UWAR MIJINAH Page 41 to 50 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / UWAR MIJINAH Page 41 to 50

UWAR MIJINAH Page 41 to 50

UWAR MIJINAH Page 41 to 50

Shureim ya tabbatar tunda yaji muryan Ummi cikin kuka,to babu lafiya tuni zuciyarsa tazargi Ummi ta fuskanci abunda Mu”azzam ke boyematane,shiyasa yasakin ma motarsa gudu cikin lokaci sai gashi ya iso Abuja,hon ya zuba maigadi yazo ya budemasa get yana masa barka da zuwa.

Cikin hanzari ya fito daga motan yashiga cikin gidan,da Ummi yafara cin karo tana zaune afalo tayi tagumi idanunta sunchanza kala alamun tasha kuka kenan,tana jin sallamar shureim ta mike jikinta na rawa take fadin”Shureim ka taimake ni don Allah,wlh mu”azzam zai kashe kansa yau kimanin kwana hudu ko Fitowa baiyi ba,babu ci babu sha..”Takareshe fada tana tsiyayar hawaye.

Baisamu zarafin mata mgana ba, ya nufi shashen mu”azzam din yahau bugamasa kofa yana fadin”Dan”uwa kazo ka bude nine…”ammh ina mu”azzam na jinsu sai dai kuma baida karfin iya tashi saboda yadda jikinsa ya saki gabadaya jininsa ke zuba ta baki ta hanci ga yadda zuciyarsa ke zafi,yana so ma ya mike ya kasa.

Hankalin Shureim ya tashi da baya yaja yama kofar duka daya ta bude, da gudu suka rankaya shida Ummi cikin daki suna kwalamai kira,Ummi kuwa kamar ta zare tsabar rudewa,sun shiga bedroom din suna kiran sunansa ammh duk basu lura dashi yashe kan kafet ba,sai da Shureim ya duba tiolet nan ma babu shi kana yafito yana kokarin Ficewa daga bedroom din ne yaji ya shuru kafan mutum,cikin wani razana yakai kallonsa kan mu”azzam wanda gabadaya jikinsa ya baci da jini cikin wani karaji ya karisa garesa yana rikosa lokaci daya yake fadin”Mu”azzam…..”da karfi cikin tashin hankali.

Da gudun gaske Ummi ta kariso wajen ganin yadda mu”azzam yazama kamar mataccen ga jini duk yabatamai jiki ai sai ta dora hannu akai tasaki ihu tana fadin”Na shiga uku ni Suhaima, mezan gani haka mu”azzam?  tafada tana tale mai ido kamar wata zararra ganin haka yasa kawai Shureim Ficewa da sauri zuwa haraban gidan yana kwalama su Ushe kira da hanzari suka fito da hannu kawai yayi musu alamar dasu biyosa,suna shiga dakin suka tarar da Ummi durkushe gaban mu”azzam tana girgizasa tana kuka da sambatu,cikin Rudewa shureim yace”Ku taimakamana mukaisa mota..”Yafada muryansa na rawa suma din cikin Tashin hankalin suke da hanzari suka tallabeshi sukayo waje dashi,su karime dake tsaye suna ganin An Fito da yallabai kamar gawa ai sai suka rikice da kuka,Ummi kuwa kamar ta zare Amota suka sanyasa shureim ya shiga mazaunin Direba Ummi kuma dako takalmi babu balle mayafi ta shige baya wajen mu”azzam tana rumgume dashi tana kukan ta shiga uku.

Advertisements

Specialist hop,suka nufa,suna isa Shureim yayi ciki yana kiran Nurses da gudu kuwa sukazo da abun daukan mara lafiya suka ciccibi mu”azzam suka dora da gudu sukayi cikin asibitin dashi,kai tsaye aka shiga emaergency dashi cikin mawuyacin hali mai wuyar fassaruwa.

Ummi zaman dirshan tayi abakin emergency tana rusa kuka,shureim yakasa mata mgana domin shima kamar yayi kukan yakeji,tabbas in abunda yake zargi ne yakama mu”azzam lalle rayuwarsa tana cikin hadari,ganin Ummi tafara tara musu mutane ne yasa ya isa gareta yana fadin”Don Allah Ummi,kiyi hakuri kibar wannan kuka,taso muje ki zauna insha Allahu Mu’azzam zai tashi bazai mutu ya barki ba..”dagowa tayi ta kallesa idanunta suncika da hawaye tace”Haba shureim inbar kuka fa kace? baka duba da ni ya nawa rayuwar zata cigaba matukar mu”azzam ya mutu ya barni,wlh rayuwata,bata da amfani ina mai tabbatarmaka nima zaku iya rasani..”Tafada tana rusa kuka.

Kallonta yake cikin tabbatar da abunda ta fada,kafin ya riko hannunta ya mikar da ita yana fadin”Naji Ummi,ammh kitashi addu”anmu kadai yake bukata ba kukanmu ba taso muje ki zauna kinji..”Dole tatashi yana riketa da ita harzuwa kan wani benci ya zaunar da ita shima ya zauna agefenta yana sakin ajiyar zuciya lokaci daya,itako Ummi hannunta ta hau kirgawa kamar tana charbi sai muyi muyi take da baki hawaye na shatata bisa kuncinta.

Sun dade shuru kafin shureim yakatse shurun da cewa”Wai duk meyajawo wannan abun ne Ummi? ni a iya sanina Mu”azzam baita ciwo makamancin wannan ba.?.”Yafada yana kallonta,shuru Ummi tayi tana kallon kasa kan ta share hawaye tace”Takan na rabasa da wannan Tsinanniyar yarinyar mana,ashe ba haka tabarmin dana ba,sai da ta asirceshi kafin ta barshi..”Cikin Rudewa Shureim yace”Wa? zahirah Kike Nufi Ummi? badai kin saka mu”azzam ya saketa ba..?’wani banzan kallon Ummi tamai kantace”kwarai ni dakaina na saka ya saketa ,..”Tafada kai tsaye.

Shureim dayayi mutuwar zaune cikin wani yanayi yace”Kan wani dalili Ummi? Gefe ta kallah kan tace”Kan daliin cin amanata da sukayi yayi mata ciki batare da na sani ba,nikuma har abada bazan hada zuru”a da Diyar Fadi ba, har abada.”Tafada cikin son tabbatarwa.

Dafe kai shureim yayi yana fadin”Shikenan Ummi,kinyi sanadiyar dakushe Farincikin Mu”azzam,wlh tallahi zahirah itace ginshikin Farincikin rayuwarki data mu”azzam gabadaya..”Yafada cikin karaya wani banzan kallo Ummi tamai kafin tatashi ta chanza wajen zama tana hararan shureim din,shiko kallonta yake yana mamakin Ummi ashe haka tayi nisa baitaba sani ba,ki raba miji da mata,kuma harkina kirari da kanki,kai Tir da wannan bakar zuciyar,zuciyar da bazata kulla maka alkhairi kan mutane ba sai sharrinsu.

Wajen awa biyu likitoci suka kwashe da Mu”azzam kafin su fito cikinsu harda Dr.Abduljabar,office kawai yace Shureim ya biyosa,ummi na ganin haka tayi zuruf tabi bayansa kamar wacce akace dama bazata ji ba,suna zuwa office din Shureim ya zauna yana fadin”Dr,ya jikin Dan”uwa na hop dai ba abunda nake zargi bane..ko?”

Yafada yana kallonsa,jinjina kai Dr Abduljabar yayi kafin yace”Nayi matukar mamakin yadda Ciwon zuciya yakama brr,mu”azzam lokaci daya,wani irin tashin hankali ne ya gani ko ya faru dashi,wanda yayi sanadiyar taba masa zuciya haka..? dafe kai Shureim yayi yana fadin”hasbunallahi wa”ni imal wakil…”Ummi kuwa dake gefe ta dora hannu kai tana fadin”menaji kuna cewa,Son din nawa ne yakamu da ciwon zuciya,na shiga uku ni Suhaima tsakani na da Shettima Allah ya isa bazan taba yafemai ba..’ Tafada tana kuka ko kallonta Shureim baiyi ba Saboda yadda ta bashi Haushi,kina neman kashe danki da kanki ammh kina sakarci kin kasa ganewa.

Dr.Abduljabar ne ma ya shiga bata baki,shureim ne ya katseshi da cewa”Dr wht iz d solution now..? Dr Abduljabar yace”Munyi nasaran dawo da Numfashinsa,ammh yanzu yana bukatar jini gaskiya,kuma dole ne aguji tuna mai da abunda zai dinga tadamai da hankali,kuma don Allah abunda yake bukata ko yake son gani to ya kasance yana kusa dashi,gudun tashin ciwonsa..”Rausayar dakai Shureim yayi kafin yace”Abunda zai gani ya kwantar mai da hankali har ya sashi Natsuwa Ummi tayi sanadiyar da yayi mai Nisa na har abada..”yafada kai tsaye yana kuma kallon Ummi,wacce tayi Tsuru tana kallonsa,shiko ko ajikinsa illa mikewa da yayi yabama Dr hannu sukayi musabaha tare da fadamasa suje a dibi jininsa domin shi yana iya bama kowa.

Leda biyu na jini aka diba na shureim aka sakama Mu”azzam wanda ke daki na mussamam babu mai shiga sai likotoci,ko Ummi duk kwakwanta anki barinta shiga sai dai ta lekasa ta jikin glasa din daya ma dakin kwanya,har dare suna Asibitin bai farfado ba,daman Dr Abduljabar yace ana sa ran farfadowansa yau zuwa gobe insha Allahu.

Sai lokacin yaduba wayarsa misseds clls ruturutu,na zulaika dana hajiya yasani dole hankalinsu ya tashi har dare bai dawo ba,haraban asibitin yafita yaje cikin msallacin asibitin yayi sallolin dake kansa,kafin ya samu Natsuwar kiran hajiya,wacce yana labartamata abunda ke faruwa tana zaune ne,sai da tazamo kasa saboda tashin hankali cikin wani yanayi ta Furta”Innalillahi wa’inna Alaihirraju”un…,Ashe suhaima bata da hankali bansani ba,ashe Suhaima haka take bansani ba,ashe bata da wayau bansani ba,sakarya kawai mara tunani,taje ta kashe danta akan gabanta na banza,shettima ko yana asara kadan ne,ita sai tafi kowa kuka da shiga damuwa”Hajiya tafada kamar tama zahirah da mu”azzam din kwallah

Shureim yace”wlh hajiya sai ma kinga yadda dan”uwa yadawo kamar wanda ya shekara yana ciwo..”yafada kamar yayi kuka,hajiya tace”Allah sarki bawan Allah,ya hadu da jarabawar Uwa,Allah ya tashi kafadunsa..,”Shureim ya karba da Amin..Kafin hajiya tace”in ita Suhaimar..? yace”Tana cikin Asibiti tana ta ma mutane koke koke..”Tsaki hajiya taja kan tace”mtseww…Koke koken banzanta,ubanwa zata ma kuka bayan duk abubda ya faru itace sila,sakarya mara wayau,kai gobe ma Kabiru zai kawoni dole nazo nacimata mutumci,kuma saita bar asibitin nan,kada ma ya farka yacikaro da ita zuciyarsa tabuga ya mutu gabadaya..”Shureim dai hakuri yake ba hajiya ammh ta inda take fita dabam ta inda take shiga dabam,sallama sukayi hajiya nakara jadaddamai gobe tana tafe.

Advertisements

Dakyar shureim ya lallaba ummi,suka koma gida don wajen basu bukatar mai jinya suke kula da komai balle shi da ko ganinsa ba”ayi balle tace saboda shi zata zauna,koda suka koma gida yadda Ummi taga rana haka taga dare tayi kuka kamar ranta zai fita,shettima ko da fadi sunsha Tsinuwa harda na bala”i,koda gari ya waye tukan Ma shureim ya tashi tasaka Ushe yakaita chan Asibitin tana ko zuwa aka hanata shiga har kuka tayima Dr Abduljabar kan yabari tashiga,taganshi ammh yahana saboda dokace sai in ya farka,nan ta zauna tana lekensa tana share hawaye.

Karfe goma tayima hajiya baraka acikin asibitin dayake dama tasan Asibitin kai tsaye tazo,Shureim shiyazo yayi mata jagora zuwa wajen da”a ka ijiye mu”azzam,wanda shima bai dade da zuwa ba,Ummi tana ganin hajiya ta fashe da kuka tatashi zata rumgumeta hajiya takauce tana fadin”Karki sake ki tabani,kuka kikeyisuhaima,ai nadauka yadda zuciyarki takekashe da rashin imani bazaki taba kuka saboda halin da kika jefa danki da kanki ba..”Sororo Ummi tayi tana kallon Hajiya kan tace cikin kuka “Ni kuma yaya..? tafada tana nuna kanta.

Gyada mata kai hajiya tayi kan tace”Kwarai da gaske,ai bandauka haka kika zama mara imani ba da tsausayi,ace ki saka danki ya saki matarsa da tsohon ciki,kuma ki koreta a daren,haba rashin imanin naki Suhaima ya wucema yadda nake tsammani wallh..”Tafada ranta bace,dukewa kawai Ummi tayi tana kuka hajiya ko ta cigaba da cewa”bansan cewa haka sakarcin naki yayi yawa ba sai yau,ke aka cuta daga karshe suke da riba,domin kin saka ya saketa,takoma gida,sun karbi diyansu sun rike sunbarki da halinki,kuma ciki jikinta inta haifeshi,nasu ne ke kuma kinga kin,rasa farincikin danki gashi kwance rai a hannu Allah ,ke baga da”n ba kuma ke baga suruka ba,kuma ke baga jokokinki ba,duk kinyi batan batatatan,kin zabi ki durkushe rayuwarki da hannunki suhaima,wlh Tir girmanki da wayonki bai tsinana miki komai sai ci baya..”Hajiya tafada kwallah na ziraromata.

Ummi kuwa akasa ta zauna tana rusan kuka tana fadin”Na shiga uku ni yaya,taya zaki dinga ganin laifi na,wlh har abada bazan yi nadaman abunda na aikata ba” Tafada tana kuka t Hajiya tace’,Baki shiga uku ba tukunnah,Sai in dan naki ya mutu gabadaya kinga nan saiki lalace gabadaya,kuma nadama bayanzu nake sonkiyi ba Suhaima,sai lokacin Nadamar naki yazo lokacin nake so yi Nadama,”Tafada cikin bacin rai.

Suna cikin haka ne ,sai ga Dr,Abduljabar ya fito daga dakin da mu”azzam yake yana fadin”Alhamdullilah brr,ya farfado yana ta kiran wasu sunaye bansan wa yake Nufi ba,zaku iya shiga ammh banda dogon hayaniya plz”yafada kamar yana rokonsu,jinjina masa kai Shureim yayi yana fadin”Babu damuwa Dr.Mungode..”Ko gama rufe baki basuyi ba,Ummi tadanna dakin da gudu batare data tsaya jin bayanin likita ba,kallonta kawai sukayi suna kada kai.

Yana zaune akan gadon marasa lafiya,an gama masa karin jinin,tunjiya yanzu ruwa ake karamai saboda rashin babu komai acikinsa,jikinsa babu riga sai dogon bakin wando,fuskarsa ta zurma ya rame sai hancinsa daya fito zuruf dashi kansa na sunkuye Ummi ta fado dakin tana fadin..”my son..”jin muryan Ummi yasashi dagowa yana kallonta,itama shi take kallon tana hawaye ta karisa kusa dashi ta riko hannunsa tana fadin”haba my son,meyasa zakayi haka? don kasaki zahirah shikenan sai akace karshen rayuwarka ne yazo,meyasa nima bazaka min adalci ba ehe mu”azzam…”tafada hawaye na gangaromata.

Runtse ido yayi kafin ya bude ya saka duka hannuwansa ya tallafeta,kafin yasaka yatsunshi yana sharemata hawaye dakyar ya iya fadin”kiyi hakuri Ummi ba laifi na bane..”Abunda kawai ya iya cemata kenan ya sadda kai bisa kafadanta yanajin yadda kirjinsa ke suya,hajiya da shureim dake tsaye suka kariso hajiya na fadin”an ce bayason hayaniya Suhaima wata kuma mganar banzar kike fadamai,tunda dai nasan ba wacce zata kwantar mai da hankali bace”

jin muryansu hajiya yasashi dagowa ganin Shureim yasa shi fadin”Dan”uwa..”yafada yana mika masa hannu,kamawa yayi yana zama agefensa yana masa yajiki,hajiya ma ta gaishesa tana tambayansa ya jiki ya amsa da cewa”Jiki da Sauki hajiyarmu ,yaushe kika zo..’? tabe baki hajiya tayi tana fadin”ban dade da zuwa,nazo ne da takaicin abunda shashashar uwarka ta saka ka aikata..”Tafada tana hararan Ummi.

Mirmishi yayi mai ciwo baice komai ba,baki Ummi tatura batayi mgana ba hajiya tace”ai zuwa maiduguri yakamaki Dole kije kiyo masa bikon matarsa in kina son ganin danki cikin koshin lafiya”Daga mu”azzam har Ummi da kallo sukabi hajiya kafin Ummi taji sai yanzu taji dadin saki ukun data saka yayi mata da yanzu hajiya tasata tayi abunda batayi niyya ba.

Ganin sunyi shuru ne yasa Hajiya fadin’ko bazaki bane…? Mu”azzam ne yayi mgana cikin sanyi da takaichi yace”Hajiya ai zahirah ta haramta gareni..”Yafada cikin wani yanayi yanajin taruwan kwallah a idanunsa, Hajiya taji gabanta yafadi tace”Bangane ta haramta gareka ba,ba saki daya kayi mata ba?..’girgiza kai mu”azzam yayi kafin ya Furta chan kasan makoshi”saki uku ne hajiya..”yafada yana dora kansa akafadan shureim saboda yadda yakejin wani hajijiya na yawo dashi.

Salati hajiya da Shureim,suka saki suna sallallami hajiya kasa mgana ma tayi ,sai kawai ta fashe da kuka tana fadin”wlh Suhaima hakkin danki bazai barki ba,sai ya bibiyeki,da hakkin yar marainiyar Allah wlh sai kin karbi sakamako gurin Allah..”tafada tana share hawaye,Ummi kuwa dukar dakai tayi ko ajikinta murna ma take daya kasance haka,hajiya babu yarda zatayi da ita yanzu.

Cikin Kasala da ciwo mu”azzam yace”Ta haihu jiya,babanta yakirani yake fadamin ranar da ciwon nan zai kwantar dani..”yafada yana yi baya ya kwanta saboda kwallar data cikamai ido gyaramai filon Shureim yayi yana mai sannu,washe baki hajiya tayi ga hawaye tace”Allahu akbar kaji ikon rabba ko,me aka samu.?.”yana daga kwance yace”twins ne mace da Namiji yace..”guda hajiya tasaki tana kallon Ummi tace”Allah na gode maka,duk wanda yakeja da ikon Allah,karshenta rai ya kashe mutum..”tafada kanta tsaye shureim ma baki ya washe yana fadin”congrat dan”uwa..Allah ya rayamana yaranmu ka kamoni fa”yafada yana dafa hannunsa mirmishi kawai mu”azzam yamai baiyi mgana ba

Mikewa hajiya tayi tana fadin”Maza tashi Shureim bama zauna ba,tashi mudau hanya kada suce munyi banza,tunda ga yadda al”amarin yakasance mu sai muje muyi barka mukuma bada hakuri..”jin haka yasa mu”azzam dagowa yana fadin”nagode hajiya..,dan”uwa kafin ku tafi kace karime tashiga dakin hirah ta kwasan mata kayanta na sawa harda wayanta duk ta baku ku kaimata”Yafada wasu zafafan hawaye na zubomai,hannusa shureim ya riko yana fadin”karka damu dan”uwa anything will be alright kaji kacire damuwa aranka insha Allahu kamar kai da kanka ne kaje”yafada yana share masa hawaye gyada masa kai kawai yayi kafin ya runtse ido,ko takan Ummi basu bi ba, suka wuce,gun Dr.Abdujabar sukaje,suna magana da shureim,nan hajiya tace”maza ya tura Nurse taje tace Ummi ta fito saboda yana bukatar hutu,saboda wlh aka barta sai ta karisashi kafin su dawo,dariya kawai Dr,yamata kafin ya amsa mata da toh.

Aiko suna tafiya ya tura Nurse tayi waje da ummi wanda,daman suna fita ya mata barcin karya don yanaji tana ta kiran sunanshi yayi mata banza,kamar yayi barci,don shi yanzu babu abunda ummi zatayi ta burgesa,lokaci kawai yake jira ya aiwatar da kudirinsa,don babu yadda za”ayi ya iya rayuwa agarin da babu hiransa ba.

Saida,suka biya suka karbi duka kayanta,wanda karime ta hadamata akwati sai da ta cika harda ko wayanta aka hado da ita,suka damki hanya ushe ne ya tukasu,don shureim bai dogon Tuki,wajajen karfe daya suka damki hanya bayan sun biya wani shagon kayan yara shureim yayi barnar kudi,ya siya kayan sai da booth ya cika,dayake basu wani yi tsaye tsaye ba shidda na yammah sai gasu akofar gidan shettima wanda sai dai suka gansu kwatsam sun shigo,hajiyace kan gaba tana rafka sallama da yakura suka fara cin karo wacce tarike baki tana kallonta kan tace”Hajiya baraka..”

Tafada wit ful suprise Afuskarta.

_*My Sisi of Life AISHA ALTO,Jinjinarki ta dabamce sisina,wlh har cikin raina nake farincikin haduwata dake, masoyiyata,Allah ya cigaba da dafa miki,kamar yadda kike dafamin,tanque so very much ina yinki tawan over wlh*_

*DON”T FORGET TO VOTE,COMMENT AND SHARE..It me Janafi*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer’s Asso*✏

_*Your limitation..Its only ur imagination*_
_*push urself,bcus no one else is going to do it for u..,Sometimes later becomes Never….Great things never come From comfort zones…*_
_*Dream it,…*_
_*Success doesn’t just find you…The harder you work for sometings The greater you’ll Find when you Achieve it.*_

*NOT EDITED*💥

*NO 26*

Itama hajiya cikin murna tace”yakura..”tafada tana mata mirmishi sauke hannu yakura tayi tana musu maraba ganinta ba ita kadai ba,daki suka shiga tana musu sannu da zuwa sheetima dake xaune gefe kan sallaya ya dago yana amsa sallamansu.

Tabarma yakura ta shimfida musu kan kafet din dake tsakar dakin tana musu maraba,zama sukayi Shureim ne ya mikama baffa hannu sukayi musabaha,suna gaisawa kafin yajuya kan hajiya su shiga gaisawa gyara zama hajiya tayi tana fadin”Kunganmu da yammh ko..? yakura ta kadai kai tana fadin”ba abun  mamaki bane hajiya,ganin ai maiduguri ma gidace agunki..”tafada tana dan dariya.

Mirmishi hajiya tayi tana fadin”kwarai kuwa,gidace agunmu balle yanzu da mukayi jikoki zuwa kam sai an gaji damu..”Tafada cikin murna yakura tace”aikam hajiya sabuwar amarya na nan na jiranki,dakuma sabon megida”tafada tana dariya cike da zolaya,dariya hajiya tayi tana fadin”Sai dai nayi maraba da sabon miji ammh banda sabuwar amarya kam..”dariya sukayi gabadaya hadda shettima.

Ruwa Yakura ta kawomusu da lemo hajiya tasha ruwa kafin tagyara zama tana fadin”ina maijegon ne,banji kamshi kunun kanwar masu jego bane?..”yakura tace”Ayyah ai masu jego suna GRA mahaifinta tun washegarin haihuwar yazo yatafi da yarsa..”Tafada ranta babu dadi,kada kai hajiya tayi tana fadin”ikon Allah,to haka kuma akayi,sai hakuri shettima wlh ba laifin mu”azzam bane,yaron ma yana chan agadon asibiti rai ga hannun Allah..”,tafada tana share kwallah.

“Ashhh….”shettima da yakura suka fada suna masu jimami kafin shettima yace”subhanallahi…,Allah ya bashi lafiya,bakomai hajiya nasan ba laifinsa bane,ni azatona Suhaima ta manta baya ta fuskanci gaba,ashe ita haryanzu bata manta da abunda ya faru ba..”yafada cikin karaya gyara zama hajiya tayi tana fadin”Shirme ne,kawai ammh ina amfanin mugun riko kamar ba musulma ba,wlh Shettima bani da lbrin abunda Suhaima ta aikata sam,bakaji yadda naji danaji lbri ba,don Allah kuyi hakuri haka Allah yaso..”

Kada kai shettima yayi yana fadin”Babu komai hajiya kaddararce babu wanda ya isa ya gujema kaddaransa..Allah ya shigemana gaba..”da Amin suka amsa kan hajiya ta cigaba da bama yakura hakuri,shiko shettima yana jinsu bai kara cewa komai ba,saboda yadda abun ya dakesa lokaci daya,ga kuma ciwon da”akace mu”azzam yana fama dashi.

Basu wani jima ba,sallar mangariba kadai sukayi, yakura ta rakasu har gidansu zahirah,bukar na gidan yadawo yana falo yana cin abinci suka shigo,bawani sanin hajiya baraka yayi ba shureim dai ya gane,yakura ne tayimai bayani,am amshesu Fuskar dai bawani Annuri mussaman bukar,suna gama gaisawa hajiya ta zube kasa tana fadin”don Allah bukar kayi hakuri ka yafema yaron nan,ko daya kada ka kullacesa ba laifinsa ba,laifin mahaifiyarsa ne,da mugun rikonta yaron ma yana chan tunda abun ya faru bai kara lafiya ba..”Tafada tana matse hawaye.

Jinjina kai bukar yayi kafin yace”Ban kullacesa ba hajiya ko kadan,kawai haushin danaji boyemin halin da yata takeci da yayi,ai ba A aure dole dai ya sakomin ita tadawo gida ba cemata akayi na gaji da ita ba,ko kuma bata da gata ba,kawai bazan iyama baffa musu bane,ammh harga Allah ni banso Aurar da diyata ma alokacin ba..”yafada cikin takaichi kafin ya cigaba da cewa”Banda ma jahilci meye ruwan zahirah da gabanta da baffa,inace mahaifiyarta ta rasu da dadewa,ammh ace shi bawa bai manta ba,saboda rashin imani tasaka asakomin y’a cikin dare bayan danta kuma ya dirkamata ciki,tsakani ga Allah hajiya anyi adalci,ko kene ya zakiji aranki in akama diyarki haka..”yafada ransa na kuna.

Kada kai hajiya tayi tana fadin”bazan ji dadi ba ko kadan bukar,toxarcin ai yayi yawa,shiyasa nazo dakaina,in bada hakuri,wannan dan”uwansa ne ya wakilcesa tundashi yana chan baida lafiya,don Allah kuyi masa aikin gafara..”shuru bukar yayi kafin yace”Babu komai hajiya hakuri duka namu ne,Allah ya kyauta gaba ya’ce tasa ansakota kuma na karbi kayana,tana arba”in zan daura mata aure taje inda ake sonta dakuma darajata,danta kuma ta jika tasha..'”Yafada da son nuna abun bai damesa ba,hajiya dai hakuri tayi ta bashi shikuma yana cemata babu komai ammh yana yabamata mgana cikin mgana ga duk alamu dai an Tunzura bukar matuka.

Maghana ya umarta data kai su dakin da zahirah take,shikuma shureim waje ya fita ya umarci Ushe daya shigo da kayan da sukazo dasu,haka ko akayi tuni yayi ta jidan kaya yana jibgewa afalo,kayane nagani na fada kamar za”a bude shago,bukar yana tambayan daga ina Shureim yace”Su suka zo dashi..”ada yaso yace su koma dashi ammh kuma girman hajiya yasa yayi shuru da bakinsa.

Tana zaune akan gado tana bawa Maccen nono,sanye take da riga da zani na wata holland mai ruwan ganye,kanta na kasa tana kallon yarinyar yadda ta bude ido tana kallonta,Namijin ko na gefenta shima yana wutsil wutsil yanaso yayi kuka,su hajiya sukayi sallama suka shigo maghna ne agaba,kana hajiya da Shureim dake take mata baya.

Da mamaki zahirah ke amsa sallaman hannuta abaki tana fadin”La..Hajiya, yaya Shuriem..”Tafada tana bayyana mamakinta lokaci daya tana cireta anono bayan ta maida rigarta karisowa sukayi lokaci daya hajiya tana zama kusa da ita tana fadin”Allah sarki diyan nan baki yi Fushi damu ba ko.?.”tafada tana daukan maccen dake jikinta ta mikama shureim itakuma ta dauko Namijin tana fadin”Allah sarki Allah kenan mai yadda yaso alokacin daya so…”Tafada lokaci daya tsausayin zahirah da yaran ya dabaibayeta harda na mu”azzam din shikanshi.

Sunkuyar dakai zahirah tayi tana wasa da kwalliyar rigarta batayi mgana ba ammh idanunta sun cika kwallah,kallonta shureim yayi yana fadin”ya jikin ki..”? yafada cikin kulawa kanta na duke tace”naji sauki,kunzo lafiya” ya amsa mata da lafiya kalau,hajiya ce keta kallon ya”yan tana fadin”Suhaima kin zalunci kanki,kin kori ni”imar ubangiji daga gidanki,ina zaki kai hakkin yaran nan,ki rabasu da ubansu gashi sunzo duniya ammh bai samu ganinsu ba..”take ta fada tana share kwallah kan ta kalli zahirah tana fadin’yan”nan kiyimana aikin gafara don Allah,wlh banda masaniyar aikin da suhaima ta aikata gareki,harga Allah tamkar mu”azzam haka na daukeki,Allah yabaku ikon cinye jarabawanku,yakuma baku juriya da hakuri…”tafada tana dafa kanta.

Wasu hawaye masu zafi suka zuboma zahirah tayi saurin gogewa ammh ina wasu nema suka kara bulbulowa tana so tayi mgana ammh takasa saboda yadda ranta yake mata daci ,in ta tuna da tarabu da mu”azzam rabuwa na har abada,kuka ne ya kwacemata ta kife kanta tana rerawa,kuka mai ban tsausayi ga wanda yake saurare,mikewa hajiya tayi ta fice dauke  da yarinyar tana hawaye dominn tsausayin zahirah bazai barta tacigaba da zama ba,shureum dake tsaye ya kalleta yana fadin”Sai hakuri ,shima din yana chan cikin halin ciwon tun bayan barinki,yanzu haka yana kwance a asibiti tun jiya..”

Da hanzari ta dago idanunta jawur tace”Yana asibiti kuma..”? tafada cikin tashin hankali gyadamata kai shuriem yayi yana fadin”shiyasa bai samu zuwa ba,saboda abunda ummi tayi yasa ya samu hrtfailure..”hawaye suka gangaroma zahirah tace”Don Allah kakira minshi awaya,nima wlh ban kara kwanciyar hankali ba,tun bayan tahota,kowani dakika yana raina,wlh ya shureim bazan iya rayuwa babu ya mu”azzam ba,ganagar jikina ce kenan maiduguri ammh Ruhina da zuciyata suna Abuja wajen ya mu”azzam..”Tafada tana fashewa da kuka.

Shureim dake tsaye saboda tsausayin masoyan biyu sai da yaji kwallah ta tarun mai, “Don Allah kakira minshi ka taimakeni indai kanaso hankali na ya kwanta..”Tafada cikin wani yanayi ganin yadda take kuka ne yashashi cemata”is ok stop craying share hawayenki bari na kira wayar Dr.Yakai masa don babu waya atare dashi..”jin hakane yasata sauke ajiyar zuciya tana share hawaye.

mikamata yaron yayi yana fito da waya lokaci daya ya lalubo Dr.Abuduljabar bugu daya ana biyu ya dauka,bayan sun gaisa yanemi alfarman sonyi magana da Mu”azzam,sai da Dr.Abduljabar yayi shuru kafin yace’Ok..ya dates kiran,minti biyar shureim ya bashi ya sake kira sai ga mu”azzam yadauka murya shake yana fadin”Dan”uwa kun isa ne..? yafada cikin halin ciwo

Gyada masa kai yayi kamar yana ganinsa yace”eh tun dazu gani ga twis wlh so fine dasu dan”uwa sai ka gansu ma..”rau rau mu”azzam yayi kafin yace”da gaske..? wlh Kuwa,zan dauko ma hotonsu macen wlh yadda kasan photocopyn ummi ce..”Wani yarr mu”azzam yaji kafin yace”Allah na godemaka,ina mamansu..”yafada gabansa na fadi,shuriem yace”Gata nan,itama ta matsa sai an kira mata kai,ammh plz dan”uwa try to be a gentle man kadai san Condtion din dakake ciki ko..”?Nasani..”yabashi amsa muryansa cikin karaya.

Mikata yayi wanda dama tuni ta zaku ji take kamar ta fizge wayan tana karba ta saka akunni lokaci daya tace” Ya mu”azzammmmm….”Tafada cikin karyewan murya kafin kuma kawai ta sanyamai,kuka shuriem dake gefe yayi saurin ficewa saboda bazai jure ganin wannan masoyan ba masu neman mutuwa kan juna.

Mu”azzam dake kwance wani yanayi yaji yana shiganshi muryan hiransa dabam take acikin mata,ko cikin dubu ta fita dabam,kwallah ta tarunmai a ido yana so yayi mgana yace ta bar kuka ammh yakasa saboda kowani dakika kukanta cinmai rai yakeyi gani takiyin shuru yasa yayi karfin halin cewa..”Zan kashe wayar indai bazaki daina min kuka ba..”yafada muryansa tafara hardewa shima kukan yakeson yi.

Jin muryansa cikin halin ciwo yasa ta danne kukanta takoma tana ajiyar zuciya dan mirmishi yayi kafin yace”maman Twins..”yafada cikin kasala tura baki tayi kamar yana ganinta tace”Ni ba wannan ba ya jikinka..”? rausayar dakai yayi yana fadin”Ni lafiyata kalau,wayace miki banda lafiya.”yafada cikin dauriya.

“Ya shureim yanzu yace kana ma asibiti tun jiya..”Girgizamata kai yayi yana fadin”Ba gaskiya ne,ni ina gida abuna..”rausayar dakai tayi tana sharan kwallah tace”mezaka boyemin ya mu”azzam? wlh tallahi halin daka ke ciki shi nake ciki,zuciyata tana zafi duk sadda na tuna mun rabu kenan,..”Tafada tana kara sakamai kuka.

Runtse ido yayi jkinsa na rawa yace”yi shuru Hirata bamu rabu ba,kuma bazamu taba rabuwa ba har abada..”yafada hawaye na gangaromai kafin yacigaba da cewa”basan haka zuciyata ta kamu ta mtsanancin sonki ba hirata,sai da kika barni bansan haka jikina ya shaku da jikinki ba,sai da kika barni,wlh tallahi rayuwata bata da wani amfani matukar baki cikin zahiri na,Baki ganni ba na lalace akanki wlh ummi batasani bane takusa rasaniii….”Yafada muryansa na fitar da amon kuka,zahirah ma kuka take tana fadin”ni wlh bazan yarda arabamu ba, kazo ka daukeni mu gudu muje mucigaba da zamanmu..”Tafada cikin kuka.

Abunda tafada din ya bashi dariya har saida ya murmusa yana fadin “Zanzo hirata insha Allahu kidaina kuka kinji,share hawayenki matar mu”azzam..”yafada cikin sigar lallashi,tura baki tayi kan tace”to shima mijin zahirah yadaina kuka..”tafada cikin shagwaba har sai da tsigar jikinsa ya tashi,da sauri yacemata “Na bari Allah hirata..'”Yafada yana goge hawayensa.

Gefe tayi dakai Tana fadin”Don Allah kabar damuwa,saboda kaga baka da lafiya kaji,kayi ka warke kazo kaga kyautar da Allah yayi maka..”Lumshe ido yayi ya bude yana fadin”Toh zan daina ammh sai kema kin min alqawarin zaki cire damuwa aranki,kikular da min yarana lafiya..”hawayen idonta ta share tana fadin'”Na maka alqawari yaya..”tafada da son tabbatarwa.

Namijin dake hannunta ne yashiga tsandara kuka mu”azzam na jinsa,tuni jikinsa ya sake mutuwa,kirjinsa na wani zafi cikin karfin hali yace”Ki daukesa mana..”tace”ai yana ma hannuna ne fa yaya,kawai rigimarsace ta motsa,yafi,macen rigima fa..”dafe kai mu”azzam yayi dayake neman rabemai gida biyu yace”Ki bashi abincisa malama,yunwa yakeji shine zaki fake da rigimarsace tatashi ko..”Yafada da sigan zolaya.

Dariya ta kyalkyacemai dashi tana fadin”Uhmm Kaji masu ya”ya..”mirmishi yayi kawai domin karfin hali kawai yakeyi,jinta cikin Farinciki yafi mai komai dadi,gyara kwanciya yayi yana fadin”wasu sunaye zamu sanya musu..”shuru tayi kan tace”Macen asamata Sunan UMMI tunda dama mai kama da itane,Namijin kuma zabi na gunka angon karni..”Tafada tana yar dariya.

Wani abu yaji aransa,Sunan Ummi,ashe har zahirah zata iya cewa asakama yarta data haifa da cikinta sunan Ummi,duk bayan dibim Abunda Ummin ta aikata mata,lalle zuciyarta mai kyau ne,cikin zubar hawaye yace”Nagode my Hirah da wannan kararramawa naki,kifadama shuriem yayi mata huduba da SUHAIMA ummina,sai Namijin yayi mishi huduba da MUHAMMED MOODU Abbana,duk da bantaba sakashi a idona ba,sai ahoto..”yafada muryansa tana bayyanar da kukan dayakeyi

Itama saitaji kukan yazomata tace”Kabar kuka,ko nima yanzu nafara maka nawa.,yazamuyi Tunda Abunda Allah ya kaddaromana kenan ammh wlh ya mu”azzam bazan iya rayuwa bai dadi baka ba,kaine ginshikin rayuwar zahirah na har abada..”tafada tana share hawaye,dafe saitin kirjinsa yayi kafin yace cikin wani hali..”Nasani hirata,Nima anan bamgaren haka take,rayuwata zata lalace matukar baki dawo gareni ba” zahirah tana hawaye tace”To taya zan dawo gareka bayan saki uku kayiman..”wani numfashi mu”azzam yaja kafin yace”Bansani ba,wlh bansani ba hirah..Ki kwanta kiyi barci sai munsake yin mgana I LOVE U SO MUCH..”yafada yana kafafunsa narawa.

Jikinta na tsuma tace” LOVE U MORE AND MORE YAYANA..” tafada tana kamkame wayar kawai sai ta fashe da kuka shima kamkame wayar yayi yana mirgina bisa gadon yana zubar kwallah,jin yadda kirjinsa ke suyane ga saitin zuciyarsa na harbawa yasashi katse kiran.

Kuka Zahirah ta fashe da shi,sai da tayi mai isarta kana ta hakura ta share hawayenta,Koda su hajiya suka dawo dakin shureim ya sake kiran wayar Dr.Nan Mu”azzam din da kansa yake fadamasa cewa ga sunanyen da zai ma yaran huduba dasu,yayi mamakin jin sunan Ummi abakinsa,ammh ganin uwa fa ta wuce wasa yasa yayi shuru da bakinsa,to hakan ta kasance ga kowa,duk wanda yaji yarinya taci sunan ummi sai yayi galala da mamaki ko bukar din ma yayi mamaki ammh sai zahirah ta shanyesu mamakinsu da cewa ita tace tana son Sunan,to wazai yi mgana Bukar yaji aransa shima yayi sa”ar samun diyata gari,koba komai ta rama sharri da alheri,kuma ya tabbata in taji sai jkinta yayi sanyi.

Shureim yayi musu huduba da sunayensu,gidansu Baffa shettima suka koma suka kwana bayan Shureim ya ijiye musu Dubu dari biyu cash na wanda xa”a siyama yara ragunan sunan,da sauran abun amfani,bayan uban siyayyar daya narkamata bayan sun damkamata kayanta harda wayanta da sukazo dashi,shureim dakin baffa ya kwana Ushe kuma dakin kofar gida aka gyaramai ya kwanta aciki, itakuma hajiya dakin yakura ta kwana wanda sun kusa raba dare suna jajantama kansu dakuma yadda rayuwar masoyan biyu zata kasance,sundai yi fatan Allah ya yayyafama soyayyar ruwan sanyi Allah kuma ya kauda mummunar kaddara.

Gari na wayewa karyawa kadai sukayi suka dau hanya wanda yakura taso su tsaya hajiya taki saboda aikin shi Shureim din,kuma da yadda suka baro jikin mu”azzam din babu dadi,ko gidan bukar din basu koma ba suka kamo hanyar komawa Abuja,sai Fatan Allah yakai lafiya,sunbar garin Ranar da”aka yankama yara firda firdan raguna yan”uwa da abokan arzuka suka taru ana shagalin taron suna,koda ma su Shureim basu zoba tuni bukar ya tanadarma yarsa komai itada yaran,ya siya musu kaya na alfarma shiyasa ranar ta dinga shiga tana fita,ammh duk wanda ya ganta sai yayi fadan maijego da rama,to bata wani cin abinci ga tsotson yara,duk da ma ana hada musu madara,Zahirah kuwa Ranta gabadaya wuni yayi ba dadi,data zauna tayi shuru sai kwalkwal kuka,babu wanda yayi yunkura hanata saboda ansa dalilinta na kuka,to yazatayi sai hakuri,tunda tahadu da uwarmiji mara imani ta maidata karamar bazawara,haka yan”uwanta keta cewa,haushin abun na damunsu suma arai kawai basa nunawane.

Tuni yara Sukaci sunayensu *SUHAIMA IBRAHIM MOHAMMED MOODU* Da *MUHAMMED IBRAHIM MUHAMEED MOODU* Sai fatan Allah ya rayasu cikin tafarkin addinin isalama,da kuma fatan Allah ba maijego lafiya mai dorewa Amin,yan group din janaf novella sun hallarta dasu da yan Uwar mijina fans1,2and3 ammh basu wani samu tarba mai dadi ba jin daga tawagar Ummi ce sukazo babu wanda yayi musu kallon arziki ba don ma bukar ya kwaba ba yasin cikin gidan nan da ansamu mai chanza wasu daga cikinsu halitta saboda Yadda suka Fusata da wulakacin da akama yarsu,jagoran Tafiyan my Sisi ce Aisha Alto da sahibata hafsat hafnan,ai jiki ba kwari suka dafafo hanya fuskar ba Annuri saboda haushi biyawa gaida mu”azzam din dasukace zasuyi ma ba wacce tabada fuska,kowacce gidanta aka sauketa jiki a sanyaye😂😛😝😜

______________

Su hajiya kuwa koda suka dawo achan asibiti suka tarar da Ummi duk da sau uku arana ake barinta shiga,tunda yau da safe yafara cin abinci,to tea kadai ma yasha,shima bada yawa ba,saboda yadda bai iya jin dadin komai abakinsa,Ummi kuwa sai jidashi take tana wani riritasa shiko kallonta yakeyi yana jin haushi abunda takemai,ta riga tagama kashemai rayuwa kuma lallabansa metakeyi ai data barshi ya karisa mutuwa yahuta itama tahuta.

Abunda ya dauremai kai zama tayi tana lallabansa da yayi hakuri ya kwantar da hankalinsa yana warkewa tayimai alqawarin auramai mace,wacce tafi zahirah sau dubu ,wacce zata dace dashi,kawai yabata lokaci sai ta sanyasa farinciki fiye da yadda baya tsammani,da toh kawai ya bita,ammh aransa yana fadin Ummi bata kaunarsa ya yarda to Wlh sai dai ta aurama kanta Auren ammh badai shi,shi in ba hiransa ba to yayi alqawarin dauwama haka har abada,domin duka sauran mata maza yake kallonsu Hiransa ce kadai ta fita dabam,komai nata dabam ne dana sauran mata,zuciyarsa tana cigaba da suya shiyasa cikin ransa ya yankema kansa mafita ya gwammace ko zai Mutu to yayi nisa da Garin ila ma da Kasar gabadaya ,don dai ya cigaba da zama anan har ya tsinci lbrin hiransa zatayi aure da wani to ya tabbata adaren zuciyarsa zata,buga ya mace.

Kwana daya su hajiya suka kara suka wuce,batare da sunfadama mu”azzam yadda bukar yadau zafi ba,hajiya dai tayita lbrin yan biyu da gayyah saboda Ummi,wanda ko ajikinta don ko a mafarki ma bata kaunar ganin ya”yan duk da mu”azzam ya haifesu ammh batajin zata sosu domin tsanar uwarsu ta shafesu,shiyasa ma batama bi takansu ba balle ma hartaji harda sunanta akasa da hajiya tafara zata fice ta basu waje,tana wani cin mgani abunta,Sunkoma saboda aikin shuriem yana ta samun waya daga wajen aiki ga gida kuma ambar Zulaika ita kadai,daga ita sa yara,dole tasa suka tafi,bayan hajiya tayima Ummi fadan kiyayen harshenta,gadai da’n nata nan data ke Tunkaho kwance ba lafiya in ta gyara rayuwarsa ta gyaru ita kara batamawa itace zata sha wuya tadai amsa da taji kawai,ammh har aran Ummi wani kudiran ne ke ranta na dabam.

*******

*BAYAN SATI DAYA*

Zahirah da kanta ta kira Asma”u wacce kewaar zahirah ya isheta,tayi ihun murna sanda zahirah ke fadamata ta haihu da abunda aka samu,ammh tayi kukan jin sakin wulakancin da Ummi ta saka akama zahirah wanda har taci burin duk randa ta hadu da Ummi saitaci mata mutumci,Asma”u tazama so cool a mkranta ba zahirah gashi watanni kadan yarage su rubuta SSSE in ta tuna haka batasan sadda hawaye ke zubomata,Itakanta Mami ta tsausayama zahirah sosai tana fadin”Yarinya karama tahadu da jarabawa iri iri na rayuwa,mami da kanta tayi ma minista mgana zasu maiduguri,domin Kawance ai baice haka ba,nan da nan ya Amince suka tashi tundaga Abuja har maidguri da abun arziki niki niki Lalle yan maiduguri sunga kauna,don kwana biyu su mami suka musu kafin sukoma ,bukar yaji tsananin Farinciki ko bakomai zahiransa ba tazama wani abu,yau gashi ta dalilinta har diyar minista da matarsa suzo gidansa suyi kwanaki domin yarsa lalle Allah Abun godiyane,Zahirah ko taji dadin zuwan Asma”u ko bakomai tasamu wanda zasu tattauna matsalanta da ita,tayi kuka sosai Asma”u na bata hakuri,domin fa babu yarda suka iya kaddarace ta riga fata.

Suma da zasu koma sunga karramawan dangin Zahirah don suma sunhada musu komai iya karfinsu suka rabu suna godiya,sun cigaba da waya da Asma”un zumuncinsu ko saima yafi da karfi.

___________

Sati daya Mu’azzam yayi a asibiti kafin asallameshi ya dawo gida,bayan yasha dokokin likita,na cire damuwa aransa,kuma yadaina zurfafa tunani da yawan zama shuru,yakuma kiyaye duk abunda zai bata maasa rai ko na mutum kona Tunani,duk ya gujesu dakuma samun ishasahen hutu,dakuma shan mgani bisa ka”ida,Duk ya amsa da toh ne kawai ammh shi yanzu taya zai iya daina tunani ai har abada an gayyato Tunani,ckin rayuwarsa ne Tunda aka rabasa da hiransa.

Kwana uku da dawowansa gida Ummi tana ta bare baren kula dashi ,karewartama dakinsa tatare ko tari yayi tadinga tambayan lafiya kenan,jama”a nata zuwa gaishesa expecially yan wajen aikinsu,gaskiya babu laifi ya samu sauki sosai tunda bai fara tsallake dokar likita ba,shima burinsa ya mike ga kansa,saboda ya aiwatar da kudirinsa domin babu gudu ba ja da baya.

Satinsa daya da dawowa gida ya tuburema Ummi shi zaikoma office,to ganin yadda take kan lallabasa tasamu ya manta da tsinanniyan yarinyarnan shiyasa ta yarda yakoma Aranar,wanda daman shima ba aiki zai kaishi ba letter ya rubuta musu na barin aiki na dan wani lokaci ma”ana Leave without pay kenan,matukar razana ma”aikatar ta razana da ganin sakon mu”azzam ko abokan aikinsa sunyi sunyi sun janyesa daga kudurinsa yaki,yace musu zai tafi karo karatu ne,to ammh abunda yabasu mamaki shine ita da kanta ma”aikatar in taga chanchantar mutum takan Turashi da kanta karo ilimi ammh shi farat daya kuma lokaci daya yace zai tafi abunda da mamaki,babu yarda suka iya illah binsa da fatan alheri.

*DON’T FORGET TO VOTE,COMMENT AND SHARE..It me Janafi*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer’s Asso*✏

_*Wannan Shafin kachokan mallakinku ne JANAF NOVELLA..mussaman masu sharhi,Fadila falalu maska(my Adila)😘,My Ummu kursoom(Abulkursoom)😍,my juwairiyyah Rogo❣,Mum khady(Kakata)💙,Malika masoyiyata❤,Suwaiba Husna,Aisha,Fatima,Abida mahamood(Anty momi)💖,Queen Aisha,Aysher,Safiyyah buhari*_
💕, _*Raliya mk,zainab Abdullahi,Anty khadija,..Kunada yawa wanda baki bazai iya furtaku duka ba,ammh duk wanda ke cikin group din Na janaf novella,ina mika godiyata garesa Allah yabar zumunci da soyayyar na har abada*_

*NOT EDITED*💥

*NO 27*

Koda yadawo gida ko Afuska bai Nunama Ummi ba,illa ma biyemata dayayi sunata hira,ya warware kamar bashi ba,Ummi taji dadi rantayayi fari, tana fata Addu”artane taci na mu”azzam yafara manta da mayyar yarinyarnan data tafida kurwansa maiduguri.

Washegari duk wani shiri nasa ya kammallah sa,kaya ko kala daya bai dauka ba,daga shi sai briefcase dinsa ya fito cikin shigansa na American Suit masu ruwan toka,ya mtse wuyansa da tie kafafunsa sanye cikin Rufaffun takalmana na fatar damusa,hannunsa kuma sanye da agogo na kamfanin Rado,fuskarsa babu Annuri ga idanunsa da suka kumbura saboda kukan daya sha jiya da daddare,har Ga Alla ba”a son ranshi zai yankema Ummi wannan Hukuncinba,domin tunda ya girma yayi wayau baitaba nesa da itaba,Tare suka rayu,akwai shakuwa da soyayyah ta uwa a tsakaninsu mai girma,wacce dalilin hakan yakeji kamar bai kyautama Ummi ba,ammh kuma zuciyarsa tana bukatar hutu,zaman agarin nan Tamkar dawo da hannun agogo bayane,zai Nesa da Ummi da kasar gabadaya ko zuciyarsa zata dawo da aiki daidai kamar yadda takeyi ada.

Lokacin Da Ummi tayi Tozali da mu”azzam sai da gabanta yafadi ganin yadda idanunsa suka zurma,kallonsa tayi kafin tace,”Son meya sameka a ido ne?,naga sun chanza kalane..?”shafa sumar kansa yayi kafin yace”Babu komai Ummi,wani abu ne yafadamin a ido,dazu da zan dawo sallar Asuba..”yafada yana kallon kasa baiso ya kalli Ummi taga kwallar data taru a idanunsa.

Bata dai yarda ba, sai ta rausayar dakai tace”Ayyah Srry muje kayi breakfast kafin kawuce kasan bansan zama da yunwa..”tafada tana riko hannunsa,dojewa yayi yaki binta waigowa tayi tana kallonsa kan tayi mgana ya rigata da cewa”Allah Ummi banajin saka komai abakina yanzu,but i promise u da na isa office zan sha tea..”Kuramai ido tayi ita duk sai taga yau ya chanzamata,bayason kallon kwayan idonta batasan dalili ba ,sai ta gyadamai kai tana fadin”Karka zauna da yunwa don Allah son u know ur condition ko.?.”

gyada mata kai yayi yana damke hannunta kafin yace”ki yafemin Ummi na…”yafada idanunsa sun kawo kwallah,matse hannunsa tayi kafin tace”Nayafemaka Duniya da lahira ibrahim,da laifin daka aikatamin da gangan da wanda ka aikatamin cikin rashin sani duk na yafemaka su har abada..”jin abunda tafada yasashi fadawa jikinta kuka na neman kwacemai Rumgunesa tayi tana fadin”Shiii..insha Allahu kukan ka ya kare son kaji..”Tafada tana shafa bayanshi,kokarin dannen kukansa yake,ammh hakan ya gagarara sai da ya sakarma Ummi wacce ta razana da yadda ya kamkameta yana kuka,ammh sai tayi la”akari da abunda yafaru,ta hau lallashinsa da bashi baki,har yayi shuru,ita da kanta ta rakasa har bakin mota ta budemai ya shiga kafin Tarufe tana mai addu’an adawo lafiya har motarsu ta fice daga gidan.

Suna Fita mu”azzam ya Runtse ido yana fadin”Ki yafemin Ummina…”yafada wasu zafafan hawaye na zubomasa kafin ya sanya hannu ya share basuyi wani nisa ba ya umarci Ushe daya paka motar cikin mamaki ya samu waje yayi parking fitowa mu”azzam yayi tare da briefcase din dake hannunsa ya mikama ushe wata marar takarda yana fadin”gida zaka koma,ka kaima Ummi wannan takardan, na manta ban bata ba kafin mu Fito,kada kadamu dani zan hau Taxi na karisa..”yafada cikin bada Umarni.

Ushe da mamaki ya sandarar dashi don tunda yake tuka yallabai haka bata taba Faruwa ba, ko mantuwa yayi sai dai ya maidosa ya dauko,ammh yau gabadaya yallabai ya chanza kamar wani bakon al”amari keson Faruwa dashi,Jikinsa a sanyaye ya karba yana fadin”Ammh yallabai daka bari na dawo sai mu karisa tare..”hannu mu”azzam yadagamai da cewa”Karka damu zan karisa,kai dai kayi hanzarin kaima Ummi sakon dana baka..”

Badon Ushe yagama yarda ba yafada mota yayi Reverse,yakoma hanyar gida,sai dabMu”azzam yaga kulewan Ushe kafin ya juya yana dauke hawayen idonsa,Karamin siririn glass din dake makale gefen aljihun rigarsa ya ciro ya saka,kan ya saka hannu ya tsaida Keke napep din daketa wucewa,nan da nan ko daya ya tsaya batare da bata lokaci ba yace”Airport zaka kaini..”hau muje yallabai..”yabashi amsa,Cikin azama yafada ciki,mai keken yaja suka fara Tafiya,basu wani jima ba,mu”azzam ya zaro wayarsa ya ciro layin dake ciki, ya saka abaki ya Tauneshi kafin ya Furzar dashi ta waje,ya kashe wayar gabadaya ya maidata aljihu.

Tafiyan minti talatin ta sadasu da Airport din ya sauka ya biyashi kudinsa ya karisa cikin Airport din,yana zuwa kuwa yasamu Jirgin da zai Tashi nan dan lokaci shine wanda zai yada zango a lagos,bayason bata lokaci nan da nan ya siya Tikiti yazauna zaman jira,domin ya kagara yafara nisa da garin Abuja,sai duba agogon Fatar dake hannunsa yake bayan kowani dakika.

Baifi Mintin arba”in da zuwa ba,aka fara sanarwan tashin jirgin kafin akafara kiran sunayen masu tashi,cikin lokaci aka kammallawa komai suka shiga jirgi ya tashi yafara yawo Asararin samaniya,Runtse ido mu”azzam yayi yana fadi afili..”Ki Yafemin Ummi na, Dan”Uwa kaima ka yafemin my hira and u too..”Yafada yana kwantar da kanshi bisa kujeran jirgin yanaji yadda kowani gaba na jikinsa ke amsawa hannu yasa yana maida sumar kansa baya yana kokarin ba kansa karfin gwiwa fadi yake”Zan iya,insha Allahu Zan iya..”wanda ke Sit din gefensa dayake A First class suke da kallo ya bisa yana mamakin to meke Faruwa da wannan ne,yana ta sambatu shikadai.

*SAFE LANDEED ZAHMUZ*😘

____________________

Tun bayan Tafiyan mu”azzam taji gabadaya yanayinta ya chanza gabanta na wayan Faduwa,kafafunta kuma suna rawa,haka kurum lokaci daya kuma zuciyarta ta hau tsinkewa sama,ta haura ta dauko wayarta ta sauko falo tafara kokarin kiran mu”azzam din ammh network yaki bari dole ta hakura ta zabga tagumi tana fatan Allah yasa lafiya.

Batawani dade zaune ba,Taji sallamar Ushe a tsakiyar falon saboda yadda tayi zurfi Atunani ko shigowar motar bataji ba ganin ushe sai da yasa gabanta ya fadi Ras!Ras!Ras,jikinta na rawa ta mike hannunta dafe da kirji tace”Kai lafiya?ina da’na yake..?

Tafada cike da tsoro da Razana,cikin girmamawa ushe ya dan rankwafa kafin ya zaro Takarda a aljihunsa yana fadin”Am srry Hajiya,yallabai ne ya aiko ne,na kawo miki wannan takardan wai ya manta ne kafin ya fita bai baki ba..”

Cikin wani yanayi Ummi ke bin Ushe dashi da zungureriyar takardan dake hannunsa da kallo,kafin tace cikin Rawan murya.”Ni..Ni..Ku..ma..”Tafada lokacin dataji zuciyarta ta tsinke,gyada mata kai yayi ,Cikin mutuwar jiki ta mika hannu ta amshi takardan tana fadin”Ina shi mu”azzam din..”?

“Yace na kawo miki,shi zai hau Taxxi ya karisa na sameshi achan..”Ai Ummi bata jira Ushe yagama bayani ba ta warware takarda, ta iske Dogon Rubutun danta mu”azzam cikin Rudewa da firgici tafara karantawa a bayyane kamar haka.

_*Assalamu Alaiki Ummi na,Ina fatan lokacin da Wannan takardan Zai Riskeki zaki yi hakuri ki dauki kaddara,Ummi na na yanke hukunci yin Nisa dake da duk wani abun jin dadi daya danganceni,ciki harda ke da Sana”ata,nazabi Na tafi na barku ko Allah zai sa na tsinci Farincikina achan,zuciyata bazata iya zama babu Zahirah ba ummi,itace ginshiki na rayuwata,Itace haske  Fitila dake haskaka rayuwata,itace komai nawa Ummi rabani da ita dakikayi tamkar kinyi kokarin rabani da Numfashi na ne,Bazan iya juran ganin Hirah bata dawo gareni ba,bazan iya juran ganinta agidan wani ba Ummi,shiyasa na yanke hukunci Tafiya chan wani waje mai Nisa inje incigaba da rayuwata harta Allah ta kasance agareni,kiyi hakuri Ummi ko na zauna wlh tallahi bazan iya yimiki biyayyah ba,nikuma bani so na zama cikin wa”inda Allah zaiyi Fushi dasu,Kiduba dakina, a saman Side drower na bar miki kudade sannan ga Atm dina na banki guda biyu,akwai makullayen motocina dana wannan gidan damuke ciki,kana akwai na wani gida nawa,wanda ke jabi road,ushe yasan da gidan ko shi kikama mgana zai kaiki,ki dinga amfani da kudin wajen biyan bukatanki na yau da kullum,kikuma rika biyan ma”aikatan dake gidan hakkinsu nasan dukiyar da na bar mike zata isheshiki har karshen rayuwarki Ummi na,Kada kuma ki wahalar da kanki wajen nemana,nariga nayi miki nisa,nisan da bazaki taba samu na ba har abada,nidai Fatana ki yafemin laifin dana aikata miki,kikuma samun albarka,Nagode daga Da”n ki mai kaunar Farincikinki..Ibrahim Muhammed moodu Allah ya hada Fuskokinmu da Alheri Ummi na*_

Ai Tunkan Ummi takai karahen takardan Ta sulale ta zube kasa lokaci daya ta yanka wani uban ihu hannunta bisa kanta tana fadin”Wayyo na shiga uku,na mutu na lalace…”Take fada lokaci daya tana buga kanta jikin kujera,Shikanshi ushe dayaji komai hannu ya dora akai yana kiran”Oh Jesus…”Su karime dasu lami dake kichen da gudu suka fito suna tambayan lafiya,sani maigadi da falalu ma ba”a barsu abaya ba suka shigo falon suna tambayan meke faruwa.

Ummi datagama haukacewa,tuni ta mike ta isa ga Ushe tadamke wuyan rigansa tana fadin”Don ubanka ina ka kaimin da’na,ina kakai min da’na nace…”?Tafada cikin tsawa tana jijjigasa lokaci daya hawaye na wanke mata Fuska,shima hawayen yake yana fadin”I don”t know hajiya i Swear…”Yafada jikinsa na rawa su karime dake tsaye sun kasa Fahimtar meke faruwa,cikin wani ja baya Ummi tayi kan ta kwasa da gudu ta fice hannunta bisa kai tana fadin”Da’na Da’na jama”a ina Da”na yake,ku nemomin da”na,wayyo nikaina..Na bani na lalace ni Suhaima banda kowa bani da kowa sai shi,ku taimakeni don Allah.”Haka take fada bayan tafice haraban gidan tana kuka da sambatu kamar zautattaciya.

Ushe ne yake koramusu karime bayanin dayaji Ummi ta karanta a takarda,ai suma dukkansu sai suka dora hannu aka suka fasa kuka,Sani maigadi fadi yake”Wlh ba hajiya kadai ta shiga uku ba hadda mu..”yafada yana share kwallah,karar faduwar abu sukaji kamar na mutum, shiyasasu Rumtuma wa da gudu zuwa haraban gidan,abunda sukagani ne ya firgitasu domin Ummi ce kwance akasa tana wani kakkafewa bakinta na Fitar da wani kumfa kamar wacce tasha Guba,kowani abu wanda zai mata lahani.

Cikin karaji da firgici dukkansu sukayi kanta suna jijjigata karime ke fadi cikin kuka”Wayyo Allah Hajiya don Allah kema ki tashi,in kika mutu ya zamuyi babu yallabai babu ke..Wayyo ni kaina kaicho da wannan rayuwar mai cike da kalubale..”Tafada tana kuka,Ushe ne yayi saurin cemusu su kamota bari ya kawo mota sukaita asibiti,haka ko akayi ya kawo mota wajen suka ciccibeta suka sanyata amota,karime ta shiga tare da ita,shikuma shida Falalu suka shiga gidan gaba,suka fice aguje cikin tashin hankali fuskarsu ko kadan babu Annuri saboda wannan Sabon Tashin hankalin da sukaci karo dashi da sassafen nan.

Specialist hop,suka kaita domin Ushe yasan nan ne Asibitin dasuke zuwa Dr,Abduljabar na kan Duty ranar,shi ya amshi unmi cikin rudewa yana fadin”innalillahi,meya faru ne haka? ina brr.? yafada bayan Nurses sun kawo gadon marasa lafiya an dorata akai kai tsaye aka shigeta da ita emargency cikin tashin hankali da rudewa saboda yadda Ummi take wani abu kamar wacce Zata fado daga kan gadon da”a ka daurata.

*********

Suko Su Uwani da”aka bari agida suna shiga gida lami ta yanke shawaran adau wayan hajiya akira Chan zaria afada musu hadin dasuke ciki,Sunyi na”am da shawaranta sai dai kuma wayar ta Ummi tana cikin password babu wanda ya iya budewa dole suka tasama waya ido,sunajiran Abunda Allah zaiyi,duk da Ummi tabasu tsausayi azahirin gaskiya komai ya faru Ummi ce sila gashi tayi sanadiyar da danta kwara daya jal aduniya ya gujemata,to wagari ya waya tsakani Ga Allah.

Achan kuwa asibiti sai da suka kwashe wajen awa biyu kafin likitocin su Fito suna share zufa,Dr Abduljabar ya kariso wajensu Ushe yana fadin”Ina brr, ne? yafada yana kallonsu,kallon kallon akayi tsakanin ushe da karime kafin karime ta bude baki ta shiga fadama Dr”abunda yafaru ushe na kara koramai bayani,baya Dr.Abduljabar yayi yana fadin”innalillahi wa”inna Alaihirraju”un…”yaketa maimatawa bayan ya dafe kansa yake fadin”why brr,?zaka ma Ummi haka,bayan kafi kowa sanin Ummi bazata iya daukan kaddarar rasaka ba..”yafada yana jin wani Raunin zuciya yana shigansa juyawa kawai yayi ya shige office dinsa, yana sallallami wayarsa ya zaro ya shiga kiran layin mu”azzam din ammh kuma baturiyar tana sanar dashi layin akashe yake,dole ya hakura ya maida akalan kira ga Dr,Shureim.

Dr Shureim na tsaka da duba patient kiran Dr.Abduljabar ya shigo wayarsa,har ga Allah yaji faduwan gaba sanda kiran ya shigo,cikin mutuwar jiki ya dauki kiran yana fadin”Dr,brk da safiya..”Cikin tashin hankali Dr.Abduljabar yace”Dr.Shurein akwai mtsala,komai kakeyi ka barshi kutaho yanzu kaida hajiya zuwa Abuja..”yafada cikin nuna damuwa,saurin mikewa yayi yana fadin”Subhannallahi Dr.Wani abu ya Faru? ko jikin dan”uwana ne ya kara tashi.?.”cikin wani yanayi Dr.Abduljabar yace”Komai ma ya rikice Dr.Mganar bazata yuyu ta waya ba,ammh ga Ummi an kawo asibiti ba yarda take,sannan ma”aikatan gidan suna fadamin wai brr,ya tafi ya bar Ummi shine sanadin shiganta halin datake Ciki..”Kadan ya rage Dr.Shureim bai fadi ba sakamakon Saurin dafe tebur din dake gabansa dayayi da hannu daya, zufa na ketomai ta ko”ina yake fadin”Allah gareka muke,kuma gareka zamu koma…”yafada lokaci daya yana datse wayan,yadafe kansa yayi yana ta kiran sunan Allah tuni idanunsa suka kada sukayi jawur cikin wata murya yake fadin”wayyo Ummi kin cucemu kin Cucu kanki,kin raba kanki da dan’ki da kanki,kin rabani da dan”uwa na,wanda tunda muka taso bamu taba rabuwa ba,koda da rana daya ba,kaichon ki Ummi,kaichonki Ummi..”yafada wasu zafafan hawaye na zuraromai,Cikin zafin nama ya tarrara kayansa ya fice domin patient din dayake dubawa tuni takama kanta tayi waje taga likita da kanshi na hawaye.

Cikin wannan yanayin yajema hajiya zubemata kawai yayi yana kuka fadi yake”Shikenan Hajiya,Burin Ummi ya cika ta rabamu da mu”azzam” yafada yana fashe mata da kuka,iya rudewa Hajiya tayi rude,ganin kukan da Shureim yakeyi gakuma kalaman dayake fada cikin tashin hankali da Firgici tace”Badai Mu”azzam ya rasu bane Shureim..? girgizamata kai yayi kafin ya hau fadamata abunda Dr.Yagama fadamasa,hannu hajiya tadora akai tana kiran Sunan Allah kafin tace”Shikenan kurunkus kan kusa,Dama Abunda suhaima takeso kenan,kuma gashi ya faru,ohni baraka Allah kabamu ikon cinye wannan jarabawan na rayuwa dakake jarabtanmu..”Tafada kwallah na ziraromata.Shiko shureim kokarin kiran mu”azzam yake awaya ammh shima ana fadamai layin akashe yake,dafe kansa kawai yayi yana digan hawaye lokaci daya yanajn tsausayin mu”azzam yakamasa domin yafi kowa sanin waye mu”azzam Tunda yace yatafi to ya tafin ne,kuma sai Abunda Allah yayi.

Duka gidan suka tarraro harda zulaika da yaran,suka nufo Abuja cikin tashin hankali wanda baya misaltuwa,Koda suka isa asibitin suka wuce direct,sun ma tarar da Ummi harta farfado tana ta wasu sambatu tana kiran sunan mu”azzam tana so asaketa ta fita,dole Alluran barci aka garkama mata,dole duk wani mai imani yaga halin da Ummi take ciki sai yayi mata kwallah,agabansu hajiya komai ya faru,hajiya waje takoma tana sharen kwallah tare da fadin”Allah mun godema ka,daga wannan sai wannan,ya Allah kabamu karfin kirjin daukan wannan al”amari..”Taketa fada tana kuka,zulaika ma hawaye take sharewa tana matukar tsausayama wannan ahali mussamman Hajiya da Ummi ga kuma mijinta wanda baya da wani wanda zai lallashesa.

Shikan Dr.Shureim daga office din Dr.Abduljabar mota yadauka Ya fice zuciyarsa na kuna,domin abayanin da likita yake masa Ummi tasamu tsoracewa ne da Firgici shiyasa take wannan zaburan kuma adokar matukar ta kara farkawa cikin wannan halin tofa sai dai ayi hakuri domin kwakwalwarta tasamu mtsala sai kuma abunda Allah yayi,yana tuki yana sharan kwallah,Maitama ya isa,yayi hon sani maigadi ya bude masa get ya sulala ciki,koda ya fito Fuskarsa babu Annuri yayi cikin gidan su lami ne da Uwani xaune afalo suna ganinsa suka mike suna mai Sannu da zuwa,da hannu ya amsa musu kafin ya Nufi farar takardan daya gani bisa center table din dake tsakar dakin domin ko da baisani ba itace silar komai

Warwareta yayi yafara karantawa kafin ya gama hawaye sun jika takardan,rumgume takardan yayi yana kuka,kafin ya dunkuleta ya sanyata cikin aljihun,dakin mu”azzam yafada,komai na nan a muhallinsa,makullayen gidajen dayace ya gani da kudin daya barma ummi,kana ga keys din motocinsa da Katin nan bankisa masu muhimmancu,wanda yake tara kudi masu yawa ya barmata,kenan da guda daya ya tafi,kuma yana kyautata zaton wanda ya tafi dashi bashi da yawan kudin da wa”inda ya barma Ummi kedasu,ya duba kayansa sunan ko kala daya bai dauka ba,banda takardun mkarantarsa dana aikinsa masu mihimmanci su kadai ya tafi dasu,saboda tsausayin Mu”azzam Shureim baisan sadda ya fada bisa gadonsa ba yana rumgume blanket dinsa yana shakan kamshin Turarensa yanajin wasu hawaye na kwararamai yake fadin”where are u dan”uwa? plz come back home we miss u so much dan”uwa..”yafada sanda ya saki kuka da muryansa saboda yadda zuciyarsa ta tsinke lokaci daya daya Tuna halin da mu”azzam din ke ciki.

__________________

Koda Flight dinsu mu”azzam ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na ikkon tashar taxi ya dauka zuwa wani babban Hotel dake garin na lagos yakama daki yayi kwanciyarsa,kafin zuciyarsa tagama shawaran inda kuma ya nufa,shima kamar yaji ajikinsa haka ya zauna yana ta kuka,acikin briefcase dinsa ya bude ya Fito da hotuna guda biyar,guda daya Na Ummi ne wanda suka dauka tare dashi Saudiya tasaka jallabiya baka,shima bakar jallabiyan ne ajikinsa yayo harami da farin yadi akansa,yana rumgume da Ummi suna dariya hoton yayi bala”in kyau an saka shi cikin Frem anyi babbam elegement dinshi.

Sai guda daya wanda suka dauka da Shuriem ne Abuja sanda aka yimsu brr calling,Suma dukkansu suna sanye da American Suit na kamfanin Armani ne,ammh shi mu”azzam yana sanye da rigansu na lauyoyi da hula sun,daki kadafan juna suna mirmishi,hoton shima anyi babban Elagement dinshi an sakashi cikin Frem,sai guda daya na Zahirah ce tana sanye da kayan mkrantarta complete harda da safa da takalmi da jakarta sabe abayanta,tana dariya aka dauketa hoton da alamu kamar ma batasan sadda akayi mata hoton ba,Gabadaya beauty Point dinta ya bayyana Fuskarta tana bayyanar da Farincikin datake ciki,hoton mu”azzam ya dauketa ne ranar da zata fara zuwa mkranta.

Sai guda biyun kuma na ya”yansane wanda Shureim,yadauko masa su  ahoto ya kawo mai yagani shine ya turasu duka awayarsa yasaka aka wankemai su kowanne an mai babban kati anyi elagement dinsu cikin Frem,wanda suke sanye cikin kayan sanyi na alfarma fuskarsu tar suna fitar da Annurinsu na jariran dake cikin kwanciyar hankali da Ni”imar ubangiji,duka yahada hotunan ya kamkame yana wani kuka mai cinrai,tuni saitin zuciyarsa ya fara zafi,yana tangadi ya tashi ya bude fridge din dake dakin ya dauko ruwa yazo ya zubo da magungunansa dayazo dashi ya hausha cikin rashin hayyaci da kewar wanda sukama mutum nisa.

Allah ya taimakama farkawan da Ummi tayi ta farka cikin hankalinta,tadaina fizge fizge takoma yin kuka,mai cinrai kamar ranta zai fita,shigowar hajiya shiya kara  tsinkema Ummi jiki tana so tatashi takasa cikin sauri Hajiya takarisa gareta tana fadin”Bari kokarin Tashi Suhaima,baki da lafiya..”Tafada tana kallonta yadda tadawo cikin wuni daya kawai,cikin kuka da wani irin tsoro Ummi ta kamkame hannun hajiya tana fadin”Hajiya mu”azzam yana gunku ko? tare dashi ma kukazo yanzu ko? don Allah karki ce da gaske ne mu”azzam yatafi ya barni don Allah karki cemin dagaskene,duk abunda ya faru..”Tafada cikin shidewar Numfashi cikin hawaye Hajiya tace”Da gaske ne Suhaima mu”azzam ya zabi yayi nisa damu saboda hallayanki da taurin kanki,dakuma rashin yafiyarki,abunda nayi ta guje miki kenan,nafada miki suhaima inbaki zubar da makamanki ba,to watarana ma Da’n naki dakike takama dashi zai zo ya kubcemiki,kika kiji,yanzu waya gari ya waya,kifadamin tsakanin keda Da shettima waye ya fadi,kuma waye keda riba..”Tafada kwallah suna zuraromata.

Kife kanta Ummi tayi akafadan Ummi tana kuka take fadin”Hajiya zan mutu,wlh mutuwa zanyi,taba kirjina kiji,wlh zan mutu bazan zauna acikin duniyar daba mu”azzam ba,bazan iya ba..”tafada tana dora hannun hajiya bisa kirjinta taji yadda yake harbawa da Sauri da Sauri,rumgumeta
hajiya tayi tana fadin”Bazaki mutu ba Suhaima nafi so kiyi nadamar abunda kika aikata kafin lokaci ya kure miki..”Cikin kuka Suhaima tace”Nayi whl nayi hajiya Nayi Nadamar abubuwan danayita aikatama Mu”azzam hajiya dana sani ban saka ya saki matarsa ba…”

“”Allah ya rabumu da aikin danasani Ummi ammh bakin alkalami ya rigaya daya bushe,mu”azzam yabarmu,kuma yayi nisa da mu domin na bincika duk inda nake da tsammaninsa babu shi babu dalilinsa..”yafada yana dafe kansa,Shureim kenan wanda shigowarsa kenan,daga hajiya har Ummi an rasa mai lallashin wani Ummi fadi take”Ni dazai dawo wlh zani har maiduguri na roki Shettima gafara Zahirah ma tadawo dakinta,indai zai fasa barina yadawo mu zauna tare ban saba da kowa ba sai shi Shureim shine uwata shine ubana,,shine da”na shine madadin yan”uwa na,wlh rashin mu”azzam tamkar rabani da duk wani jin dadin rayuwata ne..”tafada tana kamkame hajiya,shureim daya jingina da bango fadi yake”Ai shikenan Ummi,komai fa ya kwabe,..”yafada shima kamar yayi kukan.

Dr.Abduljabar ya shigo shikanshi halin da wannan Family din dasuka zama tamkar yan”uwansa suka shiga ya tabasa,dakyar ya lallaba Ummi yayi mata alluran barci bayan ta rike masa hannu tana fadin”Dr nasan kasan inda mu”azzam yake,kacemai yadawo wlh na tuba nabi Allah,kace mai eh ya dawo zanje na dawo masa matarsa indai hakan shine zaisa ya zauna dani ,wlh kaji na rantse ko yanzu sai naje maiduguri,kai likita ko a kasa ne ma indai Mu”azzam zai dawo gareni zan tafi zani wlh ku tsausayamin ku memomin da’na”Take fada lokacin da alluran tafara aiki ajikinta ta sulale bisa gadon tana Fadin..”Da’na…!…”Da gudu hajiya ta fice tana gujin kuka shureim ko baya ya juya yana shesshekan kuka,Shikanshi Dr.Abduljabar hawayen ya share ta kasan medicated glass din dake idonsa yana gyarama Ummi kwanciyarta,kafin ya kariso kusa da Shuriem yana bubbuga bayansa alaman lallashi,juyowa kawai yayi yafada jikin Dr.Abdujabar yana fadin”I feel Alone Dr.Ya zanyi shikadai ne dan”uwa na,kalli halin da Ummi ke ciki,kalli halin da Hajiya ke ciki i swear to god Mu”azzam shine ginshikin farincikinmu rashashi kuma tamkar rasa walwarmu ce ta har abada…”yafada yana mai sakin kuka.

