Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / MATAN ASOKORO

MATAN ASOKORO

MATAN ASOKORO

THE ONLY FREE PAGE
EPISODE 1️⃣
Dakine mai bala’in kyau, kana ganin dakin kaga office sabida office settings ne dakin, ga dogon couch mai shegen laushi da yaran kujera(throw pillows) saikuma chan gayar desk dake dauke da desktop keyboard da sauran su, gakuma book shelve dake dauke da litattafai daban daban daya karamai kyau, dakin cool sanyi ketashi ciki na AC. Wata mata da akalla zatai 35 ko 36yrs ne ke zaune kan couch din office din, tai shiga ta alafarma tai crossing legs dinta tanadan karkadawa, kafar yaji jan lalle tana sanye dawani takalmin hermes simple mara kwalliya orange color sai jakarta itama product din Hermes shima orange color, tana sanye dawani doguwan riga na atampa mai tsadan gaske da akamai stone work baja baja ga babban mayafinta dakana gani kasan naira tai kuka awajen nan, hannunta kuma rikeda IPhone 12 Pro Max tana daddannawa fuskanta dauke dadan murmushi daya kara bayyana kyawunta da yanda chocolate fatarta ke kyalli, kyallin hutuda jin dadi, jin karan anbude kofa yasa tadago kanta takalli kofar, wata chocolate skin likita ce dan tana sanye da farin labcoat, kana ganinta kaga baturiya amman all this black Americans tana sanye da half gown mai kyan gaske da wani red hill tadaura lab coat kan gown din, hannunta kuma rikeda wani pad mai kyau dake attach to wani kalan pen da kana gani kasan narubutu kan iPad dinne, murmushi tayi tamaida kofan tarufe sanan ta shigo ciki saida takarasa daidai kan desk dinta sanan tadau farin glasses tasaka a idanunta kafin tazauna kan kujera ta danna pad dinta sanan tadago ta kalli matar cikeda fara’a dakuma murmushi tace “Hello, Mrs Bakori right”? gyadamata kai matar tayi tace “yes” dauko pad din tayi sanan taja kujeran baya tafito tazagayo tagaban table din ta zauna kan one seater couch dake facing na matar sanan tai crossing leg itama ta kwantar da pad din ajikinta tace “this is your first time in our facility right”? Gyadamata kai matan tayi tace “right” gyadakai tayi cikeda gamsuwa tace “my name is Dr Elizabeth Matthew Browns, I am the Psychotherapist of this facility, before we start i want to assure you anything we will be discussing here is strictly confidential, all ur information and ur identity are very safe with us here, so fill free to talk to us, talk to me your Dr, I am a counselor, a Consultant, a therapist and so much more, so Mrs Bakori…..” tai maganan tana daukan pad dinta tarike da pen din a hannunta da kyau sanan tadago kanta ta kalli matar tace “I want to know u better tell me who you are” gyara zama tayi saikuma tai danjim kaman mai tunanin wani abu saikuma tace “My name is Hassana Lawal Bakori, we are twins, i have Hussaina but bata Nigeria ita, tana Dubai, am 35yrs old, am married to Alhaji Alhassan Bakori” tai shiru, iPad din Dr ta kalla sanan tace “what about kids, your record here says kinada yara, is that right”? Gyadamata kai tayi tace “oh yes, I have two children, Boys, Khalid and Khalil, twins nesu suna boarding school, they’re 14yrs old, suna SS2 dukansu” anatse Dr tace “which means sau daya kawai kika haihu? How long have u been married”? Anatse tace “15yrs” ahankali Dr tace “why? Maisa kika tsayarda haihuwa? Health complications ne yasa baki kara haihuwa ba, kokuma kece bakiso”? Dan murmushi tayi tace “my husband doesn’t want plenty children saisa bankara haihuwa ba” murmushi Dr tayi tace “so Mrs Bakori why are you here? What do you want to discuss with me, how can I be of help to you”? Tai maganan anatse ta yanda patient dinta zata kara natsuwa dakuma aminta da ita, ahankali ta gyarazama sanan ta ijiye wayanta dake hannunta gefenta sanan ta rungune hannayenta biyu akirji tareda fuzarda iska tace “is about my husband” gyadamatakai Dr tayi alamun okay tana jinta tacigaba, sake dan shiru tayi Dr ta tsaya bataredatai pressuring nataba, saikuma ahankali tadago kanta ta kalli matar tace “I don’t have feelings for my husband! kwata kwata banjin sonshi araina daidai da digo daya! baya burgeni! I don’t find him attractive! I don’t find him sexy! Bana sha’awan shi! Banmason yaneman! Bawai banajin sha’awa bane, a’a inaji amman idan yazo nemana sai inji raina na baci, kwata kwata banmason yatabani ballema wani abu ya shiga tsakaninmu, I don’t know why am like that, I need help, serious help” duk maganan datayi Dr kallonta take, saida tagama tsaf sanan tadanyi yan rubuce rubuce akan pad din sanan tadago ta kalleta, ahankali tace “you want some coffee, tea or water”? Dan facility haka sukeyi duk wanda yazo ana kawomishi any of the 3 yasha, girgizamata kai tayi tace “no am good, thank u” gyadamata kai Dr tayi itama, sanan tace “akwai wani mugun hali da mijinki yakeda shine, kokuma yana cutardake? Koyana miki wani abu dabakiso ne”? Girgizamai matakai tayi ahankali saikuma tace “not really, kawaidai mijina yana yawan gwasaleni, ya gwaleni idan inamai magana kokuma ina magana a inda yake koda badashi nakeba” “hakan nabaki haushi”? Dr tajefo mata tambayan, dan shiru tayi ta kalli Dr saikuma ahankali tace “eh, hakan nabani haushi, yana bakantamin rai” “do you think abinda yasa bakijin sonshi aranki kenan sabida yana gwasaleki”? Dr tasake mata wanan tambayan, shiru tayi takasa magana takai kusan 3min, Dr na kallonta kyar, dan ajiyan zuciya tasauke sanan tace “nasan na tsani idan mijina ya gwaleni, agaban yan aikina, yarana saikiga ya gwaleni, idan nace kaza saiyace ai kazane ban saniba koban iyaba this this this, i know is very annoying but I don’t think shine abinda yasa naji bana sonshi, No! I don’t think so” takarashe maganan ahankali, zama Dr tagayara tace “and what do you think made u not to have feelings for ur husband anymore Mrs Bakori”? Shiru tadanyi saikuma ta numfasa tace “I…..I…..I…..” muryanta yasoma breaking sosai, hakan yasa Dr tace “take a deep breath Mrs Bakori” kaman jira take ahankali tai taking deep breath sanan tafuzar, Dr tace “are you ready? Mucigaba”? Gyadamata kai tayi ahankali tace “yes Dr i am ready” gyadakai Dr tayi tace “good, I asked u a question, me kike tunanin yasa bakijin kinason mijinki yanzu? What do you think made u not to have feelings for your husband again”? Ahankali tace “because I feel he don’t love me too, shima bayasona” dan shiru Dr din tayi tana kallonta yanda taga idanunta sun kada sunyi ja, tace “auren soyayya kukayi ko auren hadi”? Ahankali tace “auren soyayya” “to mesa kike ganin bayasonki yanzu”? Shiru tayi tace “Dr my husband baisan menene lallashin mace ba, and he don’t know how to say sorry, idan zan fadi agabanshi faduwa sosai mutumin nan bazaima tashi daga inda yakeba balle yataso yazo yadagani yacemin sannu ba, saidai ya kalleni yadaukekai yace banda natsuwa saina kashe kaina hankalina zai kwanta, idan na yanke bazai cemin sannu ba, idan kaina naciwo bazai cemin sannu ba, munada family Dr kome ke damunka kana kiranshi zaizo yabamu magani, amman bazai taba tambayana konasha magani ko banshaba koyajiki ba, ko naci abinci ko banci ba, anything nida rayuwata mutumin nan babu ruwanshi, inason mijina saisa na aure shi but wanan halin dayakemin na rashin kula, na rashin damuwa dani, ko uhum ko ajikinshi yasa naji zuciyata batajin sonshi to akanme zanzo wanda bai damu da lafiya ta ba, akwai lokacin danai zazzabi sosai saida Dr yasamin ruwa barin dakin yayi wai bazai iya kwana daniba ina warin allurai da magunguna, wani zubin haka zai tafi aiki ko lekoni baiyiba, Dr kinsan mene” tai maganan tana goge wani hot hawaye daya zubomata da sauri saikuma tai murmushi tace “don’t tell me I am crying” “oh yes u are” Dr tafadi haka ahankali tareda juyawa tadauko tissue dake kwali tajuyo tabata, karba tayi ahankali sanan tadaura akan fuskanta tana goge hawayen suna zubowa tana kuma murmushi at the same time, tace “Dr i am a very very strong woman, dawuya kiga kukana, koshi banjin natabamai kuka kan abubuwan dayakemin ba, nafi karfin namai kuka, but bansan mesa yanzu nake kuka ba, eh? Why am I crying? Look what Baban Khalid is doing to my confidence and self esteem” tai maganan tana share hawayen tana murmushi duk Dr na kallonta taking note of everything, kana ganinta kasan she’s deeply hurt, babu abinda yacika zuciyanta sai lot of sorrows da damuwa but she’s wearing that strong woman face, MATA! we are going through a lot!! Dr tafadi aranta, yanda taga hawayen sun kasa dena zuba saikuma murmushi take trying to stop them takasa yasa ahankali dawani irin heart soothing voice tace “Mrs Bakori” ahankali tadago fuskanta ta kalli Dr hawaye nazubowa har lokacin tace “na’am” ahankali Dr tace “let them out, cry to me, cry for me, cry all your problems out, is part of the psychotherapy, cry, yi kuka” cikeda gardama dakuma kunanrai tace “no Dr akanme zanyi kuka kan Baban Khalid, akanme zandinga kuka kan namijin dabai damudani ba, bai damuda damuwataba, akanmene, wlh yayi kada……..” saikuma gakukan yazo bashiri, sauran maganan ma makalewa yayi awuya takasa yi, sake juyawa Dr tayi kawai tadauko kwalin tissue gabaki daya tamika mata karba tayi tazaro tana goge fuskanta, cikin kuka take magana. “Idan yara suka dawo hutu har tsoron magana nake dasu kokuma wata hira tashiga tsakanina dasu idan babbansu na nan saikiji ya gwasaleni, kinsan yara maza basuda hankali da wayau ba kaman mata bane, idan mahaifinsu ya gwasaleni dariya suke sosai fa, but bantaba nunamai yamin ciwoba saidai inyi murmushi inbarmusu wajen shikuma ya kwashesu yafita, ni kadaice baida wata matar balle nace sabida ita yakemin wulakanci kuma baya neman mata, shifa baida lokacin mata ma wani irin likimon mutumne kawai neman kudi yasani arayuwanshi, neman kudi kawai da tara kudi, weekend kawai yake zama agida shima ba kowanne ba, weekdays sai dare zai dawo, bannemi komi narasa ba, sai kulawanshi da nuna yadamu dani, this are what my heart wants, but bana samu daga wajen mijina me akayi kenan, saisa bana sonshi banajin sha’awan ba, banmaso yanemeni”.

