SARAN BOYE Page 11 to 20 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / SARAN BOYE Page 11 to 20

SARAN BOYE Page 11 to 20

SARAN BOYE Page 11 to 20

……………….Doctor na isowa aka maida Nu’aymah bedroom ɗin Hajjo. duk fita sukai suka bashi waje yay aikinsa yanda ya kamata. Sai Abubakar da aka bari kawai dan ya taimaka masa da wani abun idan ya buƙata.
        Sunyi jigum-jigum a falon Hajjo, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa wadda ALLAH kaɗai yasan minene a cikinta.
       Juyawa baba malam yay a hankali ya fice daga sashen. Sashensu ya nufa dan sai yanzune hankalinsa ya kai ga rashin ganin Umm tare da su. Babu kowa a falon, ya nufi bedroom ɗinta canma babu kowa. Fitowa yay ya nufi nasa ɗakin ko tana can. Sai dai kuma nanma babu kowa. A ɗan ruɗe ya dawo ɗakin Muh’d. Muhammad ɗin kawai ya samu yana canja Uniform ɗin islamiyya dan yanzun suka taso. Baima gansaba, sai da yace, “Muhammad ina Umm ɗinku?”
     Jiyowa Muhammad yay da sauri, fuskarsa da ɗan damuwa yace, “Abba nima ban gantaba, na shiga ko ina bata nan kuma yunwa nakeji”.
       Shigowa sosai Baba malam yay cikin ɗakin idonsa akan Muhammad ɗin. “Yunwa kuma Muhammad? Bakaci abinciba ka fita ne?”.
       “Abba lokacin nasha fura wajen Hajjo na ƙoshi, yanzu kuma zanci”.
     Kama Hannunsa Baba malam yay suka fita kitchen da tsammanin zaiga Umm a can. Sai dai kuma mai aikinta kawai suka samu tana gyaran kayan miya. Cike da girmamawa ta gaida Baba Malam ɗin. Amsawa yay yana cirar tuffah dake cikin fruit tray ɗin da suke sakawa. Ƙarasawa yay wajen fanfo zai wanke Saude tai saurin faɗin, “Baba malam kawo a wanke”. Baiyi musu ba ya miƙa mata tuffa ɗin guda biyu daya ɗauka. Sake bin kitchen ɗin yay da kallo kafin yace, “Ina Jannat ɗin take na ganki ke kaɗai kina aiki?”.
       Saude data wanko apple ta ɗaura a ƙaramin filet tace, “Nima na shigo ban gantaba, dama naje can ƙasan layine na sayo mata daddawa data bada. To nadawo kuma na duba kamar ta fita, shine nace bara na gyara ko kayan miya kafin ta dawo”. Shiru Baba malam yayi gabansa na faɗuwa. Amma sai ya danne ya kalli Muhammad dake saurarensu. Filet ɗin tuffa ɗin ya miƙa masa yana faɗin, “Karɓa wannan kaje kaci muje salla mu dawo saika zauna cin abincin”.
         Kai Muhammad ya ɗaga masa da amsar filet ɗin. Yaron nagaba yana biye da shi har suka fice. Sake komawa yay ɗakin Umm ɗin dai zuciyarsa na bala’in harbawa. Tsaye ya isketa gaban Wadrobe tana fiddo kaya da alama wanka tayo. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin ‘Alhmdllh’ a fili. Hakanne yasata juyowa da sauri dan bataji shigowarsa ba. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru tana kallonsa kawai.
       “Naje massallaci”. ya faɗa a taƙaice yana juyawa ya fita daga ɗakin. Binsa da kallo Umm tayi harya ɓace mata sannan ta ɗauke kanta hawaye na ziraro mata.
★★★★
        A ɓangaren Hajjo Doctor ya bama Nu’aymah dukkan taimakon daya dace kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfaɗo ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ƙarasa ƴan dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfaɗo.
         Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfaɗo. Dan yau ana idar da salla gaba ɗayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.
      Bayan Doctor ya kammala komai ya buƙaci tattaunawa da su Abbah. Da ƙyar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
        Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, “Gaskiya wannan karon jikin Nu’aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba’aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ƙarfafa shi”.
        Hajjo ce tai saurin faɗin,  “Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ƙoƙarin kiyayewa. Yau ɗinma kuskure aka samu kasan ajizanci na ɗan adam. Yanzu minene mafita?”.
           “To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka”.
       Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, “Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu’a insha ALLAHU zata farko cikin ƙoshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Australia ne”.
        A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani”.
      “Amin ya rabbi, nagode sosai”.
      Abbah Musbahu yace, “Muna surarenka. Wane shawarace da kai?”.
        “Dama akwai wani likita babba kuma ƙwararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ɓangaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu’aymah yana basu taimako. Matsalar ɗaya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matuƙar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ƙasar gaba ɗaya”.
            “To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta”. Cewar Abban Abdallah.
        “Ai anan gizo ke saƙar Malam. Dan ko nawa za’a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ɗin da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai haɗaka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ɗin da za’a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za’a dace. Har jirgi aka aika ya ɗakkosa daga wata ƙasar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi”.
      Babu wanda bai jinjina wannan al’amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, “To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ɗin na ganin nasa kawai, ko’a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace”.
        “Hakan shine dai-dai. Ga Number ɗaya daga ma’aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ƙarin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan haɗa muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne”.
      Rubutawa yay ya miƙama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita miƙama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ɗauka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ɗin bayanan ciwon Nu’aymah waje guda ya sake mi[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*
     *NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 16*
                 Ta zauna Gefen  Umma tana kad’a kafa.
Naseer wani irin Mugun kallo ya Mata Yana “ga dakuna can guda biyu ki duba Wanda ya Miki ki saka kayanki a ciki idan Kuma Bai Miki ba sai kisan nayi babu yanda za’ayi sama taka ki zo ki wani ce a tasar Miki daga d’aki.
Daga Haka Naseer ya mik’e fuskarsa a balain had’e ya ko kallon B’arin da Hajara take Bai kalla ba ya shige dakin Naeema ya banko k’ofar
Ni kuwa Yana shigewa na mik’e da Sauri cikin fad’uwar gaba da rawar jiki na fara k’ok’arin juyawa na koma kitchen Umma kuwa ta daka min tsawa tana na koma na zauna.
Da Sauri na zauna a gabansu Kamar Mai neman gafara kafin kace me har hawaye ya fara wanke min fuska
Umma na k’ok’arin Magana naji muryar Hindatun tana “Hajara zamu daidaita da Wanan Dan naki kuwa Kinga yanda yake min fa ita Kuma nasan badan komai yasa yake Haka ba sai Dan wanan kod’add’iyar Koda uban me ta fini oho”
Da Sauri Hajara  ta karbe tana “ki kwantar da hankalinki Ni zanyi maganinta idan Bata bar gidanan ba zata bar gidanan idan wuya ya kusa kasheta ko Kuma a fita da gawarta bantaba ganin nataciya irin yarinya Nan ba ni farkon ganina da ita naji batamin ba Dan Ni idan mace ta fiye kyau Tsanar ta nake Ni nasan Bata bar Dana Haka ba wlh akwai abinda tayi Masa ta juyar Masa da Kai Amma da sannu Zan dawo da hankalin Dana kanki Hindatu ke dago ki kalli cikin idona.
Da Sauri na Dago har a lokacin hawaye kawai ke zuba a fuskata  “Ga Auntynki Nan Hindatu matar Naseer Kuma zabina duk abinda take so shi za’ayi a gidanan duk aikin data sakaki ki tabbata kinyi Mata idan ba Haka ba wlh ranki ne zai b’aci kindai San halina sai dai ki bawa wani labari Dan Haka Maza tashi kije ki zab’a a cikin Dakunan can Wanda yafi girma ki gyara ki zo ki kwashe Kayanta ki Kai Mata ki saka Mata kuma.ruwan wanka idan kin fito ki daka Mana Sakwara muci  kinji ko bakiji ba”?
Da sauri na gyad’a mata Kai na mike na nufi d’akin karshe Dan yafi na tsakiyar girma da Umma ta zauna ita da Saffiya.
Ina gyara d’akin Ina kuka wai ni Haka rayuwata zata Kare daga wanan sai wanan Mai Nayiwa Umma Haka ta  tsaneni.
Ina Gama gyara d’akin na wanke band’akin dayake da ruwa a band’akin na tari ruwa a bokiti Yana cika na fito.
Na koma palon na fara kwaso kayan Hindatun Ina kaiwa daki Umma sai zagina take Tana zagin iyayena ita kuwa kawarta kur tamin Ido kamar zata cinyeni Ni kuwa na hau addua a Zuciyata Dan kallon da takemin yayi yawa ita kuwa Hindatu sai wani girgije girgije take Tana yatsina fuska.
Ina fitowa daga d’akin na shiga kitchen na fito da doya manya guda biyu na fara feraye wa Ina cikin ferayan naji Sallamar su Zahira.
Babu Wanda ya amsa musu bansan ya akayi ba  sai ji nayi Zahira ta kwalla wani uban ihu sai dum dum nakeji kamar irin an samu babba Ana duka.
Jikina ne ya hau rawa na runtse Ido hawaye na zubomin ko ban lek’a ba nasan Umma ce ke dukan Zahira na Dade da sanin Umma ta balain tsanar zahira Ni nasan tsanar data min ne ya shafi Zahira shiyasa ma a cikin Yarana Zahira ko muryar Umma taji sai ta nutsu kaga alamar tsoro ya bayyana  fuskar ta sosai dukan da takewa zahira na ringa jinsa a jikina ta Sha dukan Zahira ba tare da ta Mata komai ba  na Kuma rasa Mai Yar yarinya da Bata fi shekara bakwai ba ta Mata.
Zagin Zahira kawai take Tana durma Mata duka tana “shegiyar yarinya tun kina karamarki an koya Miki bakin Hali baki iya Gaisuwa ba wane irin tarbiya Naeema ta muku wato ita ta kitsa muku idan Kun gani karku gaisheni ayi yara basuda tarbiyya balle wanan Yar iskar yarinya Ni nasan yarinya Nan idan ta girma Yar iska zata Zama shegiya Mai halin uwarta”
Naseer dake Sallah a a guje ya fito daya Sallame Sallar sabida yanda Zahira ke ihu Dan ba karamin Jibga take mata ba.
Nadeeya kuwa Tana gefe tana kuka
Fusge Zahira yayi cikin wani irin B’acin Rai ya kalli Hajara Yana “Haba umma  Mai karamar yarinya Nan ta miki kike dukanta Haka kamar kin samu babba haba Umma “
“Zaka iya Rama Mata tunda na daki Yar gwal Naseeru Kai baka ganin irin tarbiyya da shegiyar matarka ta musu kwanaki Dana zo suna kallona Suka k’i gaisheni yanzu Kuma sun shigo wanan Yar iskar yarinya ta zo zata wuce ta gabana har da taka min kafa duk idonka Bai bud’e kaga irin tarbiyyar da Naeema ta musu ba sanan Dan na daketa kazo ka tsaya kana min tambayoyi Na daketa Naseer zaka iya Rama Mata nidai sukayi ba daidai ba Dole na hukunta su daga Kai har Naeema San Yaya ya rufe muku Ido Kun kasa musu tarbiyya ko baki akayi ai Dole aji kunya ai tunda yarinya Nan ta kwaso uwarta nasan inta girma ba lailai tayi albarka ba”
“Allah ya Miki albarka Zahira zakiyi Albarka insha Allahu nace Ina kankame wuk’ar hannuna da har ya yankeni jini na zuba bansani ba sosai kalmomin da Umma ke jifan Zahira dashi ya ringa min ciwo har tsanar ba iya Ni ya tsaya ba har Kan zahira da bani kadai na haifeta ba Jinin Naseer daya kasance danta na yawo a jikinta har Umma tace Zahira Yar iska zata zama baza tayi albarka ba wanan wane irin kiyayya ne kuka nake kasa kasa Ina jiyo muryar Naseer na “Umma wane irin kalamai kike Yi Haka karki manta fa yarinya Nan jikar ki ce akan me Zaki na cewa baza tayi albarka ba insha Allahu yayana zasuyi albarka Umma Dan Allah Umma kiringa kiyaye kalmomin da zasu fito bakinki Zahira fa yarinya ce ballantana kice ta mallaki hankalinta Umma Kinga yanda Kika kumbura Mata jiki fisabillilahi idan Haushin Mahaifiyarta kike ji ai Bai Kamata laifinta ya shafeta ba nawa Zahira take tsakani da Allah Naeema na iya kokari Akan yaran nan ba Kuma Ina fada Dan na kareta ba”
“Ai duka nake jira kamin Naseer ya ka tsaya iya surutai”
Naseer da idonsa ya kad’a yayi ja Bai ce komai ba ya daga Zahira da numfashin kirki ma Bata iyayi ya Kai ta d’aki dawo ya rik’e hannun Nadeeya ya d’auki Humaira da ihun zahira ya tasheta take ta kuka itama”
Nima kukan Humaira ne yasa naso fitowa daga kitchen din na d’auketa na goya ta sai Naga Naseer ya d’auketa
Hakane yasa na koma kitchen na daure hannuna da jini ke ta zuba na cigaba da aikina Ina kuka Ina tunanin abin Yi Taya ya ma Zan iya barin yayana tayaya Zan iya tafiya na bar yarana a hannun Umma da Raina Agaban idona tana azabtar min  da Yaya inaga bana Nan.
Ina cikin had’a Miya naji Sallamar Mmn Mannir nasan Minal ta kawomin tunda Magriba ta kawo Kai
Gaida su Umma take naji Umma na tambayarta daga Ina take
Mmn Mannir kuwa Tana Mata wanan tambayar tasan wacece ita kuwa ta had’e Rai tana Ina matar gidan take”?
Take Hindatu ta watsa Mata harara tana “Gani Nan nice matar gidan ya akayi”?
Wani kallon Tara saura kwata Mmn Mannir ta mata ta ja Tsaki tayo hanyar kitchen da take Jin motsina ciki.
Ni kuwa Ina kitchen Ina Jin maganr da suke jikina ya hau rawa.
Har kitchen mmn Mannir ta shigo ta ajiye abincin hannunta ta kunto Minal da Saura wata biyu tayi shekara biyu da bacci ya d’auketa tana “Gata Nan tayi bacci Naga alamar yau gidan naki a cike yake toh nidai shawarar da Zan baki shine wlh ki kwatarwa kanki ‘yanci ki rage tsoron Nan idan babba Bai ji kunyar hawa jaki ba toh jaki bazai ji kunyar  kayar dashi ba.
Ihu kawai mukaji Umma nayi ta hau kururuwa
Sosai hankalina ya tashi na rude da ganinta a bakin kitchen abinda ya ban tsoro yanda take zunduma ihu
“Yanzu Ni kike cewa jaka Yar nan Mai na Miki”?
