MATAR GWAMNA Page 11 to 20 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / MATAR GWAMNA Page 11 to 20

MATAR GWAMNA Page 11 to 20

MATAR GWAMNA Page 11 to 20

…..d’agowa nayi fuskata na rike a tattausan hannunsa idanumu ya sek’e guri daya gabana naji ya fadi tun karfi yau sosai ya rikidemun tamkar my Haidar DINA fuskarsu ce kawai Takeda, banbanci acikin rawar baki nakai hannuna saman kyakyawar fuskarsa na shafo na taba dogon hancinsa nace ” me… Ya… Sa ka.. Ke.. Kama.. da… My Haidar DINA?? hannusa yasa ya shafo hawayan fuskata ya kai bakinsa ya shanye can k’asan makoshi yace” My haskena wlh sonki yamun mugun kamu please kisoni kinji Rabin Raina Fatima bintuna? ya fada yana cizona a tafin hannuna da sauri na janye hannuna daga fuskarsa na sada kaina ina yarfa hannu nasaka masa kukan shagwaba “wayyo hannuna ancinye mun hannuna da sauri ya riko yatsar yana huramun iskar bakinsa ” Sorry my heartbeat nine ko yi hakuri bazan kuma ba ai kece kika tabamun fuska niko na cijeki ya fada ashagwab’e yana sakin hannuta dan yaga rigimace takeji babu wani san hakoransa ” my Fatimana zaki aureni?? “ni bazan soka ba duk nafara jin wani iri saboda kana mun kama da Haydar amma duka na hakura wlh shima zan cireshi araina please kafita rayuwata ko na zauna lafiya kaga kai babane ka haifeni banason namaka rashin kunya daga yau bani bakai nakai karshan maganar ina shasheka fuskata ya saki ya shafo hawayen ya shanye ya had’e face” My teemah kinsan Allah hadiye kukan ki yanzu nan ki maida wannan zazakan hawayen Wanda yafi Zuma dadi awajena idan ba hakaba Allah Rumgumarki zanyi na kamo fuskarki na nasaka harshena na tsotse hawayen tas idan kinyi musu ci gaba kigani?

kai na dago ina zaro idanu muna hada idanu naga gaskiya abinda ya fada afuskarsa neman kukan nayi na rasa har hawayen sun koma tamkar baniba na nutso murmushi yai afakaice yanajin nishadi sosai wayarsa da take kusanta ta dauki ruri bai dagaba na kalli wayar ni abun mamaki yake bani kullum da wayoyi da uban tulun kudi kusa dani wani Kiran aka sake ” my heartbeat bani wayar kusanki kallonsa nayi kamar bashi yai maganar ba baki na tabe nima na juya kaina ” haskena dake nake My Fatimana kibani wayar kusanki kinji matar gwamna? baki na turo na juyo ashagwab’e ina magana ina kallonsa ” Aminullah meyasa, kakemun hakane?? juyowa yayi amma baimun magana ba dan dama idan baisa kansa magana ko zaka shekara kana masa mita ko ajikinsa tsareni yai da rikitatun idanunsa muna kallon juna har bamu san lokaci ya jaba saida mukaji direba ya tsayar da mota da sauri na sada kaina cikin shagwaba yamun magana murya can k’asa ” my Fatimana yanzu rabuwa zamuyi sai yaushe zaki soni gabaki daya jikina ya saki jinsa nake tamkar Haidar amma na dake na dago ina turo baki ” ni bazan soka ba baruwana dakai? ” ni inada ruwa dake my heartbeat anjima zamuyi waya? ” bazan dagaba ” baki isaba kinfa kamu nasani
Muryata namiki sugar baki na murguda na bude motar taki buduwa na juyo na kallesa ashagwab’e buris yai dani ya juya kansa ya dauki zabgegiyar waya yana latsawa takaici ya cikani kamar na shakoshi nakeji kallonsa nayi yama ki juyowa haushi yasa na beka hannu na warce hawar hannunsa kallona yayi ya dagamun gira yana tambayata da idanu lfy kaina na sada wata wayar ya dauka yana latsawa murta na rawa nace” Aminullah kasheni kakeso kayi ko? nifa banason wulakanci wayar ya ajiye ya amshe ta hannuna ” ni da kikemun Ashe ba dadi to me nayi miki ko neman fada ya fada ashagwab’e ” ni budemun mota kuma insha Allah kuka ne kakeso nayi bazan yiba murmushi yayi ” my heartbeat wlh banso kiyiba dai da tuni kinyishi na shanye sweet hawayenki banaso ki fada dayawa ne ya fada yana daga mata gira banza nayi dashi na dauke kaina saida ya ida Jan fadansa yaga ko juyowa batayi ba ta kallesa ya ajiye wayar murmushi yai”my Teema uniforme dinki tayi datti sosai ya fada yana yatsina fuskarsa wani kululun bakin cikine ya tokareni hannusa ya matso ya bude mata motar ” gaskiya jeki kiyi wanki wai ya fadi yana toshe hanci ai ko juyowa banba na sabko nayi hanyar gida ina danne kukana kai ya girgiza yana sakin murmushi direba yaja motar wlh inajin dadin tsokarki burin raina wayar kusanta ya janyo ya kira wata number bugu biyu daka daga ” Alhmdllh wlh komai yanamun yada nakeso wlh yarinyar akwai tarbiya sam bata dubin abun mutum samun mace irinta sai antona yanzu matsala biyu ta ragemun itama zan kara Sata jikina har na magan ceta dayar matsalar ko ta wancan bangarance? ” ok kubi komai akan tsari bye ya tsinke Kiran ya lumshe idanusa yana sakin murmushi hannusa saman kyakyawar fuskarsa yana taba inda Watsime ta taba, watsime na shiga gida saida ta tsaya kofar parlo ta gyara nutsuwarta saide kamshin turaren Aminullah ya baibayeta duk da bai taba ko inantaba sai fuskarta da sallama na shigo suna zaune har yaya Mu’azzam sannu na musu wuff na shige bedroom d’ina inaji suna kirana ina ajiye jakata na shiga bathroom acan na cire uniforme ina sunsunawa babu wani wari saima kamshi tsaki naja nayi wanka na fito dauré da towel ko jiki ban gogeba na daura zane nasaka hijab na fito
” Aunty yunwa? nakeji dariya mu’azzam yayi ” watsime daga zuwa sai kice yunwa muma bamu ciba kusan Malika ta zauna dariya Malika tayi” my darling kafiye tsokana tashi kije kici ” Aunty kice Yaya yabar fadar sunan ” na bari tuba nakeyi murmushi tayi ta Mike tsaye ” ‘ya’yana kuzo muje kan dining binta sukayi baby sai hannu take dagawa Teemah mu’azzam ya dauketa yana shillawa ” yarinya momynki yunwa takeji bari ta take cikinta Malika ta kwanto jikinsa takai bakinta kunnesa tamasa rada idanu ya zaro ” Allah da gaske ko wasa, my tawan karfa ki kunnomun wuta ki gudu dariya tayi takai masa dukan wasa ta turo baki ” to na fasama murmushi yai ” ok yi hakuri bari na rigaki da babyn ya Mike ya nufi bedroom sai dariya take masa Teemah bayan sun gama cin abuncin suka dawo parlo ” Aunty na tafi na huta” yauwa jeki da yaranki ku huta hannusu ta ja suka nufi d’aki Malika ko ta mike ta nufi gun mijinta, Teemah suna shiga ta kwanta su shuraim suna wasansu wayarta ta fito da ita yako kirata har sau uku baki na tab’e na shiga whatsapp idanu na zaro ganin kalaman soyayya masu mutikar dadi da sanyaya zuciyar masoyi kin mayar masa nayi na tura masa *babu ruwanka dani bakace wari nakeba* hoton wata kyakyawar yarinya ce kan dp din baya online haka na tura masa *Aminullah wannan kyakyawar yar kace wow ta burgeni💋💋💋* na rufe data na na sauka wayar na kwanta idanu na lumshe ina tunanin abubuwa da dama har bacci ya dauketa su Rashesd sai wasansu sukeyi atsakiyar d’aki,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
da misalin karfe tara na dare zaune suke bayan sun gama cin abunci hirasu suke cikin nishadi Teemah tace ” yaya wlh marmarin ganin iyayye nake da Abbana dariya yayi ” ai kuna kammala jaraba zaki ki kwana biyu barima na baki su kuyi fira Kiran Abba yai ya bata daide lokacin suna tare da Nawalu yau harda kukansa sai anbashi watutunsa ya aura idan ko anyi mata aurene afada masa Abba ya rike baki yana mamakin wannan lamari wayarsa tayi kara ya daga da slm “Mu’azzam kuna lafiya ko? ” lafiya lau Abba ga mutuniyar tanaso ku gaisa ” to bata amsa tayi ” Abbana ina yini ina iyayye wlh ina kewarku kamar na taho? ” auta kiyi hakuri zaki zo ai ga nawalu ku gaisa baki ya washe hakora jawur ya amshi wayar da karfi yake magana” Allo watutu ya binni dan Allah ki dawo dan su rabu lfy ta dauré tayi dariya” lfy Nawalu sarkin kazammai uban yan dauda ya *garin Sarki* kowa lafiya ko? ” wlh lahi muke gani gun babnamu? ” to yayi kyau bashi wayar karka sake zuwa kabari idan nazo zan nemeka ” to hikenan nagode Abba yaba wayar ya nufi gida iyayye na zaune tsakar gida ya shigo ya bata wayar sun jima sosai suna hira daya bayan daya watsime yau shagwaba ta motsa sai daket suka lallabata sukayi sallama mu’azzam yau yaci dariya saida ya wuntsulo daga kujera saboda duk abinda sukayi da nawalu yanaji da Wanda Abba ya fada masa nawalu namusu zirganiya agida Teemah abinda yamata haushi dan ta tsani dariya kuka ta saka musu sai daket mu’azzam ya lallabat ya bata hakuri kafin ta sabko Malika ma danne dariya ce tayi cigaba sukayi da hirasu sai goma da rabi Teemah tayi musu sallama taje,
Tayi shirin kwanciya akwance take sai juyi take wayarta ta dauko ta duba har yanzu bai bude data ba bare ya hau online wayar ta aje tana juyi har bacci ya dauketa,, governer house Zaune suke a tamkamemen parlon su Aliyu yana manne da farin gilashi laptop ce gabansa yana dannawa da hannu daya hannu dayan waya manne a kunnesa Rauda na bayansa akwance sai dariya takeyi ” Dady kayi tsaye mana ka zagaya dani bintu na gefe kankana take sha ayangace da tulelen cikinta sai kace ya isa haihuwa shiko watansa bakwai ne sai murmushi take ” baby kibar Dady yayi waya mana wlh zanzo na sabkeki duk kinbi kinsa masa gajiya kukan shagwaba tasa ” Dadyna kaga umma ko hannunsa ya cire daga laptop ya beka yana buga bayanta ya cire wayar akunnrsa ” babyna rabu da bintu haushine takeji yi kwanciyarki bayan Dadynki dariya tayi wayar ya mayar kunnesa ya kalli bintu ya daga mata gira baki ta turo ” my man ni ko? gwalo yamata ” ke ko baby zaki san inda zaki kwana badai ajikinaba ” eh umma na kwana gun Dadyna sauran yaran kowa na sha’aninsa tamkar dare baiba makekiyar TV dake parlo manne abango game ne yaran suke masha Allah sai yau na kare musu kallo su uku
ne babban zai kai 15 year sai mai binsa zaiyi 13 year sai mace yar 10 year sai Rauda wacce take bayan dadynta tana da 7 year fararene tas kyawawane masha Allah bintu ta kalli agogon bango ” Asif mukutar muneerat Oya atashi shabiyu fah aje akwanta akwai school gobe fah” Muneerat tace ” umma munkusa gamawa Aliyu yana jinsu kai ya girgiza yana aikinsa! My man kace musu su kwanta dare yayi kalli wannan uwar rigimar har tayi bacci a bayanka nidai bazan daukaba shiru ya mata ya kalli Asif ” Oya mamana maza kuje ku kwanta TV suka kashe suka nufo gun dadynsu kiss suka masa daya bayan daya sukaje sukama bintu mukutar da Asif suka nufi bedroom d’insu muneerat ma ta nufi d’akinsu ita da Rauda tana fadin” umma ki kawomun my Rauda? ” Ok Dadynku zai kawota ba yanzu suka gama cimun fuskaba murmushi yai ya juyo da Rauda ya rumgumeta ” babyna kin gama fitina kinyi bacci kin hadani da bintuna ko baki ta tabe ta Mike ta nufi wata kwana ta shige bedroom d’inta mik’ewa yayi da Rauda ya kaita d’akinsu ya kwantar da ita saman wani hamshakin gado Addu’a ya musu ita da muneerat ya lulubesu da wani lalausan bargo ya fito d’akin bintu ya leka
tana bathroom zama yai har ta fito shi ya shiryata tsaf cikin kayan bacci sai turo baki take ” my bintu yi hakuri muje na baki wani Abu mai dadi ya dauki abarsa sai dariya takeyi saida ya kaita bedroom d’insa ya kwantar da ita da kallo tabishi parlo ya fito yajima ya dawo ya shiga bathroom yai wanka ya dauro Alwalla ya fito bai tsaya goge jikiba yasaka jallabiya ya fesa turare ya kalli bintu ” yan matana ki jirani? baki ta tabe sallah ya tayar yau ma raka’a hudu yayi ya zauna yana Adu’a bayan yagama ma kansa Adu’a da neman tsari ga makiya na fili da na boye bakinsa na Kiran my Noor dinsa yana Adu’a yajima sosai sai karfe biyu ya Mike ya cire jallabiya yasaka kayan bacci bintu anyi bacci gadon ya hayo yasa hannu ya kashe wutar d’akin ” my bintuna tashi yau kwana biyar ai nayi hakuri rikitata ya fara da salon na musamman Dole ta tashi ta bashi hadinkai can naji cikin shauki na dibarsa yace” My bintuna meyasa baki nunamun kinjin dadi ko akansin hakan sai kibarni ni daya ina sambatu please kiyi mun kuka naji inason hakan ya fada cikin wani hali shiru tamasa sai nishi kadai takeyi dan inda sabo ya saba sam bata iya sarafashi ba saidae shi ya sarafata gashi batasan yada zata lallashishiba taji damuwarsa saidai shi yamata batasan ta shiryashiba saide shi ya mata wanka ya shiryata sai dan banzan kishi da sonsa kamar ta mutu haka ya yayi ta bidirinsa shi daya haushine yasashi ya mirgina gefe bai bari ya gamsuba sabka yayi daga saman bed d’in ya shige bathroom yayi wankan tsarki bayan ya fito ta mike taje tayo wanka kusansa ta kwanta ya janyota jikinsa ya rumgumeta dan yasaba da halinta sam bata nuna masa taji dadi ko bata jiba saidai tamasa ki kam agado yayi ta sarafata amma hakan baya damunsa sonta ya rufe masa idanu yana tunanin ko haka halitarta take batajin dadin saduwa yanzu yaji yana shawar kara aure ya banbance ya abun yake ahankali ya furta My Noor tawa” my man kayi fushi ne kayi hakuri ” shiru my bintuna bakya laifi gun mijinki Aliyu maybe halitarki ce haka bakijin dadi ” my man inaji fah murmushi yai bakinta ya kamo yana tsotsa yaja musu blanket Atashi lfy Asubah ta gari,
