SARAN BOYE Page 111 to 120 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / SARAN BOYE Page 111 to 120

SARAN BOYE Page 111 to 120

SARAN BOYE Page 111 to 120

…………Motar ta ajiyesu a wani ƙauyene dan iya nan kawai zata iya shiga saboda uwar zaizayar ƙasar dake damun ƴan kudancin ƙasarmu duk ta cinye titunan. Ruwa mai uban sanyi na kwatami madam Rebecca ta samu ta sheƙama madam Chioma saboda sunyi-sunyi ta fita a motar ita da drivern madam Chioma da giya ke aiki a kanta taƙi fita.

      Firgigit ta kawo numfashi tana wani bada faɗi tamkar zata make mutum. Duk baya sukaja kam suka bata fili. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta share fuskarta tana hararsu.
     “Rebecca minene haka kuma?”.
Dariya Rebecca tayi tana miƙama yaron data ari roba a wajensa. “Inda ba hakan nai mikiba zaki tashi ne. Lokacin da ya bamu ya kusa cika kuma kinsan halinsa”.
      Zabura kuwa madam Chioma tayi ta wawuro handbag ɗinta tana ambaton Jesus. Haka yasa itama Madam Rebecca ɗaukar tata handbag ɗin suka zagaye zaftarewar ƙasar suka koma kan titi sosai. Suna tafiya suna ƙoƙarin tare mashin dake wucewa. Amma kowanne sai kaga da mutum. Sai da sukai tafiya mai nisan zango sannan suka samu mashin ɗaya. Badan zai ishesuba suka hau, dan madam Rebecca balaifi tanada jiki. Tafi madam Chioma ƙiba. Haka suka shirma cikin jejin da korayen ciyayi suka ƙawata suna nishin matsuwa. Tafiya sukai sosai kafin su isa wani ƙauye again. Anan mai mashin shima ya saukesu dan zasu hau kwale-kwale ne. Ga madam Chioma da tsoron ruwan masifa. Duk sanda sukazo wajen bokan nan a tsorace take. Shiyyasa wani lokacin tafi buƙatar Rebecca tazo mata sai ta biyata kuɗin da duk ta buƙata. Haka suka shiga kwale-kwale tanata faman ƙunshe kanta a cikin cinyoyi. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu gaɓar ruwan. Daga haka kuma suka kwashi ƙafafunsu suka nausa cikin jajenin da bazaka taɓa ɗauka akwai mutum mai numfashi a wajen ba. Amma da yake zukatansu sun bushe ko tsoro basaji. Sun iso ƙauyen da bokan yake a galabaice. Kamar yanda ƙa’idar shiga wajensa take suna isowa ƙofar fadarsa suka cire duka suturar jikinsu. Haka masu tsaron ƙofar suka basu hanya suka shiga tsirara haihuwar uwarsu (😱🤦🏻). Ba wannan ne ya firgitaniba. Dan su nasan komaima iya aikatawa zasuyi. Shigarsu wajen ne ya rikita tunanina da ɗarsa tsoron duniya a raina. Dan kuwa mutanene cike da wajen suna jiran layi kowanne tsirara yake. Abin kaico da takaici da ALLAH wadai harda musulmai a wajen, kai harma Hausawa saika samu ma’abota son duniya da ruguza lahirarsu. Manyan mutane ƴan siyasa da hasashenka bai taɓa baka ganin irinsu a wajenba sai gasu tumɓur suna zazzare idanu a fadar boka. Manyan mata masu neman duniya da gudun kishiya suma gasu nan ba’a magana. Wannan ya ƙara tabbatar min da sutura na rufawa bawa asiri a idanun mutane. Dan da yawan mutane munana ne idan ka gansu tsirara wlhy🙄.
        Sai da suka tsaya gaban wasu ƙartai akai musu wankan ƙa’ida kafin su ƙarasa su hau layi inda sauran suke. Suna nan zaune masu shiga na shiga suna fitowa har layi yaxo kansu suka shiga suma.
      ‘Wa’iyazubillah’. Ɗakin bokan cike yake da gumaka na dodannin tsafinsa ta kowace kusurwa. Suna shiga suka zube sukai sujida a gaban waɗanan gumaka. Kafin su miƙe zuwa wajen bokan dake hakimce a kujera sai kace sarki. Shima sujidar sukai masa sannan suka miƙe tsaye haihuwar tsoffinsu. Shima dai a tsirarar yake dama🤦🏻. Gashi ƙaton gaske mummuna baƙiƙƙirin matsiyacin sheɗani. Kallon madam Chioma yayi ya kece da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya haɗe fuska.
      “Yaron da kike tattali da burin mallaka yana neman ƙuɓuce miki ko? Hhhhhhhh!!!!. Ai tun farko kece kikai sakaci. Miyasa kika barsa yay aure?”.
      Kuka ta fashe da shi, “Bangaruta ba laifina baneba. Mijina nane ya cikani da daɗin baki akan ya yarda yaron ya aureta ne dan ya halakata da babanta. Shiyyasa na yarda ni kuma. Tunda nasan ka bani abinda bazai iya taɓa kallon mace da suffar mata ba”.
        “Hhhhhhh!!!!!. Yardarki kuwa ta zamar miki matsala. dan wannan yarinyar daya aura tafi ƙarfinki. A duk inda take tana zagaye da wani haske da ko iya ganinta ni kaina banayi. A yanzu haka bana iya ganin yaron ma kansa a ƙwaryar tsafina saboda kasancewarsu tare. Ke koma basa tare shima bana ganinsa a watannin nan gaba ɗaya…..”
      “Bangaruta ka taimakeni ta tsafemin shi. Na shiga uku shikenan tawa ta ƙare”.
       “Hhhhhhh taki zata ƙarene idan wannan aikin dazan miki yazam bai kamasu ba”.
      Da sauri ta nutsu tana sharar hawaye. Ya kuna ƙyalƙyalewa da muguwar dariyarsa mara daɗin ji. Kamar yanda na faɗa miki tun farko aikinmu dake kansa bazai taɓa barinsa mu’amula da mataba sai ke. dan haka ki kwantar da hankalinki wannan kam tabbatacciyar maganace hakan bazai faruba. Yanzu zakiyi ƙoƙarin rabasa da yarinyarne kawai. gaba ɗaya hankalinsa zai dawo gareki a wannan karon dan bazamuyi masa da wasa ba”.
       “Nagode Bangaruta, sai dai kumafa igiyar nan ta tukunya ta kwance, wannan shine ya girmama tashin hankalina”.
     “Karki damu da kwancewarta, mu ta wajenmu tana nan a ɗaure. Dan bazai taɓa kwanciya da wata maceba sai ke. Cike dajin daɗi ta duƙe gabansa ta sakeyi sujida🤦🏻😭. A take ya haɗa mata duk abinda zatayi akan Yoohan da Nu’aymah. Ta dire masa maƙudan kuɗin daya buƙata sannan suka fito bayan itama Rebecca ta amshi nata aka abinda ya shafeta.
     A ranar suka sake juyiwa cikin River state a matuƙar galabaice. hotel suka kama zasu kwana sai zuwa da safe su koma abuja.
_____________________
     *_VIENNA AUSTRIA_*
     Su Yoohan da basusan wainar da ake toyawa ba sunacan hankalinsu kwance. Dan wani shagon cin ƙwalam da maƙulashe na kalolon chocolate da ice-creem ya kaita. Ko sha zumamu baya faɗama Aymah shan zaƙi ba. Tako dinga lodama cikinta cike da farin ciki. Duk gargaɗin da yake mata akan tabi a sannu saboda duk zaƙin da take danƙara zai tambayetane a wajen period bata sauraresaba.
         Sun daɗe sosai a wajen, kafin su fito da ƙafa kamar yanda ta buƙata wai tanason taga gari da ƙyau. Aiko ta gani ɗin. Dan birnin Vienna ya matuƙar haɗuwa da gine-gine masu ƙayatarwa. Sai da ta fara hakkin gajiya sannan ya tsaida musu keken doki suka shiga ya maidasu masaukinsu.
        Suna isowa wanka Aymah ta shiga. Sai faman complain take wai ƙafafunta na ciwo.  Baice mata komaiba shi dai tunda itace ta ja musu shan wahalar ai. Amma da yake ta fisa baki shine take cewa shine.
    Wanka tayo ta fito tana ɗingisa ƙafa wai ciwo take mata. Da kallo kawai ya bita shi dai, ya ɗan girgiza kansa yana miƙewa da faɗin, Silly girl maganinki kenan ai”.
       Juyowa tai tana hararsa. Sai dai shi baimasan tanayi ba dan tuni ya shige toilet ɗin abinsa. Koda ya fito ya iske har tayi shirin barci. Sai dai bata kwanta ba. Tana kwance a sofa tana kallo. Shirin barcin shima yayi. Yana kammalawa wayarsa tai Ring. Miƙewa tai zata kawo masa sai taga ya nufota. Hakan yasa ta koma ta zauna harya ƙaraso. Yana amsa yaga Rich ne, sai ya maida kallonsa gareta. “Please sa hijjab muje mu ƙarasa maganarnan yana jiranmu”.
      “Okay” ta faɗa tana miƙewa. Ta ɗauki hijjabin sallarta ta saka tare da zura Slippers suka fito harabar hotel ɗin wajen swimming pool ɗin nan da mutane keta shanawarsu tamkar rana. Daga can gefen garden ɗin hotel ɗin suka koma. dan shima dai mutane ne keta hidimarsu. Aymah ta fahimci mutanen nan sam basa banbance dare da rana halan. Dan koda yaushe su dai hidimarsu suke hankali a kwance.
       Zama sukai inda suka iske Richard. Ta gaishesa da ƴar sakewa fiye da ko yaushe. Shima fuskarsa da murmushi ya amsa mata harda tsokanar wai ta ƙwace masa aboki.
      Murmushi tayi kawai batare datace komaiba. Shi dama Yoohan bai saka bakinsa ba, sai dai ya bama Rich ɗin hannu sun gaisa.
      Bayan an kawo musu Coffee ɗin da yay musu order itama Aymah aka kawo mata lipton data buƙata sai suka fara tattaunawa akan yanda zasu ɓulloma lamarin. Suna gamawa da maganar gidansu Aymah Rich ya turama Joseph saƙo akan ya janye masa hankalin Yoohan.
     Haka kuwa akayi, ko mintuna biyu da tura saƙon ba’ayiba kira ya shigo wayar Yoohan. Ɗagawa yay suka gaisa da Joseph batare da ya tashi ba. Sai daga baya kuma ya miƙe saboda magana da Joseph ɗin yace yanason suyi.
           Yana barin wajen Rich ya kalli Aymah data ɗauke kanta daga garesu tana kallon wata mata da yaranta twins da babansu dake gefensu. Sai soyayyarsu suke zubawa da tattalin ƴan yaran nasu. jitai sun bata sha’awa sosai har tana kwatanta kanta da Yoohan ace yaran nasune wai (ƴar baba malam an fara hankali kenan🤣).
      Gyaran murya da Rich yayine ya sakata juyiwa taɗan kallesa. murmushi yayi shima dan haka kawai yay zargin abinda take tunani akan mata da mijin da yaransu.
       “Inason muyi magana Please, sai dai tsakanina da ke ne banason Yoohan ya sani”.
      Cike da mamaki ta tsura masa idanun tana tsuke fuska. Saurin girgiza mata kai yayi yana murmushi. “Am sorry sister akan gidansu ne karki zargi komai”.
      Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye da ɗan shafa gefen wuyanta alamun taji kunya. Shima sai ya ƙara murmusawa dan ta birgesa. Hakan na nufin a duk inda take zata karema ɗan uwansa mutuncinsa. Wayarsa ya miƙa mata tare da miƙewa yabar wajen. Can ya koma inda Yoohan ke zaune yana waya dan ya fahimci shima hankalinsa na kansu.
      Binsa da kallo Nu’aymah tayi. sai kuma ta buɗe video ɗin data gani akan wayar, da alama shi Rich ɗin ke buƙatar ta gani. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba, saboda cinkaro da kanta a ranar data shiga ɗakin papa ta ɗakko hoto. Sai dai iya falone. har shigowar Papa da Andrew falon. Shigarsa bedroom ɗin da fitowarsa da sake komawarsa. Harma fitarta da kayan harƙallar papa da suke magana akai shi da Andrew. Cocaine ce da wasu ƙwayoyi, sai abinda ke cikin ɗayar jikkar dai bai buɗeba, hakan yasa batasan minene ba. Hannu tasa ta sharce zufar data tarar mata a goshi. Ta ƙara playing ɗayan video ɗin dake a ƙasan wancan shima. Shi kuma papa ne da wasu mutane yana bada kwangilar a kasheta duk sanda suka dawo Nigeria. Randa aka kashetan kuma a kashe baba malam shima. ‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’ ta shiga maimaitawa tana kallon inda Yoohan da Rich suke zaune. Ganin Rich nata jan ra’ayinsa ga barin kallontane ya sakata kauda kanta tana taunar lip ɗinta. A ranta kuwa sake jinjina lamarin papa take da jin tsanarsa a ranta. Lallai saita tona dukkan sauran sirrin mutumin nan duk da kasancewarsa mahaifin mijinta. To amma shi wannan Richard ɗin mi yake nufi da bata video ɗin ta gani?.
     Kafin ta nemo amsar tambayarta taga sun miƙe sun nufota. Fita tai daga cikin folder ɗin da sauri ta ajiye masa wayarsa da ƙoƙarin control ɗin kanta dan kar Yoohan ya gane.
        Rungumeta Yoohan yayi cike da tsantsar farin ciki yana faɗin, “Oh my Sweetheart ke haske ce a rayuwarmu. Rich yace yanason zama musulmi”.
       Cike da razana Aymah tace, “What?!!”. Sakinta Yoohan ɗin yayi yana dariyar farin ciki da jinjina mata kansa. kafin yace wani abu Rich yace, “Tabbas abinda X-man ya faɗa ashine gaskiya Sister. Zama da mahaifinki ya ƙwaɗaitamin son kasancewa musulmi. Hakan ya ƙara tasiri ne a raina a ɗazun dana ganku kuna salla abin ya birgeni”.
      Kallonsa kawai Nu’aymah take cike da tuhuma. Dan gani take wani ƙullinne kuma yake shirin musu ta hanyar shiga musilinci.
     Fahimtar hakan da yayine ya sakashi girgiza mata kai idanunsa na kawo ruwan ƙwalla. “Na rantse da ALLAH ni Richard inason shiga musilinci ne da zuciya ɗaya bada wani daliliba. Ki yarda ke haske ce a garemu kamar yanda mijinki ya faɗa”.
        Numfashi Aymah ta sauke tare da furzar da iska ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata a hankali. Sai kawai ta faɗa jikin Yoohan ta rungumesa tare da rushewa da kuka. “I love you so much Yah Yoohan”. Ta faɗa a bazata tana ƙanƙamesa da ƙyau.
       Da sauri Yoohan ya ɗagota yana kallon fuskarta. “Cikin rawar muryar zuwan bazatan maganar yace, “Really? Please sake faɗa naji dan ALLAH”.
       “Babu ƙarya ko yaudara a maganata. Da gaske ina SONKA Yah Yoohan. Na rantse da ALLAH ina sonka da gaba ɗaya zuciyata”. Ta kuma rungumesa.
      Ai gaba ɗaya yama manta da wani Rich dake wajen. cikin sauri yaja hijjab ɗin jikinta ya shige ciki tare da zame mata fuskarta itama ta koma ciki. lalubar bakinta yayi ya manne da nashi. Duk da kunya da tsoron abinda ya faru dake cikin ranta hakan bai hanata tayasa abinda yakeyiba batare da tasan ta zurma ba.
        Dariya Rich ya sanya musu tare da miƙewa yabar wajen, can inda suka baro da Yoohan ya koma ya zauna yana kallon wani wajen daban, zuciyarsa fal da wani irin farin ciki da shi kansa baisan na minene ba.
         Da ƙyar Nu’aymah ta ƙwaci kanta daga hannun Yoohan da ke neman sakin layi. Ta sauka daga jikinsa tare  tabar wajen da gudu. Kasa motsawa yay saboda kasala data saukar masa. Ya kife kansa a table ɗin kawai yana sauke numfarfashi a jajjere.
      Ganin wucewarta da gudu ya saka Rich tasowa inda Yoohan yake. Damtsen hannunsa yaɗan buga da faɗin, “Mara mutunci, a gabana ma babu ɗaga ƙafa”.
        Gani kawai yayi Yoohan ɗin ya miƙe ya rungumesa yana faɗin, “Thanks you Rich, thanks you so very much. Gashi a dalilin gane gaskiyarka ta faɗamin kalma mai tsada dana fidda ran samu daga gareta. Wlhy ina sonta fiye da zaton mai hasashe Rich. ashe itama zata soni. ALLAH na gode maka. Rich ka zama sanadin farin cikina”.
      Dariya sosai Rich keyi ta jin daɗin ganin farin cikin Yoohan ɗinsa da yake tsananin so da ƙauna. Suka zauna kowanne fuska ɗauke da murmushi. Cikin ɗage gira Rich yace, “Dama makauniyar soyayya kakeyi kai ashe?”.
       “Makauniyar da ko idanu ba’a yanka mataba kuwa Rich, amma yanzu ta sanadinka gashi har numfashi ta samu”.
      “To Alhmdllh, dama ni na fahimci tana sonka wlhy. Kawai dai akwai yarinta tattare da itane. But ko dai yayane ma kun dace. Dan na jima banga masoyan da suka dace da junaba irin ku. Dan haka Mr Lover Congratulations joooh”.
        “Thanks you dear. Congratulations too. Nayi farin ciki da kai saurin gane gaskiya. Ya rabbi ka karɓi tubanmu ka gafarta mana”.
     “Emen dear. Yanzu nawane zan biya? A wajenwa kuma zan biya”.
     Fuska Yoohan faɗaɗe da murmushi yace, “Shi muslinci ba’a biyan komai a wajen shigarsa. Kalmar shahada kawai zaka faɗa. Amma bara na kira Uncle first”.
      Kai Rich ya jinjinama Yoohan. Ya ɗauka wayarsa yay kiran baba malam cikin sa’a kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yay masa bayanin komai cike da jin kunyar da Aymah ta sakashi a ciki tun ɗazun. Dan duk yau ma ya kasa kiran baba malam ɗin. Yanzun ma shaf ya mantane saboda ɗokin musulintar Richard.
        A take baba malam yace, “Ina mamana? Duk bayanin dazan muku itama zata iya yinsa insha ALLAHU Yahya”.
     Cike da jin kunya Yoohan yace, “Tayi barcine Uncle. Gashi kuma Rich ɗin zai dawo gida nan 9ja gobe. Idan kuma ya bari sai yazo wajenka to”.
        “A’a Yahya. Gara dai ya cikasa niyyarsa dan ranmu ai ba’a hannunmu yakeba. Nasan kaima zaka iya masa bayani akai. indai zaka iya tuna duk yanda kayi lokacin daka musulinta”.
      “Insha ALLAH Uncle. Amma zanso kana saurarenmu”.
     Dama baba malam ya bashi. Dan haka Yoohan ya maida kiran video call. A take Yoohan ya bama Rich kalmar shahada. Bayan ya maimaita baba malam ya faɗaɗa masa bayanai masu muhimmanci tamkar yanda yayma Yoohan a wancan karon. Sai ga Yoohan da Rich suna hawaye. Sunja lokaci mai tsaho kafin baba   bashi zaɓin suna. A take Rich yace ya bashi dama ya zaɓa masa kowanne.
     Cikin jin daɗi Baba malam yace, “Akwai sahabban manzon ALLAH da sunayensu sukai fice a garemu, bara na lissafa makasu, tare da na Annabawan ALLAH da Yahya ya samu ɗaya daga cikin sunayensu shima”.
    A tare suka jinjina masa kai.
   “Abubakar, Umar, Usman, Aliy…….”
Kafinma baba malam ya ƙarasa Rich yay saurin faɗin, “Uncle inason Omar”.
        “Masha ALLAHU Son. Daga yau kazama Umar. ALLAH yasa ka zama mai koyi da ƙyawawan halayen Umar da gaskiyarsa da jarumtarsa harma da yawan ibada”.
       A tare suka amsa da amin.
Daga haka suka sake ɗan tattaunawa sannan sukai sallama da shi. Masaukin Rich suka nufa. Inda Yoohan ya koya masa wanka da alwala harma da salla. Daga haka ya barsa. Saboda gobe idan ALLAH ya kaimu Omar (Rich) ɗin zai koma Nigeria.
      Sun sake rungume juna suna hawaye da sake godema UBANGIJI. Sannan sukai nafila raka’a biyu a tare ta godiya ga ALLAH. Omar (Rich) yay sallar Magrib da isha’i dan lokacinsu bai gushe ba har sai alfijir ya keto. Musamman ma isha’i.
       Daga haka sukai sallama Yoohan ya nufi nasu masaukin cike da ɗoki da farin ciki.
      Nu’aymah dake kallo tanajin motsin buɗe ƙofar tai azamar kifewa rubda ciki dajan filo ta tura kanta ciki. Murmushi yayi yana ƙarasa shigowa dan ya rigada ya ganta. Television ɗin ya kashe tare da wutar ɗakin lokacin da yake ƙoƙarin hawa gadon. Cikin nutsuwarsa ya kwanto bayanta yana sauke ajiyar zuciya tare da saka hannu ya ɗauke filon data tura kanta a ciki.
       “Wayyo Hajjo ƙaton nan zai ɓalla miki jika”. Tai maganar cike da rikicin kunya da nauyinsa daya sakar mata.
       Murmushi yayi da rage mata nauyinsa sannan ya birkitota. Da sauri ta kanannaɗe masa jiki dan batason su haɗa ido.
       Hannunsa ya tura cikin rigarta yana ɗora bakinsa akan kunnenta. Cikin raɗa yace, “I love kunyankin nan my sweet angel, my sweetheart my Heartbeat. My everything”. Ya ƙare maganar da ɗan cizar kunnenta kaɗan.
       Kukan shagwaɓa ta saka mata tana murza ƙafafunta a jikinsa wai saita rama. yanda taketa masa mutsu-mutsu a jikine ya nema susutashi. ƙwaɗayin da yaketa dannewa tun da rana ya kasa dannuwa. Cike da kasala da tsumar jiki ya lalubi bakinta ya manne da nashi. Tun yana tunanin tsayawa iya kiss ya rage zafi har hakan ya nema fin ƙarfin ƙoƙarin nasa. Gaba ɗaya ya birkice mata. Tun tana biye masa da wauta harta koma masa kuka dan bata manta wahalar datasha daren jiyaba.
        Duk yanda Yoohan yaso haƙuri ya bar Nu’aymah hakan ya gagara. cike da fita hayyaci ya fara sarrafata. Yau ma dai an maimaita na daren jiya, sai dai kukanta ya sakashi taƙaita tafiyar batai nisan zango kamar ta daren jiya ba ya tausaya mata dan yasan bata gama dawowa hayyacinta ba.
        A take kuwa jikinta ya ɗime da zazzaɓin wahala. Hardasu rawar sanyi. Yasan ya ƙara laifi mai girma. Dan haka yayta lallashi da ban haƙuri harya samu ya kimtsa mata jiki yau ma yay gashi dan yasan zataji ciwo a wajen balle gashi yayi fami ne.
       Da taimakonsa tayi wankan tsarki, shima yayo sannan ya taimaka mata suka fito. Lallaɓata yay tasha yogurt da maganinta, kafin ya ƙara mata shirin barci. Sai da ya sake kimtsawa shima sannan ya hawo gadon ya rungumeta dan harma ta fara barci. Irin allurar ɗazun da rana ta rage raɗaɗi yay mata. Kuka ta fasa masa jikinta na matuƙar rawa. Yay saurin haɗe bakinsu waje guda. Sai da ya janye allurar sannan ya janye bakin yana furzar da iska tare da rungumeta da ƙyau a jikinsa yana shafa bayanta da faɗin, “Am so sorry sweetheart. Please forgive me”.
         Luf tayi a jikinsa tana zirar da hawayen. A haka barci yay gaba da ita yana faɗa mata kalamai masu sanyi cikin kunne da hura mata iska mai daɗi. Jin ta fara sauke numfashi na alamar barci shima saiya shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Yana ƙara jin ƙaunarta mai tsanani tana ratsa masa zuciya da dukan jikin sama gaba ɗaya. Ta zama ta farko a zuciyarsa. Ta farko a sirrinsa. Ta farkon haskama rayuwarsa hanya. Ta farko…. Ta farko…. Da yawa harma baisan iyakaba. Insha ALLAH kuma itace zata zama ta farko har ƙarshen rayuwa🤗😍.
*_Muma ALLAH yasa mu zama na farko ta ƙyawawan hanyoyi ga mazajenmu har ƙarshen rayuwa my dear fans. Ba dole sai kin kasance matar farko ba zaki zama ta farko😋😘. Kota huɗu kikaje ƙyawawan halayenki zaisa ki zama ta farko😍. Uwar gida kema dage ki riƙe gam kar a ƙwace miki ta farko😉🤗😅._*
_________________
                  Washe gari haka Nu’aymah taita zubama Yoohan shagwaɓa da raki yana faman lallaɓata da lallashinta. Tasa dole ya kira mata baba malam da Umm da hajjo. Inda anan itama hajjon ta fahimci takwararta ta kai mutuncinta gidan aurenta. Hakan ya mata matuƙar daɗi harta kaita da yin sujidar godiya ga ALLAH. Cike da tsantsar alfahari da jin daɗi ta kira Ananah ta sanar mata. Sosai Ananah taji daɗi tana godema ALLAH daya wanke Aymah cikin sauƙi a garesu bisa hikimarsa da rahamarsa. Daga haka sukai gum da bakinsu suna jiran bayyanar gaskiyar ga kowama cikin hikimar UBANGIJIN al’arshi.
