Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / MATAR MUHEED

MATAR MUHEED

MATAR MUHEED

bismillahi rahmani rahim

dukan yabo da godiya su tabbata ga Allah dayabani ikon kammala wanan littafin na *DAGA AURE NA* lpy kuskuren da keciki Allah yayafemin Allah kuma yabamu ladar inda.muka fadakar Allah yabani ikon kawo muku wanan sabon book din me suna *MATAR MUHEED* yanda nafara lpy Allah ubangiji yanunamin na kammala shi lpyy

wanan lbrn banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba idan kinga/kaga yayi kama da rayuwarka to kayi hkr wanan lbrn kirkirarrene ba gsky bane amma akoi inda zansa wanda shi anyishine true life

 

ban yarda wani ko wata yajuyaminn wanan labarin nawa ba batareda izinina ba idan kuwa akayi hk to wlh banyafe ba akiyayer

 

*wanan labarin yanadauke wata iriyar soyayya me ban sha,awa da kayatarwa ban tautsayii kuma yana dauke da darusa da dama zai illimantar ya kayatar yakuma nishadantar insha Allah*๐Ÿ˜

*love destiny and intresting story*

 

*1*

wata macece kyakyawaa wacce ita baza,a kirata dattijuwa ba kuma ba, yarinya bace kyakkyawa da kyakyawan jikinta wanda duk.da.tanacikin wahala hakan bai hanani.ganin.haka ba abunda nakasa ganewa shine ita bafulatanace ko kuwa shuwa

tana aduke abakin murhuu tana huraa wutar itaccen tana magana ita kadai

โ€œo wanan itace basaci sosai gashii wanan yarinyar takusa dawowa nasan tana dawowa abuncin nan bai nunaba rigima zai tashiiโ€

kafin takarasa rufe bakinta kawai sai ga.sallamar wata kyakyawar yarinyaa yarinyaa tashigoo wacce tsansan kyawunta saida da yafirgita ni kamar wata aljanna fara ce fesss fess masha Allah ga gashintaa har kan mazaunantaa nagama kare mata kallo yarinyar ta hadu sosai tana sanye da riga da wando na uniform dinta blue

tawuce dan dakinsuu ta ajiyee yar jakarta tafito dakin tana dire kafa

uhum uhum ummi wai har yanxu ba,a gama abuncin bane nifa yunwa nakeji

tace kinga zaki farawa mutane kukan kohh kibari ai gashi yayii kusa nunaa itacen ne ba kyau wlhh

bayan abuncin ya nuna ta kwashe abuncin suna ci wanan yarinyar tana mata fira tana bata lbrn makaranta

~suwaye wayan nan mutanen~

*farkon labarin*

 

inna wuro matar mallam illiya suna zaune ne awani kauyee na mallanjii suna da yaya mata biyu biyu asma,u itace babba sai kuma hasana mahaifinsuu malam illiya malamin muhammadiya ne yaranshii suntaso cikin addini kuma sunada illimi daidai gwargwado inda asma,u.tanada shekara 18 hasana tanada 16 hasana tasamu mijin aure wani mukutar ne dan.birnii soja aka turosuu kauyen domin yin wani aikii anan ne yahadu da hassana har suka.kulla soyayya batareda bata lokaci ba kuwa bayan sun gama aikin dayakaisu sun.koma gida sai yaturo manyan sa sukazo kuwa akayii mgn anan take suka biya komai na.auren akasa lokacii

 

abunka da kauye nan take jita jita yabiye garin cewa kanwa zatayi aure amma yayar ba mashin shinii mgn takai kunen su inna wuro sosai ransu yabacii asma,u ma harda kuka sukayi inna wuro tace to malam ni dai ko za,a fasa wanan auren ne mugani har zuwa wani lokaci

yace a a habade inna wuro karkibari zuciyankii ta yi na,am da wanan shirmen ma,na kinga inda ankasa bai halatta kanwa tayi aure ba yaya batayi ba acikin Qur,ani ko hadisi

ta girgiza kanta yace to kingani dan hk kibar mutane suta tsegumin susukasani insha Allah ba,abunda zai faru sai alkairii dan hk banason asake tada wanan mgnr kuma najanye bikin da akasa nan da sati 3 namaida nan da sati 1

sukace to Allah yanunamana

bayan kwana 5 kuwa biki ya tashii akasoma shagul mutane daga wayanda tsegumi kekawo su sai wayanda kezuwa domin ganin yanayin da asma,u keciki amma duk wanda yazo zaisha jinin jikinshi domin kuwa harma tafi amaryar cin ado bayan angama biki lpy aka kai amarya kano gidanta balaifii masha Allah komi yayi kyau kwana daya sukayi sukadawo sunyi kukan rabuwa da juna ita da asma,u

lokaci zuwa lokaci hasana tana ziyaraar suu da abun alkairii

bayan shekara biyu da auren hasana ta aihuu tahaifi da namiji tadawo gida wanka inda ranar suna yaro yaci sunan shii *MUHEDDEEN* sosai abun yabawa jama,ar kauyen mmki yanda akayi bacaka da dukiya domin zuwa lokacin Allah yasoma budawa muktar

asma,u ce kekula da yaron wankan sa kula dashi rainon shi da komi har sukagama wankan gida aka maidataa dakintaa

 

bayan shekaraa gomaa lokacin muheed shima shekarunsa goma yagirma yana zuwa skull arzikii yakara habaka agurin mahaufinshii domin anmai karin girma a gurin aiki

ana haka ne kuwa Allah yakawo wa Asma,u mijinn auren anan kuyen yake shi bafulatani ne kuma baitabayin aure ba yanada dukiyaa sosai ta arzikin gona da kuma shanuu Allah sarki wani jinkirin Alkairi ba,a wani bata lokaci ba akasha bikkn sosai inda bayan auren tatare adakin mijinta suna zamansu lpy da kaunar juna inda mijjnta malam ameenu yabiya musu hajji ita dashi aikuwa wanan abun bakaramin farin ciki yasa su innawuro ba sosai ba,awani bata lokaci ba kuwa suhau.muta sukaje birni suka shiga jirgi suka wuce

cikin farin ciki batareda wani damuwa ba suke.ibadanrsu har inda Allah ya maidasu lpyy suna birni bayan sun sauka ne asma,u tadinga kwarara amai hakan yatada hnkalin Ameenu yasa suka tari adaidaita suka wuce hospital gwajin farko yanuna masu asma,u tanada cikin wata ukuu da sati.biyu wato ma da cikin akaje aikin hajji dukansu cikin farinciki suka koma gida da wanan albishir

 

sosai ake murnar dawowansu ga kuma wanan albishir din acen.birni ma kuwa hasana tanacen dauke da cikinta itama kuma wataninsu daya dana asma,u lokacin da tazo yimasu barka da dawowa ne ma sukasan da hk

 

bayan wata bayan wata 6 kuwa kuwa haihu kowace tasamu ya macce asma,u ce tafara haihuwa bayan suna hasana itama ta aihu

akasawa yar asma,u sunan hasana amma ita haseena ake kiranta itakuwa yar hasana aka samata sunan kakarta wato mahaifiyar abbanta hauwa suna kiranta da (jiddah)

 

haka haseena tataso gidan cikin gata da soyayyar iyaye da kakani da yan uwa

bayan shekara biyu wata rana akayi ammbaliyar gulbi ruwa yaci kusan rabin mutanen yankin kuma daidai yankin gidansu innawuro ne inda kuwa harda su ruwan yaci yatafi da su sai gawarsu kawai

sosai hankalinn su asma,u ya tashi inda har sumaa ma saida tayi bayan.tafarka ayiwa.iyayenata sutura da ma sauran.mutanen garin da ruwan.yaci akayi.musu sallah aka kaisuu gidansu na gsky

hk.gaba dayan.mutanen.garin.suka tashi daga garin.suka karasa gaba da harin suka yada zango harda su asma,u ma da mijinta da yan.uwansa dasuke jin.kyashinta suka tsaneta domin.kuwa tun zuwanda sukayi yabiya masu hajja.ita dashi.dangin.shi.suka tsaneta gashi.kuma yan.ubanee shi.kadai mahaifiyar shi.ta haifa agidan tarasu duk.sauran yan uwanshi. babansu ne daya to wanan kiyayar da sukemai kuma sai gashi duk acikknsu shikafai ne yafita zakkah Allah yamai ni,ima yakeda wadata hkn yass sukaci burin sai sunga bayan shii

 

 

bayan wani lokaci hasana tazo ganin gidan amma abun mamaki sai tatarar gaba daya ruwa yamamaye gurin kamar ma wani bil,adama baitaba rayuwa agurin ba kawai sai taafadii alhaji muktar dayanzu anzama alhaji yadauketa sukasa amota sukadawo gida kullum cikin kuka take iyayenta da yayarta

alhaji yace kiyi hkr asma,u wanan.kadarace sun rasu yanxu.adu,arki kawai suke nema tace wlh ni inaji ajikina kamar yar uwara bata rasuu baa tana nan araye

adalilin wanan abunne yahadasamata hawan jinii.kuma me tsananii

bayan shekara biyar kwanaki sunja haseena tagirma sai rashin.ji.da tsiwaa.bataji.kokadan batada.tsoroo gata bawani karfi ba domin.kuwa itace zatayi.tsokana amma kuma da amfara dambe ido.zai rama.fata fata.farin.kolo.nan take dataji.wuya.zata rikida takoma.jaa๐Ÿ˜‚ amma.bazai.hana.takara jan.wani.rigimar.ba tsoronta yaran garin.sukeji.domin.tsiwarta.sukejin.tsoronta zakayi.zatan.akoi.karfi amma sai.an goga jiki.zakagane.bakomi๐Ÿ˜‚

haseena sai.girma take har ansakata a.makarantar boko dake nan kauyen da suka koma yanxu hk inda takeda hazaka sosai da kokarii domin kuwa duk akayii exam itace take fitowa da first position ganin.tanada.kokari.sosai.yasa malaman.skull din suka kaita JSS

wata ranar larba aranar ne yan uwan mahaifin.haseena.suka ajiye zasu.kasheshi

da yamma ne yana.gida.yana.hutawa suna zaune.suna.fira shida ummi.kamar.yanda.haseena.kekiranta itakuwa haseenah tana makarantar islamiya

kawai.sai.gasu.sun.shigo.maza su.biyune.dukan su sun.rufee fuskan.su.da.rawani suna.zuwa.suka.hau.dukanshi yana.ihuu. ummi.ma.ihumn.take.tana.basu.hakuri.tana.rikeau.amma.ina.karfin.su.badayaba yana.basu.hakuri.kafin.suka.tsaya yace.kuyi.hkr.dan.Allah.karku kasheni.kubar.ni da raina.idan.kudi.kukeso.wlh.zan.bakuu

suka kalli.juna.sukayi.murmushi.sukace idan.muka.kasheka.zamu.mallaki.dukiyar.ne.gaba.dayane.idan.kuma yanxu.muka.barka.ai.sammana.ne.zakayi.ba bamu.duka.ba.

yace.wallahil.azim.zanbaku.gaba.daya.

ummi.tace E E wlhh.zamu.bakuu gaba daya.dan.Alah.karku.kashe.mun.miji.kumaidamin.yata.marainiya.kumaidani.bazawara wlh.banida.kowa.sai shii

basu.saurareta ba haka.dayan.yadaga icce yabugawa.abban.haseena.a daidai wuyanshi.yayi.wata kara.tareda.kallamar shahada yace ga garinkuu.

ummi ganin tabbas ya mutu ta dora hannu.aka tasa.ihuu tadauko tabarwaa tayo kansuu ai kuwa gaba dayansu.suka gudu dayan ya gudu kafin yakarasa fita ummi tadamkoshi tabuga masa tabaryar akafa yadi rawan da yarufe fuskanshi yawarware
๐Ÿ‘€tagan hassan kanin abban Hatseenah nnnnee……

 

*idan nagan comment dinku dayawa hkn zai nunamin lbrn yakarbu agunku.sai inci gaba yawan comment yawan posting*

 

comment #
vote#
sharee#

 

*MATAR MANYA*๐Ÿ’‹
๐ŸŒน๐ŸŒน
*MATAR MUHEED*
๐ŸŒน๐ŸŒน

story~written
by *UMMY MATAR MANYA*

 

*2&3*

 

sosai ummi tazaroo ido cikinn mamaki tana kallon shii tace innalillahi mezan gani haka

yatureta tareda tashii yanadigisa yakarasa ficewa gidan itakuwa ummi zaune tayi tana kallon gawar abban hatseena takasa ma ko motssii

tana haka har haseenah tadawo tatar da su

sosai tarikeceee tasoma girga abbahn nata tana ihu tana jijigashi amma shiru baya motsi tajuyo kan ummi tana magana amma kamar tana.magana da dutse kawai sai tatashi tashiga gidan makocinsuu malam salau aminin abbanta takirashi sukazo tare tace yazo yagan halinda abbanta yake ciki bayan yazo ne shima cikin tashin hankali yaduba yagan raiyayi halinsa yafita yaje yakira liman akazo aka shiryashi aka mai sutura aka kaishi gidanshi

yan gaisuwa sunata shigowa sunayi gaisuwa ummi ko ma gaisuwan aka mata bata iya amsawa saidai tadaga kanta kawai

haseena kuwa tashaa kuka har ta wahalaa fuskan ta yayii jajaa sosaii kamar yaji har ya kumbura

bayan sadakar bakwai kowa yakama gabanshi mutuwar tasoma bin jiki

ga mutuwar iyayenta ga mutuwar mijin ta yanxu batada kowa sai yarta kawai da yar uwarta gashi kanwar tata sunyi nesa da juna

 

bayan wata hudu ummi tafita wanka haseenah kuwa tana nan tana zuwa makaranta

ummi abun yana nan yatsaya mata arai amma bata gayawa yar ta duk abunda yafaru ba kisan da akayiwa mijin ta ba
tun daga ranar bata koma ganin wayanan mutanen ba

bayan wata shida da rasuwar iyayenta kuwa sunada shekara daya da watanni da rasuwa

tana zaune a tsakiyan gida itakadai tana burkake nonon da batajima da ta tatsoshi ba

suka shigo su uku biyun wayanda sukazo ne suka kashe abbah dayan kuma yayansu ne

ummi ganin su kawai da tayi taji ranta yana baci bata cemasu komi ba

sukazo suka tsaya akanta sukace sunzo za,ayi rabon hado ne tace wanne rabon gado kuma uwarku ce tamutu ko ubanku dazakuzo kuna.mgnr wani rabon gadoo.mugaye azzalimai wlhhh karshen ku yana nsn zuwaa kuma wlh karshenkuu bazaiyii kyaubaa sai Allah ya kaskanta ku ya wulakantakuu takarasabda kuka

dayan yace kinga malama idan kingama mu bashine yakawomuba kudin dan uwanmuu zaki dauko mana mudauki hakiin mu

dayan yace kuma zamu kara yi miki kashedii akan kikara rikee mana sirrinmu wlh kika kuskura maganar nan tafito cewa mumikayi wanan kisan walahil azim kema sai kin bakinci lahiraa keda yarki wlh zamu kasheku nee abanzaa dan hk.yanda kikayi shiruu afarko kici gaba da rike sirrin

dayan yace kabarta kawai tamafada ne wlh kawai saidai kiiji ki akiyama
kinga mu kinuna mana inda kudinn suke mudauka kawai mu waree

 

tace kujee kudauka.inda kuka ajiyee
azzalimai ai koni banfada ba Allah shi yaganku kuma mudaku gaba gurinshi zamuje shine zai kwato mana encinnmuu

 

basu tsa sauraran ta ba kawai suka shigaa dakin sukasoma chajii basugan komi ba suka fito suka wuce gargeen shanuun da raguna sukasoma kuncesu suna jansuu raguna 30 ne sai kuma shannu 20 ( 50)kenan hk tana zaune tanaji tana ganii sunajan su suka wuce dasuu

duk abunan da akayii akan idon haseenah kuma taji komi maganar da ummi tayi

ahankali tashigo gidan cikin sanyi jiki hartasoma kuka tazauna kusa da ummi

ummi tayi shiru tana kallon ta daganin hankalin da take ciki tasan sarai taji.duk abunda akayii

tadafa kafadar ta ahankali tace banaso kibata ranki akan wanan abun da kikaji kiyi hkr kinjii Allah yana taredamuu

tace to amma ummi dama kinsan wanan abun amma baki taba gayamin ba dama abbahna kasheshii akayii kawai sai kwalla yashiga kwaranyomata tace wlh Allah zai saka mana kawai sbd sungan bamuda wani gatane amma wlh da ace inada yaya namiji da dole ne yakwato mana hakkinmu barema ba baxai bari hkn yafaruba wlh baxasu farayimana hk baa

ummi tace ya isa hk waya gayamiki bamuda gata ai kuwa mumukeda gata tunda munada Allah kuma nagode masa da,azurtani dake yabani ke gaki abokiyar shawara bai barrni hk ba domin da ace hk yabarni dazanfii jin radadin abun ba uwa ba uba ba yar uwa amma kuma sai yabanii ke

tace to shikenan ummi kema kiyi hkr amma yanzu yazamiyi nagan fa duk sun tafi da shanuun mu da tumakin

tace bkm karkidamu ai akoi wasu kudadee ahannuna danamasuu babbar ajiya inda baza,agani ba nasan zasu dan jima mana insha Alah kuma ai Allah bazai hanamu abunda zamuyi ba kinga jeki cire kayan kizo ga abunci nan kici kuma ga fura zan dama

tace to shikenan tareda mikewa ta wuce dakin

kwanaki suna tafiya lokaci yatafi haseenah takara girma tasoma zama yam mata ko nace budurwa inda ayanxu tana JSS 3 ne domin kuwa ummi tana matukar son tayi karatun nan tunda tafaro tana so tacika burin abbahn haseena ne domin shi kecewa yanaso tasamu illimin boko koda kuwa bazatayi aiki ba ai zata inganta rayuwanta da na yaranta

haka ummi ke kokari tana fafutukar neman kudi domin tagan haseenah tasamu illimin nan

har yanxu su hassan basu daina bibiyar suu ba domin kuwa gani suke kamar ummi zata tona asirrin su

gashi yanxu suma su ummin sun soma shiga wani hali narashin kudi tunda babu kadarori duk sundauke shanun

bayan kwana biyu suna zaune ranar haseenah ba,skull

ummi tace inaso naje kano fa domin nagan halinda su hasana sukeciki kuma inaso ne muje tare idan Allah yayi mudawo to idan kuma munyi zamanmu acen ahikenan

 

haseena tace too ni ummi ban katse hanzarinki ba amma fa kinga yanxu ina ajin karshe a karamar sakandiree kinga kibarii yanxu watanni kadanne yarage mugama kinga idan nakarbi takkardun nawa sai mutafi kinga idan munje ma idan munsamu hali sai naci gaba secondry

 

tace to shikenan balaifi ai kinkawo shawara domin nima inaso kiyi karatun nan sosai wlhh amma nagan munsoma shiga wani haline a garinan bawani abun kirki muke samu ba gakuma tsoronn wayanan azzaluman daya cikamun zuciya wlh basuda imani kowanne lokaci zasu iya zuwa su kasheemuu shiyasa nakeso mubar garin nan gaba daya muyi nessa dasu kosamu kwanciyar hnkali

tace hk ne kam ummina kinga yanxu ki shirya sai gobe kitafii kiyi sammakoh nikuwa zan zauna a gidan malam salau kafin kidawo makotansu nedasu mutumcii sosai

ummi tace to shikenan ai bama zanwuce kwana daya ba zandawo kawai burina mugajuna mugana tasan mu muna rayee

tace kai ummi dadai kinyi kwana biyu hk

tace to saidai nayi tafiyan kinsan ai ita tafiya kafin kayine kakeda ita idan kuma kariga kayi to itace da kai

haseenah tace hk ne kam

washe gari da safe tayiwa ummi rakiya har tasha inda zata hau mota bayan ummi tashiga motar tace to nidai ina kara jamiki kunne dan Allah banda rigimaa banda tsokana idan ma an tsokaneki kiyi hkr karki biyeshi kinji koh yar albarka

tayi dariya tace tab araduu ummi duk wanda yatabanii nima sai namashi bakyalewa zanba

ummi tarangwashe kanta tace to ai shikenan Allah ya shiryeki Ameen

motar tatashii sukawucee

tayi dariya tareda mata hannu har suka wucee

itakuwa tadawo cikin kauyen

bayan su ummi sun sauka agarin kanoo lpyy tahau adaidaita yakaita unguwar da tasan anan ne su hasana suke

bayan tasauka tazo tana kallon gurin cikin mmki domin kuwa gidan agarkame yake kuma da alama yajima hk

tana nan atsaye wani mutum yazo zai wuce ta tsaidashi tana tmbyr shii dan Allah masu gidan nan fa

yace ai malama masu gidan nan sunjima da tashii wlhh domin anyi shekaru gsky ai me gidan ingayamiki kudii ne sukazo masa ingayamiki likafa taci gaba kawai sai yabar wanan gidan shida iyalanshii amma fa ke kunada kama sosai da iyalinshi wlhh badan ke nagan kamar daga ruga kika fitoba ai danace koh kece hajiyar shi

itadai ummi shiru kawai tayi tace to da Allah kokasan inda suka koma

yace to wlh ni bansan inda suka koma ba kuma gashi makotansuu ma sun tashi bare ki tmby su kiji domin kila suma bazasu rass sanin inda sukeba

tace to nagode bawan Allah

yace a a bkm yayi wucewan shii

tajima sosai atsayee agurin tana tmbyr duk wanda yazo zai wuce amma amsa dayace daga karshe dai tagan bawani mafita dole tasake taran adaidaita takaita tasha tashiga mota tadawo kauyen su lokacin har duhu yayii ma

 

bayan ta iso gidan ta ajiye kayanta tashiga nan makotan su inda haseenah take tatadota tace taso muje nadawo

tace ummi yanxu a daranan lpy kuwa kika dawo

tataso suka fito tareda yiwa matar salau godiya suka wuce

bayan sun dawone tace ummi miyasa nagan duk damuwa a fuskanki

tace hmmm ina tuninee anya kuwa zamu sake haduwa da yar uwata kuwa najee kanon amma bangansu ba wai ance suntashii daga nan kuma ba,asan inda suka koma ba

tayii shiruu kafin tashare hawayen ta yadago tareda cewa to kiyi hakuri ummi na kidena kukan dan Allah Allah yana tareda muu kinji duk abunda kikagani yafaru hakan ya Allah yakadarta mana saikigan nan gaba idan darabon haduwanku Allah zai hadaku kiyi hkr kinji ummi na

tarungumee haseenah tace bkm kinji kema karkidamu Allah ngd ma sakabanii me kwantar min da hnkli

bayan wata 4 yarage wa su hasseenah Exam kawai yarage masu kammala makaranta

 

ummi tace wlh jiya na tsorata sosai da lamarin wayanan mutane zuwa fa sukayi wai sukace min sunyi mafarkin natona masu asiri

dan hk sunkara yimin kashedine ni wlh namatsuu bamubar garin nan ba ni yanke hukuncin zamu bar garinan dukda bamusan inda hasana takeba xamu shiga birni inneme koda aikatau ne nadingayi ana biyanmu musamu murawa kanmu asiri

hassenah tace ai ummi sati daya yarage mukarasa exam din sai mujira har takardar JLC namu tafito idan akabamu kinga sai muyi tafiyanmu ai koh

tace to shikenan Allah dai yanunamana

tace Ameeen

 

bayan 4weeks kuwa exam dinsu tafitoo inda exam din tayi kyau kamar yanda akeso

ummi tace yanxu kam sai maganar tafiya

haseenah tace haka ne kam

bayan kwana biyu kuwa sungama kimtsawansu sukayi wa su malam salau sallama suka wucee tashaa

bayan isarsu tashaa sukajii ana kiran abuja, abuja, abuja,

ummi tace to ko motar abujan ne zamu shiga

haseena tace E to mushiga mana mutum baisan inda rabonshi yake ba

ummi tatambaya nawa ne kudin motar abujan akace duk fasinja daya 3500 ne tace to shikenan tadauko 7k tabiya masu subiyu suka shiga motar dama gurin mutum biyu ne yarage akejira kawai aka tada motar suka dauki hanya……..

 

 

*MATAR MANYA*๐Ÿ’‹
๐ŸŒน๐ŸŒน
*MATAR MUHEED*
๐ŸŒน๐ŸŒน

 

 

 

story~written
by *UMMY MATAR MANYA*

 

*4&5*

 

A Abuja kuwa dama acen ne su hasana suka koma da maigidanta da yaransu

bayan dawowan su abujan ne MUHEEDDEN yatafi abroad karatu inda yakarancii MEDICIN yazama babban dr yatsaya yana yi aiki ne tareda su na tsahon shekara uku

DR MUHEED kwararran dr ne da kasashee sukeji da shii sosaii ya kware ya iyaa aikinshi sosai

alhaji muktar wanda suke kira da abbah yazamaa babban sojaa inda yataka mukamin General ayanxu haka yanaso ne ya ajiye aikin yahutaa domin indai duniyace antaraa akoi ta sosaii ga kuma yaron shii da Allah ya daukakaa aduniyaa kowa sonshi yake ana samar albarka domin halinshii na taimakoo

 

abangaren hasana kuwa wace suke kira da momy sosai take cikinn daulaa hankalintaa akwancee duk da kuwa tanada damuwa aranta wacce kusan duk wanda yasan ta yasanta da wanan damuwar na rashin yan uwanta harta MUHEED ma tasha sama sa kuka tana cewa yaraimaketa yanemomata yan uwanta dan Allah shi kanshi yashiga damuwa kan damuwar mahaifiyar shi domin kuwa ya sha shiga jirgi yaje kano yaje har cikin wanan kauyen yaduba koda zaiji wani lbrn amma shiru

adaya bangaren kuwa ga mtsalar kanwar mijinta hajiya binta da take fuskanta domin kuwa ita tafita zakkah acikin sauran.yan uwan mijin.domin sauran.suna da.kirki.amma hajiya.binta kokadan batasonn hjy hasana

wanan kiyayyar kuwa tasamu asaline da dama binta bawani son hasana takeva sai kuma gashi daga baya yayanta yazo yayi arziki har sukaje aikin hajji atareda hasanar ita bai fara biyamata ba sannu ahankali kuma arzikin nashi yahabaka sai wata kawarta hjy rukkayya ita bazawara ce data mijinta yasaketa sabida yawon bin malamanta da bokayee sai kuma tazo tace Alhaji muktar takeso yayan binta wato mahaifin MUHEEDEN dafarko da binta taji wanan mgn.a gsky hankalinta yatashi amma tadanne bata nunamata ba

haka suka shiga bin bokaye da.malamai

hjy binta kawai tana biyar rukky ne amma ita batason.ta aure yayanta ko kadan

duk da kuwa tayi tunanin ai dama bason hasana takeba amma gsky duk.da hk itabatason yayanta ya aure rykky domin tasan.halinta ita ba hasana ce damuarta ba kawai bataskn arabata ne da yayanta tanunawa hajiya rukky ta amince mata da kudurinta haka suka dage suka dukufa shiga bokayee da malamai akan ajanyo hankalin alhaji muktar akan rukkayya amma shiruu kakeji wai an aike bawa garinsuu abunda ke faruwa anan shine hajiya binta batason hajiya rukky ta aure yayanta domin tana ganin idan ta aure yayanta ai ko itama zatafi karfinnta itakuwa tana hasadar hakann batason ace arayuwanan haj rukky tafita da komi kuma tasan makircin ruky sarau ma zata iya shiga tsakaninta da yayanta kawai de tana biyeta ne akan itama tana kaunar hkn sosai amma duk gurin boka ko malakin da sukaje tofa bayan sun dawo haj rukky tawuce gidanta itakuwa binta zata zare jiki takoma gurin bokan ko malam tabiya shi makudan kudade akan kar yayi aikinn
batareda rukky tasani ba

to fa kunjii halinda wayanan makiran aminan suke ciki

 

momy kuwa tuni tasan kiyayyar da hajiya binta kemataa kuma tasan take taken rukkayya akan mijinta amma bata nuna komi ba saidai takara dagewa da adu,a tadanne zuciyarta tayi hkr tamaida komai ba komai ba

yaranta ma sun san duk wanan kiyayar da hajiya binta musaman MUHEED karyake kallon bintan kawai yayi shiru ne ya kyaleta kuma shima baya sontaa domin mahaifiya tawuce wasaa

jiddah kuwa itama tanajin tsanar hjy binta har wani sa,ilin ma hajiya bintan tana kusan gane hk
jiddah tana nan sak tamkar haseenah kamar suu har tabaciii tabbas jini yana aiki banbacin su dayane akalar fata ita haseenah faracee tasss jidda kuwa ita jaa cee sosai tagirma yanxu daidai girman haseenah itama tazana jarabawan GLC yanxu zataje SS 1 ne idan kasan ta kasan haseenah to zakacee sudin yan biyuu nee

 

akoi anty nafeesat da itama agidan take marainiyace iyayen ta sunrasu yarinyar kanin alhaji.muktar ce bayan.rasuwar iyayenta nr yadauko ta tadawo anan gidan anty nafisa batada matsala kokadan tanada kirki sosai.kuma tana zaune a gidan ba banbancii itada sauran

*DR MUHEEDEN* matashin saurayi ne dan kima nin shekaru 33 aduniya

dr muheed kyakyawannee namijinee sosaii fari ne tass hakan ne yasa ma sukafi kama da hassenah domin har kalar fatarsu daya gasu su ruwa biyu ne shuwah ne dakuma fulani duka sun hada muheed yana da.kyau sosai gashin ingarman namiji karfafee

muheed yanadaa illimi sosai Allah yabashi fasaha sosai duk afadin nigeria babu wani gwararen DR dayakaii shii wanda ayanxu hk yana nigeriaa ne dawo gaba daya bayan yagama yimasu aikin da suka rikeshi

akoi babban hospital dinshii da aka gini masaa anan cikin garin abujan mesuna *MUHEEDEEN GENERAL HOSPITAL*

hospital nee katafaree babu abunda ba,ayi acikin akoi kwararinn likitocii sosai ciki kuwa harda turawa ma mutane daga garuruwa suke zuwa hospital domin lpyrsyu

shi mutum nee me dukiyaa sosaii yanada kudi kuma yanada taimako al,umaa shiyasa mutane suke sonshii

miskilin mutum nee shi sosaii mgn batadameshi ba kokadan bayason hayaniya kokadan duk wanda yasanshi kuwa yasan wanan
yan mata dadama suna kawo masa hari yayan manya dama yayan gwamnoni amma kosunzo basa ganin fuska

kamis shine aminin shi nakusaa sosaii atare sukayi karatu a india bayan sun dawo kuma yadauke shi aiki

kamis mutumin kirkinee sun zama tamkar yan uwa shida muheed yasan halin muheed sosai kuma shima duk yanda ran muheed yabacii shi zai iya kwantar masa da hankali zumuntar su takai iyayee ma sukeyi

baya son raini ko kadan hkn yasa jiddah ko laifi kadan tayii masa zata sha mari hk yasa take tsoransa

 

ayanxu hk yarinyar hjy binta ce zainab amma zee ake kiranta ita ce ke masifar sonshii yasani sarai amma shi ko kallon banxa bata isheshi ba domin ya tsanii mahaifiyar ta sosai

suna mota ne shida kamis yataso daga office zaije gita agajiye cikin gajiya yake driving din yana dan tsaki

yajuyo.yakalle kamis din yace wai kamaidani drivern ka ne pls kakarbi driven dinan wlh agajiye nake sosaii kuma kace fa nafara saukeka

 

kamis yayi dariya yace kai mutumina yanxu dan.Allah shikuwa driving menene acikin.aiki dazakace har.kagaji ne amma sbd baka wani.saba.bane shiyasa yau kuma driver yaje gida yaduba iyalli dolece takawo hkn

yayi tsaki.tareda fadan banson iskanci fa ni idan.har baidawo nan da.gobe ba to.zan.samu.wani driver.ne

kamis yace to idan yadawo yagan kasamu wanin fa

yace ba ruwankaa ai saikadaushii aikin kai koh

yayi dariya tareda sorry sir ina ni inadaukan malam aminu aiki ai duk mutumin da yasaba aiki da.kai to fa bazai tabajin dadin na wanii gun ba inba kaiba

kawai yashare shi yaci gaba da
driven dinshii domin dan surutun nan da yayi har yaji kanshi yasoma ciwo

kamis murmushi kawai yake domin yasan halin mutumin nashi

su haseenah kuwa bayan sun sauka garin.na abuja basisan.inda zasuje ba kawai sai suka ci gaba da tafiyaa akafa sun wucee unguwanni da yawa suna shan.kallo.gidanjee da guraree gwananin.ban.sha,awa

har sun.fara jin.yunwa ma amma.basusan.yazasuyii ba gashi basusan.inda zasu.kwanta ba gashi.magrip sai.karatowa yake

hankalin ummi yasoma tashi tadasoma wanan tunanin aranta adu,a take Allah ya isaa tsakaninmu da wayanan mutanen da sukasa mukabaro muhlinmu muka shiga duniya inda bamusan kowa ba

haseenah hankalinta.yatafi da kallon wata motar da tawuce basuyi auneba kawai sukajii kiiiiiyy motar ta kadee ummi…..

 

oh my god nacikin motar sukafada gaba dayansu.tareda fitowa Dr wanda yake mazaunin.driver .yana.dafe da goshi yafito

haseenah kuwa da taji karar motar takade umminta tajuyo da karfi tadora hannu aka takwala karaa tareda cewa na shigaa ukku ummina

tafado.kan ummin tana ihu tana kuka

shikuwa ganin yanda tafadawa ummin ne yabashi haushi matar da batada lpy.kuma zata fada mata ajiki hk

yace ke bakida hankaline zaki karyata wlh dagataa tunkan.na marekii

haseenah.cikin tsoro taadan.dagawa ummin.

shikuwa yadauke ummin da bata ko motsi da alama ma tasuma yasata a mota haseenah ma tashiga motar da kayansu kamis ma yashiga suka koma hospital dinsuu

sai tsakii yakeeeee……..

 

comment#
share#
vote#

 

*MATAR MANYA*๐Ÿ’‹
๐ŸŒน๐ŸŒน
*MATAR MUHEED*
๐ŸŒน๐ŸŒน

 

 

 

story~written
by *UMMY MATAR MANYA*

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da ฦ™asaita take saukowa …

One comment

  1. Maragret Stanczyk

    Hi, I do think this is a great site. I stumbledupon it ๐Ÿ˜‰ I am going to return once again since i have bookmarked it. Money and freedom is the greatest way to change, may you be rich and continue to guide others.

Leave a Reply

Your email address will not be published.