*********** ***** ***********
*Bayan kwana shida*
Yaya mu’azzam ya koma gun aikinsa saimu muke sha’aninmu nida Auntyna nida Aminullah kullum sai munyi fada saboda yada yake tsokanata sai yasani kuka yakomo lallashi idan naki yin shiru yace wlh zan cutar da Aliyu gwamna Dole nake shiru duk da sonsa yamun mugun kamu saboda tsantsar kamarsa da gwamna da yanayinsa amma fur naki ya gane na kafe nace bana sonsa kuma tun ranar da ya kawoni daga school naki yada mu hadu yayi yayi dani mu hadu yaga fuskata naki kuma ko school zantafi niqab nake sawa bana yada nayi ko wajan get dan jinake yaransa da karfi za’su kamani sukai ni gunsa duk da yace yau kwanansa biyar baya gari wai yana London kullum waya muke gatsautsau nake masa cike da tsiwa nacemasa bayada zuciya yabar kirana amma ya kiya guri daya yake samuna idan ya faramun shagwaba sai nayi lakwas ina. lumshe idanu nima nashiga zuba masa shagwaba da kukan sangarta wai ya takuramun yasan ba sonsa nake ba yai ta lallabani haka muke rayuwarmu amma har yanzu bai san na fada tarkon sonsa ba saboda yada yake ririta da rikitani da kalamai ta chat yaune kwai bamuyi wayaba niko dama bana. kiransa koda wasa idan bai kiraniba duk ina son jin muryasa da yada yakemun shagwaba kamar wani dan yaro gidan gwamna ko nafasa zuwa amsar sadaka saboda tsoran karsu tareni jiya har na dawo daga school banga basawa ba basu bimuba,
yau ta kama weekend ce jiya maheeda gidanmu ta wuni nima yau na shirya naja su shuriem muka tafi direba ya kaimu bayan sallah azuhur,gidansu kamar su hadiyemu dan mamarta akwai son mutane tunda haseem yayanta ya ganni yake shiga da fice ya kasa zama dan bai sanniba Abuja yake yazo hutun karshan makune, kallon ya fara damuna da misalin karfe hudu muna zaune bayan munyi sallahr la’asar na kalleta” my maheena gida zamu inaso naje islamiyya malam wlh shekaran jiyama yamun fadan lati” muje NASA direba ya kaiki ko muje ma tare sai mudawo nagadai zuwanki lafiya murmushi nayi naje nama mama sallama tayi ta samun Albarka harda su turaruka da wani Abu aleda tabani nakaiwa aunty ina rike da hannu rasheed mahee na rike da shuriem muka fito harabar gida maheena ma direba magana sai ga haseem ya fito daga part dinsa gunmu ya nufo lokacin har direba yazo mun shiga mota dadi naji motar na fita yabiyo bayanmu a motarsa hira muke har muka kusa” my teemah kinsan Usman ya matsa ya turo nace yabari mu gama karatunmu na secondary tunda mun kusa, amma wlh jinake kamar nayi tsutsuwa na ganni gidansa wlh akwai love ranar dariya teemah tayi takai mata dukan wasa ” Allah shiryaki ke ko sai son love nide ba ruwana dukana tayi mukasa dariya dede lokacin motar ta faka kofar gidanmu muka fito har ita idanu na zaro ganin iliya mai shayi yaci uban zanzaro da wata uwar malafa akansa, kofar gidan muka karaso nayi kicin kicin zan shiga ya tare kofar ” haba bintotona wlh nafi rabin awa atsaye mai gadi yace bakyanan amma najira lokacin islamiyya kina hanya maheeda me zatayi idan ba dariya ba harda rike ciki ” wlh my Teemah da Nice nakeda farin jininki da tuni nayi aure na karasa secondary school agidana takaici ya cika Teemah ta juyo ta kwakwabe fuska tana kallon maheeda daide lokacin haseem ya Iso gunsa teema ta nufa dan iliya mai shayi ya hanata wucewa sai surutu maras kangado yake mata ga maheeda namata dariya kofar motar ta tsaya tana jiran ya fito tace ya sata cikin gidansu…..✍🏻
*😆 to masoyan matar gwamna wannan bashin jiyane naga ruwa kira shiyasa na dauré nayi muku Aradu idan comments d’inku bai munba bazaku samu na gobe ba sai zuwa Alhamis😂*
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Written By*
 Y’ar ilu 😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*🤔🤔🤔oh ni Yar ilu🤣🤣🤣yo ku irin wannan kira haka Aradu sai kukashewa Yar ilu batrin waya😂 Amma ina yinku irin total Dinan kamar yada kukeyin matar gwamna love u Lodi Lodi*😘😘😘
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page* 8⃣
…..tsaye tayi tana jiran fitowarsa motar ya bude ya fito yana murmushi ” kanwata ya dai me ya hadaki da wancan sakaran ko shara zai zubar mukune? kusansa na matsa na shagwab’e tunda ni shagwaba tabi jikina nace masa” yayamu kasan me?? ” sai kin fada? ” dan Allah muje ka rakani ciki iliya mai shayi ya matsamun wai sona yakeyi Haseem jiyayi ransa ya baci hannu ya beka da niyar rike hannuta suje gaban iliya yamasa mugun kashe yafita bayanta ya kama hannuta yaji wani uban mari dama da hagum ansa kafa an harbashi nan take ya fadi ya shakushi kinan wayar boos tayi kara ya daga” Ranka yadade hannuta zai kama dagacan yana zaune sai juyi yake saman lumtsumemiyar kujera ransa ya gama baci wani azababan kishine ya tokareshi baki ya bude daket yace” boos kabishi kamasa kwakwaran kashe amma banaso ana duka itako kuyi dubara ku hadani da ita ayau yanzu inada baki sosai zanyi kokarin sallamar kowa kafin karfe shida duk hanyar da zakubi taje amsar sadaka gidan Aliyu gwamna kuyi kokari tanan kade zan samu ganinta har nayi hira da ita kaga yanzu ta toshe hanyar da zan ganta kuyi kokari kitt ya kashe wayar sakinsa boos yai mik’ewa yai ” malam meye hadinka dani ya fada yana zage zage ” kai kashiga taitayinka bakai ba ita wlh idan kaki kayi kuka da kanka Maheeda duk ta rude harda, kuka ita da teema dan Haseem ya maru sosai😅 boos gun iliya ya nufa shiko harda,washe baki😆 ” gaskiya nagode da karamawa wai da saboda rashin d’a’a kama mata hannu zaiyi yana zuya ya matse iliya abango ai nan take ya fara zaro idanu ” kai inaso daga yau bakai ba wannan yarinyar idan ba hakaba ya nuna masa bindiga cikin rudewa yace” yallabai ayi hakuri don Allah inda yara dayawa sakinsa boos yai yanufi mota ai da gudu iliya yabar wajan Teemah da take tsaye tanaba Haseem hakuri har gun motar boos taje taname rashin kunya ” kai gabjeje baki
wlh sai nasaka anyi maganunku agarin gombe mugaye azalumi zan kira oganku na kirta masa fitsara kai nifa wlh abirni ne banida fada ku fita bayana kaida ogan ku ” Ok jeki Allah baki hakuri bamu bake oga yayi tafiya sai bayan wata uku zai dawo bazamu kara shiga zabgarki ba sai yadawo jin haka yasa ta barsa ” yauwa ayi GABA yau Ashe zanci karena babu babbaka taja tsaki ta bar gun lokacin da ta ISO Haseem ya tafi ransa abace ya dauki aniyar bazai bar teema ba saboda wannan sojan hayar maheeda tace” my teema ina kika kwaso wannan? ” dallah can rabuda banzaye wani Aminullah ne ya dameni honr direba yama Maheeda ” my Teemah gobe zamuyi zancan ta fada tana shigewa mota suna dagawa juna hannuwa har motarsu ta bace teema taja yara suka shige cikin gida rasheed yace Aunty suwaye” kai imun shiru idan ka fadawa Aunty Allah bazan kara zuwa unguwa da kaiba yaro sai baki kamar kaci hatsin kasuwa shuriem yace ” bazan fadaba parlon ta shigo
da sallama Malika na waya da Mu’azzam kusanta ta zauna ” my darling gasu sunzo wayar taba Teemah ta kara akunne” yayana ina yini? ” watsime manya Ashe gari kika tafi? ” haba yayana wlh zanyi kuka ” yi hakuri amma teemah kirika zuwa islamiyya ” yayana ina zuwa wlh yanzuma tafiya zanyi ” ok maza ki tafi banason wasa da karatu bani Malika bata wayar nayi na Mike naje na shirya Abaya Nasaka mai adon bleu da baki tayimun kayu sosai hijab ma bleu nasaka amma mai niqab ne dan inada niyar zuwa amsar sadaka turare na fesa, mai dadin gaske Wanda yaya mu’azzam ya kawomana wayata na duba naga yakirani har sau biyar jinayi inason masa, magana wayar nasaka cikin rigata na dauki Alqura’n na fito ban tsayaba na fice ” Aunty sai na dawo ” wow duk kin rufe fuskarki kinyi kyau Autar Abba dariya nayi na fice ina fitowa makarantar islamyyar
Na nufa na dabu masu naci babu su babu dalilinsu dadi naji na ciro wayar na kira Aminullah bugo daya yai picking amma kinyin magana yayi ganin nakusa makarantar yasa nace”hello yo meye na yin shiru namiji da yanga kamar mace shirundai baice komaiba ashagwab’e nace ” Aminullah ni kakewa cin fuska ko? shima shagwabewa yamun magana cikin amon muryasa mai dadin sauraro” to bake baceba kika tara maza kofar gidanku bayan kinsan inada kishi akanki my Fatimana meyasa wani dan iska yaso tabamun hannuki ” ni ban saniba yo ina ruwanka dani sai karika kashemun murya kanamun shagwaba duk kasa naji kamar inajinka araini ta fada ashagwab’e ” zakiyi bayani sai mun hadu anjima wlh sai kin gayamun dalilin da yasa kina kallon wani banza ya kama miki hannu har yanzu zuciyata zafi takemun sai na horar dake zan huce ” to ina ruwanka dani shi ai saurayinane ina sonsa wata uwar tsawa ya buga mata wacce atake ta rude ta gigice ” Zahara ni kikecewa haka wlh zaki sani anjima zamu hadu wlh sai na ladabtar dake maza kashe wayar ki shiga cikin islamiyyyar ilove haskena sai mun hadu anjima kitt ya kashe wayar idanu ta zaro atsorace ta duba gabas da yanma kudu da arewa bata ga kowaba tunani tayi garin surutun tace gata hanyar makaranta tsaki taja ” haka kawai sai kasa naji ina sonka kuma gashi na batama rai kamun tsawa baki ta turo My Haidar kana ina kai ka gujeni amma ga mai kamarka na samu yana sona gashi daga wasa ya rikice wlh bazan yadaba yau muhadu dukana zaiyi ta fada idanuta na tara kwalla zuciyarta babu dadi shigewa tayi cikin makarantar,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
governor house fitowa yayi daga wani hadaddan parlo sojoji biyu na biye dashi da bindigogi waya manne kunnansa wayoyi biyu dake rike hannun wannan karkarfan sojan dukansu ringing sukeyi bai amsaba dan magana yake da mahaifiyarsa duk da haka zaka gane bayada walwala sai zuba kamshi yake ya hade cikin wata dakekiyar shaddah grey colour tasha wani uban zubi sosai yayi mugun kyau kwarjininsa da haibarsa sun fito sosai tafiya yake cikin dataku da har yanzu yanaji da karfinsa duk shekaru sunja wata kofa sukabi sai naga anzo kofar wani ratsatsan parlour juyowa yai ya kallesu ” yallabai afito lafiya wayoyin suka bashi. adakile yace” kaisu mota zamu fita juyawa sukayi wayoyin na ta neman ceto amma bai dagaba dan wasu ba saninsu yai ba shi yafi son daga wayar mai anfani kamar yayi taimako koko akan mulkinsa kodai wata matsala da ta shafi siyasa amma ta gaskiya Abu dai mai anfani ba shirman banza ba dan tsokana kin shiga yai ya kira wata number bugo daya aka daga lankwashe murya yayi yana tari” hello my bintuna gani akofar parlo ba lfy azaune take ta mike tsaya cikin tashin hankali ta kwalla kara ta manta da wani cikinta da gudu ta nufo kofar parlon tunawa yayi yanzu zataje ta jimu ga cikin ajikinta da gagawa ya bude kofar parloun wada dukanta Gilles ce ai kuwa ya tsikayowa tana gudu hawaye shabe shabe a fuskarta ” tauraruwata ki nutsu wasa nake miki da hanzari ya nufota yana ware mata hannuwansa samansa ta fada ta saki kuka jikinta ko ina rawa yakeyi dukansa ta fara ” my man kabarmun wannan wasan nakasa sabawa rumgumeta yayi gam yana buga bayanta” sorry my bintuna bazan karaba yi shiru daukarta yayi sani yaran basu gidan yan aiki kuwa suna bangaransu sai an nemesu ya rumgumota suka nufo parlo fuskarsu ta hade ta sakalo hannuta ta wuyansa ta kamo lips dinsa tana tsotsa har yanzu hawaye takeyi cire bakinsa yai ” my bintuna bari mu isa kan kujera karki kada mijinki bana ganin gabana habarsa ta kamo tana tsotsa duk baya cikin farin cikin saida ta bashi dariya dan yau yaga rigima ta keji gashi ya tabota murmushi ya sakar mata yana kashe mata idanu ya nufi kan wasu lumtsuma lumtsuman kujeron parlon……….✍🏻
Kuyi manage ina busy
 💃🏻Yar ilu ce🤪
Rahmilu ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Written By*
 Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
🤔🤔🤔haba kukuwa masoyan matar gwamna kurmuyi haka daku mana🤣🤣🤣wlh ba Jan aji bane ina cikin busy ne sai hakuri ga matsalar wuta jiya shiyasa amma ga hinan na heko muku Na Kuma Sadaukarmuku da wannan hafin kyauta tumba irinsu🤣🤐🤐🤐🤐🤐🤐
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 9⃣*
…..zaune yayi tana jikinsa k’asan makoshi ya mata magana cikin kunneta” my bintuna yi shiru bari hawayen wasa nake miki yau duk rigima kikeji ko?? ” ya fadi yana shafar cikinta da yake motsi alamu yaron yana koshin lafiya bakinta ta cire daga habarsa “my man naji tsorone bansan me ya sameka ba murmushin gefen baki yayi baiyi magana ba ya janye rigarta ya sunkuya yanama cikin kiss yana mata chakulkuli kyalkyalewa tayi da dariya” wayyo my man kabari ji fa yada baby ke motsi” shiru bintuna babyna nakewa wasa shima dariyace yakewa dadynsa shiru tayi ta tana shafar kwantacciyar sumar kansa tanaji sai magana yake da cikin babyn sai motsi yake sosai Aliyu sai murmushi yakeyi ” babyna zakazo da wani salonka na musamman inajinka sosai ina maka mugun so babyna ya fada yana lasar cibinta idanu ta lumshe ” my man ya dago yana daga mata gira “Na’am bintuna tashi muje mubada sadaka zan Dan fita ” my man ina zaka tafi ina zuwa surutu ta fara masa tana soso masa gashin kansa shiru yamata yana sakin murmushi har tagaji ta leko fuskarsa tana dariya ” my man yan shirun sun motsa ko milonta yai a wuya saida tayi Kara ” wayyo my man zafi baiyi magana ba ya mikar da ita tsaye hannuta yaja ya nufi bedroom d’inta wani irin hijabine me shegen kyau ya hango saman makeken gadonta Wanda Dama itace ta fito dashi ya saka mata dogone har k’asa rumgumeta yayi” matata kinyi kyau dariya tayi
 tamasa kiss saman lips dinsa ” nagode mijina uban ‘ya’yana baice komaiba ya kamo hannuta suka fito adaide karshen parlo sukaci Karo da jiddah daya daga cikin ma’aikanta gidan bintu taja tsaki ta buga mata tsawa”ke jiddah uban me kike nema waye ya kiraki rumgumota yayi ” oh my
Bintuna kin fiye kishi da fitina yi hakuri muje lokaci na kurewa ai tanaga minjita ya tareta wuff tayi gaba janta yayi suka fice daga parlon Dan parlon ba karamin girma bane dashi sai baki take turowa suna karya wata yar kwana wani tafkeken Swimming pool ne da wasu irin kujeru masu masifar kyau gefe rumface ta hutawa an kawatata da kujeru masu kyau ta kusansa sukabi yana rike da hannuta suna gaba naga ko ina flower ne sai kamshi suke sun danyi tafiya kadan na hango ko ina maikatane da sojoji rikeda bindiga kallonta yayi yana murmushi Dan yaga fushi takeyi hannuta ya matsa da karfi ” Ashhh my man ni nayi fushi shiru yamata ganin security na nufosu kusan mutum biyar suna take musu baya anutse suke takawa Aliyu takunsa yake cike da dataku da salon tafiyarsa da bata canzawa tamkar yana yanga ga takunsa na kasaita to itama uwar gidan NASA haka abun yake bintu badai iya takuba kana ganinta tabbas zakasan itadan matar manyace kuma Dama itadin daga gidan akwai ta fito ta kware wajan iya tafiya ahaka har suka fito kofar get aka bude musu get suka fito suna biye dasu da bindigogi almajiran na jere daurin yan dari biyu yaba bintu dauri biyu suka isa gunsu 😂Teemah na hango zaune yau kuwa tare suke rabon suna rike da hannu juna ta kallesa ” my man murabu abiyu mana kai raba nan ni sakarmun hannu nayi gaba na raba kace unguwa zaka ko?? ” no my bintuna tare dake yau zamu raba bazan iya sakin hannuki ba murmushi ta sakar masa haka sukaci gaba da Rabon sadakar bangaran Teemah duk abinda suke kan idanuta tacika tayi fam kiris take jira tayi kuka sai hararasu take tanajan tsaki itace Rabon karshe Dan can baya take zama tafiso tayi ta
 kallonsa kafin yazo gareta tanaga sun nufo gunta ta kauda kanta bintu taba ta kusanta Aliyu ya maida hannusa aljihu yaji wayam kudin sun kare yace ” my bintuna ga wata almajira baki bataba da Sauri watsime ta dago kanta ido hudu sukayi da Haidar kansa ya dauke fuskarsa a murtike jitayi kamar muryar Aminullah tsaki taja hararasa tayi afakaice Dan jitake kamar tayi masa duka bintu ta kalli teemah taga kayan jikinta masu tsada da kyau haka kawai taji yarinyar bata mata ba da haushi haushi ta beka mata sauran kudin hannuta itama ahaushi ta warci kudin har dari biyu ta rabe abiyu idanu gwamna ya zaro cike da mamakin yarinyar bintu cikin Bacin rai ta nufi teemah zata shakota tana magana “ke yar gidan uban wacece da Sauri gwamna yaja hannunta ” haba my bintuna me hadinki da almajira ” my man to ta bude fuskarta wlh baza’a Kara bata sadaka ba kuma bazata Kara zauwaba” Oya muje idan ta bude fuskarta muninta ya firgita mun ke fa ina zan samo maganin firgita cikin tsiwa teemah tace ” wlh… bata idasaba ta kusanta ta rufe mata baki jikinta na rawa saboda sojojin da suka nufo gunsu lokacin Aliyu sunbar gurin yana rike da bintu tsawa ya bugawa sojojin yana tambayarsu me zasuma Almajirai suka bar gurin suna biye da Ogansu har cikin gida sai da suka kaisu har kusan kofar parlo suka juya
suna shiga parlo ta kafa masa rigima ahana almajiran zuwa amsar sadaka ya almajira zata rainata ta fizgi kudi ahanunta tana hararata sai lallabata yakeyi tayi hakuri tana turjewa”my man wlh sai..da Sauri ya cafke bakinta yajata kan kujera suka zube kissing dinta yayi sosai ya rikirkitata da salonsa saida ya kashe mata jiki ya saketa ya Mike yana murmushi ya nufi bedroom. d’insa bai jimaba ya fito ” bintuna sai na dawo ” my man kaje ka biyomun da my Rauda kai ya girgiza mata ” my bintuna suko sauran yarana fah ya fada yana ficewa ana kirasa awaya ya amsa yana fita daga parlon,, Teemah yau iya kuluwa ta kulu matar kusanta tace”ke ko wace irin yarinyace da bakida hakuri Dan yace muninki zai tsorata matarsa kikaso kimasa rashin kunya ai da kinsa an koramu bakiga sojojin da sukayo kanmuba “ni ai banason raini yo ina ruwana da soyayyarsu ai basai sun nuna awajeba yo meye na rike mata hannu a waje dan jaraba da wani katon cikinta kuma da kezan bama kudin Dan bana bukatarsu amma tunda kin koma bayanta wlh bazan bakiba gwara na cicirasu ta fada tana mik’ewa rumgume da Alquran Ninta ta tafi sai cika take tana batsewa
tayi tafiya kadan ta kalli kudin da bintu ta bata ” wlh bazan shiga gida da kudinan ba yo uwar mema zan da kudin kishiya bari na yagashi har zata yaga ta fasa bari dai na bada sadaka tana gangarawa taci Karo da Dan liti mai ruwa wajansa ta nufa ” Dan liti ina yini yanaga itace ya Kara Sauri “ke nifa bana harakarki wlh bazaki jazamun masifa ba da Sauri ta iskoshi Tasha gabansa” dallah can Ana binka da arziki kana gudu”kokuma kina bina da tsiyaba ni matsamun na wuce kudin ta meka masa ” amshi dama sadakace zan baka saida ya waiga baiga kowaba ya washe baki ” kai amma na gode dama yau kasuwar ruwan sai ahankali dariya nayi na beka masa shima yana dariya ya beko hannu zai amsa mota ta taka burki da karfin tsiya boos ya fito aguje yayo gunsu ai bai amshi kudinba ya rumtuma adubu ” Dan liti ka dawo wlh kafiye tsoro kudin ta cikuikuye ta NASA masa cikin hularsa da take sarkafe abaro” ke meyasa kika raina mutane muje Oga na kiranki tsayuwa na gyara na rike k’uguna ” wlh Boos kufita bayana nifa banason naci dazu fa kace kun rabu dani wlh da nasan zan hadu daku bazan fitoba ina dalili can an batamun rai nan ma ku batamun to kace masa baza’azoba sai me najima dukansu sun ficemun araina gwara na nemi Mara’s mata Dan nima inada kishi waya ya kira” Oga wai bazata zoba sai wasu maganganu take? ok na fasa kanta da bindiga kenan idanu na zaro ganin yana saita bindiga da gudu nayi wajan motar Dan har ga Allah na dauka harbina zaiyi da gaske dariya ta
ba Aminullah yada take zaro idanu kamar ba yanzu ta gama ma boos rashin kunya ba motar ya bude kafin ta iso ya kauda kansa shigowa motar nayi ina maida numfashi na ajiye Qura’an dina gefe wani irin ni’imataccen kamshin ne yake tashi jikinsa mai dadin gaske Boos ya Iso ya rufe motar ya shiga driver yaja suka tafi kallonsa nayi baima San Allah yayi ruwana ba Nima kaina na dauke na ciro wayata ina danna wa shiru bashida niyar magana nasake kallonsa ido muka hada ya tsareni da lumsasun idanunsa gabana ne ya fadi da Sauri na dauke kaina adakile yayi magana can k’asa cikin amon muryasa mai dadi”ke baki iya gaisuwaba ne? ” ina yini nace na kauda kaina bai amsaba yace”inaso nasan dalilinki na rainamun hankali d’azu wani zai kamamiki hannu an dakatar dashi sai gashi yanzu da wani k’azami Wanda ko baruwan Flowers gidana bazai munba shima zai dafaki haka halinki yake?? ” kaina na dago na kallesa raina abace ” ni wai meye damuwarka dani ne duk kabi ka takuramun yau so kuke ku kasheni ko ina ba dadi ni wlh ba halina bane ba” karya kikeyi wlh idan baki kiyayeni bako Ham wai nine kikacewa kinason wani ko ya fada cikin fushi ya kamo fuskata ransa abace ba tambayarki nakeyi ba kikamun shiru ai Dama nace miki wlh sai na horaki ya fada yana tallabo kaina ya janye niqab Dina mai hade da hijab kadan ya fito da bakina waje Dama hancina waje yake ya had’e face d’inmu wanin irin kamshi kefitowa daga bakinsa idanu na zaro cikin rawar murya bakina na rawa na bude zanyi magana naji tattausan lips d’insa saman nawa ya kama lips d’ina wani irin dumi naji da wani fitunana kamshi kafin na tantance naji ya gantsaramun cizo a labbana sama da k’asa da karfi yake cici zawa hawaye kawai suke sulalowa daga idanuna na azaba saida yaji shashekar kukana ta fito sosai ya saki fuskata cikin fada yace “gobe ki sake mun tsiwa awaya kice kinason wani sosai na tsorata da yanayinsa ga labbana suna mun radadi kai nagama da gwiwa ina rusar kuka ga inajin Sonsa yau sosai cikin zuciyata, banza yayi da ita amma kukan ya damesa ya rasa sukuni Dole ya kalleta har yanzu cikin fushi yake
“my zahara kiyimun shiru banason kukan ki haka kawai kimun laifi Dan na hukuntaki kuma kiyi kuka wlh idan kika sake cinye bakin nakima zanyi naga bakin rashin kunya, kinci sa’a ba haka naso tsawaba amma wancan din natafe sai kinzama tawa idan kinmun ba daidai ba zan miki hukunci dashi ban dagoba cikin shashekar kuka nace” Dama ai basona kakeba shiyasa kake wulakantani harda cizona gashi bakina sai zogi yakemun yau ni ban tashi asa’aba Dama yanzu gwamna yagama cimun fuska shida matarsa wai nice mai muni zan tsorata masa matarsa idan taga fuskata sadakarma da tabani banaso itace naba mai ruwa amma kakece min wai zan gama hannuna ni daga yau baruwana da My Haidar Dama baisan daniba nice nake haukana kuma Aminullah kaima baruwana da kai Dama naji ina sonkane saboda my Haidar da yana yinku iri daya da maganarku amma nafasa tunda kamun mugunta na fada cike da shagwaba ina kuka tausayinta yaji sosai da tsantsar kaunarta na ratsa jininsa da tsokarsa tattausan hannunsa yasa ya dagota da fuskarta ya janye niqab din ya kalli kyakyawar fuskata ya shafo hawayen fuskarta ya kai bakinsa ya shanye ” wow my beautiful kiss yama yatsar hannusa ya doramun Akan lips Dina da ya kumburo ” wayyo zafi ” Sorry Fatimana yi hakuri bari kukan bazan Kara cizonki ba ai duk laifinki ne ya fada ashagwab’e ” to ai Kane kacijeni ko “to yi hakuri nine na tabaki ko cikin kukan shagwaba nace” ku biyune kuka tabani na fada ina Kara sautin kukan hawayen na ya rika daukewa yana shanyewa amma naki dainawa kaina ya kwantar kafadarsa yana shafa kaina cikin wata irin murya yace” my haskena yi hakuri banason kukan yada yayi maganar yasa na tsayar da kukan ina sabke ajiyar zuciya inajin sonsa da kaunarsa na ratsani Dan babu abinda yarabasu da gwamnana sai Abu kadan “ai gwara da suka cimiki fuska haka kawai kinaso kima mace kwacan miji da rana tsaka wai ma me yafini dashine da kika nace masa kina nufin kudin da matarsa ta baki bakiso kinba wani ashagwab’e nace” eh banaso mezanyi dasu shima kishinsa yamun yawa na hakura wai Nice zan firgita matarsa da muni Hamm murmushi yayi aboye” wai kina nufin kin daina sonsa?? ” yo danme zaimun wulakanci saboda matarsa kaima mun