 

Saida tagama kukan tsaf which was taci kusan 6min sanan, tashare fuskanta tsaf takalli Dr tasake murmushi tace “don’t mind me Dr, I am not the crying type so banmasan mesa nake kukaba, so yanzu dai kinji this is my issue, banson mijina kuma sabida shima bayasona, a online naga advert na facility naku, ku baturai ne kuma psychotherapy shine specialty naku, idan mutum yanada matsala yazo yagaya muku zaku taimakamai da matsalanshi, after paying those huge money for consultation I hope zan sami maganin matsalata, kisa naso mijina back” dan murmushi Dr tayi jin maganganunta tace “I will help you Mrs Bakori, but u have to be willing to help yourself” gyadamatakai tayi, Dr tace “first of all I want to ask you one question dazai taimakamin wajen samo miki solution, was ur husband like this dakika aureshi? Haka halinshi yake lokacin dakuke dating”? Da sauri tagirgizakai tace “no bahaka yakeba, lokacin damuke soyayya wlh ko zazzabi nake zakiga shima yafara zazzabi duk yabi yadamu sosai fa bana wasaba, everything yafarane danazo na haifamai yan biyu lokacin yafara wani mahaukacin kudi, kinsan engineer ne yana harkan construction, building, titi, yanzu haka yanada kampanoni sunfi goma, manya manyan, government contracts yake samu nayin titina da wasu irin crazy building, a Nigeria kap babu kampanin daya buge nashi indai harkan kera gini ne da titina, su kansu gwamnatin Nigeria naji dashi sabida iya aikinshi da talent dinshi, to dayazo yay wanan bastard kudin shine yazo tashi daya ya chanzamin sabida yaga yadawo hot cake nima zai maidamin da kanshi hot cake, baibi takaina kawai amman ban rasa komiba, duk month inajin alert na monthly allowance dina huge sum of money, ga kayan abinci na komi da komi dakika sani inadasu adakina, kumani nafi karfi nazauna namai kuka kowani abu wlh ai yasanni, kafin yasan kudi dudda kudinshi yanzu zai iyafin na mahaifina nima nasani, Babana shine ambassador Nigeria na Thailand, kuma babana yana daya daga cikin mutanen dasuka samai hannu yazama abinda yazama yau dinan harya bunkasa, tomezai gayamin”? Shiru Dr tayi tana kallonta one thing dazata iya fadi kan this her new patient is tanada girman kai dajida kanta itama, and in this her case da mijinta dolefa daya yasauko daya ya takashine sanan zata iya samin abinda takeso wato care and his affection, wow asibiti kullum kake ganin patient daban daban, numfasawa tayi tace “Mrs Bakori, I think the first thing danaga aurenki da Mr Bakori ke lacking is communication, and that’s the first thing we are going to work on, now zanbaki one week, ur next appointment will be rana itiyau zaki dawo, but this 7days dana baki I want you to use them in trying to establish communication tsakaninki da mijinki, idan yadawo daga aiki kina zama kitayashi hira koki tayashi wanka” girgiza kai tayi, tace “ina tattara abincinshi nake kaimai dakinshi asama dan baya iya sakkowa yaci a dinning, ina ijiyewa zanfito kafin yafara kyarata, idan andan jima zan koma naje na kwaso nafito dannikadai ke shiga dakinshi sanan inwuce dakina na kwanta da safema haka, bana shiga harkanshi shima baya shiga tawa kowa yakama kanshi” shiru kawai Dr tayi tana kallonta, ahankali tace “okay, from today go u will have to change that, idan kika kaimai abinci ki zauna dashi kimai hira mai dadi” “hira!” Tafadi dadan daga murya sanan tace “dazaran nafara bashi labarin abufa zaicemin ai bahaka bane, wlh Dr bakisan mutumin nan bane, he’s so impossible, nikuma bazan bashi kaina yaraina ba chan tamatsemai a matsematsi” girgizamata kai Dr tayi, tace “Mrs Bakori, the way kike rayuuwa with ur husband is not even marriage, and u are so damn hurt pretending to be happy, if u want and respect ur happiness u need to drop this ur mentality and work things up between you two, babu laifi dan mijinki yaga weak side of u, there’s nothing wrong dan mijinki yaga kukanki, ko yaga damuwanki, inma yamiki dariya kanshi yamawa dan the two of you are one, there’s nothing wrong dankin nunama mijinki u are not as strong and harsh as yanda ake tunani, deep down u are so weak like a little baby who needed some love and support to light up her day, lemme tell u this, for u to bring yourself to this facility is because ke kanki kinsan burden din dakika daurama kanki yasoma miki yawa saura kadan ya kayar dake and u needed help, so I want you to drop all this act and listen to me and do as I say I am ur Dr” Dr tai maganan bawasa dayasa taga matar ta natsu, sanan tace “abinda nakeso dake is daga yau no more ki kaimai abinci kifito, ki kaimai sit there, help him shower ya shirya yazo yaci, if possible feed him, start conversation, a respectful conversation, idan ya gwaleki karki karaya continue batare danuna fushi or anything ba, zaigaji yadena and listen to you, idan ya gwaleki yau, gobe, jibi, gata bazai yiba, do this of this week, next week kika dawo u will tell me how it goes and we go into the next step, understood”? Ahankali ta gyadamata kai, murmushi Dr tamata tace “if that’s the case munxo karshen our session, saikuma next week right” murmushi tayi ahankali ta tashi tsaye tana gyara mayafinta, Dr tabita da kallo, matar badai kyauba, ga curve, tanada ass, ga manyan nono, tanada kiba kosasshiyar mace ce ba ramamma ba, ga fatarta baka mai kyalli, taji Jan lalle a hannu da kafa kana ganinta kaga irin matan nan masu gyara bana wasaba, matan Alhazawa but mentality ta yasa she’s not enjoying life yanda yakamata tayi.

Jakanta tadauka da wayanta sanan tajuyo ta kalli Dr tace “thanks” sanan tawuce tasakai tafice tana tafiya daidai cikeda isa, kana ganinta kaga Hajiya, like real Hajiya kudi sun zauna.

Premises din facility tayi takarasa gaban wani mota wata black SUV da batada banbanci da sabuwa karasawa gaban car din tayi saikuma ta tsaya chak ranta amugun bace takine fuska kaman ba itane tasha kuka ba, tajuyo ta kalli wajen asibitin da idanunta dasu chanza launi har yanzu suna nuna alamun sunyi kuka, wani dogon saurayine dake sanye da riga har zuwa guiwa ash color na shadda dakuma wani bakin wando shima har kasa, yana sanye da silifas din roba, yanada tsawo dakuma dan jiki kadan, fuskarshi nada haske, sai gashin kanshi so curly and a bit blonde dan ba bakin gashi bane dababu gyara kana ganinshi kaga bafulatani gakuma dan gemu shima blonde dabasuda yawa, yana gaban wani mai baron rake hannunshi rikeda rake yana balla yanasha yana hirada mai rake dake feremai wasu da wuka yana yanyankawa yana sawa aleda, dukaduka yaron bazai wuce 25-26yrs ba….. wani irin mugun tsaki taja kaman tahadiye zuciya tamutu, wanan dan kauyen direban da Baban Khalid yakawo mata shine d worst direba daya taba kawomata in her life, gashi kazami gashi dan kauye, tarasa why on earth is Baban Khalid treating her that way shiya hanata driving sanan yakawo mata wani dan kauye that can not even read anything, ita batamasan daga ina yasamo yaronba just 1month ago yakawo matashi sabida direban ta nada yakoma garinsu kulada mahaifiyarshi da aka cemai batada lpy, shi professional direba yakeda shi kullum direbanshi cikin suit yake da agogo shikuma wanan local dan kauyen yakawo mata that cannot even read ABCD to Z, koyanaso tai bala’i dashine dan tasan dagangan yamata haka ohonmai.

Jin ranta na tafarfasa yasa tajawo wayanta daga cikin jaka taciro tashiga dial calls dinta saiko ga number Martala Driver tai dailing number shi, yana tsaye bakin titi suna hirada mai rake dake yanka rake saiga wayanshi tashiga ringing dasauri yatura hannunshi cikin wandon yaciro wayan techno yar rakani toilet, musamman yasa akamai Saving number Hajiya da S shikuma Alhaji da A dan yagane idan takira yana ganin kiranta yadaura hannunshi aka amugun rude cikin hausanshi nayan kauye yace “na shiga uku na lalace, Hajiya” dawani irin gudu yajuya ya kalli asibitin hangota tsaye yasa damugun sauri yajuya yasake tura hannu cikin aljihu yaciro wata 500 yamikama mai raken yace “kai bani Hajiya ta tafito, yau nidai nasan na shiga uku” baima jira cewanshi ba ya fizge ledan yawuce, Mai rake yace “ga chanjin ka kabari” titi yashiga da gudunshi yace “nabaka” da gudu ya tsallaka titin ya shiga asibitin duk tana binshida mugun kallo, yana karasowa gabanta ko wata wata baiyiba yawani irin zubewa agabanta yace “Hajiya dan Allah kiyakuri, wlh nasan kinsha gayamin muka fita na tabbatar ina cikin mota idan kinfito, tuba nake Hajiya, Allah yahuci zuciyanki, Allah ya sanyaya kafadunki, tubanake Hajiya” ayanda takejin haushi zata iya shureshi da kafafunta tadai daure cikin fushi tace “my friend will u stand up and open car for me” dasauri yace “eh Hajiya mekikace”? Wani irin runtse ido tayi cikeda takaici tuna bamaya gane turenci, dan dagokai yayi ya kalleta ganin yanda tayi yasa yace “dan girman Allah kiyakuri Hajiya wlh daman rake nasayo miki wlh” yamikamata raken dake leda, bude idanunta tayi tadakamai tsawa. “Murtala katashi kabudemin mota nabar wajen nan!” Abirkice dukya rude yatashi garin hakama yasaki ledan raken suka watse awajen tabishi da mugun kallo dayasa yatashi da sauri yatura hannu a aljihu yaciro hadadden car key sanan yadanna lock tabudu, kafin yabude kofar owner sit yasaukarda kanshi kasa yace “Allah yahuci zuciyan Hajiya, tuba nake matan ranka shi dade, takawanki lpy uwargijiyata, shiga muje” mtswww taja wani wahalallen tsaki tajuya tashiga cikin motar ahankali kanta na mugun sarawa yamaida kofan yarufe, raken daya watse awajen ya kalla har ranshi soyake yatsugunna ya kwashe kayanshi amman tsoron masifan hajiya yake, bude gaban motan yayi ya shiga ya rufe yaja sit belt yasaka saikuma ahankali yaleko bayan sit din ya kalleta kanta na kasa tana kallon wayanta datake latsawa kaman mara gaskiya ahankali yace “Allah huci zuciyan Hajiya” dagokanta tayi tazubamai red eyes dinta dahar lokacin suke nuna alamun kuka, hakuri zai batafa amman ganin yanayin idanunta yasa dasauri yace “Hajiya kuka kikayi? Innalillahi maiya sameki anmiki wani abu a asibitin nanne? Waya batamiki rai eh inje inkoyamai hankali wlh saina barar da mutum na shemar dashi, waye ne Hajiya”? Yanda taga yadamu sosai danya nuna afuskanshi yasa har ranta saitaji dadi, dan yatsine fuska tayi cikedason yamata shiru dakuma tarin gajiya tace “nagaji ne kaini gida kawai nahuta Murtala” da sauri yajuya yatada motar yajada sauri yace “Hajiya sannu, kinga baki saba wanan aiki hakaba, keda kikeda likita dayake zuwa har gida yadubaki maisa kikazo asibiti nan kikabi layi saisa kanki keciwo, sannu Hajiya, Allah huci zuciyanki, yanda kikagajin nan bazanbi hanyar zuwa ASOKORO ba dan akwai go slow, akwai wata short cut hanya dazanbi yanzun nan zakiga munkai ranki shi dade”.

