UWAR MIJINA Page 51 to 60 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / UWAR MIJINA Page 51 to 60

UWAR MIJINA Page 51 to 60

UWAR MIJINA Page 51 to 60

     Cikin mamaki itama tatashi tana bin bayan shi tana mai mgana cikin harshen Turanci,ammh yayi mata banza,sai ma tafiyarsa dayake kamar ma baisan da halitta wata tana binsa ba,abunda yafi daure mata kai shine yana tafiya yana dafe kai alamar dai tabbas ahashashenta yakusa zama gaskiya kenan.
  Gajiya tayi da binsa ta tsaya cak tana binsa da kallo,agaban idonta ya shige hotel ko waigowa baiyi ba,abun ya shiga bata mamaki tafara tambayanta Who iz he? bata da wannan amsan,cikin mutuwan jiki takoma wajen motarta tayimata key ta shiga tajata tafice daga wajen ranta baya mata dadi,ammh tasaka aranta komai ye game da wannan mutumin sai ta sanshi,tana ji ajikinta wani gagarumin abu ne ke damunsa kuma ayadda ta lura kamar yana fama da mtsalan Rashin lafiya ne,ciwon ne dai haryanzu bata tantance wanne ne ba daga ciki.
    Tana wannan Tunanin ta iso ga wani babban gida Mai bisa ma”ana Upstair ne gidan,kuma da dutse akayi shi,gidane nagani na fada wanda tsayawa misalinshi sai na gama wannan page din bangama ba,hon tayi wani balarabe yazo ya budemata get din yana gaisheta cikin harshen larabci.
Jikinta asanyaye tayi parking motarta cikin parking space,ta fito hannuta rike da jakarta tana tafiya cikin rashin kuzari,mahaifinta dake chan sama zaune cikin wasu kujerun alfarma ,dattajine wanda akallah zai ba shekaru 65 da biyar baya ammh hutu da kuma kudi su suka boye shekarunsa,ammh Fuskarsa tana cike da farin gashi, ya kuramata ido cikin Siririn Farin gilashin dake sanye cikin idanunsa,yana hango tsantsan damuwa atare da ita,ganin haka ne yasashi mikewa ya tattara takardun gabansa ya bude wata kofa wacce zata sadashi da cikin gida.
  Da sallama ta shiga falon kafin ta wurga jakarta kan kujera tafada tana runtse ido,Muhammed dake zaune kan daya daga cikin kujerun falon yana latsa waya ya waigo yana kallonta kan ya tabe baki yana fadin”Ke wai meyasa baki da Natsuwa ne? kullum kina girma ammh kina cin kasa..”yafada cikin harshen larabci,dagowa tayi tana bankamai harara kafin tace”Eh din ina ruwanka da rashin Natsuwata..”tafada itama cikin harshen larabci.
  Ransa ne yabaci tuni ya mike yana wuci ya nufota ganin haka yasa ta mike da gudu zata gudu,sai ji tayi taci karo da mutum tana dagowa Tace”ABBIE..”Da karfi kan ta makalkalesa tana fadin”Abbie kaga Mooh ko..”Riketa Abbie yayi yana kallon Namijin yace”Ai kai ne babban banza,kaida yakamata ka ijiye iyali ammah baka da aiki sai hayaniya da kanwarka..”yafada shima cikin harshen larabci.
  Tura baki yayi yana fadin”To ammh Abbie ku bakwa ganin yadda yarinyarnan Tabi ta rainani ne.”Kai ka raina kanka..”Abbie ya bashi amsa yana jan hannun  lubna suka karisa kan kujera  falon yana fadin”Dr meya faru ne,naga kin dawo ranki bace..”gyara zama tayi tana ruko hannunsa take fadin”Abbie ina mutuminnan dana baka lbrin shi jiya..”?tafada tana kallonsa gyadamata kai yayi yana fadin”eh naji meyafaru dashi..?
  Gyara zama tayi tashiga rattafamai abunda yafaru takara da cewa”Allah Abbie Yana bani tsausayi sai danaji Shima musulmi ne irinmu sai naji inason jin wani abu game dashi,ammh yaki bani dama”Tafada cikin Nuna alamun damuwa.
  “Ke lubna bazaki kiyayi kanki da jajaye ba ko,watarana sai kin sai da kanki da kanki..”wata farar mata doguwa ta fada wacce ta fito hannunta dauke da wasu mulmulayen kulolin abinci tana jerawa bisa wani katon tebur din cin abinci mai kama da na liyafan Larabawa,Tabe baki mooh yayi yana fadin”Barta mom Allah yabata sa”a yarinyar nan shigen rawan kai da shisshigi, ina ruwanki da wani,mutum ki barsa mana ammh saboda bala”in ta sai ta yi makanta jajaye”Yafada cikin nuna abun ya isheshi Tura baki Lubna tayi tana fadin’Allah mom don baki gansa bane,Sai yabaki tsausayi..infact ma ni abunda yasa nakeson Taimakamai kamar yanada problem da irin aikina ne dat why”Harara ya bankamata kan yace’ehye yanzu zaki ce yana da alaka da aikin ki mudai kada ki kwasomana wata Annoba gida am telling u…”
“Gaskiya kam..”mom tafada mirmishi dattijon yayi yana riko hannunta yace”Don”t mind them by dota,ki taimkama mai indai ya baki dama,ni na Amince ko nan gidan ne,ki kawosa muji miye lbrinsa,in munda hanyar taimakonsa Fine,in kuma bamu dashi da baza mu rasa yadda zamuyi ba..”yafada yana kallonta da ihun murna tafada jikinsa tana dariya take Fadin”Shukuran Laka ya Abbie…’taketa fada tana ma mooh gwalo wanda yacika yayi tsab kamar zai fashe tabe baki mom tayi tayi ficewarta afalon inda sabo sun saba da halin Lubna da Abbieta wajen shigen jajaye su kowa nasu ne.
Gwarin gwiwan da Abbie yabama lubna shiya karamata karfin gwiwa cigaba da bibiyar mu”azzam sai dai kash inta isa wajen banda sallamanta Dayake amswa baya kara ko kallonta balle tasan ran zai mata mgana,kuma kullum cikin Hotel din take ganin yana shiga kenan shi bako ne zuwa yayi? daya ga alamar tafara takuramai sai ya chanza wajen zama,ammh duk da haka sai ta nemoshi,shiyasa yanzu ya daina zuwa ma kwata kwata ya gwammace yayi zamansa adaki,saboda bayason kowa ya rabeshi shine dalilinsa na barowansa gida,abunda ya lura dashi yarinya so take ta shiga rayuwarshi da karfi da yaji,shikuma abunda bazai yarda dashi ba kenan,babu wata mace datake burgesa afadin Duniyar bayan Hiransa shiyasa ko alama baijin zai ba wata Fuska harta shigo rayuwarsa.
***************
   *MAID*
    Rana bata karya sai dai uwardiya taji kunya ayau ne bayan ansauko daga sallae jumma”a dubban mutane suka shaida Daurin Auren ZAHIRAH ABUBAKAR BAHGANA DA ANGONTA ALH KABIRU BAKANO* Akan Sadaki aure Naira dubu dari lakadan ba ajalan ba.
  Bakin bukar yaki rufuwa shida angon wanda yasha babba riga da hula shima bakinan yaki Rufuwa,mutane dadama sunga wautar Bukar da irin wannan gaggawan dayayi na aurar da diyarsa tana shayarwa ai da komai miye daya bari ta yaye,ko kuma suyi shekara lokacin sunyi kwari ammh yaki dole shi sai an daura aure,in madaga baya zata tare to babu damuwa,hatta yan”uwanshi sun nuna rashin amincewarsu sunce abari zahirah ta yaye yaranta tukunna ammh sai bukar ya kawo musu Alh kabiru har gida yazo yana rokonsu dasu  taimaka adauran Auren haka tunda addini bai haramta ba,shi ma uba yake ga yaranta wlh matukar ubansu zai barmai su zai rikesu har illa masha Allah,to ganin girmansa tunda ba yaro bane yasa suka amince aka daura aure daga baya zata tare.
Ammh mutane sun kasa gane haka,suna ta zunden cewa kwadayi ne yakai bukar din to inba hakaba,saurin meyakeyi,wasu harcewa suke haka zai kare wajen kwadayi,auren da yayimata na farko,shima kwadayin yabi ammh ba”a kai ko”ina ba aka sakomai yarsa da ciki,to gawani ya sake yimata ko dandara baiyi ba,wasu harsuna cewa zaiyi hankali in wannan karan yaji lbrin anyi kudi da kan yarsa tukunnah,kuma duk masu wannan gulman,wasu daga cikin yan”uwansa ne,dakuma wasu daga ciki  lalatattun makota marasa tsoron Allah.
*WANENE ALH KABIRU BAKANO*
Alh kabir bakano haifaffan garin kano ne gaba da bayansa,aiki ne yakawosa maiduguri Shine manajan dayake rikeda babban gidan Nepa dake maiduguri,yana da tarin arziki matuka don mahaifinshi ya mutu yabarmai tarin dukiya daga shi sai mahaifiyarsa wacce suke cema inna,Alh kabiru ba yaro bane,don ko bukar zai girmemai kadan ne,shekaransa ashirin da auren Yagana wacce itama yar asalin maidugurince tun Sadda yafara aiki achan suka hadu ya aureta,tun da kuma ya aureta Ko batan wata bata taba yi ba,Hakika mahaifiyarsa inna tana bukatar ganin Jikokinta ma”ana ya”yan danta ammh kuma abu shuru,dole yasa ta shiga nema mai aure,tunda shiko ance yanema baya nema,Inna da kanta nema mai auren wata budurwan anan kanon ammh abun ban haushi yarinyar ko wata shida batayi ba ta gudo daga maiduguri tacema iyayyanta baxata iya ba dole suka raba auren,na biyu ma data nema mai bazawara ita ko tarewa ma batayi ba ya saketa na uku kuma satinta uku ya saketa tadawo gida ganin abunda yakeyi ne yasa ko inna taje neman mai Aure ake hanashi saboda dabi”ansa na auri saki,tu tana fadan hartagaji ta zubama sarautar Allah ido taci gaba damai addu’a.
  Duk abunda ke faruwa matarsa yagana ne ke asssashi,yagana macece mai kishi da son abun duniya tana matukar son mijinta kabiru shiyasa bata kaunar wata mace ta rabeshi koda uwarsa ne,itace ta lalata aurensa na farko na biyun ma ita ta mata asirin tabar gida shikenan kuma sanadiyar barinta gidan,na ukun kuma ita da kanta ta umarceshi daya saketa saboda yadda ta asirceshi sai abunda takeso yakeyi jiki ko na rawa ya saketa,to tundaga lokacin ta kafeshi ta tare gaba tatare baya,ko mganar aure kabiru bayaso amai saboda yadda yagana ta mike tsaye da shiga malamai.
Alh kabiru aboki ne ga bukar wanda sun dade suna tare tunkan auren zahirah na farko duk abunda yafaru yasani, tunda bukar na fadamai,mutuwar aurenta da haihuwarta duk yasani,Alh kabiru saboda addu”an Da inna kemai yasa yafara dawowa cikin hayyacinsa yaji shima yana sha”awar yayi aure har shima ya haihu,shiyasa tunda bukar yabashi lbrin zahirah shikenan yaji komai ya tsayamai,kwadayin samun zuru”a da ita yasa yayima bukar zencen Aurenta in ya Amince,Bukar babu yarda zaiyi domin Kabirun yanada wani mtsayin agunshi,na wanda bazai iya neman abu agunshi yahanasa ba,shiyasa ya amince da batun nasa,yaso yabari ta yaye yaran ammh Alh kabirun ya mtsa sai anyi yanzu saboda kwadayin yaran da za”a kaimai gidansa ko bakomai yau shima zaiji wani dadi matukar yashigo gidansa yaji kukan jarirai,yagana batasan da wannan auren ba,inna ce kadai ta sani wacce tayi rawa tayi juyi sai dai ita ta kwabeshi da karya fadama yagana komai tukunah sai in Lokacin Tarewan yayi.
Adaren Ranar da”aka Dauran auren bukar ya shiga har dakin zahirah ya yimata nasiha bayan ya damkamata sadakinta ahannunta,saboda rudewa  Zahirah sulalewa kawai tayi akasa tana kuka,aure kuma? takai wadan nan yaran ina? wayyo ta shiga uku kenan ya tabbata rabuwarta da mu”azzam ya tabbata,har bahna din nata yafice bata sani ba saboda yadda take kuka,yana fita tatashi da dauko little Ummi da moodu ta rumgume tana kuka tana fadin”Shikenan anmin katangar karfe da Abbanku,wayyo nikaina,wlh bazan iya zaman aure da kowa sai kai ya mu”azzam”Haka taketa fada tana kuka,maghana ne ta shigo ta sameta awannan halin ita ta zauna ta dinga lallashinta tana fadin
  “Kibar kuka yahna,halin dakika shiga shiyasa tadama mahaifinki da hankali,don Allah zahirah ki donne zuciyarki kiyima Bahna dinki biyayyah ko hankalinsa zai kwanta,mu’azzam kuma ko kin zauna aure fa ya kare atsakaninku dole ne ko kina so ko baki so sai kinyi wani auren”tafada da sigar lallashi.
  Dago kai zahirah tayi idanunta na zubar da kwallah tace”to sai ayimin aure mahgana da danyen jego,ina shayarwa,kamar an gaji dani,ai abari na yayesu ko in Abbansu ya karbesu lokacin bani da wani Nauyi akaina,yanzu ko damai zanji da hidimar miji ko na ya”ya wanda kusan hakan ma mtsala ne..”Dafata maghna tayi tana fadin”Karki damu da wannan shi yaji yagani,yace dakeda yaran yake bukata,kiyi hakuri ki tashi kije kibawa bahna dinki hakuri ki kuma fadamai kin amince da zabin dayayi miki..”Jin haka yasa zahirah mikewa ta share hawayenta ta fice zuwa dakin bahna dinta,wanda tasamu yana ta safa da marwa cikin damuwa,ta shigo dakin zuwa kawai tayi ta rumgumesa tana fadin’Kayi hakuri bahna wlh na amince da zabinka gareni dam…”Shiiiii…”Yafada yana juyo da ita bayan yasaka dan yatsa abakinta yake fadin”Nasani Yahna abun da ciwo ammh to ya zamuyi sai hakuri ki rumgumi kaddaranki Haka Allah yaso ya ga rayuwarki ta tafi,tashi kije ki kwanta ki kula da ya’yanki Allah ya cigaba da dafama rayuwarki har abada.,Da Amin ta amsa bayan ya sharemata hawaye ya rakota har daki kafin yamata sallama yakoma dakinsa fuskarsa tana bayyanar da farincikinsa.
   Mahgana dake gefe tashare hawayenta tana mai jin Farinciki koba komai tana tsausayin zahirah da mahaifinta saboda sunga jarabtar rayuwa,Ranar kwana kuka zahirah tayi kamar ta zare,kuma haka ta kwana tana kiran layin mu”azzam ammh amsa daya ne akashe layin yake dole ta hakura ta shiga da kuka tana rumgume da yan diyanta tana kukan musu maraicin dasukayi dukkansu.
_______________
*SUDAN*
Yau kimanin kwana hudu kenan tana zuwa wajen bata ganinsa,ta shiga damuwa matuka,kuma babu yarda zatayi ta shiga Hotel din saboda dokace,sai in kanada tiket wanda yakama daki kadai awajen yakeda sai dai inzaka shiga shi ya Nuna kushiga tare,Ranta babu dadi yau dinma shiyasa bata dade ba,ta mike tana shirin tafiya kamar amafarki ta ganshi yana tahowa cikin wani yanayi yadda takaremai kallo sai taga ya rameta a ido,kuma inba idonta gizo yake mata ba hada hanya yake yana cije baki,alamar dakyar yake Tafiyan.
  Wajen daya saba zama yaje ya zauna,wannan karon tsakanin kafafunsa ya tura kansa,ganin haka yasa tayi azaman karisawa, wajen tanamai sallama kamar kullum,yanajin muryanta yaki dagowa,yana mamakin naci irin na yarinyarnan,duk irin wukalancin dayake mata taki barinsa ya huta,saboda ita ya dauke kafa daga wajen ammh kuma duk da hakan bai tsira ba,dole ne yau ya chanza masauki inda bazata kara ganinsa ba.
  Dagowa yayi batare daya kalleta ba ya mike, yafara tafiya yana tangali ganin haka yasa ta bishi tana fadin,”Don Allah ka tsaya baka ganin kana neman Faduwa ne..”Tafada cikin harshen Turanci,ko waigowa baiyi ba ganin haka yasa tazura da gudu tasha gabanshi tana fadin”Plz Allow me to help u…”Tafada tana hada hannayenta waje daya.
Ransa ne yabaci ya dago Afusace ya saka hannu ya tureta tayi baya tafadi dabams,wanda sai da kugunta ya amsa yafara mgana cikin Fushi, cikin haddaden Turancinsa”Ki rabu dani mana,ana dole ne? kin dameni kin takurama rayuwata, as from today don’t ever Talk to me again”yafada daidai lokacin da tari ya sarkeshi kan kace kwabo jini yafara biyo hancinsa da bakinsa,itako suman zaune tayi tana kallonsa cikin mamaki,yadda yake Turanci lalle hasashenta yazama gaskiya,duk da chan babu ruwan wani da wani ammh har anfara taruwa ganin yadda ya duke yana taro jini ahannusa,cikin galabaita da ciwo yayi kokarin cigaba da tafiya ammh taku kadan yayi ya rike kansa dayake juyamai kafin kace me ya zube kasa warwarsa babu ko Numfashi.
  Dawani gudu lubna ta mike ta isa garesa tana jijjigasa,lokacin da jama”an dake waje suka shiga kiran sunan Allah suna Fadin”Ya Allahu..Ya subhannallahi..”kuka lubana take cikin Tashin hankali take neman Taimako,wasu larabawa ne,suka taimakata suka sakamata shi abayan motarta Ta shiga taja da wani gudu tana tuki tana waigensa daga baya tana share kwallah,.
Wayarta ta jawo ta  latsa wasu lambobi takara akunni tana fadin”DR SULTAN am coming wit a Hartfailure Patient..”tafada lokaci daya ta waigen mu”azzam dake baya hancinsa na cigaba da zuban jini,ko alamar Numfashi babu Atare da shi.
  Daga chan bangaren Dr.Sultan ya amsa dace”Ok madam..”
  *DON”T FORGET TO VOTE, COMMENT AND SHARE*
        _*Jameelatomar*_
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
_*GIFT TO:Hussain80k*_
*Intelligent writer’s Asso*✏
_*wannan Shafin sadaukarwane,gareki,BILLY S FARI..,Ina matukar godiya da yadda kike bibiyan Littafin Uwar mijinah!Janafy relli Appreciate*_
*NOT EDITED*💥
                *NO 30*
   _#Nadama_
   Cikin Abunda baifi minti goma ba, tashigo cikin wani haraban makeken Asibiti mai dauke da hawa hawan bene na gani na fada,katon Asibitine daya kusa kama dawata anguwa saboda girmansa,specialist hopital ne mallakin gwannatin kasar ne,tana kula dashi Ainun kuma duk yawancin likitocinta baki ne,daga yan india sai yan US Ameriaca,Da sauransu kalilan ne xaka ci karo da laraba,domin kowani jinsi akwaishi acikin Asibitin.
    Cikin wani Sauri ta paka motar lokaci daya tayi waje da gudu tana kiran Nurses da gudu take tanayi tana haki kamar bata cikin hayyacinta da gudu kuwa suka fito dauke dawani, dan gado na daukan marasa lafiya,tana ganinsu takoma da baya suka biyota,ganin yadda Dr lubna taje arude yasa suke komai cikin kuzari,ita ta budemusu bayan mota suka Fito dashi,dayake akwai maza cikin azama suka dorasa akai suna gungurasa zuwa cikin Asibitin.
   Suna gabda isa emargency ne Dr Sultan ya fito,Sukaci karo da Dr Lubna tana ganinsa tace”yauwa Dr,plz help me..”Tafada tana nunamai mu”azzam da”ake gungurowa cikin jini baya ko motsi cikin tashin hankali Dr Sultan yake kara gungurasa yana fadin”Oh my god mah,dis is a Serious problem,ya Allah..”yafada cikin zafin nama yana turasa da karfi,ganin haka yasa sauran likitocin dake wajen suka bisu da gudu suna dafe kai ganin yadda mu”azzam din ke zubar da jini ta baki ta hanci da Sauri suka shiga dashi cikin emargency wanda Nurses din dake biye dasu suka ci burki suko sauran likitocin suka dumguma ciki lokaci daya kofar glass din ta kulle kanta.
   Suna shiga dashi ciki suka ciccibesa suka dora bisa Ainihin gadon dayake dakin,suka fara jona jonan Na”urori bisa jikinshi cikin hanzari kowanne yasaka hand glob,Dr lubna ma cikin zafin nama take kokarin Tsaida jinin dake zuba lokaci daya Dr Sultan ke kokarin dawo da Numfashinsa,ammh abu ya ci Tura jinin ma yaki tsayawa,kuma kokarin nemo Numfashin nasa ma yaki yuyuwa,Nu”urori sai kuka suke,ganin haka yasa Dr lubna cire safar hannunta ta fice daga wajen hankalinta atashe.
  Office dinta taje ta kifa kanta jikin Tebur haka kurum taji hawaye na bin kumatunta,bata sanshi ba,bata da wata akala dashi ammh lokaci daya zuciyarta ta Aminta dashi, taimakamasa Ashe Ashe yana cikin wani hali?halin Ciwon zuciya,Tsausayinshi takeji bata Fatan ya mutu,tafi so Asamu Numfashinsa ko zataji Kadan daga Tarihinsa,kafin kace me Dr lubna takece da kukan Tsausayin mu”azzam kamar ance mata uwarta ta mutu sai da tayi ma”ishi kafin tafada Toilet ta wanke idonta.
  Awa uku suka shafe aciki kafin su samu nasarar daidata komai Numfashinsa yadawo dakyar ammh bayan Sunyi Nasarar Tsaida jininsa dake zuba,Ganin yadda jininsa yayi kasa yana bukatar karin jini cikin Minti Talatin in ba hakaba akwai mtsala,yasa Dr Sultan Fita da Sauri ya isa ga office din Dr lubna.
  Abunda yabashi mamaki ganinta tsaye tana kaida kawo hankalinta atashe ga idanunta sun kumbura alaman Tasha kuka,kallo daya yayi mata ya Fahimci tayi kuka,tana ganin Shigowarsa tanufesa tana fadin”Dr, how is he..? Hop he survive? ajiyar zuciya ya sauke yana kafeta da manyan idanunsa yace”Alhamdulillah,evertin Is normal By Now,but jininsa yayi Low fa yana bukatar karin jini yanzu bada dadewa ba”
  Saurin yin gaba tayi tana fadin”i belong to group O BLOOD..Muje ayi Taking nawa a sakamai Dr,plz bani so mu rasa wannan patient din”Tafada cikin damuwa,ganin yadda tarude ne yasa yakasa yimata gaddama kawai sai yabita suka nufi lab din,ammh tambayoyi fal aransa,akan Dr lubna da wannan Sabon Patient din data kawo musu.
     Leda biyu aka diba nata aka sanyamai cikin lokaci kadan jinin yafara gauraya da jikinsa,wasu manyan Allurai sukamai na Samun Hutu,kafin su kaisa wani daki na mussaman,Sai dai ajira Farfadowansa,itakuma lubna an bata hutu ne saboda an dibi jinin nata da dan yawa,har leda biyu,Dr,sultan ke tare da ita,yana kula da ita,Tunda shi haka Allah yaso dashi SON WACCE BATA SONSHI.
    Ita gabadaya batama ta Dr Sultan, dakefaman kula da ita,hankalinta na ga mu”azzam lokaci daya takejin wani yanayin game da mutumin,batasan Dalili ba ammh tanajin wani abu game dashi wanda batasan dalili ba,ammh tafi dorashi amizanin Tsausayi,.
  Abbie ne yajita shuru bata dawo ba shine yakirata,cikin damuwa lubna ke fadamai Abunda kefaruwa,matukar tsausayawa Abbie ya tsausaya yayi mata fatan Samun Nasara,kuma ya jinjinamata bisa halinta na son Taimakon mutane,Sunyi sallama akan sai gobe zata dawo yanzu dare yayi bazata iya yin Driving ba,Koda Abbie yake fadama mom abunda lubna tace yana fadamusu lbrin mutumin databasu Tsaki mooh yaja,wanda ke zaune falo yana latsan waya ita kanta mom din baki ta tabe,suna jin Haushin Lubna da shegen jajaye,Abbie bai wani damu ba,don kaf hallayan lubna nashine.
      Kwana uku Mu”azzam ya shafe cikin halin Suma,kafin ya farfado,koda ya farfado da lubna yafaracin karo wacce tun bayan kawo asibitin taketa kula dashi,sosai bata da wani sukuni kullum zullumi take da tunanin Farkawansa,bayan ya farka Dr Sultan ya duddubasa yaga komai Normal sai dai zai cigaba da karban mgani kuma zasu dan rikesa na wani lokaci kafin komai ya daidaita.
   Lokacin dayaci karo da lubna,ransa yabaci yana tunanin yaushe har ya yarda ya takawosa nan,Ransa kwata kwata babu dadi,yaso tabarshi ya mutu wla chan yafiyemai nan,ko ba bakomai zai huta da rikitarikin dake cikin Duniyarnan,Koda ya farka din Dr.Lubna tayi mganar Duniya ammh ko tak mu”azzam baice mata ba,Tayi ta mai Sannu da jiki da tambayan Sunansa ammh ko kallo bata isheshi ba,baima nuna yagane dashi take ba,magugunansa kuwa sai dai Dr.Sultan yabashi ammh in itane bazai taba amsa ba,Abun na matukar bata mamaki da daure kai ammh ganin condition din dayake ciki,yasa take mai Uzuri take binsa a hankali in tayi lura da yanayin mtsalarsa kila wani abu akayimai wanda yayi sanadiyar shigansa,halin dayake ciki.
  Dr.Sultan Balarabene, Cikakke mazaunin Madina,aiki ne shima ya kawoshi Sudan din,yahadu Da Dr lubna wanda ya kasance abu daya suka karanta wato abunda yashafi zuciya kuma suna yawan aiki tare,Dr Sultan dogo ne fari,kyakyawan gaske mai dauke da manyan idanuwa da dogon hanci,kota ko”ina baida makusa,tun da Allah yasa ya dora idonsa kan Lubna yaji duk duniya ba wacce yake so irinta,tun yana boyewa har ya bayyanamata,ammh Lubna taki bashi dama,bawai don bata sonshi ba,sai don ita tsarinshi kwata kwata baimata ba,infact ma batason Auren balarabe.
   Lokacin daya ga yadda lubna ta rude kan halin da mu”azzam ke ciki yasa yafara dora ayyar tambaya akanta,ammh daya tambayeta meye alakanta dashi,sai tace mai cousin Dinta ne yazo daga Nageria,bata sani bafa karya kawai ta yankamai,ammh abunda yasa yaki yarda da ita ganin ko dan”uwata ko daya bai gani ba,kuma ga yanayin yadda mu”azzam ke tafiyar da ita,sai yafara tunanin wani abu dabam,duk bin diddiginsa lubna ta toshe hanyar da zai Fahimci bawata alaka tsakaninta da mutumin dako Sunanshi bata sani ba.
____________________
*NAGERIA*
    Shirye shirye ne keta gudana takowani bangare,mussaman Alhaji kabiru dayaketa rawan jiki,tuni yafara gyaran shashen da xahira zata zauna,wanda yadaga Hankalin yagana,wanda Tana tambayarsa dalilin gyara yafadamata amaryace zata tare..Bala”i😨😰Haka yagana tafada domin abun yazomata abazata,ada taso tayimai borine sai kuma tafasa,domin tana son taji wata mai karar kwanan ne take kokarin keta mata gona.
   Lokacin dayake fadamata an Daura aure tarewane amaryan zatayi kadan yarage yagana bata Fadi Asume ba,bata kara tsinkewa da lamarin na Alhaji ba,sai da yake bata lbrin zahirah da dalilin dayasa yake kwadayin Aurenta,kutumar ubanchan inji yagana,wato Mai ya”ya ya auro ko? wato ita bibbiyu ma take haifa,lalle akwai babban tarzoma don wallahi ita bata haihu da Alhaji ba,to billahil azim babu maccen data isa ta haihu dashi,dukiyar Alhaji natane ita kadai,saboda haka koma wata mai karan kwanan ne,tazo itace zata zama ajalinta daga ita har ya”yan nata dayake murnan zuwansu,don taga in ba tafara aikasu lahira bane,Alhaji da uwarsa bazasu barta ta huta ba,..Topha.😥
****************
  Tabarayin Zahirah ko bata samu lbrin barin mu”azzam gida ba,sai daga bakin yakura fadar irin tashin hankali da damuwa da zahirah ta shiga bata lokaci ne,Mikewa tayi dafe da kirji little Ummi na kan jikinta ta saketa ba don yakura tayi saurin Riketa ba data fado kasa,hawaye kawai ke kwararamata tana maimata”Ya mu”azzam yatafi fa kikace yakura? yatafi ya bar ummi,wayyo ni zahirah duk adalilinKi Ummi komai ke Faruwa gashi yau babu mu”azzam tare dake,wlh Ina matukar Tsausayama kaina ammh wlh yakura Nafi Tsausayama Ummi matuka,ni nasan son Da Ummi takema ya mu”azzam Rasasa tamkar rasa wani shashe na rayuwarta ne..”.
   tafada bayan ta sulale kasa tana kuka yakura tasharbe hawaye tana jijjiga little Ummi datake kananun kuka,tace”Abun ba dadin ji zahirah,Wlh ance duk mai imani yaga halin da Suhaima ke ciki sai ya zubarmata da hawaye,ina amfanin muguwar gaba,wacce batada tushe ballatana makana,yau duk inda tayi hakuri, wlh da duk haka bata faru ba,an bata goma ko daya bata gyaru ba..”dagowa Zahirah tayi cikin hawaye tace”yanzu babu wandan yasan lbrin inda yake,baya da lafiya yakura inajin Tsoro,inajin tsoro kada wani abu ya sameshi,wlh ina sonshi bani son Rashashi gabadaya yakura..”Tafada tana dafe kanta dataji ya sara mata,lallashinta yakura tahauyi da cewa”hakuri zakiyi kinga ko mahaifinki baisan na fadamiki ba nakasa hakuri ne nafada miki ammh ko baffanki ai dalilin ciwonsa kenan,rashin sanin takamamman inda mu”azzam din yake,shikanshi abokin nasa yace ya bincika ko”ina ammh babu lbrinsa yaface yayi nisa da garin ne gabadaya.
  Dafe kumatu Zahirah tayi tana fadin”Hasbunallahu wani’imal wakil,Allah mun godemaka daga wannan Sai wannan”Tafada tana share kwallah kan tamika hannu ta amshi littae Ummi ta ciro nono tafara bata,tana kallonta yadda take tsotsonta da zafi zafi,alamar yunwa takeji Runtse ido,Zahirah tayi wasu hawaye suka zubomata ta furta cikin karayan zuciya”Allah ya bayyanaka ya mu”azzam,duk inda kake ka tuna dani da ya”yanka muna kewaraka bayan mutuwar sonka zai sama abincinmu son ganinka kuma zai zama abun Fata agaremu har karshen Rayuwarmu,Allah ya karemun kai ya mu”azzam aduk inda kake..”Tafada hawayenta na diga bisa Fuskar little Ummi,kamar wacce ko kamar tasan me uwar ke cewa,tasaki nono ta zuramata ido,ana haka sai moodu ya farka shida da kuka,Yakura ne tamiko mata shi tahadasu Ta rumgume tana kuka.
  Yakura dake tsaye tana kallon ikon Allah tace”Kibasu abincinsu,kibar kukanan zahirah..”idanunta na kulle tana hawaye tace”Ba Nono sukema Kuka ba yakura,suma sun ji ajikinsu sunyi maraici,maraicin uba nagartattace,basu da masaniyar samun wani makwafinsa suma suna kukan Rashin mahaifine,nikuma ina kuka RASHIN MASOYI NE..”Tafada cikin wani yanayi..
  Yakura dole tasakai tafice daga dakin saboda yadda tsausayin zahirah ya cikamata ciki,falo takoma suna mgana da mahghana akan tarewar zahirah jibi,wanda take fadamata irin dagan datakeyi da zahirah kan kin cin komai aka bata na gyara jiki,ko na jegon ma bayan tagama kin yi tayi,mahgana tace”Da an mtsamata sai tasaka kuka,wai wazatama gyara,babu ya mu”azzam dinta,ita wlh babu wanda zatama gyara..”Ki jimin yarinya to Ai hakuri zatayi da mu”azzam din yamata nisa,in ma zata saki jiko ta gyara toh,ta gyara don gidan kishiyata zata,wannan karon bata uwar miji bace,ta kishiyace.
  Hakuri kawai yakura ke bata,ko ita haushin ma mahgana taji,to miye nawani bata kayan gyara,Takaicima yahanata zama dole tayi mata sallama ko dakin zahirah bata koma ba, ta fice daga gidan Aranta tana jin kishin Auren nan,duk da saki uku ne,ammh tanajin babu dadi,ko don mu”azzam dayake mutuwar son yarinyar,ammh yazasuyi wannan karon basu da tacewa,don iya alkunya bukar yayi musu shi,wannan karan kuma kiri kiri yake nuna shi ke iko kan yarsa.
    Ana gobe tarewan sai ga dangin Alhaji kabirun wa”inda suka zo daga kano sunzo kawo kayan Akwatu,guda biyar shake da kayan arziki,ankarbesu hannu bibbiyu cikin mutumci da karramawa,sunci sunsha dakuma zasu tafi suka wuce da abun arziki niki niki,suka tafi suna fadin kabiru yagama sa”a duk da sun so ganin amaryan ammh zahirah ta rufe kofar dakinta,tana ciki tana rafzan kuka,tana auna yadda zata rayu dawani Namiji ba ya mu”azzam dinta ba, gaskiya da wuya ta iya yimai biyayyah tsakani har ga Allah, babu wani da Namijin dake burgeta kamar ya mu”azzam shine na farko kuma na karshe,so zata yarda da Auren ne,kawai don bahna dinta ammh har abada zuciyarta yana ga Shi din dai IBRAHIM MU”AZZAM.
Ashe Tun kwana biyu da suka wuce  inna Ashe da mahgana sukaje sukamata jere agidan Alhajin,wanda ko da sukaje yaganar batanan an tafi yawon bin bokaye ba zama,su kadai sukayi jerensu suna yaba tsarin gidan nata,suna fadin Nan ma zahirah tayi sa”a Ammh Allah yasa kada tafadama mtsalar kishiya bayan ta baro ta UWAR MIJI.
  Kaya sabbi Bukar yakara yima zahirah komai sabo,don ya nuna bajintarsa,Tabbas yana bala”in sonta komai ya samu wa ita yake karewa,babban burinsa yaga yawanke duk damuwar dake ranta,yazama tazauna cikinn Farinciki kamar yadda take ada,itako zahirah ko daya ba”a burgeta ba,kallon kowa kawai take,ita ta kanta kawai take da ya”yanta da kuma kwana sallar datakeyi na Allah ya tsare mata mijinta aduk inda yake,..Kiji karfin hali irin na zahirah,ga mijin ki chan,,Alhaji kabiru Nepa😂😂😂
Ko mganar shan kayan gyara mahgana da Innarta Ashe ta hadata, aiko ta sameta tayita mata fada kamar ta daketa,takuma kasa ta tsare sai da cinye kazan da”aka yimata na jego wacce ba”ayi mata ba,sai Fefesun yan shilla,da Hadin gumba wacce ake sha da madara,halin na yan Maiduguri ne domin mahgana tayi su da kanta hakanan don babu yarda zahirah ta iya take sha tana kuka,tana gamawa aka kawo turaren tsugunnne,shima Ashe ta karbe yaran tana fadin”Maza tsugunna,ana nuna miki hanya kina wani kukan iskaci,yo Shi mu”azzam din dakikema kwakwa,bafa zaki koma gidansa ba yarinya tun wuri ki dainama kuka,don gidan Alhaji nan ne gidan zamanki na har abada,ke ko Zuciya baki dashi,uwarsa tasaka yayi miki sakin wulakanci,ammh don jaraba da sakarci kina nan kina kulafuncinsa,kina ta halaka kanshi da yaransa.”
  Tafada harda dungurin zahirah akai suko yaran da harara ta bisu tana dungurar dasu bisa gado tace”Ku koyi zama ku kadai don uwartaku gidan mijinta zata,taje itama tasamu ladan Aure,bawai a iya renonku zata kare ba,Shegun ya”ya masu kama da tsinanniyar kakarsu,ni yaya yakin mun ne,tuni nace ya kawo munsu na dinga dirkamusu madara Allah ke rayawa,ke kuma abarki kici amarcinki “
kona sati uku ne..
Zumbura baki Zahirah tana kuka tace”Ni.wlh bamai rabani da ya”yana,tunda bawani ya haifamin ba,kuma aure ai bance ina so ba,Takurani akayi,kuma wlh tallahi ni babu amarcin da zanci ba zan ci Amanar ya mu”azzam ba..”tafada tana rufzan kuka wiwi..
baki Ashe ta rike kan tayi shewa tace”Ayyiriri Ayyiriri nanaye..Ohni Aishatu yau naga duniya,yo kada Allah yasa kici amanarsa don ubanki,ke in bakici nashi ba yaci naki ai,ke Soyayyah ko?to Soyayyar taci kazan kazanta,sakarya kawai,kinji in kinje ki hanasa kanki,yako turmusheki ya amsa abunsa,tunda kudi ya biya,kuma karki zauna kiyi abunda yadace ni dake shege ka fasa..”Ashe tafadi haka kan Tafice tana masifa ita kadai,Itako zahirah tana tsuguuno kan kaskon Tana hawaye ita kadai,Su little Ummi ko sunyi tsit suna raba ido sukansu sunsan Ashe ba dama.
_________________
   Wanan Zuwan da Shettima yayi da shirin zuwa maiduguri yayi, kara zuwa duba jikin Baffa,dakuma duka yan biyu,domin shine makwafin ubansu,dole Ya kula dasu,hajiya najin haka tace itama zata tunda baxai kwana ba sai su dawo,Ummi dake zaune tana jinsu ta daga ido tana kallon hajiya.Wacce ta waigo ta kalleta kan tace”Suhaima ya akayi ne?tafada tana karisawa kusa da ita,dom yau kwana uku kenan Ummi batayi ma kowa mgana ba,ko mgana kake mata sai dai kallo tana tsiyayyan hawaye.
  muskutawa tayi tana fadin”Za..Zan..zani yaya…”Tafada murya na rawa..Shureim da Hajiya suka zaro ido suka ce”ina..? atare cikin mamaki,sadda kai tayi kan tace “inda zaku..”gyara tsayuwa hajiya tayi tana hamdala aranta kan tace” *MAIDUGURI ZAMU FA..*”
Ummi tadago kanta hawaye suna gangarowa tace”eh cham zani nima yaya,na Sauke nima Nauyin dake kaina,ko abunda ya tsayamin shekara da Shekaru ya wucemun na huta nima…”Tafada tana mai Fashewa da kuka.
*Comment,share and vote*
Nice dai taku jamilaomar, ba Nagudu bace😂ba kuma kuma jut bace,JANAF NIKE.
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
_*GIFT TO:Hussain80k*_
*Intelligent writer’s Asso*✏
_*Congratulation My Anty SIS NAJATEE..,4 ur completing ur Amarxing,special,adorable,fabulous,Fantastics and Educated Novel ZAB’IN RAINA…,Ina rokon Allah yayafemiki kurakuran dake ciki,mukuma yabamu ikon amfana da darussan dake ciki,Kisani ki kara sani UR’S KANWA Love u back and moon*_😘✌
*NOT EDITED*💥
            *NO 31*
   Tun da suka dau hanya Ummi ke rafzan kuka,tsakanin Hajiya da Shureim babu wanda yayi yunkurin lallashinta, domin ya chanchanta data kokan,Ushe ne ke tukasu yayinda Shureim ke muhallin gaba,sukuma hajiya da Ummi na gidan baya,gidan su karime kadai aka bari,bayan hajiya taja kunnansu duk da tasan cewa basu da wata mtsala.
    Dayake Sun taso da wuri wajejen la”asar suka isa maiduguri,Ummi dagowa tayi tana karema garin na maiduguri kallon rabonta da garin Shekaru ashirin da wani abu,duk da garin yadan chanzamata baisa takasa gane wasu wurareba,duk da ansamu chanje chanje dakuma cigaba daga gwamnatocin dasuka gabata.
   Tsayuwar motar kofar gidan Shettima shiyakara rikita Ummi,tacikin motan take karema gidan kallo,duk da gidan yasamu gyara,ba kamar yadda ta sanshi ba,bai hanata Tunawa da abubuwa dadama ba,ciki harda sanda mai taxi ya saukesu ita da moodu da khamis suna gaba tana binsu abaya lokaci daya tasanya hannu tana toshe bakinta saboda kukan daya tahomata kallonta hajiya tayi bayan tafito daga motar tace.
  “Ki Fito Suhaima,nasani zaki Tuna wasu abubuwan,ammh ya mutum zaiyi Rayuwar kenan dama,abunda yabaka dariya watarana shi zai saka kuka..”
  jin haka yasa Ummi yin karfin halin Fitowa tana gyara,Zaman vail din dake jikinta,Shureim dake tsaye yana jiransu shikanshi Ummi ta bashi Tsausayi matuka,ganin yadda Ummi ke bin gidan da kallo tana tsiyayyar hawaye yasa Hajiya zuwa takama hannuta kawai Ta nufi cikin gidan da ita,shiko Ushe umarni Shureim yabasa daya bude booth ya debo kayan abincinsa dake ciki ya shigo dasu.
Yakura tana kichen taji sallamar kamar ta hajiya baraka,Jug ne a hannunta ta diboma baffa ruwa zata bashi magani,ta fito tana fadin”Muryan wa nakeji kamar ta Hajiya bara…”kalamanta sun makalene sakamakom tozali datayi da Ummi wacce ke tsaye tana tsiyayyar hawaye,jug din dake hannun yakura ya subuce yafadi cikin mamaki da al”ajabi ta furta.
  “Su..hai..Ma..”Tafada cikin Rawan baki Da gudu Ummi tasaki hannun Hajiya ta ruga ta isa ga yakura tafada jikinta tana fadin”Nice yakura,kinganni ko,Don Allah ki yafeni Yakura,ba laifi na bane laifin Zuciyatace,dakuma shedan wanda yake tusamin akidar tsanarku wacce bata da tushe ballanta makana,ki yafeni don Allah”
  Yakura data ke ji kamar mafarki take da Sauri Ta rike Ummi tana fadin”Suhaima kece dakanki,kice kike fadin a yafemiki lalle Allah abun godiya..Allah mun gode maka Alhamdulillah..”Tafada hawaye suna zubomata kan takara rumgume Suhaimar suna kukan Tare.
Hajiya tace ganin koken nasu yaki karewa”To mu karisa daga ciki mana,kuka ai yakare,tunda Kin gane gaskiya kuma kinyi nadama..”yakura tace”Tabbas dama mu kullum Fatanmu da addu”anmu gareki kenan”Hannun Ummi taja tana cema su hajiya bismillanku,Shureim sannu da kokari.
  Suna shiga dakin Baffa na zaune bisa katifarsa wacce aka Shimfidamai Atsakar daki dayake jikin yafara sauki,yakan iyama zama a jinginamai da Filulluka,Da murna da Farinciki yakura ke fadin”Mallam tashi yau addu”arka ta cika ga Suhaima tazo gidanka yau”
  Tafada tana jawo Ummi zuwa gaban katifar, jin Abunda Yakura kefadane,yasa Baffa dan zaro ido bakinsa na rawa yake Furta’Su..hai..Ma..Ki yafemun don Allah,wlh hakiinki ke bibiyana haryanzu’ya kareshe hawaye suna bin kuncinsa.
   Ummi ta durkushe gaban Shettima tana fadin”a”a bakai zaka nemi yafiyata ba,nixan nema,yafi kuwa saunawa zaka roka baffa,kullum ciikin aikomin da sakon na yafemaka kakeyi,nikuma na hau dogin zuciya da turban shedan,wanda bai kai ni da komai ba Sai Nadama,Alhalin na manta Allah kadai ke tsara abu kuma yatafi ayyada yaso,Yau dai gani Durkushe agabanka ina mai neman Afuwarka,don Allah kayiman aikin gafara”Tafada tana fashewa da kuka.
  Baffa na hawaye yake fadin”Wlh bakimana komai ba Suhaima,dukkanmu masu laifine,Allah ya yafemana gabadayanmu,yarabamu da aikin danasani..’Yafada cikin Farinciki gabadaya dakin suka amsa da Amin,kafin kuma ashiga gaisawa,lokacin kuma ushe ya shigo da kayan abinci godiya sosai yakura da baffa ke jeramai shureim da addu”an Allah yakara budi.
   Baffa ya kalli Shureim yace”Shikenan kuma babu lbrin mu”azzam haryanzu ko”Baffa yafada cikin jimami,shureim yasaki ajiyar zuciya,kafin yace”wlh baffa bawani lbrin duk inda nake tunanin samun dan”uwa,wlh babu shi babu lbrinsa,sai dai mucigaba da addu”an duk inda yake Allah ya karkato da hankalinsa gida”Dukkansu suka amsa da Amin Ummi ko dukar dakai tayi tana share kwallar idonta,Hajiya da yagana suka kalleta cike da tsausayawa domin itace abun Tsausayi ayanzu.
  Sai gashi nan suka zauna anata maida zence ana jajantama juna,baffa ma dake kwance,bakinsa ya bude sai hira suke da Ummi,suna tuna da,suna takaichin,abunda suka aikata abaya suna fadin dama basuyi haka ba,to daman irin wannan Ranar ake gudu wato Ranar nadama,sallar kawai yatadasu,sukayi suka dawo su xauna Yakura ta dafamusu shinkafa da miya suka zauna sunaci,ana hira cikin farinciki da Annushuwa koba komai Ummi tasamu natsuwar zuciya saboda ta sauke wani nauyi daya tsayamata arai shekara da shakaru akirjinta dayaki wucemata sai yau,data roki gafaran Shettima takeji kamar an Saukemata wani Nauyi.
   La”asar nayi,Suka shirya dukkansu zuwa gidan Bukar,wanda yakura take shaida musu yau ne,ranar da Zahirah zata tare adakin mijinta,Ummi dataji mganar kamar saukan aradu,taji wani yamm,ajikinta ita tarigasu yin gaba saboda kukan daya tasomata,Shureim  kadai aka bari gun Baffa don yace bazai iya zuwa ba,Yaga zahirah za”a kaita gidan wani,koba komai yana taya dan”uwansa kishin zahirah,harga Allah yaji ba dadi,duk dai ko batayi auren ba,yasani ta haramta ga mu”azzam.
    Lokacin da suka isa gidan nasu zahirah ya kachame da yan”uwa da abokam arzuka anata hidima cikin daki kuwa Ashe ne ta takarkare tana ma Zahirah kwalliya tanayi tana masifa tana cewa”ke wai wata irin amaryace babu gyara,ballatanama kwalliya,haka zakijema mijin Fuska kozai kozai,dake, to in zaki mike ki mike wannan karan gidan KISHIYA zaki ba gidan UWAR MIJI BA…”
Tafada tana kokarin sakamata eye shadow runtse ido zahirah tayi Ashe tayi Saurin cewa”Wlh kika kuskura kika zubomin da hawayen banzan nan naki,alqur”an zan ci ubanki adakin nan,bar ganin kina da danyen jego..”tafada tana dugurinta akai,saurin shanye hawayenta tayi saboda tasan halin inna Ashe tsab zata aikata.
  Kamar amafarki takeji muryan wata kamar na Ummi Suna mgana da mutane Afalo,Saurin kwace kanta tayi daga hannu  Ashe ta fice da Sauri ta bar Ashe da masifan cewa”Ke kinyi haukane wai…?take fada,bayan ma tuni zahirah ta fice,wacce ke sanye da wani ubansu Swice less blue yana da ratsin milk colour ajiki,kayan sun amsheta matuka sun mata das dayake ruwan zafin ya amsheta matuka tayi kyau da ita.
  Tana fitowa falo abunda tagani yasata ta daskarewa a tsaye jikinta lokaci daya taji hawaye sun cikomata ido,UMMI ce durkushe gaban,bahna dinta tana,kuka mai cinrai fitowarta yasa falon yayi tsint kallon yadawo gunta,yan”uwan mahaifinta ne,sai hajiyar Shureim,da kuma yakura sai Ummi dake durkushe tana gunjin kuka,Jin shurun yayi yawa ne yasa Ummi kallon barayin da Zahirah take,Nan suka hada ido hudu ana juna,cikin wani yanayi zahirah tahau ja baya idanunta na zubar kwallah,lokaci daya jikinta na rawa juyawa tayi zata koma daki bayan ta saka hannu ta toshe bakinta da kukan dayakeson kubcemata.
  Da Hanzarin Ummi ta mike daga durkushen datayi tana fadin”ina zaki zahirah,kema gujemin zakiyi kamar yadda mu’azzam ya gujemin ya tafi ya barni..”Tafada muryanta ta sarke hawayenta na zuba ta cigaba da cewa”Don Allah don Annabi,kiyi hakuri zahirah,kimin aikin gafara karki gujemim ke kadaice nakeda da ita yanzu wacce zata san dafin dayake damuna azuciyata”Tafada tana durkusa bayan tahada hannuwanta tana kuka take fadin’Naji na yarda ni Suhaima na zama azzaluman Uwa ga mu”azzam,nakuma zama muguwa,mara imani gareki zahirah,kada kiyi duba da mugayen hallayanta,ki juyo ki kalleni kiyiman aikin gafara,wlh natuba nayi Nadama duka abubuwan dana aikata miki,Kiyi yafemi..Ki..Ya..fe..min..”Tafada tana kuka mai tsuma duk mai Sauraro kafin tari,ya sarketa ta duka tana rike kanta.
  Zahirah data ke tsaye hawaye sungama wankemata fuska,tawani juyo da wani irin gudu ta isa ga Ummi ta dagota tana fadin”Na yafemiki Ummi,wlh bantaba rike ki araina  daidai rana dayaba,duk abunda kikayimin bana ganin laifinki,kema batamiki akayi,Kullum burina kidawo ki yafemana mahaifiyata abunda ta aikata gareki,gashi yau burina dani da ya mu”azzam yacika,ammh kuma yau ta kasance babu shi,balle yaga wannan rana mai dimbin tarihi.”Tafada tana kuka da Sauri Ummi ta Rumgumeta tana fadin”Babu Son Zahirah,son ya tafi ya barmu Alhalin ya manta cewa bazamu iya rayuwa babu shi ba, ammh komai yafaru ni najama kaina,Allah ne yake hukuntani da laifin dana aikata..,Allah na tuba ka yafemin..”tafada kuka na kecemata,kamkame juna sukayi suna kuka mai cinrai.
  Gabadaya jikin mutanen dake falon sai da yayi sanyi,yakura da hajiya kuwa kwallah suke sharewa,Shikanshi bahna juyawa yayi yana share kwallah,ita kanta Maghana kwallar take sharewa,Gyarab murya bukar yayi yana fadin”kubar kukan hakanan kada wani mtsalan ta sameku,ku zo muzauna duka a taru ayafema juna,an zama daya,abunda Allah kuma ya kaddara babu mahalukin daya isa ya hana”yafada cikin sanyin jik,hajiya ce ta isa ga Ummi ta kamo hannunta tana fadin”Muje ki zauna suhaima kinsan baki da cikkakiyar lafiya,ki rage wannan kukan don Allah..”Tafada tana riko hannunta,kam kuwa ummi ta riko hannu zahirah suka karisa cikin Falon suka zazzauna,umarni bukar yabama kowa akan azauna.
  gyara zama bukar yayi yana fadin”Alhamdulillah Allah shine abun godiya,dama abunda ake nema mutum yaringa yi kenan,yayi nadama Tunda Wuri tunkafin lokaci ya kuremasa,Babu komai hajiya Allah ya yafemana gabadaya..”yafada cikin kulawa.
  Muskatawa Ummi tayi hannunta na rike dana zahirah tace”Nagode sosai Allah ya kara girma..”Tafada bayan ta waiga bayanta itama mahgana tana rokonta gafara,nan tace ta yafemata nan Ummi tabi kowa afalon yan”uwan bukar tana cewa su yafemata,nan duka aka ayafi juna cikin mutumci da karamci,zahirah ta mike Ummi ta kalleta tace”Ina zaki Dota..”
      Zahirah ta kalleta kan tace”Ina zuwa ummi,yanzu zan dawo..”Sakin hannunta ummi tayi tana binta da kallon Tsausayi,ita bama kanta take tsausayama ba tafi tsausayama Zahirah don ita akafi cuta itace yarinya,daki zahirah takoma ta dauko yaran duka biyu ta rumgumesu ta nufo falon dasu,Ummi na ganin Fitowarta ta nufeta tana amsan littale Ummi take fadin”kai,kika iya daukansu lokaci daya,baki tsorom su kubce miki..”tafada tana kurama little Ummi dake hannunta ido.
  Mirmishi zahirah tayi tana fadin”Ai na saba ummi,banajin komai..”tafada bayan ta ijiyemata moodu gefen cinyarta inda ta dora Little ummi,Kura musu ido Ummi tayi cikin wani yanayi na fita hayyaci hawaye nabin idonta ta dago tana kallon zahirah kafin ta maida kanta gun hajiya,gyadamata kai hajiya tayi tana mirmishi,maida kallonta tayi kan zahirah kan tace”yanzu wadannan yaran ne,acikin ki sanda na koreki..”
  Tafada cikin wani yanayi,gyadamata kai zahirah tayi tana mata mirmishi tace”macen takwaranki ce ummi,namijin kuma sunan Abba,ya mu”azzam yace asamai..”Tafada bayan hawaye ya zubomata,Cikin kukan Fitan hayyacin Ummi ta rumgume jikokinta tanajin wani irin kaunarsu na ratsata,matuka cikin kuka take fadin”Ni wata irin azzaluman uwace,ni wata irin Uwar miji ce,mara rabo aduniya,nayi sanadiyar raba,uba da ya”yansa,bayan burin kowani uba yaga kwansa aduniya kaichona ni Suhaima Kaic…..”Zahirah ce ta saka hannu ta rufema ummi baki tana fadin”a”a Ummi kibar fadin hakan,komai kika ga yafaru daga indallahine,ba laifinki bane Ummi dama chan rubuttacene daga rabbil izzati.
  Juyowa kawai Ummi tayi tahadata da ya”yan ta rumgumeta tana kuka take fadin”nagode zahirah..Nagode nayi takaichin raba Son da nagartacciyan mata kamarki,nayi takaichi har in na tuna kamar na kashe kaina nakeji..”Tafada cikin kuka itakanta zahirah kukan take,ganin kukan nasu yafara yawa ne,harsu little Ummi sun fara nasu kananun kuka,bukar yace don Allah subar kuka komai ya wuce,daki zahirah takoma chan ta basu little Ummi mama,tanayi tana kuka tana fadin”ya mu”azzzam kana ina? yau ga ranar daka ke mafarkin zuwanta,yau ga ranar da Ummi tayarda tayi nadaman Abunda ta aikata..”taketa fada tana kuka.
  Karfe shidda daidai aka Fito da zahirah bayan tasha tarin nasihohi,gun iyayyanta,itako Ummi hawayenta yaki tsaiduwa,tun lokacin da Ashe ta karbu su little ummi dayake suna hannun Ummi ta kwakwumesu tana kallonsu tana kuka,tunda aka Fito da zahirah Ummi tayi Wuf tafada tiolet tana gunjin kuka,kaichonta Yanzu ita da kanta ta jagoranci wani yaketa gonar danta,wayyo ta cucu kanta,tana ji tana gani aka saka zahirah awata bakar benza wacce mijinta ya aiko aka dauketa aciki,bayan Sauran motocin gudu uku,Su yakura ne kan gaba,Hajiyar shureim kuma taso ta doje Bukar yaroketa kan taraka zahirah to babu yarda zatayi,Ummi kuma an nemeta ba”a ganta ba,kowa yasan boyewa tayi,to ai babu dadi ne sai hakuri tunda aikin gama ya rigaya daya gama,zahirah tayi kuka kamar ranta zaifita har saida muryanta ya fara dishewa,bama zata iya fadan irin Tashin hankalin datake ciki bane,ammh lokacin data yada kanta bisa kafadan yakura tana kuka acikin mota babu wanda take tunawa sai mu”azzam ajirgi sanda take rumgume jikin Yakura tana kuka za”a kaita gidan mu”azzam ammh sai gashi Tarihi ya maimata kansa,ammh kash yau gidan wanin mu”azzam za’a kaita tafiyan tasha bambam da wanda sukayi na farko,Su little Ummi ko na hannun hajiya Suma sunsha kwalliyansu shar,suma zasu gidan sabon papane dole su chakare😜
_____________________
  *SUDAN*
  Tayi parking din motarta cikin haraban asibitin ta fito tana takunta d’ai d’ai,cikin shigar pakistan Riga da wando sai wani siririn gyale data saka bisa kanta,takalmin kafanta mai dudu ne sosai,tana gabda shiga mainpalour din asibitin sukaci karo da juna,da kallo tabisa yana dagowa suka hada ido,Daure Fuska yayi ya ratsa ta gefenta ya wuce yafara tafiya cikin takunsa na sanyi.
  Cikin mamaki take binsa da kallo kan ta bisa tana fadin”Hy where are u giong…? tafada tana shan gabansa,zuramata ido yayi kafin yakara yunkurun binta gefenta ya wuce taki basa dama,marairaicewa tayi tana fadin”plz mr man,am Srry da yadda na dinga takurama rayuwarka,don Allah kazo mu koma ciki i promise u kana kara samun sauki i will let u go but not now..”Tafada tana hada hannuwanta alamar roko.
  Kauda kai yayi yayimata banza harma ta fidda rai zaiyi mata mgana sai chan taji yace”masauki na zan koma,plz leave me alone nagode da taimakoki,ni nasamu lafiya kibarni natafi am begging u..”yafada shima cikin wani yanayi,tsuramai ido tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace”Naji zan barka katafi but sai kamin alqawari yarda nakaika wajen Abbie na nadade inabashi lbrinka,bayan nan in zaka tafi to,sai ka tafi babu damuwa.”Tafada cikin wani yanayi.
  Kallonta yayi kamar zai ce, a’a sai kuma yaga rashin dacewarka haka kai tsaye yace”agree but in one condition..”yafada kai tsaye gyadamai kai tayi tana kallonsa cigaba da cewa yayi”bayan kin kaini wajen Abbanki,zaki barni na tafi bazaki kara,bibiyar rayuwata ba,indai kinyi alqawari ,nikuma zan biki mutafi wajen Abbie ki dakikace zamu..”
Shuru tayi tana kallonsa ganin yadda tayi shuru yasashi saurun ratsawa zai wuce da Sauri tace”yes Acceppted…”tafada cikin comfident,cak ya tsaya bayan ya dago yana kallonta baizata zata yarda ba, shiyasa yahadamata wannan mganar,gun motarta ta nufa shikuma ya biyota aransa yana fadin it over aie,data kaini zan kama gabana i think ma yazama dole na chanza country don kada mayyar yarinyarnan tasake binshi.
  Sun fara tafiya yamata mgana kan subiya hotel din daya sauka,babu gardama suka fara zuwa chan,da shikadai yaso ya shiga ammh lubna taki yarda,dole suka shiga tare,shiko kallonta kawai yake,tana tunanin zai gudu ne,jakar briefcase dinsa dake da muhimmam Abubuwansa kawai ya dauko daman,ai iyakar kayansa kenan,fitowa yayi bayan ya samu ma”aikatan ya mikasu mukullin dakin da tiket dinsu kafin yayi Signing na barin wajen duk da yana da Sauran kudi,don baisan ma dakin adadin kwana nawa yakama ba.
  Suna isowa gidan ta buga hon maigadi yazo ya budemusu yana musu marhaba da harshen larabci,lubna ce kadai ta amsa,ammh banda mu”aazzam wanda yawani hade rai kamar wanda aka aikomai da sakon mutuwa.
  Tana gama parking din motar a parking space ta fito tazagaya ta budema Mu”azzam ya fito yana bin gidan da kallo,Gaba tashiga yana binta abaya har zuwa babban kofar da zata sadaka da falon gida hannu ta sa ta tura kifar gillas din dake wajen bayan ta kwarara sallama cikin zazzakan muryanta,tana shigowa tabawa mu”azzam hanya tanafadin”bismillah..”
  Abbie da mom harma da mooh dasuke falon,suna hira suka dago suna amsa sallamanta,jin tace bismillah ne suka kurama kofa ido suna so suga to yau kuma wa lubna sarkin Taimako ta jajibo.
  Shiko cikin wani irin taku ya shigo falon da sallama shima,ammh cikin muryansa mai cike da sanyi da gardi da Ake kira husky voice kafin ya bayyana afalon galala sukayi suna kallonsa lubna na gefe tana mirmishi tace”Abbie yau dai ga bawan Allah danake baka lbri yau na kawomaka shi har gida..”tafada tana nuna mu”azzam wanda ke tsaye kikam yana bin Su Abbie da kallo.
  Abbie daya daskare azaune ya mike jikinsa na rawa ya Nufi mu”azzam bayan ya zare siririn gilashin dake idonsa,ya isa garesa yana shafa fuskarsa yake fadi cikin rawan murya’Fus..Kar..wa na..Ke..ga..ni..Ka..marta Aminina *MUHAMMED MOODU* ” Abbie yafada muryansa na rawa lokaci daya ya kuma sha fuskar mu”azzam din kamar wanda akacemai zai bace.
Gabadaya suka shiga rudu,mom ta kalli mooh shima ya kalleta,lubna takalli Abbie tana zare ido,shiko mu”azzam tuni kwakwalwarsa ta hasasomai wani abu cikin wata murya yace”Ba shakka sunan daka kira sunan mahaifina ne,ni dansa ne daya rasu ya bari wata hudu acikin mahafiyata”mu”azzam yafada yana kallon Abbie.
Jikin Abbie na rawa ya riko hannunsa yana fadin”ya sunan mahaifiyarka..?”Suhaima..”mu”azzam yabashi amsa,ai dawani sauri Abbie ya rumgumesa yana fadin ” _Shine,wlh Shine da”n Moodu ne da Suhaima wlh Shine_ ” Abbie ke fada yana kuka lokaci daya yana kamkame mu”azzam din tamkar wani zai kwacemasa shi.
_Hohoho,Kowa sai tambaya yake don Allah ina Janaf take?hmmm janaf na nan a inda kuke,bana cika posting bane cuz abubuwa sunman yawa,Masu tambayan digit dins am srry to say bawai ina nufin ni mai tsada bace,buh Nombartawace mai tsada,Janaf freeking fans zan baku nombata buh in one condition kada wani Namji ya kirani plz and plz ina daraja kaina,to kutayani darajawa,Females only don Allah,Kira mai amfani ko sako mai amfani,matukar kinsan baki dawani abun fada,plz and plz karkisoman Daukan Nombata,bana da wulakanci,kuma bani son ni a wulakantani,ku rike mutumcinku nima na rike nawa..I love u so much Masoyana Allah ya barkauna ta har abada_
*Here iz 09069067488*
*comment share and vote..*
     *Janafy*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer’s Asso*✏
_*Jiya naji matukar kunya alokacin dana ci karo da wasu marubuta awasu groups din sun zauna anacin Zarafin marubuta yan”uwansu,Me kukayi kenan? kuna Tsammanin kun burgene don an zagi marubuta yan’uwanku? kokowa abun alfaharikune don azauna anayi da wata marubuciya kina saka baki kina Kara bawa readers dama rainamu? To kusani kanku ku kamawa,domin ruwan Daya hadiye bukar shizaije ya dawo ya hadiye habu,duk abun dayane Hajiyata,ke marubuciya ce itama haka so baki wuce kema yafaru dake ba,matukar munaso, Amana Adalci to muma sai munma kanmu ADALCI..,Na fada na kara fada ni JAMILAJANAFTY KO A BAKIN KURA NAKE ZAN KARE HAKKIN MARUCI,DOMIN YAU GAREKANE GOBE GA WANINKA*_✌
*NOT EDITED*💥
           *NO 32*
      “”Shine wa..”Lubna ta ambata bakinta na rawa.
Dagowa Abbie yayi yana fadin”Shine,dan wajen Aminina marigayi Muhammed moodu,wanda mukayi karatu dashi a madina,kun manta kullum kwanan duniya sai na muku zence sa,? to yaron wajensa ne Allah na godemaka”yafada hawaye suna zubomai yana kara riko mu”azzam din.
  Kuramai do mu”azzam yayi kafin bakinsa ya bude yana Rawa yace”Abbah kh..mis….? yafada cikin Rawan murya da kuma sigar tambaya,kallonsa Abbie yayi yana fadin”kaima kasani ko,?sunbaka lbri na? nine Abbanka,Rumana, muhammed,Lubna ku taho ga dan”uwanku,ashe lubna dan”uwanki ne,kika damu ki taimakamai kai Allah nagode maka”
  yafada yana kara rumgumesa cikin wani yanayi mu”azzam ya rumgume Abbie khamis lokaci daya yanajin hawaye suna taru a idanunsa,tsawon lokaci Abbie na rumgume dashi kafin ya sakeshi ya riko hannunsa,har zuwa cikin falon ya xaunar dashi kan kujera yana fadin”ku zo ku zauna,yau ranace mai muhimmanci a rayuwarmu ku matso dan”uwanku ne..’yafada cikin murna.
   karisowa falon lubna tayi gabadaya kwanyatan tadaina aiki,mutumin data taikama,da yake ga abokin abbanta ashe? haba shiyasa takejin wani abu game dashi,takejin shi tamakar dan”uwanta da suka fito ciki daya,ashe ashe akwai wata alaka mai karfi tsakanin iyayensu basu basani ba,sai gashi dalilin taimakonsa har Abbanta yahadu da abunda tun tasowarsu bai taba fashin ambatansa ba daidai da Rana daya.
Mooh da mom suka zauna suma asanyaye suna bin mu”azzam da kallo,wanda shima yake kallonsu haryanzu mamaki bai bar Fuskarsa ba,kallonsa mu”azzam yayi kafin yace”a lbrin da Ummi na tabani ta fadamin tun bayan komawarka sudan,baka kara dawowa ba baka nemesu ba,itama kuma bata nemeka ba,Tun bayan Rasuwar Abbana,abun mamki taya kasan cewa Allah yayima mahaifina Rasuwa?
Kuri Abbie yayi masa da ido kafin ya Sauke ajiyar zuciya,kauda kai yayi hawaye suka ciko idanunsa suka kwaranyo Mooh da lubna suka kalli juna suna zaro ido,Abbie na hawaye? abunda basu taba gani ba itako mom ajiyar zuciya ta sauke domin ita datake tare da khamis tafi kowa sanin rauninsa duk rannar daya tuna Aminin nasa.
Hannu yasa ya share hawaye kafin ya dago yana kallon mu”azzam,hannunsa ya riko dama yana kusa dashi cikin dashasshiyar murya yace”Nasan Abokina Muhammed moodu ya rasu tun lokacin da bai dade da Rasuwa ba”
  Cikin mamaki Mu”azzam ya kallesa kafin yayi mgana Abbie ya rigasa da cewa”Zan fada muku komai yanzu..”
   Ajiyar zuciya Abbie ya sauke kafin ya fara magana cikin Raunin murya.
  _Tabbas bayan Komawata na koma cikin damuwa halin da Aminina yake ciki,shida matarsa,ganin yadda gabadaya yan”uwansa babu wanda ya amshesa daga shi har matarsa nasa,wanda koni da sukazo dani na zammanto musu shaida sunki yarda dani,bayan komawata muna waya da moodu ammh kullum na tambayenshi ya ake cike game da zaman shi da yan”uwansa sai yacemin babu komai,in na kuma tambayi ya Suhaima nan yace min komai Normal,duk da hakan ban yarda ba domin ayanayinsa kadai nakan gane yana cikin damuwa kwatsam yakirani yana fadamin Rasuwar mahaifinsa wanda yanayin yadda naji moodu namin kuka ta waya abun yadagamin hankali,domin koda muke karatu amadina moodu mutum ne mai taurin zuciya kafin kaga abunda zai sakashi kuka abu ne maigirma,shiyasa hankalina ya tashi ainun,nayi shiri zan taho Nageria sai Ciwon Suger da Ammina ke fama dashi ya tashi har akayi Addimitting dinmu a hopt,shine ya dakatar dani daga tahowa,lokacin dataji sauki nanemi na taho moodu yahanani tahowa kan inyi zamana kawai Allah yajikan baba,Hakanan na hakura da zuwa sakamakon rokon da moodu yayimin na kada nazo,shida kanshi zaizo da ankwana biyu,bazan taba mantawa ba waya ta dashi na karshe yakirani da daddare misalin karfe uku na dare mu anan kenan,yadda yakemin mgana na fahimci tabbas akwai mtsala nan da nan na rude ina tambayanshi meke faruwa ne,nan yake fadamin duk abunda yafaru tun bayan barowata da yadda Shettima da fadi su ka dinga,muzgunama rayuwarsa data Suhaima marainiyar Allah,kafin yagama bani lbri kuka ya kwacemin na tsausayin Aminina,bai bani dabam mgana ba,yace baya da lafiya yaje yaga likita kuma an tabbatarmai da yakamu da hawan jini sakamakon yadda yake matsama kansa da damuwa,kuma yanaji ajikinsa bazai kai zuwa tsawon wani lokaci ba,ga amanar Suhaimar nan yabari gareni,Bata da kowa sai shi sai ni,kuma shi baya tunanin zaiyi tsawon rai,muna cikin mgana ne kawai wayar ta wanke,nayi ta kira ammh ban samu ba,hankalina ya tashi naso na taho tun washe gari ammh bansamu Visa ba,sai bayan Kwana goma,alokacin zuciyata tagama tsinkewa da al”amuran Moodu domin wayarsa tun ranar bata kara shiga,ba Na taho Nageria ranar wata asabar na iso maiduguri da yamma lokacin misalin 5:00pm na yamma na sauka kofar gidan Fitowa daga kekenapep,kenan muka hada ido da Shettima shida Fadi sun Fito daga gidan da alama suna wata mgana ne,Suna ganina suka wani yi tsam dasu,alaman sunyi mamakin ganina,niko cikin azama na nufesu ina mika Shettima hannu,ammh sai yaki amsa ya noke hannunsa yana bina da wani malalacin kallo ban dandaraba na sake mikamai,ammh wannan karon sai ya buge hannun nawa yana fadin”mallam daga ina? bibiyan kuma na menene,? wanda yahada to yau bashi aduniya saika kara gaba kuma ko” Shettima yafada fuskarsa ba Annuri Fadi ta amshe da fadin’ah to shi nagani yaya,moodu ne dama yazo dakai,kuma yau kwanansa tara da rasuwa,ai inaga bawani Sauran bashi ko mallam”tafada tana hararata,jin kalaman dasuka fadane yasa yar jakar dake hannuna ta subuce ta fadi,tuni hawaye suka wankemin ido,cikin tashin hankali da rawan murya nake fadin”moodu..Ya…ra..su..”nafada hawaye suna kara zubomun,babu ko tsausayin Aransu ganin halin dana shiga Shettima yace”eh aka ce,kai banzan balarabe ko Hausan bakaji ance maka abokin naka ya rasu,sai ka kama gabanka ko bakaji bane”dafe kaina nayi ina tsiyayan hawaye lokaci daya na dago yana kallonsu kafin nace”Moodu ya rasu? ina Suhaima matarsa take,ku kaini wajenta”kallon kallo aka fara tsakanin Fadi da shettima kafin fadi tace”gata goye abayanmu,kai dai maye ne,karabu damu muji da abunda ke damunmu mana,ita tun da yarasu takama gabanta dama haduwar bariki ce” tafada tana yamutsa Fuska,Gyada kai shettima yayi yana fadin”kwarai makuwa,itama takara gaba,saboda haka bamu da sauran wani abun da zaka tsaya kana titsiyemu da tambaya,ka koma inda ka fito mun gode…”Yafada yana hararata dukurkushe nayi agabansu ina hawaye nace”don Allah ku taimakeni ku kaini inga Suhaima wlh amanarta moodu yabani don Allah..”shekeke suka kalleni kan Fadi tace”mun Shiga uku yaya,zai taramana jama”a,kagafa yadda yayimana durkuso yana hawaye salon mutane su farga suce wani abu mukayi masa,ka sallamesa ko kuma sai ka kira masa karti ne,sun bacemana dashi akofar gidan”Gyada kai shettima yayi yana waige waige yake fadin”inaga haka za”ayi bari Tunda yaki tafiya..”ganin yadda yake waige waigene ya sani mikewa ina binsu da kallo ina hawaye suko ko ajinkinsu saima dauke kai da sukayi kamar basu ba,jakata na dauka na rataya ina kuka nace”Allah…ya..Ji…kan..Moodu…”Amin munji don Allah katafi mungaji da ganinka”Fadi ta fada cike da masifa,hakanan inaji inagani najuya nafara tafiya ina sharan hawaye ina waigensu,duk da lokacin yammah ne ammh babu yalwar mutane,agun sosai sai jefi jefi ne suke wucewa,ahaka ina tafe ina kuka har na karisa bakin titi na samu abun hawa,Hotel naje nakama,wanda kwana nayi ina kuka,washegari tun safe na biyo jirgi zuwa lagos,kwana biyu na kara na biyo jirgi na dawo Sudan,Wanda saboda yadda mutuwar mahaifinka ta dakeni sai da na kwanta a asibiti,sai da iyayyena suka dagemin da addu’an kana na dawo daidai,Koda zuciyata bata yarda cewa suhaima ta tafi ba,ammh banda karfin gwiwan karyatawa,tunda Basu bani  wata dama da zan gane cewa ba hakane bane,sun min koran kare,suna tunanin kila dukiyan mahaifinka zan amsa kowani abu daya danganci haka,Shekara daya nayi ina fama da Nauyin Amanar mahaifinka,ammh basan yadda zanyi na cika masa wannan amanartashi ba,bani da wanda zai bani lbri game da Mahaifiyar,iyayyena suka nema aure da Rumana,yar uwatane,Shekaran aurenmu muka haifi da namiji,wanda yaci sunan mahaifinka,Muhammed muna kiransa mooh,bayan ita sai Lubna wanda daga su bamu sake haihuwa ba iyayena kuwa duka Allah yayi musu rasuwa,dukkansu sun mutu da sanin lbrin yadda nake kwana na tashi da Tunanin girman Amanar da mahaifinka ya barmin,ga sunan ka tambayesu duk kwanan duniya,sai na tuna mahaifinka da mahaifiyarka,kukan Rashinsa kuwa basan iyakaba,kullum kuma lbrin mahaifinka har sun dade da haddaceshi agidanan,ban sani ba,ban kuma ji wani lbri game da Suhaima ba,balle naji lbrin Moodu ya rasu ya barta da cikinka,Kwatsam lubna tazomin da lbrin ta hadu dakai,kuma yadda kalura kana cikin mawuyacin hali,kuma kaki bata dama,data gayamin ni nayita bata karfin gwiwan juriya akan hakan,ashe ashe jini ke bibiyanta zata sakani farinciki da fatan Sauke Nauyin daya rataya awuyana wanda shekara da shekaru yake damuna,Allah kadai ne zai iya fisalta farincikin danake ciki,tun bayan Rasuwar moodu yauce rana ta farko danaji Bakincikin dake damuna ya gushe_
   Yafada yana sharbe hawayensa,Ba Abbie ba hatta mu”azzam kuka yake ka shirban,lubna ma,kukan take mooh kuwa,shima ya dukar dakai yana sharan kwallah,haka mom wacce itafi kowa sanin yadda mijinta ke kwana cikin damuwa,jinjina kai Abbie yayi kafin yace”kaji dalilina da abunda ya faru,ina Suhaima?miya kawoka Sudan? kuma aka ganka cikin mayuwacin hali?
  Abbie yafada yana kallon Mu”azzam din,Dukar dakai mu”azzam yayi lokaci daya hawaye suka kwaranyomai Tsuramai ido lubna tayi takosa taji kadan daga lbrinsa dakyar ya bude baki yace”Sunana Ibrahim Mu”azzam,….Tiryan Tiryan yafara basu lbrin rayuwarsu tundaga farko har karshe bai boye musu komai ba,tundaga cikinsa har haihuwansa da yadda Ummi takai su shettima kotu da rayuwarsu agun hajiya baraka,da yadda rayuwa ta sauyamusu da komawarsu Abuja da hadin Auren da shettima yamai da rayuwarsa da zahirah da yadda Ummi ta datse Rayuwarsa ta hanyar rabasa da zahirah da kwaciyar dayayi a asibiti da barinsa gida zuwa yanzu dayake zaune agabansu sai daya fadamusu kafin ya karishe da cewa,”Hakika itakanta Ummi kullum cikin Tunatar dani take game dakai,tana fadamin cewa yakamata na nemeka,nine ban maida kai ga mganarta ba har zuwa yau danake mgana agabanka ammh itakanta Ummi bata manta dakai ba”
  Shuru falon yayi,tuni lubna ke rusa kuka,tun sanda Mu”azzam yafara bada lbrinsa,dama ita macece mai tsausayi ,mom share hawaye na tsausayin mu”azzam din,shiko mooh kusa dashi ya matso ya dafa kafadansa yana dan damkewa kadan kadan alamar lallashi,Abbie kuwa shuru yayi kamar ruwa yacisa kafin yace”Ashhh..Suhaima bata kyauta ba sam,ai ba”a rama cuta da cuta,da alheri ake ramawa,kuma tunda suka gane sunyi kuskure sun roketa gafara meyasa bata yafe musu ba,?Yanzu gashi duk yakin datayi daga karshe ita akazo aka cita da yaki,banji dadi ba sam,gashi ta sanyanka cikin mawuyacin halin wanda intasamu lbri Sai taji dama tunfarko bata aikata haka ba”
  Yafada cikin damuwa kafin ya dafa mu”azzam yana fadin”Bakomai Son,anytin will be alright,kayi hakuri kacire damuwa aranka ka rumgumi kaddaranka,kana tare da Abbankane bazai kara bari kayi kuka ba kaji ko’gyada maasa kai mu”azzam yayi yana sharen kwallah ajiyar zuciya Abbie ya sauke kan yace”Mooh take him to ur bedroom,yayi wanka ya chanxa kaya am make sure kabashi clipper ya aske wannan Sumar data rufe masa Fuska”yafada da sigar zolaya.
  Dan murmusawa mu”azzam yayi kafin ya mike riko hannunsa mooh yayi yana fadin”welcome bro..Naji dadin ganinka da haduwa dakai amtsayin dan”uwana,tunda nake nikadai nake rayuwa dagani sai wannan rigimammiyar yarinyar”yafada yana nuna lubna wanda ta makamai harara tana share hawaye.
Mirmishi mu”azzam yayi mai kayatarwa,yana kallon lubna wacce take kallonsa tana wani lumshe ido,dauke kai yayi yana kallon mooh kafin ya damke hannunsa yace”am hppy to bro..”yafada shima fuskarsa na nuna farincikin dayake ciki,hanunsu na sarke suka wuce zuwa shashen mooh din wanda Abbie da mom suka bisu da kallon sha”awa,itako lubna kallonsu take tanajin wani yanayi atare da ita.
  Suna zuwa dakin mooh bedroom ne mai dauke da tiolet,mooh din da kanshi yahadamai Ruwanka ya shiga yayi,yau ne rana ta farko daya yi wanka cikin natsuwa haryaji yaji dadin jikinsa yana fitowa mooh ya rigaya daya Fitomai da kayansa,riga da wando ne,black and white na kamfanin Armani,abun dariya mooh da kansa ya zaunar dashi gaban dressing mirror yajona clipper din ajikin wuta yana askema mu”azzam din gashin daya cikamai kai da Fuskarsa gabadaya mirmishi kawai mu”azzam keyi yana kallon mooh ta madubi yanaji wani bamgare daga damuwarsa ta ragu ko bakomai he met anoder Family,ya Family domin Abbie khamis yana madadin Abbansane.
  yana gamamai sai gashi ya fito ras dashi,kyansa da zatinsa tare haibansa kuka bayyana,sai dai yar ramar dayayi kawai na ciwo,kallon kansa yayi yana shafa kansa,Rabonsa da zama irin haka tun agida kafin Ummu tayi yanke duk wani jin dadinsa na rayuwa sai yau,Shima mooh din wanka yayi yasa irin kayan Mu”azzam din sai dai diffirent clour ne,hannunsu na cikin na juna suka sake fitowa falon suka iske mom na jera abinci bisa makeken Tebir din cin abinci mai kama da na villan gidan gwannati😂
  Mom tabisu da kallo sha”awa aranta jin dadin ganin zaratan mazan masu kwarjini da tsari,sannu da aiki mu”azzam ya mata,ta amsa tana kallonsa tana washe baki alamar tana cikin Farinciki,Abbie ne shima ya fito ganinsu haka shima yasashi Farinciki sosai,Rumgumesu yayi dukkansu yana ma Allah godiya,yana dagowa yaci karo da lubna tana tsaye tana kallonsu cike da burgewa waremata hannu yayi yana fadin”oya come and join us Dota..”
Da Sauri ta kariso ta gefen mooh ta tsaya bayan ta sanya hannu inda Abbie yadafa bayan mu”azzam,tana kuma kallon bayan mu”azzam din,sakin su Abbie yayi yana fadin”welcome to happy Family my Son..”yafada cikin murna mu”azzam yace”Tanque Abbie..Nagode ma Allah da yasa ina da rabon haduwa daku,haduwa da Family dina wanda sukamin nisa”jinjina kai Abbie yayi yana fadin”kadaina godemin Son iz my Duty so muje muci abinci ko?
yafada yana kallonsu kada kai sukayi suna mirmishi gaba yayi suna binsa abaya,lubna kuwa duk motsin Mu”azzam a idonta,kamar ya sani ya waiwayo karaf ko suka hada ido mirmishi ya sakarmata for d First time,sandarewa lubna tayi saboda yadda mirmishin ya daketa lokaci daya wucewa yayi yabarta itako dakyar ta karisa taja kujera ta zauna jikinta amace.
  Kowa nacin abinci ammh gabadaya attention din lubna naga Mu”azzam,wanda ko shi baima san wainar datake toyaba,bai wani ci abincin dayawa ba ya tashi,mooh yabisa suka koma falo suna hira,sai tamaida kunnanta kansu,tanaji yana fadama mooh shi lauya ne yana aiki a hight Supreme court Abuja,a inda shi mooh din kefadamai Shi Quantity Suver,yakaranta A jam’ar Malesia ayanzu haka yana aiki da gwannatin kasar sudan wajen shimfida kwalta,sunata dai hiransu mu”azzam ya saki jiki yana ba mooh lbrin yanayin aikinsu A Nigeria shima yana bashi nashi,ahaka Abbie yazo ya samesu wanda shima sama sama yaci abinci hankalinshi na gunsu tsakiyarsu ya zauna,shima aka shiga hiran dashi.
  Tagumi lubna ta buga tanajin yadda zuciyanta ke bugawa duk bayan kowani dakika matukar ta kalli mu”azzam,mom dake gefe ta kura mata ido tana mamakin meya same Lubna yau,ganin bata da wannan amsan ya sata ta mata banza taciga da cin abincinta.
_________________
*NAGERIA*
  Motar su Zahirah na tashi Ummi tayi Wuf ta fito,tana fitowa ba wanda ya ganta Waje ta fito ta iske ushe cikin mota batai wata wata ba,ta bude baya ta shiga tana fadin”Ushe mu koma Famfari..”jin mganarta kawai yayi asama kamar zaiyi mgana  sai dai ya fasa yaja motar suka Fice daga unguwar.
   Hon Suka zuba abakin makeken gidan da hanzari megadi yazo ya bude musu get motocin suka sulala ciki,Ashe ce kan gaban Fitowa tana sakin guda,itama mahgana ba”a barta abaya ba,tuni suka rikita gidan,chan wata yar yayan bukar ta fito da Turaren Wuta tana hurama Amarya wacce Yakura ta fito daga ita daga mota.
Gaba su Ashe sukayi suna sakin guda da tafi lokacin da suka nufi kofar da zata sadasu da babbar tagamemom falon Zahirah dake rike hannun yakura jitake kamar ana janta gudan ko da su Ashe suke kamar ta mutu takeji banda Tsiyayar hawaye bata komai cikin katon lifayan da aka nadeta dashi.
  Yagana dake Cikin bedroom dinta ita da kawarta Zinatu tayi wuf tatashi jin guda ya mamaye gidan,dafe kirji tayi tana kwalalo ido take fadin”Zinatu ya tabbata ga amarya an kawo,wlh ji nake kamar naje na burmata wuka agaban iyayan nata..”
Tsaki zinatu taja tana fadin”mtsewww…Sai kije ki bankamata ana miki fadan kikiyayi kiwon awaki kina zencen kyallah ta haihu,miye na damuwa keda kikasan nan da Sati daya zata koma inda ta fito..”
*Comment share and vote*
       *Jamilajanafty*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
       *Mallakar:JANAF*
       *Wattpad:Janafnancy12*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*GIFT TO:Hussain80k*
*Intelligent writer’s Asso*✏
*NOT EDITED*💥
            *NO 33*
   “Kallonta yagana tayi kan tace”Allah Qawata..”wani killer smile Zinatu tayi kafin tace”indai da mallam da boko sai fita ta barmiki gidanki da mijinki nasha ruwan walh Qawata..”
  Tafada cikin gadara da wani yatsina hannu yagana ta bata suka kashe tafadin”Shegiya qawata ko shedan na tsoron hada hanya dake'”dariya tana fadin”don uban mutun shidin shedan na hada hanya dashi,ne yo duk karatun dayane,Karatun dare dukkanmu mukayi Shiyasa har tafaru ta kare bamu Fahimci komai ba”dariya suka sheke dashi suka kara tafawa daidai lokacin dasukaji shigowarsu falon yan”uwan Alhaji da sukazo daga kano suna musu lale marhaba.
   Cikin mutumci da kararramawa yan”uwan kabiru suka amshesu akasa suka zaunar da zahirah,wata diyar goggon kabirun wacce,ake kira da uwani tayi karaf ta karbe Little Ummi dake hannun Hajiya tana fadin”Allahu akbar kaga inda akeyi don Allah,irin haihuwa jikar akbarka,Allah yasa wata shekara ki haifoma yan hudu ne ma ba yan biyu ba”tafada tana shilla little ummi wacce ke bangala dariya,nan wata ma ta karbi moodu suna tayabawa suna saka albarka.
  Hajiya ne tayi gyara murya tana fadin”To masha Allahu yaudai ga amaryanku mun kawo muku,munji dadin yadda kuka karbemu ga zahirah nan ta shigo cikinku fatan zaku riketa tamkar yarku ta cikinku domin yanzu taku ce sai,kuma kunyi hakuri dan tana da danyen jego”Uwani ce ta karbe da cewa'”Mu karba wlh Allah yabada zaman lafiya mai dorewa da hakuri da juna,yara kuma muna so inda karima akawo wlh kawu bai ki ba,shida ya kwashi Shekaru kullum ya shigo gida sai haushi wata karya kullum jiya iyau babu cigaba”tafada tana hararan dakin yagana wacce ke ciki sunajin duk maganganun da uwani ke watsawa.
Cikin Zafin rai,yagana ta mike zinatu ta rikota kallonta tayi tana huci tace”sakeni na fita naci mai cin uwar wanchan ballagazan karuwar kauyen”Tafada tana huci,sakinta Zinatu tayi tana fadin”easy madam,barta keda kikeda takamar nasu hannu yo wani burga za”ayi miki barta tayi lokacinta ne,gobe bazata yi ba ko,?”tafada tana kallonta ajiyar zuciya yagana ta sauke kafin takoma gefe ta zauna tana huci zinatu na mata dariyan shakiyanci.
  Yakura ne takatse su da yadda suke zubama zahirah kirari da kuma yabo,gefe daya kuma suna yadama yagana habaici,da fadin”amm,ina shashen uwargidan mu kaita mu damkamata amana bisa al”ada dare nayi..”Uwani ta mike tana fadin”ku taso ku biyoni kunsan matar gidan sai mai gidan”tafada cikin gatse taso zahirah sukayi suka bi Uwani inda Ta wuce kai tsaye cikin wani bedroom tana tura kofan lokaci daya da sallama.
Su Ashe na ganin haka suka hada baki suna sakin guda,masu yawo da kamshi Turare suna ta fama dashi,Suna shigowa yagana da zinatu suka kallesu shekesheke cike da mamaki har suka zazzauna bisa kafet din dake tsakar dakin,Uwani tace tana nuna yagana”ga uwar gida karfen gida,uwar gida ga amarya hasken gidan ta shigo an kawo miki amanar nan ne ta iyaye dasuke badawa tun al”adunmu na da..”
  Da gayyah tafadi maganar bayan ta wani juyamata ido,wani wulakattacen kallo yagana kebin uwanin dashi kafin tace”yo ai na aza uwani yar kanzaki ke zaki karbi amanar don naga kiris yarage ki kaso aurenki kuzo ki auri kawun naki muyi zaman kishi,dake”tafada kai tsaye lokaci daya tana balla masu Hajiya da sukayi tsuru tsuru harara
Baki Uwanu ta rike kan tace”Wane ni da kaddarar dole,ai Uwani tayi zaman kishi dake yagana watan tonon asirinki ne yazo,ai amaryar dai ita ta dace dake,domin daga kamun ludayin mutum ake gani beran masar ne,ba mutum takamar wani Namiji  mage ba”Tafada tana tura dankwalinta gaba.
zuciya ta ciko Yagana zatayi mgana Zinatu ta rigata da cewa”kai kai Qawata wannan wani turare ake busamana,kada ace dai Turaran mallakane ake turaremu dashi”Tafada tana toshe hanci yamutsa Fuska yagana tayi tana fadin”wa yasani Tunda dangin ASiri ne,in Atsaye suke to ni yagana A tafe na kwana,zencen amana plz and plz kutashi ku barmin daki,amana ban karba ba,bakuma zan karba kabiru ne tazo taji abunda nakeji inace jijiyace takawota tazo taja ta barta domin mallakin yagana ce ita kadai..”Tafada cikin izgili.
  Cikin mamaki suke binta da kallo barinma hajiya wacce ke bin yagana da kallon mamaki,itako zahirah tana cikin mayafi tana kuka,batasan sadda taji kukan ya tsaigaita ba,tadago kanta ta cikin shara sharan lifayanta tana karema yagana kallo wacce ke jifansu da mugun kallo,Ashe ne ta miki tana fadin”ikon Allah haba baiwar Allah ammh kodon ganin idonmu kya rage wani abun ko? muma saboda al”ada ne kada muki kawota kice ba”a darajaki ba,ammh kam amanarta ai mijintane kadai zamu damkamawa,keda ita kuwa kowa ya iya allonsa ya wanke,yadda za”a kirasa mijinki haka za”a kirashi mijinta,kinga duk abun daya ne”tafada tana ballamata harara kan tace”kutashi mu sada ta da dakinta dare nayi kar mu shiga lokacin ango.
Dariya suka sheke dashi atare kafin zinatu ta mike tana fadin”ke kuma asuwa,gayyah Arna a idi,jibi bakinki don Allah…”Tafada tana nunata kafin sukara tsintsirewa da dariya,Ashe kuwa ta waigo tace”Ni a ubanki da uwarki,Tambadaddiya mara kamun kai,yo gwanda kowa da kowan wanke ko banza ita kawar taki Allah ya rufamata Aure ya lullubeta kefa,banda yawan kan ta zubar ba abunda kekiyi Kasuwa duka ta kulle an rasa inda za”a sai yawon bin gidajen kawaye Ana neman kashe musu aure,kibari kiyi auren sai ki samu bakin mgana” Tafada tana huci tare da rike kugu.
  Ganin haka yasa yakura mikewa da zahirah wacce abunda ke faruwa ya daskarar da ita,yakura tacema hajiya”hajiya ku tashi mutafi.Ke kuma Allah baki hakuri mun fita hakkinki..”Tafada tana rumgume zahirah jikinta,kama hanyar Fita sukayi zinatu ta mike don mganar da Ashe ta fadamata ya dafata tayi tsalle tasha gabanta tana fadin”Ke Kuchakar cikin gida kalleni nan,ki gani nafi karfinki da dukama danginki,Koda BARIKI TA FITO(mry obam) ta ganni da bariki na wlh,nafiki tashanci,har ni zaki nunama Burauba,Haihuwar lagos girman kaduna,ba kadan iskacin da bansani ba,yo Allah na tuba wani darene,jemage bai gani,yarinyace yadda kukawota haka zakuzo ku dauketa domin Qawatace kadai take da alhakin mallakan Alhaji ita kadai bayan ita babu wacce ta isa kowacece itakuwa koda kan buzun mallam take kwana kuwa”Tafada tana tunkude Ashe,akwai Ashe ta yarfe hannunta bayan ta tsaya da kafanta mahgana tadinga jan hannun Ashe tana fadin”A’i rabasu don Allah ki wuce muje..”ammh ina sai da Ashe tace”ahhayyye nanaye..ke barikin waje ce,niko kilacin cikin gidane,nasan duk wani nau”i na iskanci da tambalewa da na rayuwar yau da kullum domin nine in nayi gohi za”a cini batare da bacin rai ba,kuma ga tarin lada🙈😳🙄🤔wata fa,Sai ta fita ta nema in akayi rashin sa”a bayan anci shegiya a zubamata na jaki,kinga ko kotanan ta miki zarrah,yo dakike fadin Alhaji,yo ai mganar banza kike Alhaji yagaji da zama da juya shima yana bukar ganin wahalarsa aduniya ya auro jinin haihuwa,kuma insha Allah shekara mai zuwa sai munzo sunan yan hudu bama yan biyu ba,Sai da bakinciki ya kashe mutum,kuma da iznin lahi Sharri sai yakoma ma maishi”Tafada tana hararansu tare da buga musu tsaki duk da mahgana nata janta,su hajiya tuni sukayi waje don wannan kalaman na Ashe ya girmi kunnansu.
  Uwani tayi kasa tasaki guda tana fadin”ba shakka mai laya ka kiyayini mai zamani..”tafada tana musu dariya kan sufice,cike da bakincikin Zinatu tace”wannan din wata yar kazakazan ce kuma,kinajin mganar data keyi..”cikin xafi yagana tace”najita kyaleta Qawata,duk zasu gane basu da wayau dagasu har amaryan da Alhajin,nine fa,billahil lazi wannan karon sai nayi abunda bantayi ba”Tafada tana wani girgiza kafa komawa zinatu tayi tana zauna tafadin”sai mun tashi tsaye don naga suma da Shirinsu suka zo”barsu barsu..Nasu shirin suka sani basu san na yagana ba”ta katseta da kallo ta bita tawani girgiza tana cije baki.
  Har bedroom dinta bisa gadonta na alfarma suka sauketa,nan da nan yakura tafara yimata nasiha tare da nunamata sai tayi hakuri,tunda taji tagani kuma da idonta hajiya ma takara danata Ashe ko karkacewa tayi tace”ke ya”n nan dago kanki ki kalleni,bawata kalmar hakuri ban amince ki zauna wa dosara ta taka kiba,gidan mijintane kema gidan mijinki ne,in tace miki zo mu zauna ki bita kizauna in tace miki ubanki to kicemata Sai dai ubanta,don uba baifi uba ba,ke wlh indai kika zauna wannan matar tashiga hakkinki ni ba kanwar ubanki bane,kibari naji lbrin kina mata kukan nan naki,kiga yadda zanyi dake,in zaki mike ga kanki ki mike ki watsar da wannan sanyin naki atoh..”
  Kowa kallon Ashe yake yana dariya itako ta sha mur tana wani hura hanci,itako zahirah banda kuka ba abunda take,to yau kuma inda Allah ya jefota kenan,angama na Uwar miji an koma fargaban kishiya,Sun mata nasiha sosai kafin suyi mata sallama su wuce,zahirah ta rike yakura tana kuka,itakanta yakura tsausayin zahirah ya kamata dakyar ta lallasheta,suka fita suka barta tana kuka,sallama sukayi da yan”uwan Allaji wanda su little Ummi ke hannunsu suna ta dauka cike da sha”awa har bakin mota suka rakasu suna musu godiya.
Kifewa kawai tayi bisa gado tana kuka tafadin”Ya mu”azzam ka yafemin don Allah..”Take fadi tana kuka kamar wata zautattaciya sai da tayi ya isheta kana tayi shuru tana zaune tana raba ido Uwani tayi sallama ita da wata suna dauke da yaran Uwani tace”To amaryanmu mai kuka ga yara sun tashi suna bukatar mama..”tafada tana mikamata Little ummi Dan mirmishi tayi da kumburarrun idanunta kafin ta sa hannu ta karbesu ta dorasu bisa gado tana fadin”Na gode fa..”dariya uwani tayi tana fadin”a’a yima kaine amaryanmu.”tafada kafin sumata sai da safe su fice,sai da suka fita ta mike ta warware lifayan dake jikinta takoma ta zauna tabasu nono daya bayan daya bayan ta kammallah ne,ta mike ta isa ga wardrope din dake dakin ta bude nan taga kayanta jere harda na yaran,over roll ta dauko musu da kayan sanyi saboda taji garin da dan sanyi sanyi ta chanza musu kaya,ta kammallah kenan taji ana mata nooking lokaci daya ana shigowa da sallama.
  Rudewa tayi tayi wani baya kamar zata fadi saboda tsoro kafin tafada bakin gadon tana janye lifayanta ta saka bisa kanta jikinta na rawa yana tsaye yana kallonta ita da yaran dake kwance gefenta suna cilla kafa bakinsa yaki Rufuwa saboda murna,dogon mutum ne wankan Tarwada bai da wani kiba,sai dai ta murjewa da hutu,Ashekaru baxai wuce hamsin da wani abu ba,fuskarsa babu muni ko kadan yana da cikar zati datake amsa sunansa na Namiji,duk acikin mayafinta ta karemai kallo,nan ta tuna tabbas tataba ganinshi Saudaya agidansu yazo wajen bahna dinta…
  Cikin Farinciki ya taka ya isa kusa da ita bayan ya ijiye ledan dake hannunsa bisa side drower,ya zaune gefen inda yaran suke yana kallonsu kuma yana kallon zahirah wacce ta kudundune kanta cikin mayafi jikinta na rawa,Cikin muryansa ta dattako yace”Alhamdulillahi..Masha Allah..”yake fada kafin ya saka hannu ya dauki moodu yana fadin” Na godema Allah bisa ni”imar dayayimin nasamu zukekiyar mata ga ya”ya har guda biyu alokaci daya”yafada yana kallon zahirah kafin yadora da fadin”ko ba haka ba amarsu ta ango..”
  tacikin mayafin zahirah ta ballamai harara ko mgana bataima ba bai damu ba illah ya cigaba da wasa dasu little ummu ya dau wanan ya ijiye yakoma ma wanchan duk tana kallonsa,ta kagara ya fice yabata waje,a takure take,tana wannan mganar sukaji yagana da karfin tana kwalamai kira “Alhaji..!
Tafada lokacin da tafado dakin kai tsaye, Tsaye tayi musu akai shiko jikinsa na rawa ya mike yana fadin”armm dama yanzu zan Fito..”harara ta ballamai kan tace”yanzu zaka fito dinta,daga baka minti goma shine kazo ka rashe ko? to maza ka wuce muje tunkafin na saba maka”tafada tana nunamai hanyar fita,jikinsa na rawa ya wuce yana waigen zahirah datayi kasake tanaganin abun mamaki batama san sadda ta leko da kanta ta cikin mayafin tana kallonsu dukkansu imani ya kamata,ganin yadda jikin Alhaji ke rawa,kyace uwarsa ne.
  Zai fita yace”ga sako nan aleda ki duba kinji ki kulle kofa sai da safe..”yafada yana ficewa da harara yaga ta bishi kan ta waigo tana kallon zahirah tace”Kinga sakamakon mai Auren mijin yagana kenan,wannan sharen fage ne,yarinya muje zuwa.”tana fadar haka ta dakamata tsaki ta fice ta banko mata kofa,kama baki zahirah tayi tana mamakin kafin ta mike taje ta sanya kofan makulli tana fadin”Allah ya raka taki gona..”tafada tana rike baki kafin takara cewa”Yo Allah na tuba ban da kaddara ai ni banyi kama da kalan wacce zata auri mijinki ba,inda kinga mijina wlh sai kin raina kanki”Tafada tana kyafci kafin ta yada lifayan nata bisa Gado ta fada tiolet lokaci daya abunda yagana da Alhaji sukayi yanzu yashiga bata dariya.
  Suko su hajiya suna komawa suka ga babu Ummi ba ushe basu wani tsaya tambayan ba”asi ba,suka samu abun hawa sukayi sallama da su mahgana da su Ashe suka wuce ana jajantama zahirah ganin yadda duka auren nata biyu batai sa”a ba,koda suka koma gida kowa ya kwanta ushe Tuni yayi barci,Shureim kuma yashiga da Baffa cikin daki suna ciki suna hiran duniya,suka shiga suna musu sannu da gida,suna shaida musu sun dawo,Yakura takoma ta rufe gida ta sanya sakata kafin takoma ita da hajiya suka dauro alwala suka shiga daki,nan suka ga Ummi kwance bisa gadon yakura tayi dif alamun tana barci,hajiya ce tace”oh suhaima har tayi barci ma..”yakura tace”dole munfa dade gidanan hajiya,jaraban matan nan yadau lokaci”hajiya ta karba da cewa”ummh kedai bari ba wacce nake tsausayama irin zahirah da yan diyan nan,don kinga ita bamai hayaniya bace..”haka sukayita jajantama zahirah kafin su hakura su kabbarta sallah,koda suka idar bayan Yakura ta shimfida musu katifa akasa tayi musu shimfida ita da hajiya suna mganar suka dasa suna mamakin jaraba irinta yagana,Ummi na jinsu tayi kamar tayi barci,ammh idonta biyu,tuni hawaye suka gama wankemata fuska kuka na neman kwacemata tayi Saurin damke bakinta kada su hajiya su jiyota,bakincikinta daya yadda jikokinta zasu rayu awannan gidan,ga yadda su hajiya ke zencen uwar gidan na zahirah bata da mutumci ko kadan,takaichinta daya komai ya faru dasu itace sila da bata raba uwarsu da ubansu ba da yanzu suna tare da iyayansu da ita kanta,ammh son zuciya da rudin shedan sun kaita sun barota,kuka take da hawaye tana sharewa.
______________
*Sudan*
  Babu shakka mu”azzam yasamu kwanciyar hankali matuka,domin mooh na debesa masa kewa matuka,yafita dashi ya xagaya dashi wurare,harta ma”aikatansu sai da yakaishi,Tsakaninshi koda lubna gaisuwace kawai bayan nan baya sakarmata fuska sosai,duk dai ita din kullum burinta ya dinga kulata,ko bamgana yake ta dinga sakamai baki kenan tana zagewa,Kuma ayawancin lokunta yasha kamata tana kallonsa,kuma koda ya kalleta bata kauda kai sai dai ta tsareshi da ido bako kyaftawa sai dai Shi ya kauda kai,sai dai tayi mirmishi tana kada kai ko ajikinta,Shiko mu”azzam yana lura da ita tsab,ko ranar yana daga sama yaga zuwan Dr sultan wajenta ammh tayimai Wulakanci,har mooh dasuke tare bayan sun dawo cikin gida ya shiga mata fada,kan wulakancin datakema,Dr Sultan Tura baki tayi tana fadin”ita batason Shi..,Tanada wanda take so.”
  Tafada direct tana kallon Mu”azzam wanda yayi kamar baijitaba,kuma da ganya ta fada,domin tarigaya data gama sanin she fall in luv kuma baba kowa bane sai na mu”azzam don kullum da tunaninsa take kwana tana tashi,ga tsananin tsausayinsa datakeji,inbata ganshi bata sukuni ko asibiti taje tana Sauri ta dawo ko dawowa tayi bata ganshi a falo ba zata bishi har dakin mooh tana gaisheshi Yana amsamata cikin sakin Fuska ammh daganan zai bata fuska tagama felekenta ta kara gaba.
  Abbie kuwa,yanata shirin zuwa Nagaria ne,sai da ya kammalla duka shirinsa kana yake shaidama mu”azzam kan yabasa Full address na gidansu achan Abuja Nageria,kuma yace yazamansa anan ko yaje bazai gayama Ummi yagansa ba sai inda yaje yadawo sai su koma tare,mu”azzam yaji dadin haka,kuma yayi na”am nan da nan ya rubutama Abbie full address din a takarda yabashi,Dama bayason komawa gida ayanzu saboda bayaso yakoma yaga hiransa tayi aure zuciyarsa bazata iya dauka ba sam.
  Kwana biyun da yin haka Su mu”azzam suka raka Abbieb khamis filin jirgi yadaga zuwa nageria Mu”azzam jiyake kamar yace zai bishi,saboda yadda yayi kewan Ummi da Shureim harda hajajju,ammh kuma kalubalen dake tattare da komawansa ne ke kashe mai karfin Gwiwa,ammh koma mene zai cigaba da fadama Allah komai yazo da sauki.
  Tare da lubna suka je,haka tun suna mota ta dinga nacinsa da kallo,tun yana basarawa harya Fusata yahade musu rai ita da mooh wanda keta mgana yana amsama sa a gajarce,ganin haka sai ya kyalesa yana tunanin kila baya son mgana ne a dat time din.
   Suna komawa gida ya wuf ya shige daki,domin yau babu shakka,an tonomai abubuwa daya game da rayuwarsa na baya kwanciya yayi Ruf da cikin yana Tunano rayuwarsa da zahirah ta baya,kowani dakika yana jin daci aransa,wani waje yayi dariya wani Wajen in ya tuna ya sharbe hawaye,haka ya wuni yana kwance ko mooh daya nemi su fita,kiyawa yayi yace yaje kawai yau bayason Fita.
_Comment dinku yafara yin low yanzu,wlh i hv a lot to do nake rage lokaci ina baku update kullum ammh yanzu kun rage sharhi kamar da,..Ina so nayi na kammallah ne kafin muyi resume skul,kuma ga tafiya agabana da zanyi,kuma da zarar na tafi bazan dinga samu time nayi muku typing ba gaskiya,so in kuna son update gobe kip ur commenting Janaf fans,in kuma kun rike kayanku,nima sai na rike update dina.,na hutama kwana biyu_😎
        *Janaftyjami*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

About Godswill

Check Also

MATAR GWAMNA Page 11 to 20

MATAR GWAMNA Page 11 to 20 …..d’agowa nayi fuskata na rike a tattausan hannunsa idanumu …

Advertisements