      Da ƙyar Yoohan ya samu yaje sukai sallama da Omar (Richard) da zai wuce Nigeria a yau. Daga haka ya dawo wajen ƴar amaryarsa sarkin shagwaɓa da shiririta. Haka suka kasance a gaba ɗaya wannan yinin cike da so da ƙauna. Dan itama tun tana nokewa da ƙunshe-kunshe harta saki jikinta duk da dai akwai kunyar tattare da ita, saboda ta kasance tarbiyyarta tun fil’azal………..✍
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 65
…………..A hankali soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta cigaba da shiga tsakanin ma’auratan masu banbancin yare da yanki cike da birgewa. Yayinda Aymah ke matsayin malama ga Yoohan a ɓangaren ilimin addini shima sai ya zame mata malami a ɓangaren sanin soyayya da rayuwa. Dan sosai yake yawo da ita a lungu da saƙo na ƙasar Austria har wasu jihohinma suna zuwa yawon buɗe ido.
      Tun tana tsoro da masa raki a shimfiɗa harta fara sakin jikinta da sabawa. Dan jarumin nata namijin gaskene babu wasa. Baya takura mata yanda zata wahala. ba kuma ya barinta ta shagala.
      Sai ga Nu’aymah tai wani irin murjewa da ƙibarta na dawowa, (kunsanfa wannan harkar na gyara wasu matan harma da mazan🙈, shiyyasa da yawa amare farkon aurensu zakaga sunyi ɓulɓul da su🏃). To ga Nu’aymah ma dai an dace. Balle abin ya haɗa da kwanciyar hankali data samu, babu mai hantararta babu mai damun rayuwarta. Abinci saita zaɓa. Kullum zatai waya ko video call dasu Umm. Ga lafiyar jikinta Alhmdllh sai ƙaruwa take ƙarayi dan tana shan maganinta da ƙa’ida kasancewar Yoohan tsaye yake akanta da tsantsar kulawa.
      Takanji yana waya da papansa da momynsa (Madam Chioma) sai dai yanda bai taɓa cewa gashi su gaisaba itama bata taɓa nuna sha’awar hakanba. Garama Momy ranar ta kira yana wanka har sau uku. Ganin wayar na wajenta ya sakata ɗagawa suka gaisa. Sai dai yanda Momyn ta amsa mata a daƙile ya sosa ranta. Dan ta fahimci har yanzu da sukai nesa da juna ba ƙaunarta takeyiba. Su Momy Destiny ne dai ta gaisa dasu kusan sau uku-uku harda su Victoria. Amma su tom and jarry mama debora ko yaya jiki basu taɓa aiko mata da shiba balle suce zasu gaisa da ita a waya. kuma taji ranar duk sai da suka gaisa da Yoohan. Gebrail nema ta lura idan ya kirashi baya ɗagawa, daga bayama sai taga ya sakashi a black list.
         Gaba ɗaya ta hana Solomon musu gadi. Dan yanzu duk inda zasuje tuburewa take akan itadai bazataba inhar sai Solomon ɗin ya bisu. Hakan yasa Yoohan ya yanke shawarar kawai ya sallamesa ya koma Nigeria, dan baiga amfanin kisan kuɗin da yake ba a dalilin zaman Solomon ɗin tare da su.
       Randa ya samu Solomon da maganar komawa Nigeria hankalinsa yayi matuƙar tashi. Ya kira iyayen gidansa ya sanar musu da hukuncin Yoohan ɗin. Hakan yasa papa kiran Yoohan ya nuna masa bai amince da dawowar Solomon gidaba. Dan bazai yarda ya barshi shi kaɗai yana yawo ƙasashen duniya a cutar masa da shi ba.
       Yanda Aymah ta tubure kuma akan indai Solomon zai cigaba da kasancewa da su sai dai ita ta koma Nigeria wlhy yasa kan Yoohan ɗaukar zafi. Yayima Aymah lallashin duniya akan tabar zancen Solomon tunda papa ya dage amma sam taƙi saurarensa. har takaisu dayin ɓacin rai ranar akai barci kowa na ƙarshen gado. Washe garima taƙi kulasa shima ya shareta. Sai daga baya yaso su shirya taƙi. (A raina nace hummm Yoohan bakasan kafiyar Aymah bane ba).
        Wannan tuburewar tata ya ƙara bashi haushi. Harya yanke shawaran ta shirya ta koma Nigeria tunda bazataji lallashinsa ba.
      A mamakinsa kuwa sai yaga ta hau haɗa kayanta. Dan itafa tabbas tayi alƙawarin bazata sake zama inuwa ɗaya da Solomon ba. Dan tsaf ta gama fahintar wannan nanema Yoohan ɗin da yakeyi akwai wata a ƙasa. tabbas da gaske akwai abinda su papa suke ɓoyewa game da Yoohan ɗin. Inba hakaba minene na nana masa guard a duk inda yake. Sannan sau biyu tana kama Solomon na waya da papa. Na farko yare taji yanayi sai turancin daya saka kaɗan ya sakata fahimtar papa ne. na biyu kuwa da turanci sukai magana. Hakan ya sata jin komai akan duk wani motsinsu Solomon yana sanarma papa. Dan a ranar shi papan har maganar ya kamata ta koma Nigeria yayma Yoohan. Amma shi Yoohan ɗin ya nuna baya bukatar yana wani ƙasa matarsa na wata ƙasa. A ransa kuwa ya ɗau alwashin Aymah bazata ƙara zama a gidanba baya kusa saboda Gebrail. Dan ba ƙyalesa yayiba. ya ɗau alwashin duk randa ya dira Nigeria sai Gebrail ya yabama aya zaƙinta.
      Ganin da gaske shirin tafiyar take ya sakashi sakkowa daga fushinsa shi. Ya fara lallashinta amma taƙi saurarensa. Saima kuka da take masa mai cin rai. Daga ƙarshe dai dole ya kira baba malam akan dan ALLAH ya lallasar masa ita. Dan shikam a yaune ya kuma tabbatar da borin Aymah bana wasa bane. Dan ko abinci taƙi ci, taƙi shan maganinta. ta birkice masa ita kawai ya kaita airport ta wuce gida kokuma ta tafi da kanta.
       Murmushi baba malam yayi kawai yana girgiza kansa. kafin ya sauke ajiyar zuciya ya farama Yoohan nasiha. Daga ƙarshe ya koma masa faɗa akan sakacinsane ai ya saka Nu’aymahn iya bijirema umarninsa. Dan haka ya nutsu sosai wajen riƙe gidansa da ƙyau. dan su mata wani lokacin zuma ne sai da wuta. Sannan wutar kara ne sai da iji. Ba’a sakaci da su sannan ba’a musu tsauri da yawa. ana riƙesune tsaka tsaki sai a samu jin daɗin duniya.
     Sosai Yoohan yaji shawarar sirikin nasa. tare da ƙarajin ƙaunarsa a cikin zuciya da ɓargo. Daga haka ya haɗashi da Nu’aymah kamar yanda ya buƙata.
        Zata fara masa kuka baba malam yay mata jan ido. faɗa sosai yay mata akan tashiga hankalinta mijinta ba abin rainawarta bane. Idan batai wasabama sai yazo har Austria ɗin ya hukuntata. Sai da ya tabbatar tayi laushi sosai da faɗansa sannan ya koma yimata nasiha. Daga baya kuma ya buƙaci jin dalilinta na takurawa akan Solomon ya barsu.
           Kasancewar Yoohan yana koyon hausa a wajenta ya sakata yin amfani da manya-manyan hausa wajen yima baba malam bayani akan abinda ta fahimta da zaman Solomon tare da su. Ta kuma bashi labarin abinda ya faru akan maganar hoto, harma da videos ɗin da Omar (Richard) ya nuna mata kwanakin baya da suka shuɗe. shi kansa baba malam ɗin hankalinsa yayi matuƙar tashi. sannan zarginsa ya fara zama gaskiya kenan. Albarka ya saka mata sosai da faɗan rashin sanar masa zance hoton da tayi tun a wancan lokacin. Duk da ya fahimci mijinta take son bama kariya akan matsalar da gajeren tunaninta ya kasa faɗaɗa mata. Yace,
      “Mamana yanzu ina hoton yake?”.
Hawayenta ta share da jan majina. Tace, “Abba yana nan Nigeria a cikin kayana”.
       “Masha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Saka wani ya ɗakkosa bazai yuwuba. Dan haka zamuyi haƙuri har ku dawo ƙasar sannan musan ta inda zamu ɓuloma al’amarin. Batun Solomon kuma bata hanyar rikici zaki yakicesa a jikin mijinki ba. Cikin hikima da wayon da ALLAH ya baku na mata da tarbiyyar Umm ɗinki zakiyi amfani wajen sakashi ya sallamosa. Ko kin taɓa ganin muna rikici da Umm ɗinki ne a gidannan?”.
     Kanta ta girgiza masa tamkar tana a gabansa. Sannan tace, “A’a Abba”.
      “To amma shine ke zakije kina rikici da mijinki. har yana taroki kina ƙwacewa? Wannan shashanci ne ai. Sannan kina zubar mana da kimar tarbiyyar da muka baki. Mu mazafa da kike gani munada wuyar sha’ani dason nuna mulki a gidajenmu, shiyyasa duk macen data fahimci haka ta iya zama damu mutane suke ganin kamar ta mallake mijintane  nanko ba haka baneba. juriyace kawai da iya zama da mijin tayi. Ki kula da ƙyau. Mahaifiyarki abin koyice a gareki akan zaman takewar aure. Babu wanda zaice ga Jannat da wata matsala a gidan aurenta. da daɗi babu daɗi ta jure ta shanye komai. Yaya muka kwana yaya muka tashi ta jurema ranta. har takai wasu na ganin tsorona takeji da yawa. Nanko ba hakan bane. Mune muka san sirrin kammmu fiye da duk wanda ke zagaye damu. Karna ƙarajin haka kinji ko?”.
       Nu’aymah na sharar ƙwalla tace, “Insha ALLAHU Abba bazaka sake jiba”.
       “To Alhmdllh naji daɗin hakan kuwa. ALLAH yay miki albarka keda mijinki damu baki ɗaya”.
      Cike dajin kunya ta amsa da amin. Daga haka suka ajiye wayar. Ta ɗan saci kallon Yoohan dake kwance ciki sofa idanunsa a lumshe tamkar mai barci. Tashi tai a hankali taje ta ajiye masa wayarsa a saman ciki batare datace komaiba.
     Shima buɗe idanu kawai yayi ya bita da kallo harta shige toilet.
_________★★
        Batare da tasan yaya zancen Solomon ya kasanceba washe garin da suke cika sati biyu. ta kama randa zasu bar ƙasar kenan. Bayan sun kammala shirinsu tsaf sukaje asibiti aka ƙara tabbatar da ingancin lafiyarta, sukai sallama da su Dr Sophia kuma. Yoohan ya ƙara siya mata sauran magungunanta suka nufi airport cike da kewar ƙasar Austria da garin Vienna. Harma da mutanen cikinsa.
           Yanzunma suna nane da jelar tasu Solomon. Sai dai kuma suna zuwa Airport ta fahimci Solo Nigeria ya nufa. ita da shi kuwa U.S zasu wuce dan Yoohan ya koma hutu. Zai kuma gudar da wani aiki a ƙasar United states ɗin, da wani taron manyan likitoci da zasuyi kuma insha ALLAH.
        Duk da basu shiryaba har yanzun ita da shi sai da ya ga farin cikin komawar Solomon 9ja a fuskarta. Shidai hakan na bashi mamaki. dan ya gaza fahimtar ƙiyayyar dake tsakanita da Solomon. Shi kansa Solo ɗin ya kula baison Aymah. Sai dai baya iya nunawa a gabansa saboda shakkarsa da yakeyi. shi kuma bai taɓa nuna masa ya fahimta ɗinba dan yanason aje inda zai taka masa birki akan matarsa.
      Shi kansa Solomon sai da sukaje airport ya fahimci Nigeria zai komai. Gashi babu damar kiran papa ko madam Chioma dan suna a tare. Sai dai zuciyarsa na ƙara jin zafin Nu’aymah. Dan ransa ya basa itace sanadin komawar tasa tabbas. Musamman da yaga yanda taketa faman moso. Dan ya fahimci kwana biyun nan daga ita har ogan suna cikin rikicine ko damuwa oho bai gama tabbatarwaba dai.
      Jirgin su Solomon ne ya fara tashi zuwa Dubai. daga can zai hau Jirgin Nigeria. Ya tafi cike da alkairin da Yoohan yay masa da takaicin Nu’aymah da tsana mai tsanani. Dan shi baimasan ina zasujeba a yanzu haka. Solomon na wucewa da kamar mintuna ashirin da biyar suma nasu jirgin ya ɗaga zuwa U.S. yana ta wajen Window tana gefensa a cikin jirgin. Sai dai ya ɗauke fuska a binsa gashi ya ɗaureta tamau. Daga ƙarshema saiya kunna lap-top da liƙa earpiece a kunne ya hau kallon film. Duk da ran Nu’aymah ya sosu saita fuske tai kamar bama tasan da zamansa a wajenba. Koda akazo tambayarsu mi zasuci catai bata buƙatar komai. Shi kuma yasa aka kawo masa coffee da biscuits.
         Lokacin da jirginsu ya sauka a U.S Nu’aymah barci takeyi. Hakan yasaka Yoohan shafa mata fuska. Sai dai tana buɗe ido ya ɗauke kansa tamkar bashine ya aikataba. Itama duk da ta fahimci shine ya tadata sai ta watsar da shi ta basar. Handbag ɗinta ƴar ƙarama kawai ta ɗauka tai gaba. Shi kuma ya jawo trolly ɗinsu sai lap-top bag ɗinsa a hannu. Yana biye da ita a baya. Sai dai da suka sakko dole ita ta koma bayan nasa dan ba sanin hanya tayiba. Da wannan damar ta ware ido tana kallon airport ɗin daya amsa sunansa airport. Sai dai ta haɗiye mamakinta a rai wai kar Yoohan ya rainata da ƙauyanci😂.
      Taxi ya ɗauka musu drop. Koda suka shiga nanma dai kanta naga Window tana kallon birnin da mutanen cikinsa. Daga haka suka isa wani haɗaɗɗen gida daya amsa sunansa gida. A tunaninta gidan nasa ne. sai dai batasan haya ya kama musu ba dan a yanzun baya buƙatar zaman hotel ɗin da ita. sannan yanason barinta anan U.S ɗinne dan yasan bazai yuwu yayta gantali da ita duk inda yakeba. Inba wajen daya san zai iya yin sati biyu kwana goma ko sama da haka ba. Amma kamar tafiyar kwana uku ko biyu zuwa sati ɗaya zai iya barinta yaje ya dawo. Inba dai buƙatar tafiya da ita taga duniya tasa suje tareba.
      Komai da zasu buƙata na gida akwaisa a cikin gidan. Shopping ɗin abinci kawai zasuje suyi da kansu saiko suturar sakawa da sukazo da kayansu. Harga ALLAH gidan ya matuƙar burge Aymah harta kasa ɓoye shauƙin hakan a zahiri.
       Duk da yaji daɗin yanda tai farin ciki sai ya basar bai nuna mataba. Ya fara shiga ko’ina ya duba gidan da ƙyau. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata tamkar yanda ya gani a yanar gizo daya kama gidan sannan ya shiga wanka.
      Yana fitowa Nu’aymah dake kwance a gado ta miƙe itama ta shiga dan wankan take buƙata itama saboda gajiya. Koda ta fito zaune ta samesa a bakin gadon yana musu order ɗin abincin ta wayar landline. Da alama dai gidan abincin yana kusa da sune, kokuma yanada alaƙa da masu gidan abincin dama can.
     Sai gashi kafin ta gama kimtsawa tai sallar magriba da lokacinta ya shiga an kawo abincin. Shine ya fita ya amso. Sai dai bai dawo bedroom ɗinba yay zamansa a falo. Sallama acan yay abinsa.
         Wani mahaukacin yunwa Aymah takeji. Hakan yasa bayan ta idar da salla ko hijjab bata cireba ta biyosa falon. Dan bazata iya basar da cikintaba ta halaka a banza a wofi. Turus tayi tana binsa da kallon mamakin ganin yanda ya baje yana ɗora abinci a cikinsa. Ta kumbura baki ƙwalla na cika mata idanu. Cike da fushin data koya kwana biyun nan ta juya zata koma bedroom ɗin. Sai dai kuma caraf taji an riƙi mata hannu. Ƙoƙarin fisgewa ta farayi hawayen da take riƙewa na zubo mata a guje saman kumatu.
      Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya dawo da ita a falon. duk yanda take watsal-watsal da faɗin ya sauketa bataso bai kulataba. Ya zauna cikin lallausar zagayayyar kujerar da aka ƙawata falon da ita kalar royal blue tana a jikinsa. Cikin hawayen da takeyi ta shiga kaimasa ƙananun duka a ƙirji da faɗin ita ya saketa bataso. Tunda yabar sonta yaje ta haƙura ta barma duniya dasu Miracle dake addabarsa da text massege kullum shi.
         Zancen nata yaso bashi dariya. Dan haka ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa akanta yana ƙoƙarin riƙe hannayenta da take kaimasa duka a ƙirji. A ransa kuwa yana sake jinjina rikicinta. Duk da ransa na raya masa wani abu game da saurin fushinta na kwana biyun nan. Sai dai bai tabbatarba dan ya san inma shine to ƙaramine kuwa sosai.
     Bakinsu ya haɗe waje guda. Tun tana turesa harya samu nasarar maida mata jiki laƙwas ta fara bashi haɗin kai. Da ga ƙarshe ya ɗauki abarsa cak suka shige bedroom inda zaiyi lallashi ɗan gaske na zallar ƙauna da babu gaurayen algus a cikinta😵. Saiga mutuniyarkun muna funfun dake faɗin zata barma duniya dasu Miracle tai luf kamar bata gidan😏😧.
            (Su Aymah babu aji🏌😑)
Sai da suka gama wadata juna da farin ciki yanda ya kamata. Yoohan ya kalli Aymah dake lafe a jikinsa idanu a lumshe alamar barcin nata na ƙa’ida zai ɗauketa. Dan duk sanda hakan ta kasance a tsakaninsu sai tayi wannan barcin. Shiyyasa yake kiranta raguwa.
        Guntun murmushi yayi da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta tare da ja mata hanci. “Silly girl! Babu abinda ta iya sai jan mutane faɗa”.
      Lumsassun idanunta da basu gama washewaba ta buɗe a kansa. Sai kuma ta tura masa baki tana maidawa ta rufe tare da tirza ƙafarta dake jikinsa tace, “Tab, kai wama ya kaika iya neman mutane faɗa”.
       Sake jawo bargon data zazzame da ƙafa yayi ya lulluɓesu da ƙyau yana ƙara sakata jikinsa. “Nine ma mai neman faɗan kenan?”.
     “Sosai ma. Tunda ai kaine dai kasa akayi wannan faɗan”.
         Dariyar data bashi ce ta sakashin yin guntun murmushi. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta yana sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu. “ALLAH na gode maka daka mallakamin ƴar rigimarnan tawa. Tare da mai ramamin gashinan yazo”.
         “A ina?”.
Tai tambayar cikin yanayin barcin daya figeta.
        “Mi kikeci na baka nazuba, zaki gani ai”. Ya faɗa yana miƙewa zaune da ita a jikinsa. Cike da shagwaɓa tace, “Ni wlhy barci nakeji”.
      “To muje ayi wanka, sai kizo kiyi Sweet girl ɗin Yahya”.
      Da taimakonsa sukaje akayo wankan. Dan barcin da bataiba na bayan lobewa ne cike da idanunta. Suna fitowa kuwa ta zube a gadon ta fara. Kayan barci ya ciro mata yazo bakin gadon ya zauna yana kallonta na tsayin mintuna uku. Hannunta ya kamo ya na kallon tafin, kafin ya juya ya tsurama yatsun idanu suma na kusan minti ɗaya. Ya miƙe inda ƙafafunta suke ya durƙusa a gaban gadon yana kallon yantsun suma na tsayin mintuna. Sassanyan murmushi ya sauke da ajiyar zuciya, ya sumbaci ƙafafun duka biyu sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Sake tsirama fuskarta ido yayi na tsahon wasu mintunan cike da so da ƙauna, kafin ya ranƙwafa kanta yana sumbatar bakinta da kumatunta, idanun har wuya. (Ni mai ɗauka muku rahotonma sai yaban dariya. Dan na kasa fahimtar inda ya dosa😂😑).
      Kayan barcin ya sanya mata, ya gyara mata kwanciya, shikuma ya koma bayin ya ɗauro alwala ya dawo yay zaman karatun al-qur’ani. Dan tunda suka fara rigimarnan ta Solomon kota ɗora masa karatun ba fahimta yakeba da ƙyau. Haka yake kwata-kwata bayason damuwa. Koyaya irin haka ta faru da shi duk sai ya fita hayyacinsa. Ya jima yana duba al-qur’anin da sauran buks ɗin kafin ya miƙe zuwa fallo ya tattaro abincin da yaci ya rage dan yasan saita tashi cin abinci tunda yunwar takeji. Kwana biyun nan haka take, batama abinci sauƙi. Kodan jinyar da tasha ne oho. Sallaya ya hau ya kabbara sallar isha’i, bayan ya idan bai kwantaba ya ɗauki wayarsa da tun ɗazun yake ganin tana haske, ya tabbatar kuma kiransa akeyi dan a silent take.
      Ilai kuwa missed calls ne na papa har guda takwas, sai na Momynsa biyar. Sai na Omar (Richard) biyu. Sauran kuma duk ba important bane a garesa dan haka baibi takansuba dan harda mayyarsa Miracle.
        Kiran papa da Momy yasan bai wuce saukar Solomon Nigeria ba. Dan haka yay kiran Omar (Rich) kawai da shima yana Nigeria.
       Sallama kawai Omar (Richard) ya amsa masa, ya shiga masa shaƙiyanci wai yanzu soyayya tasa sai ya gadama yake amsawa mutane kira a waya. Su G-boy ma jiya suka gama masa tsogumi a wajen birthday ɗin Osin da akayi a garin Lagos. Kai abokan suma da yawa sunyi wannan complain ɗin duk da dama sunsan shi Yoohan fa bai cika ɗaukar kiran da zuciyarsa ta raya masa mara amfani bane, saboda yanayin aikinsa da duk ya maidasa busy a gaba ɗayan rayuwarsa. Sai dai idan yana a cikin hutu da kansa yake bin abokan mu’amulat nashi masu muhimmanci ya kirasu su gaisa koda bazai zauna hira da kai ba. Musamman ma daya musulinta ɗin nan ya ƙara sanin darajar zuminci.
      Murmushi kawai yayima Omar (Rich) ɗin da cewa “Humm ka samin ido da yawa”. Dariya kawai Omar yayi da ga can. Dan ya fahimci ƴan miskilancinne a kusa yau. Ajiye maganar wasan yayi suka fara tattaunawa kamar haka.
       “X-man duk yanda muke tunanin aikinan bazai kasance mai sauƙiba. Amma dai na turo maka dukkan bayanan dake a hannuna yanzu ta Email ɗinka. Ni dai yanzu shawarar dana yanke, mizai hana mu sami wani amintaccen jami’in tsaro da zai taimaka mana akan case ɗin nan. Dan tabbas sai munyi kutse a cikin wayoyin mutanen gidan saboda fahimtar da nayi case ɗin babba ne dan yanada tushe”.
     Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke yana bin Nu’aymah da ta tashi zaune da kallo. Ya juya harshensa zuwa yare. “Tunaninka mai ƙyaune Omar. Inaga kuma babu wanda zai iya taimakonmu akan aikin nan sai Dawood, sai yay mana hanyar ganin bawan ALLAH nan dana taɓa baka labarin ya taɓa buƙatar na duba matarsa akan matsalar cancer ɗin mahaifa da sukai zargin tana da ita, sai dai hakan bata samuba a wacan karon sai haɗasu nai da wani likitan.. So dole zan shigo Nigeria kwanan nan, tunda kaga akwai aikin da zanzo nayima anan Lagos. Kuma shi mutumin babban jami’i ne zaifi dawood tsaya mana sosai”.
         “To shikenan, sai mu bari sai kazo ɗin saimu tattauna, insha ALLAH madam ma zata dawo nextweek tunda kuna nan”.
      “Idan kayi hakan kuwa zaka taimaka min, dan zaman Zeeynab a ƙasar nan yana buƙatar samun wanda zasu shaƙu. Inason samar mata admission ma ta fara karatunta insha ALLAH. Dan tanason karatu sosai na fahimta. Sannan tanada brain, sai dai shiriritanta yayi yawa wlhy”. Ya ƙare maganar yana satar kallonta, dan tana zaune ne tana cin abincin da yunwa ta hanata barcin nata yay tsaho.
      Dariya Omar yayi daga can yana faɗin, “Ai da sauranta ne. 18years fa. bandama hausawan nan babu ruwansu ina ƴar 18years ina aure. Sai dai kuma yanzu ni tsarinsu birgeni yake. Indai madam ta haihu min baby girl nima tana gama secondary zan mata aure”.
     Dariya zancen ya bama Yoohan. Dan haka ya murmushi yana bin Aymah da wani narkakken kallo. Itako ta zuba masa harara ta ɗauke kanta. Dan tana takaicin idan suna tare taji ya canja harshe yana magana. Sai taga kamar gulmarta akeyi🤣. Shiko tunda ya fahimta ma har yi yake danya takaleta suyi faɗan nasu.
            Cikin ɗauke kai yace, “Saina faɗa mata duk abinda ka faɗa”.
     “Kai! Kaifa baka da kirki wani sa’in dude. Ni karka ɓatamin suna wajen ƙanwata dan kaga dai tace yanzu nine yayanta, idan ka mata laifi zata kawomin ƙara na hukuntaka”.
       “Kai kuma kaji daɗi ko? Shege mai shiga hancin masoya sai anjima. Wuce ka tafi wajen Juliet ɗinka dare ne anan inan buƙatar ɗumin baby na”. Kafin Omar yace wani abu Yoohan ya yanke wayar ƙitt.
          Matsowa yay kusa da ita ya amshi spoon yana faɗin, “Wannan fake yayan naki yana takuramin da yawa Sweet girl”. Sai da ta buɗe baki ya saka mata abincin daya ɗebo sannan ta bashi amsa cike da kasalar barcin da takeji.
       “Ai shine zai dinga saitomin kai idan ka birkice. Dan kaima rigimammene silly boy”.
        Goshinsa ya shafa zuwa saman ido yana murmushi. Ya cigaba da bata abinci batare da yace komaiba. Ta fahimci yau dai halinne ya motsa, shiyyasa itama tayi shiru ta cigaba da karɓar abinci da yake bata. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan shina ta amsa zata fara bashi. Cikin marairaicewa yace, “Na ƙoshi Sweet girl. Karkisa naita ƙaton ciki kizo kina kasa ɗaukata dama gaki da rakin tsiya”.
