SARAN BOYE Page 41 to 50 » Naijagisthub

Advertisements

Home / News / SARAN BOYE Page 41 to 50

SARAN BOYE Page 41 to 50

SARAN BOYE Page 41 to 50

..Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta.

“Lafiya Darling?” papa ya faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
Rakata da idanu yay cike da so da ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.

A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
Ɗagowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure.…..”
“Aure!?” Monecca ta faɗa cikin tashin hankali.
“Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa”.
Cikin sauri Madam Monecca tace, “Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa hankali?”.
Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.

Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.

______________________________
*_SAUDIA_*

Advertisements

Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ƙunar zuciya kamar yanda Nu’aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ɗaya Nu’aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro niyya tun daga gida.
Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu’aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.

Yau ma kamar kullum Nu’aymah na ɗan yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu’aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
Kafe Nu’aymah da idanu Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu’aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da takaicinsa.
Fuskarsa a haɗe ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu’aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin, “Yah Ab minene haka wai?”.
“K kika cancanci wannan tambayar ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin, “K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu’aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
Cike da takaici Nu’aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu’aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?”.
Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu’aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har Nu’aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”. Nu’aymah ta faɗa a hasale.
“Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu’aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar Nu’aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu’aymah ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu’aymah ta faɗa tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
Duka Hajjo ta kaima Nu’aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu’aymahr

A falo kam Nu’aymah na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu’aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku……”
Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
“Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take”.
“Ya isa haka”. Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu’aymah, baisanma ita taji komaiba.
Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin zuri’ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu’aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.

Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu’aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu’aymahr ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
Bayan barin Nu’aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu’aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.

_________________________
*_NIGERIA_*

A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
Amma saboda ƙarfin hali da burinsa nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa

Kusan ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala’in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa alamar ban haƙuri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta. Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
“Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da “Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan”.
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan, kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”.
Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.

★★★★★

Airport driver ya kaisu. inda acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.

Ƙarfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya………….

[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali: No. 24

……………Baba malam daketa kaikawo na ƙoƙarin ganin komai ya kammala yanda yake buƙata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar baƙonsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ƙarfe biyun ran take a kan ƙafafunta tana hidima. Sauƙinta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta.
Omar ne biye da shi, dama yafi shaƙuwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai ada kam sunfi shaƙuwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ɗin yafi Abdallah zaman kano sai shaƙuwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar yarone mai tsananin ƙwazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son zaman Abuja ba shi.
Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya rage ɗin. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, “Umm Muhammad yaya kun kammala?”.
Ɗagowa Umm tai taɗan kalli mijin nata, sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, “Abban Nu’aymah wlhy nikam dai zakama sake rikitamu gaba ɗaya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa kai kayi wanka dan magrib ta gabato”.
Murmushi shimfiɗe a fuskarsa ya ƙaraso yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su haɗa. “Ke dai kawo na taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ɗakkosu fa”.
Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya ƙaraso wajen baba malam ɗin yana faɗin, “Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka ba. Dan nikam yau namafi kowa zumiɗin son ganin wannan baƙo mai daraja a wajenku Abba, dan naga gaba ɗaya hankalinku na kan son ganin an ƙyautata masa, yau kota abincin buɗa bakinmu bakwayi sai na baƙo”.
“Kace ido ka saka mana? Hakama malam ƙarami (baban yaron Addah) sai da ya gama ƙorafi kafin ya wuce airport ɗakkosu”. Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ƙarasa haɗa komai ita da baba malam ɗin. yayinda Omar da Addah kuma suke ɗorawa tray. Omar ne ya ƙarasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu  inda za’a sauke baƙon. Hakan kawai ya isa kasan an daratta baƙon sosai, dan duk baƙon da su Baba malam zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.

Advertisements

Sai da yaga an fita da komai sannan ya sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai dan Baba malam ɗinne ya basu dariya.
Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka shirya abincin, suka ƙara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air Fresheners masu ƙamshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a baƙin asamu mai Asthma ya cutu. Ta ɗan ɗaga labulen Windows ɗin kaɗan hayaƙin turaren ya ragu sosai. Cikin sa’a ma sai gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ɗinsa Umm nama Addah godiya.
Dan tasan badan itaba da aikin baiyi sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ƴan aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.

Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ɗin Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara’ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.

Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu kamar wasu jela ko suna ganin za’a cutama Yoohan ɗinne oho musu. Sai da sukaga ya zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai buƙata sannan sukai masa sallama suka fito, duk da basuji ya amsa musu da ƙyau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da buɗaɗɗen ra’ayinsa ya shiga masa zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ɗin nasu wani abin yaci a tsafesa.
Yana cikin shawara da zuciyarsa ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ɗinsu sai ga sallamar su Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan. Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama Momy text message ko za’a dace wayar na a hannunta ta gani.

Koda suka shigo Yoohan na’a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ƙasa ido. Abban Adawiya da suka taɓa haɗuwa a orphanage ranar da suka buge yaron nan sai ganin Yoohan ɗin ya sakashi matuƙar jin mamaki. Duk da ya jima a ransa yana zargi da hasashen kodai shine mai musu wannan ɗawainiyar. Rashin tabbas ɗin hasashen nasa yasa bai taɓa yin magana ba sai yanzu ya ɗan gwargwaɗa ma baba malam cikin harshen larabci.
Murmushi kawai baba malam ɗin yayi, cike da kulawa ya maida hankalinsa akan Yoohan da suka fahimci a takure yake da kasancewarsa a wajen. Basu damuba, dan sunyi gamo da waɗandama suka fisa taurin kai da aƙida amma cikin amincin UBANGIJI sun sami nasarar canjasu. To balle shi kuma dama suka fahimci zuciyarsa nada rangwame tunda har ya iya kasancewa maison ƙyautatawa marayu.
Duk da baba malam yaga saɓanin abinda yay tammani daga Yoohan hakan baisa ya canja komaiba daga ɗokantuwa da mutunta baƙon nasu. Hakam ɗan uwansa da ƴaƴansu basu nuna wani mamakinsu a fili ba ko ƙyanƙyamin su Yoohan ɗin, kowa ya shanye a ransa. Ba Yoohan kawai ba, dai-dai da guards ɗinsa an mutuntasu fiye da zatonsu, dan suma ca akai su zauna ayi buɗa bakin dasu. Duk da suna noƙewa saboda boss ɗinsu haka baba malam ya matsanta musu. Ganin Yoohan kuma bai tanka musu ba, yamayi kamar baisan mi akeyiba sai suka saki jiki aka kwashi gara da su, a ransu kuma suka koma zuba santi dajin kimar mutanen musamman yanda aka nuna musu suma mutanene masu daraja ba bautace kawai aikinsu ba.

Yoohan kansa da keta noƙewa da farko tuni baba malam ɗin ya tsaresa sai yaci, harda nuna masa idanfa baici da hannunsaba shi zai basa da kansa to, kuma ɗura zai masa. Karan farko a rayuwata da ni kaina mai ɗakko muku rahoto naga murmushi a fuskar Yoohan yau. Dan shi kansa a bazata ya saki lallausan murmushin ga baba malam ɗin.
Baba malam yace, ‘Masha ALLAH’ a ransa, duk da yau ya fara ganin Yoohan sai yaga murmushin yay bala’in masa ƙyau. Haka dai suka gudanar da buɗa baki cikin nishaɗi da farin ciki. Guards ɗin Yoohan dake ɗar-ɗar harda Solomon mai hasashen banza sai gasu sun kwashi gara suna washe baki dajin farin ciki a ransu.
Kiran sallar isha’i ya saka su baba malam ficewa massalaci akabar Yoohan da tawagarsa. Sai dai kuma bayan fitarsu babu jimawa shima sai ya miƙe da nufin ɗan yin tattaki ko cikinsa zai sauka. Shi kansa yasan ya jima a rayuwarsa baiyi irin wannan cin abincinba, ballema a ɗan tsakanin nan da yake cikin halin ha ula’i. Ta ƙaramar ƙofar da yaga su baba malam ɗin sunbi shima ya bi, kai tsaye ta kaisa ƙatuwar harabar massalacin kuwa.
Ko’ina ƙwanyar yake da haske tamkar rana. Ga mutane maza da mata harma da yara cike da massalacin harda mata. Yoohan yay tsaye jikin katanga yana kallonsu cike da nazari har aka tada salla. Ba massallacin kawai ba hatta anguwar kanta sai yaji ta ɗauki shiru gaba ɗaya, babu abinda kakeji sai sautin karatun salla da baba malam keyi. Lokacin da ya kammala karanta fatiha mamu suka amsa da “Amin!!!!” sai gaba ɗaya tsigar jikin Yoohan ta tashi, zuciyarsa tai wani bala’in tsargawa har saida ya rumtse idanunsa.
Baisan dalilin daya hanashi komawa ciki ba, haka ya cigaba da tsaiwa har sukai ruku’u. suka sake ɗagowa sukai sujida. Tsigar jikinsa sake tashi tayi a karo na biyu, dan yanda sukai sujidan gasu a sahu nagartacce dolene ko musulmin ya gani yaji ƙarin imani a ransa balle wanda bai taɓama yin sujudar ga UBANGIJI ba.
A hankali Yoohan ya ɗaga ƙafafunsa ya fara ja baya da ƙyar harya fice a harabar massalacin ya koma cikin gidan. Haka ya cigaba dajan jiki harya isa falon da aka saukesu da ƙyar. Tsitt guards ɗinsa daketa faman surutun santin abincin da sukaci sukayi ganin ya shigo kamar a birkice. Da sauri duk suka miƙe tsaye domin girmamawa. Solomon ya taimaka masa ya zauna.
Sai kuma duk hankalinsu ya tashi, amma yanda baiyi maganaba suma sai basuyiba sukai dai masa tsaye cike da tsoron kodai an cutar dasu ɗinne kamar yanda sukai hasashe tun farko?.

Har aka idar da sallar asham Yoohan bai dawo hankalinsa ba. Baba malam da ayau baije tafsir ba dama ya ɗauki alfarma suka sake shigowa. A yanda yaga Yoohan ɗinne ya saka hankalinsa tashi. Tambayar guards ɗin ya shigayi a ruɗe. Nan sukai masa bayanin abinda suka sani kawai. na cewar Yoohan ya fitane shan iska sai ya dawo musu a haka, dama kuma bashi da isashen lafiya, bama suyi zaton zai iya zuwa nan lafiya lau hakaba.
Ɗan shiru Baba malam yayi cike da nazarin bayanin da Solomon yay masu na rashin yin barcin Yoohan, kafin ya zauna kusa da Yoohan ya janye hannunsa daya dafe kansa da shi ya maye gurbinsa da nasa, addu’oi ya fara masa yana tofawa, ya kuma saka Abban Adawiya yin wasu addu’oin a ruwa ya miƙo masa. Kamar Solomon zaiyi maganar karsu bashi sai dai ya kasa saboda nauyin da bakinsa yay masa da kuma kwarjinin mutanen.
A gabansu akaba Yoohan ruwan addu’ar yasha. baba malan ya zuba a hannunsa kaɗan ya kuma shafa masa a fuska. A take ya fara sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ya buɗe baki da ƙyar yace, “Thanks”. Murmushi baba malam yayi kawai, kafin yace, “inaga ya kamata a kaiku masauki ka huta, dan da alama idanun nan naka barci sukeji”. Cike da mamaki Yoohan ke kallon baba malam, duk da dai ya kasa yarda su haɗa idanu da ƙyau dan bala’in kwarjini baba malam ɗin ke masa shikam. Sake murmusawa baba malam ɗin yayi. Ya ɗauke kansa ya maida gasu Omar.
“Farukh a kaisu masauki ko”. Da sauri Omar yace, “To Abba”..

Da gaske Yoohan barci yakeji fiye da zatonsa, dan haka ya kasa musama baba malam duk da kuwa shi a yau yaso su juya zuwa Abuja shi da Solomon da Manager, guards ɗinsa kawai yay shirin bari su kwana a kanon da safe suma su wuce. Amma sai yaji babu abinda yafi buƙata kamar kwanciya a yanzun.
Su Malam ƙarami sun kaisu gida mai ƙyau matsakaici dake gaba da gidansu kaɗan, inda nanne masaukin da su baba malam ɗin kan sauke baƙi daman. Tsaf yake gidan, saima uban ƙamshi mai saka kwanciyar hankali da ya keyi. Duk da babu wutar nefa nanma an tada gen…..
Abin mamaki sai ga Yoohan kamar bugagge, suna shiga wajen kwanciya ya buƙata. Yana ganin gado kuwa ya zube akai yana sauke ajiyar zuciya abin tausayi.
Takalma da necktie ma sai Solomon da Manager ne sukai
dabarar zare masa. Hakama jacket ɗin suit ɗinsa. Sai suka barsa da shirt ɗin da dogon wando kawai.

Manager ne ya kwana tare da Yoohan duk da shi Solomon baiso hakaba. Bawan ALLAH nan yanda ya kwana bautar UBANGIJI haka ya ja doguwar addu’ar samun haske daga Yoohan ɗin. Hakama su baba malam, ranar mafi yawan addu’oinsu akan Yoohan suka yisu da ga su har iyalansu. Da asuba aka kawoma Hamza abin buɗa baki, daga Yoohan har guards ɗinsa barci suke kwasa masu a lokacin.

★★★WASHE GARI★★★

Washe gari sai ga kowa ya tashi banda Yoohan, barci yake cike da kwanciyar hankali, dan haka baba malam daya zagayosu har sau kusan uku ya hana a tadashi.
An kawo musu lafiyayyen breakfast sukaci suka ƙoshi, wajen sha biyu ma aka sake kawo musu abinci nanma. Ganin har ɗaya saura bai tashiba Solomon ya bama sauran ƴan uwansa shawara akan su tafi, shima zaije ya sayoma Yoohan kaya ya kuma nema musu ticket. .
Basu musama wannan shawara ba, suka shirya suka tafi harda Solomon ɗin, dan sai da suka kaisa ya kammala uzirinsa kafin su sake maidosa gida, sukaje sukai sallana da baba malam da yake a lokacin sun samesa tsaye a ƙofar gidansa ya dawo daga orphanage ne..
Baiso tafiyar tasuba, amma sai bai hanasuba tunda ƙila sunada uziri. Ya musu godiya sosai tare da basu tsaraban da aka shiryama Yoohan ɗin dan suyi gaba da ita, suma kuma aka basu tasu. Yanda su baba malam ke musu godiyar sai duk abin ya ɗaure musu kai da saka jikinsu yin sanyi akan a ƙidarsu. Har suna hasashe a ransu dama haka musulmai keda kirki da karamci amma ake aibantasu da nuna musu suba mutanen kirki bane? To su dai gashi jiyane karon farko da sukai mu’amula da musulmai hausawa mai tsaho amma sai basuga hali mara ƙyau ɗin da ake faɗar suna da shiba saima alkairi da ƙyawawan halayya abin koyi.
Sun tafi da wannan alkairai da akai musu cikin rai sosai.

Bayan wucewarsu baifi da mintuna talatinba Yoohan ya farka. Yayi matuƙar mamakin ganin inda ya kwana, manager ya taimaka masa da ruwan wanka, Solomon zai shiga gabatarma Yoohan ɗin da kayan daya siyo masa sai ga malam ƙarami da kaya sabbi fill ya kawo. Sai kuma abinci da aka shiryoma Yoohan ɗin tunda sunsan bai karyaba shi.
Haɗa kayan Solomon yay gaba ɗaya ya kai ɗakin ya ajiye. Ya juya zai fita Yoohan ya fito. Dakatawa yay ya gaidashi cike da girmamawa. Yoohan da kejin kansa sakayau kamar ba shiba ya amsa masa idanunsa nakan kayan da Solomon ɗin ya ajiye masa. sai dai baiyi maganaba sai shi Solomon ɗinne yay masa bayani.
Zama yay ya gyara jikinsa tsaf, ya buɗe kayan duka, na Solomon ƙananun kayane, nasu baba malam kuma shaddace ruwan zuma da akaima ɗinki mai ƙyau kuma dai-dai shi kamar an gwada. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa saka kaya makamanta hakaba. Duk da kuwa suma a nasu yare suna ɗinka shigensu amma shi bai taɓa sha’awar yin hakanba. A yau kam sai yaji sun birgesa har yay sha’awar sakawa. Haka ya warwaresu ya saka.
Baisan lokacin daya furta kalmar ‘Woow!’ ba a fili yana sake kallon kansa a mirrorn ɗakin. A haka manager da shima yay shiri tsaf a kayan da aka kawo masan ya shigo ya samesa. Sosai yake yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan shima, sai ko Yoohan ɗin ke sanar masa shi bai taɓa sakawa ba sai yau. Hamza yayi mamaki sosai, duk da daga jiya zuwa yau ya fahimci su Yoohan sunada tsauri ko a cikin Christians ɗin ma, dan ya karanci yanda guards ɗinsa suka ringa gudanar da al’amiransu.

Sun fito falo Yoohan yaci abinci, bayan ya kammala babu jimawa sai ga Abba da Baba malam sun shigo. Su kansu bakinsu bai iyayin shiru ba sai da suka yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan. Ya duƙar da kansa ƙasa saboda kwarjinin da suke masa yana godiya a garesu, musamman yanda suka sakashi yay barci jiya bayan kwanaki tara daya kwashe baiyi ba.
Cikin hikima ta masu ilimi baba malam ya nuna masa basune ba, UBANGIJI ne yay ikonsa, su nasu kawai roƙone cike da yaƙinin samu. Duk da Yoohan bawai ya fahimci maganar tasu bane sosai saiya gyaɗa kansa kawai. Sun ɗanyi hira kaɗan, duk da Yoohan dai bai saki jikiba sosai. Hamza ne ke biyema su baba malam ɗin, Solomon ma baya saka baki. Wannna ɗan zaman nasu ya saka Yoohan ɗin sake jinjina mutuncin mutanen da sanin darajar ɗan adam ɗinsu. Sai da su baba malam sukayi sallar la’asar sannan sukai musu rakkiya har airportda kansu suna sake roƙon Yoohan ɗin yazo musu bikin salla harma da Manager.
Yako amsa zaizo kodan yay gaisuwa da yaran orphanage.

________________

Guards ɗin Yoohan sun iske madam Chioma ashe bata gari tayi tafiya zuwa ƙauyensu mamarta babu lafiya, saƙon kuma ya risketa bayan wucewarsu kano babu jimawa. Dan haka ta wuce hardasu joy da Gebrail. Su Victoria ne kawai da ƴan aiki suma saboda makaranta ne.
Sun shiga da tsaraban cikin gida suka ajiye har boss ɗinsu ya iso. Aiko zuwa biyar na yamma sai ga kiran Solomon yace suje su ɗaukesu a airport.

Su Abraham sunyi murna sosai na dawowar yayansu, sunata kallon kayan jikinsa mamaki na cinsu. Sai dai sun kasa tambaya dan babu fuska. Shi kuma bayan yaji komai na ciwon kakar tasu sai ya shige sashensa yay kiran momy.
Sun tattauna sosai ya basu shawarar ɗakkota a taho da ita nan Abuja ya dubata, dan ashe dama tun jiyan suke neman layinsa amma bai shigaba. Bayan sun ajiye wayar sai yay kwanciyarsa. Wani barcinne ya sake ɗaukarsa mai nauyi yauma. Bai kuma farkaba sai gabannin asuba.

Washe gari tun kusan goma na safe su Momy suka iso abuja, sun iske Yoohan ɗin ya gama shiryawa tsaf game da jikin kakar tasu. Suna isowa kuwa ya dukufa kanta. Cikin amincin UBANGIJI sai gashi tun aranar jikin nata ya fara sassautawa.
Wannan hidimar jinya ce ta mantar da madam Chioma sake bin ba’asin zuwan Yoohan kano har ma hutunsa ya ƙare yabar abujan.

*_A KWAN A TASHI_*

Babu wahala wajen UBANGIJI, dan gashi yau saura kwana biyu kacal salla, kowanne yanki na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan.
Yayinda su Nu’aymah ƴan saudia keta shirin dawowa suma a ranar sallar………..

 

 

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ɗauka.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari, maida kuɗi gida sai SAHFAT PREORDER_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).

Mamu gee
MIN ƘALB!!

Hafsat rano
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!

Safiyya huguma SIRAƊIN RAYUWA

Bilyn Abdull
SARAN ƁOYE

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

TEAM—-ZAFAFA BIYAR

ALLAH ka gafartama iyayenmu.

 

[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali: Alhmdllh, barkanku da salla. Barkanmu da dawowa filin daga.

Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓacewata ɓat tun kafin azumi. Uzirine babba kuma mai ƙarfi da bazan iya ajiyesaba ya riskeni. Amma Alhmdllh komai ya daidaita. Na kuma gode sosai da haƙurin da kukaimin.

Kufara da wannan kafin gobe idan ALLAH ya kaimu.

 

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biyaba ki haƙura domin ALLAH_*

 

No. 25

……………“Hajjo nikam mizai hana tunda kince bayan salla da sati uku za’ai bikin su Hajarah mu bari sai lokacin bikin muzo ni da Adawiya? Abinda zaki duba abune bana kusa ba, kuma gashi mu duka karatu mukeyi, musamman ma ni da nake gab da kammalawa. Idan har nace zan ringa jeka ka dawo zan iya samun matsala wlhy”.
Hajjo da ke sauraren yah Abdallah ta jinjina kanta cike da nazarin maganganun sa, ta sauke numfashi da gyara zamanta saboda ƙafarta mai mata ciwo. “Gaskiya kam Abdullahi ka fimu gaskiya daga ni harsu ɗan malam, duk da nasan suma ɗin kansu, abinda yasa wannan tunanin baizo musu ba, saboda ba’a gama dai-daita maganar su Kubrah ɗin bane ba. Na kula kamar shi mai auren Hajarah keson kawo wani tsaiko akan batun shiyyasa suka jinkirta harni na koma. Amma yanzu inaga ka barni dasu, zanyi magana ta fahimta da ɗan malam insha ALLAH”.
“Nagode sosai Hajjo, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani. Ki daɗe kiyi ƙarko hajjajun mu”.
Murmushi kawai hajjo tayi da shaƙiyancin jikan nata. Daga haka suka cigaba da firarsu har zuwa wani lokaci ya fice ya barta tana ƙarasa shiri, dan Nu’aymah nacan ta tare a massallaci tana ibadar ALLAH.

Cike da farin ciki Abdallah ya faɗa saman gadonsa yana murmushi, insha ALLAH indai su baba malam suka amince zuwan nasu ya koma sai bikin su Kubrah yanada yaƙinin samun cikar burinsa. Dan babban fatansa shine shirinsa akan mallakar Nu’aymah ya tafi dai-dai, shima ranar ɗaurin auren su Kubrah a ɗaura nasa da masoyiyarsa, farin cikin rayuwarsa.
Wayarsa ya jawo dake a gefensa, ya shiga ma’adanar hotunansa yana kallon hotunan da yaytama Aymah a wannan zuwan nasu batare da ita kanta tasan yana ɗaukarba. Ya jima yana kallon hotunan kafin barci yay awon gaba da shi a wajen
Barcin nasa bai kai mintuna ashirin da ɗaukarsa ba Adawiya ta shigo gidan ita da maman Aaida. Ganin ɗakinsa a buɗe ya sakata nufar can tana faɗima maman Aaida, “Aminiya zauna ina zuwa, naga kamar Yah Ab yana gida ma”.
Ɗan murmushi maman Aaida tayi da bata amsa cike da zolaya. “To adaibi a hankali azumi ake hajjaju”. Batare da Adawiya ta bata amsa ba ta shige tana dariya.

Hajjo da dariyarsu ta sakata farkawa da ga ɗan barcin daya figeta itama ta fito dan taji ba muryar Adawiya bace kawai. “Baƙuwa mukayi a gidan?”. Ta faɗa lokacin da take fitowa falon. Maman Aaida dake latsa waya ta ɗago idanunta ta sauke akan Hajjo. Sai kuma tace, “Barka da fitowa hajiya”.
Hajjo dake mata kallon sani tace, “Barka dai ƴar nan, gashi kuma kamar na sanki”.
Da sauri maman Aaida ta zaro idanu waje da mamaki, sai kuma ta tuna maganar hajiya datai mata gargaɗi tun farko akan zuwa gidan, amma yau tsabar taurin kai sai gashi ta biyo Adawiya data dinga mata daɗin baki……….
“To ko dai kamanni ne?”
Hajjo ta katse mata tunani. Da sauri maman Aaida tace, “Eh gaskiya hajiya inaga hakane, dan ni ƴar nance”. Cike da nazarinta Hajjo tace, “Oh to ALLAH sarki, kinsan idon tsufa ƴar nan. To barka da zuwa, halan ke ƙawar Adawiya ce?”.
“Eh hajiya”. Maman Aaida ta bata amsa a ɗarare, dan tasha jinin jikinta da kallon ƙurulla da hajjon ke binta da shi…

Ɓangaren Adawiya kam tana shiga ɗakin Yah Ab sai ta iske yana barci, ga wayarsa ajiye saman ƙirjinsa kamar wanda ya rungume mace. Harta juya zata fita, sai kuma zuciyarta ta ƙwaɗauta mata wani abu daban. Dawowa tayi da baya a hankali ta ɗauka wayar, kasancewar ta jima da sanin password ɗinsa sai batasha wani wahalar buɗewa ba. Gabanta yay bala’in faɗuwa saboda cin karo da hoton Nu’aymah da tayi, ta kafe hoton da idanunta da suka ciko da ƙwalla, sai kuma ta kalli Abdallah dake barcinsa hankali a kwance batare da yasan tanai ba. Harararsa tayi kamar idanunta zasu faɗo, mikuma ta tuna oho mata, saita ajiye wayar a inda ta ɗauka ta fito a ɗakin.
Karo da taci da hajjo ta fito suna ɗan hira da maman Aaida yasata haɗiye damuwarta ta zauna tana gaisheta.

WASHE GARI

Washe gari ya kama ranar salla, a kuma ranar Nu’aymah ta fito daga ittiqafi bayan sakkowa sallar idi. Duk da tayi ƴar rama sai gata ta ƙara haske saboda yanayin zafinsu da kuma zama cikin ac a koda yaushe. Tayi mamakin ganin Abdallah yazo ɗaukarta. Da farko taso taƙi binsa, amma ganin rana zatayi saboda yau zasu wuce sai ta haƙura ta bisa.
Motar tayi shiru babu mai magana a cikinsu har suka isa ƙofar gidansa. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar yay saurin saka lock. Juyowa tai tana kallonsa fuska a ɗaure, shima sai ya ɗaure tasan, batare da ya kalleta ba yace, “Inason muyi magana da ke a yau”.
Kamar bazata tanka masaba, sai kuma tace, “Yah Ab maganar mi? Dan ALLAH ka cire komai a ranka kamar yanda na cire nima, bana buƙatar wata sabuwar fitina dan girman ALLAH”.
Cikin zafin rai yace, “Saboda kin samu wanda ya fini? Nu’aymah minai miki ne a rayuwa har kika zaɓi sakamin da waɗanan abubuwan? Mina rasa irin na sauran maza ne…..?”
“Baka rasa komaiba Yah Ab, sai dai ka sani mu wannan itace ƙaddarar mu, UBANGIJI kuma shine yasan hikimar dake cikin yin hakan. ALLAH shine shaidata ban gujeka ba, ban kuma daina sonka ba. Sai dai wata katanga mai tsauri tariga da tayi gicci a tsakanin ƙaddarar mu. A ganina kuma babu amfanin maida yanda akayi domin bakin alƙalami ya riga da ya bushe………”
“Sai dai idan kece kika busar da shi Nu’aymah, idan har kin amince inason a wannan karon mu cika burinmu na mallakar juna, na yadda da kaifin wuƙar data datse zaren ƙaddarar mu a wancan karon, sai dai a yanzu na sake ɗaura ɗammarar ɗaure zaren domin mu zama abu guda kamar yanda mukai fata”.
Murmushi mai ciwo Nu’aymah tayi, ta gyara zama tana fuskantar Yah Ab, cikin raunin murya tace, “Yah Ab, karka manta a yanzu kai ɗin mijin Adawiya da Yusrah ne, tayaya kake tunanin zan yarda ka sake ƙulle wancan zaren ƙaddarar da kaifin wuƙa ya datsa ta. A ganina muyi haƙuri kawai da yanda yau tazo garemu, domin kuwa jiyanmu ta wuce sai labari. Muyi haƙurin fuskantar gobenmu sai muzama masu cin riba. Wlhy Yah Ab bazan taɓa iya haɗa zaman kishi da Adawiya da Yusrah b………”
Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, cikin matuƙar ɓacin rai yace, “Hakan ya zamemiki dole kuwa Nu’aymah, idan kuma kikace zakimin taurin kai, wlhy a yanzu sai kunbar ƙasarnan da Adawiya tare da takardar sakinta ɗai-ɗai har uku kuwa”. Yana gama faɗar haka ya cire lock ɗin motar tare da ficewa a fusace.
Nu’aymah da tun farkon fara maganarsa akan su Adawiya ta ɗaura hannu a ƙirji da faɗin, “Na shiga uku ni Zainab! Yah Ab mi kake faɗi haka?”. Bai saurareta ba ya shige gida, da sauri itama ta buɗe motar ta fito ta bisa da ɗan gudu tamkar zata faɗi.

Adawiya dake a ƙwance bayan motar tai saurin cire hannunta data toshe baki, dan daƙyar tai control ɗin kanta lokacin da Abdallah ya furta zai sakesu inhar Nu’aymah bata amince da buƙatarsa ba. Motar ta buɗe ta fito itama da sauri tana faɗin, ‘Tabɗi jan, ashe lokacin yin yaƙin duniya na uku ya gabato kenan, lallai yanzune za’a fara wasan na gaske wlhy’. Ta ƙare maganar hawaye masu zafi na gangarowa a kumatunta.
Tun lokacin da taji Abdallah na sanarma Hajjo shine zaije ɗaukar Nu’aymah bayan an idar da sallar idi ta ƙudiri aniyar binsa a ɓoye. Dan haka kawai taji a ranta akwai manufa a zuwa ɗaukar, dan ta gama fahimtar take-taken Abdallah tun lokacin dasu Nu’aymah suka zo ƙasar. Shinefa ta lallaɓa taje ta shige motar ta ɓoye sannan ya samama hajjo inda zatayi sallar idi a massalacin, shi kuma batare dayin wani tunani ba yana zuwa yaja motar ya wuce. Kuma harya ɗakko Nu’aymah hankalinsa bai kai akan Adawiya dake lafe a ciki ba. wadda ko sallan idi ita batayi ba.

Tana shigowa cikin gidan duk a falo ta iskesu har Nu’  Abdallahn. Duk suka bita da kallon mamaki dan sunta nemanta bayan idar da salla basu gantaba, shine Ahmad yace suyi tahowarsu tunda ita ɗin ƴar garice ai.
“Ke kuma dama ba gidan kika dawo ba?”.
Abdallah ya faɗa cikin kaushin murya dan har yanzu ransa a ɓace yake. Kamar bazata tanka masa ba, dan ranta a bala’in cinkushe yake, ji take kamar ta burmama Nu’aymah wuƙa ta mutu kowama ya huta. Amma komi ta tuna oho mata, sai tai kalar tausayi tana haɗiye ƙududun daya tokare mata maƙoshi. “Eh na biya nan maƙwafta wajen Umm-Farukh, dama wasu kayane mukai da ita zan amsarma su Aymah to kuma ma dai anyi rashin sa’a basu isoba, dama daga Mexico ake kawo matasu”.
Ɗauke kansa yay bai tanka ba, sai Ahmad ne da Hajjo sukai magana. Nu’aymah da tasha jinin jikinta akan yanda Adawiya ke magana ma bata tanka ba, sai dai a ƙasan ranta bata yarda da itaba sam.

★★★

Duk yanda Abdallah yaso sake keɓewa da Nu’aymah dan su sake cimma matsaya akan zancensu taƙi basa dama har suka wuce Nigeria bayan awanni huɗu da sakkowa idi, dan kobi takan bikin sallar da ƴan saudia ke gudanarwa basuyi ba, dama Adawiya ƙin dafa komai tai saboda takaici. Abdallah zaiyi magana kuma Hajjo ta hanashi, acewarta su da zasu tafi yanzu mizasuyi da wani abincin salla bayan nasu nacan na jiransu a ƙasarsu.

Sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba kuwa daga su baba malam, dan ana sakkowa daga sallar juma’a (da yake ranar sallar ta kama juma’a ne) suka nufi airport domin tarbar mahaifiyarsu tamkar yanda suka saba. Babu kunya Nu’aymah taje ta rungume Baba malam, dan harga ALLAH tayi kewarsa shi da Umm da Muhammad. Kai dama ƴan gidan duka.
Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya shafa kan ƴar tasa yana faɗin, “Ja’ira, duk ga iyayenku cike da wuri bakiga kowaba sai ni ko?”. Fuskar Nu’aymah washeda murmushi tace, “Abba nayi kewarka ne sosai, kuma ALLAH kullum sai nayi mafarkinka kai da Ummuna”.
Baice da ita komaiba sai murmushi kawai daya sakeyi, dan shi mutum ne mai tsananin kawaici ga yaransa, yanama ƴan uwansa kara sosai. Dan haka suma a kullum suke ƙoƙarin koyi da ɗabi’unsa akan nasu ƴaƴan.
Bayan Nu’aymah ta ƙarasa ta gaida sauran iyayenta uku suma cike da girmamawa. Suma suka amsa mata da tsananin kulawa sai suka runguɗa gaban mahaifiyarsu suna jera mata sannu da zuwa. Cike da kulawa da kewa take dubansu, fuskarta faɗaɗe da murmushi. Ta kama hannun Abba Musbahu tana faɗin, “Wayyo autana duk ka faɗa, ko azuminne?”.
Dariya Nu’aymah da Ahmad sukayi, Malam ƙarami da Omar na tayasu kuwa. Hakama su baba malam sunata murmushin akan diramar autan nasu da mahaifiyarsu.

Lokacin da suka iso gidan nasu sun iskeshi da dangi da yaransu na ma’auri duk anzo tarbar hajjo da kuma yawon salla. Inda gidan ke wadace da tarin abinci kala-kala da kowanne sashe ya tanada. An gyarama hajjo sashenta tsaf an kuma kai mata abinci daga kowanne sashe an ajiye mata. (Dama haka suke mata).
Motocin na gama tsayawa Nu’aymah bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Umm kira. Da sauri Umm dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Nu’aymah.
Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta tana faɗin, “Wayyo Ummuna, nayi kewarki wlhy”. Umm dake murmushi ta amshi ɗiyar tata da hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Nu’aymah! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne? Bakisan yanzu ba da bane, shekararki goma sha bakwai fa kina shirin shiga sha taƙwas”.
Cike da shagwaɓa ta saka kanta a kafaɗar Umm tana faɗin, “Umm ni indai ina gabanki wlhy jaririyace sabuwar haihuwa, nayi kewarki ne sanyin idaniyata. Ina Muhammad yake?”.
“Nayi cinikinsa” Umm ta bata amsa tana janyeta daga jikinta ta fice domin shiga tawagar masu tarbar surukar tasu.
Baki Nu’aymah ta tura gaba, ta ɗaga ƙafa zata biyo Umm tajiyo muryar Muhammad a bayanta yana faɗin, “Marhaban biki Aunty na”. Saurin juyowa tai garesa, sai kuma ta nufe da sauri kamar yanda yake nufota suka rungume juna cike da kewa da ɗoki.

Haka gidan ya kasance a hargitse ranar saboda shagalin bikin salla, Nu’aymah bataje ko inaba, dan bayan tayi salla taɗanci abinci sai ta shiga ta gaida kowa na gidan, kafin ta koma ɗakin Umm tai kwanciyarta, duk wanda yazo musu yawo a ranar bai samu ganinta ba, dan ta ɓoye kanta a cewarta saita huce gajiyarta da ƙyau tunda dai tasan zasu zaga gari yawon sallar gobe idan ALLAH ya kaimu ai.

___________

Kiran sallar la’asar ne ya tada Nu’aymah dake kwasar barcin gajiya. Ta miƙe da ƙyar dan jikinta ko ina ciwo yake faman mata. Wanka ta farayi, ta saka ɗaya daga cikin kayan sallarta. Tayi ƙyau sosai cikin shaddarta ruwan hoda, taji aikin stones da yay ƙyau sosai. Kayan sun mata ɗas ajiki, tare da sake fiddo haskenta saboda ƴar ramar da tayi.
Lokacin data fito Umm kanta sai da tace, “Masha ALLAH”. Hakama ƴaƴan yayun Umm ɗin su uku da sukazo mata yawon salla duk sai da suka yaba ƙyawun da Nu’aymahr tayi. Ta zauna fuskarta da murmushi tana gaidasu cike da girmamawa. Dan dukansu matan aurene, kuma duk suna da yaransu. Cike da kulawa suke amsa mata, kowanne na mata ƙorafin rashin zuminci, musamman babbarsu.
Nu’aymah tace, “Lah Aunty Zulfah wlhy ba rashin son zuminci bane, ni abinda yasa banason zuwa gidanki wannan ƙanin mijin naki takuramin yake wlhy. ya cika shegen kallo kamar ɗan daudu”.
Dariya suka sanya gaba ɗayansu, aunty Zulfah tace, “To kwantar da hankalinki, indai Fa’iz nema aurensa zaiyi, tunda ke kinƙi. Kinga nima dakin yarda ai dana samu ƴar uwata kusa dani ko…….”
Da sauri Nu’aymah ta katseta da faɗin, “Taf, aunty daina faɗa dan ALLAH, wlhy ya cika iyayi, banason namiji yayta gwalli kamar wani mace, shiba ɗan daudu ba shiba mata maza ba”.
“Amma Nu’aymah baki da kirki wlhy, kin gama ɗebema ƙanin mijin aunty Zulfah albarka gaba ɗaya”. Aunty Rafi’a ta ta faɗa tana dariya. Ita kanta Nu’aymah dariyar takeyi, Umm dai batace musu komaiba. duk da kuwa tana zaune tana jinsu.
Sai da suka tsagaita da dariyarne Nu’aymah ta miƙe tana faɗin, “Umm yunwa nakeji, ALLAH yasa akwai waina dai?”.
“Kin kuwa makaro, dan su Basira na ɗeboma ita gaba ɗaya, kinsan zakici wainar kikaƙi ɗiba ki ajiye?”. Kamar Nu’aymah zatai kuka tace, “Kai Umm! ALLAH yanzu kin daina sona, amma yanzu duk wainar dana gani ace ta ƙare? Su su aunty Basiran miyasa basu zauna sunci a sashen Addah b…….”
Harar da Umm take jefo matane ya sakata yin shiru, dan su Basiran ƙannen Adda ne. “ALLAH ya shiryeki to, to ance miki sune kaɗai suka cinye. Ga yayunki nan suma duk ita sukaci, sannan Abbanku da yay baƙo duk da baya a gidan shima ita yace akai musu kafin ya iso gidan”.
Komawa tai ta zauna kamar zatai kuka, su Aunty Zulfah nata tsokanarta wai ta amshema Muhammad guri tana shagwaɓa bayan shine auta.
Umm tasan yanda Nu’aymah keda jarabar son waina, dan haka ta dubeta sau ɗaya ta ɗauke kanta tana faɗin, “ki wuce sashen hajjo idan bata ƙareba”. Aiko zumbur ta miƙe, a ranta tana fatan ALLAH yasa ta samo.
Duk da takalman data gani na maza a ƙofar falon na hajjo kusan ƙafa biyar bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta yayunsune a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al’ajabi.
Yoohan dake zaune shima cikin Suit ruwan babypink kallon nata yake cike da mamaki, a ransa faɗi yake, ‘Dama yarinyarnan ba’a cikin Orphanage ɗincan take ba? No wander ɗazun baiga komai kama da itaba a cikin yaran’. A fili kuwa sai ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi…….
“Lafiya wai kika tsayama mutane ƙerere a kai Zainabu?”. Maganar Hajjo ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda hajjon take, har yanzu mamakin ganin Yoohan ɗin bai barta ba, “Hajjo wannan mutumin kuma ina kika sanshi?”.
“Wa ɗin?”. Cewar Hajjo tana kallon inda Hamza Manager, Yoohan dasu baba ƙarami ke zaune.
Maimakon Nu’aymah tai magana sai ta je ta zauna kusa da hajjon, matsar da bakinta tai dai-dai kunnen Hajjo tace, “Hajjo arne ne fa wlhy”. “Aina sani” Hajjo ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula.
Sosai mamaki ya kume Nu’aymah, tai tsai tana kallon Hajjon, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Yoohan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.
“Wai lafiyarki kuwa? Kina ganin mutane baki iya gaisuwa bane? Sai shegen kallo malama”. Yah Ahmad ya faɗa idonsa akan Nu’aymah. Sai da taɗan tura baki kafin ta duba Hamza manager data wuce da dukanin imaninsa tace, “Ina yini”. Cikin narkakkiyar murya da shi kansa baisan ta fitaba ya amsa mata da “Lafiya lau ƙanwarmu, kinyi salla lafiya?”. Kai ta gyaɗa masa kawai, dan duk sai taji kuma ta takura da kallon da yake mata. Ganin bata gaida Yoohan ba ya saka Malam ƙarami hararta, yace, “Shi kuma fa?”.
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Yoohan ɗin da yay tamkar baisan da zaman kowaba a falon tace, “Good evening.
Sarai yajita, amma sai ya share baiko motsaba. Sai da Hamza ya ɗan taɓasa da faɗa masa ana gaishesa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Nu’aymah tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa daga saitinsa.
Shima ɗan lumshe nasa yay ya buɗe (dan hakan ya zame masa kamar wata ɗabi’a) cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, “Kina lafiya?”.
A mugun razane Nu’aymah ta sake waigowa inda yake, har taune harshenta take wajen faɗin, “What?! Dama kanajin hausa?”.
Yanda tayi tambayar sai da ya saka su hajjo yin dariya. Hakan sai ya ƙarama Nu’aymah takaici, musamman ganin yanda Yoohan ɗin ya wani yamutse fuska, tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira, dama shi baiyi dariyarba. Sai da yazo daf da ita a hankali yace, “Yeyye girl”.
Kafin wani ya sake magana a cikinsu, ko ita ta bashi amsa Abban su Adawiya da Abban Musbahu suka shigo falon da sallama. Shi kuma ya fice yana amsa wayar.
Daurewa tai ta shiga gaishesu tana ɗan harar ƙofar da Yoohan yabi ya fice ta gefen ido, a ranta kuwa sai cewa take, ‘Oh ALLAH, amma dai gayen nan akwai munafurci, dama yanajin hausa amma duk sanda suka haɗu yake nuna mata bayaji, jibesa da wani shegen aski kamar kan zakara, sai kuwa yaga yeyye kafin yabar gidan nan yau’.
Duk kallon harar Yoohan da take Manager yana kallonta ne ta gefen ido shima, sai da Abban Musbahu ya kira sunansa ne sannan ya maida hankalinsa garesa, a ransa yana mamakin yanda alamu suka nuna akwai sanayya tsakanin Yoohan da wannan Zuƙeƙiyar budurwar data gama tafiya da dukkan imaninsa a kallo ɗaya.
Ita kam Nu’aymah da batasan yanayi ba sai ta lallaɓa ta fice dan jitai tama fasa cin wainar, yau duk yanda za’ai sai taji dalilin shigowar wannan kahirin cikin gidansu, harma falon kakarsu………..

Kina ruwa Aymah.

 

 

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).

Mamu gee
MIN ƘALB!!

Hafsat rano
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!

Safiyya huguma SIRAƊIN RAYUWA

Bilyn Abdull
SARAN ƁOYE

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

TEAM—-ZAFAFA BIYAR

ALLAH ka gafartama iyayenmu.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta_*.

 

No. 26

…………..Cike da jin haushin Yoohan Nu’aymah ta fito daga sashen hajjo. Hakan yayi dai-dai da shikuma Yoohan ɗin zai koma dan ya kammala wayar.
Karo sukayi, goshin Nu’aymah ya bugu da sarƙar Cross ɗinsa. Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Nu’aymah bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon hajjon dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi.
Yoohan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yay azamar ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe ruf.
Cikin tashin hankali Nu’aymah ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen rashin kunya.
Duk da tsawan da yay mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai taɓa faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda samarin gidansu wani ya riƙe mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a ƙirjin ƙaton kahiri, da ko yayunta basu taɓa aikata haka a gareta ba. gashi ya rufe mata baki babu damar magana. Kuma ƙarfi ba ɗaya ba………
Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ƙaru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ƙarfinta tana ƙoƙarin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure balle kai tunanin da biyu yay hakan, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.
“Ouch!!” ya faɗa da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faɗin, “Are you mad?!”.
Nu’aymah da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Eh banda shi. ALLAH ya isana kuma, wlhy ka sake gigin taɓani saina fasa maka kai, danni ba ƴar iska baceba!”.
“Silly girl! Waye ɗan iskan?” ya faɗa da turanci kamar yanda ta faɗa itama yana galla mata harara tare da cafkota, iya ƙarfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faɗawa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ɗayan hannunsa. kafin ya ɗago ɗayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yay ganin yanda shatin haƙoranta suka fito masa, ba wajen data ciza ɗin kawaiba, tafin hannun gaba ɗaya yayi jaa abinka da ba’asan wahala ba…
Nu’aymah ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Yoohan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ɗayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa ya maye gurbin hannun nasa da bakinsa. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haɗe bakin nasa da nata ya shiga kissing ɗinta.
Yanda take kuka da turesa da yakushinsa ne ya sashi janyewa daga gareta da sauri. Duk da halin daya ganta na ƙololuwar shiga ruɗani da tashin hankali hakan bai hanashi kallonta ba, tare da zazzaro mata manyan idanunsa da suka sauya kala zuwa ja.
Harga ALLAH Nu’aymah ta tsorata yau kam, dan ta tabbatar tunda har ya iya mata wannan abun a cikin gidansu to lallai zai mata duk abinda yazo masa rai. Tunda tasan su basu ɗauki keta mutuncin mace a komai ba. Amma tsabar ƙarfin hali irin na mutuniyar taku ana sakar mata baki sai ko ta murguɗa masa bakin da sake zuba masa harara. iya ƙarfinta ta turashi dan har yanzun yana manne da ita ne a bangon, amma ko gezau baiyiba balle tasa ran samun hanyar kuɓuta. Waige-waige take gudun kar wani ya fito ya gansu a haka, tana kuma hawaye, cike da tsiwa cikin harshen turancin data san yafi fahimta sosai tace,
*_“Dama ku babu abinda kuka iya sai son taɓa mata da ɓata musu rayuwa, ALLAH ya isana ɗan iska kawai. shiyyasa wanda baya salla an haramta ma sa jin daɗin duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda huɗu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin ƙabari da ranar hisabi. A duniya ana ɗebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama’a ƙyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulaƙanci da yunwa da ƙishirwa. A cikin kabari ALLAH zai ƙuntata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumurci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a baƙanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla-dalla, sannan a haɗa shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, sallah ita ce ginshiƙin addini. Idan kaƙi gaskiya zaka faɗa ɓata. Idan ba ka ji nasiha ba, zaka yi da-na-sani. Wanda baiji bari ba ya ji hoho!……”_*
Ta ƙare maganar da sake turashi da ƙarfi. Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun.
Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ƙarfi, tare da ɗora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Oh lord!, mina aikata?!”.

★★★★

A wani ɗan lungun sashensu Nu’aymah ta maƙale tana sauke tagwayen shashshekar kuka, har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Yoohan ɗin biyota yayi.
Ta ƙanƙame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmiƙewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi.
Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. ‘Na shiga uku ya biyo ni’ ta faɗa a fili zuciyarta na wani irin zallo tamkar zata faso ƙirjinta ta fito……..
“Nu’aymah lafiya na ganki anan? Mi kikeyi ne haka?”.
Duk da ganin Aunty Kubrah ce ba Yoohan ɗinba hakan bai hana Nu’aymah sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. “A..Aunty babu ko.. Komai”.
Kubrah data kafeta da ido taɗan murmusa, sai kuma ta juya bayanta tana faɗin, “Ki kwantar da hankalinki ai ba biyoki yayi ba, na tabbatar kuma babu wanda ya ganku a gidan nan”.
Wani muguwar faɗuwa gaban Nu’aymah ya sakeyi daboda jin furicin Aunty Kubrah. Cikin rawar harshe Nu’aymah tace, “Aunty Kubrah wlhy ni…….”
“Kinga kwantar da hankalinki Nu’aymah babu maiji, indai nice ko Hajarah baza taji wannan zancenba balle wani a gidan nan. Amma inason ki faɗamin gaskiya, yaushe kuka fara wannan abun ke da shi?”.
“Innalillahi! Aunty wlhy bamu taɓa yiba, yau ma na rantse shin……”
“Kinga ya isa. Share waɗan nan hawayen idan baso kike ki tonama kanki asiri ba da kanki”.
Nu’aymah duk ta sake rikicewa, tama rasa fahimtar inda maganganun Aunty Kubrah suka dosa saboda tashin hankali. Duk da ta share hawayen sun gaza tsayawa. Hannunta Kubrah ta kama har lokacin fuskarta da murmushin da Nu’aymah ta gaza fahimtar na minene. “Kinga muje sashenmu, idan ba hakaba Umm sai ta fahimci abinda ya faru, ko kinfi buƙatar hakan?”.
Da sauri Nu’aymah ta shiga girgiza mata kai, “A’a wlhy Aunty, banason Umm ta sani dan zata kasheni, dan ALLAH karki faɗa mata, wlhy kuskurene ba kuma laifina bane ba, na rantse da ALLAH Aunty ban taɓa yiba, ko hannuna Namiji bai taɓa riƙewa ba”. Ta ƙare maganar da rushewa da wani irin kuka maiban tausayi.
Komai Kubrah bata sake cewaba ta kama hannun Nu’aymah suka nufi sashensu. Ta ƙofar baya tabi da ita, dan ƙannen Addah su Aunty Basira suna falo zaune dasu Addah suna hira. Batare data bari sun gansu ba ta shige da Nu’aymah bedroom ɗinsu. Zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna a kusa da ita. Har lokacin kuma Nu’aymah kuka takeyi, zuciyarta na ƙarajin tsanar Yoohan matuƙa……..
“Ko shine Ameer ɗin Saurayinki?”.
Da sauri Nu’aymah ta ɗago tana kallon Kubrah, sai kuma ta shiga girgiza mata kai, “Aunty dan ALLAH ki yarda dani, wlhy Ameer ba saurayina bane. Wannan kuma bama musulmi bane ba, baƙone yau na fara ganinsa”.
Haɗe fusaka Kubrah tayi tamau tana kallon Nu’aymah ɗin. “Karkimin ƙarya Nu’aymah, inba hakaba wlhy na fasa rufa miki asirin, a yau da daddare zan sanarma Hajjo da Baba malam da Umm komai. Ki faɗamin tun yaushe kuke tare? Sau nawa kuma yay amfani da ke?”.
Duk sai Nu’aymah ta sake daburcewa, dan tama rasa wace amsa zata bama Aunty Kubrah, gaba ɗaya ta kasa fahimtar manufar Kubrah…….
Kamar Kubrah tasan tunanun da Nu’aymahn keyi, sai ta sassauta fuskarta tana gyara zama. Ta ɗan rage kaushin muryarta kuma ta koma magana cikin lallashi. “Nu’aymah kinsan dai yaya nake a gareki, duk abinda zan iya gani gasu Hajarah raina ya ɓaci idan nagani daga gareki dolene naji zafi, ɗiyar ƴar uwar mahaifiyata ce kuma ke, dan kuwa Umm tamkar ƴar uwar Adda take, tamafi min wasu ƴan uwan Addan. Yanzu Nu’aymah da wani ya ganki a gidannan ƙaton banza yana lalubeki mikike tunanin zai faru?, idan ma iskancin zakiyi ai gara kuyisa can a waje wani bai gankiba ko, amma a cikin gidanku? Babban gida mai daraja irin wannan? Wane kallo kikeson aima iyayenki maza damu kanmu Nu’aymah?”.
“Dan ALLAH kiyi haƙuri Aunty Kubrah, wlhy bazan sakeba wannan ma ƙaddara ce da kuma kuskure”.
“ALLAH yasa hakane to”. Kubrah ta faɗa tana wani ɗauke fuska da ƙyaɓe baki.
Nu’aymah na kuka tace, “Wlhy da gaske nake Aunty. Dan ALLAH ki yarda dani”.
“Nu’aymah idan ban yarda da ke ba minene amfanin musawar to?, tunda idan kunbar gabanmu ALLAH kaɗai yasan mi kuke aikatawa, masu iya magana fa kance rana dubu ta barawo, ɗaya tak ta mai kaya. Yau ɗinma ai bakiyi tunanin zan ganku ba”.
Ƙasa Nu’aymah ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, ‘Ita mizata faɗama Aunty Kubrah ta fahimceta ne wai? Wane rantsuwa zatai mata danta yarda ba da yardarta kafirin nan ya aikata hakanba a gareta?’.
Sai da taci kuka sosai, Kubrah na zaune na kallonta kafin ta ɗagota ta rungumeta, “Kukan ya isa haka, aina yarda ba laifinki bane. Na miki hakane kawai dan kisan baki dai-dai ba”.
“Na gode da kika fahimceni Aunty, kuma namiki alƙawarin hakan bazata sake faruwa ba insha ALLAHU”.
Ɗagota Kubrah tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alƙawarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, kije bayi ki wanke fuskarki kizo ki sake shafa hoda dan karma wani ya zargi wani abun kuma kinji ko. Ki kuma saki jikinki inba hakaba Umm zata gane, kuma kinsan halinta. Zatabi duk hanyar data dace dan tasan gaskiyar abinda ya sakaki kukan”.
“Insha ALLAHU bazan bari ta gane ba Aunty, bara ma na wanke”. Ta ƙare maganar tana miƙewa da sauri ta nufi bayin su dake cikin ɗakin. Tana wanke fuska tana kallon bakinta a mirror. Wasu hawayen sai sake ƙoƙarin zubowa suke tana dannesu da ƙyar. A fili tace, ‘Na tsaneka mugu ɗan iska mai suffar samudawa, bazan taɓa yafe makaba wlhy”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Taja kusan mintuna biyu tana kukan kafin ta wanke fuskar ta fito. Fitowar tata tayi dai-dai da shigowar Hajarah da wayar Kubrah a hannu. Da mamaki Hajarah take kallon Nu’aymahn, dan ita dai bataga shigowarta sashen ba.
“Nu’aymah yaushe kika shigo ne? Gashi kamar kinyi kuka?”. Da sauri Nu’aymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli Inda tabar Aunty Kubrah dan tana zaune a wajen, tana jinsu kuma amma ko kallonsu taƙi tayi balle ta nuna alamar tasan mi sukeyi ma. “Babu komai Aunty Hajarah, kaina ne kawai ke ɗan ciwo”.
Ƙarasawa inda Nu’aymahn take Hajarahn tayi, ta ɗago fuskarta cike da nazari……..
“Wai miye hakane? Tace miki babu komai kanta ke mata ciwo miye na damunta ne kuma?”.
Baya Hajarahn taja kanta a ƙasa tace, “Kiyi haƙuri Aunty Kubrah, ga wayarki dama Alhaji ne ya kiraki”. Ta matsa inda take cike da girmamawa ta bata wayar.
Tana amsa ta nuna mata ƙofa da ido. Da sauri kuwa Hajarahn ta fice.
Kubrah ta maida dubanta ga Nu’aymah dake a tsaye har yanzu. “K kuma ki bada himmar tonama kanki asiri kinji ko, ki wuce ki shafa hodan, idan kuma sokike wani ya sake shigowa to”.
Gaban Mirror Nu’aymah ta ƙarasa. Ta shafa mai da hoda harda kwalli, duk da dai hakan fuskar dai babu walwala.
Amma sai Kubrah batace mata komaiba suka fito falo inda su Hajarah ke hira tare. Zama tayi kamar yanda Addah dake kallonta ta Umarceta. Su Aunty Basira nata tsokanarta da faɗin ina tsarabarsu ne?.
Tun tana noƙewa dai harta ɗan ringa amsasu, amma ta gaza sakin jikinta yanda ya kamata sosai. Duk motsinta Hajarah da Addah na lura da shi, sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu.

___________________________

A ɓangaren Yoohan kuwa duk yanda su Hajjo sukaso ya zauna jiran dawowar baba malam ya gaza hakan. Yace musu zai dawo da safe yanzu yanada wani uziri.
Badan hajjo taso ba ta barshi. har ƙofar gida su Yah Ahmad sukai masu rakiyya shi da Manager. Inda su Solomon ke jiransa a mota. Kasancewar basu iske baba malam ba yasa bai shiga dasu cikiba. Yace su jirashi a waje. Dan da ƙyarma Su Ahmad suka lallaɓashi ya shiga cikin gidan. Da farko ya ce zai koma tunda baba malam ya fita. Dan dama yaso yin surprise ɗinsa ne shiyyasa bai sanar masa shigowarsa kanon ba ma.
Har drivern sa ya tada mota ya tsaidashi. Kuɗi ya ciro a cikin jakarsa rafa guda na ɗari biyar sabbi ƙal ya miƙama malam ƙarami yana faɗin, “Please a bama yarinyar nan barka da salla. Na manta ban bata ba”.
Malam ƙarami da ya fahimci Nu’aymah yake nufi sai yay murmushi. bai musa ba ya amsa yay masa godiya, dan suma daya basu sukaƙi amsa a ciki ɓata rai yayi, wai basu ɗaukesa ɗan uwansu ba. Hakanne ya sakasu amsa tunda yace barka da salla ce.
Duk abinda ke faruwa Solomon na saurarensu. Dama cike yake da haushin sake zuwa wannan gidan. Ya kuma ɗauki alwashin suna komawa wannan karon sai ya sanarma madam Chioma. Dan tsaf ya fahimci waɗan nan mutanen zasu iya jan hankalin Ogan nasu tsaf, musamman yanda suke masa hidima kamar wani sarki. Yanzu haka a gabansa aka saka babbar leda a booth wai kayan barka da salla ne aka bama Yoohan ɗin a cikin gida. Ya cije bakinsa yana satar kallon Yoohan daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu kamar mai barci ta mirror.

Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu’aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.
ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,
*Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo ƙaton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta ƙarfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ruɗu, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni’imtaccen yanayi yana masa murmushi da miƙa masa littafin nan na musulmai (Al-Qur’ani), yakan ringa ce masa_______*
*_“Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake ƙunshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman riƙo dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya ƙyaƙyƙyawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin taƙama da riƙo sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka riƙe gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga saɓama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi alƙawarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka karɓi kalmar LA’ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*
A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al’amari sai yay azamar ƙwaɓar kansa harma da alƙawarin nisanta kansa da su baba malam ɗin. Dan yau ɗin nanma da ƙyar manager ya lallaɓa shi sukazo nan ɗin. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.

Kafin su ƙarasa hotel ɗin daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ruɗanin kalaman Nu’aymah da mafarkinsa. Sai ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi.
Motocin na tsayawa baiko jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards ɗinsa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key ɗin ɗakin Yoohan ɗin yanama a hannunsa ne.
Ɗan gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin tare. Solomon ya buɗe masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga.
Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon ɗin sai ya bisa yana faɗin, “Sir lafiya kuwa?”.
Cak Yoohan ya tsaya da ga yunƙurin shiga Bedroom ɗin da ya keyi, batare da ya juyoba ya ɗagama Solomon ɗin hannu da masa alamar ya barsa.
Da baya-baya Solomon ya rinƙa tafiya harya fice da ga ɗakin, yaja masa ƙofar a hankali gabansa na faɗuwa da yanayin ogan nasu………….

Tofa, Dr Yoohan yaya dai?

 

 

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).

Mamu gee
MIN ƘALB!!

Hafsat rano
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!

Safiyya huguma SIRAƊIN RAYUWA

Bilyn Abdull
SARAN ƁOYE

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

TEAM—-ZAFAFA BIYAR

ALLAH ka gafartama iyayenmu.

 

 

[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta_*.

 

No. 27

…………Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ɗan naushi gadon da faɗin, “Noooo!!!”. Da ƙarfi kamar mai magana da wani.
Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ɗin yarinyar da ko sunanta baima sani ba. Miƙewa yay daga gadon ya shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin, ko takalman dake ƙafarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ƙarasa gaban shower ya tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ƙarfi, tamkar itace tai masa laifi.
Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon lokaci ya gama jiƙewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ƙarasa saman toilet sit ya zauna yana mai riƙe kansa da hannu biyu….

_______________________

Duk yanda Nu’aymah taso sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta miƙe daga zaunen da take kusa da Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
Sai da taɗan saci kallon Addah da tai banza dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. “Um…..u…. Zanje su Aunty Zulfah na jirana”. Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata kifa dan sauri.
Karo suka kusan ci da Malam ƙarami da ke shigowa. Tai saurin komawa da baya tana faɗin, “Yi haƙuri Yaya, bansan ka taho ba”.
Murmushi ya mata da cewa, “Karki damu Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm”. Ɗan kallonsa tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake faɗaɗa murmushin sa, “Dama ba wani abu bane, baƙon da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki. Shine naje kai miki na Iske baƙya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki”.
Tunda ya ambaci baƙo gabanta ya sake tsananta faɗuwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin gaskiya. Sai kuma ta ɗan juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin faɗin, “Ni banaso Yaya”.
Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon. Shi malam ƙarami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka shiga ƙyalƙyala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
Hajarah ce ta fara farga da yanayin Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana faɗin, Aunty Kubrah ALLAH dama nasan ba ciwon kai Nu’aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su Addah shine duk take a ruɗan nan”.
Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma mikewa tai ta bar falon tana wani ɗan murmushin da su duka basu fahimci ma’anarsa ba……

Nidai nace, “Humm”.

“K lafiya? Kika shigoma mutane tamkar wadda aka koro!”. Umm ta faɗa a tsawace tana kallon Nu’aymah data shigo falon a guje.
Duƙar da kai tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace  “Umm babu komai fa, zanje toilet ne”. Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ɗakinta da sauri.
Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai banda Umm da tabi Nu’aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta faɗa ba.

Tana shiga toilet ɗin ta maida ƙofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ƙofar ta fashe da kuka maiban tausayi. A ranta tana faɗin yaya zatai da wannan abin kunya da takaici da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da baya bautama ALLAH. Baisan idan ya saɓama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai taɓa ambaton ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine yau akan nata. ‘ALLAH ya isa bazan taɓa yafe makaba’. Ta faɗa a fili tana sake rushewa da kuka. ‘Na shiga uku ni Zainab, ni………’
“Nu’aymah!”. Muryar Umm ta hanata ƙarasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
“Nu’aymah wai baƙya jinane?”.
Umm ta sake faɗa tana matsowa jikin bayin.
Da sauri Nu’aymah tai gyaran murya. Kafin ta miƙe da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ɗaya taima mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar tata sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito.
Haɗa ido sukai da Umm da ke a tsaye tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ƙasa da faɗin, “Umm yi haƙuri, ALLAH toilet ne”.
“Toilet ko kuka?”.
Da sauri ta ɗago ta kalli Umm ɗin. Muryarta na rawa tace, “Umm toilet ne ALLAH”.
“Toilet ɗin ki kai ma kuka kenan?”.
Baki taɗan tura gaba, “To Umm gudawa fa ce”.
“Mtsoww! K dai bansan randa zaki bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani ba”.
“Kiyi haƙuri Umm”.
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka ƙureta, sam bata ƙaunar halin banza.
Duk da tana buƙatar kaɗaici haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin tufƙa da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ɗaya).
Tana zama aunty Rafi’a tace, “Hummm! Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen daɗi haka?”.
Gaban Nu’aymah yay mugun faɗuwa. Ta ɗago da dauri tana kallon aunty Rafi’a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta buɗe baki zatai magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
Wata muguwar ajiyar zuciya Nu’aymah ta sauke a ɓoye. Tare da saurin miƙewa zumbur ta nufi su Nanah ta rungume.

Zuwan su Nanah gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin yaƙi barin ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen shaƙar ƙamshin a jikin Nu’aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa da wannan ƙamshin ba. Amma sai bataima Nu’aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.

____________________

Ya jima zaune matuƙa akan toilet sit kafin ya miƙe ya fara zame jiƙaƙƙun kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito sanye da Bathrobe fara mai ɗan tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa kaɗan. Towel ƙarami ya riƙo a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
Kallo ɗaya yayma Solomon daya kasa haƙuri ya dawo ɗakin duk da korar da yay masa ya ɗauke kansa. Kan Solo a ƙasa yace, “Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani hali”.
Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ɗakin. Zama yay cikin ɗaya ya ɗora ƙafafunsa saman table ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi……..
“Ina buƙatar coffee”. Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da “Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
Ba’afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa sai ga cikin ma’aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
“Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.

Yoohan da baisan Solomon bai fitaba ya fara shan coffee ɗin a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba da zama har tsahon lokaci.
Zuwa can kuma tamkar wanda aka mintsina sai ya miƙe, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya buɗe ƙofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangyaɗi a falo, kansa ya ɗan girgiza ya nufi ƙofa batare da yayi magana ba.
Can ya fita harabar hotel ɗin da ko ina ke ƙwanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su kaɗai ke shigowa alamar masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su kaɗai ne suma, dan wasu matafiyane ba sheɗancin ne ya shigo dasu ba.
Watsar da komai yay dan shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ɗaya ya zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun ɗazun.
A cikin tunanin nasa ne hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk da ya saka ƙarar can ƙasa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ɗin dama bana ku bayi bane, na manya ne masu ji da ƴan canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa baka amsa.
Lecture ce da ga bakin Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga kunnen Yoohan raɗam. Buɗe idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren wa’azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ɗaya zakai masa kasan kaga ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren wa’azin sa.
Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa’azin nan mutumin ya miƙe, batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya koma ciki dan ya kwanta ya huta.
Ko kaɗan Yoohan baiso hakan ba, dan anzo wata gaɓa da duk mai sauraren wa’azin zai so jin ƙarshensa. Bin mutumin yayi da kallo harya ɓacema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya roƙe ya basa ya ƙarasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmiƙe masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da maganganun Nu’aymah sai lecture ɗin nan daya saurara ta sake faɗaɗa rauninsa zuwa ƙololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ɗan waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura.
Sake maida idanunsa yay ya lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga saukewa a jajjere.
A haka Solomon daya sake shiga ɗakin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar zuciya .
“Ashe kana anan sir?!”. Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ruɗanin da yake ciki na rashin ganin nasa da farko.
Yoohan da tun isowar Solomon wajen yana kallonsa ta ƙasan ido ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani shegen kallo mai cike da gargaɗi…..
“I’m sorry sir. Madam ce”.
Kafesa da ido sosai yayi, duk da kuwa yasan Momy Solomon ɗin ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya miƙe yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a tashe.
Koda suka koma ɗakin bai gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi toilet ɗin dan ya duba. Shi kuma ya ɗora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo da kauri ɗin nan ta fara fidda sauti. “Hello Mom”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi madam Chioma ta sauke da ga can, kafin cikin ƙasa da murya sosai tace, “My boy!”.
“Humyim”.
Ya faɗa a hankali cikin maƙoshi.
Murmushi mai sauti ta sake da ga can tana mai ƙanƙame filo a ƙirjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace, “Mike damunka?”.
Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya furzar da ɗan huci yana sauke idanunsa da ga table ɗin. “Ba komai Mom, bakiyi barci ba?”.
Sake narke murya tayi kamar zatai kuka. Tace, “My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna tsananin buƙatar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ƙannenka gaba ɗaya. Amma duk da ɗokin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da ka ɗauka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja mun ganka ba”.
“Am so sorry Mom”. Ya faɗa a taƙaice kawai.
Matse filo ta sakeyi sosai a ƙirjinta. Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito. Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na faɗin, “Mom goodnight, zan kwanta”. Ƙitt ya yanke wayar.
“My b……” tai yunƙurin faɗa sai kuma taji ƙitt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata ƙanƙame papa ya shigo ɗakin nata.
“Wai lafiya kika maƙale anan bayan inata jiranki a can?”.
Wani irin takaici da baƙin ciki ne ya kumeta a zuciya. Ta ɗan hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ɗaci a ranta. Amma a zahiri sai tai ɗan murmushi da cewa, “Ka bari kawai. Solomon ne ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya haɗamu dan wayoyinsa duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ƙarshe ma ya yanke wayar”.
Ƴar dariya Papa dake hawowa gadon yayi. ya jata jikinsa ya rungume yana faɗin, “Kema kinsan halin yaronki ai. Minene zai ɓata miki rai a ciki. Maybe yana buƙatar hutawa ne shiyyasa ya kashe”.
Kafin ta samu damar basa amsa ya haɗe bakinsu waje guda. Duk yanda taso ta ƙwace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar ALLAH ya bashi sa’a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai buƙaci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ƙarfi yake nuna mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun nan da bazasu gaza goma zuwa sha ɗaya ba.
To komadai minene yau ya moreta da ƙyau. Daga ƙarshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fyaɗe. Da ƙyar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama ya sacetan.

Yoohan kam koda ya yanke wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ɗazun.
A haka Solomon da ya kammala tattare kayan da Yoohan ɗin ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya lallaɓa kawai ya ɗauki wayarsa ya fice da ga ɗakin. Duk da Yoohan najinsa bai motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da faɗawa cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al’ajabi a garesa.
Gabannin asuba ya farka a firgice, da ƙyar ya iya motsa wuyansa da ya ƙage, cikin dauriya da jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ɗan sake masa sannan ya miƙe tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa huɗu sai baiyi magana ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu’a kamar yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin buɗewa. Hannu ya saka ya buɗe Window ɗin. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ƙwala kiran sallar farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ɗine ko kuma a cikin hotel ɗinma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa. Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nishaɗa na musamman…………..

 

 

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).

Mamu gee
MIN ƘALB!!

Hafsat rano
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!

Safiyya huguma SIRAƊIN RAYUWA

Bilyn Abdull
SARAN ƁOYE

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

TEAM—-ZAFAFA BIYAR

ALLAH ka gafartama iyayenmu.
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana_*.

 

No. 28

…………Sake buɗe idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ɗaya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta riƙeta. Sannan babu wata sarƙa ko ƙarfe da suma suke amsa sunan ginshiƙi a gareta. Da rana hasken *_Rana_* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ƙawata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al’ajabi. Hakama da yammaci lokacin faɗuwar rana takan ƙawatu da kalar sky blue da na yanayin faɗuwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ɗaya. Babu kuɗin haraji babu na ƙarshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai taɓa jiran mu biyasa da ko taro ba?  ‘saboda shi ɗin *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KAƊAICE SA)’_*
Wani yanki na zuciyarsa ya bashi wannan amsar.
Samun kansa yay da sake lumshe idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data faɗo cikin kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son sanin ni’imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ɗin nasa ne.
‘Tabbas ina son sanin ni’imar dake cikin addinin musulinci?’. Ya amsa tamkar shi ɗin akeyima tambayar kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ƙasa cikin giza-gizai alamar lokacin faɗuwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
Tabbas wannan tambaya ta tsayama Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ƙarasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai sannan ya iya barin jikin Window ɗin zuwa toilet.
Ji yake a ransa bazai taɓa samun nutsuwa ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana buƙatar sanin (Hanyar fahimtar ni’imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).

A gaggauce ya gudanar da komai. Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ƙananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai gajeren hannu. Sai ya ɗora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie ba, maɓallin shirt ɗinma ba duka aka rufe ba. Cikin ƙamshinsa ya baro cikin hotel ɗin batare daya nema inda su Solomon suke ba.
Safiya ce sosai a garin, hakan yasa da ƙyar ya samu keke napep, shima da mutum ɗaya a ciki. Bai damu ba, duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ɗin. Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ƙyar ya iya haɗa hausan ya bashi amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin abubuwa sosai saboda mu’amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza’a rasaba suma ɗai-ɗai ne.
Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya miƙama mai napep ɗin. Da mamaki shiko yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba. Sake miƙo masan da yayne ya saka mai napep ƙoƙarin haɗa ɗan turancinsa ya sanar masa naira ɗari da hamsin ne kuɗinsa. Duk da dai turancin bai haɗu da ƙyau ba Yoohan ɗin ya fahimci mi ya faɗa. Dan haka ya ajiye masa kuɗin a jiki yana faɗin, “Na baka ne duka”. Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya kasa haƙuri sai da ya dara.
Yoohan baibi takansa ba ya nufi ƙofar gate ɗin su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
Sau uku yay Knocking sannan maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo yana tambayar “Wai wanene haka da farar safiyar nan?” dan yasan su Baba malam ta ƙaramin gate sukaje massallaci yau.
Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay har sau biyu bashi kaɗai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya gama ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin yace, “Samari lafiya kuwa? Mikake nema ko buƙata anan?”.
Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan kalmar (lafiya da wasu ɗai-ɗai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ɗinma dai ba fahimtar yayi ba. Sai ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
“To bakajin hausa kenan?”. Maigadi ya faɗa a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana zuwa). Kafin Yoohan ɗin yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yunƙurowa Yoohan ɗin yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ƙofar.
Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake fitowa cikin massallacin. Sai kuma sautin karatun yara da shima alama ta nuna daga harabar massallacin ne.
Nufar gate ɗin massallacin yayi, kasancewar shi a buɗe yake sai ya samu damar shiga kansa tsaye. Sai dai bai kai tsakkiyaba wani cikin almajiran malam ya tsaidashi da sauri, dan kallo ɗaya zai tabbatar maka Yoohan ɗin ba musulmi bane.
Anyi sa’a almajirin malam najin turanci, sannan kuma duk zuwan da Yoohan yayi gidan sau biyu ya gansa. Ba ƙaramin daɗine ya kama Yoohan ba jin cewar almajirin malam najin yaren da shima yake ji. Cikin sauƙi suka gaisa ya sanarmasa wajen malam yazo. Kuma yana cike da ƙaguwar san ganinsa domin dalilin babban uziri.
Duk da almajirin malam yayi mamaki hakan bai hanashi yarda zaima Yoohan ɗin iso ba. Dan haka ya nuna masa wani ɗan dakali alamar ya zauna ya jurasa. Shi kuma ya juya cikin massallacin inda yasan malam na zaune yana karatu da azkar kafin ya fara karatu ga magidantan anguwar dakan ɗauki karatun safe da baya wuce zaman awa guda.

Yoohan bai zauna ba. Sai ma faman bin massallacin yake da kallo. A ransa yana sake jinjina ƙoƙarin da su baba malam sukai wajen ginashi. Dan ƙaton gaske ne, kuma ya ginu da gini mai ƙyau. Gashi an shafesa da farin fenti yanata ɗaukar ido tamkar ba’a shiga cikinsa, sai shukoki da suka sake ƙawata shi suma. Ko ina kuma a tsaftace yake. Daga wajen da yake tsaye yana shaƙo daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga massallacin wanda kullum safiya da maraice Nu’aymah ke zuwa ta sharesa ta saka turaren wuta da kalolin Air Fresheners masu daɗin ƙamshi……….
Kukan wani yaro ne ya katse masa tunanin nasa. Ya ɗan juya inda yake jiyo kukan. Hakan yayi dai-dai da fitowarta daga cikin ajin da take koyarwa riƙe da bulalar dorina. Sanye take da dogon hijjabi mai hannu fari tas dan har yana jan ƙasa. Hannunta na dama riƙe da Al-qur’ani, na haggu kuma bulala. Yanda take jijjiga bulalan tana magana da nuna yaron ne ya sakashi shagala da kallonta. A ransa ya raya, ‘Ashe kowa ma masifa take masa?’. Jiba dai yanda takema yaro ƙarami duk da kuwa bayajin mi take faɗa. Amma yanayinta ya nuna faɗa takeyi dan tama saka yaron kneeling ne a ƙofar ajin………
“Yahya! kai ne da safen nan?”.
Maganar baba malam ta katsesa daga kallon Nu’aymah daya shagala yi. Numfashi ya sauke tare da juyowa ga baba malam ɗin. Baba malam daya juya yana kallon abinda Yoohan ɗin ya shagala kallo shima ya ɗauke kansa ya maido garesa. Sake mai-maita masa tambayar yayi a karo na biyu.
Yoohan da ya sunkuyar da kai ƙasa yace, “Uncle, inason sanin minene ni’imomin dake a cikin addininku na musulinci?!”.
Ba baba malam da yayma tambayarba, hatta Abban su Abdallah dake fitowa daga massallacin sai da ya taka wani uban birki.
Baba malam da jikinsa ya hau tsuma yace, “Yoohan sake maimaitawa naji”.
Babu musu Yoohan ya kuma faɗin,
“Ina son sanin ni’imar dake cikin addinin musulinci?!”.

الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.

Sai ya durƙusa a ƙasa yay sujida hawaye na sauka masa a fuska.
Yoohan dake binsa da kallo yay saurin duƙawa shima yana zaro manyan idanunsa a waje. durƙushewa yay gwiwa bibbiyu yana kallon malam harya ɗago daga sujidar da yay.
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya kama Yoohan suka miƙe tare, sai kawai ya jawosa jikinsa ya rungume.
Duk da ba yaune karan farko da aka fara yima Yoohan irin wannan rungumar ba sai yaji ta yau ɗin kamar daban ce a rayuwarsa. Kamar ba irin wadda Papa da sauran mutane ke masa bace. Kamar girman ta yau ɗin na musamman ne.
Baba malam ya ɗagosa da sauri tare da riƙe hannunsa. Yace, “Lallai yau zaka fara sani da ga rahamar UBANGIJINA, domin kuwa, *HASKE da RAHAMAR UBANGIJIN* al’arshi ta bayyana a zuciyarka da harshenka Yahya!. Sai dai bazaka taɓa fahimtar tarin ni’imomin dake cikin musilinci ba daga wajensa har sai ka shigo cikinsa”.
Yoohan da bai fahimcesa ba yay shiru yana kallonsa ƙasa-ƙasa. Sai kusan seconds goma ya ɗago kaɗan ya kalli baba malam ɗin da ƙyau, sai kuma ya sake maida kansa ƙasa. “Uncle ban gane mikake nufi ba”.
Murmushi baba malam yayi, ya sake gyara tsaiwarsa cikin harshen turancin da suke magana yace, “Ina nufin bazaka taɓa fahimtar ni’imomin dake tattare da wannan addini mai daraja ba har sai ka kasance musulmi Yoohan. Ta wannan hanyar ne kawai zaka ƙwanƙwaɗi madarar ni’imar UBANGIJI fiye da zaton hasashen ka”.
Babu ko tantama Yoohan yace, “Inhar zan sani ɗin ta wannan hanyar zan biya ko nawane na shiga addinin naku dan na sani, dan na tabbatar idan ban sani ɗinba natsuwa zata cigaba da yin nisa da ni har abada”.
“UBANGIJI kai ne gagara misali a tunanin hankali ko hasashen zuciya. Tabbas kai mai ikone ga wanda kaso, a kuma lokacin da kaso. Yahya shiga addinin musilinci ba’a biyan ko sisi. *_ALLAH maɗaukakin sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda zai taimaka
musu na arzikinsa, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“Kuma ban halicci aljan da mutum ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana bukatar da su ciyar da ni. Lalle ALLAH shi ne kaɗai mai azurtawa kuma ma’abocin karfi sosai”._ Suratuz Zariyat, aya ta:56-58.
*_Mutum a halittar da ALLAH ya yi masa zai bautawa ALLAH ne shi kaɗai inda za’a bar shi, ya zama mai son ALLAH ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya
ɓata wannan (dabi’ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin sheɗanun aljanu da na mutane su ke ƙawata mata na abinda sashin su yake yi wa sashi wahayi na ƙawatacciyar Magana kawai don ruɗi, shirka wata aba ce da ta zo daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da ALLAH
ya yi wa mutum, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“To, ka tsayar da fuskarka ga wannan addini kana mai kaucewa shirka, halittar ALLAH wacce ya halicci mutane a kan ta, babu mai canza halittar ALLAH”._ Suratur Rum, aya ta: 30.
*Kuma Ma’aikin ALLAH (S.W.A) ya ce: “Dukkan abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi”. Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.*
Dan haka Yahya UBANGIJI baya buƙatar ko sisi da ga gareka face amsa kalmar *_La’ilaha illallah……._*”.
Sosai abin ya bama Yoohan mamaki da wannan bayani na baba malam. dan haka ya gyaɗa kansa yana mai gyara tsaywarsa da faɗin, “Na shirya amsar wannan kalma Uncle”.
Murmushi sosai ya sake faɗaɗa a fuskar baba malam, batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannun Yoohan sukabi ta ƙaramar ƙofa zuwa cikin gida. Abban su Abdallah na biye da su zuciyarsa fal tunanin inda ya taɓa sanin mai kama da Yoohan ɗin a wasu shekarun baya..
Sashen mahaifinsu kai tsaye suka nufa, ko ina fes yake dan ana gyarawa saboda sukan zauna a ciki musamman randa sukaso nishaɗi. Duk hidimar bikin salla ma jiya a ciki sukayita su huɗun. Sai da duk suka zauna, Yoohan da Abban Abdallah kowa nama ɗan uwansa kallon sani baba malam ya katsesu da faɗin.
*_“Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Muhammadu MANZON ALLAH ne”_*.
_“Waannan kalmomin shahada guda biyu, sune ƙofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka ƙunsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
1-Ma’anar kalmar shahada: Ma’anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da ta ƙunsa, zahiri da baɗini, malamai sun haɗu akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta ko yin aiki da abin da ta ƙunsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kaɗai matsarkaki maɗaukaki.
_Rukunan wannan kalmar (shahada) sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore haƙƙin bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kaɗai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta ƙunshi kafircewa ɗagutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Maɗaukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da nuna masa ƙiyayya da yin kuɓuta daga gare shi._
*_Wanda ya faɗi wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai faɗeta ba. ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ɗaya.
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai jin ƙai”.(Baƙara: 163)._*
*_Kuma Maɗaukaki ya ce: “Babu tilastawa game da (shiga) addinin
(musulunci), haƙiƙa shiriya ta bayyana daga ɓata, saboda haka wanda ya kafirce wa ɗagutu kuma ya yi imani da ALLAH, to haƙiƙa ya riƙi igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masanine”._* (Baƙara: 256)
_Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya ƙudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko wanda yake da ikon ƙirƙira, kuma ya ƙudurci cewa yin
imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kaɗaita ALLAH da ibada ba, to haƙika faɗin kalmar (La Ilaha
Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya._
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ka ce (da su): “Wane ne yake arzuta ku daga sama da ƙasa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al’amura?” To za su ce: “ALLAH ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?”
(Yunus: 31).
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ko wane ne ya halicci sammai da ƙassai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki
masu ƙayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da ALLAH, A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)”. (Naml: 60)._*
Kuma ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wanene ya halicce su?, Lallai za su ce: “ALLAH ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?” (Zukhruf: 87).

*_“Ma’anar Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_Ma’anar shaidawa lallai (Annabi) Muhammadu
MANZON ALLAH ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da
labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a kansa, kuma ba za a bautawa ALLAH ba sai da abin da ya
shar’anta._
*_Tabbatar Da Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_ MANZON ALLAH ne: Shaidawa lallai (Annabi) Muhammdu Manzon
ALLAH ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken yaƙinin cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawan ALLAH ne, kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ɗayansu, kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin ALLAH ba shi da komai daga siffofin ALLAH, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar
sunnarsa a baki, a aikace, kuma a ƙudurce._
*_ALLAH ya ce: “Ka ce: ya ku mutane lallai ni MANZON ALLAH ne
zuwa gare ku gaba ɗaya” (A’araf: 158). _*
_Kuma ya ce: “Ba mu kuma aiko ka ba face zuwa ga mutane baki ɗaya, kana mai gargaɗi da bushara” (Saba’a: 28)._
_Kuma ya ce: “(Annabi) Muhammadu bai kasance uban ɗaya
daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon ALLAH ne kuma cikamakin Annabawa” (Ahzab: 40)._
_Kuma ya ce: “Ka ce tsarki ya tabbata ga Ua
UBANGIJINA, ni ba
kowa ba ne face mutum kuma Manzo” (Isra’i : 93)._
Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi Muhammadu Manzon ALLAH) ya ƙunshi al’amura kamar
haka:
Na farko: yarda da Manzoncinsa da ƙudurceshi a ɓoye cikin zuci.
Na biyu: yin furuci da haka da harshe a bayyane.
Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na ƙarya.
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Sai ku yi imani da ALLAH da Manzonsa, Annabi Ummiyyi¹, wanda yake imani da ALLAH da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya” (A’araf:
158)._*
Na huɗu: gaskatashi a kan dukkan abin da ya ba da labarinsa.
Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da dukiyarsa da ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya; domin shi MANZON ALLAH ne, kuma haƙiƙa sonsa yana daga cikin son ALLAH, da so saboda ALLAH Haƙiƙanin son MANZON ALLAH shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa da
taimakonsa da jibintarsa.
*_ALLAH ya ce: “Ka ce: idan kun kasance kuna son ALLAH, to ku bi
ni, sai ALLAH ya so ku, ya kuma gafarta muku” (Ali Imran: 31)._*
Kuma ANNABI tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: “Ɗayanku ba ya zama mumini har sai ya soni fiye da mahaifinsa da ɗansa da mutane gaba ɗaya” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas ALLAH ya yarda da shi.
*Kuma Allah Maɗaukaki ya ce: “Saboda haka waɗanda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma
bi hasken da aka saukar a tare da shi, to waɗannan su ne marabauta” (A’araf: 157).*
Na shida: Ƙudurce cewa sunnarsa asali ce ga shari’ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Alƙur’ni mai girma take (wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a saɓa mata domin hankali ya ci karo da ita.
Na bakwai: yin aiki da sunnarsa da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da miƙa wuya zuwa
gare shi, da yin hukunci da shari’arsa da yarda da ita.
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Na rantse da girman UBANGIJINKA ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami
wata ƙunci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma miƙa wuya gaba ɗaya” (Nisa’: 65)._*……………

About Godswill

Check Also

AUREN FANSA Page 41 to 50

AUREN FANSA Page 41 to 50 Mairo Gafai Allah ya baki lafiya yasa anyi a …

Advertisements