 

Chat me up directly by clicking on this link
https://wa.me/+2347012181461

 

_This is the only free page of this book, like I said, wanan novel din bakaman normal novel dina bane, I interviewed so many couples, I want to show the world inda akafi samun matsaloli arayuwan auren mu tayau and how to go about it. I trust my fans, u all knows yanayin rubuta, ku gyara zama, wanan littafi shine ga darasi gakuma dadi, lemme say it again please πŸ”ž, anybody less than 18 shouldn’t read this book, thank you._

Chat me up directly by clicking on this link https://wa.me/+2347012181461

_This book is 2k, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank and send evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting_

 

 

 

 

πŸ’« _MATAN ASOKORO_ πŸ’«

 

✍🏾M SHAKUR

_RANAKUN POSTING *SUNDAYS*, *TUESDAYS,* *FRIDAYS*_

_DAN GIRMAN ALLAH KARKI KARANTA THIS BOOK IN BAKI BIYABA, KUJI TSORON ALLAH_

 

EPISODE 2️⃣

 

Ko alamun taji magananshima batayiba saima cigaba da danne dannenta datayi awaya tana chatting a group dinsu na ASOKORO WIVES, gajiya tayi saikawai ta ijiye wayan sabida yanda kanta kewani irin sarawa datarasa maisa, sanan gently ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido. “Hajiya wai lapiyanki kalau”? Bude idanunta tayida sauri jin Murtala yasake mata tambaya ta madubin mota suka hada ido dan gajeren wahalallen tsaki taja tamaida idanunta ta lumshe su ahankali back, maida hankalinshi yayi kan tukin harsu ka shigo ASOKORO District, Usman katsina street suka shiga yay horn agaban wani makeken mansion da tsayawa bayaninshi aikine ganin ba’a bude gate dinba yasa yace “auuuu kullum saina manta abin nan” yay maganan yanadan juyowa ya saci kallon Hajiya yaga tana kaman bacci danhar lokacin idanunta a lumshe yasan inda idanunta biyu datamai bala’i kan kullum saiya mantada remote din da ake bude gate dinsu dashi, remote din dake motar yadauka ya danna gate din yabude sanan yasa kan motan suka shiga cikin gidan gate din yarufe kanshi, kafin ahankali yabude kofa yafito sanan yazagayo ta bangarenta yabude kofa tareda bending kanshi cikeda respect yakira sunanta ahankali danya tadata daga bacci. “Hajiya, Hajiya” dan bude idanunta tayi ahankali tazubasu akanshi awulakance, baidamuba yace “mun iso gida ne daman saisa natadake” yunkurowa tayi tanajin kaman kanta zai fice amman saita daure tafito hakan yasa shima ya matsa yakoma baya, fitowa tayi daga motar ta tsaya da kyau da sauri tasake kulle idanunta jin wani irin jiri take gani hakanan all of a sudden, hakan yasa Murtala daya koma baya yace “Hajiya karkice nacika tambaya amman kaman bakida lpy wlh, duk jikinki ya nuna hakan” bude idanunta tayi tazubamai wani matsiyacin kallo dayasa yaji cikinshi ya murda ahankali yamaida kanshi kasa, daukekai tayi tace “kwasomin jakata da wayata” tai maganan sanan tajuya tafara tafiya gashi daganan parking space zuwa flat dinta dadan tafiya, amman hakan take tafiya ahankali dai dai gudun kartaje tazube dan bamatasan meke damuntaba jitake kaman sauran kiris jikinta yakasa daukanta, akwai staircase haka dazai sadata da kofan shiga flat dinta ahankali take hawa staircase din cikeda karfin hali irin nata da kyar ta iya daga kafanta tahau na karshe batasan meya faruba tadaijita akasa sharaf, sanan kuma taji ihun Murtala sama sama, kara lumshe ido tayi tabude sanan taga Murtalan agabanta ya tsugunna ya haukace yakasa tabata sama sama takeji yana Hajiya, Hajiya, sake lumshe tayi tabude batasan meke going on ba tadaiga waya akan kunnenshi saikuma kawai taji yadauketa, kadan kadan take bude idanunta she could feel and see yanda heart dinshi ke beating, ke racing sosai na fargaban kar wani abu yasameta saikuma dip ta dauke wuta.

Kwantarda ita yayi akan katafaren doguwan kujeran dake falon cikin jerin hadaddun kujerun dake wajen, sanan yatashi da sauri hannunshi har rawa yake ya shiga dailing number Alhaji for the second time yamugun damu dudda yasan Hajiya was never nice to him but still baisan wani abu yasameta…….

 

Wajen 30 big men ne zaune awani babban conference room, sunci uban suit, wani hadadden magidanci mutum dake zaune kan kujeran CEO ne ke magana yana bayani da turenci, ringing dawayanshi yasakeyi for the forth time yasa yakalli wayan, daukan wayan yayi a hannu yatashi tareda fadin “excuse me” sanan yafita daga conference hall din yakara wayan akunnenshi, kafinma Murtala yay magana yashiga balbaleshi da masifa. “Ka kirani kace tasuma nace ka dauketa ka shiga da ita ciki zan kira Dr, basaika jiraba, saidamuna kake da kira kasan wani irin meeting nakeyi ne? Kaiwani irin wawan bakauyen yarone wai? In nagama I will call d Dr yazo yadubata, kawai yanzu ka tsaya tareda ita, karka barta ita kadai, babu abinda zai sameta ai Hassana is a strong woman she will be fine” ya katse wayan zai maida a aljihu saikuma yaciro yama kashe wayan gabaki daya dan yasan Murtala baida hankali he will keep calling him this meeting is very important anjima idan suka gama zai kira Dr su yasa yaje yadubata, da sauri yawuce yakoma ciki wearing a smile akan face nashi yace “sorry gentlemen let’s continue”……

 

Jikin Murtala har bari yake gabaki daya yama rasa maizaiyi gashi babu kowa gidan, dan ka’idan su shine ma’aikatansu basu kwana, da maid, gardener da sauransu duk dasafe suke zuwa suyi aiki sutafi, koma sunanan shibaisan mezaimataba, yana tsaye kanta chan yaga tai wani irin nishi ta bankare ta tashi, saikuma tafara Jan numfashi kaman numfashinta naso yadauke tana kakkama wuyanta, tsugunnawa yayi gaban kujeran cikeda damuwa yana tura hannunshi a aljihu yana ciro wayanshi zai sake dailing number Alhaji yace “Hajiya meke damunki na shiga uku, Hajiya badai mutuwa zakiyiba” ina Hajiya bamatasan wayeke akanta ba, yay dailing number kashe, sau uku yana kira wai akashe daidai lokacin tafado dagakan kujera tana nishin idanunta na kakkapewa shibaimasan meyakeba kawaidai yaganshi ya dauketa ko nauyinta bayaji yafita da ita daga dakin yawuce yabude mota yasata yagyaramata kafafuwa yarufe sanan yashiga gaba danna remote yayi gate yabude yasakai yafice aguje yana tuki yana juyowa yana kallonta yanda yaga tana battling da numfashi yasa kawai yasaki kuka. “Hajiya kiwa Allah karki mutu, kar yan biyu sudawo Marayu wayyo Allahna” kawai shima yahau kuka kaman yaro, wani babban government asibiti dakenan a ASOKORO yakaita yay parking yana kuka sosai yay cikin asibitin yana ganin wani Dr yafito shida nurse kawai fizgo hannun Dr yayi yana kuka sosai, Dr ma tsorata yayi dan yadauka mahaukaci ne yace “Malam lafiya”? Cikin kuka Murtala yace “Hajiyata batada lpy likita zoka taimaka mata dan Allah bata iya numfashi” jin maganan dayayi yasa Dr yabishi Nurse din dasuke tarena binsu har motansu yakaishi yabude Dr naganin yanda takeyi yama nurse alamu data kawo gado dasauri nurse tajuya shikuma Dr yashiga motan trying to help her yabude mata baki yana tambayan Murtala dake kuka har lokacin yace “meya sameta”? Cikin kuka sosai yace “kaman kanta keciwo saita sume saikuma tafara nishi haka” daidai ankawo gadon da za’a daurata, kallon gadon yayi ya kalli yanda Dr da Nurse ke kokarin cirota su sakata agado yace “ina zaku kaita”? Dr da hankalinshi baya kanshi yace “ward mu mata treatment” dasauri yace “likita karufamin asiri kabata magani anan cikin mota kokamata allura kawai mutafi yan gidansu basa kwanciyan asibiti sunada likitansu na gida, yanzu ma babu kowa agidan ne” likitan baimabi takanshi ba dan daga gani kasan illiterate ne, idan yabar matarnan within good 10min heart dinta zai daina aiki tamutu dan as it is ma yanzu heart dinta is very weak, ciki sukaida ita Murtala nabinsu abaya yana gayamusu zasu sashi a matsala, suna shigarda ita emergency room suka rufo kofa hakan yahanashi shiga, zama yayi akasan wajen yana share hawaye na tausayi dakuma fargaban irin fadan dazaisha awajen Hajiya da Alhaji yau yamusu asalin karambani wlh.

 

Yana zaune wajen wata nurse tabude kofa tafito yana ganinta yatashi da sauri yace “Ya jikin Hajiya”? “Da sauki, yanzu munsamata oxygen and per hour is 15k, yanzu anaso kai deposit din naira dubu hamsin” da sauri ya kalleta yace “eh dubu hamsin” gyadamai kai tayi tace “yes inba hakaba bazamu cigaba da treatment dinta ba, yanzu dai ansamu munyi stabilizing situation din idan kabiya kudine zamu cigaba” shiru yayi kaman wawa saikuma yace “kucigaba to bari naje nadauko kudin agida” Nurse din tace “you have an hour daga yanzu zuwa Magrib” juyawa yayida sauri yafita yaciro wayanshi yana dailing number Alhaji amman har lokacin akashe, rasa yanda zaiyi yayi yawuce yakoma mota yaja motar yakoma chan gidan, bangarensu boysqutars dakinsu yawuce direct, wata katuwar ganamasgo yayi yabude sanan ya shiga cirowa yana ijiyewa kan katifa sanan yaciro watayar leda baka yakoma gefe ya zauna yabude ledan albashinshine dayake cirewa yayi saving duka duka 80k ne yamaida ledan ya kulle sanan yatashi yafito daga dakin dasauri lokacin ana shirin kiran salla komawa asibitin yayi yabiya kudin komi yarike sauran 30 a aljihu sanan yatafi masallaci kafin yadawo yasake samun wuri gaban dakin ya zauna yasake ciro wayanshi yay dailing har lokacin wayanshi akashe abin yabatamai rai amman kuma meruwanshi shidan aikine tashi yayi yawuce masallaci jin ana kiran isha’i yayi yafita waje yaje yasha shayi da indomie sanan yadawo yasake zama awajen shiru babu wanda ya cemai wani abu har bacci yasake kwasheshi yay kwanciyanshi kan yar kujeran yana sharara baccin shi gwanin ban tausayi kana ganinshi kasan yagaji…..

 

 

Kaman an tsikareta tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba gidanta bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she’s sick but inane nan? Yunkurawa tayida kyar ta tashi tazauna tanadanjin jiri kadan, sanan ta kakkalli gefenta but babu jakanta babu wayanta balle takira wani, sakebin dakin asibitin tayida kallo taga emergency room ita kadaine aciki nothing to talk about wanan wani irin local daki takene, jitayi warin asibiti da dakin keyi na irritating nata yasa cikeda karfin hali irin nata ta yunkura tasauka daga kan gado tana zura takalminta takama karfen da ruwan kejiki dasauri ta lunshe ido, ahankali taja tasaka hannu tabude kofan tafita tana tafiya kaman zata fadi, tabi wajen dakallo babu kowa a wajen kaman ance ta kalli side dinta Murtala tagani ya kudundune jikinshi kan kujeran wajen yana bacci yana sosa hannu daga gani kasan sauro ke cizonshi, tsareshi tayida idanu ranta nabaci mesa zaikawota irin wanan asibitin, wani irin sarawa kanta yayi sabida bacin ran dataji saikuma wani irin mahaukacin jiri yazomata tai baya zata fadi tana kokarin rike karfwn da ruwanta ke sagale shikuma yabugi bango yay lara hakan yasa firgigit Murtala yafarka tareda dagokanshi ganin Hajiya idanunta na juyawa tana kokarin faduwa but tana kokarin hana kanta yasa yawaniyi tsalle yace “Hajiya” tareda tarota tafada kan kirjinshi, ko kawo wani abu baiyiba kawai yadauketa chak dukya rude sanan yaja karfen ruwan yabude dakin yace “mesa kika fito Hajiya aidakin kirani” ahankali tabude idanunta tana kallon fuskanshi yanda damuwa yanuna ko’ina akan fuskan, kirjinshi nabugawa fat fat fat tsoron karta fadi dayaji yasa taji something that is very very strange azuciyanta, she just wish and wish inama Baban Khalid ne haka looking so worried and so concern about her datafi kowace murna aduniyan nan. “Hajiya!” Firgigit tafarka daga tunanin dataje ashema harya zaunar da ita kan gado, cikeda damuwa yace “menene kikeso maiyasa kika fito tsakar daren nan? Jirifa ke mugun damunki? Meke miki ciwo yanzu? Nakira Dr”? Tunda yakemata tambayoyin take kallonshi saida yagama sanan tahade rai tace “ubanme nakeyi awanan kazamin asibitin? Wayakawoni nan?” Shiru yayi yasaukarda kanshi kasa shidaman yasan yayi laifi. “Ina maka magana kamin shiru Murtala!” Tadakamai tsawa dayasa tasake kama kanta dasauri jin kaman zaifita tace “wa…..” ganin yadago kanshi ya kalleta yasa tahadiye sauran wash din tai maza ta cire hannun tasake daure fuska zatai magana yace “Hajiya dan Allah kiyihakuri kinji, bakida lafiya baki bukatan hayaniya da fada ko fushi, kinajin sauki zan gayamiki komi kinji Hajiya” ahankali tajinginar da bayanta da bango tanadan yatsine fuska tace “ka kira Alhaji? Meyasameni, mesa kakawoni nan”? Yanda tamai maganan babu wasa yasa yace “kina sauka akan mota kika fita kin fara hawa stairs kawai naganki akasa kina wani irin nishi………” nan yagayamata komi har zuwa yanzu, dan murmushi tayi tace “ayya meeting din must be very serious, jeka kiramin Dr” tai maganan kaman bakomi da sauri yafita daga dakin, daidainan hawayen data rikesu tunda yafara gayamata abinda yafaru yazubo mata sharrrr yanzu inda ace Murtala bai kawota wanan kazamin asibitin ba dahaka zata mutu abanza, Baban Khalid bai kira Dr ba saima kashe wayanshi dayayi irin ko ajikinshi dinan, baimaso adameshi da batun rashin lafiyanta yana aikin office, Baban Khalid Mijine wai ko Makiyi? Ta tambayi kanta! Jin alamun tafiya yasa da sauri ta share hawayenta tass, daidai anbude kofa Dr yashigo Murtala biyedashi yana kallonta yace “Hajiya kuka kikayi”? Wani irin mugun kallo tamai tace “fita daga dakin nan zanga Dr” babu gardama yajuya yafita yarufomusu kofa, Dr yay murmushi yace “why are u treating someone that saved your life today like this”? Murmushi yayi yakaraso gabanta yana gyara karin ruwan yace “I understand he’s your driver, but koma a direban ne i must applaud his effort, I am telling u dabadan guy dinan ba we would’ve lost you by now, at the time daya shigo dake this hospital inda ace kin kara just 5min without seeing a Dr da heart dinki yadaina aiki, haka yashigo dake he was crying sosai” dasauri ta kalli Dr tace “crying”? Murmushi Dr yayi yace “abin yabaki mamaki ko kema, aiko kuka sosai kaman yaro wai dan Allah mutaimaki Hajiyan shi, ya tsareni wai a mota zan miki treatment baki zuwa asibiti da kyar fa yabari muka shigodake that zakiyi fada” for the first time tadansaki murmushi iya lebe, saikuma ta kalli Dr tace “what is wrong with me Dr, maisa nai passout like that”? Kujera Dr yaja yazauna sanan yace “kinada wata damuwa ne, is there anything wrong with you or bothering u”? Wani kallo tamai saikuma ta tabe baki tace “ni babu abinda kedamuna, namaka kala damai damuwa ne kakemin wanan tambayan” shiru Dr yayi yana kallonta, daga this magana datayi yagane yes tanada damuwan but she’s the hard and strong type no need to even pressure her bazata fadimai ba hakan yasa yace “some of your results are out, some kuma sai gobe dasafe, kinada hypertension, and heart dinki at this junction is very very weak, bawai kinada ciwon zuciya or anything bane no! Just that heart dinki is weak, dole ki kulada kanki tsantsa dam at any point u can just collapse kimutu, dole kicire ma kanki damuwa, you should put yourself first before anything and anyone, kome kikasani dat will make u happy just be doing it, duk wani abu dake baki damuwa da matsala avoid it, I am sorry idan maganan nan yazo miki like this, I see u are strong u can handle it, and I also believe now that I tell u you will do all u can to keep yourself happy and healthy, so just do that” tunda yafara maganan tai shiru tana sauraronshi harya gama, sanan ya kalleta yace “any question” murmushi tayi kaman ba ita yabama wanan hard details din on her health ba, tace “i want to leave dazaran gari yawaye how much is my bill zan muku transfer” da sauri Dr yace “is not advisable for you to leave kibari mugama miki treatment, and issue of bill kuma your driver yayi taking care of that” da sauri ta kallai saikuma tasauke kanta ta kwanta akan gado tace “once it’s morning am leaving, I have my Dr he will take it from here” yanda take maganan zaka gane bawai permission take magana ba, murmushi Dr yayi yasakai yafice yasaba da irin matan nan masuji dakansu ga shegen girman kai da fadin rai shidai Murtala na zaune bakin kofa yaga Dr yafito yawuce hakan yasa yatashi ahankali yabude kofan kaman matsoraci yaleka hada ido sukayi da Hajiya yanda tabishida kallo ba kyaftawa yasa yasauke idanunshi kasa yace “Hajiya dama na leko nagaya miki ina nan bakin kofa idan kina bukatan wani abu kawai kidan bubbuga wanchan drawer inajin karan zan shigo kinji” yanda ta tsareshi da idanu batare datace wani abuba yasa ahankali yajuya yamaida matada kofa yarufe ahankali tasauke ijiyan zuciya itama tarufe idanunta.

