Breaking News
Home / HAUSA NOVELS / NAFEESAT

NAFEESAT

NAFEESAT

*EPISODE* (1)acc

 

‘Yanmata ne su biyu da shekarunsu be gaxa 24years ba, suna xaune a tamfatsetsen Palo da yagaji da haduwa cikin luntsuma-luntsuman kujerun da aka qawata Palon dasu, sun hade Kansu sai latse-latsen waya suke, ihun da sukayi ne yasaka wata matashiyar yarinya da bata haura 19years ba tafito daga dakinta da gudu tana tambayansu lafiya? Bayan data xauna akan hannun kujeran dasuke, wacce ke riqe da wayan CE tamiqa mata cikin xumudi take fadin

Da Allah Ihsan duba kiga wadannan akwatunan sunyi matuqar kyau wlh, su nakeson sweety yamin gaskiya na FASA wadancan da nata6a nuna masa

Ta6e baki Ihsan tayi bayan tagama gani tamiqa mata wayan tana cewa

Ke dai aunty Nafeesa baki da aiki sai ganin abubuwa a social media kina cewa shi yaya xaimiki, duk da laifin Momy ma datake biye miki, ita kuma aunty Baseera tana xugaki shi kuma yaya yana biyewa shirmenki

Hararanta Nafeesa tayi tace

Wato shirme nakeyi ko Ihsan? To laifi ne Dan na xa6i abinda nakeso asakamin? Yanxu fa mun shigo xamanin wayewa ne ba gidadanci ba?

Ke dalla kyaleta ‘yar baqin ciki CE wannan yarinyan, in kika biyeta zata maidake sakara CE, in baxata iya gani ba ta6ace anan wajen

Baseera take fadin hakan.. ‘Dage kafada Ihsan tayi tana ta6e baki tamiqe takoma kan 3sitter dake nesa dasu kadan takwanta tare da mayarda earphone din dake rataye saman wuyanta cikin kunnuwanta tana latsa waya.. Wayan Nafeesa CE yasoma ringing, murmushi tayi bayan taduba me kiran tace

Kinga dan halak din yaqi ambato

Amsa call din tayi takanga akunni tana ci gaba da murmusawa lokacin datake fadin

Sweety yanxu nake tunaninka araina fa sai gashi kakira

Kyakykyawan murmushinsa me qara masa kyau da kwarjini yayi yana juyawa akan kujeran dayake, cike da nishadi yace

Allah ko Nafee na? But baki kiran ba har nariga ki?

Yafada yana lumshe fararen idanuwansa

Uhm yanxu nakeson fa kiranka, wayan ma na hannuna kakira

Tafada tana sakin murmushi qasa-qasa

I know! that’s why naji ajikina, kina gida ne ko school?

Ina gida sweetyna, yaushe xaka dawo?

Maybe sai dare, xan raka Haidar duba kayanSa da’aka sauke mishi ne, kinason ganina ne?

Yaqare maganan yana kwantar da kanshi jikin kujeran.. Dariya tasaki me sauti tace

Akwai labari ne but sai kadawo

Okey kikulamin da kanki bye 👋

Aje wayan yayi saman table yana murmushi tare da kallon Haidar da yabuga tagumi yana sauraronshi.. Gira daya yad’age 😉

Lafiya? Wannan kallon fa?

Ajiyan heart Haidar yasaki yacire tagumin dayayi yace

Ai Kaine kaxama abin kallo dole nakalle ka, mamaki wlh kake bani kamar ba kai bane kake cewa Momy ta liqa maka jaraba, but now kajone kunata xuba love har da saka rana

Ya son ranka? Kuma nan da one month asha biki ba

Al’ameen yafada yana miqewa tare da miiqa yana yarfe hannayensa

Kai ‘Dansa ido tashi muje naraka ka, ka daiji abinda Nafee na tace “jirana takeyi

Tashi Haidar yayi yana dariyan shaqiyanci yace

Ai da katafi kiran nata, ba sai kanunan kana soyayya ba nasani, nima very soon xan shigo layi ai

Da ka kyautawa kanka kuwa

Cewar Al’ameen yana kad’a keeys dake cikin yatsunsa.. Fita sukayi daga office din suna xantawa..

About Godswill

Check Also

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel

NI DA MALAMATA Complete Hausa Novel Page 1 . …..Cikin yanga da ƙasaita take saukowa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.