Naseer a guje ya fad’o kitchen din mmn Mannir kuwa ta saki baki cikin mamakin sharrin da Umma ke neman Yi Mata
Kuka umma ta saka ta kalli Naseer dake ta tambayar Mai ya faru
Ta hau cewa “wanan yarinya Nan ce tayi Sallama muka amsa tana ganinmu taja Tsaki ta wuce mu ta shiga kitchen dinan shine Ni Kuma nayi mamakin tsakin da ta Mana shine na biyota naji dalilin dayasa ta Mana Tsaki Ina zuwa naji tana cewa Naeema wacce jakar ce wancan Yanzu Naseer har maganata Naeema keyi da wasu har a shigo Inda nake ace min jaka toh wlh daga yau Kar na Kara ganin kafar matar Nan a gidanan wlh daga yau Kar na Kara ganinta da Naeema idan ba Haka ba daga Kai har Naeema sai na dau mummunan mataki akanku da ganin matar Nan ba matuniyar arzki bace”
“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu mama da girmanki kike karya da girmanki Zaki min sharri Ni nace Miki jaka kiji tsoron Allah”
Naseer kana kallo tana cemin Ina karya bazaka dau mataki ba”
Mmn Mannir Bata Bari ma Naseer yayi magana ba ta mik’a min Minal tana “ba sai kin biyo ta Haka Zaki rabani da Naeema ba ki kwantar da hankalinki bazan Kara zuwa ba kamar yanda kikeso sabida na lura bakyaso kowa ya rab’i Naeema Sabida ki yi ta azabtar da ita Kar tayi hulda da kowa ballantana a kawo mata d’auki toh Bari kiji na fada miki kiji tsoron Allah domin shi sharri Dan aikene watarana zai dawo Miki tun a gidan Duniya Allah ke hisabi kuma Zaki ga karshenki  Naeema Zan tafi xan Kuma baki shawara idan Kinga akwai cutarwa a zamanku ki hakura da Naseer tunda Zama da danta ba Dole bane daga Haka ta bangaje Hajara tayi wucewarta.
Umma kuwa hannu ta hau tafawa ta kalli Naseer tana “Ashe gulmana Naeema keyi Ashe Haka Naeema take bin mutane tana musu gulma ta abin har ya Kai har da ta  tamin sharri
Dama Haka kike Naeema toh wlh daga yau  makarantar ma kin daina zuwa tunda acan kike haduwa da mutane kiyi gulmana har ki zageni Naeema Ina uwar mijinki toh wlh duk zagin datamin ba Ni ta zaga ba uwarki ta zaga Kai Naseeru wlh Tallahi na soke zuwa makarantar ta  ko k’ofar gida bana so Naga kafarta a da sati daya zanyi Amma na ma fasa tafiya sai na kwana biyu shegiya Mayya”
Daga Haka ta juya ta barni a durk’ushe Ina ta kuka ko kad’an ban kawo sirrin Dana gayawa mmn Mannir zata zo ta tona a gaban Umma ba Dama gudun Haka yasa tun farko naki Gaya Mata ko Naseer ma ai bazai ji dadi na fadawa wani maganar ba duk ba wanan yafi bak’anta min Rai ba sai makaranta data ce bazan koma ba Allah yasan idan akwai abinda ke faranta min a rayuwa  yanzu Bai wuce makarantar da nake zuwa nake samun ilimi ba sosai nake Kara sanin rayuwa sai gashi lokaci guda Umma ta katsemin   Mai yasa mmn Mannir zata min haka”
Dafani da akayi yasa na Dago Naga Naseer ne da idonsa ya kad’a yyi ja idan ba karya idona yamin ba har hawaye ne ya Dan kwanta a idonsa
“Kiyi hakuri Naeema ki cigaba da hakuri watarana sai Labari nafiki Jin ciwon abinda ke Miki Amma ba komai Zan sadaukar da farincikina na faranta Miki idan Naga Umma ta cigaba da matsa Miki Zan sawwaake miki sabida ki samu yancin  Mahaifiyata ce bansan ya zanyi da ita ba Dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da gayawa Allah Yana sane damu ko auren Nan data k’ak’a bamin ba so nake ba tilasta min tayi idan kin Gama kizo akwai sakon da Mallam Musbahu ya bani na baki”
Daga Haka Naga ya mik’e da Sauri ya nufi dakina da Minal a hannunsa.
Ahaka na daka Sakwaran Ina kuka Sosai naji komai ya ficemin a Rai na ringa Jin inama inada damar da Zan gudu da yayana ko bara ne ma na ringa Yi a titi Ina ciyar dasu Amma aka cigaba da Haka zaa Kai ga na gudun Dan na gaji Kuma Ina gudun ba’a garin Nan Zan tsaya ba Tasha zanje na hau motar da zata kaini garinmu.
Har daki na Kai musu abincin Dan sun bar palon Hindatu da Kawar Umma ne kawai a zaune Umma da alamar ta shiga bandaki.
Nazo fitowa Hindatu ta tsayar Dani tana na kawo Mata wani lemon Bata San wanan tace tana hararata
Haka na fita na dauko Mata wani na fito daga d’akin na shiga d’akina Dan nayi Sallah Magriba Dan Ina shiga d’akina Naga Zahira a kwance tayi rub da ciki bayanta yayi jawur dayake farina ta d’auko sai sauke ajiyar zuciya take.
Naseer Kuma na d’aga gefenta Yana Dan mulka Mata jikinta da Robb bandaki na shiga da Sauri sabida kukan dake neman k’wacemin.
Ahaka naci kukana na Godewa Allah  nazo na tadda sallah Ina iddarwa na maida kaina nayi Sujjada na fara kuka Ina rokon Allah ya kawomin d’auki.
Naseer shima Yana daga daya barin nawa bansan.mai ya hanashi zuwa Massallaci ba ahaka mukayi sallar Isha muna iddarwa.naje kitchen na dauko Mana abinci dayake indai Naseer na Nan a faranti daya muke ci da yaran Minal ce kawai nake Dan Bata a baki Sabida Naseer da su Zahira na zubo abincin Dan bazan iya cin abincin ba sabida b’acin Rai.
Zahira har lokacin sauke ajiyar zuciya take Ni Kuma bana San ma na jawota jikina Dan yanda nakejin Raina kuka zanyi sosai bazan iya rarrashinta ba.
Naseer shima gani nayi ya kasa cin abincin ya hau bawa Nadeeya abinci a baki ganin Zahira Taki cin abincin yasa yace Mata taci Mana bud’ar bakinta sai cewa tayi “wlh Tallahi Abba ban yiwa Umma komai ba Nadeeya ce ta fara gaisheta shine na tsugunna Dan na gaisheta Dan Haka Umma ta koya.mana mu ringa tsugunna wa idan zamu gaida babba shine Ina tsugunnawa ta hau dukuna wlh ban Mata komai ba ta karashe tana fashewa da kuka.
Kau da kaina nayi Sabida hawayen dake tsere a fuskata Naseer kuwa sai daya hadiyi yawu Mai daci kafin ya jawo Zahira jikinsa ya hau Bata hakuri Yana Bata abincin a baki wanda dak’yar ta fara karbar abincin tana ta sauke ajiyar zuciya.
Yana cikin Bata muka ji a banko k’ofar Umma ta fado d’akin tana “badai kana nufin a d’akin ta zaka kwana ba ka dai San sai kayiwa Hindatu kwana bakwai ko”?
Dan Haka maza kazo ka wuce matarka na jiranka kafin Nan da wani wata Taran wanan Mai gindin haihuwar ta Kara haifo Mana Yarinya Mara tarbiyya”
Daga haka ta zabgamin harara ta  Kara banko Mana k’ofar.
Daga Ni har Naseer babu Wanda yayi   magana a cikinmu Ni zuwa yanzu ma na kasa kukan filin sai na zuci
Naseer shima sai daya Dade Bai motsa ba Bai Kuma min magana ba kafin Naga ya mik’e ya janyo jakar kayansa yan Ciro wani bak’in Leda ya bud’e.
Yana “Ga sakon da Mallam Musbahu ya bani  na kawo Miki”
Da Sauri na saka hannuna na karba na duba Yar wasikar da yamin Inda yake cemin na rataya wani rubutu daya nanade da takarda a bakin k’ofata.
Sai wani shima da akayi rubutun a ciki aka nannade shi da laya yace na makala a kaina Amma na ringa kiyayewa idan Zan shiga bandaki na ringa cirewa ya Kuma ce Kar manta na ringa kwanciya da alwala a jikina.
Sosai naji dadin Aiken da Mallam Musbahu yamin Naseer ne ya ratayamin a saman bangon kofata na samu pin na makala abin akaina.
Zage zagen da muka jiyo Umma nayi na Naseer ya rainata yasa ya mik’e da Quraninsa a hannu da Sallaya da carbi  ya kalleni yacemin sai da safe.
Bance masa komai ba ya fita a Daren ranar xan iya cewa sai bacci barawone ya sace Ni akan sallaya.
Naseer kuwa Yana shiga d’akin yaga Hindatu taci kwalliya ta Dane gado tana ta Masa fari Umma kuwa Dama a Palo ya barota da jar  doguwar Riga ita da kawarta.
Bai kalli Inda Hindatun take ba  ya hau Kan darduma ya bud’e Quraninsa yayi gyaran murya Hindatu kuwa ta duro da.sauri ta tsaya gabansa tana “Wai an Gaya maka Ni hoto ce ko wancan kanjalalliyar matar taka Haka kake Mata idan ka shiga d’akinta.
Karatun da Naseer ya fara Yi da k’arfi cikin zazzakar murya yasa ta fice da sauri.
Yanaji Umma tana kiransa daga nesa Dan Bata iya isowa bakin kofar ba ya shareta ya cigaba da karatunsa Dan ko umman ma da Karatun zai koreta daga gidan
Sosai ran Hindatu ya b’aci ta hau  surfawa Umma masifa Umma na Bata hakuri.
Washegari sai Dana shirya su Zahira Dan su tafi makaranta wani irin bakin ciki ya Kara turnike Ni da yanzu nima na shirya na tafi.
Tamkar baiwa haka na zama.a gidan Dan sosai nake bautawa Umma da Hindatu dake balain.jin haushina Dan gani take duk sabida Ni Naseer yak’i kwanciyar Aure da ita Dan karatun Qurani dayaga basa so kawai yake yi daddare da safe Kuma sai ya fito ya shiga d’akina ya Sha baccinsa zuwa Sha biyu ya fice daga gidan.
Yana fita kuwa Haka zasuyi ta zagina har Hindatu ta ringa gwada kawo  hannu jikina
Abinda na lura dashi basa iya biyoni dakina su mun Dan Umma ta Sha gwada shigowa d’akina sai Naga ta koma da gudu ta ringa cemin Mayya.
Banma San a rahama nake a baya ba sai da Hindatu tazo gidan ko hanyar waje Umma Bata barina nayi.
Naseer kuwa ya Sha fadan ya Sha zagi a wajenta Akan yak’i kula Hindatu shi kuwa sai dai ya Bata hakuri yace akwai adduar da yake yi yana gamawa zai kulata.
Ranar da su Umma suka cika sati da zuwa da sassafe na farka kamar yanda na Saba na Dora abincin Safe na fito na tashi su Zahira Dan na shirya su su tafi makaranta.
Zahira na fara yiwa wanka ta zauna a d’akin Dan indai Umma na Palo Bata fita Haka take zama adaki a yarana Zahira tana da balain San kallo duk Santa da kallo idan Umma na palon hakura take Haka ma take tsoron Hindatu sabida rankwashin da take Kai Mata a Kai.
Nadeeya ita Kuma rawar Kai ne da ita da Wasa hakane yasa Ina Mata wanka ta fito waje na hau yiwa Minal duk na dauka suna d’akin sai dana Gama yiwa Humaira na fito daga band’akin na ajiye Humaira Akan gado na fita zuwa kitchen Dan na juye ruwan tea d’in.
Ina gama juyewa na fito
Naga Umma ta Sha bakakken Kaya har kasa gefenta Kuma Hindatu ce tayi irin shigarta Haka kawai naji gabana ya Fadi da muka hada Ido ta min wanan murmushi nata Mai tsinka min zuciya da Sauri na shige d’akina Ina jan Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha.
Ina shiga d’akin naji duk ba a nutse nake ba ahaka na dauko Vaseline na hau shafawa su Zahira Sam ban lura Nadeeya Bata d’akin ba sai Dana Gama shafawa Humaira na lura Nadeeya Bata dakin.
Da Sauri na kalli Zahira cikin fad’uwar gaba Ina tambayarta ina Nadeeya take”?
Sai tacemin ai Ina mata wanka ta fita waje aguje ko wandon ma Dana d’auko musu Bata saka ba.
Hankalina a balain tashe nayi waje na tsaya a Palo Ina dube dube banganta ba na shiga kitchen  da Sauri Ina kwalla Mata Kira Nan ma shiru.
Kara dawowa nayi na shiga band’akin palon shima Bata Nan bana shiga d’akin Umma Dana Hindatu Amma sabida tashin hankali Haka na shiga Ina kwallawa Nadeeya Kira amma banganta a d’akin ba.
Haka kawai naji jikina ya fara balain rawa cikin tashin hankali Nazo tsakiyarsu Umma Ina  “Dan Allah Umma kungane min Nadeeya”?
Umma ko.kallona batayi ba sai Hindatu ce tacemin ajiyarta Kika bamu”
Da Sauri nayi waje na sauka ringa hada stair uku biyu Kamar Zan hantsulo sabida tashin hankali.
Lukman babban yaron Naseer da fitowarsa kenan Yana bud’e shagunan Naseer na nufa da Sauri.ina tambayarsa ko ya ganemin Nadeeya ko amsa gaisuwar da yakemin banyi ba.
Girgiza min Kai yayi Yana Bai ganta ba.
Ban tsaya ma Jin Mai yake cewa ba na Kara Hawa Sama Dan sai yanzu na tuna Nadeeya Bata iya saukowa sai dai a sauko da ita Dan balain tsoro ne da ita Dan Zahira ce ma take iya Hawa bene amma Nadeeya ko lekowa tayi ta kasa aguje take ja da baya Dan gani take zata iya fadowa Dan mmn Mannir har tsokaneta take ta ringa daukarta kamar zata jefota idan tazo.
Ina hawa sama na ware murya Ina cigaba da Kiran Nadeeya ya Ina duba kowane lungu da Sako nice har da duba karkashin kujera da gado.
Umma da Hindatu suna zaune a Inda na barsu ko gezau basuyi ba kamar ma basu San da hallita ta a wajen ba.
Zubewa na yi a gabansu Ina “Dan Allah Umma Baku ga Nadeeya ba wlh Ina Mata wanka Nan ta fito Palo Kuma Bata iya sauka kasa sai dai a d’auketa Dan Allah Baku ga Inda tayi ba”?
Ba Wanda ya kulani a cikinsu kamar ma bad’asu nake   magana ba hannu na Dora a kaina na fara zabga Sallati na Kara d’aukar hanyar waje a guje ko Humaira danake juyo kukanta daga d’aki ban bi ta kanta ba
A bakin kofa na ci Karo da Naseer da tunda ya fita massallaci Bai dawo gidan ba Dan yaje kasan layinmu adduar mutuwar wani bawan Allah daya rasu.
Ina ganinsa nasan shima lukman ya Gaya masa Banga Nadeeya ba
Kara tambayata yayi “Wai baa ga Nadeeya ba”?
Ban iya bashi amsa ba na cigaba da kuka Ina na shiga uku da Sauri Naga ya hau saman Benen batare da yabi ta kaina ba  nabi bayansa da Sauri……….
[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*
     *NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 17*
              D’akina ya shiga kansa tsaye Yana kwallawa Nadeeya Kira  ya fito ya duba koina yana “Wai kamarya Ba’a ga Nadeeya ba sai kace almara Taya ya daga yiwa yarinya wanka ta fito kice baki ganta ba”?