      Murmushin da batayi niyyaba ta saki. Ta kwanto a gefen hannunsa tana lumshe ido da faɗin, “Duk ƙaton cikinka zan iya da kai malam”.
      “Oh wow!!. Da gaske?”.
    Miƙewa tai zata gudu yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. A cikin kunnenta yace, “Yarinyar nan kinfa ƙware wajen guduwa ba’a gama magana ba”.
         Da sauri ta taune lip ɗinta na ƙasa tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ni kaga barci nakeji ALLAH. Ka barni na kwanta kona maka barci a jiki”.
       “Ai jikinki ne baby”. Ya bata amsa yana miƙewa ɗauke da ita suka haura kan gadon. Fitilar ya rage musu yana gyara mata kwanciya a jikinsa da ƙyau. Kanta ya sumbata suka sauke ajiyar zuciya. Ɗagowa itama tayi ta sumbaci laɓansa da shafa kwantaccen sajensa. Cikin sauke murya sosai tace, “I’m sorry. Nayi alƙawarin bazan sake ba insha ALLAHU”.
       “Thanks you sweet angel. ALLAH yay miki albarka. Nima kiyi haƙurin ɓata miki rai da nayi. Insha ALLAH bazan ƙaraba humyim?”. Ya ƙare maganar da cusa kansa a wuyanta yana shinshina. Ƙanƙamesa tayi dan salonsa a kullum mai wahalane a gareta…..
______________★★
         *_ABUJA NIGERIA_*
      Isowar Solomon Nigeria shi kaɗai yayi matuƙar tadama papa hankali. Duk da baice dasu komai ba saboda darene anan 9ja sanda ya iso ɗin. Amma sai papa ya kasa haƙuri ya shiga antayama Yoohan kira a waya. A lokacin shi kuma bai kulaba dan wayar na’a silent ne. Itama Madam Chioma tashin hakalinta ganin Solomon ɗin shi kaɗai babu Nu’aymah babu Yoohan ɗinne ya sakata kiransa taji su kuma suna inane? Amma sai yaƙi ya ɗaga. Daga ƙarshe ma sai suka daina samun layin nasa gaba ɗaya. Da wannan tashin hankalin suka kwana. Duk da ma barcin nasu rabi da rabi sukayisa.
        Aiko gari na wayewa suka nemi Solomon da shima dai kiran nasu dama yake jira. Dan shima ɓacin rai bai barsa yayi isashen barcinba. Kwana yayi yana mafarkin Nu’aymah da tsanarta ke ƙara hauhawa masa a rai a kowane daƙiƙa na rayuwarsa.
       A falon papa ya samu Momy da papan. Bayan ya gaishesu suka buƙacin bayanin dawowarsa babu su Yoohan. Tsaf ya kwashe komai ya faɗa musu harda ƙarawa da ƙarya. A take ransu ya ƙara ƙololuwar tashi. Papa ya miƙe a fusace yana faɗin, “Lallai yarinyarnan ubanta dama ya turota gidan nan ne bisa wani dalili. Darling bani keys ɗin sashen John. Dole na bincikima ɗakin yarinyarnan yau……….✍
(Munga idi hotonmu😱🏃).
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 66
………….Da sauri madam Chioma ta shiga ɗakinsa ta kwaso spare keys ɗin gidan ta kawo masa. Amsa yay ya nufi sashen Yoohan ita da Solomon biye da shi. Kai tsaye ɗakin Nu’aymah suka shiga. Ɗakin yayi ƴar ƙura, dan ma Yoohan duk ya tattare abinda yasan ƙurar zatai masa illa. Buɗe-buɗe suka shigayi a lungu da saƙo na ɗakin. Har cikin Wadrobe ɗin kayanta dan tsabar rashin mutunci. Duk abinda idonsu ya gani bai musu ba sai sun masa filla-filla. A haka Madam Chioma ta dinga tiɗo kayan Nu’aymah a ƙasa har hoton nan data ɗaukko ɗakin papa ya faɗo.
      Duƙawa tai ta ɗakko farar envelope ɗin, ta ɗaga bakin zata buɗe kira ya shigo wayarta. Gajeren tsaki tayi da ɗora hotan a kan fallen Wadrobe ɗin ta zaro wayar a aljihunta, ganin Madam Rebecca ne ya sakata ɗan juyawa ta dubi papa. Sai tai saurin barin gaban Wadrobe ɗin tama fice falo danta amsa kiran.
      Faɗowa hoton yay ƙasa kasancewa bata ɗaurashi da ƙyau ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Solomon wajen. Take hoton yayi ya matsa jikin Wadrobe ɗin ya cigaba da tiɗo kayan ƙasa shima yana bincike dalla-dalla kamar yanda madam Chioma yaga tanayi.
         Tsaf suka gama harmutsa ɗakin basu sami komaiba. Kayan sakawarata ne kawai sai turarurruka da buks ɗinta na addini dana boko. Shiru sukai kowa ransa cike da jin zafin rashin samun komai. Papa ya fara jan tsaki ya fice. Solomon ma ya bi ɗakin da harar ya takema papa baya. Madam Chioma suka bari ƙarshe tanata dube-duben inda zataga envelope ɗin nan amma ta rasa. Ta ɗan juyo zatama Solomon tambayar koya gansa ta shuresa da ƙafa batare data saniba. Kasancewar santsin tiles dana envelope ɗin ya sakashi tafiya suuuu sai ƙarƙashin gado. Taji ƙaran wucewar abu, hakan yasa tahau waige-waige. Sai dai kuma bataga komaiba. Tana niyyar fita ta hango farin takarda a ƙasa mai kama da envelope ɗin. Ɗauka tai ta buɗe sai taga zane ne Aymah tayi a ciki na teddy bear. Cike da takaici tai wurgi da takardan tare da shurar kayan Aymah da suka watso ƙasa tai ficewarta itama.
         Cike da jin zafi suka yini a wannan yini. ga Yoohan yaƙi ɗaga kiran kowa a gidan hatta da su Uncle Mike da papa ya saka su kira masa Yoohan a bisa wayonsa.
      Sai dai baisan Yoohan duk a lure yake da komaiba. Ya kumayi shirin tsaf akan ƙin amsa wayar kowa tunda yasan dai bai wuce zancen Solomon. Shi kuma ya riga da ya gama yanke hukunci dan yana buƙatar farin cikin matarsa da mallakar zuciyarta yanda ya kamata. Hakan kuma bazai tabbata ba har sai ya faranta mata kamar yanda iyayenta suma suka faranta masa a rayuwa. Sannan shi kansa a yanzu yaga kasancewar Solomon tare da shi a ko’ina babu wani tsari ai. Kodan kiyaye martaba da mutuncin iyalinsa. yana da kishi kuma gaskiya.
       Kiran da yaso kawai ya dinga ɗagawa a wannan yinin. Gefe ɗaya kuma yana manne da matsarsa sarkin taɓara suna shan sharafin soyayyarsu. Dan duk hanyar da yasan zata saki jiki da shi ita ya kebi da kulawa a gareta.
               Da gaske kuwa aikinsa na yin ƙyau ga jikar ɗan jibiya. Dan sosai karatun nasa ke tasiri akan Nu’aymah yanda ya kamata. Tasan taso Yah Ab kamar zata mutu. Amma lallai da gaske soyayyar ƙuruciyace tai ɗawainiya da zuciyarta a wancan karan da kuma darajar jininsu daya kasance guda. A yanzune take banbance minene ma soyayyar ga mahaɗin rayuwarta.
       A hankali ta fara sabawa da yanayin ƙasar U.S ɗin. Ƙasar ƴan gatan duniya masuyin yanda suka gadama a cikinta babu ƙasar data isa nuna musu yatsa. Hatta da U.K ɗin ma data rainesu a yanzu shakkarta suke saboda hatsabibanci da tsaurin ido irin na ƙasar ta Amuruka.
         Kwannsu biyu da zuwa Yoohan ya fara aikin daya kawosa. Hakan yaɗansa ta koma yini ita kaɗai a gidan. A rana ta huɗu ma sai kusan gabannin asuba ya dawo gidan. Nu’aymah bata da tsoro sam tun fil’azal. Sai na Duhu da allura kawai. Hakan yasa Yoohan bai taɓa ganin damuwa a fuskarta na barinta gida da yake ita kaɗaiba. Duk da shi duk inda ya shiga tana nan manne da ransa da zuciyarsa.
     Kaɗaicin da yake tunanin tana a cikine ya sakashi kaita tai register ɗin sabon layinta ya ɗora mata akan waya. Tare da saita mata duk wani folder na yanar gizo ta koma harkokinta da ƴan uwa da abokan arziƙi. Takoji daɗin hakan dan har ya fahimta akan fuskarta bayan runguma da sumbata daya sha da godiya.
        Samar da Sim card a wayar Aymah ya ƙara nutsar da ita. Dan kullum Umm da Hajjo cikin mata nasiha suke da ɗorata akan abinda ya dace. Harma baba malam da Ananah da Addah ba’a barsu a bayaba. Hakama Aunty Hajarah wata shaƙuwace take ƙara shiga tsakaninsu tana koyama Aymah dabarunsu na ƴan zamani akan gidajen aure. Dan tasan wautar ƙanwar tasu.
      Alhmdllh aikinsu na ƙyau kuwa. Dan huɗubar tasu nama Nu’aymah tasiri sosai. Har shi kansa Yoohan na fahimtar hakan. Dan randa suke cika sati guda da zuwa U.S da kanta ta samesa da zancen ya kaita tayo shopping dan ta ringa musu abinci. Ita ta gaji da jagwalgwalon turawan nan gaskiya.
            Kallonta yayi da kulawa yana ajiye wayarsa da yake dannawa. “Uhm yaushe kika iya girki?”.
     Yay mata tambayar da iya gaskiyarsa. Dan shi dai harga ALLAH ba taɓa sanin ta iya yayiba. Ya dai fahimci a fanin gyaran gida yarinyar gwarzuwa ce. Dan yanda gidan nan yake shan gyara a wajenta yana sakashi farinciki matuƙa. saboda a rayuwa yanason tsafta.
          Cike da ƙwaɓe fuska take dubansa daga kwancen da take a shakkiyar falon akan carpet. “Amma wlhy ka ragemin daraja. Girkinne kake tambayar yaushe na iya? Kira Umm ko Abbana kaji to. To ALLAH har Abba inama girki, dan nafi Umm ma data koyamin iyawa. Dan ni idan naso a yanzun sai in haɗa maka idea ɗin kalar girkin da zaisa ka manta kunnenka a cikin plate”.
         Da ƙyar ya iya danne dariyarsa ya murmusa kawai. Sakkowa yay daga kujerar da yake zaune ya zauna a gefenta ya jingina jikinsa da kujerar tare da ɗan karkatawa. Hakan yasa ta dawo kamar a jikinsan take dan ya miƙe hannunsa ta bayanta a jikin kujerar. Anan kuma ya tanƙwashe ƙafarsa ɗaya, ɗayar ku a ajiye ya ɗaura ɗayan hannunsa bisa gwiwar ƙafar.
      “Sweet girl! Dan ALLAH da gaske kin iya girki?”.
     Wayarta ta ɗauka batare data bashi amsaba ta shiga ma’ajiyar hotunanta. A take ta ƙwaƙulo masa pictures ɗin abincin da tayi lokacin da yay tafiyar nan. babu musu kuwa ya amsa yana kallo ɗaya bayan ɗaya a tsanake. Harga ALLAH yaji abincin ya birgesa harma yaji ƙwaɗayin abincin 9ja. Amma dai kuma bai gaskata ita ɗin tayiba. Dan haka ya mannata da jikinsa tare da saƙalo hannunta saman cikinta yana shaƙar ƙamshinta ta jikin dokin wuyanta.
      “To muje muyi shopping kenan, dan nidai sai anyi a gabana zan yarda. kuma nine zan zaɓi abinda za’a dafa idan kin yarda. Idan kinyi dai-dai kinada ƙyauta ta musamman. Idan kika kuskure akwai hukunci na musamman”.
        Cike da gatsen sanin ta iya ɗin ta juyo kanta da ɗora hannunta saman fuskarsa ta shafi sajensa. Da wani salo tace, “Na yarda da wannan game ɗin Mr Man”.
         Hannu yasa shima ya tallafo fuskarta tare da ɗora laɓɓansa akan nata yaɗan tsotsa. Jin zai zirma ya saka Aymah galla masa mintsini mai zafi a cinya. Sakin mata kai yayi yana sosa wajen da ɓata fuska kamar zaiyi kuka. Ta miƙe da sauri tana dariyar shakiyanci da faɗin, “Maganin mai kwaɗayin bakin mutane kenan”. Ta ƙare maganar da shigewa bedroom ɗinsu tana dariyarta.
     Murya ya ɗan ɗaga yanda zata jiyosa da ƙyau. “Silly girl! ALLAH kinci bashi, nasan ta inda zan fanshe muguntarnan da kikafi ƙwarewa a kai ai”.
       Dariya Aymah dake jiyosa daga ɗaki tayi tana zira skirt pink a jikinta irin mai bajewa gaba ɗaya ɗin nan. (Buje inji hausa😂lol). T-shirt yellow sosai da tambarin heart a gaba ta saka a saman skirt ɗin. Sannan ta gyara fakin din gashinta ta ɗaure a tsakkiya tare da naɗa gyale baƙi maiɗan girma sannan ta ɗaura pink jacket mai ƙyau a sama. Sosai tayi ƙyau, musamman yanzu datake ƙara yin wani uban haske jikinta na bajewa da ƙyau ƙibarta na dawowa. Ga ƙirji ya sake cika masha ALLAH. Taɗan saka hoda da lipstick pink kaɗan. Tana saka turare dai-dai misali ya shigo ɗakin. tsayawa yay kawai yana kallonta dan ta masa masifar ƙyau. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe a kanta da sakin ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana ayyana sirrin dake cikin auren ƙaramar yarinya mai yawan gaske. A fili kam baice komaiba sai ida shigowa da yayi ya ɗauka riga shima ya saka a saman singlet ɗin jikinsa. Sannan ya ɗora jacket baƙa shima data sake fidda masa sirrin ƙyau na angwanci dake ɗawainiya da shi.
      Gaban mirro ɗin da Aymah ke ƙoƙarin saƙala sidebag ta wuyanta tana daidaitata a gefen cikinta ya ƙaraso. Hannu yaɗan buɗe mata batare da yayi magana ba. Sanin abinda yake nufi ya sakata ɗauka gwangwanin turare batare da tace komaiba itama ta shiga fesa masa. Sannan ta ɗauki comb ta taje masa sumarsa data sake cika kan sosai saboda ƙaunarta da yakeyi, sai dai kuma yanzu askin arzikine a kan ba irin na daba. Sajenma gyara masa shi tayi tana magana cike da tsogumi.
       “Nifa karya zam inama kaina ramin muguntane ma. Inje na gama gyaraka wasu tambaɗaɗɗu can suyita kallemin miji. Wlhy duk wadda ta kalla ALLAH ya isana ban yafe ba”.
        Cike da neman magana yaɗan waro idanu waje da faɗin, “Uhm uhm fa Sweet girl. Matan U.S ɗin nan shegen ƙarfine da su ba irin na 9ja bane da kika gama rainawa kina karya musu ƙafafu da fasa musu baki. Su laƙaɗa miki shegen duka zasuyi babu ruwana”.
      Sosai ta turɓune fuska tana zuba masa harara. Tace, “To na rantse kuwa zakaja kafin mu dawo gidannan a fara wucewa damu police station ɗin garin nan, saboda ɓalla ƴaƴan jama’a zanyi na zubar a banza. Dama gasu ba ƙwariba girman ƙanƙara da Ice-creem da biscuits”.
        Ransa fes da fahimtar soyayyarsa dake tattare da matarsa ya rungumota ta baya dan tana gama maganar ta juya tana ajiye turaren data fesa masa. A cikin kunnenta yace, “I love you irin trillions ɗin nan My Cutie”.
     Hannu tasa zata ture masa fuska danfa taji haushin zancen ƴammata da yayi mata. Harda Miracle da tuni ta manceta a babin rayuwarta. tunda ita dai tasan itace ta taɓa ɓallama ƙashi da fasama baki.
     Da sauri ya riƙo hannunta yana dariya. “Na tuba wasa nake. Ai wannan Zenabu ɗin har abadan a bada, insha ALLAHU ita kaɗaice da Dr Yahya goshpower har ƙarshen numfashi. My angel kece kaɗai uwar ƴaƴana da yardar UBANGIJI. Ke kaɗaice sirrin Yoohan in ALLAH ya yarda. Daga ke babu wata mace data isa sanin koda sirrin murmushin Yoohan ne balle ma ta raɓu miki miji My Noorunnisa”.
      Cike da jin daɗin jin kalamansa da suka sanyaya mata jiki ta juyo a hankali ta jingina da mirror ɗin, shi kuma tana fuskantarsa. Ƙwallar da suka taru mata a ido suka ƙarama idanun ƙyau ta zuba masa. A hankali ta motsa laɓɓanta wajen faɗin, “Idan nace kai na dabbane, ina nufin na dabban har ƙasan zuciya da bugun numfashina My boo. Tabbas bani kaɗai bace haske a gareka. Kaima haske ne a rayuwata. Dan ka cetoni daga wahalhalun jarabawar rayuwa da ƙaddara ta tilasta zamansu a tafin hannuna. I love you so very much Yah Yoohan”. Ta ƙare maganar da faɗawa jikinsa ta rungumesa.
        Idanu ya lumshe a hankali yana mai ƙarɓarta da hannu biyu. harga ALLAH yanama yarinyarnan soyayya da ƙauna mai tsanani. Wanda ɓata lokacine wajen zama yayta faɗa da fatar baki. Tana riƙe da wasu darajoji da martabobi da mace tagari ce kawai ke iya samunsu a wajen ɗa namiji.
       “I love you more…. More…. More and more Zeeynab ”.  Ya faɗa shima cike da shauƙi da sarƙewar harshe a cikin kunnenta. A tare suka sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗaggo daga jikinsa. Sumbatar laɓɓanta yayi yana lumshe idanu da sake buɗewa a kanta. Kafin ya juyata suka kalli mirror ɗin yay musu hoto. Sosai sukayi ƙyau kuwa. Tamkar ka sacesu ka gudu dan tsabar dacewa da sukai da juna. Daga haka yaja hannunta suka fice a gidan gaba ɗaya. Cab suka samu zuwa wani haɗaɗɗen shopping mail da Amerikawan ke ji da shi. Dan yasan zasu samo duk abinda zasu iya buƙata a can.
        Aiko sosai wajen ya birge Nu’aymah. Babu kunya balle damuwa tattare da ita ta shiga kashe kwarkwatan idanunta tana jinjina jin daɗin duniya da turawan nan keyi. tare da ɗunbin jin tausayin Africans da wahalar Yunwa da kashe-kashe ta gama jigatawa da fiddamu a hayyacinmu gaba ɗaya.
        Yana riƙe da hannunta suke duba duk abinda zasu iya buƙata. Kasancewar kowa harkar gabansa ya keyi babu ruwan wani da wani sai suke komai kansu tsaye. Bayan sun kammala shopping ɗin suka fito ta ɗan wajen mail ɗin kafin a gama musu packaging ɗin kayan zasusha coffee.
          Sosai Nu’aymah yanzu take bala’in son coffee. Ta rasa dalilin hakan. Dan dacan har haushi takeji yanda Yoohan ya ɗauki amanar kansa ya bama coffee ɗin. Amma tunda suka dira U.S ta koma tamkar mayya akan coffee.
         Shi dai Yoohan yakanyi dariyane idan yaga yanda take bankarma cikinta. Cike da shakiyanci yake faɗin, *_Bugun daga kai sai mai tsaron gida kenan_* duk yanda Aymah taso fassara kalmar nan tasa ta kasa. Da taga ma wahala kawai take bama kanta sai ta daina damuwa da sanin. Daya faɗa sai ta zuba masa harara kawai ta cigaba da hidimarta.
        Sunsha coffee suna ƴar hirarsu cike da farin ciki. Dan kayansu tuni an tura musu gidansu. Kusan zaman awa guda sukayi a wajen sannan suka miƙe. Gaba sukai wani shagon sai da tsuntsaye dake tsallaken mail ɗin. Aymah ta zabi wasu kyawawan tsuntsaye mata da miji dake cikin keji. Yoohan ya biya yana tausayama ƴan kuɗaɗensa da yau Nu’aymah kema ɗibar karan mahaukaciya😂🤣. Zata ƙara nuna wasu yay saurin riƙo mata hannu yana magana da ƴar hausar daya fara iyawa a wajenta.
       “Hy madam ki taimaka mani karki ƙaremin kuɗi anan. Bakiga munyi shopping ba, kalli wallet ɗinafa”. Yay maganar yana nuna mata cikin wallet ɗinsa kamar zaiyi kuka.
        Ƴar dariya tayi ƙasa-ƙasa da cewa, “Humm sarkin raki na haƙura. ALLAH zai baka wasu masu albarka tunda ka farantama iyalinka rai ne. Kaima ALLAH ya faranta maka da ƙyaƙyƙyawan sakamako My boo”.
       Murmushi yay cike da jin daɗi. Dan duk wautarta ya shaideta da iya lafazi mai daɗi a garesa. Ko tsiwa take masa zaka samu babu kalaman raini a ciki sam. Sumbatar laɓɓanta yayi da kashe mata ido ɗaya, yace, “ALLAH yay miki albarka my Sweet girl”.
       “Amin my Boo”. Ta amsa masa cike dajin daɗin addu’arsa. Daga haka suka fito yana riƙe da cage ɗin ƙyawawan tsuntsayen masu daddaɗan kuka. A ƙafa suka ɗan ringa tafiya suna hira kamar yanda Aymah ta bukata. Ya fahimci tanason ganin kanta a inda bata saniba. Shiyyasa yake biye mata wajen ɗan fita da ita dan tai farin ciki, ya kuma rage mata kewar ahalinta daya rabota a cikinsu ya kawo nan ya ajiye.
      Saida suka gaji da tafiyar sannan ya tare musu abin hawa suka ƙarasa gida. A barandar gidan suka iske shopping ɗinsu. dan haka ya buɗe gidan suka dinga kwasa suna shiga da kayan ciki har suka kammala.
        Sallar la’asar data riskesu a hanya sukai ƙoƙarin gabatarwa. Bayan sun idar Aymah ta fara wucewa kitchen ɗin. Kayan da duk suka siyo ta fara buɗewa tana ajiye komai inda ya dace da zamansa. Tana kammalawa kenan ta ɗakko tukunya zata ɗauraye Yoohan ya shigo waya manne a kunnensa yana magana. Idonsa a kanta ya dafe kitchen cabinet ɗin dayin ɗan tsalle ya haye samansa ya zauna. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta ita dai, dan ta fahimci wayar tasa mai muhimmanci ce.
         Sai da ta gama wanke duk abinda zatai aikin da shi sannan ta jawo rigan girki ta ɗaura. Dai-dai kuwa da kammala wayar Yoohan. Sauka yay ya nufeta da ɗan alamun gajiya tattare da shi. “Wlhy duk kin gajiyar da ni Sweet girl. Inata murna yau zan huta a gida bazanje asibiti ba. Amma sai da kika sakani yawo”.
        Hararsa ta ɗanyi tana riƙe ƙugu da duk hannayenta. Cike da rigima tace, “Uhm uhum uhmyy. Wani aiki sai rago dai wlhy”.
      “Oh nine ma ragon?”. Ya faɗa yana wani hangame baki.
      Gira ta ɗage masa tana wani juya idanunta manya masha ALLAH. Tace, “Na gaske ma”.
         Wata dariyar mugunta yayi yana matsota, da sauri ta manne jikinta da cabinet ɗin tana marairaice fuska. Kafin ta samu damar magana yazo dab da ita. Matseta yay a wajen ya hanata ko guntun space yana wani ɗage gira sama da ciskule fuska. Hannayensa na a gefe da gefenta ya kai fuskarsa gab da tata suna shaƙa da busama juna numfashi. Ga idanunsu cikin na juna kowa kwarjini da sirrin na ɗan uwansa na ratsa masa jiki da zuciya. Da wani irin karya harshe na ma’abota shauƙin soyayya yace, “Yarinya kema kinsan ni ɗin ba rago bane. Amma zan sake tabbatar miki kuwa a yau ɗin nan da iznin ALLAH. Sai wannan bakin rakin naki ya kai titi saboda neman agaji”. Ya ƙare maganar da ɗallar laɓanta da yatsunsa biyu.
           Da sauri ta dafe bakin hawaye na cika mata idanu. Ta kai hannu bisa damtsen hannunsa yay saurin kaucewa yana wata shaƙiyyar dariya ƙasa-ƙasa dan yasan muguntar da zatai masa.
     Kumbura tayi tai fam. Cike da haushi ta kama rigar zata kunce ya riƙe hannunta. “Ai yarinya baki isa ba. Kin riga da kin yarda da game ɗin nan dan haka girki dole ne”.
       Baki ta tura masa tana kwaɓe fuska da faɗin, “Na fasa game ɗin. Girkinma sai dai kay…..”
        “Hhh daga baya kenan hajjaju Zenaba ƴar farar bakanuwa ƙyaƙyƙyawa”.
    Yay maganar da riƙota hannunta ya maida ɗaurin rigar yana mata wani dariyan iya shege a gefen wuya.
        Gaba ɗaya neman susuta mata jiki yake da salonsa. Saurin zame jikinta tai ta koma gefe tana faɗin, “Ai inba yau a kwai gobe indan ALLAH ya kaimu. Ka ɗauka yau ɗin kaine a sama ni a kwana. Sai dai kuma zaka dawo kwanar ne ni na koma ciki…”
   Ta ƙare maganar da wani salo tana kashe masa ido ɗaya.
       Da gasken gaske saƙonta ya iso inda ta turosa. Dan gaba ɗaya jijiyoyin Yoohan suka saki dama kwana biyun nan rakinta ya sakashi ɗan bata ƙafa. Lip ɗinsa ya cije da ƙarfi yana wani jan ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba ya jawo wayarsa ya miƙa mata. Yana mata wani kallo ƙasa-ƙasa. Amsar wayar tayi da tura baki gaba tana ƙunƙuni. Ta kalli hoton abincin da ƙyau sannan ta ɗan dubesa ta ɗauke kanta tana murmushi.
        Kujerar dake gaban tebir ɗin tsakkiyar kitchen ɗin yaja ya zauna. Ya wani miƙe ƙafafu da bajewa da ƙyau, irin fa shine boss ɗin nan.
         Nu’aymah bata sake bi ta kansa ba ta fara ƙoƙarin ɗaura girkin tana addu’a a ranta da fatan yin komai yanda ya kamata.
         Ko ɗauraye cokali bai tayataba, tunda ta fara. Yama ɗauke kansa gaba ɗaya daga gareta sai danne-dannen waya yake yi hankalinsa kwance. Duk da kuwa a baɗini duk wani motsinta nakan idonsa ne.
       Kasancewar ta kwana biyu batai girkin ba yasa takeyin komai cike da ɗoki. Kafin cikar awa ɗaya kuwa sai ga ƙamshi ya gama gauraye kitchen ɗin gaba ɗaya har falo. Shi kansa Yoohan shaƙa yake cike da jin daɗi da kwaɗayin son cin abincin. Tsaf ta kammala komai ta gyara kitchen ɗin da ɗauraye duk abinda ta ɓata duk yana zaune dai yana kallonta. Abincin ta zuba a plate tare da ɗan ɗora kwalliyar data ƙara ƙawatashi ta ɗauki cokali tazo ta dire gabansa tana wani shan ƙamshi.
      Idanu ya tsirama abincin dake ta tashin ƙamshi mai saka yunwa. Kafin ya ɗago ya kalleta. Ɗauke fuskarta tai gefe murmushi nason kufce mata. Sai kuma taje ta tsiyayo apple and orange juice ɗin data haɗa a glass cup tazo ta ajiye shima a gabansa. dai-dai yana gyara zamansa. Bai fahimci minene ba, amma yaga sanda take markaɗa abu dai. Cokalin ya ɗauka ya ɗiba abincin kaɗan ya kai bakinsa tare da yin bismilla. Duk da daɗin daya ratsa masa baki da kunne da ƙwaƙwalwa sai ya wani yamutse fuska harya haɗiye. sake ɗiba yay yaci nanma fuska a yatsine. Aymah dai na kallonsa baki a ɗage dan tasan wlhy ƙarya yake yace abincinta babu ɗanɗano.
       Cike da son danne dariyarsa na ganin yanda tai da fuska ya kai lauma ta uku. A hankali ya lumshe idanunsa da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Sai kuma yay mata alamar jinjina da kashe ido ɗaya ya haɗe yatsunsa biyu👌🏼 alamar komai zam.
       Itama ajiyar zuciyar ta sauke a hankali da juya bayanta idanunta na cika da ƙwallar farin ciki dajin ƙaunar Umm ɗinta mai tsanani. Dan itace ta maidata tauraruwa wajen tsayawa akanta tun tana ƴar mitsitsiyarta. Ƙanƙantarta baisa Umm ta taɓa rangwanta mata ba akan aikin gida duk da sunada mai aiki. Kamo hannunta da Yoohan yayi ya ɗora bisa cinyarsa ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
      “K ta dabance Cutie”. Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa cikin rigarta.
      Idanunta ta lumshe itama da kai hannunta ta shafo kwantaccen sajensa mai laushi dake cin kuɗaɗe wajen gyaransa. Kiss ya bata a wuya tare da ɗagowa ya kamo fuskarta ya manne bakinsu waje ɗaya. Bata hanashi ba. Dan ya riga da ya koyar da ita wannan sirrin.
      Sai da taga wasan na neman canja salone ta ƙwace kanta da ƙyar tana masa dariya. Sai ko ya ƙwaɓe fuska tamkar zaiyi kuka dan da gaske ya zurma da yawa.
         Plate ɗin abincin ta ɗauka ta ƙaro musu tare da ɗakko juice ɗin gaba ɗaya shima. Sai lokacin Yoohan ma ya ɗauki wanda ta fara kawo masa yasha yana sauke ajiyar zuciya. Cike da ɗage gira yace, “Kin haɗu a abubuwa da dama Hausa girl”.
     Murmushin jin daɗi tayi, dan har ranta tanajin nishaɗi idan ya kirata Hausa girl. Tana son yarenta tana alfahari da shi fiye da zaton mai karatu. Tanaji a ranta komi ta zama dolene duniya tasan itaɗin ƴar ƙabilar HAUSA ce gaba da baya.
       Sunci abinci cike da farin ciki, yana bata tana bashi har suka kammala. Da taimakonsa yanzu kam suka tattare wajen suka fice a kitchen yana faɗin ta zaɓi ƙyautarta.
    Ita dai dariya take masa kawai. Sai da suka fito falo ya zauna da ita a jikinsa sannan ta dubesa tana murmushi. “Soyayyarka da kulawarka a gareni kaɗai ta isheni tukuyci my sweet boo”. Tai maganar cike da salon da take ƙara ƙwarewa wajen koya a hannun Aunty Hajarahn mai sonta da ƙaunarta.
      Rungumeta yay a jikinsa ƙaunarta na sake ratsasa. A ƙasan ransa kuwa godiya yakema ALLAH da samunta tare da jin girma da darajar iyayenta a cikin ransa. Fatansa ALLAH ya basu ƴaƴa masu albarka suma su basu irin wannan tarbiyyar tata abin son kowanne ɗa nagari.
__________★★
      Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa ga Nu’aymah da Yoohan cike da farin ciki da tattalin juna kasancewar har yanzu a amarci da ɗokin juna suke. (Kunsan shi farkon aure dama haka yake. Za’aita nunama juna soyayya cike da zalama. Ku kanku jin kanku kuke tamkar babu ya ku a duniya. Sai rayuwa ta fara nisane abubuwa ke fara tsauri. Sai dai da yake UBANGIJI mai rahama ne da jinƙai sai kaga hakan baya hana a nunama juna soyayya da kulawa koda saɓani na shiga. Duk da jarabawa kan ratsa a zamantakewar ma’aurata kaga matsalolin nata yawaita fiye da hasashe. ALLAH ya cigaba da zaunar damu a gidajenmu lafiya tare da mazajenmu da ƴaƴanmu da abokan zamanmu baki ɗaya mata sarakunan gaskiya a fadar gaskiya😘😍🤗).
      Kwansu goma sha uku a U.S Yoohan yay shirin zuwa Oman yin wani aiki na kwana biyu. Daga can kuma zai wuce Nigeria insha ALLAH.
         Yasha taɓara kuwa a wajen Aymahn sa. Dan kuka sosai ta dinga yimasa akan saita bisa. Da ƙyar ya lallaɓata da tabbatar mata Juliet matar Omar (Rich) tana zuwa daga 9ja a daren yau. Idan ma batason zaman anan gidan ita kaɗai sai ya kaita gidan Juliet ɗin ta zauna a can harya dawo.
     Da ƙyar ta amince kuwa. Shima sai da aka haɗa da hajjo wajen lallashi. A ranar kuwa Juliet ɗin ta iso. Sun tarbi juna da mutuntawa. Kuma har cikin zuciya Nu’aymah taji zata iya zama tare da Juliet ɗin. Musamman yanda taga itama Juliet ɗin na nuna mata ƙauna da yaba komai nata tana sake taya Yoohan murna. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana bin mutuniyar tasa da kallo ƙasa-ƙasa.
      Washe garin da zai wuce sai da ya rakata gidan Juliet sannan ya wuce ya barta da kewarsa kamar yanda shima ya tafi cike da tata kewar.
★★★★
          Tamkar jira jikin Aymah keyi Yoohan ya wuce ta fara ƙananun ciwuka. Kullum da zazzaɓi take wayar gari, zuwa ƙarfe ɗaya na rana kuma sai ya gudu. Tun Juliet bata fahimtaba harta fahimta saboda shaƙuwar dake ƙara shiga tsakaninsu da Nu’aymah. Dan Juliet tanada sauƙin kai sosai. Bata taɓa kuma nuna ƙyamar addinin Nu’aymah ba koda kuwa akan fuskartane. Wani lokacinma idan Aymah na salla ko karatun Al-qur’ani har zama take taita kallonta. Dan itama zuwa yanzun tasan mijinta Omar (Richard) ya musulinta…………✍
*_Gaba ɗaya na manta yau monday fa😥🤦🏻🏃😂_*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/1, 2:39 PM] +234 806 331 2486: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 67
…………Juliet taso kiran Yoohan ta sanar masa amma Aymah ta hana. A cewarta ta barsa wai dama ta saba irin wannan zazzaɓin duk shekara. Asibiti ma taƙi yarda suje sai magani data amsa tasha. Daga haka ta fara ɗan ƙarfafa kanta duk dan ta kwantarma Juliet ɗin da hankali ganin ta damu. Gashi itama fama take da kanta dan cikine da ita ɗan wata kusan takwas.
      Dole Juliet ta barta, sai dai duk motsinta na akan idonta. Ita har mamakin yanda Nu’aymah ke bankar coffee takeyi babuji babu gani. Gason yawan kwanciya bisa tiles wai sanyin take so.
        A hankali tama daina cin abinci, dan kotaci sai tayi amansa take samun sauƙi. Hakan na damunta, sai dai ta kasa faɗama ko Juliet ɗin balle Umm da Hajjo da Addah da kusan kulumm sai sunyi waya. Ko sun kirata ko ita ta kirasu sai taita ƙarfafa kanta yanda babu mai ganewa. Sai dai Uwa dabance. Dan Umm kan tambayeta anya tana lafiya kuwa? Dan a muryarta da yanayin sanyin da tayi na rage surutu da rawar kai Umm takan ji kamar Aymah na cikin wani haline. Amma sai take cemata babu komai, kawai yanayin wajene.
     Juliet nada coffee powder a gida, sai dai kota haɗama Aymah bata sha sai dai suje shagwan shan coffee ta sha tayo guzirinsa kuma. A duk sanda sukai waya da Yoohan ko video call kam sai taita ƙarfafa kanta harda masa ƙarfin halin tsiwa wai karda ya fahimci halin da take ciki.
       Batasan kallonta kawai yakeba, dan tun kafin akai haka ya gama fahimtar shigar ɗan tayin cikinsa a mahaifarta. Sai dai ya barma ransa har ALLAH ya bayyana ikonsa da kansa tunda shima hasashene kawai da shegen ganin ƙwaf irin na likitanci bisa baiwar da UBANGIJIN al’arshi ya azurtasu da shi.
_________________
      Kwanan Yoohan huɗu a ƙasar Oman ya wuce Nigeria. A abuja ya sauka, sai dai maimakon ya tafi gida direct sai ya sauka a hotel ya kama ɗaki. Dan dama babu wanda yasan da zuwansa ƙasar a cikin su papa. Yama toshe duk wata hanyar da zasu iya samunsa a waya tun barinsu Austria. Ya fi son yazo su fuskanci juna akan maganar Solomon ɗin fiye da suyi magana ta waya.
        A daren ranar ya samu aka samo masa Number ɗan sandan nan da ƙyar ta hanyar wani abokinsa da shima ɗan sandan sirrine babba.
     Gajiyar daya kwaso ce ta sakashi yin barci da wuri ranar ko waya da Aymah baiyiba. To itama dai da yake ranar zazzaɓi ya mata rigif ko nemansa batayiba ma.
      Washe gari ƙarfe goma na safe Omar (Rich) ya iso hotel ɗin daga birnin Lagos. Ya iske Yoohan ɗin cikin shirin suit royal blue da sukai masa masifar ƙyau. Musamman yanzu da yay wani ɗan ɓul-ɓul dashi saboda madarar angwanci data hudashi. Rungume juna sukai cike da so da ƙyauna da begen juna. Kai kace basa waya kullum. Bayan sun gama ƴar chapter ɗinsu da suka iya suka fito gwanin sha’awa zuwa motar Omar ɗin. Omar ne ya jasu zuwa headquarter ƴan sanda na jami’an tsaron sirri suna ƴar hirarsu.
      Sai da suka gama shan tambayoyi da uban bincike kafin su sami damar shiga da taimakon abokin Yoohan ɗin da aka sanarma zuwansu daga baya.
     Da ƴar dariya Dawood yake kallon Yoohan daya ciskule fuska saboda haushi binciken da akaita musu yana faɗin. “Yi haƙuri bokan turai, wlhy banyi tunanin zakuzo a yau bane da nazo na tsaya a gate ɗin na jira isowarku ai. Tunda aka ɗora mana adalin shigaba a hukumarnan tamu tsaro ya ƙara tsauri dan sam bashi da wasa”.
       Dariya shima Omar yayi yana taɓe baki. Yace, “Kai Dawood manta da lamarinsa kewar matarsa ke ɗawainiya da shi badan wannan binciken yake fushi ba”.
    Hararsu Yoohan yayi su duka amma baice komaiba. Da haka suka ƙarasa can sama inda office ɗin oga kwata-kwata na hukumar DSS yake. Duk da Dawood yay masa bayani akan zuwan su Yoohan ɗin sai da suka jira shi ya fara shiga office ɗin sannan ya fito yay musu iso.
      Ƙyaƙyƙyawan dattijo ne da a shekaru a ƙalla zai iya kaiwa 64 Zaune a kan kujerar office ɗin hankalinsa gaba ɗaya akan Computer ɗin dake saman desk ɗinsa. Batare da ya ɗago ba ya amsa musu sallamarsu cike da nutsatstsiyar muryarsa mai tarin kamala da dattako.
       Sosai kwarjininsa ya cika zukatan su Yoohan duk da bai ɗago sunga fuskar tasa ba da ƙyau. Da hannu yaɗan nuna musu kujerun yana faɗin, “Bismillanku”.
     Kusan a tare Omar da Yoohan suka sauke ajiyar zuciya da duban Dawood dake ƙame a tsaye. Kai shima ya jinjina musu alamar su zauna ɗin. Zaman sukayi tare da haɗa baki wajen faɗin, “Good morning sir”.
        Cikin ɗan fesar da iska Boss *_Jawaad Abdul-aziz Yusif tafida_* ya ɗago gaba ɗayansa fuska babu walwala kamar ko yaushe yace, “Good Morning”. yay maganar da miƙa musu hannunsa alamun suyi musabuha.
      Omar ne ya fara miƙo masa hannun suka gaisa, kafin ya miƙama Yoohan da shima zuciyarsa ke wani bugawa da harbawa da sauri-sauri. sai dai cike da dauriya ya faɗaɗa fuskarsa da murmushin ƙarfin hali.
      Da ga shi har Boss Jay zukatansu suka buga da ƙarfi. Hannun Yoohan ya dinga rawa dan yama kasa ƙarasawa da shi inda na Jay dake ƙoƙarin zare glass ɗin idonsa yake.
       Hakan yayi dai-dai da shigowar wata kamilalliyar mace da shekarunta zai kai kimanin 53 cikin office da sallama, hannun ta riƙe da takardu. Sanye take cikin doguwar rigar jallabiya baƙa. Shigar tata ta ƙara fidda kamalarta da mutuncinta ga mai kallonta.
       Akan mijin nata ta fara sauke idanunta da mamakin yanayin data gansa. Sai kuma ta maida dubanta ga abinda yakema kallon ruɗani da tsoro. Baya tayi da sauri har takardun hannunta na watsewa a ƙasa. Saurin sunkuyawa Dawood da ke binsu da kallon mamaki yayi yana tattare takardun da faɗin, “Am sorry maa”.
        Bilkisu bata iya cewa komaiba sai takawa da tai da sauri inda Jay yake. Zatai magana yay saurin damƙe hannunta alamar shi ya dawo cikin hankalinsa. Girgiza mata kai yayi alamar kartace komai. Sai ma wayancewa yayi da faɗin, “Wai nikam da gaske likitan da naso gani ruwa a jallo shekara ɗaya data shuɗe ne amma hakan ya gagareni a gabana?”.
       Duk da Yoohan yaji sam a ransa ba wannan batun bane jefa adalin ma’aikacin cikin ruɗanin ganisa sai shima ya sauke ajiyar zuciyar da sam bata samun nutsuwa bace. Cike da ladabi ya jinjina kansa yana murmushin ƙarfin hali. Dan wani masifar kwarjini da Jay ya masa. Yace, “I’m very sorry sir. Nasan ni mai laifine sosai a gareka”.
      “No no no son. Inama mutane irinka uziri sosai ni a rayuwa. Dan haka manta kawai da wancan batun, tuni an kauda matsalarma”. Jay ya faɗa yana maida glasess ɗinsa akan ido.
      Cike da jin daɗi Yoohan yace, “Thanks you Uncle”. Sai kuma ya ɗan kalli Bilkisu da alamu suka nuna har yanzu tana a cikin ruɗani ita dai yace,  “Good morning maa”.
         Da wani irin sanyi tace, “Good morning dear”. Shima Omar (Rich) da al’ajabi ya cika gaisheta yayi. Ta amsa masa da kulawa shima tana duban Jay da har yanzu idanunsa akan Yoohan suke. Kauda kansa yayi ya ɗan dubeta saboda taɓa masa kafaɗa da tayi. Murmushin ƙarfin hali yay mata da nunama su Yoohan ita faɗin, “My wife. Itace naso na kawo maka a wancan lokacin muka gagara samun dama. Itama ma’aikaciyace a wannan hukumar. Amma Alhmdllh, daga baya mun fahimci babu waccan matsalar da mukai zargi”.
       Cike da girmamawa Yoohan da Omar sukace masha ALLAH. ALLAH ya ƙara kiyaye gaba.
         Amin suka amsa musu. Bilkisu data fahimci zamanta a wajen zai iya kawo matsala sai tai ɗanyi murmushi da ranƙwafawa saitin kunnensa tai magana. “Bara naje, su Zuhrah na jirana zamu wuce. Ga takardun nan duka na haɗo maka na case ɗin matar nan mai safarar ƙwayoyi”.
      Kansa ya jinjina mata kawai yana murmushi. Yana son ɗan sumbatar matarsa babu dama. Dan haka ya kashe mata ido ɗaya cike da salon ƙwarewar manyan masoya😉😂.
      Itama murtani ta maida masa da nata salon taima su Yoohan sallama ta fice. Numfashi Jay ya furzar a ɓoye. sannan ya maida duka hankalinsa gasu Yoohan da kansu ke a ƙasa. Dan gaba ɗaya zuciyar Yoohan ta gaza samun nutsuwar zama a waje ɗaya. Yadai dage yanata ambaton sunayen ALLAH kozai samu sassauci daga abinda yakeji cikin jininsa.
         “Tom Doctors ina saurarenku. Dawood ya sanarmin kuna son ganina cike da magiya a garesa. Ina fatan dai lafiya ko?”.
       Omar yace, “A lafiya lau sir. Wani taimako mukazo nema ne a wajenka da alfarma akan wani case”.
       “Okay. Babu damuwa. Dawood zoka ɗauka dukkan bayanansu dan kar a samu kuskure ko”.
        Da tsantsar girmamawa Dawood yace. “Okay sir”. Yay maganar da ƙame jikinsa waje guda yana buga kafarsa ƙasa. Hannu Jay yaɗan miƙar alamar amsawa. Daga haka ya ciro takarda da pen ya zauna ya fara sauraren bayanin da Omar ya farayi kasancewar Yoohan ya sanar masa komai dangane da gidan su Aymah akan abinda yaji daga gareta da wanda ya sani.
        Sai da ya kai aya Jay ya sauke numfashi yana janye pen ɗin da yake gogawa saman laɓɓansa. Ya ɗan murmusa da faɗin, “Babbar magana. Ɗan jibiya family kam ba ɓoyayyan gida bane. dan ahaline na masu daraja saboda ilimin addini da harkokin kasuwancinsu. So dama akan samu irin waɗanan rikice-rikicen da ZAGON ƘASA a irin mafi yawan waɗan nan gidajen. Shi kuma zagon ƙasa Kamar wani SARAN ƁOYE ne mai cin rai da ruɗa tunanin wanda akemawa. So na tayaku murna tare da shigowarku cikin hasken musulinci. Na kumayi alƙawarin taimaka muku wajen ban kaɗo abinda kuke buƙata bisa son ƙyautatawarku ga Sheikh Soorajidden Hashim. Saboda nima malamina ne ai. Kuna ambata masa sunana zai baku labari. Har ɗaurin aurenku naje ma. tabbas kwanaki dana buƙaci zuwa wajensa muyi magana ya sanarmin zaiyi tafiya za’aima yarinyarsa aikin ƙwaƙwalwa a ƙasar ƙetare”.
     Da jindaɗi a fuskokinsu suke dubansa.
    Shima murmushi yayi yana zare glasess ɗinsa. ya cigaba da cewa, ”Ina ƙaunarsa sosai dan yayima rayuwata hidima mai yawa. Insha ALLAH nima bazan gajiya ba wajen bankaɗo azzalumai masu cin dunduniyarsa. Sai dai wannan aikin dolene ya kasance na sirri”. Yakai ƙarshen maganar da duban Dawood.
      “Dawood! Ina buƙatar ganin Bilkisu Jawaad”.
      Da sauri Dawood ya miƙe yana faɗin, “Okay sir”.
      Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dawood ya dawo tare da matashiyar mace da bazata gaza shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba. Daka ganta babu tambaya kasan jinin Boss Jawaad Abdul-aziz ce. Sanye take cikin wando da riga na Uniform ɗin hukumar. Da alama itama jami’ace a hukuma (dan ƙari. Bilkisu ƴar bilkisu jikar bilkisu kenan😉. Ita ƴar sanda, mamanrta ƴar sanda. Babanta ɗan sanda😝. Wani aiki sai Jay😂lol).
       Fuskarta cike da miskilancin data gada wajen iyayenta ta ƙame tare da salute ɗin mahaifinta kuma oganta a wajen aiki. tace, “Sir gani”.
      Daga Yoohan har Omar kallon mamaki suke mata. Dan basa buƙatar ƙarin bayanin komai game da Biljay.
       Takardar da Dawood ya rubuta ya miƙa mata cike da bada umarni a gareta matsayin oga ba mahaifiba. “Duba min wannan takardar”.
      “Okay sir” ta faɗa tana ɗaukar takardar. Cike da hazaƙar ƙwarewar aiki ta duba rubutun takardar tsaf, kafi. ta ɗago ta kallesa tana sunkuyar da kanta da ƙamewa. “Na duba Sir”.
       “Me kika fahimta?”.
“Report ne na case ɗin ɓoyayyun mutane masu laifi”.
       “Masha ALLAH. Little bee kece zakiyi wannan aikin. Waɗanan sune masu kawo Report ɗin. Zakiyi joining ɗinsu kuyi aikin tare. Sai dai kece zakiyi kutse a cikin gidan ko mubi ta wata hanyar insha ALLAH. Kinsan banson wasa, bana son kuskuren ganganci akan aiki, so be careful”.
      “Insha ALLAH sir”.
Kai ya jinjina mata da maida dubansa kan Dawood. “Dawood tare zakuyi wannan aiki da ita, so zata kasance ƙarƙashin control ɗinka, dukanku kuma zaku kasance akan umarni”.
     Shima ya amsa da “Okay sir”.
Daga haka Jay ya maida dubansa gasu Yoohan. “Doctors waɗanan nan sune zasu taimaka muku akan wannan case. Insha ALLAH daga nan zuwa kwana uku zamu san wadda zata shiga cikin gidan matsayin maiyin hutu a wajen Sheikh. Sauran aiki duk zasu yisa baku da damuwa. Sai dai dole kuma sai da hannunku a ciki dan kun fisu sanin sirrin gidan a yanzun. Zaka haɗata ƙawance da matarka ta waya. Dan wasu abubuwan ta hanyartane zasu sami haske sosai. Duk abinda ya dace zaku cigaba da ji ta hanyar Dawood, dan shine oganta”.
      Godiya sosai su Yoohan suka shiga yimasa. Dan sam basuyi tunanin samun mafita cikin sauƙiba haka daga garesa oga kwatakwata da ganinsama ke da matuƙar wahala. Yanda bai musu bayani akan matsayin Bilkisu a garesaba suma basu tambayaba duk da sunada buƙatar ji.
      A tare da shi suka fito office zuwa massalaci saboda kiran sallar zuhur. Bayan an idar da salla kuma sukai masa sallama da ƙarin godiya suka wuce cike da farin cikin wannan karamci da samun sauƙi. Sai dai ƙasan ran Yoohan shi kaɗai yasan mi yakeji game da Jay ɗin.
    Koda suka ɗauki hanya kasa haƙuri Omar yayi sai da yayima Yoohan maganar kallon da yaga Jay ɗin na masa da matarsa. Harma hanata maganar da yayi. Tare da cewa nifa, “Wlhy fisgen kamannima kukaimin”.
        Da mamaki Yoohan yace, “Kamanni kuma?”.
      “Yes X-man. Wlhy a fisge kunyi kamanni like na jini haka”.
      Nannauyan numfashi kawai Yoohan yaja da ƙarfi ya fesar batare da ya iya cewa komaiba har suka ƙarasa wani gidan cin abinci. Anan sukai lunch da cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafesu. Daga haka sukawuce General hospital wajen Dr Shikurah. Sai dai sunyi rashin sa’ar samunta wai batama ƙasar.
     Yoohan yayi gaisuwa da abokan arziƙi suka koma hotel ɗin daya sauka. Omar ya jima a wajensa dan har dare suna a tare sannan ya koma gidan papa dan acan ya sauka shi. Amma sai bai faɗama kowa Yoohan na ƙasarba.
      Washe gari Yoohan yaje kaduna yin wani aiki. Sai washe garin daya cika kwana uku a 9ja ya dawo. Dai-dai da ranar da Little bee zata shiga gidan baba malam kenan. Dan haka kai tsaye gidansu ya nufa. Sai dai kawai su Madam Chioma suka gansa tsilum tamkar daren Christmas inji su.
___________★★
          Tun wucewar su Yoohan Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye a office ɗinsa. Gaba ɗaya man kan sa ya gama tsiyayewa tas akan wannan kamanni. Goshinsa ya murza da cewa, ‘Kai anya kuwa. Dolene nasan wanene wannan yaron’. Ya ƙare maganar da ɗaukar telephone yay kiran Dawood.