 bata tunda ka cijeni abaki na fada ina kukan shagwaba ashagwab’e yace” wayyo zan mutu my Fatimana bata sona ni sai kinsoni munyi aure mun zuba love agidanmu kin rika goyona ya fada cikin shashekar kukan wasa da Sauri ta dago ta kalleshi bakinta na rawa ta kamo fuskarsa tana hawaye ” Aminullah yi hakuri ina Sonka tunda gwamna baya sona kaiko kana sona kuma kuna yanayi dashi wannan kadai ya isa yasa naso ka Dan Allah kabar kuka ina Sonka amma zan rika cemaka My Haidar na fada ashagwab’e ina shafa fuskarsa Wanda babu alamar yayi wani kuka saima idanunsa farare tas da suke haske wani irin murmushi yakeyi afakaice ya dago ya na kallonta ya hade face ashagwab’e yace” ni banason haidar bari nasake wani kukan da Sauri tace” to yi hakuri bari nace My man da Sauri yace” banaso shagwab’ewa nayi” to my chocolatyna ko?? gira ya daga min yana murmushin gefen baki a ashagwab’e nace “Allah ni idan bakaso shikenan ” gud my life thanks inaso ina sonki har na koma ga Allah ya fada ashagwab’e ” ni my chocolatyna sai karikamun shagwaba inajin wani irin sonka kabari Allah zanyi kuka fah?? ” please karkiyi kuka my Fatimana amma bazaki Kara komawa amsar sadakaba ko?? ” ni ba ruwana da My Haidar matarsa kadai yakeso ni baya sona tunda kuna kama shikenan suje can su cinye junansuma ba ruwana wlh kaima idan kasan matarka irin ta Haidar ce wlh gayamun tun wuri Nacireka araina Allah bazan auri iri kuba saboda ina da kishi bari gani na yar yarinya dani
Cike da mamaki ya kalleta ” da gaske kike my life?? ” eh wlh yo ni bazan yada inason mijina arikamun iko dashiba Allah bazan aureka in dai kanada mata hankalinsa ba karamin tashi yayi ba amma ya dake ya shiga lallabata da kalamai masu tsada amma fur ta bijire” Ok naji zamuyi maganar my Teemah nasan maganinki wlh bazan yada kisamun hawan jiniba zanyi wa abun tufkar hanci tun wuri gwara daga baya asan abunyi motar tayi tsaye kofar gidansu Teemah ashagwab’e tace”my chocolatyna kalleni nama hoto ko mun rabu zai debemun kewa hannusa ya Dora kan bakina ” wlh zan baki mamaki My life ayanzu kinyi karya ki bujiromun sokike kisani a masifa Oya matso muyi pic ya janyota kusansa amma ko kusa bai rabeta ba Dan baya fatan hakan ya amshi wayar hannuta ido cikin ido suke kallon junansu cikin wani irin shauki na so kala uku ya duka yanaso ya rumgumota amma hakan ba ra’ayinsa bane saboda gudun raini wayar ya bata” Oya shiga gida ki turomun pic din ina Jiranki zamuyi waya wlh idan baki dagaba duk ranar da kika shigo hannuna zaki raina kanki baki na tura na kwakwab’e fuska idanuna sun kawo kwalla” wlh idan kikamun kuka zan baki mamaki ni banyi kuka ba kinason tarwatsamun zuciyata sai kece zakiyi,hadiye kukan nayi saida na bude motar na fito na leko ” wlh my chocolatyna da gaske nakeyi na fasa Sonka haushin abunda Haidar yamun har yanzu araina jinka nakeyi kamar shine tunda kuna kama baki ya ciza ya matso da Sauri zai damkeni na zuba da gudu kai ya kada yana bin motar da yagani kofar gidansu teemah da kallo, har direba yaja motar sukabar gun tsaf ya saita nutsuwarsa ya dawo Aminullah sak yace” Boos inason kusama yarinyarna idanu da kyau daga yau karku Kara bari taganku har bayan na kammala daideta ruwan da takeson bullomun dashi? “Ok Oga angama waya ya dauka yakira wata number bugo biyu aka daga” Alhaji Saif girman na baka ya Niger? Ok gud akwai bincike da nakeso kamun daga gobe zuwa jibi ka bani bayani zan turoma da komai da nake baukatar sani arubuce ina jira ok thanks bye ya tsinke kiran ya dafe kansa hankalinsa duk baya jikinsa yana jin tsoron wani Abu karya biyo baya da zai tarwatsa masa mafarin cikinsa motar ta karya kwana har ta bacewa ganina Teemah na shigowa gida suka hada idanu ya harde Hannayensa akirjinsa tayi turis tana nunashi da yatsa ” mekazo yi……. ✍🏻
Yar ilu ce🤪
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Written By*
 Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣0⃣*
……”lfy dai ko naga kadawo?? ta fada bakinta na rawa murmushi ya sakar mata “lafiya kanwata wlh naji bazan iya hakura bane na dawo amma meye hadinki da wannan mutumin da yanemi hallakani?” yaya Haseem kayi hakuri sasune akeyi cikin fada fada yace “to wlh basu isaba kowama Dan iskan kansane akanme za’a takuraki haka kawai idanu nazuba masa ina kallon ikon Allah warsu mai gadima dariya abun ya bashi kamar ba d’azu ya gama maruwaba” yanzu dai kayi hakuri zamuyi magana anutse zan shiga cikin kar anty tamun fada” OK kije din zamuyi magana gobe insha Allah ki gaida Aunty? ” to taji na fada ina tafiya kai ya girgiza ya fito kenan zai shiga mota yaga boos gindin motarsa atsaye fuskarsa ya hade ya iso gun motar ” kasan abin da nakeso da kai wlh ka fita daga harakar wannan yarinyar cikin fada ya dago “bazan fitaba ubanwaye ya turoku wani gigitaccen Mari boos ya zabgawa Haseem har ukku a take hancinsa da bakinsa jini ya rika zuba ya shakesa ya Nuna masa bindiga “wlh mutarkar baka rabu da ita ba zan maka illa duk Oga ya hana duka amma kai taurin kaine dakai ya fada yana sakinsa ya fadi k’asa wanwar ya nufi mota yashiga sukabar gun haseem ya Mike yana Allah ya isa,
Ya shiga motarsa yabar gun amma ya tsorata da lamarin tun kafin yarinya tasan yana sonta har ya fara shan dukan maza akanta Dole zai gagauta janyota jikinsa ta soshi idan yaso komai amasa ma, Teemah tana shiga parlo bedroom ta wuce malika bata parlo wayarta ta buye ta ajiye Alqura’anin ta shiga bedroom ta dauro Alwalla Ana kiran magarib ta fito tayi sallah koda ta gama bata tashi tana Adu’ar Allah ya cire mata son Haidar da Aminullah Dan taji haushin abinda gwamna ya mata, saida aka kira sallahr isha tayi ta Mike wayarta ta dauko taga bai kiraba zama nayi bakin gado ina kallon pic din da mukayi da Aminullah tsantsar kamarsu da Aliyu nake gani jinayi sonsa ya lumku azuciyata sai dai kishi ya rinjayeni yanzu nafi son Mara mata Malika ce ta kirani da Sauri na Mike na boye wayar na fito “Fatima me kike kinki fitowa? “Aunty sallah nayi kusanta na zauna muna hira “yayanki yana gaisheki? ” Aunty kiramun shi Dan Allah “yanzu bazamu samesa ba bari na kira miki Abba “yauwa yayata nagode bugo biyu Abba ya daga suka gaisa ta bani”Abbana wlh kamar nazo nakeji” auta yi hakuri zakizo kiyi karatu dai yanzu ai kunkusa samun hutu “Abba ina iyayye?? ” gata Auta amshi ku gaisa kinsa nawalu da lado sun adabeni wlh har tausayi suke bani goro da kifi baya gabce mana kukan shagwaba nasama Abba sai daket yashawo kaina nayi shiru yaba iyayye wayar “iyayye ina yini? ” Auta ya karatu kursiya kawarki ta haihu fah? ” wayyo dadi iyayye ku gaidamun ita wlh da dahali da nazo sunah
“ta haifi danta namiji saura ke duk abin ana zaginmu wai kin girma ba aure har shekara16 bakida aure” dan Allah iyayye kibarsu basuda aiki a birni wlh ko yayeni ba’ayiba daga nono bare wani aure “mudai dan Allah ki tsayar da miji ayi magana yar uwarki ma tanada17 year aka mata aure kema kiyi qoqari kafin lokacin” iyayye mubar maganar bani Abbana wayar ta bashi mukaci GABA da hiramu munjima sosai kafin muyi slm na kashe wayar “Anty Malika kursu gawata ta haihu na girma nayi d’a wlh dukan wasa ta kaimun “wlh ke ko Allah shirya ai ba yau kikeda yaraba ko shuriem “eh momy Aunty mune diyanki Rasheed yace “Aunty kinfi sona ko “wlh dukanku ina sonku Malika tace”ku tashi muje muci abunci kan dining mukaje yau tuwan tukakiyar shikafane da danyar miyar kub’ewa taji busasan kifi mukaci mukayi dam muka dawo parlo muna hira sai karfe goma nama Aunty saida safe mai sunan iyayye sai kuka take na dauketa saida Malika ta samata nono abaki tayi shiru, ina zuwa wanka nayi nasaka kayan bacci na Haye gado wayata aikuwa kira ya shigo kin dauka nayi dan nayi Alkawalin bazan sake daukan kiransaba bare muryasa ta tadamun hankali naji duk bana ra’ayinsu da ya dameni da kira pic dinsa na kalla na sumbata na kashe wayar baki daya na boyeta da alkawalin bazan sake kunnawaba nayi Adu’ar bacci na shige cikin bargo har bacci yayi gaba dani,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Zaune yake a hamshakin parlonsu Wanda ya gaji da haduwa saman wata lumtsumemiyar kujera farin gilashi manne kan kyakyawar fara fuskarsa Laptop ne gabansa amma baya dannawa yaransa yake kallo yana murmushi yada suka cika parlon da hayaniya game sukeyi na mota jikin makekiyar TV yar bango Rauda ta kafa musu rigima sai sun bata alhalin ba iyawa tayiba bintu da ke gefe tanashan kayan itatuwa ta kallesa “My Man juyowa yayi ya daga mata gira” ka musu magana suje su kwanta ni inada bukatar mijina murmushi ya saki dama yasan yau tunda ta kafa masa rigima da botsanci na banza sex takeso daket ya bude baki ya kira Rauda”baby Rauda zo kiji da gudu tayi wajan babanta ta fada kansa”dady gani rumgumeta yayi yamata kiss “baby kin fiye rigima kibarsu suyi wasansu bintu ta matso gunsa”my man ni ina magana fah dariya Rauda tayi ta sabka daga jikin dadynta ta koma gun bintu ta rumgumeta”umma me akayi “bakeba ce kika gudu gun dady ta fada tana rumgumeta tana Sosa mata kanta nan take ta fara lumshe idanu dan dama bacci takeji mik’ewa tayi da ita daket tayi bedroom d’insu Aliyu ya kalli yaran “Asif Oya kuje ku kwanta dare yayi kashe TV sukayi sukazo gun dadynsu kowa yamasa kiss shima yamusu atare suka gama baki”good night dady”night yaran dady dariya sukayi suka nufi d’akunansu Laptop ya shiga dannawa har bintu ta fito cikin shirin kwanciya bata masa magana ba ta wuce bedroom d’insa laptop din ya kashe ya Mike ya kwashe wayoyinsa ya kashesu baki dayansu ya nufi bedroom d’insa har ta kwanta kai ya girgiza dan ya gano fushi takeyi bathroom ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan bacci agagauce dan so yake ajima yayi sallahr nafila
gadon ya hauro ya kashe wutar d’akin “my bintu fushin me kike ya fada yana janyota jikinsa shiru bata amsa maganaba rikirkitata ya fara yana gaya mata kalamai masu dadi da sanyaya zuciya sai gata ta fara dariya ta sakar masa jiki har suka lula duniyar ma’aurata jiya iyau shi yayi kidansa da rawarsa bakinta nishi yayi yayi tamasa kuka amma tace shi kullum sai yayi ta fadin Abu daya ita bazatayi kuka ba wasu irin abubu ya fara mata amma wlh sam batayiba shima fasa zantutukan yayi yaci GABA da kashe arana yau kin sabka yayi saida ya gamsu dan yanajin dadinta sosai matsalarta daya bata masa yada yakeso shiyasa baya mata kuka sai sambatu sai karfe biyu ya sarara mata da kansa ya kaita yamata wanka yasamata kayan bacci ya koma shima yayi wanka tsarki jallabiya yasaka fara tas sai zuba uban kamshi yakeyi ya tayar da sallah bintu tun tana kallonsa har tayi bacci dan yau ya bata kashi dayawa bai gama sallaba sai karfe uku ya zauna yayi Adu’a yajima sosai daga karshe ya sako Noor d’insa yayi Adu’a Allah ya tabbatar da alheri dan yanzu ashirye yake da tunkarata sonta yake sosai yanajin itad’in rabin rayuwarsa ce duk baya hada kowa da bintunsa mik’ewa yayi ya cire jallabiyar yasa kayan bacci ya haura gado ya rumgume bintunsa ya jamusu blanket Adu’a dauke bakinsa har bacci ya saceshi Noor d’insa tazo masa da zazakar muryata tana masa irin hirarakin da ta saba masa na yaci GABA da adalci akan mulki makiya bazasu taba nasaraba akansa yanzuma akwai Wanda yakeson ganin karshensa amma bazai iyaba yaci gaba da Addu’a da temakon marasa karfi da yawaita sadaka, hakane yayi ta mafarkin Noor d’insa Asubah ta gari,
***********************************
*Agurguje bayan wata biyu*
Zuwa wannan lokacin abubuwa dayawa sun faru cikin ko harda kauracewa Aminullah da teemah tayi kamar wasa tun ranar har yau bata kunna wayaba duk wata hanya da Aminullah yabi akamo masa teema abin ya gagara hankalinsa ya tashi sosai maganar zuwa sadaka ma ta fasa tace har abdan kuma duk da haka yana manne aranta taurin zuciyace irin tata haseem aboye yake bibiyar teemah da yake tana yawan zuwa gidansu gun maheeda har suka shaku soyayya sokeyi sama sama tace wlh gwara ta aureshi da ta tsaya jiran gwamna da baisan da itaba kuma ko yasaniba wlh bata sonsa tunda kishi gareta Aminullah tafasa duk da tana sonsa gwara ta rabu dasu ta auri saurayi shiyasa suke soyayyarsu da haseem tunda bashida makosa yanzu haka bata Nigeria tana Niger kauyen garin sarki saboda hutun makaranta da suka samu saide abin mamaki gidansu Teemah wlh idan ka gansa bazakace akauyen garin sarki yakeba saboda wani k’ank’areran gidane aka musu dan madedeci akauyen Wanda yazama abin kwatance yanzu sunan kauyen yakoma *sabon garin sarki* sai kace haka Teemah abin yana bata mamaki tayi tayi da Abbanta ya fada mata Wanda ya musu yace ta tambayi mu’azzam shiyasa tayi shiru zatonsa ko shine ya Gina musu bintu matar gwamna ta haihu yarta mace jiyane akayi sunah na kece raini agarin Gombe manya mata da mazajensu masu fada aji da wasu masu hannusa da shuni da masu tsaki da ruwa asiyasa sun hallacin gun sunan yarinya taci sunan fatima bintu zahra wlh tsayawa fadin irin shagalin da akayi bata lokacine gidan TV da radio ko ina zancan akeyi matar gwamna Aliyu Muhammad Damba ta haihu Wanda kuma ajiyarne abin mamaki aka daurawa Noor d’insa Aure bashida labari duk bazaice ga Noor dinba,
Da misalin karfe biyar watsime ce ita da kursiya kawarta ta fito daga gidan kursiyar suna tafe suna hira tana goye da baby mai sunan iyayye diyar Malika tun shekaran jiya sukazo ita da mu’azzam “kursiya kinsan me yake bani mamaki? ” sai kin fada wai jiya duk inda nayi sai acemun Amarya wai an dauramun aure to kinsan jiya ban wuni agida ina gidan haja nanu ta hanani zuwa ko ina acan na kwana sai yau da safe nazo gida wlh abun mamaki yake bani na tambayi iyayye sai tamun dariya tana rumgumeni Aunty malika ma haka yaya mu’azzam wai sai yace ai ni yanzu na zama babbar mace”Dariya kursiya tayi “nima baban jafar haka yace wai an daura miki aure da wani hamshakin mutum mai kyau kamar aljani wai ajirgin sama sukazo damagaram aka kawosu amota dagacan wai harda bindiga da wasu irin mutane amma nima ban yadaba tunda lokacin yace bayanan ya shiga binni dayazo yaji labari tsaki naja “wlh kibarni da shegun kauye Dole na koma watsime mai Allo naci uwar mutane dama sunzo sun samana idanu wai watsime masu gidan birni dariya kursiya tayi akofar gidansu ya’u na zaune da tiredasa tako yi gunsa aransa yace jarababiya yanzu haka sai ta warci halewa ahakane ta samu hamshakin mutum ya aureta aikuwa warta tayi taba kursiya ta kara wartowa banza yamata dan jiya gun durin auranta ya samu Alheri suna dab da shiga gida Nawalu ya taresu yana kuka “wlh watutu Allah ya isa da yaudarata da kikayi hine kika auri dan binni kika barni ” Aradu nawalu banson raini ubanwaye yacema nayi aure ni akuyace za’a aura dani ba shawara ya’u yace “Wallahi an d’aura miki aure jiya ai kedin mai sa’ace aduniya auran balarabe kaiko nawalu wlh karaba kanka akwai masu masa tsaron matarsa nide baruwana halewar ta zubar ta kurma ihu bata saurari nawalu ba da yake famar kuka tayi cikin gida da gudu kursiya tabi bayanta arikice Nawalu ma ya shige cikin gidan yana dadin wlh dama nasan watutu bazaki ci Amanata ba…… ✍🏻
Yar ilu ce🤪
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*Written By*
 Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣1⃣*
…..iyayye na kitchen tana girki taji kukan Autarta da gudu ta kado”,to wane dan kinibibin ne? ya tabo matar manya da gudu ta fadi gaban iyayye tana kuka dagota tayi ta rumgume”Auta me ya faru yi hakuri kimun bayani Malika ta ISO ta sinto yarta tana dariya “iyayye kinsan kwanan zancan ai cikin kuka teemah tace “iyayye auren Dole kukamun dawa kuka d’aura inada fa saurayina Haseem yayan kwata daide lokacin nawalu suka shigo shida kursu iyayye ta jata suka zauna nawalu ya duka “iyayye ina yini dan Allah tunda bataso ku warware adaura dani don Allah teemah dai sai rusar kuka take ta rumgume iyayye Malika tacema nawalu”dan Allah Nawalu tashi ka tafi mik’ewa yayi yana fatar majina ya fice kursiya tazo kusan teemah tana bata hakuri “Watsime dan Allah yi hakuri ai bazasu aura dake ga Wanda bai daceba Malika tace “kibarta zata hakuri sautin kukan nakara Mu’azzam ne ya shigo da sallama Teemah ta mike
Ta nufi gunsa tana kuka”yaya mu’azzam kasan da Wanda akamun auran Dole naje na rokesa awarware? ” zo ki zauna muyi magana kanwata kiyiwa iyayanki biyayya sun ga dacewar hakan ne shiyasa kusan sa na zauna saman tabarma “da farko dai kiyi hakuri nine jagoran wannan aure watanin biyu da suka wuce wata number ta kirani ina Lagos mutumin ya nemi yana sonki da aurene kuma bai buyemun duk alakar da take tsaniku ba ya tabatarmun da kema kina sonsa har waya ya baki amma shine ya hana kinuna yace ya turo nan Niger anyi bincike an tabatar kinada tarbiya kuma shima ya gwadaki ta hanyoyi dayawa ya yaba da tarbiyarki saidai kunsamu matsala kince bazaki auresa ba kin daina sonsa tunda yanada mata ya rokeni nazo yanaso ya aureki amma sai matarsa ta haihu ranar sunan yanaso a d’aura muku aure idan yaso daga baya idan kin kammala karatunki na secondary school sai ayi biki agidansa zaki cigaba da karatu bayan munyi hakane nazo Gombe muka tafi niger dashi ya nemi su bashi auranki da farko Abba yaki saida nayi masa bayani kema kina sonsa kuma gwamna da kike mafarkin samu tun kina yarinya shine ubangiji ya baki lokacin da kekuma kika cire tsammani Abba jin abinda Auta ke mafarkin samune yace ya bashi ganin irin gidan da sukene yasa aka rubjeshi
akayi ginin zamani kuma sunyaba da dattakunsa sunsan zai rikeki Amana akayi tambaya da kudin gaisuwa da komai akajiye magana idan matarsa ta haihu za’a d’aura aure to Allah ya sabketa lfy ai muma saboda auranne mukazo shekaran jiya bayan anyi fatihar suna shida tawagarsa da magabatansa sukazo aka d’aura aure suka koma Teemah kin zama Matar Aliyu Muhammad gwamna sauran amshoshin tambaya da basajar da yamiki da yada ya fara sonki sun gunsa shine zai baki amsa ihu na kwarara na fara birgima ina kuka”wlh iyayye bana sonsa Allah sai yasakeni yo mai zanyi da mai mata matar ma masifafiya kuma baya ganin kowa da gashi sai ita “iyayye tazo ta dago “Auta yi hakuri bakisonsa “eh wlh banaso Kenan dama shine ya canza fuska yace Aminullah nide banaso araba auran idan anaso na zauna lfy yo ni mezanyi da mijin wata dariya su Malika suke mata ta kara sautin kukanta ta saki iyayye ta nufi d’aki da gudu akwatinta ta bude ta ciro wayarta ta kunna dan akwai chaji tana kunnuwa ta danna number Aminullah bugo biyu ya daga cikin kuka tace”Aminullah wlh kazo ka warware auran da kasa aka kulla dan bana so haka kawai kasa amun auran dole ina yarinya karama to ni banaso wlh sai anrabu wlh banaso k’asa yayi da murya”oh oh oh Sorry my Noor zakiso ni kafin mu hadune son da kikemun zai dawo kara sautin kukan nayi” dama basaja kamun ko? ” yes My Noor My Fatimana my yar babyna yi hakuri bari kuka bana kusa bare na shanye sweet hawayenki kara ihun kukan nayi”wlh sai mun rabu Ashe duk wayo kamun kaine gwamna idan nace kuna kama komai naku iri daya sai ka shareni to idan bakima kuka hada nide banason mijin wata sai an rabu na fada ina kuka”Ok My Noor please bari kukan yanzu duk son da kika mun kin daina my zahara to idan kinaso mu rabu yi shiru maza share hawayenki ki fadamun ya za’ayi mu rabu da sauri na goge fuskata ina turo baki kirana yayi cikin wata irin murya mai dadi can k’asan makoshi “My Noor yar babyna me kikeso ayi? “nifa wlh babu wata kashe murya da zatasa na sadako nide ka turomun takarda ta inada saurayi Haseem shi zan aura wata uwar tsawa ya dakamun baice komaiba ya tsinke Kiran fashewa nayi da kuka ” to kaje kayi fushin wlh sai an rabu bana sonka waje ta fito tana kuka iyayye tace” gaskiya ni koke koke nan ya isheni ina dalili Auta zo yi hakuri zamuyi wani Abu bakiso jikinta na fada “eh banaso Mu’azzam dariya ya bushe da ita ya Mike kursu ma dariya takeyi” iyayye ce kursu ta tafi gidanta wlh babuni babu ke yanzu na gano masu kaunata wayyo iyayye Abba yamun auran Dole bakinta ta rufe mata ta jata dama da hijabi a jikinta teemah ma da hijabi “Malika mutafi gidan haja Nanu wlh banason kukan bari na kaita can dariya malika tayi suka fice daga gidan
Nigeria kasancewar jiya akayi sunah yau Aliyu gwamna bai fita ba dan har yanzu yan tayasa murna Karin aure da yayi da murna haihuwa da aka masa yau baije ko inaba hutawa yake abinda ya jima bai samuba hutu kwance yake saman wata lumtsumemiyar kujera arumfar shan iska sojoji sai shawagi sokeyi idanunsa a lumshe ya dafe kansa ransa abace saboda abinda Noor dinsa ta fada masa da tijara da bintu take masa tun jiya ta hanashi sukuni ga kuke kuke da takeyi da fitsara iri iri wayoyinsa sai ringing suke idanu ya bude yanajan tsaki screen d’in wayar ya kalla ganin sunan hajiyarsa na yawo saman screen d’in yasa ya dauka ya kara akunne “Hajiyarmu barka da yamma?” Aliyu Haidara ya gajiyar taron jama’a”Alhmdllh nakiraku wayar akashe gobe inaso nazo Damba”Aliyu kabi Fatima ahankali kaine kamata laifi Karin aure tana jego tace kana ta mata abubuwa marasa dadi idanu ya zaro”to Hajiyarmu zan gyara ina Aminullah ne yau banji ya kirani ba “ai kuwa bayajin dadi ga matarsa ma tun safe takenan Aliyu sai anjima lokacin sallah ya kusa”to zan kiraku insha Allah murmushi tayi ta tsinke Kiran mik’ewa yayi boos ya kwashe wayoyin yana biye dashi har kofar parlo ya amshi wayoyin ya tora Gilles d’in kofar parlon ya shiga da sallama da gudu yaran suka taresa rumgumesu yayi yamusu kiss daya bayan daya ya kallesu” maza aje ayi shirin yin sallah da gudu suka nufi dakunansu har Rauda gunta ya nufo tana zaune tana shayar da zahara tanaga ya nufo gunta ta Mike da yarta ta nufi bedroom dinta kai ya girgiza ya bita zata rufo kofa yayi Saurin shiga ya matseta abango ya amshe babyn ya shimfide ta k’asa ta zube ta rushe da kuka dukowa yayi ya ciccibeta ya rumgume ya nufi kujera da ita dukansa ta fara akirji”wlh Aliyu ka sabkeni meye hadinka dani zaka tabamun jiki ka saukeni da sauri ya cafke bakinta ya fara tsotsa cizo ta gantsara masa tun karfi kin sakin bakin yayi haka ya zauna da ita saman kujera zare bakinsa yayi ya zuba mata lumsassun idanunsa”amshi kiyi ta cizona indai zaki huce my bintuna turesa ta fara yi tana kuka”Aliyu ka sakeni na barma d’akin matseta yayi”anki ba’aza a sake kiba gumun matata zanji wani banza kallo tamasa tace “hummm wlh Aliyu.. sanin ba Alheri zata fadaba da sauri ya kame bakinta wani irin cizo ta gantsara masa tana dukan kirjinsa kallonta kawai yake bakinta yasaki dan ba karamun cizonsa takeba matseta yayi gam ya tallabo kanta ya k’ura mata lumsassun idanunsa yaga har tayi rama tausayi tabashi dan yasan kishin bintunsa akansa ba sauki fuskarta ya shafa can k’asan makoshi yayi magana sai magana take gayamasa”my bintu kinutsu muyi magana banaso na bata miki rai kinfa sanni yanzu ma saboda nine nayi miki laifi me na miki kika hadani da Hajiya? wani banzan kallo ta watsa
masa………✍🏻
kuyi manage ina busy
Ladingo yar ilu🤪
Rahma ummu Fareesa ce😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
 ____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*DEDICATED TO*
*SAMIRA BINT* *ABDALLAH*
Lalle kedin ta dabance bazan manta dakeba har abadan Wlh kinsamu matsayi mai girman gaske azuciyata Nagode kwarai Allah yabar zumunci🤝🏻
*🌹Masoya masoya masoyan matar gwamna hakika naji dadin yada kuke Nuna tsakwaron tsantsar kaunarku ga Matar gwamna wlh bansan da kalmar da zan gode muku ba bantaba tunanin zata samu higa hakaba😂Dan haka korafunku ya karbu na a dinga muku posting kullum insha Allah akullum zaku samu matar gwamna sai dai sabar da lahadi ne kawai bazan mukuba Dan haka sai😂😂😂 abarmun waya ta huta Aradu nima na huta gaisuwa maitarin yawa gabaki dayan masoyan Matar Gwamna I love u Mazga Mazga Ana kyawun tare🤝🏻🤝🏻🌹*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣2⃣*
…..”eh Aliyu na fada karya nama duk abunda na fada meye bakamunba ta fada tana hararanshi hawaye ya wanke mata fuska rumgumeta yayi gam”to naji kin fada my bintuna iyayan kishi nide hakuri nake badawa uwargidana abar kaunata ya fada yanason had’e bakinsu kanta ta kauda cikin kuka tace”Aliyu kabarni na samu nutsuwa don Allah ka sakeni na koma parlo yaranka na jiranka ku tafi masallaci ni yanzu na gane iyakata agidanan ba’a sona kansa ya dafe”oh my god my bintuna yi hakuri bari kuka nasan nayi laifi a sasauta mun my wife waye bayason bintuna yanzu yaga rundunar sojoji da yan sanda akansa cikin kuka tace” wlh Aliyu kaine saidai kaje adaureka murmushi yai ya manna mata kiss “wlh inason bintuna ai da wanine ya fada yau sai an daureshi agarin gombe tashi maza muje parlo kar yaranmu suga damuwar abar sona bintotona yar fara kyakyawa buge buge ta fara tana kuka”Aliyu ka sakeni banaso kana tab’ani ni zakawa dadin baki “my bintuna bari musha Dan minti kadan ko nasamun kan matata turesa ta fara Dole ya fara mata wani irin salonsa yana birkita mata lisafi sai gata tayi shiru tayi lamo jikinsa tana sabke ajiyar zuciya sai turo baki takeyi murmushi ya sakar mata ya manna mata kiss saman idanunta ya Mike da ita har bathroom ya wanko mata fuskarta sai hararasa take ta fito daga bathroom d’in ta tsaya daga kofa ta rike k’ugunta”Allah Aliyu yau bazan barka ka rumtsaba kuma ko wacece ta auremun mijina ta shirya zaman huquba wlh bazan barta taji dadi ba shiru yayi ya gama Alwalla ya fito ya kamo hannuta bakin gado ya tsaya ya saki hannuta ya dauki baby zahara ya manna mata kiss agoshi”my fatimana kiba momy hakuri hararasa tayi tabar masa d’akin ta fito parlo ta zauna Asif yace”umma ina dady “Asif gani babyn ya dora mata acinyarta k’asa yayi da murya”my bintuna i love you natafi masallaci kibar cewa Aliyu My Man yafi dadi ya fada yana daga mata gira kallon yaran tayi taga hankalinsu baya kanta kai ta kauda ta fara shayar da yarta. muneerat tazo ta zauna”umma ki
miki Reno “ok bari ta koshi kai Aliyu ya girgiza ya kama hannu mukutar da Asif suka fice Rauda tazo ta Haye cinyar bintu tana mata kiss”umma babymu mai kyau ko? ” eh maza kuje kuyi Alwalla muneerat tace”muyi ai Kiran sallah Muke jira zarema yarinyar nono tayi”Muneerat riketa na shiga bathroom na fito wlh karki kuskura kiba Rauda yata cikin farin cikin ta amsheta yarinya masha Allah kyakyawa sak Aliyu ta fito mik’ewa tayi ta nufi bedroom wayarta ta zage daga chaji ta kira wata number bugo daya aka daga”kuka ta saki wlh Mummy ni bazan iya hada mijina da wataba jinake zuciyata kamar ta fashe inada mugun kishi akan My Man DINA wlh jinake kamar nayi hauka yazanyi dan Allah ko na barmasa gidansa kai wlh bazan barma wata dusa mijinaba daga can naji ance”haba Fatima bintu kiyi hakuri bawa baya wuce kaddarasa ni yanzu amatsayina na mahaifiyarki zanso na fito da yar cikina agidan mijinta Wanda ta fi so uban ‘ya’yanta don Allah ki ajiye hankalinki ki tuna Aliyu na kaunarki baiyi aure dan ya tozarta kiba kiyi hakuri zan turo mamu har gida ta kara nusar dake wlh karki kuskura ki biya kawayan gwamnatoci kice zaki bijirewa mijinki kimarki ta zube abanza ina fada miki gaskiyane amatsayi na na mahaifiyarki kiyi hakuri fatima cikin kuka tace”mummy naji insha Allah sallama sukayi ta tsinke Kiran ta fada saman gado tana wani irin kuka” ya zan iya ganin My Man dina da wata mace Allah ya soni macan yar kauyece marar aji mara wayewa kucaka wai asirine suka masa komai wlh zataci kutumar ubanta la’ada waje da kafarta zatabar
gidan Aliyu Muhammad Damba Kowa,naka wlh yarinya kinyi kadan banda ke ko mai ajima wayaya wacce Takeda ilimi Aliyuna yafi karfinta bare kucaka mace irinki wlh kinyi kuskuran hada miji dani zaki gane bakida wayo tayama zai hada jiki da yar kauye yanzu haka garin yawan kyautarsa da Alherinsane ya temakesu iyayanta suka bashi sadaka shiko ya amsa wlh yar kauye kucaka Dole kibarmun mijina duk cikin kuka take magana kanta ta daga sama ta shiga tunanin rayuwarsu ta farko shin wai
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
 jama’a wai waye Aliyu gwamna *Asalinsu* Aliyu Muhammad Abdullahi Damba kowa,naka shine cikeken sunansa Aliyu haifafan garin Damba ne nan kauyan Gombe fulanin asaline gaba da baya Muhammad Abdullahi Damba cikake bafulatanine d’a daya tilo gun Abdullah Damba Allah yayi musu Arzikin shanu da gonakai na uban mamaki kasancewar shidayane gun iyayansa ya samu gata da ilimi Addini da boko har yakai munzalin aure aka masa aure da yar kawunsa jallo hurairatu yarinya mai hankali da nutsuwa bayan aura’su da shekara daya ya gama karatunsa ya samu aikinsa acikin garin Gombe duk ba wani albashi bane mai tsoka kasancewar shidayane gun iyayansa sukace bazai zauna gidan hayaba suka sayar da shanu suka saya masa gida mai dakuna biyu da kitchen da makewaya atsakar gida suka tare da matarsa haka rayuwa taci GABA bayan shekara daya da tare warsu ta haifi yarta mace taci sunan kakarta mahaifiyar Muhammad wato Halimatu suna kula da ita sosai duk suna nuna mata faranci bayan haihuwarta da shekaru hudu hurairatu ta sake haihuwar d’a namiji zankadede fari kyakyawa ajin farko Wanda tun ranar da aka haifesa Allah ke musu budi ta ko ina yaron kawai farin jini makota ta ko ina shigowa kallonsa sukeyi yan Damba ko kusan kwansu da kwarkwatarsu
suna Gombe gidan kasa amshesu yayi kunsa dai fulani🤭ranar sunah yaro yaci sunan Aliyu Haidar, bayan haihuwarsa so biyu tana haihuwa yaran barai shiyasa yake zuba sangartasa son ransa saida ya shekara bakwai aka haifo k’anansa Aminullahi kamarsu daya da Aliyu saide shi bakine Alyu ko farine tas bayanan sai Habibullah sai yan mata biyu tagwaye saffah da marwa Aliyu tun yana yaro miskiline na gaske sam fara’a bata damesa ba sabanin k’annesa masu fara’a tundaga haihuwar yan biyu haihuwa ta tsayama hurairatu badan takaiba Allah dai ya tsayar da ita idan ka kalleta bazaka tab’a cewa ita ta haifi yara shidaba alokacin haka sukaci gaba da renon yaransu guda shida maza uku mata uku sun taso cikin gata da tarbiya dukansu makarantar gwamnati sukeyi amma kaf cikinsu Aliyu ya fisu ilimi nesa ba kusaba tudaga Primary har zuwa secondary school Aliyu yake zuwa na farko bai tab’a yin k’asaba yana samun kyau tutuka sosai harda kudade Wanda iyayan suke Tarawa basa kashewa gashi da farin jini gun malamai da dalibai baya shiga harakar kowa amma idan anyi ba daidai ba zaiyi magana tun lokacin kyawunsa ya baiyana duk bayada sakin fuska ga miskilanci idan zaka shekara kana masa magana to fah bazai kallekaba sai yayi ra’ayi sabanin k’annesa Aminu akwai fara’a habibu ma haka yan matan ma ba ruwansu to dama dama halimatu itama akwai miskilanci haka tafiya ta tafi Aliyu ya shiga Federal University kashere Wanda tsabar miskilancin sa duk da haka duk Wanda yayi ba daide ba koda malamaine a lokacin zai fadama gaskiya kuma baya barin acuci mutum shine kaf marantar aka dasa masa suna shugaba yan mata ko suka Adabi rayuwarsa Wanda shiko basa gabansa dan yanada burin karatu mai zurrfi saide Abu daya Aliyu bashida rowa duk rabin alherin da zai samu zai
rabasane ga mutane da basuda shi duk suma bawai arzikin bane dasu sosai Dan ya hana kakanninsa yawan sayar da dabobinsu suna kawo musu dukiya saboda ba laifi hanya ta budewa Muhammad har ya sauya gida mai dakuna biyar shida yaransa suna watayawa amma Aliyu Allah yayisa da tausayi duk abin da zai samu rabas dashi yakeyi ga Wanda bashida cinyau bare na gobe Aliyu kyakywane ajin farko fari dogo mai manyan idanuwa ingarma namiji kirasa ta karfaface kirjinshi abode yake ko ina gashine jikinsa yanada dogon hanci idanunsa alumshe suke idan ya kalleka zakayi zaton bacci yakeji bai fiye maganaba gashi miskinin gaske abokinsa daya har yau da yazama wani bai canzaba wato Jamil shi yaci maganin zama dashi ahaka har ya gama karatunsa dan ya karanci fannin business ne dan kasuwanci na burgeshi bayason aikin gwamnati yafison kasuwanci bayan kammala karatunsa da wata hudune ranar kamar amafarki aka kawo masa takarda wai zai tafi k’asar waje karo ilimi akan business gwamnatice ta biya masa yaunin karatunsa saboda kwazonsa har ya tubure baza shiba dan Aliyu juyayen mutumne ra’ayinsa yake bayabin ra’ayin wani sai Muhammad yasa baki da kakansa Abdullahi ya yada ya tafi Amerika
 Wanda zuwan NASA ba karamun anfana yayi da hakanba kara goge aharakar business da sani rayuwa acanne suka hadu da bintu wacce daga temakonta da yayine awani gidan cin abunci saura kadan anyi mata fade Allah ya kawoshi ai kuwa tasha fada agunsa da takaicin iyayan da suke turo ‘ya’yansu kasashan waje karatu babu wani matakan tsaro suna yawo inda sukaga dama daket da yarakata gidansu ta shawo kansa ta masa bayanin abun da ya faru tace wani baturene ya takura mata itako tayima iyayanta alkawali zata rike mutumcinta baza saurari kowaba saide ko dan k’asarta idan ta hadu da mutumin kirki kamarsa ta nunasa tsaki yaja ya tafiyasa bayansa tabi Ashe kusan juna suke to shine mafarin haduwarsu da binta tundaga ranar bintu ta nacema Aliyu sam baya kulata amma da yake wayayace gata shagwab’ab’a da abin dariya haka zata iskoshi gidansa ranar da babu karatu tayi ta masa shirme ta dora masa girki tun baya kulata yana mata korar kare har ya fara kulata saboda dariya da take sasa duk ba yayi agabanta sai ta fita haka shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu bintu tana mugun son Aliyu da kishinsa shima ya kamu da sonta duk bai gaya mataba kasa daurewa tayi ta fada masa bai musaba suka kulla soyayya mai karfi bintu akwai mugun kishi har makarantar su Aliyu take zuwa aboyé taga ko mata sunyi masa magana tasha danbe da mata tasha fasa kan ‘ya’yan turawa da bakar fata saida Aliyu yamata Jan ido ta sasauta dan tasan halinsa bashida dadi zai watsar da lamarinta shiyasa take takawa asannu ahaka har tagama karatunta tace bazata tafiba sai Aliyu ya gama saida
 yamata Jan ido yace wlh zai fasa auranta tukun ta koma Nigeria, kullum cikin waya suke har Allah yayi shima ya dawo Fatima bintu y’ace ga Alhaji Taheer mai kudi su ukune gun iyayansu mussadeeq ne babba sai nana barirah wacce suke cewa mamu sai bintu auta sun taso cikin gata da kulawa sun samu tarbiya sunyi karatun Addini da Na boko mahaifinsu Allah yamasa arziki yanada dukiya sosai bintu shagwababiyace ga fadan masifa da b’aci kuma sunfi sonta shiyasa takeda rashin kunya bayan ta gama secondary school tace bazata cigaba da karatu a Nigeria ba Dole mahaifinta ya kaita America har Allah ya hadasu da, Aliyu bintu farace tas yar duma duma mai matsagaicin tsayi kyakyawace tanada hanci da idanu matsagaita bata fiye gashiba amma ba laifi tsabtarta da yawan kwaliyarta ya kara mata kyau akwaita da jiji dakai saide bata cika wullakanta talakaba fagen iya tafiya da daukan dressing ba’a cewa komai akwai ta aji tanada farin jinin samari sauranyita daya Jafar sun so juna tafiyata karatu ne sanadin rabuwarsu bayansa bata so kowaba sai haduwarsu da Aliyu
bayan dawowar Aliyu da wata ukku iyayansa suka tsaya masa ya fara business da kadan kadan Allah yake ma kudin albarka har kwangilar gidaje yake soyayyasu da bintu tayi karfi sosai bintu ta Rigada ta karanci Aliyu Dan haka idan yana mata miskilancinsa ko ya basar da ita bata damuwa tunda abin ajininsane millions biyu ta basa kan ya amsa suyi aure yace Allah ya kiyaye masa daga karshema ya mata kwakwaran kashedi karta kuskura ta sake masa haka lokacin ya tura iyayansa neman auranta aka samusu ranar aure kuma lukacin business din Aliyu ya fara bunkasa mahaifin bintu ya basu kankarenan gida indan anyi biki su zauna Aliyu ya kiya yace idan tana sonsa to ta zauna inda yake meye ya nema ya rasa aduniya da har za’a bashi gudun muwa daga gidan mace bayaso
 Dole tacewa babanta abarshi yayarsu Aliyu tayi aure harda yaranta yan biyuma duk an musu aure yanzu dagashi sai Aminu da Habib agidan Aliyun suke dan madedecin gidane mai masifar kyau da tsari d’kuna ukune kowane da toilet aciki kitchen dinsu mai kyau nan su Aminullah suke da zama suna karatunsu, haka akayi auren Aliyu da bintu ansha biki Dan auransa yayi armashi sosai daga kowane bangare su Jamil babban aboki ya taka rawar gani sosai abikin dama shi yayi aurensa tun aliyu na waje karatu komai cikin dattaku Aliyu yayi rawar gani ba laifi bintu Tasha akwatuna da kaya tamkar wani hamshaki kowa ya yabawa Aliyu shugaba sunan da yabishi tun makaranta anan gidansa ta tare suna son juna kamar zasuci junansu yaji dadin samunta cikakiyar budurwa Wanda yasha raki ba kadan ba haka yayi ta lallabata har ta warke sukaci gaba da budirinsu matsalarta daya bata masa yada yakeso agado saide shi yamata da ya takura tasa masa kuka Dole zai hakura yana lallashinta dan yana mugun sonta mutika saide idan miskilancinsa ya motsa Dole itace mai bibiyarsa da lallashi shiko tunaninsa duk haka mata suke agado saide abokinsa Jamil yaji yana zuga matarsa to dayake shi ba ma’abucin magana bane bai tsaya ya fuskanci inda zancan ya dosaba haka sukaci GABA da rayuwa har ta samu ciki murna ba’a maganar har cikinta ya isa haihuwa ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ba bata lokaci suka tafi hospital ta haifo Danta namiji kyakyawa mai kama da Abdullahi sak ranar naga murna gun dangi uwa dana uba kuma lokacin Aliyu lamura sun bude masa ta ko ina……….. ✍🏻