Wajensu Umma da har lokacin basu nuna sun San Mai ke faruwa ba ya nufa Yana “Umma Dan Allah bakiga Nadeeya ta fito daga d’akin Naeema ba?
“Toh ko Ni na saceta da zaka zo kana min tambaya”?
B’acin Rai ne yasa Naseer yace a Dan tsawace “Umma daga tambaya sai kice ko saceta kikayi wanan wane irin magana ne”
Tsaki da Bai shiryawa fitowarsa ba yayi ya wuce waje fuu Hajara kuwa ta girgiza Kai tana har dasu Tsaki yayi kyau”
Zuwa lokacin Ni nasan jinina ya hau sabida tashin hankali.
Daga farkon layinmu zuwa karshen layin mu Haka muka zaga muna kwallawa Nadeeya Kira Amma shiru.
Mmn Mannir da itama ta fito ita da yaranta tuni ta fasa fita suka hau tayamu Neman Nadeeya makotana suna da balain kirki Dan ba iya matansu ba har da mazajensu Haka suka hau tayamu neman Nadeeya Inda sukayi ta mamaki idan nace musu daga wanka ta fito na nemeta na rasa Kuma duk Wanda yasan Nadeeya yasan Bata iya saukowa daga Sama.
Kukan ma kasa wa nayi sai sallati nake har komawa nake gidan na shiga d’akina Naga ko zan ganta har zazzaga kayan wardrobe Dina nayi ko shigewa tayi Amma ba Nadeeya babu labarinta Humaira kuwa har ta gaji da kuka tayi shiru a bayan Zahira da itama ta hau kuka.
Sosai nake mamakin Umma da ta kasance kakar Nadeeya da Bata nuna ta damu da neman da muke wa Nadeeya ba hasali ma tea Dana dafa Suka zubo ita da Hindatu da kwai suka dauko gwangwnin Madara Dana Milo suna Shirin hada shayi su sha
Waje nake so na sake yi Amma na tsinci kaina da nufar wajensu Sabida daga murmushi danaga.umma na min yasa nasan tana da masaniyar Inda yata  take.
Agaban Umma naje na zub’e Ina “Umma Dan Allah na hadaki da Wanda ya halliceki ki gayamin Inda Nadeeya take Umma daga d’akina ta fito Kuma Kuna zaune anan ta fito daga d’akina Dan Allah Umma kimin komai idan ta Kama yau na hada kayana na bar gidanan wlh Zan hada Dan Allah ki dawomin da Nadeeya na tuba Umma Nadeeya bata Miki komai ba Ni na Miki Aunty Dan Allah Kuyimin Rai karku yiwa Yata komai”
Nace Ina k’ok’arin kamo hannun Hindatu
Adaidai lokacin da Naseer ya shigo da Sauri kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake
Turus yayi Agaban mu Yana yiwa Umma da Hindatu wani irin kallo da yaga kayan shayi a gabansu
Cikin wani irin murya ya fara magana Yana “Umma Anya ke Kika haifeni kuwa Umma Anya  Gaskiya Abba da Baba Suka gayamin da sukace ke Kika haifeni Umma ‘yata ce fa ta b’ata ake nemanta Umma jinina fa yata da ta kasance jika a gareki ita ake nema Umma Kika zauna ke da Wanan tsinaniyar zaku hada shayi ku Sha alamar ba Abunda ya shafeku Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma Dan da kina kaunata bazaki ringa min abinda kike min ba Zaki so farinciki na Umma mak’ota da masu wucewa ma suna tsyawa sabida su Tayani neman Yata amma ke kin zauna Zaki sha shayi wane irin kallo kike so a Miki Umma ga wayanda suka san ke Mahaifiyata ce Umma Koda baki hada jini Dani ba Bai Kamata ace mutum Mai Rai sukutum guda ya b’ata batare da kin nuna damuwarki ba Umma,Umma lamarinki ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro Umma insha Allahu Zan ga yata Kuma zan kawo karshen komai Dan Nagaji Umma”
Daga haka yayi ball da flask din gabansu ya shige daki ya canzo kayan jikinsa ya fito da Sauri hannunsa d’auke da mukullin motarsa da k’aramin passport din hoton Nadeeya da aka Mata lokacin da zaa Saka su a makaranta ya fice da sauri.
Ni kuwa na durk’ushe a wajen na cigaba da kuka na kasa yarda Wai Nadeeya ta b’ata yarinya da nayiwa wanka da hannuna ko wando babu.
Maganar da Umma keyi cikin huci yasa na tsayar da kukana Ina kallonta
“Yau ni Naseer ya ke d’agawa murya yake min ihu sabida yarsa ta Bata lailai Naseer yayi Nisa ba karamin asiriceshi wanan tsinananiyar tayi ba ba dai Dan Nadeeya kike wanan kukan ba ba Dan Nadeeya Naseer yamin ihu Ina mahaifiyarsa ba toh sai ku ganta nagani”
“Duk wannan Abun fa laifinki ne Hajara ke Kika bar yarinya nan ta zauna dashi har yanzu har ta juyar Masa da kwakwalwa ace yau sati biyu da auren mu ya kasa kallon Inda nake tsabar wanan kanjalalliyar ta asirice shi ki barwa Umma komai ta Miki maganin shegiya”
Ta ce tana jefomin harara
Umma kuwa tayi wani irin murmushi ta mik’e tana k’ok’arin shiga daki.
Da Sauri na rik’e kafarta na saki ihu Ina ta taimaka ta fitomin da yata wlh idan Naseer ne Zan rabu dashi a yau
Tureni tayi ta shige daki.
Zahira dake lab’e a bayan kofar dakina ta fito ganin Ina ta rusa kuka Ina Kiran sunan Allah Dana Nadeeya ba irin tunanin da ba darsu a Raina ba Kar dai su Umma kashemin Nadeeya sukayi.
Zahira Humaira ta mik’o min dake ta tsalla kuka daga ita har Minal ba Mai Kaya a jikinsu sai Zahira karbar Humaira nayi na sa Mata no-no a baki take ta karba na umarci Zahira ta d’auko wa Minal Kaya ita da Humaira.
Tana tashi Mmn Mannir ta shigo ita da wasu makotana wasu ma ban San su ba duk sun zo min jaje sai Kara tambayata suke Taya Nadeeya ta b’ata ban ma iya musu magana ba sai bani baki suke suna kwantar min da hankali akan za’a ganta an Kai cigiya gidajen radio har da tv dayake Naseer nada Abun hannu duk an raba musu passport din Nadeeya.
Ni dai har lokacin sai Naga kamar zanga Nadeeya ta fito daga d’aki.
Mmn Mannir kuwa Humaira ta karba daga hannuna ta goyata Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na daura alwala na fito na hau Kan Sallaya na tadda Sallah karatun Sallah ma da k’arfi na ringayi Ina kuka a Sujadda kuwa Haka na ringa rokon Allah ya Kare min yata a duk Inda take ta dawo gareni cikin koshin lafiya Ni nasan su Umma ne suka daukemin ‘ya har tsawon wane lokacin Zan ringa irin wanan rayuwa a yau na gaji wlh na gaji ya zama Dole na dau mataki.
Ina iddarwa na  fito nayi k’ofar gida Inda duk makotana suke tsaye duk Yan layin ban gansu ba sun tafi neman Nadeeya daidai da masu shaguna duk basu bud’e ba sabida mutuncinsu Amma ace uwar mijina ita Tana daka ko a jikinta.
Waje daya na samu na zauna Ina ta tunanin ganin ta Inda zanga Nadeeya ta b’ullo addua kuwa na fili Dana zuci Haka na ringa Yi.
Lukman da danladi Mai Kai su makaranta sun dawo gidan yafi a kirga Akan suji ko an ga Nadeeya Amma shiru ba a ganta ba ahaka har Yamma tayi babu Naseer babu dalilinsa.
Kuka nake sosai Ina rokon Allah ya karemin Nadeeya har yanzu na kasa yarda Wai daga fitowa Nadeeya wanka an nemeta an rasa.
Naseer kuwa kudi ya saki sosai ya bada cigiyar Nadeeya gidajen radio da unguwa unguwa har Inda baa yi tunanin zuwa ba Haka aka ringa neman Nadeeya da passport din hotonta Sallah ma Naseer ba a nutse  yake Yi ba har kunyar ya cewa mutane daga wanka Nadeeya ta fito aka nemeta aka rasa sai kace wata Kaya.
Ahaka suka danganta neman Nadeeya kusufa kusufa lungu da sako kwaryar Kano baa ganta ba wajen Magriba Naseer da wasu Yan unguwarsu suka tsayar da motarsu Dan suyi sallah a wani unguwa kawo dayake unguwar Bata fiye cika ba a wanan lokacin Kamar daji ne sai a lokacin ake yankar fili ake ginawa.
Daya daga cikinsu ne ya nausa wajen daji dajin da yayi fitsari ya fito yayi alwala daga nesa dashi ya hango wani katon Rafi  ruwa nata Dan gudu gashi wawakeke wata Yar karamar yarinya ta bada baya tana Dan jefa abu a ciki ba Kaya a jikinta.
Murza idonsa yayi ya sake murzawa  idonsa duk da Bai ga fuskar yarinya ba sai yake ganin kamar Nadeeya Amma Dan ya gasgata zargin da yake ahaka ya ringa matsawa kusa da yarinya kafin a hankali yace “Nadeeya”
A hankali Nadeeya ta juyo idonta yayi jawur hancinta duk Majina kana gani kasan taci kuka ta gode Allah wajen a ruwan yake ma da alama baa fiye wucewa ta wajen ba
Ihu ya saka ganin Nadeeya na ganinsa ta fara k’ok’arin mik’ewa tana mik’a Masa hannu Dan Dama Mai kawo Mata d’auki take nema shi kuwa cikin zafin nama ya Isa wajenta ya tarota da Sauri Dan kiris ya rage ta fada ciki.
Wani irin ajiyar zuciya Nadeeya ta ringa saukewa tayi lamo a jikinsa jikinta yayi zafi zau.
Shima Salisun kamkameta yayi yayi wajen da suka Parker motarsu da har Naseer ya iddar da sallah ya gaji da jiransa.
Kamar a mafarki ya hango ya fito da Nadeeya rungume a kirjinsa Bai San lokacin da ya nufesu da Sauri Yana “Mai ya sameta? A Ina ka ganta”?
Yace Yana karbe Nadeeya daga hannunsa ya hau tattab’a jikinta Inda Nadeeya tana ganin Abbanta ta fashe da kuka tana Kara kamkame shi.
Naseer kamar ya maida ta cikinsa ya rungumeta Yana shafa jikinta
Salisu kuwa ya hau bashi labarin yanda ya ganta ya Kuma ringa Al ajabin yanda Nadeeya ta iya zuwa tunda Goron dutse  zuwa Kawo idan ba mutum ne ya kawo ta Nan ba Taya zaayi tazo Nan
Naseer Bai iya Jan motar ba sai salisu ne yaja motar shi kuwa ya zauna daga bayan motar da dayan makocinsa suna ta mamakin Inda suka tsinto Nadeeya Naseer kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin kukan Nadeeya a kirjinsa Yana Jin wani irin suya a kirjinsa shi ba yaro bane yasan d’auke Nadeeya akayi Kuma ba wasu ne.suka d’auke.ta ba sai Mahaifiyarsa tunda yasan wacece ita.
Baiyi magana ba har suka iso gidan da mutane ke cike Suna jajanta b’atan Nadeeya.
Naeema kuwa taci kuka ta gode Allah tayi zaman dirshan a kasa Ana ta Bata baki
Tsayuwar motarsu yasa ta mik’e da sauri Inda Naseer shi.kuma ya bud’e motar ya fito rungume da Nadeeya
Mutane na ganin ta suka hau hamdala suna “Alhamdulillah Anga Nadeeya a Ina aka ganta”?
Sosai mutane Suka nuna farincikinsu da ganinta suka hau tambaya inda aka ganta.
Naeema kuwa da Sauri ta ture mutane ta karbi Nadeeya daga hannun Naseer tana sauke wani irin ajiyar zuciya.
Ta rungume Nadeeya Gam tana hamdala
Hajara da Hindatu ihun Murnar anga  Nadeeya ne yasa Suka fito daga d’akin da Sauri suka lek’o ta saman bene cikin tsananin mamaki Dan bakin ruwa Suka kaita Kuma suna da tabbacin fad’awa zatayi ta mutu Amma ga mamakinsu Wai an ganta Kuma su sun San Inda suka kaita sai anyi dagaske xaa San wajen.
Wani irin ihu Hajara ta saka ta sauko daga Kan benen ta zub’e a kasa ta hau buburwa ta cire zaninta ta Yar ya rage daga ita sai Dan skirt sai kuka take Tana zubawa kanta kasa.
Mamaki ne ya rufe mutane suna kallonta tare da mamakin Mai ya kawo ihun nata ita da zatayi farinciki anga Nadeeya (wlh page dinan babu fiction ko daya a gaske Haka matar Nan tayi Dan bakin ciki an ga Nadeeya)
Ni kuwa ko kallonta banyi ba na rungume yata na haye sama
Naseer kuwa kamar kasa ta bud’e ya shige Dan kunyar yanda take ihu tana watsawa kanta kasa Wai Nan da Sunan Mahaifiyarsa ce wato gawan Nadeeya taso gani
Mutane kuwa da basu San Mai ke faruwa ba hakuri Suka hau bata suna ba kuka zatayi ba ta Godewa Allah da aka ga Nadeeya ba Kuma abinda ya sameta.
Naseer shima da Sauri ya hau saman bene Yana Jin kamar kirjinsa ya fad’o
Sai Hindatu ce ta sauko ta dauko mata zaninta ta mikar da ita suka koma ciki.
Da yawa ta basu mamakin abinda tayi sabida tunda aka fara neman Nadeeya Bata lek’o ba Amma abin mamaki ana ganinta ta fito tana ihun kuka Mai hakan ke nufi.
Wasu Kuma basu kawo komai ba sun dauka kukan farinciki take da ganin Nadeeya.
Ni kuwa Ina shiga ciki d’akina na wuce da Nadeeya na kullo k’ofar na kwantar da ita na fara duba jikinta Naga babu abinda ya sameta sai kafafunta dai da suka balain suntume sukayi budu bud’ da kasa
Sai jikinta da yayi zafi sosai.
Bana rabo da ruwan zafi hakane yasa na hada ruwa Mai balain zafi na wanke Nadeeya tas na Kara zuba wani na hau dadanna Mata kafa sai danaga ya fara Sab’ewa sanan na dauko robbb na shafe Mata jikinta dadin wankar yasa take bacci ya d’auke ta tana ta sauke ajiyar zuciya Ni kuwa na zuba Mata Ido hawaye na sauko min ko a Ina su Naseer suka ganta.
Naseer kuwa a Palo ya zauna ya rik’e kansa sabida azabar ciwo da tunanin halin mahaifiyarsa ahaka su Hajara suka hawo sama tana ta kuka
Suna dab da wuce Naseer
Naseer ya dago Yana “Umma ba Haka Kika so ba ko?kin so ace gawar Nadeeya na shigo dashi gidanan Umma Mai na Miki Haka Dan Allah Dan annabi Umma Mai na Miki Dan Allah Dan annabi ki gayamin na nemi yafiyarki Umma”
Naseer yace Yana durk’usawa Akan gwiwar sa kukan dayake  d’annewa  ya kwace Masa.
Hajaran Bata ce komai ba ta Shige d’akinta tana Jin kanta na ciwo sabida a rayuwarta Bata da burin daya wuce taga Naeema ckin bakin ciki  a Rayuwa tunda ta kasa rabata da Naseer gwara ta Taba abinda tasan sune ranta Dan taso Zahira ta d’auke Dan ta lura itace Mafi soyuwa a wajen Naeema sai Zahira bata futo ba Nadeeya ta fito sai gashi cikin sauki wai har anga Nadeeya bama ta mutu ba da ranta lailai Naeema tabbas akwai abinda ta taka da Bata iya cin Galaba Akan ta.
Har wani zazzabin bakin ciki tayi
Naseer shima halin mahaifiyarsa da matsanacin tunani sai daya saka Masa zazzabi
Ni kuwa Ina daga d’akina Ina Jin duk abinda Naseer ke cewa Umma kukan da Naseer keyi ya tab’ani sosai hakane yasa na Sha alwashin kawo karshen wanan matsalar da muke ciki.
A Daren ranar duk mu ukun babu wand yayi baccin kirki Dan Naseer zazzabi halin mahaifiyarsa ya hau Yi ko shigowa d’akin baiyi ba a palon yayi kwanciyarsa ko sallah daya Saba yi daddare  ma a ranar baiyi ba Ni Kuma hanyar da zata bille Dani ya hanani bacci ita Kuma Umma bakin ciki. Duk Abubuwan da takemin Ina tsallakewa gashi shugabarsu tayi fushi tace zata kwace komai daga hannunta tunda Naeema tana neman fin karfinta.
Washegari Nadeeya ta tashi fes ba wanan kumburin ahaka na had’asu na musu wanka na rufo kofata na nufi kitchen Dan na Dora Mana abinci banyi tunanin shiryasu su tafi makaranta ba Naseer ma ban ganshi a palon ba Dan tunda ya fice da asuba bana Jin ya sake dawowa sosai naji Ina tausayinsa.
Daga Umma har Hindatu banji motsinsu ba har na Gama Abunda nake na ajiye musu nasu a Palo na Kai Mana namu daki Dana Naseer.
Dan nayi alkawarin har na cimma burina bazan Kara Shiga dakinsu ba.
A faranti daya muka ci Abinci da yayana Sansu na ratsani Ina kwarara musu addua a Zuciyata.
A hankali Kuma Ina tambayar Nadeeya yanda ta ba ce bamu ganta  ba Bata iya min magana ba Dan tana da Dan nauyin baki.
Har Minal ta Dan fita baki.
Wajen karfe goma na safe na fito daga d’akina bayan na kulle k’ofar dakina har lokacin Naseer Bai dawo ba Kuma banji motsinsu Umma ba Naseer nafi damuwa nasan halin da yake ciki ba Umma ba hakane yasa nayi waje.
Ina su lukman suka hau gaisheni suna tambayar Nadeeya Ni kuwa nace Tana Nan lafiya Lau daga Haka na wuce gidan mmn Mannir Dan zuwa yanzu banida dai Sama da ita bayan Naseer dan naji Dadin yanda ta nunamin damuwarta jiya tamkar yar uwa ta Haka nake ganinta.
Banyi tunanin Zan sameta a gida ba Dan na d’auka taje makaranta  amma Ina zuwa na sameta taji dadin ganina anan muka gaisa taso ta tada maganar abinda ya faru tsakaninta da Umma  har ta Dan sakomin zancen tana zargin ita ta d’au Nadeeya Ni kuwa na Kau da zancen na hau Gaya Mata abinda ke tafe dani da taimakon danake so tamin Dan Nagaji da irin wanan rayuwar da muke nida yayana Kuma idan na biyewa Naseer Haka zamuyi ta zama muna cutuwa.
Sai data Yi Dan Jim kafin tace zata taimaka min ta hau tsaramin yanda zamuyi take naji dadin shawararta Inda ta tsaramin duk yanda zamuyi Amma fa tana tausayin Naseer.
Murmushi kawai na nata Dan Mai daki shi yasan Inda yake Masa yoyo.
Sallama na Mata akan Zan dawo anjima
Ina koma wa gida Naga Naseer ya dawo idonsa ya fada sosai yayi wani sanyi kalau kamar mara lafiya Bai cemin daga Ina nake ba na Shiga d’aki na dauko masa abincinsa Ina k’ok’arin ajiyew yace min azumi yake bance komai ba na dauke abincin na mayar kitchen na fara k’ok’arin Dora Mana abinci Rana Ina cikin girkin Hindatu ta shigo ta ajiye kwanuka tare da dalla min harara sai anan nasan Ashe ma suna Nan
Ina gamawa na Kara shigewa daki a Inda Naga Naseer har yayi wanka zai fita.
Yacemin bazai dawo da wuri ba fatan dawowa lafiya kawai na masa Yana fita na dauko katon akwatina na hada Mana kayanmu nida Yara sai danaga ba kowa a palon Naja akwatin na Kai gidan mmn Mannir Kuma cikin ikon Allah babu Wanda ya ganmu.
Kamar Naseer yasan Mai nake shiryawa tunda ga ranar Bai Kara fita ba.
Nima sai neman hanya nake kwana biyar da faruwar.haka Umma ta fito palon Wanda tunda aka ga Nadeeya ta shige daki ban Kara ganinta ba sai ranar Dan Hindatu kawai nake ganin tana Shigar musu da abinci.
Wani irin kallo take min Ni kuwa na dauke kaina Zan iya cewa wnan shine Karo na farko a rayuwata da naki gaisheta.
Girgiza Kai tayi ta had’e Rai ta zauna a Palo Naseer kuwa Yana ganin ta fito ya mik’e ya fita.
A ranar wani kallo Umma take jefamin na tsana Kamar zata kamoni ta yankani Ni kuwa Ina Gama ayyukana na shige daki.
Washegari jikina duk ba kwari na shirya su Zahira suka tafi makaranta
Wajen Sha daya Naseer na fita na goya Humaira na karewa d’akina kallo hawaye na zubomin
Na ajiye wa Naseer wasika a karkashin gado na fito da ga d’akin
Banga kowa a palon ba Ina fita na amshi kudi wajen lukman a cikin kudin Naseer wajen Dubu goma wanan lokacin.
Na dau hanyar makarantarsu Zahira Ina zuwa nacewa mallamarsu inasan zamuyi tafiya ne an Mana rasuwa take ta Kira su Zahira suna zuwa na rik’e hannunsu muka hau tafiya sai da muka je karshen layin na had’u da mmn Mannir dake ta jirana da akwatin kayanmu…..
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*
     *NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 18*
          Bansan hawaye nake ba sai da mmn Mannir da itama Naga jikinta duk yabi yayi sanyi tace “Anya Naeema kina ganin wanan matakin shi ya dace ki d’auka?Anya kina ganin kinyiw Naseer adalci kuwa?
Ban iya ce Mata komai ba Dan matsawar nayi magana kukan danake dannewa zai iya k’wacemin Agaban yayana Zahira tana da wayo tunda muka fito daga makaranta take min tambayoyi Ina zamuje yanzu ma sai kallona take.
Mmn Mannir itama sosai Naga idonta ya kad’a yayi ja Ina biye Mata Haka zamuyi ta tsayuwar  hakane yasa na Ciri hannu na fara k’ok’arin tsayar Mana da taxi Dan lokacin ba adaidaita sahu.
Dak’yar muka samu Wanda ba kowa a ciki na sunkuyar da kaina nace ya kaimu tasha.
Sai daya fito ya saka Mana kayanmu na bud’e bayan na saka su Minal Ina k’ok’arin kamo hannun Zahira ta Kara cemin “Umma Ina zamuje Dan Allah idan tafiya zamuyi mu tafi da Abba Kar shima Mama ta ringa dukansa dayake mama suke ce Mata”?
Hada Ido mukayi da mmn Mannir da har hawaye ya fara zubo Mata tana daukewa sabida Kar a gani.
Ni kuwa na saka Zahira a cikin motar da k’arfi Dan banasan magana kukan danake dannewa ya fito.
Ina zaunar da ita na shige na rufo k’ofar Ina k’ok’arin yiwa Mmn Mannir godiya Naga ta bud’e gaban motar ta hau.
Ba Wanda yayi magana a cikin mu har muka Isa Tasha muka sauka na biya Mai taxi bayan ya sauke Mana kayanmu
Mmn Mannir ce ta shigemin gaba wajen Nemo motar garinmu aka cajemu na biya sai da su Zahira suka hau sanan na juyo na rik’e hannun mmn Mannir Ina “Nagode da alkhairinki a gareni bazan manta dake ba”
Hawaye ne ya hau zubo Mata ta damke hannuna tana “Naeema Dan kin dage ne Zaki tafi da kin hakura kin zauna wuya Bata kissa watarana sai Labari da Zaki bani hadin Kai wlh zamuyi maganinta ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga bakya Nan kin Kuma tafi da duka yaran wlh Naeema bazaiji dadi ba”
“Bazaki gane ba Mmn Mannir bazaki gane Hatsarin Zama na da Naseer ba Mmn Mannir da iya Ni kadai ummaa zata tab’a kila na iya jurewa da iya Ni kadai zata ganawa azaba kila na iya daurewa ko Dan sabida yarana Amma me Umma yanzu ta bar kaina ta koma Kan yayana Wanda duk abinan sabida su naki tafiya tuntuni Akan me Zan cigaba da zama yau idan Allah ya karemin Nadeeya gobe nasan salon da zata zomin dashi wlh Nagaji mmn Mannir ko baccin kirki bana iya yi na rasa Mai na Mata laifine Dan na auri danta yau kina ganin da iyayena suna rayye zata min abinda takemin banida kowa sai Allah sai Naseer toh shima Naseer din tace sai mun rabu toh na rabu dashi rabuwar mu bazai saka na kasa cigaba da rayuwa ba na barwa Naseer wasika Akan ya sakeni bazan iya ba Zan koma garinmu ko wanke wanke na ringa Yi Ina ciyar da yarana Dan bazan tab’a barin yarana da Naseer mahaifiyarsa ta kasheminsu ba Wlh mmn Mannir banji Ina nadamar matakin Dana dauka ba wlh nesa ma danayi daga gidan bakiji iskar danake shak’a Mai kyau ba nidai kawai ki Tayani da Addu’a watarana insha Allahu zamu sake had’uwa”
Mmn Mannir kasa magana tayi sabida kukan da take dak’yar na kwace hannuna na Shiga motar Ina shiga muka samu Karin passenger daya Yana shiga motar mu ta d’au hanya
Haka kawai naji wani Abu ya tsayamin a mak’oshi tambayar da Zahira ta Kara jefomin Akan tafiya zamuyi mu bar abbansu yasa na kifa kaina akan hannuna na fara kukan danake ta dannewa tun lokacin Dana shirya rabuwa da Naseer.
Allah yasan ba Haka naso ba Dan mijina Yana Sona Yana Kuma iya kokarinsa Dan yaga ya kyautata Min nida yayana Amma mahaifiyarsa ta daka tsalle tace sai mun rabu bansan Umma tsanar da takemin har ya tashi daga kaina zata iya tab’a min Yaya ba
 gaba gaba kila wuka zata d’auko ta caka musu ni har mamakin halinta nake Dan wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ko ragon layya a da idan zaa yanka tausayi yake bani sai da akacemin babu kyau na daure na daina Dan bana ma tsayawa Inda ake yanka d’abba Amma Wai Umma ita ce take zuba wanann zalincin har Yara kanana Bata Bari ba idan dai har zata iya yiwa Nadeeya Haka na tabbata ma Naseer Bai tsira a wajenta ba.
Addua kawai nake Allah yasa  na Gane hanyar garinmu Dan shekaru dayawa rabona da can toh waye ma nawa acan ne inama Ina zuwa Naga Yaya Aliyu yazo shima Yana nemana inama na samu wasu suzo suce sune dangina inama na tambaya Mahafina ko Mahaifiyata.wani nasu da yanzu na samu wajen zuwa Amma ba komai Haka zanje ko makotammu na da idan na samu na tambayesu game da gidan da mahaifina ya Bari dan nasan kila yana hannun Mai unguwa idan Allah yasa basu siyar Mana ba sun ajiye Mana kayanmu sai na zauna nida yarana na nemi sana’a.
Biscuit da ruwa na siyawa su  Nadeeya da sai Dana tashe su daga bacci.
Zahira ce kawai batayi bacci ba ta Yi jigum da biscuit dinta a hannu ta kasa ci Dan sai data karamin tambaya na daka Mata tsawa akan ta kyalleni naji da iya damuwar da nake ciki.
Sai da mukayi nisa da Kano Naji wani irin tausayin Naseer ya rufeni ko ya zaiji waya sani ma ko har yaje gidan yaga wasikar abinda nakejin Kuma nadamarsa Bai wuce ce Masa danayi na tafi garin kaduna ba Dan nasan kila ya tafi can neman mu alhalin ba can mukayi ba.
Ahaka nayi lamo Ina kallon Motocin dake ta tsere a titi Ni nasan Umma sai ta kusa taka rawa sabida murnar tafiya ta.
Naseer kuwa tunda ya bar gida yake Jinsa kamar Mai zazzabi ahaka ya daure yayi ta zama a katon shagonsa daya bud’e dake sabon gari dake d’auke da kayan electronic Dan Naseer Kam fanin arzki sai daya ce alhamdulillah dan shagunansa zasuyi uku a sabon gari shidda kenan har Dana kofar gidansa.
Yanzu Haka ma Yana Gina wani katon gida a kasan layinsu ko Naeema Bai gayawa da ace mahaifiyarsa Bata Sako shi a gaba ba da ace mahaifiyarsa ta rungumi Naeema a matsayin matar danta da ya ce shi kam ya samu rabon duniya sai dai Kuma na lahira.
Sam yaji zaman shagon ya gundureshi ba Kuma yajin dadin jkinsa hakane  yasa duk da yawan mutane dake zuwa siyayya ya Sallame su akan bayajin dadin ya rufe shago ya nufi gida.
Ganin lokacn tashinsu Zahira ya kusa yasa ya tsaya a makarantar su Dan saura Yan mintina su tashi
Kansa tsaye ya shiga cikin makarantar ya nufi office din headmistress din tana ganinsa ta hau gaishe shi tana Masa gaisuwar rasuwan da aka musu
Cikin mamaki Naseer yace Bai Gane ba
Itama headmistress din cikin mamaki ta Kora Masa zuwan Naeema makaranta da Sunan an musu Rasuwa ta tafi da su Zahira.
“Kin tabbata Mahaifiyarsu ce tazo ta d’auke su”?
“Itace Mana Alhaji Naseer yanzu ma wajen awa biyu kenan”
Naseer Bai tsaya jiran sauran bayananta ba ya fita da Sauri gabansa na fad’uwa Mai ke faruwa Naeema tazo ta dauki su Zahira lokacin tashi baiyi ba ko Ummansa ce ta Kara musu wani Abu
Da ikon Allah ya Kara sa gida ko parking Mai kyau baiyi ba ya hau sama g da balain sauri.
Naeema ya hau kwallawa Kira Yana kiran sunansu Zahira Haka kawai gabansa ya tsinke ya Fadi daya shiga d’akin naeema.ya duba koina Bai ganta ba fitowa yayi da Sauri.ya fada Kitchen nan ma Bata nan.
Da sauri ya fito ya Kara sauka kasa.
Yana sauka ya hau tambayarsu lukman ko sunga Naeema da Zahira.
Dukansu girgiza Masa Kai sukayi sai Mai Zama a dayan shagon ne yace yaga ta sauko ita da Minal da Humaira a goye a baya tayi hanyar titi.
Naseer Bai tsaya ya Gama Jinsa ba ya da dan gudu ya nufi gidan mmn Mannir daya San Nan kawai take zuwa Sosai yaji Yana tsoron darsa tunani a Ransa akan ko wani abun ne ya faru addua kawai yake.Allah yasa tana gidan mmn Mannir.
Tsabar tashin hankali Bai tsaya Sallama daga waje ba ya fada cikin gidan da Sallama a bakinsa
Mmn Mannir dake zaune ta buga tagumi tunda ta dawo ta mik’e da Sauri tana sallati ganin Naseer a rude yasa jikinta ya hau rawa cikin jarumta tace.masa.lafiya
Naseer da Sauri ya hau tambayarta inda take ita da Yara.
Ita kuwa tace masa Bata ganta ba sosai taji wani irinn tausayinsa daya zaro Ido Yana sallati.
Ya juya da Sauri ya bar gidan
Sosai hankalinsa ya tashi   ya koma gidan a hargitse
Yana Kara kwallawa Naeema Kira Dan gani yake.kamar Tana gidan..
Sai a lokacin tunanin shiga d’akinsu Umma ya Fado Masa.
Da Sauri ya fada d’akin suka dago  suna kallonsa
“Umma Mai Kika yiwa Naeema Dan Allah Banga Naeema ba Banga yarana ba Umma Mai Kika musu Dan Allah ki gayamin kimin komai Umma Banda rabani dasu”
Wani irin kallo umma.ta hau yi.masa Hindatu kuwa ta fara zuba Mai harara cikin kishi a ranta tana ayyana Allah yasa ma Naeema ta mutu
Umma kuwa taja Tsaki ta Kau da kanta.
Fitowa ya Kara Yi daga d’akin Yana sallati
Ya Kara Shiga d’akin Naeema tsabar rudewar da yayi ya hau daddaga Kaya ahaka ya d’ago pillow har zai mayar ya Ajiye yaga farar takarda
Baisan lokacin daya dauka ba Yana bud’ewa numfashinsa ya fara barazanar d’aukewa
“Kafin kaga wasikar Nan munyi nisa Naseer Kayi hakuri da matakin da na dauka Naseer nagaji da ace Umma iya Ni takewa Zan iya jurewa Amma yanzu ta fara tab’a min. Yaya daga ni har Kai munsan ita ta d’auke Nadeeya duk sabida kiyayyar da takemin na rasa Mai na Mata idan bamu rabu ba Naseer watarana zaka rasani ko ka rasa yayanka Wanda nasan hakan sai yafi maka ciwo akan dai rabuwar mu banida kowa sai Allah sai Kai Amma Umma ta dage sai mun rabu na dauka auren data saka kayi zai saka na samu sassauci daga wajenta Amma bansamu sassauci ba sai Karin azaba hakane yasa na yanke guduwa da yayana muje garin kaduna ko Allah zai kawo Mai taimaka Mana rabuwar mu sai yafiyemin alheri Naseer kayiwa Umma biyaya ngd da alherinka a gareni dafatn bazaka…..
Wani irin sallati Naseer ya doka cikin fitar hayyaci Bai ma iya karasa.karantawa ba ya fita aguje ya nufi d’akin Hajara takarda rik’e a hannunsa Yana “Umma shikenan kin kasheni Umma Naeema ta gudu ta barni ta tafi da yarana sabida azabar da kikee gana Mata Umma kalli takardar Nan kiga mai tace Umma Naeema ta shiga duniya da yayana innalillahi wa Inna ilaihi rajiun”
Hajara duk da batayi karatu ba karbar takarda tayi ta mik’e zaune Dan Dama a kwance take “Mai kace Kara maimaita min naji kace Naeema ta gudu da Yara”?
Umma Naeema ta gudu da Zahira da Nadeeya da Minal da Humaira Umma tace ta gaji da azabar da kike gana Mata Umma Mai na Miki kika tarwatsa.min rayuwa? Mai na Miki kika rabani da farincikina”?Umma Naeema fa Bata da kowa sai Ni Umma Mai yasa kikemin Haka idan wani Abu mahaifina ya Miki kike San ki dau fansar hakan akaina ki gayamin na nemi yafiyarki Umma uwa da tausayi aka santa umma uwa Bata cutar da dan data Haifa Umma ban miki komai ba kina ta cutar Dani Ina Miki biyayya daidai gwargwado Naeema tana Miki bansan Mai yasa Kika dage sai kin rabamu ba gashi dai ta tafi min da yara har su hud’u”
“Rufemin baki shasha lusari Kai yanzu akan mace kake kuka ka dagawa kanka hankali Haka?Kai yanzu Sabida Naeema ta rabu da Kai kake wanan surutan?anya Naseeru Haka yarinya Nan ta barka?Naeema kadai ce mace a  Duniya ko sai akace ma Dan ta rabu da Kai rayuwarka tsayawa zatayi? Karka manta fa kana da kudi kana da damar da zaka auri duk kalar macen da kakeso ta kuma Haifa maka maza”
“Ni kuma Mai matsayina a wajensa kenan da kike cewa zai auri wacce Ransa keso”?
Hindatu tace tana jifan Hajara da harara
“Ga Hindatu Nan dame Naeema ta fita Naseeru”?
“Ya kake Abu kamar ba Ni na Haifeka ba”?
Naseer kallon Hajara kawai yake hawaye na zubo Masa shi kadai yasan halin da yake ciki shi kadai yasan Mai yakeji a zuciyarsa.
Juyawa yayi a hankali ya fice daga d’akin Yana dafa bango Dan sosai yake Jin jiri na neman kayar dashi
Yana fita Hajara ta hau rawar murna rabonta dataji ta a farinciki Haka har ta manta gaskiya tafiyar Naeema da yaran ya balain faranta mata take ta fara addua Allah yasa Naeema ta lula duniya Tama hadu da ajalinta ita da yaran Dan batasan Nasser ma ya kalli wani Abu da zai tuna Masa Naeema.
Palon ta fito tana washe baki ganin Bata ga Naseer a palon ba  yasa ta zauna a kujera palon tana zai Gama koke kokensa ya gama ne.
Zamanta da Yan mintina Naseer ya fito daga d’akin Idonsa ya kad’a yayi jawur.hannunsa rik’e da mukullin mota yayi hanyar waje.
“Ina zakaje”?
Ko kallonta baiyi ba ya fice waje.
Gidan mmn Mannir ya Kara komawa da takardar a hannunsa Dan gani yake kila tana da masaniyar Inda Naeeema taje
Yana k’ok’arin Sallama mmn Mannir ta fito cikin tashin hankali ya Mik’a Mata takarda Yana
“Dan Allah Mmn Mannir idan kinsan wajen Wanda Naeema taje a kaduna ki gaya min nasan bazata ki Gaya miki ba sai dai kawia ki boyemin Dan darajar Allah ki gayamin idan kinsan Inda zata a kaduna ki taimakamin sabida kananan yaran data tafi dasu Naeema kanta Bata gama mallakar hankalinta ba ba kuma ta da kowa babu Kuma Wanda ta sani karki boyemin Dan Allah idan kin sani ki gayamin”?
Sosai ya kashewa mmn Mannir jiki bare data ga Yana ta hawaye
Tayi wa Naeema alkawarin bazata gayawa kowa ba Amma a yanzu Anya zata iya cika alkawarin data daukar Mata bayan taga halin da Naseer yake ciki
“Dan Allah kigayamin mmn Mannir Kar ta  fada hannun mugayen mutane”?
“Naseer a gaskiya Mahaifiyarka ta takurawa Naeema Mahaifiyarka tana cin zalinta sabida tana ganin Bata da kowa mai Naeema ta Mata Haka data tsaneta nidai bansan Inda Naeema taje ba ta dai cemin zata gudu Amma bansan dgaske ta gudun ba sai yanzu da kazo kana tambayata Amma a gaskiya bansan Inda taje ba da nasani Zan Gaya maka”
Mmn Mannir tace tare da kau da kanta data tuna girman Alkawarin data daukarwa Naeema
Naseer cije lebb’ensa yayi batare da sake cewa komai ba ya tafi.
Motarsa ya bud’e ya Shiga ya zauna ya rufe Ido yana tunanin ta Inda zai fara neman Naeema wa ta sani a kaduna da zata tafi wajen wa zataje ?Mai yasa Naeema zata Masa haka ta gudar Masa da Yaya shi akaran kansa akwai abinda yake tsara musu Gaya Mata ne kawai baiyi ba Dan ya Kara shirya su gudu zuwa wani garin na Dan lokaci kafin suga ko  Umma zata hakura ta kyallesu.
Amma sai gashi Naeema.ta gudu da yayansa tashin hankalinsa Bai wuce Ina zata je ba wajen wa Kuma zata sauka Bai San har Naeema tayi wayo yin wanan tunanin ba Naeema daya sani tana da tsoro Mai yasa zata Masa Haka yanzu idan sun Isa kaduna Ina xasu kwana ita da yaran tunani iri iri Haka ya ringa yi  kirjinsa na Masa nauyi.
Take zazzabi Mai zafi ya rufeshi
Sai su lukman ne Suka Gane bashida lafiya Suka Kira likita a kasan layinsu yazo ya duba Naseer ya mishi  allura ya Sha magani.
Dak’yar ya koma cikin gida Inda Yana Hawa sama.yaga Umma taci kwalliya ita da Hindatu fuskarsu kamar gonar auduga  sai cin kaza suke Bai kallesu ba ya Shiga d’aki a ranar ko runtsawa baiyi ba washegari da sassafe ya dau hanyar kaduna.
A takaice sai daya kwana uku a kaduna Yana bulayi duk da Bai San takaimaimai Inda zai ga su Naeema ba a cikin kwana uku ya zama kamar mahaukaci Dan ko wanka baya yi balle ya  samu cikakken bacci.
A ranar daya kwana biyar a kaduna Yana yawon nemansu Naeema Tasha tasha.unguwa unguwa ya yanke zuwa garin su Naeema Dan Haka kawai yaji kuma zuciyarsa ta karkata can.
Naeema
Duk da sauye sauyen da aka samu a garin na cigaba hakan Bai Hana ni Gane unguwarmu ba rabona da garin tun rasuwar mahaifina da Mahaifiyata  kaina tsaye gidan Mai unguwa na nufa da su Zahira da har kuka suka ringa min da Sunan sun gaji.
Sosai na ringa adduoi a Raina Akan Allah yasa Kar Mai unguwa ya canjamin sabida Yana ganin iyayena sun rasu.
Ga mamakina muna Isa ya.gane Ni Suka Kuma Mana tarb’a Mai kyau Inda naji wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa Wanda rabona ma danaji Haka Zan iya cewa tun kafin na auri Naseer.
Sai da muka huta daddare ya aika a kirani Inda ya hau tambayata  mahaifinsu Zahira dafatan lafiya yagani da Yara.
Kuka na fashe dashi na tsinci kaina da karyar Naseer s’akina yayi
Sosai ya nunamin baiji dadin abinda ya faru ba ya min nasiha akan na rungumi kaddara zasu rik’eni tunda banida kowa sun Kuma Yi zaman mutunci da mahaifina Amma fa sai.na mayar dasu Zahira Dan bazai  iya rikesu ba baima Kamata na taho da yaran gabadaya ba.
Anan hankalina ya tashi danaji abinda yace kuka na fara yi.masa inaso na Gaya masa gaskiya abinda ke faruwa bakina yamin nauyi Kamar an dinke inaji Ina gani yace na tashi na tafi idan an kwana biyu zai saka a cikin yaransa wani ya rakani na mayarwa Naseer yayansa.
Sosai hankalina ya tashi na hau nazarin abin yi Inda a karshe na yanke kafin ya karamin magana gwara na Gaya masa gaskiya ko da zai iya taimakamin tunda Naga gidanmu na Nan a kulle Dan har maganar gidan yamin akan mallakina ne gwara na gyara na zauna a ciki nida yarana Dan canjin hannuna na ringa juyawa.
Ranar da muka cika kwana biyar a garin washegari.na karbi mukulin gidan nace Zan je na Dan gyara.
Na tafi da yarana gabadaya shigata gidan ya hau fad’omin da irin Rayuwar danayi da.iyayena cikin so da Kauna da kwanciyar hankali.
Haka kawai na samu waje na zauna na hau bawa yayana labarin iyayena  da yayana da ya tafi soja har yau banji labarinsa ba da irin San da sukemin.ina basu labari Ina kuka Inda mahaifina yake yawan Zama nake nuna musu Ina murmushi kamar ance na juya na kalli bakin kofa Naga Naseer a tsaye ya zubomin Ido Yana kallona badan nasan Naseer ba danace mahaukaci ne a tsaye a bakin kofa…….
Iabarin na da Dan tsayi shiyasa nake typing kullum na matsu Nazo. Ta tsakiyar labarin Dan haka inaga Zan Dan daddatse sabida mu fara Dan bana shiri da novel Mai tsayi Nan da Nan nake gajiya😃😃😃
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*
     *NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 19*
Cikin fad’uwar gaba na d’auke kaina banji dadin yanda mmn Mannir ta karya alkawarin data daukar min ba ba yanzu naso Naseer ya ganmu ba naso sai mun Dade na samu hutu kafin ya ganmu kasan Raina Kuma tausayinsa ne ya cike min zuciya  amma kuwa saman fuskata hade Rai nayi Dan bazan tab’a binsa ba nafi jina cikin kwanciyar hankali tunda na baro Garin Kano
Jiki ba kwari ya daga Minal Ya Dan matsar da Zahira da Nadeeya da suka kankameshi suna ihun murnar ganinsa.
Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena
Ya sauke wani irin ajiyar zuciya.
Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had’a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana
Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k’arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad’aya.
Shi kuwa ganin naki kallonsa yace “Taimakamin da ruwa in Sha Naeema”
“Mik’ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan.
Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d’ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa.
D’auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb’ensa duk ya bushe.
“Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani”?
Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba
“Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu’a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin dashi kana kallon irin dukan da take wa Zahira duk sabida tsabar tsanar da tamin ta ringa jifanta da mugayen kalamai Wai baza tayi albarka ba Yar iska zata Zama kuka na fashe dashi Dan kalmomin Nan data jefi Zahira dashi ya balain yimin ciwo na cigaba da Magana Ina iya wanan Bai isheta ba ta d’auke min Nadeeya tsabar bakin cikin an ganta Naseer ta fito tana kururuwa Tana watsawa kanta kasa Naseer da kiyayyar ta zata tsaya iya kaina wlh Zan jure amma yanzu ta fara tab’a min Yara bazan jure ba Naseer ba tare aka halliceni dakai ba zaka iya rabuwa Dani ka cigaba da rayuwarka kana da Daman da zaka auri Mata hud’u ka Shimfid’a irin rayuwar da kake so dasu a ganina idan kana kaunata zaka so samun kwanciyar hankalina na Kuma Rayu cikin farinciki Ina kaunarka har a Raina Amma idan akwai cutarwa gwara mu hakura ka sauwake min ikon Allah yasa kagani a zaune a yanzu har nake maka magana a cikin Minal ba irin azabar da Umma Bata gana min ba ta window na duro danake nakudarta sabida Kar ta kasheni banajin addua Zai iya sauko da Umma ta kaunaceni Allah na tuba Umma sosai nake ganin tsanata a idonta Dan Haka Naseer na hadaka da girman Allah ka sauwakemin albarkacin  yaran Nan ka gyara min gidanan da iyayena Suka barmin na  Rayu da yayana cikin kwanciyar hankali idan ma bazaka iya bani jari ba Ni zan nemi aikin da Zan ciyar dasu Naseer Dan Allah ka sauwakemin na gaji wlh Nagaji”
Na karashe Ina fashewa da kukan da nakejin yinshi ne kawai zai saka naji zuciyata ta rage nauyi da zafi idan har Zan tuna wani zalunci da umma tamin sai kirjina yyi nauyi Haka Zan ta kuka har sai naji sanyi a Zuciyata
Naseer kuwa Bai iyamin magana ba in Banda idonsa daya kad’a.yayi ja jijjiyoyin kansa sukayi rud’u rud’u ni nasan sabida gaban yayansa yake shiyasa yake ta mayar da hawayen daya cike Masa ido.
Zahira kuwa da Nadeeya duk da karancin shekarunsu Haka suka hau kuka suma.
Naseer kuwa kamar maganuna bulala Suka Masa a jiki a Haka ya zauna jiki duk ba kwari nasan Dan muna gaban yarane da ya janyoni ya rungumeni ya rarrasheni.
Sai Dana ci kukana na koshi na mik’e tare da d’aukar Humaira.
Ban kalleshi ba nacewa su Zahira suzo mu koma gidan Mai unguwa Dan ko tabarma babu a gidan namu bansan wayanda suka kwashe ba
Naseer Bai mana magana ba har muka fice
Muna zuwa na bawa Zahira tabarma da ruwa a buta Akan ta Kai Masa yayi sallar Magriba.
A hanyar Kai masa ruwa da tabarmar
Mai unguwa ya ganta ya hau tambayarta inda zata je ita kuwa tace Masa Abbanta zata kaiwa.
Take Mai unguwa ya hau washe baki cikin farinciki zuwan Naseer
Yana iddar da sallah ya shigo har d’akin da aka bamu muka zauna da yayana ya daga labulen Yana “Ashe babansu yaran Nan yabi yo sahu Kai Masha Allah naji dadin zuwan da yayi Allah ya daidaita ku Dama kullum sai nayi addua akan Allah ya sa ya mayar dake dakinki Dan shine rufin asirnki an Riga an haifi Yara har hudu ai sai Kuma ayita zaman hakuri Allah ya Kara kau da fitina Zan Masa magana shima Bari na saka a kiramin shi
Nauyin Mai unguwa da yanda ya nuna farincikin zuwan Naseer yasa na kasa Koda magana har ya fice daga gidan.
Sosai naji da gasken bazan koma gidan Naseer ba shiyasa na bi dashi ta ruwan Sanyi Dan ya bani takarda ta Amma idan yak’i kuwa ya zama Dole na fito na gayawa Mai unguwa halin da nake ciki da mahaifiyarsa nasan shima idan yaji bazai so na koma ba tunda neman rayuwata Dana yayana mahaifiyarsa take.
Ana iddar da sallah ishai Mai unguwa ya aiko a kirani
Ina zuwa yace na Kira Masa Naseer ba yanda zanyi Haka na juya na nufi gidanmu  Dan na Gaya masa rufin asirinsa shine ya sauwake min cikin ruwan Sanyi sabida bana San na ringa fallasa Sirrin mahaifiyarsa.
Ga mamakina Ina Isa Naseer na zaune a Inda muka barshi ga tabarma da ruwan da Zahira ta Kai Mai a gefe ya tsurawa waje daya Ido  kirjinsa sai sama da kasa yake
Bansan lokacin Dana taka da Sauri na Isa wajensa tare da durk’usawa a gabansa ba
Yana dagowa ya wawuroni ya kankameni cikin wani irin murya daya karyar min da ba iya zuciyata ba komai na jikina
“Naeema taya Zan soma rayuwa batare da ke ba Taya Zan soma rayuwa da wata matar idan ba ke ba Naeema nafiki Jin ciwon halin da kike ciki sanadin halin Mahaifiyata na kamu da mumunan hawan jini ban taba fada Miki bane Naeema Tayaya Zaki ce na sawake Miki ya kikeso nayi da Raina ke da yarana nake gani nayi farinciki da Ana canja uwa da na Dade da canja Umma badan Mahaifina da Abba sun tabbatarmin da ita ta haifeni ba Naeema da sai nace Umma ba Mahaifiyata bace Dan Uwa da tausayi aka santa uwa bata cutar da dan data Haifa na rasa yanda zanyi da Umma nayi nasihar nayiwa waazin duk tak’i ji bakece Bata kauna ba Naeema Ni data Haifa nine Bata so Dan tasan farinciki da kwanciyar hankalina kune Naeema wlh da Umma zata ce na mallaka Mata duk abinda nake dashi zata barni mu Rayu cikin kwanciya hankali ko daki dayane na Kama Mana na ringa dako muna ci muna Sha da.naji dadi na.rasa yanda Zan mata  Dan Allah Naeema rabuwa Dani bashine mafita  ba na yarda Zan Kara nema miki wani gidan batare da saninta ba Ni Kuma zance Mata har yanzu banganki ba”
“Naseer bazan koma Garin kano ba sai dai ka gyarmin Wanan gidan ka ringa zuwa kana ganinmu “
“Ya zamuyi da Karatun yaran namu kasuwanci na fa danake yi a garin Kano wlh Zan iya takuna bazan Bari Umma ta.san naganki ba Zan ringa zuwa ko sau ukune sati Dama akwai wani karamin gida Dana siya a sharada inaso na zuba Yan haya tallansa akamin Mai gidan na bukatar kudi shine na siya kawai Zan gyara miki ki koma can wlh Umma bazata Sani ba”
A takaice duk ta Inda na b’ullowa Naseer sai ya zame ya kalamanceni abinka da tsakanin mata da miji sai Allah tuni Naseer ya shawo kaina duk alwashin Dana Sha yabi iska muna zuwa gaban Mai gari yayi wa Naseer fada da naseeha washegari muka fara shirye shiryen komawa Naseer sai lallab’ani yake Yana riritani (Nafeesa Naseer na balain Sona rabuwa daya k’iyi  Dani ya jawo Mana masifu da ko makiyina bana fatan yyi kwatan rayuwar da mukayi)
Matar Mai unguwa ita ta yarfamin kitso da Jan lalle na garjajiya yayana ma.aka musu kitso
Naseer kuwa ya cika Mai unguwa da abun arzki da matansa da yayansa tun kafin mu taho aka fara gyara gidanmu Inda Naseer ya bawa Mai unguwa kwangilar Ana Gama gyarawa a nemi Yan haya a saka a ciki kudin Kuma ya ajiyemin.
Hotel ya Kama Mana da muka iso sosai Naseer jikinsa ke rawa kamar Wanda yayi sabon aure duk wani Abu daya gani sai ya siyo Mana Dan sati daya ya kama Mana abinda ke fita dashi kawai gyaran gidan sharada ne da Abubuwan bukata da zamu yi amfani dashi.
Inama Umma ta saka Mana albarka a aurenmu ta daina daga Mana hankali da sai nafi kowace mace dacewa da gidan miji Dan ranar da muka kwana biyar Naseer ya siyomin set din sarka da dankunne har da zobe na daham Dubu talatin a lokacin ba karamin kudi bane sababin Kaya kuwa Haka ya cike Mana shi a akwati biyu atamfofi na ma kuwa Mai karamin kudi a ciki shine dari bakwai Wanda a kudin yanzu Zan iya yin Dubu biyar.
A Dan tsakanin kuwa sosai na dage da Addu’a Naseer kuwa shima Bai zauna ba.
A ranar da muka cika sati daya muka tare a karamin gidan Naseer dake sharada.
Cikin kwana biyu ya samowa su Zahira makaranta har da Minal suka fara zuwa
Har wani Dan sheki yake Yi na kwanciyar hankali.
Ni kuwa Inda ya kasance d’akina sai Dana rataya abinda Mallam Musbahu ya bani Dan dazan tafi sai Dana cire na kaina kuwa bana Wasa dashi sai idan Zan shiga bandaki nake cirewa Ina fitowa kuwa na maida kayana.
Dak’yar na  samu na Shawo Kan Naseer akan ya koma gidan  Sabida Kar Umma ta zargi wani Abu Yama nuna Mata ya hakura Dani zai zauna da Hindatu anan ya harareni nayi dariya nace yayi maganinta cikin sauki da kafarta zata gudu sai a lokacin yace na kawo shawara Mai kyau shi Kuma zai na karyar tafiya Yana zuwar mana.
A ranar da zai koma goron dutse da yamma Inna zuwaira da zata iya haifata tazo gidan Ashe Naseer Mai Tayani Zama ya Nemo min wacce Kuma zata ringa Tayani aikace aikace idan ya dawo Kuma sai ta tafi idan zai tafi sai ta dawo.
Sosai naji dadin zuwanta Dan Zan samu Mai debb’e min kewa kila ma har Abu Idan ya shigemin duhu Zan iya neman shawarar ta.
Naseer sai daya ajiye Mana komai har da kudin da bansan Mai zai yi.dasu ba Wanda har dagewa.nayi bazan karba ba Dan cemin yayi kullum sai yazo har abinci ma anan Zai  ringa ci kwanciyar bacci ne zai ringa Mai dashi gidan.
Wajen karfe Tara ya Isa gidan fuskarsa kalar tausayi kamar gaske irin neman Naeema yake.
Tun Kan ya karasa Hawa sama yake jiyo Shewa.
Da Sallama ya tura k’ofar
Ba Wanda ya amsa sai juyowa da sukayi gabad’aya suna kallonsa Hajara har da mik’ewa tayi dage tana kallon bayansa Wai ko ya dawo da Naeema sai data ga shi ka dai ne ta washe baki tana “ko Kai fa ka hakura kazo ka zauna da Yar albarka tace.tana nuna Masa Hindatu.
Naseer Bai ce komai ba ya hau kallon mutanen palon Hindatu ce da Saffiya da Lami har dasu Tijjani sun zauna a tsakiyar Palon sai barjen Naman kaza suke ga kwalaban lemo a bubude.
Wato ma budurinsu kawai suke da Naeema ta tafi shi Kuma daga tafiyarsa shine su Saffiya suka dawo gidan.
Ba wacce yayiwa magana a cikinsu har Tijjani dake gaishe shi
Ya d’auke kansa tare da nufar d’akinsa Kai tsaye yana Jin muryar Umma tana duk hade Ransa Naeema bazata dawo ba idan ma.zai ware ya ware.
Sai daya Dan gyara d’akin ya watsa ruwa ya kwanta ya hau tunani su Naeema Dan lokacin ba wayar hannu da ya Kira yaji lafiyarsu Naeema
 Dan kwanakin da yayi dasu ba karamin nutsuwa da kwanciya hankali ya samu  ba babu abinda ya Kai Zama da iyali dadi.
Bai San da shigowar Hindatu ba sai ji yayi ta fado kansa shi kuwa ya mik’e da Sauri ya wancakalar da ita ya fara binta da wani mugun kallo Yana “duk ranar da Kika Kara shigomin daki wlh sai na balla Miki kafa juya ki fita”
Hindatu da Sauri ta fita ko minti biyu baayi ba Suka dawo d’akin da Hajara cikin masifa ta fara magana tana “Wai Mai kake nufi dani.ne. Naseer akan me zaka auri Yarinya Kuma ka ringa wulakanta ta toh wlh ka kaini bango Kar sake ka Kara korarta daga d’akin Nan Dan nan da wata tara inaso a haifomin jika Ni naga masifa duk da shegiyar matarka ta Shiga duniya ka ki nutsuwa ka dawo hankalinka toh wlh ka nutsu Dan nasan Tama Dade da mutuwa an rage mugun iri”
Wani irin kallo Naseer yabi Hajaran dashi ya d’auke kansa Bai ce Mata komai ba sai data gaji Dan kanta ta fita waje tare da Kara rufo musu kofa har da su mukullin.
Hindatu kuwa har da wani murmushnta ta Kara haye.gado tana murmushi.
Naseer shima mik’ewa yayi ya kullo k’ofar da mukulli ya zare ya saka key din a aljihunsa ya Shiga bandaki ya dauro alwala yazo ya hau Kan Sallaya.
Tuni ya ware murya ya fara karatun Qurani Hindatu kuwa ta mik’e hankali a balain tashe ta nufi wajen kofa ta fara jijigawa sabida Karatun sosai yake kona fatar jikinta.
Naseer kuwa Yana ganin Haka ya mik’e ya Ajiye Quraninsa ya nufi wajen Hindatun ya rik’e hannayenta biyu da k’arfi ya cigaba da karatunsa da k’arfi Yana tofa Mata yawun bakinsa.
Hindatu kuwa da iya karfinta take ihu tana Kiran sunan Hajara Dana Mahaifiyata take Hajara ta Gane Mai ke faruwa hankalinsu ya tashi.
Hajara kuwa ta bud’e k’ofar d’akin sai dai Naseer ya kulle k’ofar ta ciki itama da Sauri ta dawo Baya
Abinda basu fiye Yi ba b’acewa Dan sai Abu yaci tura sosai suke amfani da Wanan karfin.
Akan Dole Hindatu ta b’ace daga hannun Naseer
Duk da Naseer ya tsorata sai Haka ya cigaba da karatunsa da k’arfi tsoro na Kara shigarsa
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*
     *NA SADNAF*🌸🌸
®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_
*Free Novel*
*Page 20*
               Duk da yasan Hindatu da mahaifiyarsa suna cikin kungiya Bai San haka Abun yake ba yanzu macen da take tsafi wacce take Mayya mahaifiyarsa ta aura Masa Maganar Allah ne basa so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d’auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b’ace sai da yaga zahiri.
Sosai.ya Kara k’arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida.
Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d’akin ya shareta
Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b’aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab’a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub’e a kasa suna k’ok’arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d’akinsu ta d’auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu.
Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba
Kafin ma suyi magana har ta b’ace.
Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad’an Bata San abinda zai  rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k’arfin.
Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba  sai da aka  Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci.
Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik’e a firgice
Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik’e yayi band’akin palon ya d’aura alwala ya fito.
Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo  gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan.
A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa.
Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta.
“Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak’antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka”
“Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b’ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b’ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah “
“Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b’ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi
Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon.
“Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik’e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure.
Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba”
“Naseer  a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin  ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta  saka ka fice daga hayyacinka”
Naseer tashi yayi ya Shiga d’aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad’a kamar zata Ari baki.
Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan
Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna  zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta
Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala  yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa
Yana dawowa kuwa gidan ya d’auko Quraninsa a Palo ya hau karatun Qurani Dan sosai yake so su Umma su ma su bashi space ya sarara Amma ga mamakinsa ba Wanda ya tashi a cikinsu ya gudu kamar yanda suka Saba.
Sosai kansa ya daure da mamaki Hajara kuwa sai jefa Masa harara take sai daya Kai Aya ya mik’e zai Shiga d’aki tace “wato k’arfi da yaji kake so mu bar gidanan babu Inda zamuje Naseeru muna Nan tare da.kai zanyi maganin taurin kanka
A Haka rayuwa ta kasancewa Naseer da Naeema.
Acan  yake yin komai kwana ne kawai baya yi a gidan shima da an kwana biyu zai cewa Hajara tafiya ta taso Masa ahaka zaije yayi sati ko sati biyu a gidan Naeema sosai suke taka tsantsan Dan Kar Hajara ta  gano  suna tare.
Duk da lokacin sosai ta matsa Masa da zancen aure har mamaki take yanda Naseer din yake rayuwarsa batare da ya damu ba gashi ba komai na tsafi da zasu iya gano komai a game dashi Koda akwai yanzu idan Suka so ganin Naeema ta mudubi basa iya ganinta har mamaki suke Nan kuwa basu San layyar data saka a kanta bane.ya hanasu ganinta shugabarsu ma sai cewa.tayi kila ma Naeema mutuwa tayi shiyasa basa ganinta
Naeema sosai Jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna Mata har ta ringa tunanin duk wanan lokacin Mai yasa dabaran hakan Bai fad’o musu ba.
Naseer shima sosai ya samu kwanciyar hankali sai zai je gidansa da mahaifiyarsa take ciki yake d’auko wata fuskar ya aza idan yaso ma tsokano Hajara idan tana Masa zancen aure shi kuwa sai yace Mata Shi bazai yi aure ba sai Naeeema ta dawo anan fa Hajara xata hayayyako kamar zata masa.baki tayi ta cewa Naeema ai ta mutu ko ba mutuwa tayi ba Bata isa ta dawo gidansa ba.
Ahaka har sai da suka kwashi watani shidda cas watarana ya dawo daga gidan Naeema.
A Palo ya tarar da Hajara ta balain had’e Rai Safiyya Kuma tana zaune a gefenta.
Gaishe ta yayi ya mik’e zai wuce d’akinsa Hajara ta dawo dashi ya zauna.
Ta fara magana cikin b’acin rai “Naseer kana so kaga b’acin Rai na ko kana so sai na balain Bata maka kafin  mu shirya dakai ko ka Nemo matar aure ko na nemo maka da kaina na gaji da ganin ka Haka ko na nemo maka matar auren
Sai ka wulakanta ta kamar yanda ka wulakanta Hindatu na baka Nan da sati biyu ka nemo matar aure idan ba Haka ba wlh da kaina Zan Nemo maka Kuma baka Isa ka wulakanta ta ba”
“Tom Umma Zan nema Ina ta ganinsu babu wacce tamin ne Amma insha Allahu zanyi kokari na nema din”
Daga Haka ya mik’e ya shige dakinsa
Fada Hajara ta ringa yi bayan ya Shiga d’akin Saffiya kuwa ta tab’a ta tana “Umma Anya Yaya baya tare da Naeema kuwa “?
Wani irin hantsulowa Hajara tayi daga Kan kujeran ta dafe kirjin ta tana “Mai kikace Suna tare fa  kikace Mai kika gani kikace Haka”?
“Umma kema kinsan yanda ya Naseer yake San Naeema yake Kuma San yaransa banajin da basa tare zai samu kwanciyar hankali Haka ke bakiga yanda.yaya ya danyi kib’a Yana sheki ba wlh kila Raina Mana hankali yake”?
“Zan Miki baki wlh Safiyya karki soma min wanan fatan idan suna tare a Ina ya ajiyeta Naga dai gida yake zuwa ya kwana sai idan tafiya ta Kama shi yake kin kwana a gida kin manta bama.ganinta a mudubi shugaba.kuma data duba da kanta tace kila hatsari sukayi suka mutu”
“Hmmm toh shikenan tunda Kikace Haka Amma nidai gani nake da Yaya baya tare da Naeema bzaki kansa fes Haka ba”
Mik’ewa Hajara tayi da Sauri tana “idan kuwa hakane Safiya na gano rainamin hankali sukayi wlh sai nayi wa Naseer baki wlh sai na kashe Naeema da hannuna Kinga Banga ma ta zama ba ya zama Dole mu koma Calabar muje mu bawa Shugaba hakuri ko Dan na ringa sanin abubuwa da ke wakana wlh tunda ta kwace komai namu banajin dadi Banga ta zama ba ya zama Dole mu d’auki hanya gobe”
Sosai hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba.
Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad’an ya Kara siyan  fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari.
Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa.
A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema.
A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji.
Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu’a duk da Bata tab’a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar.
Hajara kuwa dak’yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi.
Satinsu uku a Calabar suka dawo.
Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo.
Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba.
Ahaka ya b’oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa.
Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali.
Yana tashi ta kalli Safiyya tana “Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki”
Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba
Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada.
A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan.
Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa.
Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad’uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har  Naseer ya tafi.
Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba
Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran.
Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira
Zumbur ta mik’e tsaye
Tace “Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema”
Yaraf Hajara ta zub’e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik’ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me”?
Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d’auko ta zata hada Masa kudinsa.
Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada.
Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema.
Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu.
Ina zaune naji Ana buga gate da balain k’arfi mik’ewa nayi cikin fad’uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina.
Inna zuwaira ce ta bud’e gidan tana bud’e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya.
Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi…….ƙama Hajjo yana faɗin, “Da wannan zaku gansa dole, dan ƙa’idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya taɓa ganin likita akan hakan”.
     Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake miƙama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ɗin da aka bashi a cikin file ɗin ya ajiye.
     Kasancewar lokacin sallar isha’i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ƙara duba Nu’aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
     Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.
_★__★_
      Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu’aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ɗauka file ɗin nata ya fice da shi zuwa sashensu.
      Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu’aymahr ba itama batace da shi ƙala ba har suka kwanta.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
_______________________
WASHE GARI
_______________
          Alhmdllh Nu’aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
     Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
    Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu’aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
    Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu’aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu’aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
     Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu’aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu’aymah ba.
     Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
         “Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu’aymah da Yusrah duk suna hawaye.
         “Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu’aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu’aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu’aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za’ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
     Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za’a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
       Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu’aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
    Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.
      Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu’aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za’a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
      Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu’aymah.
        Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu’aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
       Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
        Hajjo ta jima tana lallashin Nu’aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
_______________________
______________
DUBAI
________
              Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu’aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
     Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
     Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
       Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu’aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu’aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.
“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki🤣😏”.
               Haka ta yini ita kaɗai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ɗauke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
         Abdallah bai dawo hotel ɗinba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ɗauke kansa. Ya ɗauka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ɗaya daga rukunin kujerun ɗakin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ƙofar. Adawiya ta miƙe jiki na ɓari zataje ta buɗe ya ɗaga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
       Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ɗakin.
      “Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?”. Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu’aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ɗauka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.
★★★★
        Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ƙasarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ɗaya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
     Shiko gaba ɗaya ya ɗauketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ƙasar ya maidashi kwana shida zasu wuce.
         Tun a randa Nu’aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ɗin ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu’aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
            Karan farko da tun faruwar al’amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu’aymah itama.
        Bayan sun gaisa cike da so da ƙaunar juna irin ta ɗa da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumuɗi yace, “Momy ashe Nu’aymah ta dawo?”.
       Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, “Uhmm! ta dawo jiya”.
        “Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake kuɓuce minba Momy, a yau ɗin nan ina durowa koda magriba ne sai an ɗaura mana aur……”
         “Kai! Shashasha dakata min. To idanma mafarki kake maza ka farka ka dawo hayyacinka. Wai kai Abdallah wane irin sakaran banzane halan? Ka fita idanuna tunkan na rufesu da kai a ciki wlhy. Bara makaji na maka mai kankat. Wlhy tallahi idan naga ƙafarka a ƙasarnan batare da ni nace kazoba ALLAH ya isa ban yafe maka ba…..”
         “Momy!!” ya faɗa cikin tsananin tashin hankali.
     “Yes! Abinda kaji shi na faɗa. Idan zakai haƙuri da waɗanda aka baka kayi. Hauka akeyi da za’a manna maka mata har uku ƴan family ɗaya uban ƴan son zuminci? Itama Yusrahn ina nan ina nema maka hanyar barinta wlhy. Adawiyar dai ta tsira tunda ALLAH ya sota ka baro ƙasar da ita da wuri. Idan suma sunada nasu zaɓin nima inada nawa ai, amma aka nunamin fin ƙarfi da ƴan uwantaka. Kai kuma shashasha da yake baka kishina hakan ko damunka bayayi. To wlhy kama cire wannan tunanin a ranka. Kuma ko a waya ka kira wani cikin iyayenku kace a ɗaura maka aure da Nu’aymah shima ban yafe makaba. Idan wannan maganar tasa ka kirani karka sake kirana”.
    Ta katse wayar batare da ta jira cewarsa ba.
      Sosai jikin Abdallah ke tsuma. Haƙoransa har wani bada sautin ƙara suke saboda rawar da bakinsa keyi. So yake ya faɗi sunan Momy amma ya kasa haɗa kalmar waje guda dan tsabar rikicewar da yayi.
      “Yah Ab lafiya kuwa?”. Adawiya ta faɗa tana ɗaura hanunta saman kafaɗarsa. A fusace ya ɗago ya hankaɗe hannun nata tai taga-taga ta faɗa saman kujera. Ko kallonta baiyiba yay wurgi da wayarsa ya nufi bathroom da sassarfa. Yana shiga ya sakarma kansa shawa ruwan na saukar masa a jiki batare da ya cire kayaba.
     Kalmar ALLAH ya isar Momy ce keta masa kai kawo a zuciya har kana hango sama da ƙasan da ƙirjinsa keyi na.
       Adawiya kam tana ganin ya shige ta miƙe idanunta cike da hawaye. Da ƙyar ta ɗangyasa ƙafarta data buge da centre table ta isa inda yay wurgi da wayarsa. Addu’a take ALLAH yasa babu lock. Cikin sa’a kuwa babun, sai dai hoton data fara cin karo da shi a fuskar wayar ne yasata jin wani irin zafi tamkar an soki zuciyarta da mashi.
       Hoton Nu’aymah ne da sukayi ranar walimar gama makarantarsu. Tayi masifar ƙyau a hoton, dan ɓakar doguwar rigar data saka na Material ɗinkin yay masifar zama mata a farar fatarta. Ga idanun nan sun bala’in fitowa cikin kwalli har wani ƙyalli suke saboda haske. Tayi ɗan murmushinta loɓar kuncinta data gemunta ta fito raɗam. Sosai Adawiya ke faman taunar lips da ƙarfi tamkar zata hudasu, duk da tasan hoton tunkan shi Abdallah ma ya gani hakan bai hanata jin zafi mai tsanani ba. Da kyar ta iya danne ranta ta shiga dan son ganin dawa yay waya. A fili tace, ‘Momy!. To mita gaya masa daya fusatashi haka har yake neman karya ni a banza?’. Bata da mai bata wannan amsar, gashi kuma batasan inda wayarta takeba balle ta kira wani ta tambaya. Tanajin tsoron yin amfani da tasa kuma yazo ya kamata. Da sauri ta ajiye wayar inda ya jefar jin za’a buɗe ƙofar bayin.
       Tsaye yay cak a ƙofar bayin yana binta da kallon tuhuma fusatar zuciyarsa na daɗa bayyana saman fuskarsa………….✍
        Kuyi haƙuri, jiya man kaina ne ya tsiyaye tas yasin na kasa typing😖.
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.
*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.
*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*
No. 7
…………….Sosai gazawar Umm take ƙoƙarin bayyana ga kowa. Dan gaba ɗaya yinin yau da Nu’aymah ta yisa a ranta. Tun tana kukan zuci kamar yanda ta saba har hawaye suka kai ga fara sakko mata daga idanu.
        Wajen misalin biyu da rabi na rana Baba malam ya shigo gidan. Kamar yanda al’adarsa take inhar ya dawo daga wajen aiki sai ya fara zuwa sashen Hajjo yaga lafiyarta. yauma haka ne. Zaune ya isketa a falo Imran na tausa masa ƙafa yana kumbura baki dan ta sakashine dole.
     Murmushi Baba malam yay da zama a ƙasa gefenta kaɗan da ajiye mata ledan kayan fruits idonsa akan Imran ɗin da shi sam hankalinsa bai kai kansa ba.
           “Imran ya naga fuskar a kumbure? Ko dai aikin innah ne ba’a son yi?”.
     Kallonsa Imran yay da sauri, sai kuma ya saki ƙafar Hajjo ya nufi baba malam ɗin yana sake tunzura baki gaba. “Baba sannu da dawowa”. Kafin Baba malam ya bashi amsa Hajjo ta katsesa. “Dan gidanku dawo ka cigaba, inba hakaba kasan ALLAH nasan ta inda zan rama mai ƙwalelen ƙeya kawai”.
      Dariya Baba malam yayi yana kallon yanda Imran ɗin ya cika yay fam, sai kuma ya kalli Hajjo da itama ta kumbura farar fuskarta da duk tai tamojin tsufa tana zubama Imran ɗin harara……
       “Ni wlhy na gaji Hajjo, kumafa Momy jirana take zan mata aika”.
     “Oh! Uwarka ta fini kenan?..”
Baba malam yay saurin haɗiye dariyarsa da matsawa kusa da ita gab ya kama ƙafar tata ya aza saman ƙaramin filon kujera. “Kinga Inna manta da shi kinji, idan shima yana tsoron ɓatama mamarsa nima ai gani tare dake ko?”.
         Murmushi tayi kamar ba itace da fuska a kumbure ba. Sai kuma ta watsama Imran ɗin harara tana faɗin, “Tashi ka fitarmin a falo to kirikun banza, indai nice ai inada ranata yaro”.
     Tashi Imran yay da sauri dan ganin Hajjo ta kwakuso filon kujera da alama dukansa zatayi. Sai da yaje bakin ƙofa sannan ya juyo. “Ai dai gobe idan ALLAH ya kaimu zamuyi komawarmu Abuja…….”
     Kafin ya rufe baki ta tilla masa filon, kwasa yay da gudu ya fice yana ƙyalƙyala mata dariya.
        “Wlhy Ɗan malam ƴaƴanku sun fetsare musamman ma ƙarshe-ƙarshen nan. Kaga akace maka Imran da Muhammadu da Jafar sunfi kowa rainanima a gidannan”. Hajjo ta faɗa a ƙufule.
      Cike da girmamawa da lallashi baba malam yace, “To kiyi haƙuri inna zan musu faɗa kinji, yanzu dai ƙafar ciwo take miki ne?”.
        “Kaɗan take ciwon dai, na neman man zafin daka siyomin shekaranjiya na rasa inda yake, na tabbata cikin ƴaƴanku wani ya ɗaukesa. Ƙilama Zainabu c…….” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa saboda tunawa da tai Nu’aymah ma bata gidan. To ita kaɗaice ke mata yanda ta gadama a cikin jikokinta a zauna lafiya a gidan. Dan suna mugun ɗasawa da Nu’aymah saboda duk aikin da ta sakata yimatashi take. Hatta da wanki Nu’aymah ce kema Hajjo. Hakama gyaran sashenta. Sai ko Adawiya itama sunaɗan shiri, amma ƙa’ida kullum sai sunyi faɗa.
      Ɗan murmushi baba malam yayi mai ciwo, dan shima a kullum ɗiyar tasa tana a ransa. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Karki damu innah insha ALLAH zansaka Abubakar ya saya miki idan zai baro company. Sannan zanma Doctor Kabir magana yazo ya duba ƙafar, idan kuma asibitin zamu koma to”.
      Jikinta a sanyaye ta ɗaga masa kanta, harya miƙe bata iya sake cemasa komaiba. Sai da yaje gab da fita sannan ta kira sunansa. “Ɗan malam!”. Juyowa yay da sauri yana ƙoƙarin haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi da amsawa da “Na’am Innah”.
         “Har yanzu babu labarin Zainabu dai ko?”.
     Murmushin yaƙe yay mata wanda yafi kuka ciwo, ya ɗan girgiza mata kansa da faɗin, “Innah tasan inda taje ta ɓoye kanta ai. Randa ta buƙaci ganinmu da kanta zata nememu, ki kwantar da hankalinki wannan yabar damunki”.
     Bata iya cewa dashi komaiba yanzuma. Dan damuwa ƙarara ta hango a saman fuskarsa da cikin idanunsa. Amma dan ƙarfin hali sai yay mata murmushi sannan ya juya ya fita.
          Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka ya isa sashensa. Da tsarabar da yayo ta fruits ya fara cin karo a falo alamar driver baiga kowaba ya ajiye a nan. Ya ɗanbi ledojin da kallo kafin ya ida shigewa cikin corridor ɗin da ɗakunan barcin su Umm suke. Kansa tsaye ɗakinta dake can ƙarshen dogon corridor ɗin ya nufa, yay sallama kusan uku a ƙofar ɗakin babu amsa, sai kawai ya tura ƙofar ya shiga da sallama.
       Tsaye yay cak a ƙofar ɗakin riƙe da handle ɗin kofar yana kafe Umm dake zaune a saman gado, Muh’d na kwance ya aza kansa bisa cinyarta yana barci. Kan yaron take shafawa a hankali, kanta na kallon p.o.p idanunta na tsiyayar da hawaye.
         Haɗiye tasa damuwar yay ya ƙarasa cikin ɗakin sosai. Harya zauna a bakin gadon kusa da Umm bata motsaba. Ya ɗaura hannunsa saman nata dake shafa na Muh’d. Nannauyan numfashi ta sauke da ɗago kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna ita da baba malam ɗin. Sai tai azamar saka hannunta na haggu ta share hawayen fuskar tata tana maye gurbinsa da murmushi.
       “Sannu da zuwa Abban Nu’aymah. Yaushe ka shigo ban saniba? Gaba ɗaya na gajine shinefa nace bara nazo na………” hannunsa yay saurin ɗorawa akan bakinta alamar tayi shiru. Yasan ba wani abune ya saka wannan kame-kamenba sai dogon gargaɗin daya gindaya mata akan karta sake masa maganar Nu’aymah koda da wasa ne. Umm macece ita mai biyyaya da gudun ɓacin ran mijinta, duk abinda ya nuna bai masaba ƙoƙarinta shine dainashi tai masa wanda zai sakashi a farin ciki koda ita zai cutar da tata zuciyar kuwa. Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙara mata kima da daraja a gareshi, tare da sake girmama soyayyarta a ranshi.
     Miƙewa yay ya ɗauki Muh’d a hankali ya matsar dashi can gefe ya kwantar. Ita dai tana binsa da kallone har ya dawo ya zauna kusa da ita sosai. Kamota yay ya kwantar da kanta a ƙirjinsa. A tare suka sauke nannauyar ajiyar juciya. Hawayen da taketa ƙoƙarin karsu zubo suka ziraro a guje suna sauka bisa jikinsa.
        Idanunsa ya lumshe tare da sake kwantar da ita jikin nasa da ƙyau, ya zame ɗan kwalinta yana shafa kanta dake cike da gashi dogo mai yarfin furfura ɗai-ɗai alamar girma ya fara kamata. Sake kwanciya tai sosai da cigaba da hawayenta.
    Sunja tsahon lokaci a haka har saida akai kiran sallar la’asar sannan. Itace ta ɗagashi da sauri. Hakan yasa ya farka daga barcin daya figesa shima. Tunda abinnan ya faru bai sake yarda sun kwana ɗaki ɗayaba tun randa ta kwana babu lafiya. Hakan yasa suke tsananin kewar ɗumin junansu. Matsar da fuskarsa yay gab da tata ya sumbaci goshinta da dogon hancinta.
     Ɗan murmushi tamasa da sadda kanta a ƙasa na alamar jin kunya. Shima yay murmushin yana sauke ƙafafunsa ƙasa. Batare da yace mata komaiba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Ki tada Muh’d yay alwala mu wuce massallaci”.
       “To” ta amsa masa tana binsa da kallo.
__________________________________
              Ana shiga sallar la’asar jar motar na shigowa cikin layin. Parking yay a ƙofar ƙaton gate ɗin gidan yana kallon gate ɗin massallaci. Kafin kuma ya maido dubansa kan Nu’aymah dake a gefensa hannu da idanunta da baki a rufe tana gyangyaɗi.
       Ɗauke kansa yay ya kashe motar gaba ɗaya. Bai fitaba, saima kwanciya yay jikin kujera ya lumshe idanunsa dake a cikin baƙin glasess ɗinsa.
       Kusan mintuna uku da tsayuwarsu Nu’aymah ta farka. Sai dai kasancewar idanunta da bakinta a rufe suke sai bazaka fahimtaba. Addu’a kawai take jerawa a ranta na nema agajin UBANGIJI. Sai da aka fito massallaci mutane suka gama shashsharewa, sai hayaniyar yara ƴan islamiyya dake cikin harabar massallacin. Kusan biyar na yamma Baba malam ya fito daga cikin massallacin shi da wani maƙwafcinsu suna magana. Saurin tashi yay zaune da kallon Nu’aymah, yay azamar saka hannu ya ɗaye mata salataf ɗin da suka rufe mata baki da shi. Ƴar ƙarar azaba ta saki tana faɗin, “Mugu kawai, ALLAH zai sakamin”. Bai kulata ba ya kwance mata idanunta da hannunta suma. Wani irin farin cikine ya saukar mata a rai ganinta a ƙofar gidansu. Tana zumuɗin fita ya dakatar da ita.
      “Malam ɗauki akwatinki ki wuce da shi”.
     Juyiwa tai da sauri tana kallonsa batare da ta saki handle ɗin ƙofarba. “Bansan kallo, ki ɗau akwatinki nace”.
          “Minene abin kallo a jikin naka banda baƙin hali da zalunci. Ni dai nasan banbar gidanmu da akwati ba mizaisa kuma na ɗauka na shiga da shi…”
        “K!!!” ya daka mata tsawa a fusace. Hakan ya sakata dakatawa daga ƙoƙarin sake buɗe ƙofar ta juya tana watsa masa harara da manyan fararen idanunta masu yalwar gashi. “Minene namin tsawa malam?”. Maimakon ya bata amsa sai ya ɗaga mata yatsun hanunsa biyu dake a cikin safa yana faɗin, “Kinada zaɓi biyu. Koki ɗauka akwatin nan kokuma wlhy na maidake inda muka fito, kuma wannan tafiyar itace zata zamemiki ta har abada keda gida”.
     Kafinma ya rufe baki ta miƙa hannu baya ta sungumi ƙaramin akwatinta ruwan hoda mai ƙyau. Batare data sake jira yace uffan ba ta buɗe murfin motar ta fice abinta.
          Sosai gaban baba malam ya faɗi, yabi Nu’aymah dake jan akwati zata shiga gida da kallo harta tura ƙofar ta shiga, kafin ya maido dubansa ga motar data ajiyeta. Akan idonsa mai motar yay reverse yabar anguwar.
    Duk yanda yaso danne ransa suci gaba da magana da Alhaji Mani hakan ya gagara. sai kawai yay masa sallama akan yayi haƙuri anjima zasu ƙarasa maganar.
       Da mamaki Alhaji Mani yabi baba malam da shi harya shige gida da kallo.. Ya ɗanyi shiru alamar tunani. Ganin bai hasaso komaiba sai kawai ya girgiza kai shima ya juya ya shiga nasa gidan da masallaci ya raba tsakaninsu da nasu Baba malam.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
__________________
__________________
             Nu’aymah na isa tsakiyar gidan ta yadda akwatin ta kwasa da gudu zuwa ciki tana ƙwala kiran sunan Umm da Hajjo, dan gani takema tafiyar ɓata mata lokaci takeyi na isa garesu.
        Ba Umm da Hajjo kaɗaiba kowa ma na gidan sai da ya fito, yaran ne kawai da suka wuce islamiyya babu. Samarinma yawancinsu sun dawo daga wajen aiki da makaranta ga waɗanda ke jami’a.
         Wani irin tsalle Nu’aymah tai ta ɗane wuyan Umm dake tsaye a ƙofar sashenta tamkar wata gunki. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam gidan a matuƙar fusace.
         “K!! Nu’aymah! K!! Nu’aymah kina ina?”. Baba malam dake shigowa tun daga gate ya fara kwala ma sunanta kira kamar zai haɗiye harshensa.
       Da sauri Nu’aymah ta saki Umm jikinta na wani irin rawa, dan abin yazo mata a yanda batai zatonsa ba. Akwatinta dake yashe a ƙasa ya shura da ƙafa yana faɗin, “Zoki ɗauka ki koma inda kika fito kafin harshena ya furta miki abinda har ki ƙare rayuwarki zai zame miki musiba”.
        Idanu sosai Nu’aymah ta zaro waje jikinta na sake ɗaukar tsuma. Muryarta na rawar fitar kuka tace, “Abba……” Katseta yay a tsawace yana nuna mata hanya da yatsansa.
     Ba’ita mai laifin kawai ba, kowama yayi tsuru-tsuru a gidan hatta dasu Abba Rudwan sun kasa magana, dan sunsan ran yayan nasu a matuƙar ɓace yake. Hajjo ce kawai zata iya sakashi ko hanashi a irin wannan yanayin. Gashi kuma bata fitoba, ƙila wanka takeyi.
        “Ba dake nake magana ba ne?!!”.
Fashewa da kuka Nu’aymah tayi ta durƙushe ƙasa. “Abbah wajen waɗanda suka sacenin kakeson na koma?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, dan yama ɗauka maganarta raini da iya shege.
          “Lallai Nu’aymah kin girma! Ashe wayonki da iya tsara abubuwa har ya kai haka ƙarfi? Ki sanar mana kinbi saurayi saboda kar a aura miki Abdallah sannan ki dawo mana da wani sabon rainin wayon saceki akayi?. To idan saceki akayi uban wanene ya rubuta saƙwannin da kika barmana? Wanene kuma ya sacekin? Wanda naga ya ajiyeki yanzu shima wanene?. Duk sai ki bamu waɗanan amsoshin muna saurarenki?”.
       Kai Nu’aymah ta shiga girgizawa tana hawaye. “Wlhy Abbah bansan komaiba akai. Bansan su wanene ba? Bansan wanene wanda ya ajiyeninba nima? Sannan ban ajiye saƙon komaiba ga kowa wlhy”.
       “Nu’aymah!!!”. A tsananin tsawace baba malam ya kira sunanta. Sai da hantar cikin kowa ta kaɗa da tsawarsa. Itama tai baya ƙasa wanwar jikinta na ɓari na tsabagen tsorata. Dan bata taɓa ganin fushin mahaifinta irin hakaba duk da tasan yanada zuciya.
           Nufarta yay tamkar wani mayunwacin zaki, sai famar huci yakeyi jikinsa na tsuma.
      Da sauri Abban Abdallah da Abba Mustapha suka sha gabansa yana gab da isa ga Nu’aymahn. Kareta sukayi yanda bazai ko iya ganinta ba balle ya taɓata.
         Sake ɓaci ransa yay, ya kallesu da jajayen idanunsa da ƙwalla suka taru a ciki. kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya juya zai zagayesu ya damƙeta.
      Caraf aka riƙe masa hannu. Dan haka ya tsaya cak batare da ya shiryaba. Hajjo data fito yanzun nan saboda tsawarsa da taji ta kalli hannunsa data riƙe da tana sake tamke fuska batare da tayi magana ba.
        A take dukkanin jikinsa yay sanyi laƙwas, sai wata irin zufa data shiga tsatstsafo masa a goshi. Sun kai kusan mintuna biyar a haka ana kallon kallo tsakanin duka ƴan gidanma. yayinda Umm tunda Baba malam ya shigo ta sulale ta koma ciki tana hawaye.
         Da idanu Hajjo tai masa magana da yaren da tun yana yaro ya haddace sa, kafin ta saki hannunsa a hankali ta nufi Nu’aymah dake durƙushe ƙasa tana kuka har yanzun. su Abbah zagaye da ita suma har yanzun suna bata kariya daga baba malam. Kamata hajjo tai ta miƙar da ita ta rungumeta a jikinta. Nu’aymah ta ƙanƙame Hajjo sosai tana jan numfashi da ƙyar. A hankali kuma sai idanunta suka fara lumshewa, kafin kowa ya farga tama sume.
         Hajjo da taji ta mata nauyi tai ƙoƙarin ɗagota amma ta kasa. Gabantane ya faɗi tace, “Kai Mustapha zoku duba yarinyarnan kamarma bata da rai”.
      Ai kafinma ta rufe baki sun kama Nu’aymah da hanzari. Yaraf tai baya jikin Abban Adawiya alamar dai da gaske bata numfashin. Sake tashi hankalin kowa yayi, duk sauranma suka matso suna ambaton Innalillahi….
      Ɗaukarta Abban su Adawiya yay ya nufi sashen Hajjo sauran biye da shi. Yana kwantar da ita bisa kujera Ahmad na miƙo ruwa daya ciro a fridge. Amsa Abban su Abdallah yay ya zuba a hannu sannan ya shafama Nu’aymah a fuska. Ko motsi bataiba balle ai tunanin farfaɗowar ta. Sake tashi hankalinsu yayi. Ahmad da Malam ƙarami suka durƙusa da saurin kama ƙafafunta suna murzawa, suma su Abba hannayen Nu’aymah suketa faman murzawa. Amma abin tashin hankali ko motsi bataiba har lokacin.
          A yanzu kam kowa ya fara tunanin ciwon Nu’aymahr ne ya motsa, dan haka Abba Musbahu da bai jima da shigowa gidanba yay saurin faɗin, “Inaga a kira Doctor ɗinta, kamarfa ciwontane ya motsa”.
        Cikin kuka Hajjo tace, “Kirashi Musbahu, dan ALLAH ka kirashi da sauri. Innalillahi……… Zainabu karki mutu ki barmu kinji”. Kukan Hajjo ba ƙaramin sake ɗaga hankalinsu yayiba, matan ma sai faman share hawaye sukeyi.
        Duk abinda ke faruwa akan idanun Baba malam ne dake tsaye a jikin daga ƙofar falon Hajjo yana kallonsu. Kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Nu’aymah zuciyarsa ce, yana dannewa ne kawai, amma bazai yuwu ya bari son da yake mata ya hanashi hukuntata akan kuskurenta ba, dan yasan icce tun yana ɗanye ake tanƙwarashi, idan ya bushe karyewa yakeyi.
      Sun cigaba da ƙoƙarin ganin ta farfaɗo kafin Doctor ya iso, sai dai fa ko motsi babu wani sashe na jikinta dake nuna alamar zaiyi ma………..✍
Tashin hankali😪, kumuje zuwa.
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.
*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements