WAZAN AURA Page 1 to 10 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / WAZAN AURA Page 1 to 10

WAZAN AURA Page 1 to 10

WAZAN AURA Page 1 to 10

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
“Wayyo Allah  na Ummu ki daukota muje Asibiti karta mutu, “Uhmmn yanzu Sumayya ina muka ga kudin da zamu kaita asibiti kin san in munje ba kudi ba wanda zai kallemu,  “wai Mutanen   duniya yanzu Ummu basa taimako ne, wlh nima in na zama wani Abu nan gaba bazan taimaki kowa ba”Kull kar in Kara jin kin fadi haka Sumayya, wani Kakari da ihu da Wanda ke kwance tayi, duk sukayo kanta kakkafewa idonta yayi, Da gudu tayi Hanyar Kofar gidan  ta fitowa taci karo da wani makocin su yana dan gungoro mashin dinshi dayayi faci, da gudu ta karasa gareshi “don Allah Mudi ka taimakemu Yar uwata ce bata da lpy ka taimaka mu kaita asibiti, “subhanallahi badai Sikilan nata bane ya tashi, “eh shine wlh suna karasawa suka ga Ummu tana rungume da ita tana kuka da sunbatu, “don Allah Maryama ki tashi karki tafi ki barmu a duniyar nan, “Kamata Ummu Sumayya mu kaita asibiti, “Mudi bamu da kudi fa, “kamata haka mu tafi Allah zai rufa Asiri, Sumayya yi Maza kitaro abun hawa kan hanya, da gudu Sumayya ta fita, su kuma suka kamo Maryama suka fito da ita tamkar da matacciya, sai a lokacin na karema ta kallo kyakyawa ce na ajin karshe sai dai daka kalleta zaka gane bata cika koshin lpya budurwa ce yar kimanin shekara Ashirin Amma sbda lalurar dake tare da ita zaki dauka yar sha hudu ce,
Suna fitowa suka tarar har Sumayya tazo da me Nafef din, haka suka samu suka sata ciki yaja su, Sai Asibitin Aminu kano teaching hospital, Suna isa aka shige da ita,
Sukuma suka tsaya a waiting room, Me napep ne ya biyosu “Hajiya baku bani kudina ba, “Nawa Zamu baka, “kudinku Dari biyar”Haba Mallam ga dai dari biyu nan, kayi hkr”gskya Hajiya Anmun son rai, wlh kuje ku da Allah, “Haba bawan Allah mare lpy fa muka dauko ba taimakone a duniya don Allah kayi hkr wlh shikenan mun badon haka ba dana cika ma, karkace ka barni da Allah, “Oho nima fa mai nake sawa a Napep din nan ba ruwa ba, ehe, wata matane dake zaune take jin duk abunda yake faruwa, ta ciro dari uku a jakanta kudin ma duk Yaji jiki Daga gani itama bashi gareta ba, ta mika mai bako kunya ba tausayi ya karba yayi gaba yana maganganu, “Baiwar Allah mun gode Allah ya saka da alheri, “ba komai Allah ya rufa mana Asiri, Sumayya ce keta kaiwa da dawowa, “Ummu ina Mudin?  Ai ya tafi tun dazu, nasha zai tsayane ya taimaka mana da wani abun, “yadai ce bari yaje ya dawo,
“Suwaye yan uwan wacce aka shiga da ita Emergency yanzu?  “Gamunan Ummu ne da Sumayyah suka hada baki gurin fadin haka, “likita na nemanku, “to muje, binta sukayi a baya suka shiga Office din hade da Sallama, wani Farin kyakyawa matashi ne zaune a Office din yasa kayan likitoci da, alama shine likitan ita kuma Maryama tana kwance kan gadon dake Office din, Amsa musu Sallaman su yayi ba tare daya dago ya kallesu ba, zama sukayi suna jiran jin me zai cemusu, sai da ya kai gurin minti goma suna zaune baice musu komai ba, har Sumayya ta fara tsaki sbda ita fa a ka idanta bata jure wulakanci, “oh Sorry kune  yan uwan Maryama Nuraddeen  wurno, “eh mune Doctor, “kun san tana da sikila koh? “Eh mun sani Doctor, “Ok to gskya ciwonta ne ya tashi kun san shi wannan ciwon ba wuyan ya shanye ma Mutum jini, in so samune ma a ce duk ending Month a dunga kwashe jininta Ana samata wani, yanzu dai kafin abata duk wani taimako tana bukatar Jini Leda uku, “wayyo Allah a debi nawa doctor a samata, ko Leda goma ne, “how old are you dazakice a debi jininki, ko ba haka bama ba,a diban jinin mace Sai ya zama dole, yanzu in zaku kawo wanda, za,a dibane zaku biya Dubu bakwai na diba da test din da za,a yimata, in kuma siya zakuyi zaku biya dubu sittin Leda uku, “don Allah doctor ka taimaka mana wlh bamu Da wannan kudin, bamu da Wanda zai taimakemu bamu da kowa, mu yan gudun Hijirane Daga garin Sokoto duk an kashe mana Ahali gaba daya dukiyoyin mu sun salwanta, “dakata baiwar Allah bashi na tanbayeki ba, zaku iya fita kuje can ku nemo, haka kuke ai kudunga karya kuna batama Hausawa suna, tashi yayi ya tafi har ya kusa fita ya juyo in har baku kawo kudi ba,  nan da Awa uku zaku iya rasata yana gama fadin haka yayi ficewanshi, dukewa Ummu tayi ta saka ihu, “shikenan nasan mun rasaki Maryama ina zamu samu wannan kudin, dagota taji anyi Sumayya ce ta dago Mahaifiyan nata ta fara magana cikin Dakiya, “Ummu bazamu taba rasata ba zanje duk inda zani sai na nemo kudi a yau dinnan Nayi miki alkawari, da sauri ta juya tayi hanyar fita Office din, da sauri Ummu ta biyota tana kwala mata kira, ina ai ko waiwayota batayi ba tai gaba,,,,,,,,,!!!!
Kudai cigaba da bin alkalamin yar mutan zazzau yanxu aka fara wasa farin girki, shin Sumayya ina zata samo kudi har dubu sittin don yima yar uwanta aiki, to nima dai ban sani ba kubi ni sannu a hankali✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Follow me on whatpad
ZainabSalihu933
More Comment more typing ✍️✍️✍️✍️
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(POOR GIRL)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love 💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U (UOM KHADY)
MARUBUCIYAR:
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
Na sadaukar da page dinnan ga duk wani wanda Basu da gata Basu da Mai taimaka musu, Ubangiji bai manta daku ba, ku kyauta ta Ibadunku ku kadaitashi gurin Bauta, kuyi hakuri ku rungumi rashinku, Shi da kanshi ya fadamana yana tare da masu hakuri, Allah ka rufamana Asiri duniya da lahira Ameen ya Allah.
💘💘PAGE 3TO 4💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Fitowan Ummu bakin Asibitin yayi dai dai da tafiyar Sumayya a Napep,
“Ya Allah ka karemun diyata duk in da zata shiga a fadin duniya, Karka ba ma Mutum ko aljan damar cutar mu da diya, 😭 tana fadin haka tana kuka, juyawa cikin Asibitin tayi ta zauna jikin wani bishiya, ta zabga tagumi,
*************************
Itako Sumayyah tana tare me Napep tace mai kasan gidan Govnor yace mata “eh nasani Amma keko yarinya me zakije yi gidan gwamnati? “
“Nidai kawai tunda kasani muje Kawai,
Direct Sumayya gidan gwamnati suka nufa don ita a dan karamin tunaninta
Da haukanta na kuruciya ai su shugabanni ne kuma Malaminsu yasha fada musu cewa hakkin Al’uma yana wuyar shuwagabanni, bata san cewa su shuwagabannin namu ba haka suke ba Basu tausayawa talakawansu tsakanin su da talaka sai lokacin zabe in ya zo, shine suke sanin talaka nada Anfani a gurinsu, itakuma ta kudurta ma kanta saita ga govnor tace ya taimaka ma Rabin ranta karta Mutu, ta na isa Ungwar  mai Napep ya sauketa a farkon layin yayi mata nuni da gidan daga nesa ya tafi abunshi, sauka tayi ta fara tafiya, sai ta fara ganin jami’an tsaro kota ko ina tundaga farkon unguwar gabadaya kallon ta sukeyi sbda wasu yamutsatstsun kayane a jikin ta duk sun kode ta kasan doguwar rigan ma ya yage dinkewa tayi da tsare da allura,  haka hijabin da ke jikinta duk ya yage har ta wuyan hijab din rike wuyan hijabin nata takeyi sbda karya fadi, duk da haka tsaf tsaf take bata da datti ga kwantaccen gashinta da ya kwanta gaban goshinta, kyakyawa ce Sumayya Yarinya ce yar shekara goma sha uku a duniya gata tana da irin saurin girman nan,   Amma yarinya ce mai basira da iya sarrafa magana, gata da kafiya da juriya da rashin tsoro don ita tun tana karama bata da tsoro kuma in tamaka wani abu zaka dauka yar shekara Ashirin ne,  akasin Yayarta data kasance Matsoraciya, duk wanda ya taba mata Yaya to bashi ba zaman lpy don sai ta hada mai jini, gata akwai zuciya,
“Ke ina zaki iyeh? wani security ne ya taso yazo ya tareta daga shiga gidan gwamnatin don sunga tabbas nan ta nufa kuma in aka barta shiga zatayi, lpy Malama muna tanbayarki kin mana shiru, sai data gama kare musu kallo tsaf tace musu”nazo gurin Govnor ne, gaba dayansu kwashe mata da dariya sukayi, wani a cikin su ne yace mata”Haba yan mata anfada miki ganin Govnor ganin mai talle goro ne, kowani karabiti ne zai ganshi, sai kinada Appointment dashi kuma yasan da zuwanki, “to kusamun Appontamant din mana don ni wlh bazan bar nan ba sai naga Gwamno, juyawa security yayi suka kashe ido da yan uwanshi, sukayi wani murmushi mai ma’anoni da yawa, dayan ya fara shafa kai “yan mata kwantar da hankalinki zaki ga Govnor badai Govnor ba tace “Eh shi,  “to kin ganshi kin gama, kin ganninan nine na hannun daman Govnor, biyoni muje, haka ta bishi a baya har suka shiga cikin government House, wani guri yabi da ita tana ankare da hanyar da suke bi, har suka isa wani guri da ba hayaniya ba Jama’a a gurin kaman  ba cikin gidan ba, kuma tana lura da duk in da suka wuce sai ance mai Oga anyo kamu kenan wannan yar shila haka akwai kwasan gara yau kenan, da Fatan za,a rage mana, “karku damu, wani guri suka je wucewa taga wani hadadden gaye ya fito rike da jaka a hannun shi can kuma taga ya kira wani security, sai  taga ya daddan na wasu abu a jakar sai ta bude kudine cike da jakan, tsayawa tayi tana kallon shi ji take kamar ta bigeshi ta kwace kudin don da ganin wannan baida da wani karfi, cire wasu kudin yayi ya ba security “kayi kokari ka shigo mun da ita fa Karka bari kowa ya ganka lokacin dazaku shigo, “angama ranka ya dade, yana jujjuya kudin “kudi masu gidan rana in kana dashi ka wuce gori, juyawa yayi ya tafi shikuma gaye ya bude Motan ya ajiye jakan kudin bai rufe ba ya juya zai tafi karaf suka hada ido da Sumayya data tsaya tanata raba ido, gabanshi ne Yaji ya fadi, da sauri tayi gaba tabi wannan security, waige waige ya farayi, bai ga inda tayi ba, “kai dama Ana ganin Aljanu da rana ne, don dai wannan yarinyar tafi Kama da aljana, niko nace yallabai Mutum ce, juyawa yayi ya shige ciki,
“Dallah Malama ina kika tsaya naga alamar baki son ganin Govnor din, “wlh bawan Allah ina so, ka taimaka mun, “to Naji duk abunda na ce kiyi karki min musu Kinji? “To insha Allah indai ni zan ga gwamna ai da sauki, “sosai zaki ganshi, wani daki taga ya bude yace mata ta shigo, “a nan ne zan ga gwamna? “Eh mana shiga tayi,  kallon dakin tayi dakin ya hadu falone madai daici Yaji royal furniture’s farare kal kal ga wani madaidaicin TV jikin bango dasu home teather kananu masu kyau gefensu ankawatasu da wasu golden flowers, tana can tana kalle kalle, har yaje ya kulle dakin ya dawo kusa da ita ya zauna matsawa tayi tace”mallam ina gwamna meye kakeyi haka, dora yatsan shi yayi akan bakin shi, yace mata “shiiiiishh kibani hadin kai kin san rayuwar duniya taimakeni in taimakeka ne, in kin taimakeni kin bani Zuma nima in taimaka miki kiga Govnor, in kuma kin ki in danne ki in miki  ta karfi, kuma bazaki ga Govnor ba, ga mamakin shi dariya yaga ta kamayi, ta tashi tana mai kallon baka da hankali, “ni tun farko inda ka fada mun haka da baka wahalar da kanka ba, a zuciyan ta kuwa ji take kaman zai fado saboda tsananin tsorata da jin abunda yace, “muje to ko a falo zamuyi harkan washe baki yayi yace kice ke yar hannune ashe?  “Sosai ma Amma don Allah kanada igiya? “Mezakiyi da igiya kuma? “Oh ashe ma kai baka kware a harkan ba kenan, ai wani style ne Sai anyi Anfani da igiya, “ok yana fada yana washe baki aikuwa kaman ina da wani bari in duba kicin dina, “tom binshi da kallo tayi shege ramammen banza ita data daure wanda suka fishi ma ta bugi banzaye, balle shi da daga gani sigari ya tsotse shi, jeka kawo igiyar daureka dan iska kawai, Agogon dake dakin ta kallah taga har anci Awa daya da barin ta Asibiti, “yauwa Baby gashi ko, to cire hijab dinta tayi ta ajiye gefen gadon dakin, karban igiyan tayi, tsayawa tayi kuma ta rasa ta ina zata fara, can wani dabaran ya zo mata, yauwa ka kwanta mana, shiko banzan kamar wani sakarai haka ya kwanta yana wani washe baki, “ke zaki ciremun kayan koh Baby, “Eh Karka damu cire mishi riga ta farayi tanayi tana istigfar har ta cire mai, daga igiyar tayi taga ashe ma uku ne a hade,  “ka rufe idonka Karka bude Sai nace maka ka bude, kaji “to baby ba matsala, igiyar ta jawo ta cire guda daya, hannuwar shi ta Kama ta fara daurewa, ta tabbatar ya dauru don Sai da yayi karan Azaba, “Haba baby ban son raki fa, “na bari sorry, a zuciyarta tace kai ka san Wani Sorry, kafanshi ta Kama ta fara daurewa aiko ya bude idon shi da Sauri “wai ke lafiyan ki haka akeyi zaki dunga daureni, banza dashi tayi ta cigaba da abunda takeyi, tun yana daukan abun wasa har ya fara, mata bala’in ta kwance shi baison style din wannan ai iskanci ne da mugunta,
Hhhhh dariya Sumayya tayi “to sannu dan bunsuru,!!!  yau ba, abunda zai hana in dan dakeka  daga kaina bazaka kara marmarin yi ma wata yarinya fade ba,  igiyar da batayi Amfani dashi bane ta daukeshi ta fara zanan shi dashi ihu ya farayi, ta samu kyalle ta daure mai baki saboda karya cika mata kunne Sai da ta mai jini da majina, ta dauki Key din ta bude dakin ta fito, sai Sauri takeyi kokarinta ta isa inda taga saurayin nan na dazu, Fatan ta bai tafi da kudin nan ba ta rokeshi ko shi zai taimaka mata, tana isa taga ba kowa gurin Sai Motar da taga saurayin ya saka jakan kudin nan dazu da Sauri ta isa gurin Motar tana zuwa, ta leka Motar ta hango jakan a ajiye akan seat din jawo murfin tayi Sai taji ya bude, wani ajiyar zuciya tayi, waige waige ta farayi ko zataga wani na kallonta, aiko dataga bataga kowa ba jawo  jakan kudin tayi Sai taga ya bude,  hannunta na rawa tasa hannu zata dauki kudin kara wani abu taji ta bayanta firgigit tayi, ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Please 🙏🙏🙏
Follow me on whatpad
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comPart one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(CLEVER GIRL)
fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR :
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
Na sadaukar da Page dinnan gaba daya ga Dillalai Family Allah ya Kara mana dankon zumunci ya hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki daya, Ameen ya Allah.
💘💘PAGE 5TO 6💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Da Sauri ta waiga Sai taga ashe wata kyanwace ta sagale a wani karfe shine datayi tsalle Sai karfen ya fado, shine yayi wannan kara😂 nasan reader har kun tsorata koh, da Sauri ta dauki rafa daya a cikin kudin ta cusa cikin riganta ta maida Motar ta rufe juyawa tayi tana tafiya a hankali ba wani alamun tsoro ko fargaba a tare da ita  duk security da ya ganta bai cemata komai sbda anganta da Oga dazu, tana isa gate aka bude mata, ta fita, haka ta cigaba da tafiya harta kai karshen layin, nan ta fara falfala gudu, wata Babban motane tasha gabanta kasan cewar layin ba kowa, ungwar shirune, wasu manyan mutane ne suka fito daga Motan fuskan nan ba Rahma Kwata Kwata “GB ku riketa fa kalan wanda Oga ke sone fa, kasan kusan sati daya kenan muna yawan bamu samu ba gashi yau abu har gida karku sake ta gudu, haka sukayo kanta kaman mahaukatan zaki juyawa tayi ta diba a na kare su kuma suka ce dawa Allah ya hadasu,
Gudu takeyi kaman ranta zai fita don ta tabbatar in wa innan mutane suka kamata shikenan bata ba kara ganin Ummun ta da yar uwanta, in bata kuma ya rayuwarsu zata kasance, tuna haka yasa ta kara wani masifan gudu kudin data dauko ne, taji faduwar rafa daya dayan ma na shirin faduwa, haka ta kara damke daya, ta cigaba da gudun ta ga Ungwar da uban nisa kafin a fito hanya, ga karfinta ya kusa karewa, gashi su kuma Basu da niyar dena binta kokarin su su kure mata gudu, ta gaji don kanta,
Zuwa tayi ta tsallaka wani dutse tayi tuntube ji kake Tim ta fadi kanta ya bugu da dutsen, Amma karfin hali irin nata kokarin mikewa takeyi, jirine ya dibeta, ga wani tsafi dataji a kafarta, kara ta kwallara, sbda Azaba, dai dai lokacin da suka kariso gurinta matsawa baya ta farayi, a tsaunen datake, “don Allah kuji tausayina karku cutar dani ni kadai na ragema Mahaifiyata, Sun kashemun Uba sun kashe mana yayyina da yan uwana sun tarwatsa garin mu da Ahalin mu, don Allah kumin rai, “hhhh Oga kajita fa waya fadamiki yan mata mun san Allah, to mu Umarnin Ubangidan mu Kawai muke bi, gunda ki tsayama mu cire abunda zamu cire a jikin ki ta sauki, ko kuma mu miki ta Azaba, idon ki kawai zamu cire da halshenki, da Nonon ki guda daya kacal, fashewa da wani irin kuka tayi tana tuno da Addu’a da kullum Ummu take koya musu,
Addu’a na neman tsari Addu’a ce mai karfi, a lokacin da kke neman taimakon ubangiji:
Bismillahil lazeey la ya dhurru ma’ah ismihi shai’un fill Aradhi walah fis sama’i wahuwas sami’un Aleem, Addu’an da ta dunga mai maitawa kenan, a cikin ranta, “GB!!! “Na, am oga, “bani wukar nan, da askan nan, “angama Oga miko mishi yayi, “ku bankaremun ita, to nufanta sukayi gadan gadan.
Wani mahaukacin iska sukaji yayi sama dasu kafin su isa gareta, dukan su saida suka tsorata har itama Sumayya Sai data tsorata wani kyakyawan saurayine ya bayyana, yace “duk wanda ya fasa tabata a cikin ku, ko in ce duk wanda ya shirya mutuwa ya taba yarinyar nan, “kai a waye dubeka kanajinka kaman tsinke, “ai abun ba, a nan yake ba, “GB gamamun dashi, “angama oga Nufo mutumin yayi gadan gadan,  yana isowa ya kawoma saurayin nan duka, yaga ko motsawa baiyi ba, aikuwa kafin ya maida hannunshi Sai ganinshi yayi a sama Ana hajijiya dashi, Saurayin nan da Hannu daya ya dagashi, hadashi da gini yayi tuni ya sume, yace akwai wanda yake bukatan ya bishi, tsagayawa daya yayi, yaje ya kamo Sumayya yasa mata wuka a wuya, “Karka sake ka motsa in ba haka ba zan kasheta, bai gama rufe vaki ba Yaji sauka dutse a kanshi, da Sauri ya yarda wukan, Sumayya tayi Sauri ta dauke wukar wani ne ya nufota gadan gadan, “Sumayya da Sauri ta waigo ganin wani ya nufota da gudu da wuka a hanunshi aiko wani tsalle saurayin nan yayi Sai gashi gaban mutumin nan wukar hannun mutumin ya kwace ya hankadashi daga daga yayi ya fada kan Sumayya dake tsaye tayi ready da wukarta a hannu, fadowar dazai yi Sai a kan wukar hannunta, jikake lubus a cikin shi, ihu tayi hadi da tureshi, jinine ya tsartu mata gaba daya hannunta ya baci da jini da riganta don tuni hijab dinta ya fadi, na shiga Aljanna nayi kisa, ganin haka yasa sauran suka ranta a na kare,”shegu mushirikai kawai tashi Kinji, “wai dazu Sai Naji kaman Sunana ka fada bawan Allah, “au wai dama sunanki Kenan kawai ni zuwamun yayi raina naga kuma kin dace da Sunan shiyasa na fada fa, “wai ya akayi kake jin Hausane don Nidai Banga alamun kayi Kama da Hausawa ba, kafi Kama da larabawa, ko indiyawa, dariya yayi mata”kema ai hakane,  inda kika iya nima haka na iya,  kema ai bakiyi Kama da bahaushiya ba, “nidin ai kai kafini kyau, kamar wadda ta  tuna wani abu da Sauri ta mike, ihu tayi ta koma ta zauna tana rike kafanta, wayyo kafata bazan iya tafiya ba kuma Banga kudina ba, zanje kar Yayata  ta mutu, “kwantar da hankalinki rayuwa da mutuwa duk na Allah ne, ba wani bawa dazai iya hana wani mutuwa indai lokacin shi yayi, ki yarda da kaddara mai kyau ko mare kyau, Kinji?  Muga kafan Kama kafar yayi ya ja da karfinshi,  “shishhh wayyo Ummu zan mutu, yi hkr kanwata zaki ji sauki, Addu’a yayi ya tofa mata a gurin take taji duk azaban datake ji ya tafi, ba wani sauran ciwo a gurin, “mike mu gani kanwata tashi tayi taji kaman bata taba jin ciwo ba, miko mata kudi yayi, ga kudinki malama kiyi Sauri kije ki kai Allah ya bata lpy, “kai ina ka dauko mun duka sun fadi fa, “dama ina biye dake lkcn da suke binki shine naga kin yar shine na daukomiki “ngd sosai, juyawa yayi zai tafi, “baka fada mun sunanka ba kaikuma kasan nawa, “Mujaheed, haka kawai yace mata yayi gaba abunshi.
Tashi tayi ta fito daga dan kangon da suke, tana fitowa ta ganshi jingine da get din wani gida ya zuroma inda zata fito ido, tana fitowa Sai ga wani mai Napep kaman an jefoshi ita dai bataga zuwan shi ba kawai ta ganshi a gabanta ne, Hajia Muje  koh, shiga tayi tana kara leken  shi, tana daga mai hannu, juyawa tayi kafin ta juyo ta nemeshi ta rasa, jingina  tayi ta rufe ido tana tunanin irin jarumtar shi, da karfinshi gashi daga ganinshi dan hutune, bai saba wahala ba, “hajia mun iso kai Mai Napep har mun iso, wai ya akayi kasan inda zanzo ma, ai wannan mutumin ya fada mun fitowa tayi, tana fadin “nawane kudin ka, kije kawai an biya, “waya biya wanda kika gan mu tare, tom ngd sosai don Allah in ka koma ka kara mai Godiya, juyawa tayi ta shige cikin Asibitin Sai a lokacin ta fara tunani wannan mutumin ai baiyi Kama da masu Napep ba, kuma sun mata Kama da Mujaheed.
*************************
Hango mutane tayi sun taru a wani guri, da Sauri ta karasa gurin, Ummu tagani durkushe rungume da Maryama tana kuka, hade da sunbatu “karki mutu Maryama, ki tashi wai ku ko likitocin nan bakwa taimako ne iyeeh  wlh ya’ta inta mutu bazan taba. Yafe muku ba, da Sauri ta karisa ta rungume su  “Ummu ta mutu ne badai ta mutu ba, inko haka ya faru duka sai na kashe likitocin nan ” da gudu ta tashi ta shiga doctors ward tana kiran doctor kuzo ku dubamun yar uwata ga kudin na samo✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Please 🙏🙏🙏
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Part One free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(EXPECTED DIE😭)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love 💖
Story
WRITTEN BY:
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY:
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR :
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
Na sadaukar da wannan page din ga yarana yammata Allah ya rayamun su,  Nana Khadija (Baby Nana)
Badiyat (Iftihal)
Aminatu(baby Amnat)
💘💘PAGE 7 TO 8💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
“Ke baki da hankali ne zaki shigo ma Mutum Office ba sallama ba komai,!!  “Dakata doctor ba kudi kke bukata ba to ga kudin nan na kawo kazo ka dubamun yar uwata, Matukar yar uwata ta mutu kaima sai na kashe wlh ta karishe maganar cikin daga murya, shikan shi likitan ya tsorata da yanayinta ga hannunta duk jini, gashi tana kara zaro mishi manyar idanuwanta,
“Calm down  ina yar uwan taki?  “Gata can kun yasar da ita a waje saboda baku da tausayi da Imanin na kasa da ku, tana tafiyane take fadin haka,  yayin da likitan yake ta binta a baya kafin su isa likitan yakira Nurse  sun isa gurin dasu Ummu suke durkushe, nan da nan aka dorata a Emergency Bed, suna gungurata nan da nan aka samata oxygen, suna isa ward din Sumayya da doctor Salim suka iso ward din, shigewa dakin yayi Sumayya ta mara mishi Baya zata bishi, “please ki jira a waje, “Doctor bazai yuwu ba sai na shiga inga halin da yar uwata take ciki, tana fadin hakan gami da shigewa dakin itama, waya doctor din yayi nan da nan sai ga wasu Nurses sun iso nan suka dibi jinin nata suka tafi lab.
Twenty minute later sai gashi an kawo result da jinin da za,a samata, dama already Doctor ya gama seating mata canula ya bata diazapharm ya mata Allurar Catarflam Ana zuwa da Blood din kawai samata akayi, Bayan ya gama samata ne ya rubuta musu recipe akan suje su biya kudin test dana jini dana gado, shikuma yayi ficewarshi Sumayya ta bishi da harara kaman ta shake shi takeji, Ummu ne tazo ta ruku hannayenta duka biyun “Sumayya jini ne a hannunki ina kika samu jini,  inna lillahi wa Inna llaihir raji’un, fashewa da kuka tayi ta rungume Ummun nata “Ummu yau nayi kisan kai Ummu da Hannu na wlh,!!!  “Subhanallahi garin yaya wa kika kashe mun shiga Aljannah kuma zamu dawwama ciki,😂Uwa ta gari kenan memakon ta kirama kansu shiga uku, shine tace sun shiga Aljanna, kiraga yan uwana musamman ma mata, bai kamata don wani abun firgici ya sameki ki bude baki kina ihu kina fadin kin shiga uku, kina kara jefa kanki cikin bala’ine in baki sani ba yar’uwa sbda haka mu kiyaye, Allah ya sa mu dace Ameen 🙏🙏
“Ki zauna Ummu zan miki bayani duk abunda ya faru, zama Ummu tayi “ina jinki diyar Albrka, nan ta kwashe duk abunda ya faru ta fadama Ummu, kara fashewa Ummu tayi da kuka, tana kara rungume yar tata, “Allah na gode maka daka kubutar mun da yarinya, ka kara karemun su a duk inda zasu shiga a duniyar nan, kayi musu katanga ga duk wani azzalumi, ka kare dukkan yan uwa musulmi, “Ameen Ummu bari inje in biya kudin in dawo, “to ki kasance mai Addu’a a duk inda zaki shiga a fadin duniyar nan, ki kula da kanki ki kare martabanki, karki bari abun duniya ya rudeki ki zubar da martabanki da Allah ya baki, duk tsanani da rashi karki kara daukan abun Wani, nima insha Allah bazan gajiya ba gurin muku Addu’a, Allah ya tsare sai kin dawo, “insha Allah Ummu ngd Allah ya barmu tare Allah ya kara Lafiya da Nisan kwana, “Ameen ya Allah diyar Albrka.