 

Hakanan tasami kantada mikarda hannunta zuwa kan drawer kaman mai tsoron drawer tadan buga kadan kafin tagama janye hannuwanta tadawo dashi jikinta taji anbude kofa da sauri karasowa gabanta yayi yadukar dakanshi kasa cikeda girmamawa yace “Hajiya gani, me kikeso? Nakiramiki likita ne”? Samin kanta tayida bude idanuwanta kadan ta kallai saikuma ta dauke kanta ta kwanta akan gadon taredajan bargo ta juyamai baya sanan ahankali murta chan kasa tace “ga kujera kazauna anan, waje akwai sauro gari na wayewa zamu tafi” “angama Hajiya yanda kikeso haka za’ayi ranki shi dade, Allah karamiki lafiya Hajiya” yay maganan yana daukan kujeran ya matsarda ita baya zuwa chan jikin bango sanan ya zauna, yaso zamanshi awaje atleast yadan mike hakarkari akan kujeran amman wanan dole sai zama yatsine fuska yayi yana gyara zama ya jinginar da kanshi ga bango sanan ahankali ya lumshe ido yana sauke ijiyan zuciya, ko 2min ba’a yiba bacci yay awon gabadashi sai minshari waaaauuuuuu! Juyowa tayida sauri ta kallai jin yanda yake munshari kaman rago, ahankali ta gyara kwanciyanta tana binshi da kallo tundaga kan kafarshi dake cikin silisaf din gida, yanada babban kafa dan diddigenshi ma awaje yake silifas din yamai kadan ga kafarshi fara itama, sai bakin wandon jikinshi na jeans dayay datti sosai, yatsine fuska tayi tabi rigan da kallo itama tai datti gashi kirjinshi very huge ga fadi gakuma cika kaman yana daga karfe, ahankali tasauke idanunta kan wuyanshi fatarshi suli suli gadan gemunshi dabaida wani yawa, saikuma tasauke idanunta akan fuskarshi ahankali tafadi azuciyanta Murtala fa mugun kyakkyawane, kauyanci darashin son gyarane yasa yake hakafa, and he is so innocent, despite the fact bata sakinmai fuska, batamai murmushi kullum cikin fada takemai dudda mugun tsoronta dayakeyi dan yana mugun jin tsoronta samada Alhaji ma dan yana hira da Alhaji sosai, itako bayayi da ita, but despite all of this he saved her life, yamata abinda ko mijinta baitaba mataba, she’s so grateful to him dudda bata nunamai ba but har kasan zuciyanta taji dadin abinda yamata and for the first time duk tsanan nan datamai na dan kauye ne bai iya karatu ba duksai taji yakau. Kiran salla dataji anyi yasa tadan gyara kwanciya tace bari atada sallan asuba saita tadashi sutafi gida she needs a very clean and hot shower, lumshe idanunta tayi ahankali tana sauke ijiyan zuciya komida Dr yafadi mata suna kara mata yawo akanta, how will she stay happy now, kodai ta tattara taje gidansu tazauna cikin family tane koda na one month ne, but tana zuwa za’ai sensing something is wrong and Baban Khalid ma zai yardane yabarta taje gida tai one month, sarawa da kanta yayi yasa tahakura da tunanin tasake juyowa tazuba idanunta kan Murtala lokacin ana shirin tada sallan asuba. “Murtala” takirashi ahankali, firgigit yabude idanunshi dake cikeda bacci ya kalleta hada ido sukayi da sauri yatashi tsaye yana sosa kanshi yace “Hajiya gani, akira likita ne? Mekike bukata”? Girgizamai kai tayi softly tace “tafi masallaci kai salla kana dawowa saimu tafi” gyadamata kai yayi yajuya yana tafiya ahankali yafita tabishi da kallo ita karan kanta tasan yagaji.

 

_Hi Ladies let’s deliberate small on this issue. Yanzu if Hajiya start developing something ma Murtala will you all blame her or blame mijinta?_

_zuciya batada kashi, kuma zuciya aba ce da bata tambayan permission dinka kafin taso abu, idan tarasa abu anan dazaran tasami abun awani wuri saita fara son abun, hakane ko bahaka bane ladies?_

_Alhaji Alhassan Bakori ya kyauta abinda yayi???_

_mezakuce game da Murtala our 26yrs old driver that is simply doing his work? Mekuke ganin nan gaba zai faru tsakanin shi da Hajiya?_

_so far what have you learnt in this page??_

07012181461 chat me up a watsapp this is my number.

 

 

 

 

πŸ’« _MATAN ASOKORO_ πŸ’«

 

✍🏾M SHAKUR

 

EPISODE 3️⃣

 

6 nasafe dot yashigo tareda Dr, duk zaune suka sameta abakin gado, Murtala dake gefen Dr ya rusuna yace “ina kwana Hajiya” ko kallon Murtalan batayiba ta kalli Dr yace “i told you am leaving” dan murmushi Dr yayi yakaraso inda take rikeda da wata yar paper da pen yace “I just need you to sign this then u can go” karban takardan tayi tana karanta content din yace “is DAMA form, discharge against medical advice” signing tayi tabashi sanan tasauka daga gado ahankali harda dan gudu Murtala yakaraso gabanta yace “Hajiya zaki iya tafiya kona daukeki kokuma na dauko miki kujeran guragu”? Yanda yayi maganan saida yasa murmushi yadan subuce mata daga baki kawai tawuce tai gaba tabishi yabita abaya harzuwa motansu, baya yabude mata tashiga ahankali tazauna yarufomata kofan sanan yakoma gaba ya shiga yaja motar, itakuma tadauki jakanta dake kasan motan tabude taciro wayanta dake ciki hakanan tasami kanta dacire lock din wayan ganin babu miss call kodaya na Alhaji yasa ta maida wayan ta ijiye ta kauda tunaninshi aranta, har gida suka karaso ya danna remote gate yabudu ga mamakinta saitaga motan Baban Khalid direbanshi na wanke motan, tunkafin ta sauko direban ke gaidata, fitowa tayi ahankali rikeda jakanta Murtala yafito yashiga gabanta yamika mata hannu yace “kawo jakan narike” girgizamai kai tayi tace “jeka huta kayi kokari” sanan tawuce shi, juyawa yayi ya kalleta sanan yace “Hajiya zaki iya wuce benen”? Chak ta tsaya jin tambayanshi har ranta taji diran maganan kaman zata juyota kallai saikuma ta daure bata amsashi ba tashiga hawa benen dazai sadata da kofar shiga falon ta, tanajin muryan Murtala yana Alhamdulillah Hajiya tawuce batare data sake sumewa ba, Emus sannu da aiki, shikuma Emus yana sai yanzu kaganni, bude kofa tayi ahankali tashiga falonta.

 

Zaune Alhaji yake kan dogon kujera dagashi sai wata white jallabiya hannunshi rikeda remote yana kallon tashar CNN dayan hannunshi kuma rikeda mug na lipton yana, jin anbude kofa yasa yadago kanshi ya kalleta hada ido sukayi yace “Hassana ina kika kwana”? Kaman bazata kulashiba tajuya tamaida kofan tarufe sanan tajuyo ta kalleshi ahankali tace “asibiti” da sauri yadaura hannunshi asaman goshinshi yace “laaaa kinganni fa ba shaf na manta wanchan direban yaron naki yakirani ba nacemai bari nagama meeting zan kira Dr yazo, kwata kwata bamu gama meeting dawuri ba, I came back very late dakina nawuce na kwanta sai this morning ma naga bakinan ashe” jitayi wani abu ya tsayamata awuya saikuma ta daure takakalomai murmushi batare datace komiba tashigo zatai stairs yace “ina magana kuma zaki wuce” juyowa tayi ta kalleshi tace “kace mene”? Wani kallan kallo yamata yace “fushi kikeyine I told u meeting nake saisa ban kira Dr ba na manta, but bagashinan u are fine ba, ainasan ki u are a very strong woman” ahankali tace “Allah ko, tom godiya nake” tana maganan tajuya da sauri tai sama gudun kar hawayen dake gabda zubomata yazubo yagansu kofar dakinta tabude tashiga ta maida dasauri tarufe saikukan yazo sosai tacigaba da dannewa tasaki jakanta awajen tabude bathroom dinta da sauri tabude tap tafashe da kuka sosai jikinta har wani bari yake, what is this life? Is her husband husband ko enemy? This is the second time take tambayan kanta, tayaya za’ace mutumin da aka dauramusu auren, akace cinta shanta, suturanta, lafiyanta komi nata yatashi dagakan iyayenta yakoma kanshi yadawo mata haka, ankira bawan Allahan nan ancemai tasume she’s unconscious, yama kashe wayanshi batare dayakira Dr ba, yadawo baima dubata adaki ko lafiyanta lauba, sanan yaganta yanzu koyace mata yajiki, so yanzu idanda tamutu baidama hassara saidai yaranta suyi kuka ko, she’s not his business, baima sonta dan saikanason wani zaka damudashi, jin kanta yafara sarawa yasa dole ta tsayarda kukan tawanke fuskanta tareda kashe tap din tacire riga tai wanka da ruwan zafi sosai tadauro towel tafito daga bayin, gaban mirror ta tsaya idanunta sunyija tana goge jikinta da karamin towel, ahankali ta ijiye towel din kan chair bayan tagama tsanewa sanan tamika hannu zata dauki cream kenan taji anbudemata kofa hakan yasa tadaga kanta, Alhaji ne yashigo daure da towel a waist washemata baki yayi yamaida kofan yarufe itakuma tacire idanunta daga kanshi shigowa dakin yayi yazota bayanta ya tsaya yakai hannunshi kan kafadunta yakama yana kallon fuskanta tamudi yace “harkinyi wanka Hassana”? Bataredata kalleshi ba ta tsiyaya mai a hannu tace “uhm nayi wanka” murmushi yasakeyi yasaukar da kanshi yana kallon very big ass dinta yakai hannunshi yadaura akai yace “how far? Come please let’s do it sharp sharp danna fita I have a meeting by 9” batare data kalleshiba still tana shafamai a hannunta tace “not today please, cus am not in the mood” daure fuska yayi yadago kanshi ya kalleta tamadubi ganin mai abinta take shafawa yasa yakai hannunshi kafadanta yawani irin juyoda ita da karfi ranshi abace yace “what do you mean by u are not in the mood? Look how erect I am” yanuna dick dinshi dayamike ta towel yace “is this how u want me to go to the office, waike wace irin mace ce”? Yay maganan da fushi daidai lokacin tadago idanunta dasukai ja sosai takallai tace “kaima wani irin mijine Alhassan? I was so sick kakasa kiramin Dr, nadawo you couldn’t ask me yajiki or me akace yana damunki, meyasa kika suma, all you want is sex and sort out your desire ta jikin your sick wife? What kind of husband are you Baban Khalid? Mtswww u piss me off i swear” tafadi tanaji kaman ta watsamai mari, cikeda zuciya yace “nikikama tsaki”? Wani kallon raini tamai tace “I hope u know u deserve much more than that, I would’ve done more kawai darajan su Khalid kaci, and get out of my room please bazan iya hayaniya dakaiba I need absolute rest” tana maganan ta tashi daga gabanshi tawuce gaban wardrobe tabude tana kokarin nemo kayan dazata saka, shikuka yabita da kallo, strictly yace “as your dutiful husband Hassana, I command you to come here kibani hakkina” ko kallonshi batayibama tacigaba da neman kayan dazata saka kaman batajima meyaceba, takowa yayi yazo gabanta cikin fushi yace “waini kika komarda mahaukaci badake nake magana ba? Nace kizo kibani hakkina”? Juyowa tayi kaman yanda yake mata ihu tamai itama tace “tell me which of my hakki kaima kake saukewa? Nai rashin lafiya ko ajikinka inda namutu mai zaka gayama yaranmu eh? Kadamu dani ne ko kadamu da lafiyata wanne daga ciki? Kamin yajiki ko sannu dajiki? And kanada audacity kawani zo kanacemin nabaka hakkinka” cikin fushi yace “ke yarinya ce dazan tsaya ina tambayanki yajiki? Are u not old enough to take care of yourself? Yara ake tambaya yajiki not a 36yrs old woman maman 14yrs old children, see banda time dinki, jikinki nedai ko kici kanki, tafiyan ma danace nafasayi zan tafi, am going to China zanje nasayo some machines na construction, bansan randa zan dawoba, it might take a month or 2, bye woman” yawuce fuuuu yafita daga dakin, hawaye taji zasu zubomata tadaure tahana kanta tadau wata simple gown na cotton tasaka tahau gado taja bargo tarufa tana kokarin sa kanta bacci, tana kwance awajen taji fitowanshi yanajawo suit case ko lekowa baiyiba balle yamata sallama yawuce yatafi abinshi.

 

 

 

 

_DUK WACCE TAKARANTA THIS BOOK BATARE DAYA BIYABA ITADA ALLAH._

Tun tana tunane tunane sama sama har bacci yay nasaran awon gaba da ita, batawani jimaba ta tashi sake sako wani wankan tayi sanan tai salla ta tashi ta shirya cikin wata gangariyan shadda orange sanan tasauko kasa rikeda wayanta, dinning takaraso tana bude hadaddun kulan dake wajen taga maid tai lafiyayyen girki kala kala, masa tadeba da miya sanan tazuba ruwan lipton a cup tazauna tanafaraci ahankali tana tunanin kota kira Dr ne kokuma karta kira yazo yadubata, yatsine fuska tayi tace “anjima zata kirashi” saida taci tai nak sanan ta tashi ahankali tafito falo tazauna tareda daukan remote zata saka wani abuta kalla, zee world tasa sanan tamikarda kafafuwanta kan table din din tsakiyan falon tafara kallo.

 

Sosai tai nisa a kallon taji anyi knocking kofa, ahankali tajuyoda fuskarta ta kalli kofan, wani bakauyene still knock doors bayan akwai door bell. “Hajiya nine Murtala direba ne” yafadi da karfi dayasama tabude idanu kadan wondering saikace yashiga zuciyanta yaji metacene, dan daga murya kadan tayi sabida yajita tace “shigo” bude kofan yayi ahankali kaman matsoraci sanan yadago kanshi ya kallo cikin falon hada ido yayida Hajiya dake zaune kan kujera itama tajuyo tana kallonshi lumshe ido tayi kadan saikuma tadauke kanta tamaida kan TV ganin Murtalane wanan karan yayi wanka yasaka wasu riga da jean wankakku dayamai kyau dan rigan jane, ganin yanda tadauke kai yasa yashigo dakin da sauri gudun karya batamata lokaci yarufo kofan sanan yakaraso har tsakiyan falon ahankali ya zube akan center carpet din yana facing nata, kanshi akasa yace “dama nazo naduba kine Hajiya, ya karfin jiki”? Kaman bazata kulashi ba amman har ranta taji kalman yazo yadubatane, ahankali tajuyo tazuba idanunta akanshi, cikin soft voice tace “naji sauki Murtala” dasauri yadago kanshi yakalleta kaman yanda take kallonshi yawani sakin mata one cute smile dayasa tadauke kanta da sauri jin gabanta yafadi cikeda murna sosai yace “Hajiya naji mugun dadi kince kinji sauki, wayyo Allah na wlh dadi nakeji” shifa harga Allah yake magana yanda yakeji kuma haka yake fadi, batare data kalleshi cikeda isan nan daji dakai irin nata tace “maisa kaji dadi dannace naji sauki” ko kadan baikawo komi aranshi with a very free mind and innocent heart yace “sabida ina sonki Hajiya!” Dasauri tajuyo ta kalleshi sabida yanda maganan ta dira aranshi, baidena murmushin dake karamai kyauba yana kallonta yace “wlh Hajiya bakiga yanda nadamu ba dabaki da lpy ba, inason uwardakina banson naji komi yasameta” ganin yanda tafarsara maganan daban abinda shi yake nufi daban from the look in his face yasa tasake daukekai but she could feel the sound na dariyanshi and his excitement. “Hajiya kina bukatan wani abune naje nasayo miki” kin kallonshi tayi ta girgizamai kai, hakan yasa ahankali yatashi yana murmushi yace “bari natafi, babu kowa agidan idan kina bukatan wani abu ki kirani awaya Hajiya, Allah karamiki lpy, Allah yaja kwana Maman Yan biyu” yafadi tareda juyawa yay hanyar kofa, harya daura hannunshi kan kofa ahankali yaji tace “Murtala” dasauri yajuyo yace “na’am” saikuma yadawo harda dan gudunshi yazo gabanta yazube yace “gani Allah yataimaki ran Hajiya” batare data kalleshiba har lokacin tv take kallo tace “shekaranka nawa” da sauri yace “ashirin da shidda Hajiyar Allah” gyadamai kai tayi still bata kallaiba saidai shi dake kallonta kaman yasami TV, ahankali tace “a ina Alhaji yasamoka? Bani labari” washe baki yayi ya gyara zama da kyau yace “a kauyenmu yanada gona, munamai aiki, duk cikin masumai aiki nafisu kwazo sabida inaso nai aiki sosai dan afi biyana natara kudi sosai” juyowa tayi ta kalleshi tace “mezakayi da kudi haka”? Murmushi yamata sosai saikuma ya lankwaya kai yace “Umma na zan kaimawa” “Maman ka”? Gyadamata kai yayi, dasauri tace “ina jinka, bani labarin Mamanka maisa kake aiki sosai sabida ita” murmushi yadanyi yace “tanada ciwon daji, amman yanzu ma taji sauki sosai, kingako Hajiya ni kadai Umma ta haifa, nida nataso bansan Babana ba tace yarasu, itama Umma ta tsufa sosai, tanada gona itake daukana muje gona harna iya noma, muna noman albasa, ridi, masara da sauransu shimuke saidawa musami kudi, to data fara ciwone ina fitowa daga kauye na kaita asibiti shine harna saida gonanmu mukai magani dashi amman bata warkeba muka dawo, shine makotanmu mutumin yadauki Umma kaman mamanshi dagashi har matarshi yace mukowa na hausa muna kaita wani kauye kusada namu karban magani kuma saishi yay aiki, nikuma ya nemamin aikin gonan Alhaji nafara, har ranan da Alhaji yazo yaganni yace namai wai inada gwazo ga iya aiki zai kaini binni yasani makarantan koyan mota, koda nafadawa Umma ya yarda duk sukace naje ni namijine dole nafita na nema, Alhaji yasa aka kawoni

 

 

 

_DUK WACCE TAKARANTA BATA BIYABA BAN YAFEBA_

aka kaini koyan mota ko sati biyu banyiba na iya shikenan bayan kusan wata biyu naga yakawomin wanan katin nan yauwa license na tuki yakawo ni gidan nan yace zan dinga tukaki shikenan” yakarake maganan yana murmushi sosai take kallonshi zucuyarta na ayyana mata abubuwa kala kala, murya chan kasa tace “kadade rabonka da ganin Umma” gyadamata kai yayi ahankali, murya chan kasa tace “baka kewanta”? Dan murmushi yayi yace “inayi…..” saikuma yaydan shiru ya saukarda kanshi kasa kafin ahankali yace “inayi sosai” yanda taga yasaukarda kanshi kasa yasa takirashi gently. “Murtala” dagokanshi yayi yace “na’am Hajiya” gani tayi idanunshi sun cikada hawaye sosai dasauri tadauke kai jin heart dinta na beating sosai tama kasa magana, ahankali taji yanajan majina dadan shesheka, kasa daurewa tayi tajuyo ta kalleshi taga kuka yake awurin, dan murmushi tayi tace “inane kauyenku”? Bayan hannunshi yakai yana share fuskanshi sanan yace “chan wani kauyene hanyan Kano” murmushi tasakeyi tace “tomka shirya gobe zakaje kagano Umma jibi saika dawo ko” tai maganan ahankali da murya kaman tana lallashinshi, dago rinannun idanunshi yayi yakalleta sanan ahankali yace “dagaske Hajiya” gyadamaikai tayi batare datai magana ba hakan yasa yafashe da murna dakuka duka biyun yanajin wani irin farin ciki da kaunar Hajiya dabaitaba jiba yace “Hajiya nagode, nagode” saikuma yatashi yana share fuskanshi yace “nagode Hajiya, Allah yamiki albarka” saikuma yajuya yace “bari naje Hajiya, wayyo yau ina cikin farin ciki sosai Hajiya nagode” yay maganan tareda bude kofa yafice duk tana kallonshi she don’t know why kodan yakulada ita ne but she finds him so attractive and adorable gashi dan kauye dashi so innocent, kwanciya tayi akan dogon kujeran haka tana kallo buni buni yana fadomata arai har tahau bacci.

 

 

 

 

_RANAKUN POSTING ARE SUNDAYS, TUESDAYS, FRIDAYS_

Wuraren 6 family Dr su yashigo gidan, Murtala ya shigodashi har falo sanan yafita bayan Hajiya tasauko kasa cikin shiga ta alfarma.

Boysqutars dinsu yawuce yashiga yana hada kayanshi bini bini Hajiya nafadomai arai saiyay murya ahaka har aka kira magrib yawuce yatafi masallaci saida akai isha’i sanan yafito yadawo gidan yana tafiya ahankali, wayanshine tadau ringing ciro wayan yayi ganin Hajiyane yasa yakai wayan kunne dagudu yace “Allah ya taimaki Hajiya” “ina jiranka afalo” tafada ba wasa atattare da ita, da sauri ya katse wayan yay hanya flat dinta bude kofa yayi ahankali yashiga bakinshi dauke da sallama zaune yaganta kan kujera tana sanyeda wani simple gown na cotton dayakaimata har kasa irin na baccin nan pink color, kanta sanye da pink turban mai kyau idanunta sanyeda white glasses tadaura pillow kan laps dinta dai Mac book kan pillow tana aiki a system kafafuwanta sanye da indoors shoes pink masu shegen kyau kaganta she looks so adorable bazata taba yarda ta haifi 13yrs old children ba, kasama gaisheta yayi saiwani irin kallonta dayahauyi gabaki daya tatafi da imaninshi, jin shiru not the usual Murtala mai zuba yasa tajanye idanunta dagakan laptop din tadago kanta ta kalleshi hada ido sukayi dan kamashi tayi yana kallonta wani irin kunyane yakamashi saiyadan juyarda kanshi ahankali cikeda kunya kaman ta tuhumeshi yace “Hajiya wlh wlh kinyi kyau, gelashin nan yamiki kyau” yakarashe maganan yana juyarda kanshi gabaki daya, har kasan ranta taji dadin maganan shi this is abunda Baban Khalid bai taba nunamata ba, duk kyan dazatayi aduniyan nan ko kalloma bata isheshi ba, daurewa tayj bata nunamai ba saitadau wani rapa data ijiye agefen ta nayan 500 sababbi gal tajuyo tace “gashi” juyowa yayi ahankali yasake kallonta hada ido sukayi gabanshi nafaduwa sosai sake ganinta dayayi, babu gardama yakaraso yasaka hannunshi yakarbi kudin cikin muryanta dake nuna tsantsan natsuwa dakuma isa ga dadi tace “kudinka daka kashe a asibiti ne wanan” murmushi yamata sosai still yana kallonta yakasa magana, sake daukan another rapa nayan 500 tayi tamikamai kai hannu yayi zai karba yana kallon fuskanta still kaman yanda take kallonshi, mistakenly hannunshi yataba fatar nata wani irin shock sukaji dukansu atare da sauri ta sakinmai kudin ya karba sanan yadan koma baya jikinshi narawa ahankali batare data kalleshi ba tace “kai using wanan kasaima Umman ka abu” zubewa yayi awajen yace “Allah ya ampana, Allah yabiya bukatu Hajiya, Allah kuma yataimaka” “zaka iya tafiya” kaman jira yake yajuya da sauri yafice daga falon, yasauka yadauki hanyan side dinsu yana mamakin what is wrong with him idan yana tareda Hajiya.

 

 

 

 

This book nakudine idan kinaso chat me up directly by clicking on this link

https://wa.me/+2347012181461

 

Harya bude kofa yafita bin bayanshi tayida kallon sha’awa, kawai pride ne da wlh she can ask this boy nawa yakeso tabiyashi just to fuck her, yaron is super caring, and he appreciate her, yanzu dudda ta girmeshi sosai tana 36 yana 26 but still yana ganin kyanta a idanunshi kyanda haryama tafida Imaninshi, she is tired gosh! Tagaji da everything and anything, but taje therapy Dr Elizabeth tace “she should try and make things work between ita da shi, dudda tasan dazu dinan ya mugun bata haushi ne tadawo daga asibiti baima cemata sannu ba yazo waikuma yana bukatan sex, now see rashin shi, rashin kulawan shi, tsananshi datakeji yasa she’s seeing the bright side of this illiterate direba, ahankali tasaukar da system dinta ta ijiye a gefenta kan kujeran, sanan tamika hannu tadauki wayarta taciro number shi datai saving da Husband tana kallo, jitake kaman inta kirashi ajinta dakomi nata yazube, daurewa tayi da kyar tai dialing number shi, kaman bazai daukaba wayan na gabda tsinkewa yadauka, akufule kaman inda yanada iko zai iya dukanta ta wayan yace “why are you calling me woman”? Arayuwanta abu nafarko data tsana shine miji yawani dinga kiran matanshi da woman, she find the word way too insultive, daurewa tayi tahadiye komi tace “I call to check up on you ne, naga 10 yayi baka dawo…b……” “akan ubanme zan dawo eh Hassana” yamata uban ihu dayasa ta matsar dawayan daga kunneta dan kaman zai ciremata dodon kunne, cikeda fushi yacigaba yace “Hassana nifa, me Alhassan Bakori ina nemanki, kibani hakkina but u were telling me all sort of nonsense you this wawiya woman, kinsan waye ni? How dare u turn me down like this eh”? Yasake dakamata tsawa kaman wata yarshi dayasa ta lumshe ido tana nishi sama sama, anya kuwa, can she do this, Dr I don’t think this man can change, sake daurewa tayi tasauko da pride dinta to the lowest, ahankali tace “kayakuri! Nasan baka tafi China ba tunda nakiraka naji wayanka yashiga, kamanta dakomi just come back home let’s talk properly” “you must be very very stupid Hassana!” Yazuba mata zagi da turenci dayasa tawani ware ido irin ni mutumib nan ke zaga haka, cikeda fada yace “kindauka ni Khalid ne dazakiyi manipulating like that after everything you’ve done to me, wlh bazan dawo gidan nanba nai yaji, harsai kin kira all your family members you told them what you’ve done to me, sanan su kira secretary dina suyi booking appointment na ganina sanan suzo subani hakuro suyi biko inba hakaba wlh bazan dawo gidan nanba anan hotel dinan zancigaba da, what you did was so unforgiving, ni ni Hassana, ni mijinki nine zakiyi turning down, kiki barina nasami natsuwa when u know moretban anyone u are all I have as a wife, ki aiko ayi bikona if u are really sorry” at this junction ma dariya yabata irin dariyan takaicin nan, dan murmusawa tayi kadan cikeda muryan rainin wayo dan dama ta iya muryan tace “ashe zaka shekara kasha zamanka ko ajikina” subhanallah jiyayi kaman tazubamai barkono ajiki ihu yayi yace “nikike gayawa haka”?

 

 

 

 

WANT BUSINESS ADVERT OR PROMOTION AWANAN NOVEL DIN CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK

https://wa.me/+2347012181461

Cikin fushi tace “akwai wani a inda kakene banda kai”? Cikeda fushi yace “are you talking to me Hassana, me me your husband dani kike”? Cikeda takaicinshi tace “please i want to sleep if you don’t mind zan katse wayan” “you dare not cut that call Hassana!” Yafadi sounding so serious and so pissed off hakan yasa bata katse wayanba ta tsaya, cikeda zuciya yace “ni kikema rashin kunya, talking to me kaman am your mate, Hassana ni kika raina, wlh to bari kiji saina kara aure” “is that all you got?” Ta tambayay tace “bismillah ai kanada gidaje dayawa ka auro dubu ma inkaka dama, indai wanan bakin halin nakane daka koyo to wlh babu macen dazata iya zama dakai, baka damu dakowaba sai kanka selfish man” kaman zai fasa wayan tsabagen ihu yace “I will deal with you wlh, mad woman kawai, nabarmiki gidan, kuma I will tell all your friends na Matan ASOKORO nan how stupid and disrespectful u are towards me your husband, I will tell them namiki yaji sai kinyo bikona, I will shame u in this world, daikin kasa fita waje, zakiga abinda zan miki, that girman kai da pride din dakikeji I will so shatter it en, dani kike I will break your ego u will see” yana fadin haka ya katse wayan yarda wayan itama tayi ta jinginar da kanta jikin kujera tareda lumshe ido, it seems kaman mijinta shine her biggest enemy in this world, wai what is missing in aurenta ne? She is doing her best, Baban Khalid yasha mata abubuwa tana dannewa bata nunamai, just today data hanashi kanta shine zai yadata sabida yasan abinda tafi tsana kenan, what is all this Ya Ilahi, she hates this man and yanzu ma he’s making her to hate him more, all this therapy data fara sabida shi is all bull shit.

 

 

 

 

_DUK WACCE TAKARANTA THIS BOOK BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA_

07012181461 IS MY NUMBER CHAT ME UP DIRECTLY.

✍🏾M SHAKUR
Yautunsafe ya shiryo kayanshi tsaf yafito yayi wanka yasa wata shadda blue datamai kyau sai kallon flat din Hajiya yake yasan idan yakirata yanzu bata tashiba baikuma son yatadata hakanan yabude kofa rikeda kayanshi yawuce yatafi saikuma yanaji kaman karya tafi yabar Hajiya ita kadai agidan dudda yasan yanzu dagari yawayen nan nan badajimawaba yan aiki zasu cika gidan da kyar ya lallashi kanshi yawuce yatafi.

 

 

 

Zaune yake a hotel din wuraren 10 na safe yana sanye da bathrobe yadauki system yana aiki as usual kana ganin dakin hotel din kasan bakaramin daki bane dan baida banbanci dagida har cikin yanada shi dan presidential suit yakarba, knocking dayaji anyi yamasan waye dansunyi magana yace “common in Attajiri” tunawa yayi kofan bazai budeba yasa ya ijiye system din yatashi yay kofan yabude wani budewa wani babban mutum ne dazasuyi mate saidai shi yafishi kiba gakuma katon pot belly, yana sanye dawata mahaukaciyar shadda yaci babban riga, hannunshi kulle da Rolex gakuma takalmin kafanshi na Luciano, shaking hannu sukayi Baban Khalid yace “kai namijin duniya, kai namijin duniya, Attajiri ko Attarudu” wani irin dariyan manya mutumin yayi kikikiki yace “kowanne daga cikinsu is fine, muje daga ciki kagani Gwamnati” shiga sukayi dakin Baban Khalid nagaba Attajiri nabinshi abaya yana binshi da kallo harya zauna saikuma shi ya tsaya yace “yanaganka awani bubbushe ne iyye? Jibi fatarka bata kyalli bata mai mai saikace talaka, kai meke damunka hakane? Masu kudi irinka idan kaga fatarsu zaka dauka madara ce tsabagen kyau daban sha’awa” tabe baki Baban Khalid yayi yace “uhmm, kadai kawai zauna” couch din dake facing gadon yazauna yana facing nashi cikeda rashin jin dadi yace “ince badai Hassana bane”?

 

 

 

 

Cikeda takaici yace “towayene ma inba itaba Attajiri” cikeda masifa Attajiri yace “bakaine ka tsaya kaman wani baho ba duk lokacin da matanka taga dama tai fitsari acikin ka sanan kazubar, kanada irin wanan kudin kana sauraron iskancin mace, tuni zan karo mata uku duka alokaci dayama idan tana bala’inta ni inachan ina morewa” cikeda takaici yace “Attajiri kaima kasan bana sha’awan mata biyu tun muna yara kasan wanan bangaren nawa, kai kafi kowa sanin wahalan danasha a hannun kishiyan Mamata, I can’t imagine any woman on this planet ta wulakanta min yarana yan biyu na koma tamusu ihu” dasauri Attajiri yace “tokai gwamnati banda abunka wace mace ta isa tamaka haka, ai duk shegiyar daka cire daga kangin wahalan gidan ubanta ka kawota gidanka ta tabamaka yara danna mata saki zakayi washe gari kaje ka auro wata, ga matanan kaman leda duk ina ka danna kafa zaka gansu pacha pacha, indai da kudinka babu macen data isa ko kallon banza tama yaranka dane ake wanan wlh Gwamnati, kai banda abinka dama ina zamanka da Hassana zaiyi dadi? Kanada kudi ubantama nada kudi, ai yanda kakeji da kanka haka itama takeji da kanta, katashi aure yar gidan talaka sharaf zaka auro kuma yarinya yar shila, saidai matsalan yayan talakawa basu iya samun wuriba, hahahhahha”

 

yadan kwashe da dariyanshi irin na boss sanan yace “yar talaka zaka auro wacce zaka batada kudi tadinga binka irin matan nan da idan kayi fushi har kuka zasu dinga maka suna rokonka karufa musu asiri, ance kudi baya sayan komi billahillazi abokina karyane, kudi nasiyan komi na duniyan nan saidai in mutum baisan ta yanda ake siyaba” suka kwasheda dariyan iskanci, cikeda takaici Baba Khalid yace “can you believe it Attajiri waini zanjema yarinyar nan tacemin ita bazata bayarba sabida tai rashin lafiya bance mata yajiki ba, ni namayi yaji bazan komaba” dasauri Attajiri yace “ohoho, banda abunta irinmu bamu tambayan mata komi yooo ita tama isa ai saidai suyi rashin lafiyan sanan suzo sucemana sunji sauki Baby nagode da kuladani, kuma bazaka komaba katashi komawa gidan nan saidai ka koma da amarya, inda ninekai mata biyu zan kara alokaci daya, daya bazawara wacce mijinta ya danna mata saki, tayanda tana auranka zata darajaka tasan aurenta nada auren wahala tayi sanan tabiyu kuma ka auro yarinya danya sharaf, kabula abunka kaci ana maka godiya iyaye na zuwa maula, kuma kanuna musu duk wacce tamaka hauka danna mata saki zakayi ka koreta daga gidan nan fess zakaga ana kappa kappa dakai, sanan dukansu agidan nan zaka zubasu wlh kanayi kana gumama Hassana tasan cewa kaiba nawasa baneba” wani irin kwashewa sukayi da dariya bana wasaba, da kyar suka tsayarda dariyan Baban Khalid yace “to yanzu yaya za’ayi zanyi managing mata guda biyu a lokaci daya kuwa? Sanan gakuma Hassana su uku kenan” “kai waketa wani maganing kai manager ne? Suyi managing kansu dai kai kazuba musu kudi kayi gaba abunka” dasauri yace “itakuma Hassana nasan yanda zanyida ita wlh zata ganewa hayazaki saitasan tayi kuskure abinda tamin” “correct yanzu kai magana Gwamnati amman da ka tsaya kana wani magana kaman wani wawa” murmushi yayi sosai yace “to yanzu dai yaya zamuyi banda wacce nakeso” dasauri yace “kai! Wake maganan wani wacce akeso anan wurin? Yanzu dai akwai wata mata danagani a office dinka, mai zuwa muku shara da mopping” dasauri yace “Mrs Saudatu” dasauri yace “yes ita kaga matarnan akwai kayan harka ajikinta kuma bakacemin mijinta yamutu ba?” Dasauri yace “yes mijinta yamutu, tanada yara uku though wai basa tareda ita suna family mijin ni tausayi ma tabani nabata aikin sabida yaran” dasauri yace “to itace bazawaran dazaka aura, worker dinka ce dagudu zata yarda and kabata kudi dajin dadi she go craze follow u, banda haka kanuna mata bakasan auren yadauki lokaci zaka mata komi na kayan daki, kawai tafadama nawa takeso sadaki azo adaura aure bakason bata lokaci period zakaga jikinta yafara rawa, kafin auren ma kana kiranta office fara da bata…
Inkika karanta batare dakin biyaba zaki biyani ranan dabaki dashi, this book is not a free book, pls support me.

 

 

 

Wuraren 12 yakai office direbanshi yafito yabudemai baya yafito yana sanye cikin suit yayi kyau, security guard nahangoshi yabudemai kofa ya shiga, anan reception yaga wata mata zaune da Hijabinta ash color ajikinta dayadan kunne takusada gefen wuya, black beauty ce itama kyakkyawa abinta kana ganinta kasan ba yarinya bace zata iyayin 39 kokuma 40yrs haka, saidai batada jiki kaman Hassana, ita siririya ce, tana ganinshi harwani ijiyan zuciya tasauke tana addu’a Allah yasa ba laifi tayiba wanan da sakatare yace “Oga yakira yace tajirashi karta tafi, batare daya kalleta ba ko amsa gaisuwansu yawuce sama sanan yabude katafaren office dinshi dayake a gyare yashiga tareda zama a chair, saida yabata kusan 15min dudda babu abinda yake sanan yadauki wayar office yakira sakatare yace “aturomai ita” ijiye wayan sakatare yayi ya kalleta yace “Sir is ready to see you now” gyadamaikai tayi ahankali sanan ta tashi itama tai sama saida tai knocking kofar aka bata izinin shigowa sanan ta shiga ahankali tareda kofa yana zaune yakafeta da idanu, sanan yanuna mata daya daga cikin kujerun dake gaban desk dinshi yace “sit” karasowa tayi tazauna gabanta nafaduwa tama kasa magana batasan anything dazaisa tarasa this her work dan ana biyanta da kyau dashi take saima yaranta da mahaifiyarta yan abubuwan daba’a rasaba, anatse cikeda tsoro tace “yallabai gani nan Allah dai yasa bawani laifin nayiba, ance kana nemana duk tsoro yakamani” murmushi yasakin mata ahankali saikuma yagyara zama yadaura hannunshi kan table yace “niba yaro bane, sanan kema ba yarinya bace, so I would like to skip all the talk and cut to the chase” dasauri ta gyadamaikai har lokacin gabanta nafaduwa, sanan anatse yace “aurenki nakeso nayi Saudat, ni bana harkan yara ko harkan iskanci, kinmin inaso na aureki na killaceki agidana a inuwata, all abinda kawai nake bukata itace yardanki da amincewanki, banson kiyi tunanin kaza kaza kaza ko abubuwan dazaki kawo gidana kokuma wani abu, nariga nasan kewacece, nasan karfinki saisa zandaukemiki duk wani nauyin kayan daki dawace tsiyace ke kawai kadai zaki shigo gidana, sanan bansan wanan hayaniyan bikin da sauransu niba yaro bane, sonake dazaran kin yarda kawai a daura aure dayar walima nazo nadaukeki nakaiki dakinki” yanakaiwa nan yay shiru yana kallonta kaman yanda take kallonshi in a total shock, saikuma tadaura hannunta akan kirji tace “Yallabai ni? Kodai mistake kayi? Ninefa Mrs Saudat mai shara da wanke bayi da mopping a kampaninka” gyadamata kai yayi yace “kwarai kuwa nasan kece, kuma kedin yanzu nake kokarin namaidake matar mai kampanin gabaki daya” yay maganan yana kallonta yana murmushi yace “by the way bazan takuraki ba, zan baki dagayau zuwa gobe dan banison bata lokaci kiyi tunani, idan kin yarda ayi, gobe war haka ina jiran amsa” gyadamai kai tayi tama kasa magana still, saikuma ahankali tatashi zata juya yace “tsaya” juyowa tayi takalleshi wasu code ya danna a drawer table dinshi sanan yajawo table din kudine burjik aciki, rappa na dubu dubu yadauko guda uku that’s 300k yamika mata yace “take this, use it ki bata kanki dashi, ina jiranki gobe” kallon kudin tayi tana zaro ido daikuma ta kalleshi, babu wasa yace “karba mana Saudat nakine” mika hannu tayi ta karba zata zube tamai godiya yace “banson godiya wuce kitafi” wucewa tayi tafita daga office din rikeda kudi, tana fita ta tsaya taciro handbag dinta tazuba kudin aciki sanan tasauka kasa tafita tana wani irin farinciki wayyo dadi.

Tana fita yakira number Attajiri yace “nayi yanda muka tsara” kwashwwa da dariya Attajiri yayi yace “she is coming back with a yes na me tell u kawai kaman kayi aure kagama, ga wanan gidan, uwarsu da su kansu yaran sun rude, Maman harda kukan murna, nace musu gobe zamuzo tare, sati biyu mukeso asa sunce sun yarda, yanzu kira masu furnitures azuba kaya afalo, kasake komi sabo sabida kar hassana tabaka problem kayan falon dana kitchen duk akai store kazuba sabo komi yazama mallakinka kayanta atattare matasu a store” cikeda farinciki yace “angama abokina” .
*************

 

 

 

 

Tana zaune a falo itada yar aikinta dake matsa mata kafa akai sallama yar aikin ta tura ta amsa saigata tashigo tace “wai Alhaji yaturosu” shigodasu tasa akayi, gaidata sukayi cikeda respect sanan sukace “Hajiya Alhaji ya aikomu, yace mu kwashe duka kayan falon nan, da kayan kitchen dakuma kayan dakunan sama banda naki mukai chan store, wai za’a zuba komi sababbi ne” shiru tayi kaman mai tunani saikuma tace “okay” tashi tayi takalli yar aikinta tace “zaki iya wucewa gida yanzu Bibalo tunda kinga aiki za’a min” “tom Hajiya” tai maganan tanayin hanyan waje itakuma tawuce sama tashige dakinta tareda maida kofa tarufe, daman dakunan saman bawani kayan kirki bane aciki dudda kowanne da hadaddun gado aciki ga dakunan fadi da girma sosai, tanaji anata kwashe kwashe ana fitarda kaya hakanan taji tana kewan Murtala dayananan dayanzu tasa yafita da ita dan kara ya isheta, haka sukai aikin nan har yamma basu gamaba saidai suka hakura gobe zasu dawo sukarasa, koda ta sauko kasa saitaga gidan kaman banata ba, komawa kawai tayi sama abinta.

 

Washegari ne suka karasa fitarda komi sanan aka fara wani irin mahaukacin Fendi, ko’ina na gidan harda kitchen din, dansai fentin yabushe tass sanan za’a shigoda sababbin kaya, kawai she’s feeling way to lonely inama ace ranan visiting yaranta ne yau dataje school dinsu wlh kota gansu taji dadi, tama rasakan gane gyaran me Baban Khalid yakeyi duddda tasan yanada yawan gyara gida, but tasan at this point dasukai fada bazai gyara gidaba to kodai that’s his own way of saying sorry ne, kwanciya tayi kan gado sanan takalli agogo taga 6 but haryanzu Murtala bai dawoba kodai bazai dawo yaubane amman kuma baya ketare dokanta, gashi har masu aiki sun gama sun bude kofofi da windunan falo sun tafi sabida fentin yasha iska, tashi tayi tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla tazauna tana lazimi tai kewan gidansu tanaso taje gidansu taga Babanta, kuka takeji amman tahana kanta tadaure kawai tazauna tai shiru tana wajen aka kira isha’i ta tashi tayi tai shafa’i da wuturi sanan tasake zama tai shiru gabaki daya ranta bayamata dadi.

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da Ζ™asaita take saukowa …

One comment

  1. I need a job like driver like security guard

Leave a Reply

Your email address will not be published.