Lallashinsa ya shiga yi yana fadin”Kabar kuka zai dawo very soon…Inaji ajikina shima duk inda yake yana cikin halin dakuke ciki,insha Allahu Soon brr zai dawo gida da zarar zuciyarsa tayi sanyi.”Shureim ya dago yana kallonsa idanunsa jawur yace”Babbar illar Dr.Shine bazai kula da kansa ba,zama zaiyi cikin lalura karshe zuciyarsa ta buga ya mutu,inda,baya da kowa,mukuma yabar zukatanmu cikin zullumi da saka rai na har abada..”yafada yana buga kansa da garu saboda yadda zuciyarsa ke amsawa,dakyar Dr.Ya lallashesa suka fito daga dakin yakaisa office dinsa yana basa baki har ya samu natsuwa,koda ya fito ya iske hajiya zaune fuskarta ta kumbura saboda kuka,ga zulaika ma nata fama da yara, itama ta sha kuka,hajiya na ganinsa tace yazo ya tafi da zulaika gida tasamu tayi wanka taci abinci taba yaran nan,ita tana nan,Yayi na”am da batunta ya umarci zulaika data tashi su tafi harda karime hajiya tace su wuce wanda lokacin dare yayi,itakuma hajiya dole dama abarta ta kwana da ummi saboda yanayin yadda take farkawa,shi Ushe tundazu yakoma gida cikin alhini.

Koda Sukadawo gidan ba wanda ya runtsa su lami duk suna falo xaune jugum jugum,inda suka saba sauka nan zulaika tafada tayi wanka tayima yaranta kafin tayi  sallolin da’ake binta ko abinci dasu lami suka kawo mata kadan taci shureim kuwa shashen mu”azzam yashige yana ta kuka dakyar zulaika ta lallabasa tayimai wanka ta shiryasa,dakyar ya yarda yasha tea tabashi paracetamol yakoma ya kwanta domin ciwon kai ne da zazzabi suka rufesa,gefe itama ta kwanta rumgume da yaran tana share kwallah tsausayin mutanen da suka kasance jarumai ammh yau Ranuninsu ya bayyana.

_________________

Wahegari Tun safe mu”azzzam ya fita neman ma kansa mtsaya koda yaje Airport na birnin ikko jirgi daya ne zai tashi da karfe 9:00am na safe kuma zai yada zangon A EGYPT,Cikin ransa yayi kasake yana ayyana Zuwansa garin da baitaba zuwa ba, kawai wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi Kayi rayuwa achan mana,ka manta Abbanka yaje chan,Umminka tayi rayuwa achan Tabbas nima Zan maimata Tarihi zai maimata kansa,Zan isa garin na SUDAN nima in taba rayuwata achan,koba komai garin da Ummi na da Abbana suka fara haduwa ne.

Tuna haka yasashi saurin yanka ma kansa tikiti da sauran chuku chuku abunga ga masu dashi nan da nan komai ya kammallah ko hotel din daya kama bai koma ba,daman daga shi sai yar jakarsa ya fito zama kawai yayi yana jiran tashinsu zuciyarsa ta matsu ya bar kasar Nageria kasar da babu komai cikinta sai kunci.

9:00am din kuwa jirgin ya tashi ya lula dashi cikin sararin samaniya cikin wani yanayi Mu”azzam ke maimata inda zashi da karfi.. ” *SUDAN*

_*Godiya ta mussaman ga masoyana masu bibiyana,Nagode muku sosai ga wadanda suka kirani sukamin sannu da jiki epecially thanks to u my Sisi of life Aisha Alto,da ke my kakus mum khday,my esha,Aisha bello ina godiya,sai my juwairiyyah Rogo,dake my Queen Eshart,and u my Shatutu,ina matukar godiya da kulawanku,Tanque so much my Habibaties*_

*DON’T”FORGET TO COMMENT AND SHARE AND VOTE ME ON WATTPAD JANAFNANCY12,masu bibiyar wanchan account din toh na chanza account mai son kamani ta chan ga user name dina dana chanza..one luv janaf fans*

*JameelatOmar*
*UWAR MIJINA…!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_

*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy12*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer’s Asso*✏

_Wannan shafin ta gaisuwan,Sada ZUMUNTA NE,na marubuta yan”uwanah.._✍👉

_*FEEDHOM❤,Khadijat Beebeenmasoya(Uwata),Aysha sada machika,Hafsat Hafnan(Sahibata😘),Aisha Alto(my sisi of life),Hauwa s zaria maman uswan(Mommata),Khadijat Candy(Mamata),Billy Abdul(yayata),Sa”adatu Alkali D/Tsafe(Bestyta)😍,Ramlart R manga(Real maidambu),Sis Narja”art(Antyna),Beeba muhammed(Bebatina),AminaOmar Fana(Aufana),Fatima Adamu(Mumfdly),Mum kausar(Dotana),Halima Abdullahi(kanwata),Sainah Ummu meenal(Antyna),Mom Afra(Boss me),Ameena Abba(Anty meena),My meeragee,Meemartjj(kanwata),Lasminzy,Fatima Sardauna(Mrs Sardauna),Hauwa”u M U(Smasher),Sa”adatu bintu Abdullahi,Bby maryam,Ummy yusra,miss zahra(Kawata),Teemaswra,Jamila k/Mashi(My Namecy) Sadiya Sidi said(my Sharifiya),Miss Xark(Kishiyata)😘,Asmee sani,Chubado muhd(Uwar dakina),hapsy kawar arziki,jabaka writer,kamal no love Sardaunah(gaye nah)😂,maman hanan(Deen),maman weedad,Maryam obam,Nusiba uk(Kawata)Raheenat m Abbakar(Yar garinmu),Sameena Aliyu(My samee)Zainab Dahiru wowo,And u makociyar kwarai Fadilat talba,Safiyyah Aliyu wakili,Ummu Abideen, Sis mugirat musa..,Wayyo ni dadi kasheni wlh Kuna da yawa,Dukkanku nayi zaman Amana daku ina rokon Allah aduk inda kuka sanya kafa Allah ya cigaba da dafa muku Amin,ina matukar sonku mazga mazga😍Santala santala😘Kai dukanku nace muku Bhahoot bhahoot*_😂💕😛

*NOT EDITED*💥

*NO 28*

Lokacin da jirgin,ya Saukesu a filin jirgin na kasar egypt,bata chanza zani ba,domin Wani hotel daga cikin manyan Hotel din dake kasar,ya kama ya zauna domin bayada zabi,tunda baisan kowa ba agarin.

Kwanansa uku akasar ammh ko kofar dakin dayakama bai Fito ba,yana cikin daki komai yake bukata sai dai Ma”aikatan hotel din su kawomai bayan yayi musu mgana,Tuni magungunansa suka kare ga yawan kwana dayake baya barci,damuwa tafara mai yawa, mugun ciwon kan nasa,da kuma jirin daya ke fama dashi na neman yadawo,baya komai daga kwanciya sai sallah shikadai ke tadashi,komai na duniyan nan yadaina mai dadi kwata kwata ya rigaya daya sallamama rayuwar jin dadi kwata kwata.

Sai dai yayi Asati daya a egypt kafin ya karisa cikin birnin Sudan din,wanda chan dinma, Hotel yakama yayi zamanshi,baya ko marmarin Fita ma yaga kalar garin saboda yadda yake faman yaki da zuciyarsa wajen manta abunda ya faru dashi,ammh duk kwana duniya da hoton hira dana yaransa yake iya barci,inko ba haka ba,yadda yaga rana haka yake ganin dare,ga yadda yanayin jikinsa ya rikice gabadaya,ammh kuma yakasa daina zafafama kansa tunani balle yanema ma kansa mafita ,koda na fita yanemi mgani ne.

_________________

*NAGERIA*

Duk wani bawa mai imani inyaga halin da Ummi ke ciki sai ya tsausayamata ballema in aka samu mai Raunin zuciya sai ya zubarmata da kwallah,Kallo daya zaka mata kaji gwiwanka tayi sanyi saboda yadda Ummi takoma kamar ba ita,ta rame tayi baki ta lalace kamar ba hajiya Suhaima ba yargata yar kwalliya,ammh lokaci daya rayuwa ta juya mata baya,bata cin abinci kullum sai kuka kamar wacce ta zare,sati daya tayi a asibitin aka sallameta bayan magungunan da”aka rubuta mata,yawancinsu duk na hawan jini ne,saboda yadda jininta yayi bala’in hawa,koda Dr.Abduljabar yayi ta lallashinta dakuma bata shawaran ta rage Tuanin jinsa kawai takeyi ammah har abada indai ba mu”azzam dinta bane yadawo an gayyato Tunani da rashin kwanciyar hankali a rayuwarta na har abada.

Koda suka koma gida bata chanza zani ba,Hajiya na nan Tare da ita,don tace ina zata tabar Suhaima cikin wannan halin dole ta zauna tare da ita,shureim shima sati daya yayi cur kafin ya tattara matarsa da yaransu sukoma zaria,shima badon aikinsa ba wlh da dawo nan zaiyi ya zauna su jajantama kansu tare,saboda shima ayanzu baida wani kuzari,domin Rashin mu”azzam tamkar rasa wani bangare na shi wanda maidasa abu ne mai wuya.

Lokacin Da Shureim yakira chan maiduguri yana tambayan bukar ko mu”azzam yazo nan,fadan tashin hankalin da suka tsinci kansu bata faduwa,Shettima fadi yayi wanda yayi sanadiyar samun paralayze ma”ana gefen jikinsa na dama yadaina aiki ga bakinsa ya karkace yana zubar da miyau babu kafa babu baki,Yakura ma fadin halin data ke ciki bamai dadi bane,ga wannan abu ga kuma laluran Shettima wacce ta kamasa sanadiyar rashin sanin inda mu”azzam din yake,Shikanshi bukar yaji ba dadi,da lbrin barin mu”azzam  gida,duk da tuni ya ya yafemai wlh baya rike dashi aransa,Dole tasa aka boyema Zahirah bukar yahana kowa ya fadamata ko mahgana ya gargadeta akan karta kuskura ta fadama zahirah wannan lbrin ko tasamu natsuwar kula da yaranta cikin Aminci batare da wani mtsala ba,duk da tana cikin halin damuwa,ga laluran data samu baffa,wanda ranar dataji wuni tayi tana kuka kamar wacce ta zare,kullum kuma cikin gwada nombar Mu”azzam din take ammh bata shiga amsa dayane ake bata wayar akashe take,tayi kuka kamar me aranta tanaji kila ya mu’azzam ya barta ne,bari na har abada tunda gashi ya yanke duk wata hanyar da zata sadata dashi,kuma tasani yana waya da wanda yaso,ita batasan Abunda ke faruwa ba.

Yara kuwa suna cigabada da Samun kulawa yadda yakamata,dayake nonon na zahirah mai kyau ne  ga ishshen madara dasuke samu,shiyasa lokaci kadan sukayi bulbul dasu gwanin sha”awa ba”a chanza musu sunaye ba,Ummi da moodu ake kiransu yaran in ka gansu kamar ba yan Sati hudu ba da haihuwa saboda yadda suka fara wayau dasu,Tuni bukar yagama tsaida shawaransa kan zahirah Bayaso ta samu lbrin Tafiyan mu”azzam tana gidansa yafi so ko zata samu ya kasance tana gidan mijinta ne,shiyasa duk wani shiri ya gudanar ko gudanar da neman Auren gun yayyinsa akaje susuka ka gudanar da neman auren harta da sadaki an biya, kawai ranar daurin aure ake jira,ganin halin da baffa yake ciki yasa bukar dakatar da daurin auren da zarar Zahirah tayi arba”in   yabari baffa yakarajin sauki kafin komai ya kamkama.

________________

*SUDAN*

Kwanan Mu”azzam goma baitaba marmarin Fitowa ba,sai ranar daya gaji da kwanciya,kawai sai yaji aransa yanaso ya fita koda kuwa harabar hotel din ne,shiyasa ya kokarta ya fada tiolet yayi wanka,sakamakon baizo da kaya ba,kuma bai samu sukunin siya ba kayan jikinsa su yake maimatawa,gashi sunyi datti sun chanza kamanni ammh ko ajikinsa haka ya kakkabesu ya maida ga sumar kansa tayi yawa,ga yadda kasumba ta tarun mai,duk wanda yasan Mu”azzam indan ya gansa lokaci daya bazai shaidasa ba, bawani kwalisa,ba wani gayu bawani fesa turare in ga gansa alokacin kace wani saurayin Kauye ne saboda yadda ya saki rigar takusa zuwa cinyarsa,kuma ko tek tie dinsa bai saka ba,nikaina dana kallesa sai naji dariya hade da kuka lokaci daya ya kubcemin saboda tsausayin yadda rayuwa ta maida matashin Barrister kuma dan kwalisa maiji da Naira da Kwalisa yakoma lokaci kadan.😭😭😭

Fitowa yayi yana tafiya kamar bashi ba saboda yadda bai da lafiya domin kansa juyamasa yake,ammh kamar ingizashi ake da fitan da zaiyi,koda ya kariso haraban Hotel babu ruwan kowa da kowa jajayen Fata ne ,da larabawa keta kaida kawosu babu mai kallon wani balle har yakula da mai kakeyi,ba irin garinmu Naija ba,da in aka fara kallon mu’azzam ana dariya sai ya raina kansa😂,

wajen Hotel ya fita yana tafiya ahankali yana kalle kallen gefe,yayi Tafiya mai dan nisa kan ya isa waje daya ga mutane na zama,waje ne ba” killace yake ba,fili ne gefen wajen wata koramane datake gangara tana zubar da ruwa fari kal dashi,mai ban sha”awa,daga chan gefe kuma wasu fararen duwatsu ne suka barbazu awajen tako”ina ga kuma wata kasar rairayi mai laushi wajen,tuni wajen yazama yana bada iska sosai da sanyin dadi,shiken sai mutane suka samu wajen zuwa su zauna,ko mutum inzai dan hutu dadai sauransu,har wani ma”ikatar saida Lemuka masu sanyi sukayi amfani da wannan damar suka kara raya wajen,suka baza ma”aikatansu awajen,inkazo duk abunda kake bukata na ababen sanyi zasu kawo maka in ka gama ka biya,shiyasa wajen yake tattara kowa da kowa kama daga yan kasar harda baki masu zuwa daga kasashe mabambamta Kuma mafi akasari baki sunfi moran wajen Tunda yana daura Da hotel din wajen.

Gurin yabawa mu”azzam sha”awa matuka shiyasa ya karisa ya zauna kan daya daga cikin duwatsun dake wajen wa”inda aka gyarasu akallo daya bazaka ce duwatsu ne wanda Allah ya kwafa ba,saboda yadda aka kawatasu kamar wasu mulmulayen kujeran zamani nazama,ruwan dake wucewa ta tsakanin koramar ya tsurama ido kawai yana kallon Ransa nadan sanyi saboda yadda iska ke kadawa,koda ma”aikatan kamfanin lemun suka karisa ko dawani abu dayake bukata hannu kawai ya daga musu alamar baya bukatar komai,basu damu ba,Suka wuce tunda waje ne daya hada kowa da kowa harda bakaken fatan ma akwai balle shida fatarsa ta hade taxama ruwa biyu babu wanda zai kallesa yace ba dan kasar bane.

Yaji dadin wajen sai gashi har dare ya raba baisani ba,sai daya duba agogon ahannunsa yaga har 12 ta wuce kafin ya yunkura ya tashi,da kafansa yasake komawa cikin Hotel din,sallolinsa dasuka kufcemai ya fara ramawa,kafin ya jawo kan wayar dake cikin Dakin Hotel ya daddanna wasu lambobi magana yayi kan abunda yake da bukatar akawo mai,babu dadewa ko akayi Nooking din kofar ya bude ya amshi babban Farantin da”aka shakosu da kayan marmarin ma”ana Fruit domin sukadai yake iya ci yadan ji dadi bisa bakinsa,ammh bayansu tunda yabaro Nigeria bai kara saka wani abinci abakinsa ba.

Mu”azzam yasamu wajen zuwa domin yanzu kullum da gari waye zuwa yayi sallar azahar yake fitowa yazo gunan yazauna yana,kallon shige da ficen mutane,kuma baitaba cin komai agunka ba,sukansu ma”aikatar gun sun ganesa shiyasa ko yazo basu bi takansa saboda susan ko sunje baya bukatar akawomai wani abu,kuma kullum da kaya daya yake yawo kamar wani mahaukaci in ka gansa bazaka iya shaida dan wani jinsi bane saboda yadda Gashi da kasumba suka cikamai Fuska babu kyan gani.

Tadade tana zuwa wajen,kuma inbazata manta ba,kullum wajajen wannan lokacin take ganinsa yana zuwa yazauna shikadai yana kallon waje daya,kuma bayama kowa mgana kuma baitaba shan wani abu ba,wani lokacin sai dai ta ganshi yana sharan kwallah,kimanin Sati daya kenan take lura da Mutumin tun bata maida kai hardai tafara Fuskanta wasu abubuwa agame da shi,na yadda yake mu”amalansa awajen tafara dora ayan Tambaya akansa amtsayinta na babbar likitan zuciya ta fahimci yana fama da wata damuwace wacce take saka shi kebewa daga mu’amala da mutane,haka kurum takejin zata taimakeshi tayi alqawarin in tazo gobe zatamai mgana taji kodaga ina yake,kuma mike damunshi..? kuma shi dan wani kasa ne? me kuma ya kawoshi nan din?

***********

Kimanin Sati hudu kenan Da Tafiyan mu’azzam ammh har zuwa wannan lokacin babu amo ba lbri,Ummi kuwa babu yarda take domin babu abunda ya chanza zani gabadaya ta rame ta lalace kamar ba ita ba,ga yawan kuka ga damuwa,kullum Dr.Abduljabar cikin zuwa dubata yake yana auna jninta tare da kawo mata magunguna,Ummi sai ta wuni ta kwana batama kowa mgana sai dai ta kalleka hawaye yana zuba daga idonta inko ta bude baki zatayi mgana to mganar kenan”Ina Da”na ko kaga Da’na.?Shiyasa rashin mganar bata ma Dr.Abduljabar yace shine mafi a”ala saboda in tana yawan irin haka sai kwakwalwarta tasamu mtsala,hajiya ke tare da ita haryanzu tana taimakamata nasihohi da ban baki kan Ummi ta dau kaddara da hakuri tacigaba da addu”a insha Allahu Mu”azzam zai dawo gareta,jin hajiya kawai take ammh ita tanaji ajikinta ta kusa mutuwa tabar duniyan gabadaya,domin bazata iya jure zama haka babu mu”azzam dinta ba.

Shureim na zuwa duk weeked wani lokacin yazo shida zulaika ko kuma yazo shida yaransa,wani zubin kuma shikadai,wannan zuwa ne,yaje maiduguri ya duba jikin Shettima wanda halin dayake ciki sai da yasa Shureim ya zubar da kwallah,baffa na kuka yana bama Shureim sako,kan ya rokan masa Suhaima data yafemasa dayake yanzu ansamu yana mgana saboda andage da magani,Dakuma arokan masa mu”azzam shima ya yafemai saboda duk shine silan komai,shi kuka shureim kuka ,yakura kuka,wani abun tashin hankali kuma bukar yazo ya sameshi agidan nan yake bashi goro da minti  dauren Auren zahirah sati mai zuwa.

Iya Rikicewa Shureim ya rikice,Duk da yasan cewa dole daman zahirah zatayi aure,to ammh su little Ummi ba da Moodu yaza”ayi dasu,kamar bukar yasan abunda ke ranshi yace”Kada yadamu zata cigaba da shayar da yaran har zuwa ta yayesu kafin suzo su karbi yaransu shi mijin nata ya amince da hakan,shikuma mu”azzam Allah ya bayyanasa”Sadda kai kawai Shureim yayi yana goge kwallah,Yakura ma daki ta shige tana ta kuka,daya nemi ganawa da zahirah kiri kiri bukar ya hana yace”bata da masaniyar duk abunda ke faruwa hatta da ko auren da za”a daura mata,saboda haka bayason yaje ya tadama yarsa da hankali yayi hakuri kawai sun gode Allah bar zumunci”Babu yarda Shureim ya iya banda hakuri domin kome yafaru baiga laifinsa ba,duk Ummi ce taja wannan abun da bata saka mu”azzam ya saki zahirah ba,da duk haka bata faru ba,Sakon dayazo dashi na madaran yaran da kudi yabawa bukar,sai kayan abincin dayazoma su yakura dashi suma ya saukemusu kafin yayi musu sallama yamika hanya,yana mai tsausayama mu”azzam domin ya hadu da jarabta kala kala.

Agaban Ummi shureim ke maidama hajiya yadda sukayi da bukar,hajiya na hawaye take Furta” Allah Sarki mu”azzam Allah yazama gatanka a duk inda kake..”tafada tana share kwallah kan tacigaba da cewa”Shikuma bukar inda yayi hakuri ko shekara yaran sunyi kafin yayi Tunanin aurar da ita,ammh wannan danyen Hukuncin daya yanke sai naga kamar yayi tsauri,tunda ko baimata aure ba,yasan cewa bazata koma ma mu”azzam ba..”Hajiya tafada cikin tsausayi Ummi dake zaune kawai gani sukai tatashi tana kuka ta haura sama,da kallo suka bita,domin yanzu gabadaya sun ma daina bata laifi Tsausayinta suke ji yadda rayuwa ta maidata,kai bama Ummi ba hatta fulawowin gidan susan cewa babu majinginar gidan,babu bangon gidan domin Namiji shine gida,Ko ma”aikatn gidan suma sun san sun rasa bango buhun sigari kowa ya lasheka sai yalashi siga,Shureim bai tsaya ba washegari nayi ya koma zaria saboda aiki.

_________________

*SUDAN*

Kamar koyaushe tana gama duba patient dinta ta fito daga cikin asibitin motarta ta hau wata kirar 4matic,ta nufi wajen domin ta wasa wukan yau sai tayimai mgana,haka kurum take jin,tana son jin wani abu game dashi,ko kwanaki da taso mai mgana tafiyace ta kamata zuwa india shiyasa bata koma wajen ba,sai jiya daddare ta dawo shine yau bayan fitowanta daga asibiti ta nufo wajen kai tsaye.

Illai kuwa tana paka motarta idonta yakai mata kanshi yana zaune,inda yasaba zama,da kuma kayan data saba ganinsa,cikin kuzarinta ta fito daga motar bayan ta sanyata ciki key,ta fara takawa, zuwa garesa kai tsaye ta nufi inda yake,har ta tsaya agabansa baisan da tsayuwar mutum ba,saboda yadda yayi zurfi cikin Tunaninsa tadade tana nazarinsa kafin tayi karfin halin cewa

“Hy…”Tafada tana mika masa hannu,dagowa yayi cikin mamaki da alja”abi yana kallonta kyakyawan macece fara ce tas mai daukeda da doguwar Fuska hancinta har baka yake,ga dan karamin bakinta wanda yasha jan jan baki,Tana sanye da wata doguwar rigar abaya baka sai mayafinsa wanda ta yane kanta dashi,Fuskarta sanye cikin wani siririn farin glass,sai kafarta dayake sanye da wani takalmi baki mai tsini,sai hannunta na dauke dawata jaka baka da makullim motarta.

Cikin dakika kadan ya karemata kallo,kauda kai yayi bai maida mata da martanin mganarta ba,sai ma yayi kamar ba dashi take ba itakuwa jikintane yayi sanyi lokacin data ci karo da Fuskarsa saida ta tsorata harta dan ja da baya,ammh ganin yadda yawani dauke kai yasata kara matsowa takara cemai hy da yaran hindu,nan ma yayi mata banza,takoma larabci,nan ma yayi mata banza,takoma French nan ma yayi mata banza,kai duk yaren duniyan nan tayi mishi yaki tankata,ganin haka ne yasa cikin tamtama tace”Assalamu Alaika…”Tafada tana shakkar shi din musulmi ne

Jin Tayimai sallama yasa,yadago yana kallonta cikin mamaki sanin muhimmanci sallama yasa ya bude baki kamar mai koyon mgana ya amsa mata chan kasan makoshi,wanda ita kadai ne data ke kusa dashi taji abunda yace”Amin wa”alaikis salam..”yace kafin ya kauda kai.

Mirmishi tayi kan tace”Wow..u are a muslim..?Tafada da sigar tambaya,ko kallonta baiyi ba, cikin jin dadi ta zauna kujeran dake fuskartanshi tana fadin”My Name is *DR LUBNA KHAMIS*, “Tafada tana kallonsa kafin ta zuramai ido tana fadin”U…”?Tafada tana zakudamai kafada,sunan data fadane yasa ya kalleta kamar zaiyi mgana kawai sai ya kauda kai ya mike yafara tafiya batare da ya ko kalli barayin data ke ba.

*DON”T FORGET  TO COMMENT VOTE AND SHARE*

About Godswill

Check Also

MATAR GWAMNA Page 11 to 20

MATAR GWAMNA Page 11 to 20 …..d’agowa nayi fuskata na rike a tattausan hannunsa idanumu …

Advertisements