Sai next page zamu gama labarinsun da irin rayuwar da sukayi kafin Aliyu yazama gwamna🌹
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
 ____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣3⃣*
……ranar sunah yaro yaci sunan Muhammad mahaifin Aliyu suna kiransa da Asif haka sukaci GABA da rayuwa cikin so da kaunar juna Asifa har yayi wayo Aliyu zuwa yanzu Allah ya bunkasa dukiyarsa sosai bayan Shakaru uku bintu ta sake haihuwa wani d’a namiji mai sunan Taheer mahaifin bintu suke cemasa mukhtar Aliyu dan murna kamar yayi hauka dan Allah yayi masa mugun son yara baiki duk shekara ta haihuba itace dai take kiyawa mahaifin bintu yaji dadin karar da Aliyu yamasa yaron yanashan gata lokacin aka ida Gina kamfanin Aliyu mai Suna *AB Sauki Kamfani* Wanda ake sarafa kayan zamani iri iri Wanda ya samu daukaka sosai ga business d’in motoci yanayi da harakar kwangilar gidaje Aliyu yayi suna agarin Gombe saboda komai NASA mai saukine ga yawan kyauta da sadaka da sauransu haihuwar bintu ta uku ce wato haihuwar muneerat ya tamfatsa gida a unguwar NEW GRA wlh fadin ginin gidan b’ata kokacine dan wlh babu abinda baisaba najin dadin duniya tamkar gidan shugan k’asa dan yanason matarsa da yaransa suji dadin rayuwa sosai haka iyayansa ma ya tamfatsa musu gida lokacin Aminullah yayi aure shida habibullah haka sukaci GABA da rayuwa soyayyarsa da bintu ko babu abinda ya rage duk da bata masa yada yakeso agado wani sa’inma idan ba tasoba bata yada suyi sex amma idanbtaso ta kafa masa fitina iri iri idan yan miskilancin na kansa ko kallo bata ishesaba bayan tare warsu da shekara daya yan siyasa sukayi masa taron dangi da karfi suka sakasa siyasa sunce irinsu talakawa keso shiko ya kiya sun jima suna bin kansa kusan shekaru hudu kafin ya yarda ya shiga siyasar amma yace bazaiyi mulkiba da wayo da wayo suke jansa jikinsu har yasaki jiki bayan haihuwar Rauda ne dai ya shiga siyasar ruwa tsumdum yada yaga talakawa nashan wuya sai ayimusu alkawali idan sunyi zabe za’a musu Abu kaza amma shiru kakeji malam yaci shirwa haka tafiya tayi tafi yawan kyautatawa jama’a da yakeyine Jama’ar gari kuwa sukace atsayar da Aliyu takara gwamna suna so tun bayaso har yaji sha’awar abun a ransa amma zaben farko makiyansa manyan yan siyasa da basuson cigaban talakawa suka shiga suka fita sukayi murdiya akace baiciba shi ko ajikinsa talakawan garine da masu goyan bayansa cikin manya aka fara tashin hankali saida ya shiga gidan radio da TV yayi magana ya basu hakuri ya nuna masu lokacine baiba idan lokacin yazo to fah babu Wanda ya isa ya hana dan haka suyi hakuri daganan ne komai ya lafa shima yaji babu dadi amma saboda Noor d’insa da take karfafa masa gwiwa cewar yayi hakuri lokacinsa na tafe amma hakan bazata faruba sai ta kusantosa yanzu lokaci baiyiba tukun na mulkinsa to haka akaci GABA da rayuwa Noor na k’asan zuciyarsa yanaso yaga ranar wannan da tace sai ta baiyana k’asarsa zaici mulki yana mamakin wanna Al’amari duk yanajin ba mutum bace amma yana sonta bai taba manceta cikin Addu’ar saba haka ko akaci gaba da rayuwa har Allah ya kawo lokacin da Aliyu ya hau kujera gwamna cike da nasarori masu yawa talakawa najin dadin mulkinsa sosai har zuwa wannan lokaci da bintunsa ta haifo masa Fatima bintu Zahra ya kuma aure Noor d’insa rabin ransa yar babynasa Wanda ita dashi suke mugun son junansu tun basu gaba junansu labarin yanda ya ganeta da yada ya saka fuskar Aminullah to nima jira nakeyi sai yaba Noor d’insa labari sai na dauko muku rahoto, labarin rayuwarsu ya k’are sai kuma kafce yanzu bintu da Teemah
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bintu tana nan kwance har akayi sallahr isha zahara take kuka muneerat ta kawo mata ita amsarta tayi suka fito parlo ta zauna tana shayar da ita har Aliyu suka dawo daga masallaci ko kallonsa bata yiba shima ko yan miskilancin sun motsa masa baice mata k’alaba sai dai idan sun gama ido ya daga mata gira kiransa akayi ya daga waya hayaniyar yaransa tasa ya Mike ya nufi wani Hadaddan parlo ya zauna yana waya da mutanansa yan siyasa bintu ta cika tayi fam jinta ko dawa yake waya ya keb’e oho sai tsaki take ja Dan dai tasan halinsa Idan ya kebe yana waya ba’a kawo masa raini har ta mike taje ta masa tijara ta fasa ta daukin kodirin yau bazata barshi ya rumtsaba oh bintu arage kishi fah😆
*Niger* tun bayan fitarsu iyayye watsime kuka take kirtawa ahanya daket iyayye tasha kanta tayi shiru har suka isa gidan haja Nanu da sallama suka shigo haja Nanu na gindin murhu ta amsa”Aisha ya dai Fatima bintu meyene ake kuka sakin iyayye tayi ta rugu gun haja Nanu ta rumgumeta tana kuka”haja Nanuta da ranki kika bari su Abba sukamun auran Dole”asha Fati yi hakuri ta raketa ta kalli iyayye”Aisha jeki gida barni da kawata ajiye hankalinki zata bar kukan murmushi iyayye tayi ta juya ta koma gida haja Nanu taja hannu watsime suka koma saman tabarma har yanzu kuka takeyi harda shasheka”haba Fatima kiyi hakuri bari kukan goge fuskarki kiji wani labari kuma na fada miki yada za’ayi yanzu dai kina son gwamna mijinki ko bakiso kuka nasaki mai sauti”Nanu kubar cewa mijina ni banaso” to naji amma ai sonake na koya miki wayo irin namu na manya yanzu yaushe zaku gama Hutu? “da saura fah amma naji aunty tace tare zamu koma wai akwai gyaran da za’amun na meye? nanu tace” ai shine zan baki shawara gyarane za’a miki Wanda idan gwamna ya ganki zai rabu dake amma da sharadi sai kin daina koke koke kin fasa cewa bakya sonsa ai da kansa zai rabu dake inji ni nake miki wannan zance farin ciki ya kama Teemah ta rumgume Nanu tana dariya”yau kakar kwarai naji dadi ni Dan ina sonsa haka kawai sai na zauna da kishiya matarsa masifafiya tab ai wlh gwarama arabu yaushe “Nima dai shi nagani gwara kiyi shiru da kansane zai nemeki karki k’ara kuka ki ajiye hankalinki Ana gama gyaraki zai rabu dake, haka haja Nanu tayi tama Teemah wayo itako sakara tahau ta zauna sai fadi take gwarama suyi sutafi gombe amata gyaran ko ya rabu da ita tana gidan haja nanu har bayan isha, zaune suke suna cin abunci ita da haja Nanu sai labari take bata na dariya teemah sai kyakyatar dariya takeyi”wayyo cikina Dan Allah haja nanuta kibarni haka ai da nazo da wayata da na dauki hiranan na turawa haseem yasha dariya”ke wlh ahir dinki kirabani da hauka kibari har Aliyu ya ganki tukun “to nabari ai ni haushinsa nakeji waifa Nanuta kinsan wani abun haushi? ” ina fa nasani idan ba kin fadamun ba watarana naje amsar sadaka ya wani rike hannuta suna yawo cikin jama’a Dan tsabar iyayi wai nice ma zan firgitata saboda tsabar munina “dan Allah ki sharesu ai kawai kiyi shiru abunki inace mun gama magana kince baki sonsa amma kinmun hiranan tafi so dari to ina ruwanki dasu tunda baki so “baki ta zumburo gaba “eh banaso shikenan ta tashi ta wanko hannuta ta dawo ta zauna” wai kin koshine? “nakoshi Nanu idasa bani labarin Abbane ya shigo da sallama Teemah ta Mike da gudu ta riko hannusa
“Abbana yau ban gankaba shine kamun auran Dole ko? ” Haba Auta waneni yi hakuri dariya haja Nanu tayi hannuta ya kamo suka zauna ya gaishe da mahaifiyar tasa”haja Ashe kinata famar lallashi “to yazamuyi ai mun kashe magana kuka ya k’are ko? ” eh ya kare Abba Nanu ta koyamun wayo da an gyarani da kansa zai rabu dani “Auta wannan wani irin haukane Nanuce tayi masa yaren fulatanci ta yada bazata ganeba dayake ta iya amma ba sosaiba yace “oh hakane Auta yanzu dai kinbar kuka ko? ” nabari Abba hira sukayi sosai sun jima saida dare yayi sosai Abba zai tafi ta bishi gida nanu tayi tayi su kwana ta kiya Dole tabarta suka tafi, lokacin da sukazo su Mu’azzam da su iyayye har sun gaji da hira kowa ya kwanta Mu’azzam da yaransa suna tare Malika da yarta nagun iyayye suna daga kwance suna hira da malika d’akin ta fado sai kumbure kumbure take Malika ta kalleta wayarta ta dauko ta kunna gun iyayye ta nufa ta kwanta ta rumgumeta”Auta an dawo ai na zata acan zaki kwana” iyayye kalli ta Nuna mata wayarta”ai munada labarinta mijin kine ya siya miki kuka ta sakama iyayye tayi wurgi da wayar Malika ta bushe da dariya iyayye ta rumgumeta”yi hakuri Auta ai na mantane Ashe bakyaso ko? Kai ta daga” iyayye kice Malika tabarmun dariya “ke Malika barimata dariya “to Allah ya bata hakuri iyayyen ma dariyar take kumshewa mik’ewa teemah tayi taje tayi wanka tayi shirin kwanciya ta dauki wayarta ta kwanta jikin iyayye tana danna wayar taga har yanzu bai kiraba tsaki taja”yo karka kirama yo da wa zai dauka suna jinta suka mata shiru tunda idan sunyi dariya kuka zatayi pic d’in da sukayi tare ta zubama idanu tana kallo wani mugun kyau sukayi sai yanzu ta tabtar da Haidar ne fuskace kawai ya saka kuma fuskarma me kamarsane sak ahaka tana kallon pic har bacci ya fara fizgarta ta rumgume wayar tayi bacci iyayye ta janye wayar ta ajiyeta gefe tana dariya “yarinya sai fitina Wanda ba asone za’arika kallon hotonsa har ayi bacci lokacin Malika ma tayi bacci iyayyen ce ta jima kafin tayi bacci, Asubah ta gari,
****************
*Bayan kwana biyar*
Yau su teemah zasu koma gombe saboda abubuwan da za’a fara koya mata da tsumin da za’a fara mata da gyaran jiki agidansu Mu’azzam da sauran abubuwa dai dan shiga gidan gwamnati Dole sai mace ta amsa sunan mace Dole su gyarata kafin aure yada shima zaisan mace mai daraja ya aura bangaran teemah ansamu an mata wayo cewar da an gyrata Aliyu zai rabu da ita tahau kai ta zauna ta Saki ranta kullum sai Aliyu ya kirata duk da yanada haushinta haduwarsu yake jira ya gyara mata zama amma idan ya kira bata dauka ko so daya shi mutumne da baison raini shiyasa kwana biyu ya daina kiranta kuma takama masifa harda su kuka tayi ta kallon wayar tana cewa matarsa ce ta hanashi kiranta su iyayye idanu suke zuba mata suna kallon ikon Allah abun yana basu mamaki tace bata sonsa amma bur ta ishesu da rigima tana fushi Haidar yakita saboda matarsa, shiko Aliyu abubuwan sun masa yawa ga rigimar bintunsa danma ta Dan rage kwana biyu yayarta mamu tayi ta mata nasiya to da Dan sauki haushinsa daya baya jin murya Noor d’insa dan yace bazai k’ara kiran taba har ta dawo Gombe yasan sai tunaninsa ya adabeta ta rasa sukuni ita bintu da tafara rigima yake zautata da salonsa sai masifar ta ragu kafin dare nace lalai Aliyu namijin duniyane, tun jiya ya tafi Abuja wani baban tarono akeyi gidan shugaban k’asa Wanda za’a kwashe tsawon kwana biyar anayi Wanda ya hada manya manyan shuwagabani na k’asa k’asa shine da ya kira bintu ta adabeshi wai yanzu haka gun amaryasa ya tafi kauye shiru ya mata Dan shima miskilancin na kansa ko kallo bata isheshiba,ya tsinke Kiran Dan yadauki niyar su dukansu biyun da babbar da k’aramar zai sharesu ya zuba musu idanu yaga iya gudunsu yasan halin kowace yasan irin son da kowace take masa da yada shima yake son kowace cikinsu da salon son kowace daban daban azuciyarsa Dole zai basar dasu ko ya huta kwana biyu bayason hayaniya da rigima to sun sakashi a gaba Dan haka yayi watsi da lamarunsu yana harakokin gabansa,
tun safe teemah take yawon ban kwana gidan yan uwa da makwabta misalin karfe biyu na rana su Malika da yaranta cikin shiri suka fito har anshigar da kayansu mota kursiya kawar watsime harda kuka tunda tazo sama da wata guda kullum tare suke teemah tana gidanta ko ita tana gidansu teemar rumgumeta teemar tayi itama tana kuka saida iyayye ta janyeta mu’azzam dariya suka bashi sai darawa yake “haba Watsime kiyi hakuri ai zaki dawo itace babbar kawa kuma da ita za’a rakaki”iyayye kima yaya magana Abba yace”yi hakuri auta wasane yake miki kursu kema yi hakuri ai bazata jimaba zata dawo karki damu kukan ta daina sukayi sallama cikin walwala tana karama teema godiya dan kaya ta bata tafi kala biyar Wanda bata taba tunanin zatasa irinsuba haja Nanu taja teemah gefe guda ta kara mata wayo harda su dariya take ta rumgumeta”wlh shiyasa nake sonki kakata dariya akayi ta musu nawalu nacan gefe aboye sai matsar kwalla yake yana kallon teemah amma bai isoba lado ko kin zuwa yayi tunda mai gari yayi musu kwakwaran kashedi akan wlh za’a dauresu idan suna ma matar manya magana shiyasa ya hakura dan akwaishi tsoron iko mota suka shiga cike da begen kauyansu da iyayyensu shuriem harda kuka abarshi gun iyayye sai daket mu’azzam ya lallabashi yayi shiru yace gobe zai maidoshi teemah na rike da hannusa iyayye saida mu’azzam ya tashi mota ta saki tana kwalla suka rarasheta ita da Abba saida tayi dariya dukayi sallama Malika na musu dariya”yo ni bazaku lallasheniba zungurata mu’azzam yayi yama motar key sai hannu ake daga musu har suyi nisa “my darling harda zun gura ai Dole nayi kishi sai ita daya ake riritawa” nifa wlh baruwana daku kukasa akamun auran Dole shiru suka mata gudun kar suyi dariya tayi kuka gudu mu’azzam yake sosai har yafita akauyen garin sarki watsime sai raraba idanu ake ana kallon hanya ana matsar kwalla……✍🏻
💃🏻Yar ilu ce🤪
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
 ____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣4⃣*
……tunda Teemah suka
Kama hanyar gombe Mu’azzam bai tsayaba idan kaga ya tsaya sallah za suyi su Teemah yauma ansha madara mai sanyi har angaji amma yau idanunta kyam bata rumtsaba har suka shigo garin gombe yau da wuri suka shigo shadaya na dare saura suka shogo garin gombe suna zuwa kowa ya nemi makwancinsa saboda gajiya da bacci teemah tana shiga bedroom d’inta wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta cire zanin gado ta canza wani Dan akwaita kynkymi saman bed ta fada ta shige cikin blanket wayarta ta duba tana zumburo baki ta k’urama pic d’in Aliyu idanu”Allah babu ruwana dakai My haidar ni sai mun rabu shine Dan bana daukan kiranka sai kafasa kirana ai hakkina ne ka kirani ko bana daukaba yi tayi kamar zata kirasa ta fasa ta ajiye wayar tana karanto Addu’o’in bacci bata wani jimaba bacci ya dauketa, bangaran Malika da mu’azzam bayan sun kwantar da yaransu suka shiga bathroom sukayi wanka tare suka fito sukayi shirin bacci suka zube saman bed saida suka garji junansu San ransu yo akwana biyu ba’a haduba sama da sati sai can tsakiyar dare suka sararama juna akaje akayo wanka aka bingire sai barci Asubah, ta gari,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
zaune Bintu take a Katafareran parlonsu Wanda ya gaji da haduwa yasha kayan alatu yaranta duka sunyi bacci sai zahara itako kukan dare gareta bata barin bintu bacci k’urawa wayar hannuta idanu tayi Aliyu tun jiya yaki kiranta tarasa dalili tsaye ta Mike ta nufi makekiyar TV dake manne jikin bango ta kashe kai komo ta fara tsakiyar katoton parlon nasu”wallahi dolene My Man ya rabu da kucakar yarinyar nan tun Kafin ta shigo gidan tanason hadani da mijina Wanda Muke da shekaru goma sha shida da aure yarinyar da aka Haifa ashekara aurena Dan ubanta shine zata rabani da mijina to daga yau na ajiye fitina dashi zan sasauta masa keko yar kauye kucaka zaki raina kanki wlh zahara ce ta fasa kuka gunta ta isa ta zauna ta dauketa tana shayar da ita kiran numbersa tayi bata shiga duk numbobinsa da ta kira basa shiga hankalinta ya Kara tashi amma tunawa haka yakeyi duk dare ajiyar azuciya ta sabke tana zubar da hawaye mik’ewa tayi rumgume da yarta ta nufi bedroom kwanciya tayi ta rumgume yarta itako sai harbe harbe take batada almun bacci bintu hawaye shafe shafe a fuskarta har bacci ya dauketa asuba ta gari
**********
bayan sati daya yau su Teemah suka cika sati daya da dawowa daga Niger Mu’azzam ya komabakin aiki sai su Teemah suke rayuwarsu da el uwata da yaranta teemah na zuwa islamiyya hutunsu na karshe haryanzu bai kareba Aliyu har yayi kwanakinsa biyar a Abuja ya dawo gombe har yau babu wacce yakira cikinsu harakokin gabansa yake yayi watsi da lamuransu har ya dawo teemah tin bata damuwa abin ya fara damunta harda su kuka take daga baya tayi watsi saboda batada lokaci saboda gyaran da ake mata da fara koya mata salon tafiya da magana da iya kwalliya da Jan aji kullum idan an kaita gidansu mu’azzam sai yamma take dawowo gida. tayi shirin tafiya islamiyya abinda yasa ko ta maida hankalinta kan abinda hajiya mansura take koya mata saboda rigimar da take musu ita bata sonsa tunda mata gareshi sai sun rabu shine suka mata wayo idan ta tsaya ta koyi komai atsari tayi kyau da iya magana da shagwab’a Aliyu daga ya ganta zai rabu da ita amma ba yanzuba sai angama shiryata jin haka ta tsaya ta maida hankali Ana koya mata sai an gamasu su kwaliya da iya magana da kwarkwasa da iya tafiya da iya dress za’a fara na jiki da tsumi Dan yanzu yayi wuri, suko wa innan sunsa Dole mijinta zaiso ganin matarsa suyi zance, bangaran bintu kuwa tunda taga Aliyu yayi watsi da ita Dole take kiransa tana masa Mita baide kulata har yadawo zuwa lokacin tayi laushi Dan bata jure rashinsa amma da ya dawo saida tayi masa tas miskilancin na kansa bazan ya mata ta gaji ta fada samansa tana rusar kuka tausayi ta bashi Dole ya kulata ya lallasheta yanuna mata salonsa har taji sanyi aranta to shine fa yanzu ya Dan sami kan bintu ta Dan sabko amma ba dukaba idan kishin ya motsa gaba take sakashi da fitina teemah ko har yanzu baibi ta kantaba itama bata kirasaba yasa dai Ana kula masa shiga da fitarta saide baisan gyara ake kaita gidansu mu’azzam ba tunaninsa dan babu makarantane take zuwa yini shima tunda yazo bai samu isashan lokaci ba ya huta
da misalin karfe biyu da Rabi hajiyar mu’azzam zaune take a parlo tana sauraren redio BBC Teemah ce ta fito daga wani d’aki ita da wata mace ta hade cikin Riga da siket na shadda colour green dinki ya mata cif saide rigar ta matseta kirjinta yawa zasu fasa rigar su fito kuma hannu rigar karamine agaskia teemah tayi mugun yin kyau sosai fatarta sai uban sheki takeyi ga kwalliyar da mansurah ta koya mata yau bata gogetaba tayi mata kyau mutika haka suka fito sai wani shegen taku take tana baza uban kamshi gun innah ta nufa ta zauna”ah Fatima zara’u ya dai mansura tace”bamu gamaba ba fah wai kawartace babu lfy shine tace zata ganinta amatse take? ” asha Allah bata lfy cikin yanayin yada ake koya mata salon magana tace”innah na tafi ko?? ta fada tana langwabe kai alamun shagwaba dariya hajiya tayi “to ai rashin lfy ce jeki amma ki kira mijinki ki fada masa”ai na fada masa”to amma kuma wannan kaya Dan iya koyan daukan dress ne sun kamaki sosai danma bakida jiki “hajiya hijab zan saka fah har k’asa gaskiya gwara ayi A ida gyaran ko ya rabu dani nashakata innah na tafi” sai kin dawo ko nace sai gobe mik’ewa tayi”innah sai gobe dai zan jima mata ta fada tana dakar hijabinta mai niqab da hannu ta saka shima green color ne sai uban kamshe takeyi ta fito da hannuta waje tare suka fito da hajiya mansura wacce ta kware agyaran jiki da tsuma mace da iya kwalliya da tafiya koyan magana da shagwaba da kwanciyar aure da sauran abubuwa dai na mace tazama shalelen miji sunanta yayi fice kaf fadin Nigeria Dan aikinta akwai kwarewa, sosai saide tsada yanzu duka abubuwan da zata koyama teemah har zuwa aurenta saida aka tisa mata nera million guda kash duka kudin sadakin teemah ne suka bayar mu’azzam neko da wannan aiki, yace yanaso kanwarsa ta zama itama sha kallo gidan gwamna kudinta zai maida mata arone yayi yace shine ya dauki yaunin gyaran suna fitowa. direban hajiya mansura yazo daukarta”yauwa muje sai mu ajiyeki wacce unguwace?” Buba shago” to ai muma nan
 Muke ai bazamu bar matar manya ta shiga adaidaita ba baki teemah ta tab’e suka shiga motar direba yaja suka tafi, mansura na Kara mata fada tafa rike duk abunda take koya mata shiru tayi tana gyada kai kwatance ta rika ma direba har kofar gidansu Maheeda ta bude motar ta fito tayi mata godiya kofar get na nufa ina dab da shiga gidan naji tsayuwar motar Boos da Sauri na juyo na kallesa ya fito ya nufoni”hajiya oga na kira maza kizo tsayuwa na gyara cikin tsiwa nace” baza’a zoba anki ba’a zuwa na fada cikin sanyin murya Dan Sam mansura ta hanani daga murya wayar Aliyu ya kira bugo daya ya daga lokacin yana zaune akatafareran parlonsa na saukar baki dan yanzu yagama da jama’a acikin nutsuwa yayi magana yana lumlumshe idanu”Boos ya akayi?”Oga wlh matarka ce mukaga tazo gidansu kawarta idan gayan nan yake amma na tabbatar baya gari yana bauchi mik’ewa yayi zaune ransa ab’ace “maza kayi mata wayo ka kaimun ita gidana na NEW GRA wlh zata sani kitt ya kashe wayar ya kira wata number bugo daya aka daga “inason fita yanzu kitt ya kashe kiran ya Mike dama cikin shiri yake shadda ce green colour jikinsa yayi masifar kyau sai baza kamshi yake yana fitowa yayi Karo da bintu rukumkumeshi tayi tana kuka”wlh Aliyu ba idan zaka ai naji kana waya wai ashirya tafiya niger yanzu “bintu please kibarni na dawo karki karamun zafi wai meye nufinku akaina wlh duk zanyi maganinku sakeni kinji my zahara na kuka kije ki bata mama janyeta yayi ya kamo hannuta tana tirjewa ya nufi parlonta da ita kicin kicin yayi da fuska ya zaunar da ita “wlh my bintu zaku sani kiyi hakuri naje na dawo babu niger din da zani zahara ya dauko da kansa ya samata nono abaki bintu sai hararasa takeyi ganin babu fuska yasa tayi shiru kiss ya mata agoshi ya fice haka kawai taji bata yada da fitarsa ba ji take kamar tabi bayansa Dan dai tasan halinsa yau da takwana gidansu bangaran Boos kuwa jin Oga ya kashe wayarsa ya fara magana yada zataji “Oga tace bazata zoba wai wayone zaka mata Dan karabu da ita tace Dan Allah kayi hakuri ka rike mata igiyar aurenta tana Sonka bazata iya rabuwa dakaiba abarta ko? har NASA Kafa zan shiga gidan da Sauri na juyo “Kut kai ni yaushe na fadama haka nida nake neman maraba dashi to wlh sai nashiga motar muyita ta kare na nufi motar da Sauri dariya taba Boos gun motar ya ISO ya budemun na shiga motar
boos ya shiga driver yaja muka kama hanya dube dube na fara” Boos kake kowa ina Ogan naku ai baya motar? ” ranki shidade yana gidansa na hutawa mana ai can zamu kaiki daganan yayi shiru bai sake magana ba”wlh babu inda zanje ku saukeni babu Wanda ya kulani dole nayi shiru ina ciza bakina ina tuna yada zan masa wayo ya sakeni da irin abubuwan da hajiya mansura ta koyamun cikin sati guda dariya nayi ta farin ciki”ai My Haidar idan kasan wata ai bakasan wataba inama abubuwan da aka fara koyamun da yada nayi kwalliya yau wlh nasan da takardata zani gida dan na kara baka tsoro Allah har hijabina zan cire ina karai raya da salon shagwab’a Allah da kafarka zaka gudu kana cewa kumaidata gidan su na fasa auranta ni ko na fito cikin farin ciki na rabu da mijin masifafiya uwar yan jaraba can ku karata da ita yaushe ma gari cike da samari zan zauna da mai mata wayartace ta dauki ringing tana dubawa taga Maheeda picking tayi ta kara akunne”my mahee kiyi hakuri yanzu zanzo ina hanyar kaso aurenane cikin maganar rashin lfy tace”ke my teemah ban ganeba dan Allah kinmun bayani yada zan gane please kimun hausa daide lokacin motar ta tsaya kofar wani hamshakin get”ke bari na fito sai na baki labarin yada zakici dariyaki kyauta kitt na kashe wayar honr daya driver yayi aka wamgamemasa get suka Cinna hancin motar gidan idanu nazaro ganin irin wannan gida makekensa ko ina shifokine da adon flowers ga rumfunan shakatawa can gefe Swimming pool ne da rantsatsun kujeru wasu arnan motoci guda biyar nagani milk colour d’in ta tafi dani sojoji sai shawagi suke baki na ciza saboda keta dan nasan yanzu zan tsorata Ogansu ya fito da gudu nasan haushin haka zaisa ya sakeni Boos ya budemun mota fuskata a sake na fito gaba ya shiga ina binsa abaya taku nake cikin nutsuwa da Jan aji tamkar na shekara ina koyan tafiyar ta gaban Swimming pool muka wuce mukabi wata yar hanya sai gamu
akofar wani hadaddan parlour………✍🏻

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements