hospital ba sai ga su momy da anty sun shigo , da sauri Afnan ta fito daga bedroom d’inta tana fara’a , oyoyo anty , anty ce tace ” y’ar albarka tako a hankali duk a tunaninsu cikinne da ita , zama tayi kusada anty suka fara gaisawa ,

Ya jiki suka yi mata dakuma cewa dadynta na gaisheta ya gwada lambarta a kashe ,ina amsawa Afnan tace ” ina zuwa ta mik’e , momy da anty ne suka fara cewa masha Allah daughter takusa samun baby , jin alamun tafiyar mutum yasasu yin shiru , Abdullah ne ya fito sanye da shadda fara alamun yayi wanka ya sauya kaya da bak’ar hula da agogo mai ruwan golden ba k’aramin kyau yayi ba , samunsu momy yayi a parlor , yaji kunya matuk’a dan bai lura dasu ba , k’arasowa yayi ya durk’usa ya gaishesu kana yace ” a gaida dady , komawa ciki yayi , jin k’amshi yasashi nufar kitchen samunta yayi tana suyar dankali da k’wai ,rungumota yayi ta baya yana cewa haba my baby ashe su momy ne sukazo shine ko ki gayamin , galla masa harara tayi tare da janye hanunsa , tabbas yasan yayi laifi , had’e hanuwansa yayi alamun bada hak’uri , bata tsaya saurarasa ba ta zuba abincin a plet ta barshi a gurin , samunsu tayi a tsaye da mamaki ta kallesu tace ” anty yanaga kun tsaya ? anty ce tace ” zamu tafi ne a’a ku tsaya dan Allah kuci momy ce taja hanun anty suka fice , jiyo fitarsu yasa Abdallah fitowa da gudu dan yaji alamun kukan Afnan 20k ya dank’a mata a hannu.yace ” yi sauri ki mik’a musu nayiwa driver magana zai kaisu , da sauri ta fice har sun isa bakin get tafara k’wala musu kira anty ce ta tsaya tare da cewa ” mai ya kaiki fitowa keda bakida lpy ,

 

Rau rau tayi da ido ta mik’awa anty kud’in , k’in karba anty tayi tace ” mai muka kawo miki dahar zaki bamu kud’i haka , anty.Abdallah ne yace ”ma ku tsaya driver ya kaiku, suna cikin magana suka hango drivern su yazo d’aukar su nasiha suka k’ara yimata kana ta mik’a musu kudin ta shige gida idanunta cike da hawaye , tana bud’e get ta shige da gudu bata lura da mutum a parlor ba ta wuce da d’an gudunta , Abdallah yarasa wane laifi yayi mata mai girma haka amma yasha alwashin yau insha Allah zai shawo kan matsalar .”

Gado ta fad’a ta kifa fuskarta tafara rera kuka inta tuno hoton data kalla sai sabon kishi ya tashi takuma k’ara volume d’in kuka .

Kwanci tashi asarar mai rai yau satin momyn Sadiq uku a gida iyayenta sun yin Allah wadai da tarbiyar da ta za6arwa kanta , sukanyi waya da Sadiq amma bata ta6a gaya masa bata gidan Abdallah ba ,tana tsoron halin da zai shiga inhar yaji wanan zance.

Tun daga ranar in Haisam ya shigo Uwani 6uya takeyi wai kunyarsa takeji , shiko abin haushi yake basa , yaza’ayi ace y’ar wanan ficikar itace zai aura , rabonsa da gidan yau kwana biyu kuma bai ta6a tsallaken rana ba , abin yaba mama mamaki sosai ,ita kanta tana tunanin kamar bata yimasa adalci baYau kowa keta shirye shiryen komawa gida kasancewar sun sami hutu , tunda Sadiq yake had’a kayansa yaji gabansa yayi wani mumunan fad’uwa bai kawo komai a ransa ba yaci gaba da shirye shiryensa , lokaci ya tafi kowa anzo d’aukarsa shikam baiga walk’iyar motar gidansu ba mamaki ne ya ishe shi dan dadynsa baya wasa wataran ma shine yazo da kansa ya d’aukeshi to yau lafiya ? ci gaba yayi da zama har aka kira sallalhr mgrib babu ko alamun wata mota , mai gadin makarantar ne ya dubeshi yace ”yaro ni zan kulle makaranta gashi iyayenka basuzo ba Sadiq kam hawaye ne suka zubo a fuskarsa dan yayita gwada number dadynsa shiru ta mahaifiyarsa ma a kashe , ficewa yayi ba tare da yasan inda zashi ba , gashi dare ya fara jakar dake goye a bayansa ya bud’e tare da ciro kud’i , zasuyi dubu goma ganin wani alo ansa hotel yasashi sauke jakarsa yana tunanin shiga ciki to Allah yasa kud’in ma su ishe shi , haka ya kuma d’aukar jakar ya nufi bakin get yana k’wank’wasawa ,

Waye? mai gadi yace daga ciki , nine inji Sadiq d’aki nazo kamawa , jinjina kai mai gadi yayi kana yace ”yaro mai ya raboka da gidan iyayenka kazo wani guri kwana ? bayani Sadiq yayi , mai gadi ya tausaya masa , yace ” to zuwa gobe sai ka nemi gidanku ko eh Sadiq yace” ya shige ciki .”

Ya kama d’aki akan 5k

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

 

EPISODE 43 & 44

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Ɗakine rantsatse mai kyau kasancewar makarantar tasu ba a cikin gari take ba shiyasa kuɗin hotel ɗin yayi sauƙi , bayan yayi wanka ya fitoda ragowar ragowar milk ɗinsa da bredi batare da jiran abin haɗawa ba ya hau sha sbda wata masifaffiyar yunwa dake addabarsa , sai da ya cika cikinsa ya yi salolin da ake binsa sanan tunani ya fara yimasa yawo a kwanyarsa , yana da tambayoyi da dama amma yanzu kam bashida mai amsa masa ,dan tunda yazo duniya harya kai ga shiga makarantu dadynsa bai taɓa bari yayi fushi ba yanzu kam kuka ya fara yana cije lips .

Cikin fara’a ya shigo bedroom ɗinta samunta yayi tana duba fuskarta a mudubi kasancewar kanta na kallon abinda ke gabanta ne yasashi shigowa kai tsaye ba tare da yayi magana ba ,kawai ji tayi an rungumo ta a fusace ta juyo da nufin masifa , kwarjinin da yayi mata ne yasata sunkuyar da kai , ɗaukarta yayi cak kamar baby ya maye gurin zamanta ya ɗorata a cinyarsa , wayarsa ce ta fara ruri babu ƙaƙƙautawa tsaki yayi ya ɗauka , da can ɓangaren Sadiq yace ” dady ka manta tun jiya mukayi hutu ?da yake shima ɗin ɗan duniya ne Abdallan yace ” lla am sorry ai na manta yanzu kana ina ne ?, kuma har ga Allah zuciyarsa bata yimasa daɗi ba tabbas Sadiq zai iya gano komai a dawowarsa hutunnan , Afnan dake gefe yaron ya bata tausayi ta share hawayenta tace ” muje mu ɗaukoshi zuwa gobe , duk da zuciyar Abdallah babu daɗi amma hakan bai kasa sashi jin daɗin kalamin Afnan ba , bayan tayi magrib Abdallah yana masallaci sai da tayi isha’i sanan ta kunna whtsapp , ganin wanan number da tafi kowacce ɓata mata rai tayi saƙonni nata shigowa , hankalinta ne ya kar karta gurin ganin hotuna ne ,

Wannan karon taga abinda ya matuƙar girgizata hotonta tagani daga ita sai pant da bra innalilahi Afnan tace ” tare da dafe kanta da ya fara sara mata nashiga uku a ina nayi wanan hoton? duba rubutun ƙasan hoton tayi fara karantawa tayi ,
Barka da hutawa matar Alhaji Abdallah kinga wanan hotunan naki ?” to kikayi wasa Abdallah zai gansu da idanunsa garama kibini a hankali Afnan ce ta miƙe ta sakawa ƙofar key kana ta dawo ta zauna taci gaba da ƙarewa hoton kallo tana mamakin har da yaushe ta taɓa wanan shigar , cigaba tayi da karanta saƙon taji budurwar tace ” yanzu dai abinda nakeso shine kisa mijinki ya aureni , Afnan jin zancen tayi kamar saukar aradu ,saurin kashe datar tayi tareda dai’daita nutsuwarta takuma shafa powder a fuskarta , jin alamun shigowar Abdallah tayi hakan ya sata ƙara gyara jikinta,

Murmishin yaƙe tahau yimasa dan tana tunanin inhr yaga wanan photon to kashinta ya bushe , Abdallah mutum ne mai lura da ankara ,yana ganin Afnan na wanan yaƙen dariya ce kawai baiyi mata ba amma a zahiri baiyi mata kyau ba kuma ya fara tunanin da akwai abinda yake faruwa da Afnan taƙi gaya masa ne , kasancewar da abinda ya dawo dashi ,ya riƙo hannunta tare da rungumota suka nufi kitchen soyayyen dankalin data soya ɗazu ya zubo musu tana rungume a hanunsa suka dawo parlo a baki ya fara bata tanaci tana zuba shagwaɓa ,amma a ƙasan zuciyarta tana fargabar ranar da sharin wanan budurwa zai hau kanta , kawar da zancen tayi kar Abdallah ya ganota.”

Kwance yake yanata saƙa da warwara shin ko ya amince da maganar mama na auran Uwani ne ? wata zuciyar ce tace ” aikuwa da ka auri ciwon kai , dafe kansa yayi dan yama rasa tunanin me zaiyi wanan wace irin jarabwa ce ? ya tambayi kansa , tashi yayi ya dawo palo kallon palon ya shigayi yaushe rabonsa da shara , tsaki yaja kana ya koma bedroom ɗinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa , yana fitowa ya zauna nanma dai tunanin ne ya addabi zuciyarsa , badan yaji ance Afnan tayi aure ba da babu abinda zai hana ya dawo da ita , wasu siraran hawaye ne suka zubo masa , sharewa yayi ya fara shafa mansa mai ƙamshi , bayan ya gyara sumar kansa ya feshe jikinsa da turare , yaje gaban drower buɗewa yayi ya tsaya a gurin yana tunanin kalar kayan da zai sa tuno kalar kayan da Afnan takeso yayi wato farin boyel da farar baƙar hula da takalmi baƙi sai agogo fari , bayan ya sa ne ya dubi kansa a mudubi yai wani murmishi wanda ya ƙara fito da ainihin kyansa can kuma ya dake tare da ɓata rai , to wa nayiwa wanan kwaliyar ? hhhh lol niko nace Uwani …key ɗin mashin ɗinsa ya ɗauka tare da rufo ƙofar ya nufi waje ,Faty da ta fito daga maƙota ganin Haisam ya tuno mata da Afnan hawaye tabb ƙwayar idonta ta shige gida ,Haisam bai lura da abinda ke wakana ba yaja mashin ɗinsa ya nufi gidansu mama , dan yanason zuwa gurin aiki da wuri.

Da isarshi anguwar tasu ya hango Uwani taci ɗamara tana shirin faɗa da wata budurwa wacce a shekaru ta zarce ta amma tana shirin faɗa da ita taɓɓ , Haisam ne ya jinjina kai kana ya tada mashin ɗinsa ya nufi gida , yana shiga ya sami baba a kan kujera ƴar tsugunno yana shan kunu , baba na ganin Haisam ya hau washe baki yana fara’a , durƙusawa Haisam yayi ya gaida baba amsawa baba yayi yace ka shiga ciki a zubo maka kunun naƙoshi Haisam yace ” tare da miƙawa baba dubu biyar , baba zai yi magana Haisam yace” baba kayi shiru kawai ,share hawaye baba yayi kana yace ” Allah yayi maka albarka Allah ya baka mata tagari Allah ya yalwata arziƙinka , dajin wanan adu’ar sai da jikin Haisam yayi sanyi sosai,

 

Saurin miƙewa yayi dan kar mama ta ritsashi a gurin , kasancewar da tazara kaɗan tsakanin gurin da baba ke zaune dakuma ɗakin mata , yasa Haisam wucewa can kukan Uwani ya jiyo da robar ɗibar ruwa yayi gashi robar a fashe ,dariya ce taso kuɓuce masa sai ya gimtse , Uwani ce ta kalli Haisam da yabata haushi a rayuwarta ta tsani abu ya faru da ita aƙi jajanta mata tace “ɗan yaya ɗan gayu wlh kayiwa wanan yarinyar magana dan ni ba sa’ar wasanta bace tamm,

Kallon inda take magana da girgiza yayi bai ce mata komai ba ya nufi ɗakin mama , shiga yayi ya zauna kasancewar ta shiga wanka , Uwani da baƙin ciki ya isheta kasa zama tayi a ɗakin tayo waje , mama ce ta hangota a zaune bakin ƙofa tana bubuga ƙafa alamun masifa , a ‘ a Uwani me kuma ya faru?” fashewa tayi da kuka tace ” ina cikin ɗibar ruwa a famfo shine wata gardiyar budurwa tazo ta janye bokiti na tasa nata ,shine nikuma na janye nata shine suka yimin taron dangi harda fasamun bokiti , Haisam tun yana dariya a ciki ciki bai sani ba ta yanzu harda ƙya ƙyatawa maganar yarinyar na sashi dariya

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

EPISODE 45 & 46

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Mama ce ta shigo tace “wato kanaji tana kuka baka fita kaga wacce suke faɗan da ita ba ? sunkuyar da kai yayi tare da cewa mama ai tafi mai faɗan ƙarfi , hakan ya kuma tunzura Uwani tukuma fashewa da kuka ,

Safiyar Laraba ƙarfe 7:am dai dai Afnan ta shiga wanka sbda zuwa ɗauko Sadiq tunda Abdallah ya lura da harda wanke kai zatayi dan yaga ta ɗauki shampo , ya ɗauki wayarta cikin azama yafara bincike ko ina na wayar gallery ya shiga , mai hankalinsa yayi ga hotunan wayar gana bikinsu gana ƙawayenta , gurin hotunan whtsapp ya shiga cin karo yayi da hoton ta daga ita sai pant da bra innalilahi Abdallah yace ” ya cigaba da bincika wayar sai kuma ya ga hotonsu shida husna , kansa ya fara ɗaurewa a ina husna ta san numbar Afnan ? dama sunada alaƙa da ita ne ? komawa whtsapp yayi anan yaci karo da lambar Husana sbda ya haddace ta a kansa ba tun yau suke tare ba, gir giza kansa yayi tareda cije lips ɗinsa , yasan sharrin Husna fitowar Afnan ne ya sanyashi ƙare mata kallo dan ya riga ya ajiye wayar bayason ta fahimci akwai wata matsala , janyota yayi ya kaita gaban drees mirror ya zaunar da ita gaban stool ya shafa mata mai kana ya shafa mata hoda , taƙi sakewa dan tana tunanin yaga pic ɗin ,

Kasancewar yayi nashi wankan bayan ta gama shiryawa suka fito dama driver ya shirya suka ɗauki hanya direct gurin da Sadiq yayi musu kwatance suka tsaya , Abdallah ne ya ƙara kiransa yace ” sun ƙaraso , daga can ɓangaren Sadiq ya ratayo school bag ɗinsa ya fito bayan ya bada keys ɗin ya nufi bakin get , yiwa mai gadi sallama yayi ya buɗe murfin get ɗin , hango motar dadyn yayi ɗan nesa da da get ɗin , ya ɗanyi tafiya mai tsayi kana ya iso , ba tare da yayi magana ba ya buɗe gidan gaba ya zauna yai kicin kicin da rai ,

Afnan ce tace ” ayi mana afuwa , Sadiq dake cika yana batsewa ya dubi side ɗin da dadyn ke zaune yaga bama tashi yakeyi ba , dane danen wayarsa yakeyi hawayen da bai shirya zubowarsu bane suka zubo masa , sharewa yayi ya maida hankalinsa ga kallon titi ,Abdallah ko yana kallon Sadiq duk wani abu da yakeyi yanzu kam ya fiddashi daga cikin jerin ƴaƴansa , tabbas Sadiq baiyi kama da jininsa ba , suna cikin tafiya naji Abdallah yace ” driver juya zuwa wancan titin kaf ɗinsu ba susan ina zasuje ba hakan yasa kowa yai shiru ya zubawa kwalta ido tunda suka shiga layin gabab Sadiq ke faɗuwa , Abdallah ne yace ” is ok bayan driver yayi parking suka fito banda Sadiq da ya zauna bama shida niyar fitowa.”

Wata tsawa Abdallah ya daka masa mai firgitarwa , ba ƙaramin firgita Sadiq yayi ba dan a iya saninsa dadynsa baya ko yimasa kallon banza bare wanan tsawar a tsorace ya fito , shima driver dake gefe lamrin ya matuƙar bashi mamaki dubada irin soyayyar da Abdallah ke yiwa ɗan nasa katse tunanin yayi dan yaga sun shige ciki Sadiq ne a baya kamar wanda aka doka , dan ya firgita matuƙa ,

 

Gidane dai dai misali bazaka kirashi da gidan talakawa ba ,zadai ace gidan masu rufin asiri gidane mai ɗauke da ɗan madai daicin get sai filin tsakar gidan da yake malale da siminti daga can ɓangare hagu wani kasko ne guda biyu masu flawoyi ,ƙofar da zata sadaka da sashe matar gidan itace ƙofar dake kallon ymma kasancewar ƙofofi biyune kusan a jere , babu sashin da Abdallah bai sani ba dan haka ya shige ƙofar dake ɓangaren dama suma suka rufa masa baya , da sallama a bakinsu suka shige matar gidan na tsakar gida tana wanke wanke ta ga su Abdallah , washe haƙora tayi tare da cewa” lalle marhabun barkanku to kai Sadiq ka shiga dasu man jiki a sanyaye Sadiq yayi musu jagora zuwa babban palon gidan , zaune take a cikin ɗaki a gefen katifa taci kuanta ta godewa Allah musamman da sukayi waya da Sadiq ya faɗa mata a hotel ya kwana ta razana sosai , jiyo muryar mamy na kiran sunan Sadia yasata aiyanawa a ranta cewar ai harda Abdallah ma ,

Miƙewa sadiq yayi yahau bankaɗa labule yana duba islam wato autar mamy , bankaɗo na ɗakin da momynsa ke ciki yayi da sauri ya isa gareta ganin hawayen fuskarta yasa shi fara shre mata hawaye ,

Afnan dake zaune gefen Abdallah da sai yanzu ta sami damar yin mgna tace ” ina mukazo ? gidansu momyn Sadiq ya bata amsa a taƙaice , jan bakinta tayi tai shiru kana ta zubawa sarautar Allah ido , mamy ce ta shigo hannunta ɗauke da jug na ruwa da food flaks na abinci ajiywa tayi a gaban su Sadiq kana ta zauna kujera mai kallon tasu , sauka yayi daga kan kujerar yace ” mamy barka da yamma mamy ywwa barka ya gida ya aiyuka lpy lou Abdallah yace” Afnan ma gaisheta tayi kana shiru ya biyo baya , Abdallah ne yace ” nakawo Sadiq ne , da alamun damuwa mamy ta dubeshi tace ” Abdallah naji duk abinda ke faruwa yanzu dai inason kayi haƙuri dan Allah banda tone tone , sunkuyar da kai Abdallah yayi yace ” mamy momyn Sadiq bata kyauta min ba wlh eh nasani , labarin bashida daɗin sake mai maitawa dan Allah kadubi darajar maraici ka maidata ɗakinta , Afnan sai yanzu ta gano abinda ke faruwa cikin sanyin murya tace “dama bakwa tare da mmn Sadiq? ko kulata bai yi ba shigowar momyn Sadiq da Sadiq ne suka shigo palon .”

 

Kallonsa ya kai gareta kana ya sada kansa ƙasa dan jiyakeyi kamar yaharbeta amma bashida mafita , kuma yana tausayawa rayuwar mutanen gidan kasancewar su masu ɗan ƙaramin hali , gashi mamy nason matsa masa oh Allah Abdallah yace ” lokacin da yakai dubansa ga Sadiq ya kauda kansa gefe , shikam ya tsani zina kokuma ɗan zina ,sake kai dubansa gurin mamy yayi kana yace ” da sharaɗi inhar ta amince bazata jemin da Sadiq gidana ba , wata razananniyar ƙara yasa tare da cewa” to waye mahaifina ki nunamin .”

Muryar Sadiq sukaji Afnan ce ta miƙe tare da riƙo masa hannu , cikin kakausar murya Abdalah yace ” karki kuma gigina taɓashi ba jinina bane !!! timmm mamy ta faɗi sumammiya , da sauri Afnan da momyn Sadiq sukayi kanta mai adu’a nayi mai ɗibo ruwa nayi ,duk da haka Abdallah bai dena zazzaga bala’i ba , momyn Sadiq ce tace “inhar kazo kawomin shi ne to , inkuma kazo tayar mana da hankali ne sai ka faɗa , Afnan dai lamarin ya ɗaure mata kai ta rasa wane lamari ne ke shirin faruwa da rayuwarta ?” a zuciyarta take wanan batun , eh duk inda kika ɗauka haka ne , cewar Abdallah dan zan temaka na maidake wlh bacin tausayinki da nakeji babu abinda zai sa na maidake !!!, mamy na farfaɗowa ta tsinkayo maganarshi ta ƙarshe , cikin dauriya dajin zafin kalamin nasa tace ” Abdallah abin bai kai ga haka ba mungode basai ka mayarda ita gidanka ba , daganan ta shige ɗaki , dukaninsu suna tsaye Sadiq ko yabi mamy ɗakinta
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

EPISODE 47 & 48

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Afnan da tun usulinta batason tashin hankali tafara kuka tare da durƙusawa a gaban Abdallah ta riƙo masa hannu , kana tace ” dan darajar iyayenka ka kaida ta , bai yi magana ba sai ficewa da yayi daga ɗakin , momyn Sadiq kasa magana tayi sbda baƙin ciki Afnan ce ta rungimeta suka dinga kuka, bayan fitarsa driver ya shigo a guje tare da cewa hajiya mai gida na mota yana jiranki ,sallama tayi musu kana ta rufawa mai gadi baya , buɗe murfin motar tayi ta shiga suka miƙi titi , babu mai cewa kowa komai , shikam zuciyarsa tafar fasa takeyi kamar garwashi gaskiya da ba zina tayi ba zai iya mai data amma tuna abin ya kasance da haka yana ganin sai dai su haƙura kawai , horn ɗin da driver yayi ne ya tabbatar musu da cewar sun iso gida , buɗe murfin motar tayi da sauri ta fice tana kuka , tana shiga palo ta wuce bedroom ɗinta da gudu ta faɗa gado tana wani irin kuka mai cin rai , ita kam tafi tausayin Sadiq ɗin a kan mahaifiyar tasa , can kuma wata zuciyar tace ” ke meye naki na tausayin sa bayan bakida alaƙa dasu? gaki a cikin matsala ,

Kawar da zancen tayi ta ɗauko wayarta , lambar momy ta dannawa kira ring ɗaya ta ɗauka , sallama Afnan tayi bayan momy ta amsa Afnan tace “ya dady da anty suna lpy momy tace .

“lafiyarki kuwa Afnan?” naji muryar taki tayi kama da ta mai kuka , kuma dai dai ta muryar tayi kana tace ” llah momy wlh ba komai nayi missing ɗinku ne inason zuwa , momy ce tace ” to shine zaki ɓata ranki ? ki kwantar da hankalinki muna lpy karki dinga tada hankali kinga ba ke kaɗai bace , waro ido Afnan tayi kana tace ” momy nikaɗai ce man au wai kun ɗauka cikine da ni ? eh momy tace ” hmm wlh banida komai , cewar Afnan , momy ce tace ” Allah zai kawo ki kwantar da hanlalinki kinji , to tace ” tayiwa momy sallama , numbar anty ummi ta kira dan tasan tayi laifi yaushe rabon da suyi waya.”

Lokacin taga gidan Haisam tana cin azaba gurin mama batada wata uwa banda anty ummi yanzu kuma da ta auri burin iyayenta shine zata watsa mata ƙasa a ido ina , jin an ɗaga wayar ya sata cewa aslamu alaikum , daga ɗayan ɓangaren anty ummi tace ” walaikissalam Afnan kinanan? uhm anty da farko dai ayimin afuwa dan Allah , nasan ban kyauta ba , share zancen anty tayi da cewa karki damu yarinyata ,

nan suka kuma gaisawa kana sukayi sallama , turo ƙofar da Abdallah yayi ne yasata kai dubanta ga inda ya ke , tsaye yake a bakin ƙofa ya zura hannayensa cikin aljihu , ya kallonta.

Zaune suka a wani tsararren palo wanda yaji kayan more rayuwa wannan palo shine zakaji ana yiwa kirari da aljannar duniya , hajiya Maryam ce zaune kusada mai gidan nata wato Alhaji Aliyu mai nera , Alhaji Aliyu mai nera shaharaten mai kuɗi ne na ji da gani , sananne ne kowa ya sanshi a babu wanda zaka yiwa kwatancen sunansa yace ” bai sanshi ba , shine uba ga Husna ƴa ɗaya tilo da Allah ya basu ,Husna tayi karatu sosai musamman ma na boko , har yanzu taƙi fito da mijin aure da zarar Alhaji yayi magana mahaifiyarta zatace guda nawa take karya takura mata , akwai wata rana tana cikin tafiya a motar ta , sai motar ta sami matsala , tana tsaye bakin titi motar Abdallah tazo wucewa , bayan ta sa masa hannu alamar ya tsaya ta roƙesa da ya temaka ya rage mata hanya zuwa gidansu,

Suna cikin tafiya tana satar kallonsa dan Abdallah kyakyawane in baku manta ba , suna isowa tace ” ya bata lambarsa , baiyi mata musu ba ya bata har ya zamo daga wanan rana tana kiransa suna gaisawa , kwanci tashi asarar mai rai , Husna ta fara nunawa Abdallah tsantsar soyayya tun bai san tanayi ba har yazo ya gane , wata rana yazo gidansu badan yaso ba sai cewa da tayi zasu gaisa da mahaifiyarta , yake gaya mata shikam yanada mata , Husna tayu baƙinciki amma kadancewarta wayayya ta nuna babu komai gashi yac” bai shirya yin aure nan kusa ba , itadai a tata zuciyar ta ƙudiri aniyar auransa ko ta wane hali wanan kenan.

Alhaji ne ya dubi Hajiya Maryam yace ” lokaci yayi da zan fitarwa da Husna mijin aure sbda lokutan da na ɗaukar mata sun cika , kukan da Husna ta fara ne yasa su Alhaji juyowa kallonta , kuma bai fasa maganar ba , Hajiya Maryam ce tace “a wanan karon ina goyon bayanka ai tanada samarin ruwan ido ne yasa take rainawa mutane hankali , Husna batada zaɓi banda dole ta karɓi zaɓin iyayenta amma kuka yaci ƙarfinta ,tashi tayi da gudu ta haura samma inada ɗakinta yake , ta faɗa gado tare da sakin wani sabon kukan , tunanin Abdallah da yayi mata nisa tafara yanzu yazanyi duk wata hanya da zanbi dan haddasa musu fitina na kasa dole nabi abinda su hajiya sukeso , da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarta .”

Abdallah ne ya ƙaraso kusa da Afnan ya ɗauketa ya ɗora akan cinya kamar ƙaramar yarinya , raɗa mata yayi a kunne wai two days mai ya sami baby na ne tadena bani kulawa ?” narkewa Afnan tayi kana tace ” nikam babu ruwana da kai , mekuma nayi ? cewar Abdallah , Afnan ce tace ” dan me bazaka dawo da matarka ba ?” walwalar fuskar Abdallah ce ta gushe ya kalli Afnan yace ” zaki iya zama da miji mazinaci ? zaro ido tayi tana kallon Abdallah da idonsa ya ciko da ƙwallah tare da girgiza kai , to inhar bazaki iya ba karki ƙara yimin zancenta akwai maza a duniya bani kaɗai bane autan maza ya kamata kisani babu ni babu momy sadiq!!!!!.

Jin zancen nasa babu daɗi takeyi amma babu inda zatayi dole ta kawar da zance dakuma tinanin momy Sadiq ta rungumi mijinta , rungumota yayi yana shafa mata gashin kanta tare da murza ƴan yatsunta , itama fara yimasa wani salo tayi na daban dama tayi amfani da maganin da momy ta bata , tunda naga Abdallah ya fara harata yasani rufo musu ƙofa nayo waje.

Yau Afnan ta tambayi zuwa gida , daƙyar Abdallah ya barta amma da sharaɗin karta daɗe, tun safe tayiwa momy waya akan gatanan zuwa , kowa na gidan murna yakeyi dan an daɗe ba’a haɗu ba , momy tasa an shirya mata abinci kala kala, dady ma yau bai fita ba sbda yanason su gaisa da ƴarsa ,

Abdallah na fita ta fara shiri tana gyara gado taci karo da kuɗi masu yawaa tunani ta fara ko Abdallah ya mance dasu ne , ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani , Abdallah me mai kiran amsawa tayi tare da cewa ka isa lpy , lpy lou sweety ina kewarki dariya Afnan tasa tare da cewa ” kai mijina daga fitarka ? eh man Afy jinake kamar in dawo , zaro ido tayi kamar yana ganinta tasan inhar sukaci gaba da maganar zai iya dawowa yayi mata haramiyar zuwa gidansu , am sorry Allah ya dawomin dakai lpy mijina akwai tanadin da nayi maka so karkaji komai , nidai fatana karka bari ƴan mata su kallemin kai , dariya sukasa a tare kowa ya ajiye wayar , dafa ƙirjinta tayi kana tace ” my man rigima , tacigaba da shirinta

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

EPISODE 49 & 50

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Biki ya kankama na Haisam da Uwani kasancewar mama tace ” inhar yabarta to yabar mata , badan yaso ba ya amince da abinda takeso tunda bazata fasa ba , fatanshi dai Allah ya sanya musu albarka shikenan , hidindimu akeyi sosai sbda yanzu Haisam kuɗi sun zauna masa ba laifi harya siyi mota mai kyau ya kuma sauyawa gidan nasa fenti komai dai yayi masha Allah ,

Dama tunda iyayen Maimunatu suka zo suka kwashe kayanta ya kulle ɗakin sai yau da za’ayiwa ɗakin fenti ya buɗesa , kowa sai sam barka yakeyi amma ana cece kuce akan amarya ,ranar ɗaurin aure kowanne na dangin mama da magoya bayanta suna farinciki sosai , da yamma za’a kai Uwani tunda taji alamun zuwan motoci tafara kuka ita bazatabi wancan mugun ba , karyazo yana yimata mugunta , kowadai lallaɓata yakeyi tunda Uwani dole sai lallaɓo , tun a mota take rafka salati da koke koke kamar wacce za’a kai gidan yanka , ana isowa ƙofar gidan nanma sai da aka ririƙeta tana neman guduwa ,

Mutane sunga tashin hankali , faɗa aka yimata mai shiga jiki duk rashin kunyarta sai da jikinta yai sanyi , musamman da aka cemata banda yiwa mijinki musu banda yimasa rashin kunya , kasancewar tana tsoron ace wutar jahannama yasata yin laushi da duk wata masifa tata , haka suka tafi suka barta tana kuka , amma a ƙarƙashin zuciyarta tsoron Haisam ne fal.

misalin ƙarfe goma da rabi kowa ya watse sai raba ido takeyi tana daga zaune a tsakiyar gado taji alamun turo ƙofa, shi kaɗai ne sai wata ƙatuwar leda dake hanunsa , gyata zaman ɗan mayafin tayi kana ta kalli ledar Allah yasa kazace , Uwani tace ” lokacin da ta haɗiyi wani mugun yawu , zama yayi bakin gado tare da cire agogon hanunsa ya miƙe , Uwani tashi muje muyi sallah sai da taɗan harareshi kana ta miƙe , kunsan dai mai hali baya fasawa amma a tunaninta ta rage rabi ,

Bakinnan kamar wanda aka ja dan fushi ita ba sallar bace damuwarta cin kazar shine matsalar ta , tana yin alwalalr ta dawo ɗaki ta zauna gefen gado , Haisam na shigowa yace ” tashi muyi sallah ko kulashi batayiba ta miƙe sukayi sallahr ya shafa kanta yayi mata adu’oi kana yayi mata ƴan tambayoyi game da tsarki dakuma wanka da alwalah , ba laifi tayi koƙari ta wanan fanni.

Jira take sai kuma taga ya miƙe ya ɗauko plet da wuƙa ya baje kazar gata ƙatuwa , wani yawu takuma haɗiya , so takeyi taji yace ” mata sakko kuma badan yau sabuwar kunyarshi takeji ba da babu abinda zai hanata daka wawa, sai da ya tsiyaya mata milk a cup kana yace ” bismillah har sikel na harɗeta ta sakko ta zauna ko irin yangar nan babu tafara bawa cikinta tanayi tana lumshe ido mamaki ta bashi, sai ya tuno darensu na farko shida Afnan lokacin da ya shigo ƙin buɗe fuska tayi kuma da ƙyar taci kazar bawata mai yawa taci ba amma ita wanan ko na bakinta bata gama ci take ɗaukar wani.

Tsayawa yayi kallon ikon Allah bata damu da rashin cinsa ba sai suɗe hannu takeyi, da ya gaji da dane dannen wayarsa ya miƙe ya nufi ɗakinsa , a gajiye yake hakan yasashi kwanciya ‘a madai daicin gadonsa bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi .

Saida takusa cinye kazar sanan ta ajiye ragowa a kan table taje ta faɗa gado tana tsalle ashe haka aure yake tabb shine naketa kuka , yasin danasan kullum haka za adingayi da ban tada hankali ba , naci ta yau saura ta gobe yasin su inna zasu ganni nayi mulmul , dahaka itama bacci ya sureta .

magunguna momy ta haɗawa Afnan sbda momy mace ce mai son taga ta mallaki zuciyar miji bata hanyar boka ba , ta hanyar magunguna da turaruka ,da kissa hakan yasa dady yafi sonta itako anty bata ganewa maganin mata kasancewarta bata jituwa da magani shiyasa take masa kallon ko in kula , wasu zafafan turaruka momy ta haɗawa Afnan a wata ƴar leda kana ta ƙara da ce mata kartayi wasa da shan magani dakuma kula da abubuwan da mijinta yakeda buƙata , karkuma ta zamo mai ɗaga murya akan ta mijinta ta zamo mai tausayi da iya kallo dakuma iya tafiya , ta ƙara da cewa ” ta yawaita amfani da turaruka masu daɗin ƙamshi karta dinga barin kanta yana daɗewa batare da ta wankesa da shampo ba .

 

godiya Afnan tayiwa momyn ta , momy ce tace ” bawai na gama bane , abu na gaba inaso kisan wani sirri shi namiji inda kika juyashi haka zai biki tausayi fara’a iya kallo iya tafiya dadaɗan kalami uwa uba kuma ɗaukar wanka da iya kissa ,karki zamo kina zama nesa dashi a yayin da kuke tare ki zamo masa tamkar yayayyar yarinya ina fatan duk waɗannan abubuwan sun shiga kunnenki ,zuwa gaba zan baki wasu muhimman sirrukan , yanzu miƙomin wancan zumar , miƙewa Afnan tayi ta kawowa momy zumar momy ce ta buɗe tare da cewa ki kafa kanki ki shanye ki ɗauko madara a store ki fasata itama ki shanye , akwai dabino a wanan kwanon ki ɗibo kici shima yana temako sosai basai na fayyace miki komai ba.

Kiran Abdallah ne ya shigo wayarta momy ce tace ” ɗaga mana amma ki sanyaya murya , gyara muryarta tayi ta kara wayar a kunnenta tare da cewa aslm my man barka da yamma ykk ya aiki , Abdallah dake zaune a office yana shirin dawowa gida yace ” baby nagaji , ƙara kashe murya Afnan tayi tace ” nima gani a gida nakasa dawowa , whatt Abdallah yace ” ya mukayi da ke ?uhm uhm to ba sai ka biyo ka ɗaukeni ba , ganin momy ta fice daga ɗakin yasata cewa banason in koma inga bakanan shiyasa ban dawo ba, ok Abdallah yace ” to ki kwantar da hankalinki ganinan zuwa dady ya dawo ne ? eh cewar Afnan gurinshi ma zani , to sai na ƙaraso , Allah ya tsaremin kai , amen y Allah cewar Abdallah,

Momy ce ta shigo take cewa Afnan tashi kije dadynku ya shigo ‘ok Afnan tace “tare da miƙewa ta nufi palon dady , da fara’a ya amsa gaisuwarta tare da cewa ya maigidan naki yana lpy Afnan tace sukaɗan taɓa hira ta miƙe domin zuwa shirin tafiya gida ….

 

Yau kwanan Uwani biyar iyakaci ta dafa indomie shine ya dawo abincinta , tun ranar da Abdallah yace ” ta dafa masa ya koya inda zatayi shikenan tasamu shikam yanzu yama haƙura dayin faɗa tunda ba ji takeyi ba ,

Daren talata Haisam ya dawo ƙarfe tara lokacin tana kallo a palo sannu kawai tace “tacigaba da kallonta intaga ana wurga ƙwalo tadinga cewa “banza ka cafe man yawwa nawan , Haisam ya gaji baya buƙatar hayaniya ya fito yana yimata maganar tadena ihu ,harara ta zabga masa kana tace “ni banason gulma kaima zoka zauna ayi kallon dakai.”

Ran Haisam ne ya ɓaci yace ” ni kike gayawa haka ? bata ƙara kallonsa ba sai cigaba da kallon ta da tayi shiko tunanin hanyar da zai gyara mata rashin kunyarta yafara , murmushin mugunta yayi yazo kusa da ita ya zauna tare da jawota jikinsa , zatayi magana ya haɗe bakinsu tare da sakar mata hote kiss masu zafi , nifa ka dena banason iskanci , Haisam ne yace ” biyani kazata , ninace ka siyomin bai ƙara bi ta kan maganar ba yafara shafa mata gashi yana sauke wahalalen nunfashi , jin yafara shiga wani yanayi ya kulle ko ina ya sunkuceta sukayi ɗakinsa , a gadonsa ya kwntar da ita , dukda kukan da takeyi bai hanashi cimma burinsa tare da mayar da ita cikakkiyar mace ba , ya daɗe yana aika mata da saƙonninsa kai kace sabon shiga , Uwani bakifa ya mutu banda kiran wayo babu abinda takeyi sai kuma faɗar Allah zai sakamin ,

Mirginawa gefe yayi tare da shafo ƙirjinta yana ƙara sauke nunfashi tabbas ya sami nutsuwa sosai , yanzu ne ya fara tunanin yarinyar mutane , a razane ya miƙe ya tallafo kanta idanunta shaɓe shaɓe da hawaye , tashi kiyi wanka cikin muryar kuka tace ” wlh bazan iya ba tausayinta ya kamashi ya temaka mata sukayi wanka itakam yanzu ɗaukar ɗan iska rayiwa Haisam .

 

 

LOKACI NA TAFIYA YAYINDA KOMAI KE SAUYAWA CIKIN WATA GOMA.

 

Uwani tasami ciki ta haifi yarinya mace mai kamada Haisam yanzu kam duk wani surkule ta rageshi kuma Haisam ya koyat da iya soyayyar sa haka suke rainonon yarinyar mai suna Aneesa wacce taci sunan mahaifiyar Uwani wato HAJARA .

 

Zaune na hango Afnan a ɗaki da ɗan ƙaramin cikinta wanda zai kai wata uku tayi kyau ta ƙara ƙiba da haske , soyayya a gurin Abdallah sai wanda ya daɗu , Anty wato yayar dady tasami cikon burinta dady ya gina mata gida yakuma siya mata mota da direba sbda mijinta ya rasu tin shekarun baya da suka wuce

 

 

Kowane gida ya yalwatu da arziki dakuma farinciki mama kam tana kula da jikanta dai dai gwargwado .

 

 

ALHAMDULILH ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANAN LITTAFI ABINDA NA FAƊA DAI DAI ALLAH YA BAMU IKON CIGABA DA RUBUTA DAI DAI AKASIN HAKAN ALLAH KA YAFE MANA ALBARKACIN WANAN WATA MAI ALBARKA SAIKUMA ALLAH YA HAƊAMU A LITTAFI NA GABA .

 

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da ƙasaita take saukowa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.