*************************
Sallama tayi Amma dukansu ba wanda ya Amsa mata, suna can suna hira, matsawa ta karayi gurin tagar “wai hala Arnane a gurin nan ko kurame ?  “Kut ke Uban waye kikecema Arna, “oh Ashe ba kurame bane ko Arna rashin sanin darajar Mutane ne da sanin falalan Amsa sallaman yasa nake muku sallama kuke wulakantani, “An wulakanta kin yar matsiyata kina da abunda zakiyi ne? Bata gama rufe baki ba ta dora mata Mari hagu da dama a kuncinta, “Ni nafi karfin wulakancin kuma ubangiji ne kadai yasan matsiyaci tsakanin nida ke, sbda haka ki kiyaye gaba, karki kara saka iyayena a zancenki, da Fatan kin gane, dukansu yan matan gurin sai kowa tayi gum, itako wanda tasha Mari an barta dafe da kunci tana takaicin wai kaman wannan katsamiyar yarinyar ne zata daga hannu ta mareta a gaban mutane, aiko zata san ta mareta, sai ta dau mataki akanta, mikamusu recipe din tayi suka fada mata kudinta ta biya ta kara gaba,
*************************
Washe gari da Wuri Sumayya ta koma gida taje don ta sama musu abunda zasuci, gidan nasu gidane na kasa sai daki daya da fale fale ma aka zagaye gidan sai dan makewayi shima da aka tsagaye da fale fale, ba siminti a gidan, Kofar dakin nasu ma da zumma suka kulle, Bayan ta kwance Kofar ta shiga dakin, dakin ba komai sai dabe don dakin ma baida siminti sai dan kullin kayansu a gefe sai wani tsohon zanin gado da matashi guda biyu da suke shinfide a tsakar dakin sai wani tsohon cocila da suke haska daki dashi, can gefe kuma wani kwando ne ajiye da dan kwanoni da tukunyar dasuke girki sai wani roba dasuke Tara ruwa sun rufe da wani balallen murfi, Amma dakin nasu fes fes yake ba datti ko kadan, zuwa gurin roban dasuke Tara ruwa tayi ta dauki wani yankakken jarka da aka mai dubara aka samai hannun bokiti, ta dibi ruwan ta nufi makewayin su, tayi wanka, Bayan ta fito ne, ko man dazasu shafa basu dashi, jakan kayan su ta dauko ta fara cirowa rasa ma Wanne zata sa tayi duk wanda ta dauko sai taga ya dan yage, da kyar dai ta samu wata riga da zani tasa da dauko wani kodaden jan hijabi tasa fitowa tayi ta Kama hanyar kasuwa,domin tadan sissiyo musu abunda zasu bukata,
*************************
Kasuwan wambai ta fara zuwa sbda ta tsinto musu yan kayayyakin gwanjo, haka ko ta samo musu su Pakistan da yan kwancen atanfofi irin wanda ake saidawa din nan wanda Basu ji jiki ba sosai ta sissiya musu daganan ta dan sissiyamusu takalman roba guda bibbiyu, kwari ta wuce taje ta dinko musu hijabai, da kayan robobi dazasuyi Anfani dashi ta karo musu tukunyar girki, kayan Abinci taje ta siya musu harda kwadon kulle kofa duk sai da ta siya musu da kyar take tafiya, sbda  Nauyin kayan dake hannunta, sai ji tayi ance “hajia tafiyace da Sauri ta waigo don jitayi kaman tasan wannan muryan, “lah kaine Me Napep din ranan nan Koh,? “Anya ni kinga ban ganeki ba ma, ina zamuje? “Hausawa zaka kaini “to fitowa yayi ya kwashi kayanta ya samata a cikin Nafep din sannan ta shiga shima ya zagaya ya shiga yaja suka fara tafiya,
Kaman ance ta waiga ta gefenta sai kawai suka hada ido da shi, a cikin wasu Motoci na alfarma, jiniya na tashi Alamun wani mai mulki ne zai wuce haka ababen hawa suke ta basu guri, lokacin da suka hada ido da ita tayi Sauri ta kauda kanta, sbda suna dab da motan ne, ji tayi yana waya yana fadin ranka ya dade eh yanzu naga yarinyar shekaranjiya nan, Ok a bita a zo da ita kenan?  Ok angama sir, “Me Nafep don Allah ka kara gudu Na shiga Aljanna wlh zasu kasheni kamu gudu,!!! kara wuta Me Nafep yayi inda sukuma suka rufa mai baya,,,,, ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Please 🙏🙏🙏
Yar mutan zazzau ce😍😍😍
Part One free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(ACCIDENT WALK)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY :
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR:
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
Wannan page din nakine Uwata ta kaina Allah ya kara miki lpy da Nisan kwana,
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
💘💘PAGE 9 TO 10💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Waigawa baya tayi taga alamar Motar nan fa mai kirar Benz AMG din nan tana binsu, a baya, “Don Allah Mallam ka kara gudu banaso su kamani in suka kamani kasheni zasuyi wlh!!”
“Karki damu namiki alkawarin bazan taba bari su cutar dake ba Kinji?”   Duk inda suka bi kawai kauce musu akeyi, basu ankare ba kawai sai gani sukayi wata babban mota tayi sama dasu, haka suka dunga gun gure akan titi a cikin Napep din, Amma duk da haka bai sa sun fado daga Napep din, itako Sumayya ba irin Addu’a dabata dunga yi ba, sai gashi Napep din nasu ya tashi ya tsaya kamar yadda yake, Mutane ko sai Salati akeyi an sadakar da cewa sun mutu, saboda irin bugun da motar ta musu sai da glass din Napep din ya fashe, sai Ubangiji yanuna ikonshi dukansu ba wanda Yaji ciwo a cikin su, Napep din na tsayuwa yako kara tada ta suka cigaba da tafiya yayin da Motan da suka biyosu suka juya tunda suka ga sun fadi din nan,
    “Alhmdulillah ya Allah lallai na yarda Addu’a takobin Mumini,  bawan Allah ngd sosai, gashi na jamaka an bata ma Napep,”   “karki damu duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi,”
    Dai dai Kofar gidansu suka tsaya kasancewar gidan nasu a kan hanya ce, fitowa yayi ya sassauke mata kayayyakinta gaba daya, duk wannan abun da ya faru ba abunda ya fadi a ciki, “Mallam ngde Nawa ne kudin ka?”  Haba ki barshi kawai, Allah ya kare gaba, ga Number wayata nan in kina bukatan zuwa wani guri ki kirani i insha Allah ni kuma zanxo,”  binshi tayi da kallo tana Mamakin meyasa yace haka, kodai shima macucine yake so ya yaudareta, kai wannan baiyi Kama da Mugaye ba.
Itama da bata da waya da Mai zata kirashi, bata ankare ba saijin tashin Napep din tayi, yaja yayi gaba, ajiyar zuciya ta sauke, ta fara kwasan kayan tana shiga dashi cikin gida, Bayan ta gama kwashe kayan ne, ta kwance zumman data kulle Kofar dashi ta fara fitowa da kayan dakin gaba daya, ta shinfida musu Ledan kasa data siyo musu, da yar tabarma duk ta siyo da wani Second din  akwati  kwashe kayansu tayi wanda suka riga suka ji jiki ta fita dasu, wanda ta siyo musu kuma ta fito dashi tsakar gida don ta wankesu.
     Tana wankin ne tana girka musu shinkafa mai barbaden Yaji da Mai, Bayan ta kammala wankin ne, taje ta dibo musu ruwa a makotan su, sai da ta cika musu abubuwan dasuke sa ruwa, ta kara share gidan tsaf, tayi wanka ta zuba abinci a wani container mai murfi data siyo musu da zuba  tafasashshen ruwan zafin data tafasa a wani karamin flask duk data siyo shi yau, tana Aikin ne tana Sauri duk hankalinta na gurin su Ummu da rabin ranta kota farfado ko bata farfado ba Allah masani Bayan ta kammala komai, ta kwashe musu kayansu ta shirya musu a akwati, ta dauko Abinci da ruwan tsafin ta fito ta kulle musu Kofar dakin,
  Fitowanta gida kenan zata tafi Asibiti sai ganin Mai Napep din tayi a gaban ta, “Malama muje koh?” Mamaki ya fara bata wai Ya akayi yake sanin fitanta ne, Koda yaushe yana bibiyanta,  “Malama tunanin me kikeyi hakane?”  “Ba komai shiga tayi,  ya Kama hanya,  ita kuma tana jira taji yace mata ina zamu taji bai cemata komai ba.
*************************
Da gudu ta shigo layin nasu tundaga nesa ta fara buga horn tun kafin ta kariso estate din “Oga ga fa Hajiya nan ta iso yau daga ganin irin tafiyar da ta shigo dashi ungwar nan akwai matsal”  tun kafin ta kariso ya danna remote din dake hannunshi get din ya bude kasancewar dama get din Automatic get ne, a tsiyace ta shige gidan dogon tafiya tayi, yanda tasha round about din gidan,  inda tsakiyanshi water fountain ne yana zubo da ruwa gefenshi wasu flowers ne masu launin pink roses ruwan nan na zuba a kanshi, haka tasha kwanan gurin ga wasu security zaune gurin da gudu suka tashi don sun san halinta zata
 ciki dasu, bata wani tafiya mai Nisa ba, ta isa parking place nasu wanda gurin parking din ma kanshi abun kallo ne, sbda lafiyayyun Motocine a gurin na alfarma sunkai talatin, ko gyara parking batayi ba ta fito ta shige ciki da gudu tana kwala ma “Mamma!!! Mamah!!.
Vote
Share
Comment
Pleassse✍️✍️✍️✍️
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(GOVNOR GIRL)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY:
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR:
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
Wannan page din nakane dan uwa prince Isma’il na baka kyauta😍😍Allah ya bar zumunci.
💘💘PAGE 11 TO 12💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
**********************
“Mammah!!  Mammah!!!”  Da Sauri Hamshakiyar Matar datake zaune a wani hadadden kujera irin na alfarma don tsayawa ma lissafo muku haduwar falon bata time ne, ita kanta Matar ta hadu irin  cool light skin take dashi, tasa wani Bowel less wanda akallah zai kai dubu dari biyar, tayi ado  da wani dan kunne da sarka na diamond hannunta yasha jan lalle kannan Yaji uban attached daga ganin ta kasan kudi da hutu ya zauna a tare da ita, Zaune take ta dora kafanta kan jikin wata dattijuwa tana mammatsa mata Kafa, jin kiran da yar lelenta kemata ne yasa ta tashi a rude tana Waigawa har tana tun kude yar dattijiyan nan, “lafiya  yar Auta waya tabakine meyake faruwa?” Duk mahaifiyar nata ta jeramata wadan nan tanbayoyin a jere,  dai dai lokacin da wani hadadden matashi yake saukowa daga steep shima a rude ya fito, gurin dasuke tsaye ta rungume Mammah tana ta ihu kace yankata akeyi  “Calm down my sister who touch u eyeh tell me,?
Cikin shagwaba da sangarta ta fara magana,  ” Can u imagine Brother wai yau ni Ikram wata yar matsiyata zata daga hannu ta Mare ni,!!” ta karishe maganar tare da kara fashewa da kuka a tare Mammah da Sultan suka hada baki gurin fadin “What!!?”  “Dats y nace miki ki hkr da wannan Aikin mekike bukata a duniya Baby iyeeh!!  Gashinan a banza wata yar talaka wanda bata da matsayi yar matsiyata har ta samu dama daga hannu ta mareki a banza,”!!
    “Is enough Brother Kai a tunaninka taci banza ne wlh sai na dau mataki a kanta”.