        Dandanan Dawood ya amsa kiran boss. Nuna masa kujera yayi alamar ya zauna. Bayan kusan mintuna uku ya ture files ɗin gabansa yana kallon Dawood ɗin.
      “Dawood nikam a ina kasan yaron nan ne?”.
      Cike da girmamawa ya bashi amsa da faɗin, “Sir, tare mukai secondary school da su”.
      “Masha ALLAH, lallai kayi masa sani na sosai. Anan cikin abuja suke?”.
        “Yes sir. Ai yaron sanannen Pastor ɗin nanne Goshpower mai ƙaton catholic church ɗin nan dake a wuse2”.
     Ɗan jimm Jay yay yana kallon
Dawood. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan yana wani guntun murmushi mai kama da an masa dole. “Okay thanks you, zaka iya tafiya”.
     Miƙewa Dawood yayi tare da salute ɗinsa ya fice yana mamakin tambayoyin ogan nasu.
      Dawood na fita Jay ya shiga Google. Bayanai ya nema akan dukkan handles ɗin papa dake a social network. Cikin mintuna ƙalilan kuwa suka watso masa komai. Facebook, Twitter, Istagram, Telegram, dama wasu daban-daban. Harda youtobe chennal da suke ɗaura dakan abubuwansu na church ɗinsu. Numfashi yaja ya furzar tare da shiga kowanne shafi ya duba followers nashi da duk wani posts da yayi a kai. Yawanci duk akan church ne dai.
       Komawa yay bincike akan pictures nashi. A take kuwa suka bashi su da yawa. ‘Oh my GOD!!’. Jay ya faɗa da matuƙar razana. Gaba ɗaya kansa ya sake kullewa. yama rasa kalar tunanin da zaiyi dan da gaske shi dai ya shiga ruɗani. Ta yaya hakan zata kasance bayan shi shaidane akan abinda ya tabbatar a zahirin gani da ido. To amma inhar ta tabbata a tunanin da zuciayarsa ke bijiro masa lallai sai dai idan akwai yaudara a lamarin kenan, ko kuma…… Yay saurin girgiza kansa alamar ba haka baneba sam. dan da sun sani ai.
      A wannan yanayin Bilkisu ta sake shigowa ta samesa. Rungumesa tayi ta baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya zagayo da ita gabansa. Kaɗan ya ranƙwafo ya sumbaci laɓɓanta da goshinta.
       “My Boss ina baƙin naka suke?”.
“Sun wuce Miemaa. sai dai ina cikin ruɗani wlhy”. Yay maganar yana jan hannunta wajen kujerarsa.
     Zama tai a kujerar tana bashi amsa itama. “Bakai kaɗai bane a ruɗani. Ni kaina rikicewar ta hanani zama na gudo nabar su Ummie acan”.
      Ta bayanta ya ranƙwafo yana nuna mata abinda ya samo game da papa. Ƙwarai da gaske ta cika da mamaki itama saboda ganin hoton papan. Dan haka sukayi zaman tattaunawa yay mata bayanin dukkan hukuncin daya yanke. Tare da alƙawarin zuwa wajen baba malam kozai ƙara samun wasu bayanai ta wajensa game da papan tunda sun zama surukai.
     Ta gamsu ɗari bisa ɗari da hakan. Harma da zuwan wani cikin gidan, dan Little bee bazai yuwu taje gidan baba malam ɗin ta zaunaba saboda mijinta da wahala ya amince duk da yasan dokar aikin. Amma zai tura ƙaramar ƴarsu autar su Little ɗin mai suna Afrah akan case ɗin da su Yoohan ɗin suka kawo report.
_____________★★★
         Lokacin da Yoohan ya shigo gidan ya iske duk suna church. Sai guards ɗinsa kawai da maigadi aka bari alamar papa yaji shawararsa ta kwanaki kenan. A cikin gidanma daya shiga ya samu Blessing. Cike dajin daɗin ganinsa da tunanin tare yake da Aymah ta shiga masa welcome. Ya amsa mata kadaran kadahan. Ya kama ƙafar benen zai haura Blessing da haƙurinta ya ƙare tace, “Sir Aunty fa?”.
      Juyowa yay ya ɗan kalleta yana lumshe idanu da buɗewa. Sai kuma ya ɗan mata murmushi a bazata dan bata taɓa ganiba. Shi kuma jin daɗin nuna kulawarta ga matarsane ya sakashi yin murmushin. Sai da ya juya ya cigaba da hawa steps ɗin sannan ya bata amsa da, “Tana can na barota. Kina missing nata ne?”.
        Cike da haɗiye ɗokinta tace, “Sosai ma Sir. I miss her so much”.
     “Thanks you”. Ya faɗa a taƙaice yana idasa hayewa.
      Da sanyin jiki Blessing ta koma kitchen dan ta haɗa masa wani ɗan abun duk da baice yana buƙata ba.
      Shikam Yoohan ƙofar sashensa ya buɗe ya shiga. Mayen ƙamshin turaren da Nu’aymah ta fara amfani da su yana nan nane da sashen. Cike dajin sabuwar kewarta ya shiga yana kalle-kallen falon. Tsahon mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya ya nufi bedroom ɗinsa. Harya tura ƙofar ya shiga sai kuma ya fasa ya dawo da baya. Bedroom ɗin Aymah ya nufa, yana ƙoƙarin saka key ya buɗe ya ga ƙofar a buɗe. cike da mamaki ya tura da sauri ya shiga. Turus yaja ya tsaya yana kallon yanda aka hargitsa ɗakin. Kayanta na sawa duk a watse a ƙasa. Littatafanta hardasu Al-qurani duk an yasar. Saurin ƙarasawa yay inda Al-qur’anin izu sittin ke a kife a ƙasa alamar jefarma da shi akayi. Ya ɗaukesa ƙwalla na cika masa idanu. Wani masifaffen fushi na yunƙuro masa da tarar masa a ƙirji.
       Babu wanda yazo masa a rai da yin wannan aikin sai Gebrail. Kodan dama yana nan a maƙale a ransane oho. Ajiye Al-qur’anin yay saman mirror ya fito a matuƙar harzuƙe yana ƙwalama Blessing kira….
     Hakan yayi dai-dai da shigowar su madam Chioma cikin falon suna dariyar shirmen Abraham. A kusan tare suka tsaya cak suna kallon yanda yake sakkowa daga upstairs ɗin da gudu-gudu. Ga wani razanannen kira da yake ƙwalama Blessing. Yana gama sakko idonsa ya sauka akan Gebrail da yake shigowa kusan a ƙarshe.
      Ture Blessing dake isowa gabansa jiki na rawa tana amsa kiransa yayi gefe. Cikin rufewar idanu na rashin ganin su mama debora ya nufi kan Gebrail da duk ya daburce saboda tsorata na rashin gaskiya. A bazata Yoohan ya saukema Gebrail wasu gigitattun maruka a jajjere bisa kumatu. Kafin wani ya samu damar jin ba’asin wannan tashin hankali ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukansa da shi kai kace ALLAH ne ya aikosa. Gaba ɗaya idon Yoohan ya rufe, Al-qur’anin nan kawai yake ganowa yashe a ƙasa da Nu’aymah a sume a randa Gebrail ya shigar mata.
       Tunda su madam Chioma suke a rayuwarsu basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin da matsanancin fushin Yoohan ba. A take falon ya rikice da kuka da kururuwar ihu. Ina Yoohan sam bama yajinsu. Laftar Gebrail dake ihu yashe a ƙasa iya ƙarfinsa kawai yake ta ko ina.
      Duk yanda madam Chioma da su mama debora ke kuka da masa magiya basa gabansa. hakama guards ɗin gidan kowa ya gagara matsawa inda Yoohan yake. Solomon da suka dawo tare da su Madam Chioma da yay ƙoƙarin matsawa wai ko Yoohan ɗin zai sauraresa sai da ya samu rabonsa. Dan zuba masa belt ɗaya Yoohan yayi jiki. Da wani irin mahaukacin tsalle da ihu yay gefe saboda azaba.
          Dukan Gebrail Yoohan yayi sosai har sai da yaga ya daina motsi, dan har papa daya shigo gidan tare da su Uncle Godwin bai sauraresuba. Sai da yay tiɓis shi kansa sannan ya jefar da belt ɗin gefe. Daga Momy harsu Joy kan Gebrail sukai suna kuka. Yayinda Momy Destiny ta riƙo Yoohan da shima ƙwalla ke silalo masa tsabar zafin zuciyar da yake a ciki. Zaunar da shi tayi a cikin kujera.
        A can gefe kuma Omar (Rich) daya shigo yanzun ne gidan, saboda ya fita tun safe. Tun a compound sauran guards ɗin gidan ke sanar masa abinda ke faruwa. Da sassarfa ya ƙaraso falon. A yanayin da yaga Gebrail da ihun Madam Chioma daya hargitsa falon da kururuwar cewar Gebrail ɗin ya mutu ya saka bama su Solomon daya gama shan tasa azabar umarnin cicciɓar Gebrail shi da sauran guards ɗin sufice da shi zuwa asibiti.
          Sannan ya ƙarasa inda Yoohan ke zaune yanata huci har yanzu da sassarfa. Cike da tashin hankali ya kamashi ya miƙar batare daya saurari ihun da Maman madam Chioma kema Yoohan ɗin a kai ba. Dan ya tabbata shirun da yay mata zuciyarsa sake kumbura take. Idan kuma har ya miƙe wlhy zai iya bugeta itama dan Yoohan ALLAH yay masa zafin zuciya na bala’i.
         Duk abin nan dake faruwa papa da su Uncle mike na tsaye suna kalonsu tamkar wasu gumakan farkon karni. Hakama baƙi da suka ɗan fara shigowa ziyara sunyi cirko-cirko da tsoro.
       Harabar gidan Omar ya fita da Yoohan da binsa kawai yake cike da rufewar ido. Turasa yayi a mota ya maida ya rufe tare da zagayawa mazaunin driver yaja ya fice da shi daga gidan. Kai tsaye hotel ya nufa da shi. A motar ya barsa yaje ya kama ɗaki sannan ya dawo ya sake kamashi ya shiga da shi ciki.
       Koda suka shiga cikin ɗakin zubewa Yoohan yayi a kujera kawai yana sauke wasu azababbun huci masu ban tsoro. Ruwa mai sanyi Omar ya ciro a fridge yazo ya miƙa masa. Fisgar robar ruwan kuwa yayi ya kafa kai. A mamakina sai gashi ya shanyeta tas yayi wurgi da robar yana juya idanunsa dake jajur abin tsoro.
____________★★★
         A ɓangaren Jay kuwa tun randa su Yoohan sukaje wa jensa a ranar kasa haƙuri yayi, da yamma liƙis ya shirya shi da Afrah suka nufi kano ta dabo gidan baba malam. Abinda bai taɓa yiba. Dan bai taɓa kai iyalansa gidanba tunda suke mu’amulat nasu.
     Sosai baba malam yaji daɗin ganinsa. Dan yamasa ziyarane ta bazata. Ya kumaji daɗin zuwa da Afrah da akai. Wadda bai taɓa saniba a ido, sai dai a baki. Shima bawai ya taɓa tantance ƴaƴan Jay ɗin maza ne ko mata ba. Duk da kuwa Jay ɗalibinsa ne sosai. Dan ya sanshi ne a dalilin mijin Ummu. Dan shiɗin ɗalibin mijin Ummu ɗinne acan saudia. To acan suka taɓa haɗuwa da Jay shi baba malam yaje miƙa gaisuwa ga malaminsa, shi ko Jay yaje  gaida Ummu ɗinsa ne da kuma yin Umrah shi da iyalansa.
       Tun a can suka ƙulla alaƙa. Bayan sun dawo Nigeria kuma Jay ya ringa zuwa ɗaukar karatu wajen baba malam ɗin a duk ranakun weekend lokacin suna a gari ɗaya.
      Har cikin gida baba malam ya kai Afrah. Inda ta samu ƙyaƙyƙyawar tarba a wajen Umm da Muhammad mai saurin sakin jiki da mutane. Cike da ƙwarewar aiki irin na Afrah data sha tun a cikin uwa da uba ta dinga jan Umm da hira akan hotunan Aymah data gani a falon. Umm kam tanada son yara. Gashi Afrah ta shigar mata rai lokaci ɗaya dan ta tuna mata da tata ɗiyar dake nesa da ita. Duk da kuwa Afrah zata girma Nu’aymah da kusan shekaru huɗu ma da wasu watanni, Afrah zatai shekaru ashin da biyu.
      A take Muhammad ya shiga bama Afrah labarin sister ɗinsa. Umm na tayasu da dariya dan sosai drama ɗin Aymah yake bama Afrah ɗin. Har ranta kuma taji kaɗayi dason ganinta.
       Lokacin da Baba malam ya shigo dan kiran Afrah da Jay ke jiran su wuce dan jirginsu ya kusa tashi sai Muhammad duk yay kalar tausayi. Umm ta haɗa mata kayan kwalliya da su kayan fulawa tanata saka mata albarka da godiya. Tare da roƙon ta dinga zuwa musu ziyara dan ita dai sosai yarinyar ta shigar mata zuciya…………….✍
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
[7/2, 2:08 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No 68
_______________
INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA…_
_KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR 🇩🇪 GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA… WADANNAN KAYA *MAAB LUXURY HOME* DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN *MAAB LUXURY HOME* SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA…_
_MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME…_
_SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR…_
_INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA😉? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH *MAAB LUXURY HOME* TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA.._
_AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN *MAAB LUXURY HOME*, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE.._
_MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:_
_DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR._
_DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN *MAAB LUXURY HOME*, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA: _
_INSTAGRAM: MaabLuxury home._
_WhatsApp number: +491521 4642007_
_Facebook: Maab Luxury Home_
_Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com_
_suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria. _
_KYAU, INGANCI, RAHUSA… SAI MAAB LUXURY HOME_
_______________
   No. 68
…………Sun fito har ƙofar gida Muhammad biye da su zai mata rakkiya. Shima Jay ya jashi a jiki da kulawa. Anan ne yake tambayarsa miyyasa yaga yana fushi. Hawaye cike da idonsa yace, “Uncle Please ka bar mana Aunty anan ta zauna. Kaga Aunty N Uncle Yoohan ya gudu min da ita. sai ni kaɗaine a sashenmu. Ni kuma inason na dinga ganina da abokiya kamar Aunty N”.
      Cike da ƙaunar yaron Jay ya sumbaci kumatunsa yana ƴar dariya. Yace, “Oh woow sarkin wayo. inko hakane na maka alƙawarin Aunty Afrah zatazo maka hutu dan tana hutu dama yanzu haka”.
     Cike da ɗoki Muhammad yace, “Uncle yaushe?”.
     Yanda yayi ɗin har saida yasa baba malam da Afrah da Jay dariya. Jay yace, “Karka damu zaka iya ganinta a koda yaushe”.
      Duk da Muhammad yaso jin ranar da zatazo dai sai yayta ɗoki. ya koma cikin gida da gudu ya sanarma Umm.
     Bayan wucewar su Jay da kwana biyu Muhammad ya addabi su baba malam da zancen yaushe Aunty Afrah zata zo? Shifa idan bazatazoba to shi a kaisa gidansu yay hutu. Ganin ba hutu suka samuba shi sai baba malam ɗin ya kira jay da bukatar yaushe Afrah zata zo ɗin. dan sufa an saka musu zuma a baki kuma duk sun ƙagu. Hakan yama Jay daɗi, dan shirinsu na tafiya yanda ya kamata cikin rahamar ALLAH.
      Bai wani ja zancenba yace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kawota da kansa insha ALLAHU. Wannan shine dalilin samun ƙofar shiga gidan su Nu’aymah da Afrah ta samu domin cika aikin ysyarta. Dan haka a safiyar yau kuma lahadi ta tashi da shirin tafiya can zatai zaman wata ɗaya rak insha ALLAHU.
      Sai karfe biyar na yamma Anuwar ya gama shirin kai Afrah kano gidansu Aymah. Dan haka bayan ya kammala shirinsa tsaf ya saka Al-hassan Ya kira masa ita a can sashen Uncle Anuwar. Dan ita acan take zaune kamar yanda little bee ma acan tai rayuwarta har tayi aure. Tsakaninta da sashen iyayenta sai dai tazo gaisuwa kawai ko hira. Amma ita Uncle Anuwar da aunty Nabeelah ne iyayenta. Sauran yaran kuma Miemaa da Abie.
      Tana zaune a falo hankalinta akan lap-top tana hidimarta Al-hassan ya shigo  da sallama. Kasancewar yayima Aunty Nabeelah laifi yau da safe. ta kuma tabbatar masa idan ta kamashi sai ta zanesa sai ya dogare a bakin ƙofar yana kalle-kalle. Daga can yace, “Aunty Afrah kizo Abie na kiranki”. Bai jira ko amsarta ba ya shilla waje da gudu saboda leƙowar aunty Nabeelah dake kitchen dan jin muryarsa da tayi.
     Aiko mi Afrah zatai inba dariya ba. Tace, “Mamma wlhy kin hana auta Sukunin shigowa sashen nan yau gaba ɗaya. Ɗazun ina kallonsa daya hangoki kin fita har faɗuwa yake wajen tiƙar gudu zai shige sashensu”.
     Dariya Nabeelah tayi itama da faɗin, “Ai ya gama gudunsa babu fashi saina ruɗa masa jiki da bulala tunda shi bayajin magana. Iskancin yaron nan baya tashi sai ya ga su Miemaa na gida. To in ALLAH ya yarda shi abin nema da tsokana ya samu a wajensa tunda yasan basa bari a taɓasa”.
      Miƙewa Afrah tai tana dariya da zura Slippers a ƙafarta. “A daiyi haƙuri Mamma na. Bara naje Abie na kirana inaga ya gama kimtsawa”.
      A take mood ɗin Nabeelah ya canja. Cike da damuwa tace, “Kai ni dai wannan aiki nasu Abie yana moremin, da ƙarfi da yaji ya maida kowa jami’insu a gidan nan, ALLAH banason kina nesa dani ko kaɗan. Amma yaya zanyi, nanda lokaci kaɗanma zaki gudu gidan aurenki ki barni da kewa ta haƙiƙa kamar yanda little taimin.
      Ƙasa Afrah tayi da kanta kawai cike dajin kunaya. Sai dai bata iya cewa komaiba dai.
        Sallamarta Nabeelah tayi ta tafi dan tasan Jay jiranta yake. Ilai kuwa ta iskesu a falonsa shi da Miemaa suna jiranta. sai da tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga. Bayan ta durƙusa ta gaishesu ne Jay ya nuna mata gabansa alamar ta zauna. Babu musu tazo jikin ƙafafunsa ta zauna cike da ladabi da ƙaunar iyayen nasu.
      Gyaran murya Jay yayi yana kallonta fuska babu wasa. Yace, “Afrah!”.
       “Na’am Abie”.
Ta amsa masa kanta a ƙasa.
      Zamansa ya sake gyarawa sannan ya cigaba da faɗin, “Inason ki nutsu ki saurareni. Duk da bani da fargaba a kanki game da aikin nan tunda nasha sakaki inason sake jaddada miki muhimmancin na wannan lokaci. Kisa hankalinki da ƙyau dan banason kuskure a ciki. Baba malam yanada muhimmanci mai girma a gareni dake kanki. Inason kiyi komai da ƙwazo da hikima ok?”.
       “Insha ALLAHU Abie zanyi duk yanda kace. Kuma zan kula nayi komai yanda ake buƙata. Kudai tayani da addu’a”.
        “To Alhmdllh, addu’a kuwa dama akoda yaushe cikin yi muku ita muke. ALLAH ya baki nasara yay riƙo da hannunki kiyi komai cikin sauƙi. Wannan camaras ne”. Yay maganar yana miƙa mata wasu ƴan ƙananan dutsuna tamkar diamonds kusan goma. “Dasu zaki tafi, inason kibi duk sashen gidan ki maƙalasu a kowanne parlors. Idan sun wadata har Backyard na gidan dan suma wajene da masu baƙin hali zasu maƙale suyi magana. Ki ajiyesu da tsantsar kulawa yanda babu wanda zai gane minene. Duk da nasan koda a zahiri suke bawai ganewar zasuyiba inba dai ganinsu da yawa yasa suyi tunanin wani abun kuma daban ba. Inhar kika samu nasarar saka cctvs ɗin nan a ko ina na gidan to aikin zaizo da sauƙi insha ALLAHU. Dan zasu bamu damar kula da motsin kowa hankali kwance. Banason Little da Dawood susan komai kan camaras ɗin nan, wannan aikinane ni kaɗai zakimin.  Abu na biyu shine saka ido akan duk wani baƙo da zai shigo gidan. Ma’aikatan gidan da yaran gidan suma. Banda wauta da surutu mara amfani, duk da namasan waɗanan ba halayenki bane. Biyayya ga nagaba. Aiki basai ance tashi kiyiba tunda nasan iyayenki sun tsaya akanki babu abinda baki iyaba. Dan ALLAH ki kula da mutuncin kanki dan gidane family house akwai samari a ciki. Duk da har raina bana zargin rashin tarbiyya daga wannan zuri’ar koda a mafarkina. Amma dai dolene na jadada miki kame kanki da kuma kula da ibada dan na fahimci aikin zai kaiki har cikin azumi dake gabatomu”.
        “Inasha ALLAHU Abie zaka sameni mai kiyayewa”.
    “To ALLAH yay miki albarka da sauran ƴan uwanki baki ɗaya”.
      Amin ta amsa ita da Miemaa dake saurarensu. itama daga baya ta ɗora da nata nasihan da wasu dabarun aikin. Duk da kuwa tunda aka tsura maganar cikin koya mata take salo-salo harma Jay din kansa. To Alhmdllhi kuwa tana haddace komai. Dan dama itama bata wasan yara bace wajen tsayawa tsayin daka akan aikin nan da ba yau iyayenta suka fara tsundumata a ciki ba.
        Anuwar da kansa ya kai Afrah ɗin Kano. Dan akwai harkar business ɗinsa da zaiyo acan. Koda jirgi ya diresu kuwa ana sallar magriba. Amma duk da haka sai ya fara kaita suka gaisa da baba malam yay sallar har isha’i acan sannan ya wuce nasa harkokin. Duk da baba malam ɗin yaso ya kwana anan amma fir ya ƙi saboda uzirinsa.
         Da ga Muhammad har Umm sunyi matuƙar jin daɗin zuwan Afrah. Dan gaba ɗaya saita ɗauke musu kewar Nu’aymah. Tun a daren Umm ta kaita sashen hajjo ta gaisheta. Nanma ta samu tarba sosai a wajen ƴar tsohuwar. Dan nutsuwar Afrah ɗin ya saka hajjo jinta a ranta. Taita tsokanarta kuwa tamkar yanda takema jikokinta idan taso. Afrah komai bata iya cewa sai murmushi. Dan miskilace ta gaske itama kamar little. Tama dama Jay da bily ɗin a miskilanci dan ta gada a uwa da uba da yaya. Idan kaji tana hira da dariya to Mammata ne (Nabeelah) ko Daddynta (Anuwar). Sai ko Miemaa da Abienta shima.
       Basu baro sashen hajjo ba sai lokacin kwanciya. Umm ta kaita ɗakin Aymah da aka gyara mata tsaf, kayantama tuni suna can. Sosai ɗakin yayma Afrah ƙyau. Taita kallon hotunan Nu’aymah da aka mammaƙala a bango. A hankali tace, ‘Masha ALLAH ƙyaƙyƙyawa da ita kuwa’.
_______________★★★
           *_U.S_*
   Sosai Nu’aymah batajin daɗi. Dan ma Juliet tsaye take sosai wajen kula da ita. Dan ta fahimci laulayin ciki takeyi. Sosai taji tausayin yarinyar ya kamata. Yaushema aka gama rainonta da za’ace itama ta samu ciki. Gaskiya tana mamakin ganganci irin na baƙar fata. Kasa haƙuri tayi sai da taima Omar wannan complain ɗin. Shiko yay dariya tare da mata faɗaɗɗen bayanin data gamsu, harta koma bin Nu’aymah da addu’ar fatan sauka lafiya.
              Duk da Aymah tanata ɓoyema kowa halin da take ciki na ciwon da ita ɗauka take Thypoid ɗinta ne ya motsa yau dai ta tonama kanta asiri batare data farga ba. Dan suna waya dasu Umm da Muhammad ya takura a kira a kirata ya sanar mata yayi sabuwar Aunty. Bayan sun gaisa da Afrah da Muhammad ɗin Umm ta amsa wayar suka gaisa itama. Cike da shagwaɓa Nu’aymah tace, “Umm Yah Yoohan yazo?”.
      “Oh dama ya shigo ƙasar?”.
“Eh Umm. Yaufa kwanansa uku”.
      “To Abbanki ya manta, ni koma maganar bamuyi da shi ba. Amma kinsan shi da uziri, nasan zaizo insha ALLAH”.
       “Umm idan yazo kiyi min yajin daddawa da farin yaji, da ɗan wake, da alawan madara, da iloka. Da fara. Da manja. Da aya suyan gishiri. Da…….”
       “Oh ni Firdausi wannan lissafin kumafa Nu’aymah?”.
       Baki ta tura gaba kamar tana gabanta. “Umm duk so nakeyi fa dan ALLAH”.
       Ɗan jimmm Umm tai na hasashe. Sai kuma tace, “Niko Nu’aymah ai period ɗinki ya dawo ko?”. Tai mata tambayar cike da salon bugar ciki irin na manya.
      Zimbir Nu’aymah ta miƙe zaune. Dan ita kuwa man kanta ma ya tsiyaye tas ta shafa’a da zancen rashin ganin period. Ai idanma bata manta ba rabonta da jini tun na abinda ya faru. A randa ta fara jin alamun zuwansa kuma Accident ɗin nan ya faru suka wuce Austria. Daga nan bata saniba tayi ko batayi ba? Tunda bata cikin hayyacinta……..
      “Kinajina kuwa Nu’aymah?”. Umm ta katse mata tunani.
    Da ɗan rawan muryan shiga ruɗani tace, “Umm wlhy ni tun na lokacin nan ban sakeyiba. Na shiga uku Umm na kamu da wani ciwo ko?”.
      Dariya ce taso kufcema Umm, amma sai ta gimtse da sauri tana saurin faɗin, “A’a lafiyarki ƙalau. Inaga saboda kinyi wancan rashin lafiyarne shiyyasa. Zanma mijinki magana ya baki magani”.
     Cike da sanyin murya tace, “To Umm. Amma dan ALLAH ki haɗamin duk abinda nace idan Yah Yoohan zai taho yazomin da su. Harda garin dawa na tuwo fa Umm. Da daddawa da kuka da bushashshen kuɓewa dan ALLAH”.
         “To zan haɗa miki duka insha ALLAH. Amma kayan kamar zasu masa yawan ai Nu’aymah”.
     “Ni dai Umm dan ALLAH ki taimakeni. Wlhy duk banason abincin garin nan yanzu. Coffee kawai nake iya sha sai gasashen kofi. Amma sauran abincin da naci sai nayi amai. Abincin Austria yafi na nan min daɗi”.
       Umm dai na murmushi ta amsa mata. Daga haka sukayi sallama dan Juliet jiranta suke zasu fita shagon shan coffee ɗin na ƙa’ida. Itama taɗan motsa jiki daga can.
____________★★★
         Tunda ya kawosa hotel ɗn ko sau ɗaya bai tambayesa miya fruba. Shi kuma baice dashi komaiba dan ransa a ƙololuwar ɓace yake. Yadda Al-qur’anin nan yafi komai zafafa masa zuciya. Dan har yanzu fushinsa yaƙi sauka. Daya rufe ido dan yai barci sai ya hango Qur’an a ƙasa a yashe. Daga ƙarshe dai har dasu yin hawaye.
      Sanin halinsa idan yay fushine ya saka Omar yanke shawaran kiran Nu’aymah. Juliet ya turama text message dan taja ra’ayinta.
       A lokacin basuyi ko mintuna biyar da shigowa gidan ba. Aymah na kwance a falon saman tiles idonta a rufe. Sai dai ba barci takeba. Hasalima tunanin Yoohan takeyi dan rabon da suyi waya tun jiya da yace mata zai koma Abuja daga kd….
      Gyaran muryar da Juliet tayine ya saka Aymah buɗe ido tana kallonta. Juliet ta ɗaga mata gira ɗaya tana murmushi, yayinda duk hannayenta ke akan cikinta tana shafawa. “Da zaman tunani ai gara kiyi kiransa” tai maganar cike da tsokana. Murmushi Nu’aymah tayi da gyara kwanciyarta tana fuskantar Juliet ɗin. “Ke dai faɗa mana gaskiya. Ko kina kewar Yah Umar ne ni zaki nanamin?”. Kusan a tare suka kwashe da dariya. Juliet ta miƙe tana faɗin, “1-1 kenan. Ni bara naɗan watsa ruwa na kwanta”.
        Juliet na shigewa Aymah ta sauke numfashi. Cike da son jin muryarsa kuwa ta lalubo hotonsa a wayarta tana kallo. Kamar kuma an tsikareta sai kawai tai kiransa. Shigowar kiran Aymah yayi dai-dai da sake sakkowar hawayen Yoohan. Dan ji yake kamar zuciyarsa zata ƙone. Sam dukan da yayma Gebrail ɗin bai wadacesaba….
     Kamar bazai kula wayar ba sai kuma ya buɗe idanu a hankali. *_My Sweet girl_* daya ganine ya sakashi ɗauka a kasalance. A kunne kawai yasa batare da yayi magana ba. Daga can Aymah ta sauke sassanyan numfashi. Sai dai itama batayi maganarba. Sun share kusa sakan goma sannan ta ƙara sauke numfashi da faɗin, “My boo yau miskilawan ne a kusa?”. Shiru baiyi maganaba. Hakan yasata fahimtar akwai damuwa. Dan a ɗan zamansu ta fara fahimtar wasu da yawa halayensa. Musamman fushinsa da farin cikinsa. Kwanciya ta gyara tana lumshe idanu. Cike da nutsuwar data ɗan farayi na wahalar ciwo tace, “Waya taɓa ɗan lelen Abba ne? To lallai ya nema wajen ɓuya tun kafin na kira Abba na sanar masa ɗan lelensa na fushi da kowa har Silly girl ɗinsa”.
       A bazata murmushi ya ɗan kufce masa. Sai dai idanba lura kayi ba bazaka taɓa fahimtar yayinba. A hankali yace, “Parrot, ke dai bakison barin bakin mutane ya zauna shiru”.
     Baki ta kumbura cike da sakalci tace, “Ai yanzu parrots ɗin biyu ne. Dan kaima ALLAH ka shigo tawaga Yah Yoohan”.
     “Silly girl”.
Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa.
      Murmushi tayi mai faɗi tana lumshe idanu. Sai kuma ta dai-daita muryarta, cikin nutsuwar da inta gadama zaka sameta da ita tace, “I’m so sorry My Handsome. Nifa kaga idan aka bani haushi a gidanmu mi nakeyi da?”.
       Yace, “Uhm-uhm”.
Sake gyara kwanciyarta tayi tace, “Sai in ɗauki Al-qur’ani naita karatu. Zakaga inata kuka a farko, kafin wani lokacin kuma sai na samu nutsuwa na cigaba da karatun da nishaɗi. Cikin amincin ALLAH bana ajiye Qur’anin nan sai zuciyata tamin sanyi”.
      Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Murya da matuƙar sanyi yace, “Zeeynab I love you. Ke ta dabance a rayuwata”.
      Murmushi tayi kawai. Kafin a hankali tace, “Thanks you Uncle Boo”.
     Kansa ya jinjina mata a hankali. Sai kuma ya yanke wayar batare da yace mata komaiba. Omar dake gefe yana jinsa sai dariya yake dannewa. Batare da Yoohan ya kallesa ba yace, “Umar Al-qur’ani”.
      “Okay bara na kawo maka a mota”.
  Cikin mintuna ƙalilan Omar ya dawo masa da Qur’ani. Tashi yayi yayo alwala ya dawo ya zauna. Cike da bin shawarar Aymah ya fara karatu. UBANGIJI mai Rahma mai jin ƙai sai ga Yoohan ya sami nutsuwa cikin lokaci ƙanƙani. jiyay tsoron ALLAH ya ƙara ratsashi. Ya shiga jeramasa kirari da godiya bisa koyarwar Nu’aymah.
      Umar ma yaji daɗin ganinsa ya dai-daita a lokaci ƙan-ƙani, dan haka yaje ya samo masa abinci har suka ɗan zauna suka tattauna akan abinda ya farun. Omar yaji a ransa ba Gebrail bane ya shiga ɗakin Aymah. Ya taka sawun ɓarawone kawai da kuma zafinsa da Yoohan ɗin yakeji dama. amma sai yay shiru baice komaiba. Dan yafi buƙatar Yoohan ya fahimci wanene mahaifinsa da kansa.
______________★★
          A gidan su Yoohan kuwa uffan papa baiceba game da dukan Gebrail da aka kai asibiti a sume da Yoohan ɗin yayi. Su Uncle Mike ne ma keta faɗa da son jin miya kawo rikicin? Sai dai amsa ɗaya suke samu. Shine kowa bai saniba. Dan iya abinda idanunsu ya gani kawai suke faɗa jama’ar gidan.
     Har zuwa lokacin da labarin farfaɗowar Gebrail ɗin yazo kunnensu papa dai yaƙi yace uffan. Sai da daddare bayan sunje sun duba shi a asibiti bisa tursasawar mama debora da maman madam Chioma da yau sukaci masifa har bakunansu sukai tsaho. Bayan barowar tasu asibiti ne papa ya kira Baba malam da shi har yanzu ma baisan Yoohan na ƙasar ba. Dan sunata shirye-shiryen bikin sauka da auren yaransu na gidan marayu nanda bayan salla babba. Yayi Busy da yawa. Rabonsa dayin waya da Yoohan tun yana Oman.
      Yasha mamakin ganin kiran papan. Amma sai ya ɗaga yana ambaton sunan ALLAH. Baiyi sallama ba, sai cewa da yay, “Barka da dare Pastor Goshpower. Yau kaine ka tuna da Soorajidden bin Hashim?”.
      Wani wawan tsaki papa ya sauke a jere. Batare da jiran cewar baba malam ba ya fara zazzaga masifa. “Kai ɗin banza da zan ɗauki waya na kiraka. Gargaɗi na kira na maka a karo na farko kuma na ƙarshe. Ka rikitamin yaro gaba ɗaya ya fita hayyacinsa. Sai yanzu na gama fahimtar manufarka akan ɗana. So kake ka maida minshi ɗan ta’adda shiyyasa ka aura masa wannan shegiyar ƴar taka mai zuciyar dutse? To wlhy Sheikh Sooraj kafin kaga bayana nine zanga bayanka. Sanna kayi gaggawar sakarmin kurwar yaro. Ka kuma saka ya maido maka ƴarka gida tun kafin lokaci ya ƙure maka. Idan ba hakaba na rantse saina halakata da hannuna kafin kaima na halakaka…”
     Kafin baba malam yace wani abu papa ya yanke wayar. Nannauyar ajiyar zuya baba malam ya sauke kawai yana girgiza kansa. a gaba ɗaya kalaman papa babu wanda ya bashi tsoro. Abinda ya fahimta kawai shine cikin fushi yake. Duk da kuwa yasan papan zai iya aikata duk abinda ya lissafa masa. Abinda kawai ya sakashi a ruɗani shine, ‘Miya faru?’.
      Ganin bashi da mai bashi amsa sai kawai ya ajiye tunanin ya cigaba da harkar gabansa.
__________★
       Yoohan ko takan gidansu bai sake biba. ya dai saka Omar zuwa da mai saka keys ya sabunta duk keys ɗin dake a sashensa. Da yake lokacin duk ƴan gidan sun fita, su mama debora kuma na wajen Gebrail sai babu wanda yasan mi akayi. Solomon dai yaso shiga ya duba sai dai fitowar Omar yay masa katanga da hakan. Dan yana kai mai saka keys ɗin shi fitowa yay dan ya hana su Solomon ɗin kowacce damar sanin abinda ya farun. Sosai ya jima da fahimtar wanene Solomon dama. Labarin korosa da Aymah tasa akayi kuma da Yoohan ya bashi ne ya sake tabbatar masa akwai wata a ƙasa. Sai dai komai sake ɗaure kansa yakeyi shikam. Dan baiga miye dalilin aikata abu a sarƙaƙe da su papan keyiba game da Yoohan ba.
           Shiri yay tsaf domin shiga Kano. yanason daga Kano Lagos zai nufa. Yay kwana uku su juya U.S shi da Omar.
     Misalin huɗu kuwa Yoohan da Omar suka iso anguwar su Nu’aymah. Kasancewar anata hada-hadar shiga salla sai kawai suma sukai alwala suka shiga. Bayan an idar sun fito Yoohan yaketa faman jan ƙananun tsaki saboda kallon damutane suketa musu. Duk da yasan wasu a cikinsu sunriga da sun sanshi zuwa yanzun. Amma duk sanda zaizo basa iya daina binsa da kallo kamar wani baƙo. Ya rasa mi suke kallone wai? Gashi shi kuma ya mugu-mugun tsanar a sakamasa ido.
      Umar daya san dokar dai yanata murmushi. Dan ya tabbatar kallon ne ya bama Yoohan ɗin haushi. Bai dai ce komaiba har suka sami iso daga baba malam ta hanyar malam ƙarami daya fito ya gansu. Sakawa yay malam ƙarami shiga dasu cikin gida, shi kuma ya nema alfarmar ɗalibansa shima yabi bayansu. Sashen hajjo aka kaisu. Dan mutuniyar Yoohan ce yanzu sosai. Danma bajin zancen juna sukeba sai da tafinta. Amma a wannan karon hajjo ta fahimci Yoohan ya fara jin hausa kaɗan-kaɗan. Takoji daɗi, duk da harshen nasa a karye yake. Wani abunma koya faɗa bata ganewa.
      Sosai aka cika musu gaba da kayan ciye-ciye. Shi dai Omar nasa kallo ne da tayasu dariya. Dan yau ne karan farko daya shigo gidan. Anan baba malam ya samesu kuwa. Suka gaishesa da tsantsar girmamawa. yayinda shima da kulawa yake amsa musu da tambayar iyali. Da ga haka suka ɗan zauna hira. Anan hajjo kejin Omar ma abokin Yoohan ɗinne, kuma ya muslinta. Daɗi sosai ya sake kama Hajjo. Lallai tarkonsu ya kama kurciya. Dan ga nasasorin auren Yoohan da ɗiyarsu nan sun fara bayyana.
      Daga Sashen Hajjo baba malam ya shiga da su dan su gaida Umm. Yasan dai ganin Yoohan ɗin zaisa taji sanyi a ranta da raguwar kewar Nu’aymah. Aiko hasashen baba malam ɗin yayi dai-dai. Dan sosai Umm taji ɗunbin daɗi, duk da kuwa akwai ƴar kunya a tsakaninsu. Dan daga ita har shi babu wanda ya iya saka idon juna. Da yake sun iske Addah a sashen itama suka gaisheta. Ta amsa musu da kulawa tanata tambayar ɗiyarta Nu’aymah.
      Suna ɗan hira da Addah ne, wadda ta kasance duk akan Nu’aymah Afrah da Muhammad da suka dawo daga islamiyya suka shig falon da sallama. Kallonta duk su Yoohan sukayi. Itama fuska ɗauke da nuna rashin sani a garesu, dan miskilace ta gaske, ga salon aiki. ta shiga gaidasu tana ƙoƙarin wucewa ɗakin Aymah daya zama nata yanzu batare ta nuna alama tama taɓa ganin mai kama dasu ba a rayuwa. Su dai da kallo kawai suka bita. Yayinda Yoohan ya miƙama Muhammad hannu alamar yazo garesa.
       Muhammad akwai wayo, dan haka tsaf ya gane Yoohan. Hannu ya bashi sukai musabaha. Yoohan ya shafa kansa yana murmushi, yace, “Oh my dear Friend ka ƙara girma fa”. Cike da jin daɗi Muhammad ya zauna kusa da shi yace, “Thanks Uncle. Ina Aunty N ɗina?” Yay maganar yana waige-waigen neman Nu’aymah.
           Murmushi Yoohan yayi yana ɗan rungumo Muhammad ɗin jikinsa. Yayinda Omar ke bashi amsa yana dariya. “Ta maka wayo tana U.S abinta”. Da ƴar damuwa Muhammad yace, “To Uncle yaushe zatazo itama?”.
       Yoohan yace, “Soon insha ALLAH Darling. Amma karka damu idan kunyi hutu zan kaika ka ganta”.
     Daɗi sosai ya kama Muhammad, nafa ya shiga tsallen murna su Addah na masa dariya.
      Sai bayan isha’i su Yoohan suka bar gidan da kayan Nu’aymah ghana must go guda. Baba malam baicema Yoohan komaiba game da wayar da sukayi da papa. ya da masa nasiha cikin hikima shi da Omar ɗin akan muhimmanci iyaye. Ta hakane Yoohan ya ɗan tsargi akwai abinda ya faru kenan. Amma sai shima baice komaiba.
        Ƙarfe goma na dare suka wuce Lagos. Inda zasu kwana uku yay aikin daya kawosa 9ja ɗin.
★★★
       Tunda suka shigo lagos Yoohan bai samu kansa ba. Aiki yake tuƙuru tamkar yanda ya saba hidima ga al’umma. Ya ɗanyi wasu ziyarce-ziyarce dake ransa. Batare daya sake bi takan su papa ba suka wuce U.S shi da Umar.
  *_U.S_*
        Kasancewar su Nu’aymah sunsan da dawowar mazajen nasu a ranar da safe Juliet ta maida Nu’aymah gidanta. Yaɗanyi ƙura kaɗan kuwa saboda rashin mutane. Dan haka Juliet ta taimaka mata suka gyara duk da Aymah na hanata. To itama dai ƙarfin haline dan a jigace take komai. Bayan sun kammala Juliet tai mata sallama ta koma nata gidan.
      Cike da ƙarfin hali Aymah taima Yoohan girki. Da ƙyar kuwa ta kammala tai wanka. Batare da tabi takan wani kwalliya ba tai shiri cikin Bomshort jeans bleu da pink top kawai tazo falo ta kwanta a ƙasan tiles kamar yanda takeyi a yanzun. Duk da kuwa da farko taci alwashin masa kwalliyar tarba amma hakan ya gagareta. Cike da rashin jin daɗin jiki kuwa barci yay awon gaba da ita a wajen. Ga zazzaɓi mai zafi daya fara saukar mata na yamma.
        A ƙagare Yoohan yake da son ganinta. Hakan yasa yaƙi yarda su hau cab ɗaya shi da Omar. Duk da kuwa kusan anguwa ɗaya suke. Sai ma an fara sauke Omar ɗin a gida kafin a ƙaraso nasu.
        Tsabar zumuɗi a barandar gidan yabar kayan da yazo dasu ya shige ciki. Sassanyan ƙamshin daya doki masa hancine ya sakashi lumshe idanu. Kafin ya buɗesu a hankali kan Aymah dake kwance a ƙasan tiles barcin wahala yay gaba da ita. Kallonta yake da matsanancin shauƙi da kewa. Ya taka a hankali zuwa inda take. Tsugunnawa yay a gabanta ya ɗaura tattausan hannunsa saman fuskarta dake shining na masu ciki ya shafa yana sauke ajiyar zuciya. Ko motsi batayiba kuwa. Sai ma numfashi da take saukewa a hankali. Zamewa yay ya zauna. ganin baya ganinta da ƙyau sai kawai ya kwanta shima ya ɗora kansa saman filon datake kwance yana kallonta da ƙyau. Sai dai kwanciyar tasu ta kasance tamkar kai da ƙafa bawai a jere ba. Hakan yasa goshinsa na saitin haɓarta ne. Itama nata goshin na saitin tasa haɓar. Yanda take busa masa numfashinne shima yana busa mata nasa ya sakashi sauke ajiyar zuciya idonsa ƙyam akan ɗan bakin tsiwarta. Matsar da kansa yayi a hankali ya daidaita bakinsu. Tare da ɗora hannunsa ya ringumo kanta jikinsa ya fara kissing nata cike da zalama da kewa.
       Cikin barci Nu’aymah taji salon da duk duniya na mutum ɗaya ne a gareta. Batare data buɗe idanuntaba cikin kasala itama takai hannu bisa kansa ta ringumosa tana mai bashi haɗin kai yanda tasan yana buƙata. Sunfi minti shida a haka sannan ya barta yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan harga ALLAH harya hau network.
      Shanyayun idanunta ta buɗe a hankali tana kallonsa. Dan har yanzu yana akan filon bai tashi ba. Murmushi yay mata mai sanyi, ya maida hannunsa akan fuskarta suna kallon juna cikin ido.
    “Welcome my boo”.
Tai maganar a hankali kamar mai tsoron ajisu.
     Lumshe idanunsa yayi ya sake buɗewa a kanta. Cikin ɗan sake matsar da kansa jikin fuskarta yace, “Sweet girl mike damunki?”.
     Maimakon ta bashi amsa sai hawaye shar. Saurin tashi yayi zaune har jikinsa na rawa……….✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 69
______________
INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA…_
_KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR 🇩🇪 GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA… WADANNAN KAYA *MAAB LUXURY HOME* DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN *MAAB LUXURY HOME* SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA…_
_MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME…_
_SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR…_
_INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA😉? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH *MAAB LUXURY HOME* TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA.._
_AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN *MAAB LUXURY HOME*, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE.._
_MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:_
_DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR._
_DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN *MAAB LUXURY HOME*, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA: _
_INSTAGRAM: MaabLuxury home._
_WhatsApp number: +491521 4642007_
_Facebook: Maab Luxury Home_
_Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com_
_suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria. _
_KYAU, INGANCI, RAHUSA… SAI MAAB LUXURY HOME_
______________
     No. 69
…………“Oh God baby”. Ya faɗa da kamota ya tayar zaune. Sakata yayi cikin jikinsa ya rungumeta. A tare suka sauke ajiyar zuciya kowa kewar ɗan uwansa na ratsashi.
         Sake lafewa tai a jikin nasa tana mai shaƙar ƙamshinsa da ke mata daɗi sosai. Yayinda shi kuma ɗumin jikinta ke ratsashi, tare da tausayinta har ƙasan zuciyarsa. Harga ALLAH yana matuƙar son yara. Musamman a yanzu da yayi aure. Badan hakaba daya cire mata cikin nan dan tayi ƙanƙanta yake gani. Duk da kuwa shi likitane daya zaga cikin duniya. Yayi gamo da mutane iri-iri harma waɗanda basu kaita a shekaruba ya gansu da cikin kuma sun haihu lafiya.
      Jin tana neman fara barci ya shafa mata fuska. Idanun ta buɗe a hankali da ɗagowa ta kallesa. Sai kuma ta bi jikinsa da kallon mamaki. Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda ash color mai duhu. Tasha ɗinkin da yay dai-dai da samarin wannan zamanin. Hardasu hula ƙube. A bazata murmushi ya suɓuce mata. Ta sake kwantawa a jikinsa da zagayesa da hannayenta tana murmushi.
      “Hausa man”. Ta faɗa cike da shauƙi.
      Murmushi yayi mai faɗi ganin taji daɗin ganinsa da shigar yarenta. Ya miƙe ɗauke da ita yana ƴar dariya da faɗin, “Hausa man mijin hausa girl”. Dariya suka ƙyalƙyale da shi a tare, dan yanda yay maganar dole ya baka dariya. Ta kai hannu kan tattausan sajensa dai-dai yana zama da ita a kujerar. Tace, “Mun haɗu fa da yawa. Dan irinmu a tarihi kaɗanne”.
       Murmushi ya sakeyi mai faɗi yana lumshe ido da buɗewa a kanta. Zai bata amsa kira ya shigo wayarsa. Karkatawa yay kaɗan ya ciro wayar a aljihun gefensa. Hakanne ya bama Aymah damar sauka dan ta tuna ko ruwa bata bashi ba. Da kallo ya bita yana sauke wani nannauyan numfashi da har ya kai Osin jinsa da ga can.
           Cikin son ƙarfafa kanta ta haɗa masa ruwa da kofi a ƙaramin tire. Duk da ta fahimci bai cika damuwa da kayan lemo-lemon nan ba ta ɗauka masa shima. Falon ta dawo inda ta barsa har yanzu yana waya. Ta ajiye tiren a table taɗan kallesa. Shima idanunsa ƙyam akanta. Lemo ta fara nuna masa, ya girgiza mata kai alamar a’a. Hakan yasa ta buɗe ruwa. Koda ta miƙo masa sai ya haɗa da hannunta ya maidata saman cinyarsa. Jin numfashin daya furzar ya saka Osin faɗin, “Mr X anya kuwa kana cikin nutsuwarka?. Nikam sai anjima. Ina magana kanata min uhm, ah, a’a”.
     Murmushi Yoohan yayi mai sanyi yana kai hancinsa bisa dokin wuyan Nu’aymah. Osin bai jira amsarsa ba ya yanke wayar cike da jin haushi dan magana dama yake masa akan su papa. Shi kuma harga ALLAH Yoohan hankalinsa gaba ɗaya Aymah ta tattareshi kojin Osin ɗinma bayayi da ƙyau.
       “Yah Yoohan zakasa na jiƙamu fa”. Ta faɗa cike da shagwaɓa”. Tai maganar tana ɗan ture masa kai Jin yana neman ruɗar mata da jiki. Bai iya cemata komaiba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ta gama narkar da shi. Ya kamo hannunta da ruwan ke ciki ya kai bakinsa kozai samu sassauci. Dama gashi ƙishin yakeji. Tas kuwa ya shanye shi.
      “A ƙaro?”.
   Kai ya girgiza mata da lumshe idanu yana jingina kansa da kujera.
       Gaba ɗaya ƙoƙarin Nu’aymah neman gazawa yakeyi, cike da son danne halin da take ciki tace, “Muje kayi wanka ga abinci ma”.
         Idanun ya buɗe ya zuba mata su. Dan ya fahimci tanayin komai da ƙarfin haline. Yanzu haka har cikin jikinsa jin zafin nata jikin ya keyi. Baice komaiba ya kamata ya miƙar yana faɗin, “Fara bani abincin naci yu nwa nakeji”.
       Koda suka zauna a dining ɗin duk sai taji batason ganin abincin kuma duk da itace ta girkashi. Fahimtar hakan da Yoohan yayi ya sashi cemata taje ta kwanta zai zuba. Da sauri kuwa tabar wajen. Binta yay da kallon tausayi, tana ƙoƙarin kwanciya a ƙasa yay saurin faɗin, “No ba ƙasaba. Koma saman kujera ko kije ɗaki”.
     Sosai ta ɓata fuska zatai kuka. “Please Yah Yoohan, wlhy banason ko ina sai nan. Yafi min daɗi”.
      “Bazai yuwuba Sweet girl, wannan sanyin illane a gareku ai. Indai kika kwanta a wajen nan tofa na fasa baki maganin zazzaɓi kawai zan haɗa da allura….”
      Kafinma ya rufe baki ta haye saman kujera tana hawaye. Murmushi ya ɗanyi ganin yanda ta kwanta da juya masa baya. Bai sake yin maganaba ya hau cin abincinsa yana yabama ƙoƙarin ta, dan shikam yanzu ya sallama mata akan iya girki kuma.
        Juye-juye Aymah ta dingayi a kujerar tana ƙunƙunin, sam kwanciyar batai mata daɗi ba, ita tafi son ƙasan saboda sanyin tiles. Yoohan dai na kallonta amma baice komaiba. Sai da ya kammala cin abincinsa hankali kwance sannan ya miƙe. Dan yama tuna kaya na waje. Zuwa yay ya shigo da su duka. Duk da Nu’aymah na jinsa bata juyo ta kallesaba. Cike take da haushin an hanata kwanciya a ƙasa. Babban akwatin kayanta da yazo da shi ya kai ciki, ghana must go ɗin kuwa ya barta anan falon dan baisan mine a ciki ba. Amma yanda yakeji ƙamshi-ƙamshin abubuwa yasan dai ba kaya bane. sannan akwai nauyi ma.
     Cak ya ɗauki Aymah daga kujerar ya nufi bedroom da ita. Ƙin motsawa tai, sai ma fuska data kumbure na fushi. Shi dai baice komaiba ya kwantar da ita a gado yana sumbatar goshinta. Daga haka ya cire kayansa ya wuce toilet yin wanka.
      Koda ya fito ya sameta a gadon bata sauka ba yaji daɗi. Dan baiyi zaton zata haƙura ba. Boxer kawai ya saka ya haye gadon, yanason yaɗan huta daga uwar gajiyar daya kwaso a sati biyun nan.. Sai yanzu ne ya fahinci ashe barci ƴar rigimar tasa tayi, yay murmushi mai ƙayatarwa da sumbatar laɓɓanta da idanu. ‘My Trouble maker an kusa zama mah-mah’ yay maganar yana ɗaga rigarta da ƙara faɗaɗa murmushinsa. Sunkuyawa yay ya sumbaci cikin da babu alamar akwai wata hallita a ciki. Sannan ya fara magana tamkar jinsa ya keyi, “Little boss how are you?. ALLAH ya kareki. ya fiddoki duniya lafiya, yasa kizam mahaddaciyar Al-qur’ani kaman Mie-mien ki. Ki kumayo kamanninta”. ya ƙarasa faɗa da ɗaga kai yana kallon fuskar Aymah dake barci batasan yanayi ba. Kwanciyarsa ya gyara da rungumeta. Kamar kuwa jira take sai ta sake lafewa dan sanyin jikinsa.
        Barci sukasha sosai. Sai dai Alhmdllh lokacin da suka tashi zazzaɓin Aymah ya sauka. Tare sukayi wanka bayan Yoohan ya mata gwajin fitsarin da batasan na minene ba. Tsabar wauta kuma bata tsaya tambayarsaba. Ta zata dai ko complain ɗin maganar rashin ganin jinin da sukayi da Umm ne ta sanar masa tunda shi Doctor ne. (Umm ba irinki bace madam😬).
     Ta rigashi fitowa. Dan sai da ya jira result sannan ya fito. Duk da ya jima da zargin ɗan tayinsa hakan bai hanashi farin cikiba. Ya ɗagata yanata juyi da ita. Tun tana tambayarsa lafiya harta koma tuntsura dariya kamar yanda yakeyi. Da ƙyar ta samu ya sauketa a godo suna faman hakki.
     Yasha murnarsa batare da Aymah tasan dalilinta ba. Dan ya ƙi sanar mata. Acewarsa ba yanzunba. Duk da taso tajin saita share kawai. Musamman da ganin ɗinkinan daya yo mata cike da akwati. Lesss, shadda, atamfa. Dan a cewarsa yana son ganinta a kayan hausawa sosai. Tayi mamakin ganin ɗinkin dai-dai jikinta kuma. Koda ta tambayesa yaya akai yasan seize ɗinta haka? Sai cewa yayi abun sirri ne. Ta fahimci yau jan rai yake mata akan magana. Nanma sai ta share ta shiga jera masa godiya da addu’oi.
      Ya ce shifa tabar masa godiya dan akwaima lefenta a kansa wanda baiyiba. Aymah dake dariya tace, “Ai gashi anan kayi my boo”.
     Hancinta ya lakace da faɗin, “No. Wancan special ne hausa girl. taso muje kiga saƙon Umm”.
       Tunda Aymah taga duk abinda tacema Umm an haɗo mata shi saita haukace da murna har Yoohan na mata dariya. Ta tasa fara gaba ta hau ci harta bashi tausayi. Dan yayi-yayi taci abinci taƙi, tace sai dai suje shagon shan coffee. Haka dole bayan ta gama cin farar da shan su alawar madara ya ɗauketa sukaje shan coffee ɗin. Tako shawosa bana wasaba harda guzirin na anjima. Shi dai gaba ɗaya sai take bashi tausayi, dan yasan da bata shan coffee.
       Haka su Nu’aymah suka cigaba da kasancewa suna rainon ɗan tayin cikinsu ita da mijinta abin sonta. Duk da yaƙi faɗa mata gaskiyar zancen cikin, a yanzu bata da abinci sai kayan da Umm ta aiko mata da su. Randa tayi tuwon dawa miyar kuka ta tsare Yoohan wai sai yaci. Dan itama ai taci abincin yarensa lokacin da aka kaita gidansu. Shiru kawai yayi yana kallonta idanu na farfar dan shikam dai harga ALLAH miyar kukar har saka masa tsigar jiki tashi take. Garama tuwon yana masa kallon amalan yoroba. Dan yana ɗanci a dalilin joseph data zama abincin yarensane. Ganin yanda yakeyine ya saka Aymah yin fushi. Marairaice mata yayi akan tayi haƙuri shi wlhy bai iya ci ba. Batama nuna taji miya faɗa ba.
     Ganin da gaske fa fushin ta ɗauka ya tilasta masa daurewa ya rintse ido ya matsa kusa da ita. Muryarsa har sarƙewa take wajen faɗin, “To kawo zanci Sweet girl. Shiru ta kuma masa tana cin abinta cike dajin daɗi harda lumshe ido, gashi ya sha yajin daddawa da man shanu kuwa sai ƙamshi yake. Sake marairaice mata yayi cike da lallashi.
      “Nace zanci ai ko. Tunda Unborn ɗina yanaci nima a bani zanci, yi haƙuri”.
       “Sai dai na baka da hannuna, dan karma kaita zubashi a riga ban saniba daga baya kaje ka zubar”.
    Ta bashi dariya, amma sai ya gimtse dan ya kula itafa da iya gaskiyarta take maganarta. Yace, “To na yarda”.
      Laumar farko dai Yoohan sai da ya riƙe numfashin sa sannan ya korata da ruwa batare da ya tauna ba. Lauma ta biyuma haka. Ana uku ƴar rigimarsa ta tubure bata yarda ba. Yoohan dai kam yaga takansa. dan rigimar Nu’aymah dabance a rayuwa. Dole-dole kuwa sai da ya tauna lauma ta ukun nan. Daga haka yace. Dan ALLAH tayi haƙuri ta barsa haka tunda koya yakeyi. Dariyar mugunta taita masa kuwa.
       Tun daga ranar daya fahimci zatayi tuwo sai ya gudu. Idan kuma ya fita asibiti sai ya bigi cikinta yaji mitaci ko zataci. da yaji batun tuwo sai yaki dawowa da wuri. Tun Aymah bata fahimtaba harta ganosa. Aiko saita daina sanar masa idan zatayi. Haka ta dinga ritsashi akan cin tuwon nan dole. Tun yana gudu bayaso har ya fara masa daɗi. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ya iya ci kuwa. Shima kuma komawar da yay Nigeria sau kusan uku duk xuwan da zai dawo sai yazo da wani abinda yasan na yaransune. Sai dai cikin ikon ALLAH kuma ita Aymah ciki ya sakata ci take hankali kwance. Dan yanzu kuma komai ci take anbar coffee. kayan wajen Umm ma duk zuwa sai yazo mata dasu.
      Watan su Aymah ɗaya da sati biyu a U.S Juliet ɗin Omar ta haihu mace mai kama da ita. Su Aymah ansha murna. Sai taji itama tanason ta haihu. Tako dage harda addu’a a cikin salla (😂bar wahal da kanki baby Aymah).
       Shi Yoohan baisan tana addu’ar ba shiyyasa bai sanar mataba. Dan a lokacinma baya ƙasar shi. Sai da ya dawone yaga baby. Omar ɗinma yana 9ja bayan haihuwar da kwana ɗaya yazo. Dan dama yaso Juliet ɗin taje Nigeria ta haihu taƙi. Yarinya dai taci suna biyu. Aysha & Lisa, Dan shi dai Omar duk abinda ya dace uba musulmi yayi akan ƴaƴansa shi yayi akan baby Aysha. Itako Juliet da yake dama bawani bidi’oin suna sukeba suna kawai ta sakama yarinyarta bayan wanda Omar ɗin ya saka mata. Saima yazam itama yanda Nu’aymah ke kiran sunan Aysha ɗin yana mata daɗi. Sai gashi tafi kiran yarinyar da Ayisha ɗin. Saboda daɗin da Omar yaji har ƙyauta yayma Nu’aymah da godiya. Tare da roƙonta dan ALLAH taita jan Juliet ɗin a jiki ko itama za’a dace ta gane gsky. Aymah ta amsa masa. duk da tasan hakan abune mai wahala ga baturen ba’amuruke irin Juliet. To amma komai ai na ALLAH ne.
_________________★
        *_KANO NIGERIA_*
Anan kano ta dabo kam Umm najin daɗin zama da Afrah data ta fara aiwatar da aikinta cike da ƙwarewa da nutsuwa. Gaba ɗaya ta ɗauke musu kewar Aymah. Koda yaushe Muhammad inhar ba makaranta ya wuce ba yana nane da ita. Itama tana matuƙar son yaron, dan yana ɗauke mata kewar ƴan ƙannenta.
      Haka ma tana matuƙar jin daɗin zama da baba malam da Umm. Dan mutanene masu dattako matuƙa. Ita da hajjo kam ai ba’a magana. Daka gansu tamkar jika da kaka. Kai gaba ɗayama al’ummar gidan Afrah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da kowa. Dan malam ƙarami harya ƙyasa. Ita kuma taƙi sanar masa tanada mijin aurenta a hannu. Dan gab ma ake da saka musu ranar aure tunda iyaye duk sun shaida tuni.
       A cikin dabarun da ALLAH yay mata a sashe su Nu’aymah ta manna cctv ɗin nan mai kama da stones. Hakama sashen hajjo da duk wasu gurare na cikin gidan batare da kowa ya farga da itaba. Bata da wata ƙawa mai shekarunta a gidan, dan haka taita jan yaran gidan jikinta sosai. Dan su Adawiya ma har yanzu suna Abuja. Admission ma za’a nemar musu su fara karatu tunda na Adawiya yasha kashi. Su baba malam sunso ta koma saudia ɗin ta cigaba hajjo ta hana hakan. Acewarta su jira dai suga iya gudun ruwan Abdallah ɗin.
         A cikin kwanaki goma da Afrah tayi a gidan ta kammala aikinta na manna camaras a duk inda ya dace. Sosai Jay yaji daɗin ƙwazon ƴar tasa. Hakama Bily.
        Sai kuma ta koma bama Dawood da little, Yoohan, Omar bayanai akan duk motsin ƴan gidan. Da wanna suka fara aywatar da aikinsu batareda jama’ar gidan sunsan sirrin ba. Hatta da Nu’aymah batasan hidimar da akeyiba. Dan koda Yoohan ya koma U.S bai sanar mataba. Takan dai gansa yayi serious a lap-top duk dare. kuma baya zama latse-latsen sai tayi barci. Inko har yazam ta farka to yabar aikin kenan. Dan duk dabarar da zaiyi ya ajiye abinda yake ya sani.
        A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har aka shiga watan azumin Ramadan. Wanda ya kasance na farko ga Yoohan da Omar. Sosai Aymah ta yabama ƙoƙarin Yoohan randa aka kai azumin farko. Dan ko irin nuna yau ya fara ɗin nan bai nunaba. Itacema sai da ta karya nata saboda jiri data dinga gani, daga ƙarshe kuma taita amai.
       Omar U.S ya koma domin yin azumi. Hakan yasa kullum anan wajen Nu’aymah yake zuwa shan ruwa. Wani lokacin ma harda Juliet suke zuwa da Baby Ayisha.
       Azumi nada kwanaki goma sha biyu hutun Afrah ya ƙare. Ta tattara ta koma Abuja cike da kewar su Umm. Dan ita dai taji masifar daɗin zama da waɗanan bayin ALLAH musamman cikin azumin nan. Su kansu duk sai da sukaji babu daɗi akan komawar tata. Sai dai babu yanda suka iya tunda zata koma kan aikintane.
        An kammala azumin watan Ramadhan lafiya. Ansha kuma bikin salla a ƙasashen musulmai. Yayinda su dai su Aymah sai ɗan yawo sukai anan U.S, da ɗanyin nasu bikin sallar anan cikin gida.
     Tsakanin Yoohan dasu papa har yanzu basu taɓa masa magana akan dukan Gebrail da yayiba. Dan komawar da yayi 9ja can gidan ma ya sauka abinsa. Sun kuma tarbesa kamar yanda suka saba. Ya iske su momy Destiny sun koma. Hakama maman Madam Chioma. Mama debora kawai ya iske da sauran ƙannensa sai guards ɗin gidan su Solomon daya koma gadin nadam Chioma yanzun. Gebrail kam tunda yaji Yoohan ɗin yazo gidan ya gudu. Har yabar ƙasar kuwa basu haɗuba. Daya sake komawama yay wajen  kwana goma shima wasan ɓuya suka dingayi da Gebrail ɗin.
        Wannan shiru da sukai ya bama Yoohan mamaki matuƙa. Badan dukan da yayama Gebrail ba. Sai dai maganar Solomon da baiji sun sake tayar masaba. Sai dai kuma shima baiyi magana ba ya bar Solomon ɗin cigaba da kasancewa da shi da sauran guards ɗinsa duk sanda ya shigo Nigeria. Duk inda ya shiga suna tare anan kam.
_____________________
           A kwana a tashi babu wahala sai ga cikin Nu’aymah ya shiga watanni shidda. Tun cikin azumi kuwa ta fahimci ciki gareta. Murna taitayi zasu samu baby suma. saɓanin yanda Yoohan yay tunanin zata tayar da hankalinta. Aiki shima yaji daɗin yanda ta nuna murnarta akan Unborn ɗin nasu. Wata ƙaunarta mai girma na sake faɗaɗa masa a rai.
        Ganin laulayin ya rage mata a lokacin sai kawai ya shiga ƙoƙarin nema mata admission. Wannan abu ya saka Aymah murna harda kuka. Dan tanason karatu sosai a rayuwarta.  Addu’a ta dage ta dingayi babu dare babu rana akkan samun gurbin karatun nan. Su Umm ma sunsha addaba akan su tayata da addu’ar. Har Muhammad tasa ya faɗa a islamiyya wajen ƴan ajinta su mata addu’a.
      To Addu’a dama takobin muminine ai. Balle gashi result ɗin Ayman da Yoohan ya amso a gida wani zuwa da yayi dama yayi ƙyau masha ALLAH. Sai gashi kuwa an dace. Ranar kowa yasan Aymah ta samu cikar burinta. Yoohan kam ai yafi kowa shan kallo dacin dariya a wannan rana, sannan kuma yasha tukuyci mai tsoka da ba’a bama yaro mai ƙiwa.
      Da taimakon Juliet yay mata komai daya dace, dan itama tanayin wani course ma a cikin makarantar yanzu haka. Sai dai a online take ɗaukar lecture. Da wannan damar Yoohan ma yay amfani akan Aymah. Zata dinga ɗaukar lectures ta online. Idan kuma taso shiga school bai hanata ba bayan ta haihu. Yayi hakane saboda yanayin jikinta.
      To da yake itama yanzu lallaɓa cikin take sai ta amince (wa yaga ba sabanba su Aymah za’ayi ƴaƴa😂).
        Umm, baba malam, hajjo ne kaɗai sukasan da zaman cikin Nu’aymah a kaf jama’ar gidansu. Dan ko Addah Umm bata faɗamawa ba sam. Tabar abinta a zuciya wai randa Nu’aymah tazo kowa ya gani. To kuma anyi sa’a duk wautar Aymah da surutu ita bamai irin sakin zance ɗin nan bace ako ina. Dan ko su Umm ɗin ai ba fitowa fili tai tace musu tanada ciki ba. Sune suka fahimta ita da hajjo. Baba malam ma a wajensu ya sani.
        Cikin ya mata ƙyau sosai a jiki, sai dai yasata ta ƙara ƙiba, kumatun sun fito masha ALLAH. Idan Yoohan najin neman magana yakan tasata gaba yayta dariya. Ita kuma taita hawaye dan yanzun dai kam bakin tsiwarnan duk ya mutu. ta kanta takeyi duk tazama wata shiru-shiru.
  ★★★★★
      Akwai aikin da Yoohan zaizo yi Ƙasar ghana, daga nan kuma zai shigo Nigeria akan case ɗin gidan su Aymah. Dan zuwa yanzu sun tattara abubuwa da yawa ta dalilin Afrah. Sai bayanan sirrin da jay ya tattara ta hanyar camaras ɗin nan wanda shi da bily kawai suka san dasu. Amma suma ɗin basu duba komai ba a yanzu, dan sunbar komai ne ya tattaru, So suna son fara buɗe abubuwa a bayyane insha ALLAH a hankali. Sun san kuwa a wata uku kenan da zaman camaras ɗin a gidan sun naɗi abubuwa iri-iri, musamman daya kasance ansha shagalin bikin ƙaramar salla da babba, duk kuma ahalin gidan sunzo, idan ka cire Abdallah da yay hijira.
      Shirinsu na farko dai yanzu shine fara kama Rabi. Daga haka sauran abubuwa zasu cigaba da tafiya a buɗe. Nu’aymah taso biyo Yoohan a wannan karon. Sai dai kuma ya lallaɓata akan ta bari sai hutun ƙarshen shekara idan ALLAH ya kaimu. Tunda baifi saura wata ɗaya da sati biyu ba. Batai masa musu ba, dan yanzu duk ta ƙara yin laushi, danma wahalar cikin ta mata sauƙi sosai zuwa yanzu Alhmdllh. Gashi kuma dama cikin fari. Ga kuma karatunta da ke mata matuƙar daɗi. Dan harya kaita da mantawa da wasu su madam Chioma. Lamarin papa ne dai kam sun tattauna da Omar sosai a wani zuwa da yayi U.S ɗin. Annan take faɗa masa gaskiyar lamari game da hoton data ɗakko a ɗakin papa ɗin, harma da waɗanda ta gani. Abin shima ya bashi mamaki sosai. Nan shima yake sanar mata abinda ya taɓa faruwa tsakaninsu da Jay kwanaki. Itama sai abin ya tsaya mata a rai. Har taji sha’awar son samun kusanci da zuri’ar Jay ɗin. A take Omar ya bata Number Afrah. Dama Afra ɗin ita tanada ta Aymah, kirantane dai bata taɓa yi ba. Dan sanda tana a gidansu sai dai su gaisa a wayar  Umm ne. Tun daga sannan suke ɗan kiran juna a hankali, suna kumayin chart lokaci-lokaci kasancewar duk sunyi busy.
     To yanzu dai sun ajiye magana akan duk sanda taje 9ja zata bashi hoton ya gani, daga nan sai su san tudun dafawa akan wannan al’amari. Daga haka suka ajiye batun.
       Sai dai kuma abinda su Aymah basu saniba ita da Omar shine tun randa Jay yaga Yoohan bai hutar da kansa ba a bincike dabin diddigin papa. A hankali duk wani motsin papa ya kasance akan idon Jay batare da shi yasan hakan na faruwaba. Dan ya rigada yayi imani da cewar ya toshe duk wata hanya ta leƙen asirinsa daga wasu mutane koda jami’an tsarone. Sai gashi shi Jay yama kansa hanyar da yake kallon papan tsirara.
       Dirar safe Yoohan yayma 9ja wannan karon. ya kuma sauka a Lagos ne. Sai da ya kwana uku sannan ya ƙaraso Abuja. Kamar ko yaushe ahalin nasa sunyi murna da zuwan nasa. Musamman ma madam Chioma da duk zuwa saita banka masa kayan tsibbunta a abinci yaci. Sai dai duk da bataga wani canjiba daga garesa tana ɗauka aikinta na tafiya dai-dai. Musamman da bata taɓa jin ya zauna yimata zancen Nu’aymah ba.
       Tun isowarsa gidan Gebrail ya gudu kamar yanda yakeyi yanzun. Tun dukan da Yoohan yay masa bai sake yarda sun haɗu a inuwa ɗaya ba. da zarar yaji labarin zuwansa yake barin gidan, bakuma zai sake shigowaba sai Yoohan ya koma kokuma yaje wani jahan aiki. Duk da Yoohan na lure da Gebrail ɗin bai taɓa nuna yasan yanayi ba. Gaba ɗaya yi yake tamkar ya manta da wani halitta Gebrail a cikin ƙannensa.
      Blessing da su Favour yasa suka gyara masa sashen nasa wannan karonma. Bayan ya watsa ruwa yaɗan miƙe a gado yanason ya huta. Sai da ya fara kiran Aymah suka ɗan taɓa hira sannan ya kwanta. A ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awan gaba da shi.
          Madam Chioma da tun shigowar Yoohan gidan yau ta kasa zaune ta kasa tsaye ta fito wankan maganin da boka Bangaruta ya bata a gurguje. Zama tai gaban mirror ta shiga tsara kwalliya kai kace fita zatayi. Sai da ta tsuke cikin wando da riga da sukai mata matuƙar ƙyau sannan ta feshe jikinta da kalolin turarruka masu tsada da ƙamshi. Gashin Attachment ɗin nan sai uban walƙiya yake da ɗaukar ido kasancewar sa mai uban tsada. Cike da takun gayu da ƙasaita ta fito daga sashenta dan papa baya nan yayi tafiya yau kwana biyu. Mama debora dasu Victoria kuwa tasa sunbar gidan a cikin shirinta. Ta aika Blessing kuma kasuwa. Amma abinda bata saniba Blessing ɗin batakai da fitaba saboda toilet daya kamata. Kanta tsaye sashen Yoohan ta nufa, hakan yayi dai-dai da hawowar Miracle sama hannunta ɗauke da five alive da kofi. Waya takeyi da wata ƙawarta tana bata labarin zuwan Yoohan. Saurin ɓoyewa Mira tayi dan kar madam Chioma ta ganta, tare da jan wani shegen wawan tsaki dayin kamar zatai jifa da kwalin lemon. Sai kuma ta fasa saboda uban kuɗin data kashe wajen yima lemon haɗin magunguna saboda Yoohan. Itama kanta cikin gayun take na kece raini. da alama kuma sashen Yoohan ɗin ta nufa. Sai dai gashi Maman Yoohan ta ruguza lamarin. Ranta cike da ƙuna taje ta zauna a kan wasu kujeru biyu dake a upstairs ɗin tana huci da bama ƙawar tata labarin abinda Momyn Yoohan ɗin tai mata. Zugata ƙawar tata take famanyi daga can akan ya kamata Miracle tazo suyi duk yanda zasuyi wajan raba Yoohan da uwar tasa.
         A ɓangaren madam Chioma kam ta shiga da dukanin gadaranta sashen ne. Key ta sakama ƙofar falon sannan ta nufi ɗakin Yoohan kai tsaye. Baisa a ransa kowa zai shigoba, musamman da yasan yanzu Momy ta bar masa ɗabi’ar banza na shigo masa sashema gaba ɗaya. Dan duk zuwannan da yakeyi bata shigowa, sai dai idan shine yaje sashenta gaisheta kosu haɗu a falon papa. Shiyyasa yake kwance abinsa daga shi sai boxer yana barci hankalinsa kwance. Ga iskar ac na shiga da ratsa masa ɓargo.
       Nanma maida ƙofar tai ta rufe harda saka key. Kafin ta ƙarasa gaban gadon jikinta har tsuma yake saboda ganin a yanda Yoohan ke kwance. Duk da ma yayi rubda ciki ne. A hankali ta zauna a bakin gadon saitin kansa. Ta kai hannu kan sajensa da ke bala’in burgeta. Cike da ƙwarewa a bariki ta kwanto jikinsa tana sauke nannauyan numfashi, sai kuma ta shiga yin sama da hannun nata ta tura cikin sumarsa. Dan tasan tun yana yaro yanason a dinga masa wasa cikin kai. Yanda take da hannun nata a cikin sumarsa ya sakashi sauke ajiyar zuciya a cikin barci. GGashidama mafarkin matarsa yake. Sai abinda madam Chioma ke masa yay tasiri a garesa.
        A hankali yay juyi gaba ɗayansa ya koma ringin gine. Kansa kuma ya ɗora akan cinyarta ɗaya dake a gadon. Wani irin daɗine ya kama Madam Chioma dan duk zatonta aikintane yay tasiri. Ranƙwafowa tayi da fuskarta daf da tashi tana wani lasar baki tamkar mayya. Yayinda hannunta ɗaya ke yawo a jikinsa. Tana gab da kai laɓɓanta kan nasa ALLAH ya bashi ikon farkawa a dalilin jin ƙamshi saɓanin na Aymahr sa. A wani irin matsanancin tashin hankali ya angizata daga ranƙwafomasa da tayi, danshi da farkoma yayi zaton Miracle ce…………✍
 *_Wayyo tazo kwartanci😱🏃🏃🏃_*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
    Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
  09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 70
…………Sai dai kuma ɗagowar da zaiyi cikin matsanancin fushi sai idonsa akan Momynsa daya yasar a ƙasa. A matuƙar razane yace, “What!!. Momy! Innalillahi wa’innalillahirraji’un”. Cikin karkarwa jiki ya shiga bin ɗakin da kallo, tabbas daga shi sai ita ne, hakan na nufin ba Mira ba. Ƙirjinsa ya sake bugawa da ƙarfi. Yay azamar jawo rigarsa dake gefe danya saka Madam Chioma da ALLAH yaba damar tashi tai saurin riƙe masa hannu. Dan ita haukanta gaba ɗaya bai nuna mata maganinta baya aikiba. Faɗa masa tayi ajiki tana faɗin, “Haba my boy ya kake abu kamar wani…….”
      Ai kafinma ta ƙarasa ya sake hankaɗata da rawar jiki. “Momy kina lafiya kuwa? Ninefa Yoohan?! Kodai kinsha barasa ne?!”.
       Duk da mamakin yanda yakeyi ya fara sata dawowa hayyacinta, ga zafin maguzar daya sake mata hakan bai hanata sake nufosa ba. Hankalin Yoohan ya sake kololuwar tashi, dan shi yafi tunanin Maman tasa bata a hayyacinta ne. Ta sake riƙe rigar daya ke ƙoƙarin sake kai hannu ya ɗauka tana wani narkewa hawaye na zirara mata. “My boy kaine mafarkina. Kai ne farin cikina. Tunda ka kai shekarun girma ka ɗauke hankalina ga kowanne namiji a duniya. Hatta da papanku baya birgeni gaba ɗaya duk da auren soyayya mukayi. Please masoyina kazo na baka zumar da wata a duniya bata taɓa baka itaba, na maka alƙawari……..”
      Duk yanda Yoohan yaso jurewa yama mahaifiyar tasa uziri ya kasa, dan haka ya fisge hanunsa data riƙe wani matsanancin tsoro na sake kamashi. Da sauri ya nufi hanyar ƙofa danya kuɓuta. Sai dai kuma ya sameta gam alamar ta kulle. Sunayen ALLAH ya shiga kira babu ƙaƙƙautawa, yay azamar kaucewa ganin ta sake nufoshi ido rufe. Dan har ta cire rigar jikinta tana ƙoƙarin cire wandon ma.
     Wata azababbiyar ƙara da hatta Miracle da Blessing dake ƙasa a laɓe sai da suka jiyosa ya daka mata.
        “Momy!!!! Are you mad?!!” Ya faɗa yana hankaɗata da iya ƙarfinsa da matsanancin fushi dan gaba ɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwa a tashi. Sai ko gata a ƙasa wanwar. Wata wahalalliyar ƙara ta saki saboda faɗawa datai akan hannun damarta.
      Ya cigaba da magana cikin fushi na ficewar hayyaci. “Wane irin ruɗaɗɗen al’amarine haka momy? Momy na tabbatar wlhy baƙya cikin hankalinki. Ninefa ɗanki Yoohan. Mikike shirin aikatawa haka?!!…….”
       “Cikar burina John. Idan har bakai tarayya dani ba zan iya halaka Yoohan. Dan ALLAH ka daina ɗaga murya kazo gareni. na maka alƙawarin a yau duk ƙishirwarka ta shekara da shekaru sai na gusar maka da ita, nima ka gusarmin da taw……”
       Da sauri ya tura yatsunsa cikin kunneta alamar baya buƙatar jin kalamanta. Sai da ya fahimci tayi shiru sannan ya nufeta. Da wani irin zafin nama ya kai hannu ya fisge key ɗin ɗakin daya hanga a yatsan hannunta. Ƙara ta saki dan taji zafi. Shiko ko saurarenta baiyina ya nufi ƙofa ya buɗe ya fice. Rasa inda zai dosa yayi a sashen nasa. dan ko ina a kulle yake. Cikin azama ya nufi ƙofar falon ya buɗe dan tabar key ɗin a jiki. Yana buɗewa tana fitowa daga ɗakinsa da jan jiki tana kuka da roƙonsa karya tafi.
         Da wani irin mugun sassarfa ya fice yana karasa saka t-shirt ɗin daya fito da ita a hannu. Wani irin mahaukacin jiri yakeji, kansa tamkar zai tarwatse saboda firgici. Da steps bibbiyu ya sauka a benen. Hakan yasa Miracle dake ɓoye fitowa ta biyosa da sauri tana ƙwala masa kira. Yana gab da ficewa ƙofar falon gaba ɗaya ta riƙo masa hannu. A wani irin juyowa tamkar wani walƙiya yayi sai jin saukar tagwayen maruka tayi a duk kumatunta. Kafin ta dawo hayyacinta ya hankaɗata ya fice abinsa duhu na mamaye masa cikin idanu. Hakan yasa sam ya daina ganin hanyar da yake ajiye ƙafa da ɗaukewa……..
★★★
           A hankali yake buɗe idanunsa ya saukesu akan Omar dake a kujera zaune. Nauyin da sukai masa ne ya sakashi sake maidasu ya lumshe a hankali.
       “Sannu Son”.
Muryar Dr Shikurah ta shiga kunnensa. Sake buɗe idon yayi a hankali yana mai juya kansa kaɗan ya kalleta itama. Babu zato sai kawai sukaga hawaye na gangaro masa ta gefen ido. Da ga ita har Omar dake jera masa sannu shima a tsorace suke kallonsa. Dr Shikurah ta shiga jera masa tambayar ko wani waje na masa ciwo ne?.
       Karan farko yay guntun murmushi mai ciwo da ƙunan zuciya. Dan ya tabbatar da ciwon da yakeji a zuciyarsa gara ace duk jikinsane ke masa wannan ciwon da raɗaɗi zaifi masa sauƙin ɗauka. Yunƙurawa yay a hankali zai tashi zauna. Sara masan da kansa yayine ya sakashi saurin dafewa yana faɗin, “Ya ALLAH!”.
        Da sauri Umar ya riƙosa. Yana faɗin, “Dude be careful mana”. Yayinda Dr Shikurah kuma ta gyara masa filo Omar ya jinginasa a jiki itama tana jera masa sannu tamkar zata fasa kuka. Dan har ikin ranta takejin zafin halin da yake ciki. Gyara masa drip ɗin da ake ƙara masa tayi, kafin ta dubi Omar da shima dai yana cikin tsantsar damuwa. “Omar kodai allurar za’a sake masa ne? Barcin kamar bai ishesa ba”.
     Kafin Omar yay magana Yoohan yay saurin girgiza kansa. “A’a Momy babu buƙatar haka. Bazan iya sake kwana a ƙasar nan ba, dan zuciyata zata iya bugawa…..”
       Cikin katsesa Umar yace, “Taya zakai maganar barin ƙasa kana a cikin wannan halin? kana son yin wasa da lafiyarka ne komi Yoohan?”.
      Kallon Umar ɗin yayi da idanunsa dake jajur yana wani murmushi mai ciwo, gazafafan hawaye na ziraro masa a saman kumatu. “Bazaka ganeba Omar, duk bayanin dazan maka bazaka fahimceni ba. Tafiyata ba itace wasa da lafiyata ba, zamana a ƙasarnan shine wasa da lafiya ta. A yanzu haka inajin tamkar na rufe ido naga bana numfashi saboda ruɗanin da ƙwaƙwalwata take a ciki. Umar ni Momy zata n……”
     Sai kuma ya fashe da kuka mai cin rai batare daya iya ƙarasawa ba. Jikinsa sai wani irin rawa na ɓacin rai yakeyi dan Yoohan akwai zuciya dama. Hankalin Dr Shikurah da Omar ya sake ƙololuwar tashi. Umar ya riƙo hannunsa yana lallashinsa. Amma sam hankalin Yoohan baya a jikinsa gaba ɗaya. Babu abinda ƙwalwarsa ke tariyo masa sai abinda ya faru shi da Momynsa tamkar a film. Gaba ɗaya ƙwalwar kansa da tunaninsa neman jirkicewa suke.
      Wani irin bahagon numfashi ya fara ja da ƙyar alamar motsawar Asthma ɗinsa. Hankalin Omar yakai matuƙa a tashi, dan yasan Yoohan nashan wahala akan Asthma ɗinsa. Takan daɗe bata tashi masa ba. Amma duk lokacin data motsa yana shan wahala sosai. Gashi shi koma yawo da inhaler bayi yakeba saboda yana jimawa bai yiba.
        Ganin abin babbane yasa Dr Shikurah tambayar Umar a ruɗe.
     Shina Umar ɗin a rikice yace, “Mom yanada Asthma, sai dai tana jimawa bata motsa masaba. Da alama yanzu kuwa itace”.
       “Hasbinallahu wani’imar wakil”. Dr Shikurah ta faɗa tana fita da hanzari.
       Babu jimawa sai gata ta dawo suka shiga bashi taimakon gaggawa ita da Omar. Basu ƙara samun nutsuwa ba sai da Yoohan ya koma barci mai nauyi.
     Cikin sauke tagwayen ajiyar zuciya Dr Shikurah tace, “Omar anya kuwa ba wani abune mai girma ya firgita ɗan uwanka ba?”. Duk da Umar yasan ainahin abinda ya faru. saboda Blessing ta sanar masa ta waya sai ya ɓoyema Dr Shikurahn. “A’a Mom, faɗowar Momynsa daga benen ne kawai ya firgitashi”.
        “ALLAH sarki, ai jikin nata itama da dauƙi, duk da bata farfaɗo ba har yanzun, amma Alhmdllh bataji wani mummunan ciwobama kamar yanda mukai hasashe”.
     “ALLAH ya basu lafiya”. Umar ya faɗa a taƙaice. Daga haka Dr Shikurah ta fita daga ɗakin.
          Fitar Dr Shikurah ɗakin tayi dai-dai da shigowar Papa da Uncle Joshua cikin asibitin. Dan isowarsa kenan ƙasar ya iske gidansa a harmutse. bayan ya tambayi dalili aka sanar masa Yoohan ne ya yanke jiki ya faɗi batare da ansan dalili ba. Wajen biyosa kuma madam Chioma ta faɗo daga bene. (Dan su iya abinda suka gani kenan. Miracle da Blessing ne kawai sukasan ainahin abinda ya faru. Su kuma babu wanda yace komai. ita dai Blessing tsoron rasa aikinta takeyi. Itako Miracle bamusan dalilinta na ɓoyewarba).
     Sun sanar masa Richard yazo gidan a daidai faruwar al’amarin, shine ya tafi da su asibiti su duka. Wannan shine dalilin zuwan papa a sibitin da hanzari.
        Kasancewar Yoohan sannan likita duk ma’aikatan sun sanshi. papa na ambatar sunansa da kuma tabbatar musu shi din mahaifinsane ko sai gashi an rakosa har office ɗin Dr Shikurah. Itace ta fara kaisu ɗakin da Madam Chioma ke kwance a sume har yanzun, sunata dai tsammanin farfaɗowarta. Duk an mata dressing ciwukan da taji, tare da gyara mata tsagewar ƙashi data samu a hannunta.
        Papa harda su hawaye yayi na tausayin matar tasa. Dan yasan yanda take tsananin son ɗan nasu. Suko su Dr Shikurah sai faman masa sorry sukeyi. Daga haka suka fito zuwa ɗakin da Yoohan ke kwance shima. Anan ma hankalin papa ya tashi da ganin halin da yaronsa yake a ciki, dan tashin Asthma ɗinsa sunsan bata musu daɗi.
*_WASHE GARI_*
         Washe gari suka tashi da farkawar madam Chioma. Sai dai tanata faman raki akan hannunta. Dan kuka ta dingayi kashirɓan kamar ƴar yaye. Papa kuwa dake nane da ita yana tayata da tattali.
      Yoohan kam Alhmdllh tun a daren ya farka. Ya kuma takurama Omar sai ya nema masa ticket ɗin wucewa U.S. duk lallashin da Omar ya dinga masa sam yaƙi saurarensa. Ya dage akan shifa sai ya bari ƙasar. Kuma bayason papa ya sani. dan duk da ya farka duk shigowar da papa yazoyi dubashi sai ya nuna bai farka ɗinba. Badan Umar yaso ba dole yaje ya nema masa ticket, sai dai bana zuwa U.S bane direct. Amma duk da hakan Yoohan yace ya yarda. Sannan yaje gidan ya haɗoma Yoohan ɗin kayansa na buƙatar yau da kullum kamar su waya da sauransu.
     To kuwa a safiyar yau ƙarfe goma batai masa a asibitinba. Dole Omar ya fita da shi a ɓoye batare da ko Dr Shikurah ta sani ba. Shine ya kaisa airport ɗin ma. Yanaji yana gani Yoohan ya wuce ya barsa da damuwa.
      Asibitin ya dawo, inda ya tarar anata neman Yoohan. Shima kawai sai yayi pretending ɗin shiga cikin ƴan nema. Dan baisan wace amsa zaiba papa akan tafiyar Yoohan ɗinba. Bayan kuma shi kansa Yoohan ɗin ya masa magiya da roƙon bayason su papa susan ya wuce da saninsa.
             Jin Yoohan ya wucene yasake birkita madam Chioma, yanda ta tashi hankalin nata har mamaki ya bama Uncle Joshua shi dai, amma sai baiyi maganaba dan hakan ba huruminsa baneba. Daga ƙarshe ma allurar barci sukai mata saboda yanda take faman rubzar kukan ita dai a nemo mata yaronta. Shi kansa papan itace ta sake birkitasa. Dan yasan dai Yoohan bazai ɓataba. Abinda kawai ya tsaya masa a rai shine minene ya saka Yoohan ɗin tafiya bayan kuma baida lafiya?. Dama tun jiya yaketa tunanin akan faɗuwar da akace yayi babu gaira babu dalili tunda har waya shidai yayi da shi a ranar da safe, kuma baiji wata damuwa tattare da yaronsa ba a lokacin da shuke wayar. Dan shine ma yace karya faɗama Momyn nasu zai dawo a jiya yana son ya mata surprise ne. Har Yoohan ɗin na masa dariya akan hakanma. Sai kuma gashi ya dawo ya iske waɗanan rikitattun tashin hankali da gaba ɗaya ya rasa makamar riƙewa akan faruwarsu.
___________________
       Nu’aymah na gidan Juliet Omar ya kira akan taje gida ga Yoohan nan a hanya. Abin ya bata mamaki dan sunyi da shi sai nan da sati biyu ma zai koma. Haka dai tai shiri ta koma gidan nata ttareda Juliet da tai mata rakkiya danta tayata gyara waje. Duk da ma tasan baza’a samu datti sosai ba tunda duka yau kwananta biyar da barinsa.
     Babu dattin dai kam sosai. Amma sai da suka gyara komai tsaf. Juliet ta tayata sukai har girki saboda tausaya mata da takeyi na halin da take a ciki. Sai da suka gama komai tsaf sannan ta wuce tabar Aymah na wanka.
       Bata wani jimaba ta fito tai shiri cikin doguwar rigar atanfa mai faɗi data ɓoye cikinta. Wayarta ta ɗauka ta nufo falo dan yunwa takeji ta bala’i. Turus ta tsaya tana kallon Yoohan dake kwance a kujerar falon idanu a lumshe. koda wasa bataji motsin shigowarsa gidanba sam. Cigaba tai da takawa a hankali inda yake. Batare da tayi magana ba ta zauna a gefensa da kai hannunta ta janye nasa hannun daya dafe kai da shi.
      A hankali ya buɗe idanunsa dake jajur ya zuba mata su. Itama kallonsa take cikin ido sosai. Sai kawai yaji zuciyarsa ta ƙara raunana. A take hawaye suka cika idanunsa. Ɗayan hannunsa ya kai saman cikinta yana murmushin ƙarfin hali.
     Ita dai Aymah kallonsa take tamkar wata sokuwa, dan yanzu kam sai dai ta bama wani labarin mijinta badai ita a bataba. Cikin sanyin murya tace, “Baka da lafiya?”.
        Haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi yayi da ƙyar, sannan ya yunƙura ya tashi zaune yana cije baki daboda kansa dake masa ciwo har yanzun. Zama yay da ƙyau ya rungumota jikinsa, hannunsa nakan cikinta yana shafawa a hankali. Cike da raunin murya yace, “I miss you Sweet girl”.
       Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa kalar tambayar ɗazun. Murmushi ya sakeyi da sumbatar kanta. “Lafiya ta ƙalau baby, sai dai kewarki ce”. Duk da Aymah bata yardaba saita ƙyalesa kawai a hakan. Itama ta rungumesa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Duk da ciwo da ƙunar da yakeji zuciyarsa na masa bai hanashi bata haɗin kai ba. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ɗinma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.
       Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ƙoshi. Hankalin Nu’aymah ya sake tashi matuƙa saboda ta kasa gane kansa gaba ɗaya. da ƙyar dai ta samu yaci kaɗan ya sata ta ɗakko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.
      Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ɓoye mata ne kawai.
*_KANO NIGERIA_*
           A lokacin da madam Chioma ke can neman sa’a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ƙwamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa.
     Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yunƙuri aka fisgota ciki tare da daɗe mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ƙarshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ɗakin da bata saniba. Da matuƙar tashin hankali ta tashi tana ƴan waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa baƙon waje aka kawota……
        Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Murɗeɗen ƙatone da iya gani kasan ya damƙi namiji ma sai ya shinshino ƙamshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ɗakin dake tare da kujera ɗaya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, “An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki”. Ya ƙare maganar da juyawa ya fita abinsa.
     Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ƙoshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ƙila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta sha, dan ita kaɗai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan…
      Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sauƙi sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ɗaya a asibitin. Ranta dai na nan danƙare da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.
____________★
          Bayan isowar Umar kai tsaye office ɗin Dawood sukaje. Sai da sukai zaman jiran Bilkisu Adam Makaho, mata ga Oga Jay sannan, dan itace oga kwata-kwata akan case ɗin. Tana isowa kuwa suka amsa kira ta hanyar telephone.
       Sun sameta a office ɗinta. Bayan sun gaisheta ta basu iznin zama. Sam babu wasa tattare da ita, dan yanzu bayan miskilancinta girma ya ƙaru ga daraja. Babbar Officer ce da aikinta ke girgiza sansanin duk wani mai kunnen ƙashi.
    Batare data kallesu ba tace, “Dawood azomin da matar nan”.
     “Okay maa”. Dawood ya faɗa da sauri yana miƙewa. Kusan mintuna goma sai gashi ya dawo tare da Rabi dake wujiga-wujiga, dukta fita hayyacinta a kwanaki goma kacal. Kuma babu zagi babu duka. Zai gurfanar da ita a ƙasa Bily ta hanashi. Wata kujera dake can gefe ta bashi umarnin ya bama Rabi ta zauna. Shi dai Omar nata kallonsu ne da mamakin ganin yanda Rabi ta koma. Gashi kuma ko ƙwarzanen duka shi dai bai gani a jikinta ba. Itako bama ta gane Umar ba saboda a jigacen da take.
          Little bee ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izini. Tai salute ɗin mahaifiyar tata kuma ogarta a wajen aiki kafin ta ajiye takardun hannunta a tebir ɗin. Takardun Bily taja gabanta ta duba kafin ta ajiyesu gefe ta kalli Rabi.
        “Nasan dai zuwa yanzu kinsan a inda yake ba wajen wasan nanaye bane. Dan haka ya rage ruwanki nutsuwa ki bamu duk amsar tambayar da zamu miki, ko kimana ƙarya”.
      Muryar Rabi na rawa tace, “In ALLAH ya yarda bazanyi ba ranki ya daɗe”.
      “Wannan ya rage naki”.
Bily ta faɗa cikin halin ko in kula tana sake ɗaukar takardun da Little bee ta shigo da su. A gaban Rabi ta diresu dai -dai lokacin da fuskar Yoohan dake zaune a office alamar yana a asibiti ta bayyana a cikin lap-top ɗin da Omar ya ajiye inda Yoohan zaiga kowa dake office ɗin.
        “Wannan takardun bayanai na duk abinda ke cikin wayarki. Randa kika sayi layi, randa kika fara ɗorashi a waya. Sau nawa kina canja shi a wasu wayoyi. Mutanen da kika taɓa kira ko suka kiraki duk akwai bayanansu anan. Dan haka ki nutsu sosai”.
        “In ALLAH ya yarda ranki ya daɗe”.
       Kallon sashen da Dawood da Little bee suke Bily tayi, kafin ta kalli lap-top ɗin. Kai Yoohan ya risinar cike da girmamawa ya gaisheta. Itama ta amsa masa da kulawa kafin ta nuna masa Rabi.
     “Ina fatan kana ganinta da ƙyau?”.
“Yes maaa!”.
        Duk da Rabi ta kalli fuskar lap-top ɗin itama bata kawo komaiba, tadai ga kamar hoton mijin Nu’aymah, kafin tunaninta ya faɗaɗa Little bee ta katseta da faɗin, “Minene sunanki?”.
         Murya na rawa tace, “Rabi?”.
“Shekararki nawa kina aiki a gidan Sheikh Soorajidden Hashim Jibiya?”.
       “Goma sha takwas. Dan an kainine lokacin matarsa nada tsohon cikin dake wahal da ita dan na taimaketa”.
    “Kin taɓa aure?”.
             “Eh na taɓayi harda yarana biyu”.
  “Keda ke aure miya kaiki gidan aiki har tsahon wannan shekarun?”.
      “Ranki ya daɗe ai auren ya mutu ne a wancan lokacin. To domin neman na kaina saina samu aikatau ɗin dan nayi saboda iyayena duk sun rasu ni marainiyace”.
       “Ƙwaɗayin zama gidan masu kuɗi yasa baki sake tunanin sake ƙara aure ba kenan?”.
       Shiru tayi kanta a ƙasa ta kasa bada amsa. Shima Dawood da yay maganar sai ya shareta da ga haka ya sake jeho mata wata tambayar.
     “Waye ya kaiki gidan?”.
A take ta ruɗe jikin na rawa, sai in ina take ta kasa bada amsa. Hakan yasa Dawood daka matsa gigitacciyar tsawa. Fashewa Rabi tayi da kuka. “Dan ALLAH ku gafarce ni zan faɗa”.
     Babu wanda ya tanka mata. Sai bindiga da little bee ta ciro a gefen ƙugunta ta dire a gaban Rabi. Hakan yasa ta kuma diriricewa. Cikin hadiye kukanta tace,
       “Ranku ya daɗe ni bansan ainahin wadda tasa aka kaini gidan ba. amma naje ta hannun wata matace amma yanzu ALLAH yay mata rasuwa”.
       “Oho, idan na fahimci amsar nan taki kenan dama an kaiki gidan ne da wata manufa? Ba wadda kike a wajenta bace tasa aka kawoki gidan!!”.
     Yoohan yay magana a matuƙar zafafe. Maimaita mata Dawood yayi da hausa. Dan duk da Yoohan ya haɗa da kalmomin hausa a maganar Rabi bata fahimta da ƙyau ba. Amma shi Alhmdllh yana fahimtarta sosai tunda jin nasa yafi faɗi da baki.
       A take Rabi ta ƙara rikicewa, dan har ga ALLAH tazatafa hoton Yoohan ɗinne kawai a wajen. Suma dai su Bily yanda yay maganar duk sai da ya sakasu kallonsa. Tebir ɗin Little bee ta daka da hannu, da tsawa tace, “Ki basa amsar tambayarsa malama kin ɓata mana lokaci”.
       Jikin rabi na cigaba da rawa tace, “Ranka ya daɗe ba haka nake nufi ba. Ni dai kawai an kawonine na kula da mai ciki, daga haka babu wani dalili dana sani na rantse muku da girman wanda ya halicceni”.
      A karan farko taji saukar mari mai gigitarwa a fuskarta. Kafin ta dawo hayyacinta Dawood ya ƙara mata wani. Sannan kuma Bily dake zaune duk tana kallonsu ta hanata kuka. Dole Rabi ta haɗiye hawayenta sai ajiyar zuciya.
     Dawood yace, “Inhar zakiyi mana ƙarya to zakiyita amsar irin waɗanan marukan babu ƙaƙƙautawa. Wa kikema aiki a gidan?”.
     “Wlhy yallaɓai iya gaskiyata nake faɗa muku. Bani yima kowa aiki sai Hajiya Firdausi matar Sheikh Sooraj ɗin”.
           Sai a yanzu Umar yay magana. “Eh ansan dama ita kikema aiki a zahiri. a baɗini kuma akwai ogarki mai sakaki shiryamata sharri ita da tilon ƴarta. Bayan ƙyautatawar data dinga miki a rayuwarki na tsahon shekaru goma sha takwas”.
       Dawood ne ya sake fassara mata. Dan haka cikin rawar harshe da kuka mai cin rai tace, “Na rantse da ALLAH. wlhy tallahi ban taɓa cutar da Hajiya Firdausi da zuriyar ta ba. Ko Nu’aymah da muke yawan faɗa wani lokacin ina takalartane kawai wlhy saboda nasan bata barin saita kwana. Amma bada wata manufaba. Ko a mafarki bana fatan na cutar da waɗan nan bayin ALLAH ai balle a zahiri”.
       Cike da ɗaurewar kai suka shiga kallon juna. Amma duk da haka bayan Dawood ya gama sanarma Omar abinda ta faɗa sai Umar ɗin ya bada vr ɗin nan na kwanaki da sukaji tare da Nu’aymah. Aka kuma tabbatar mata a wayar wanda aka samu.
       “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ni Rabi. Wlhy wlhy kinji na rantse ni ban taɓa waya da mai aikin Nu’aymah ba. Hasalima sam ban santaba tunda randa akazo za’a wuce da ita abuja a sashen hajjo Umm taje ta sameta itama. Yanzu haka ko zaku kasheni bazan iya nuna fuskartaba balle harna samu Number ta nayi waya da ita akan Nu’aymah. To niko idan ta faɗamin halin da Aymah ke ciki gidan aurenta ribar mi zanci bayin ALLAH?”.
        Tsawa little bee ta daka mata. “K bama son rainin hankali. Idan kince bake bace waɗan nan lambobin dake akan wayarki harda ta Uwaliya ɗin na uwar waye? Wa kuma ya sakasu da har zaiyi zaman magana da su a wayarki batare da kin saniba?”.
       “Wlhy iya gaskiyata nake faɗa muku. Ni yanzu haka ko waya zanyi ma sai naba Muhammad ya dubamin lamba. Dan shine kemin sebi idan ko zansa lambar wani ɗan uwana. Idan kuma zanyi kira shima ke dubamin abinda ya samun dan banyi boko ba. Da Nu’aymah ko Adawiya kemin, to sai suyita jamin rai, shine na koma bama Muhammad ganin ya iya. Amma ni lambar ma ƴan gidan bata kowa gareniba wlhy”.
     Hannu Dawood ya ɗaga zai ƙwaɗa mata mari Bily ta dakatar da shi. Dan ita duk shirun datai musu nazarin komi takeyi. sannan kuma Jay ma duk yana saurarensu daga office ɗinsa ta hanyar na’ura. Shinema yay saurin cema Bily ɗin kar Dawood ya mareta yanzun ta hanyar abibda ke a kunnenta da su basu fahimta ba.
     Dakatawa kuwa Dawood yayi yana huci. Bily dake kallon Rabi cike da nazari tace, “To amma ranar da Nu’aymah tai bleeding ko zamu iya sanin miya faru? Dan bincikenmu ya nuna mana kece kika bata abu na ƙarshe tasha a gidan. Daga haka ta fara ciwon ciki sai jini kuma ya ɓalle”.
      Shiru Rabi tayi tana tunani dan tama manta. Sai zuwa can kuma tace, “Lallai kuwa ranki ya daɗe kamar anyi hakan. Ta sakani na dafa mata ruwan shayi baƙi”.
       “Kenan a ciki kika saka mata maganin zubda jini da aka ɗauka cikine ta zubar??”…………..✍
*_Tofa masu karatu man kai na fa zai fara malalewa a dalilin amsoshin Rabi, nama rasa mizan tunano kuma. amma bari mu bita muji wace amsa zata bada a gaba??😱🤧._*
ZAFAFA BIYAR 2021

About Godswill

Check Also

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End)

UWAR MIJINAH Page 71 to 80 (The End) “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi …

Advertisements