“Ai ya zama dole kuwa Auta ki dau mataki don ni ban dauki talaka a bakin komai ba a duniyar nan face bawa makaskanci matsiyaci,   Ya subhallah aikuwa Mammah kinyi kuskure a rayuwarki babu wanda yasan matsiyaci sai Ubangijin daya haliccemu, zai iya yuwuwa ma tafi ki daraja da daukaka a gurin Ubangiji,
   “Brother muje ina son magana dakai”  “ok muje wani hanya suka bi Nidai Banga alamun kofa gurin ba,  Amma ga mamakina sunq isa gurin wani abu suka danna kawai saiga kofa ta bayyana wani kalan Model classic door ne mai ruwan cement budewa yayi yana anbatar sunayen su tare dayi musu well come, shiga sukayi sai gasu a kan lifter Kofar ya koma ya rufe can na hangosu saman benen na uku, banda inda naga saurayin ya sauko dazu, zagayowa sukayi sai gasu a wani falo wanda yafi na kasa haduwa da komai da komai, daga wall paper din da ake ma falon design dashi har set din royal furniture’s dakin Ash colour ne da white, kujerun suka nufa suka zauna, haka suka gama maganar su ban samu daman jin me suke cewa ba, dariya suka kwashe dashi tare da tafawa “dat is my Kanwa shiyasa nake son ki gurin iya hada mugunta but kin tabbatar zan kwashi dadi?”
   “Sosai ma Brother”  “baki da matsala zan sami  su KK da B gay da su JJ kawai zamu yi Aikin tare,”  rungumeshi tayi “shiyasa nake son ka my sweet Brother”.
   “Yah to Baby wlh I need u fa,”  “Haba brother ko dazu fa da safe na baka, kuma kaga yanzu na dawo gidan nan na gaji,”
 “Haba baby kin san dai ke din ne akwai sweet shiyasa ban gajiya dake, please muje ko sau dayane ki ban don wlh a Yanzu in baki ban ba akwai matsala, kuma B gay baya kusa dana rage zafi dashi, “Uhmm Naji kawai muje in baka but bazamu dade ba,”
   “Yauwa kokefa my sweet Baby tundaga falon ya fara cire mata kayan jikinta, suka hade bakin su guri daya suna ba juna hot kisses daukanta yayi ya nufi wani daki da yake cikin falon da ita, baka jin komai sai tashin nushin su, Niko nace wa’iyazibillah ya kamata iyaye musa ido game da yayan mu, kina zaune a gida a matsayin uwa Amma baki san me Ya’yanki suke aikatawa ba, dole a matsayinki na uwa kisa ido sosai akan hakan,  zamani ne yanzu yazo da zaki ga Uba yana lalata ya’yanshi, yaya ya lalata kanwarshi,  Uncle yanemi yanshi, Wannan masifa da muke ciki sai dai muce Kalu Inna lillahi wa Inna llaihir raji’un, Allah gamu gareka ka karemu ka kare mana Imanin mu, ka kare mana ya’yan mu da kannin mu da dukkan yan uwa musulmi baki Daya.
***********************
Suna isa cikin Asibitin ya sauketa tare da Mata Allah yaba mai jiki lpy, ta Amsa mai da Ameen, tana shiga dakin taganta Zaune ta juya baya, da gudu taje ta rungume ta Bayan ta ajiye kayan hannunta “Alhmdulillah Rabin raina karki kara tafiya ki barni ina sonki,”  da Sauri ta waigo itama ta rungume kanwar tata tana mai zubar da hawaye cikin sanyin Muryanta irin na marasa lafiya take magana tana kuka, “ina sonki Yar uwata ke rayuwata ce gaba daya nayi kewar ki na tsawon lokacin danake kwance banda Lafiya, please karki kara saka kanki a irin hadari dakika jefa kanki duk Ummu ta fada mun yanda akayi, please rayuwarki ga Ummu tafi rayuwata a gareta Anfani don ni inaji a jikina nidin ba mai tsawon rai bane, please ko Bayan raina kicika mun burina na zama lauya kuma ki tabbatar kin bi mana hakkin Ahalin mu da muka rasa, dariya tayi hade da kuka, tsayawa tayi ta share hawayenta,  ni nasan kanwata Jaruma ce macece mai kamar Maza tunda har ta iya karawa da yan garkuwa da mutane ta ceto mu tabbas nasan zata cikamun burina😀ta karishe maganar tana mai murmushi,.
   “Don Allah Rabin raina ki daina fadin haka taya kike tunanin rayuwata zata inganta Alhalin bakya raye hakan bazai taba yuwuwa ba, Insha Allah zamu rayu tare kuma mu mutu tare,!!  Ta karisa maganar tanajin wani irin tausayin kansu, Ummu ce ta kurama ya’yan nata ido tana mai jin tausayin halin da suke ciki, da wani irin rayuwa zasu fuskanta nan gaba, basu gama tunanin da sukeyi ba gaba dayansu ba, sai gani sukayi Ana shigo da cattun cattun din su Maltina, madara, drink’s da sauran kayan ciye ciye, gaba daya mamaki ya rufesu wannan kayan daga ina, basu gama Mamaki ba sai da suka ga an ajiye musu Rafar kudi yan dubu dubu guda biyu,. ✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow
Please 🙏🙏
Yar mutan zazzau ce💞💞
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(CONTINUATION  THE STORY 1)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY:
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY :
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR
💗💗GIDAN GADO💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
wannan page din gaba daya naku ne Yan GIDAN GADO Fans group ina yinku irin sosai din nan.
💘💘PAGE 13 TO 14💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM,
*******************””*****
“Malam lafiya wannan kayayyakin daga ina haka?”  “Hajiya wani ne a waje yace mu shigo dashi kuma gadon farko yace,”  “to bai fadamuku inji waye bane”
    “Gskya Hajiya bai fadamana ba sai dai zaki iya tashi ki fito ki ganshi,”
Da Sauri Ummu ta mike tace musu muje in ganshi, suna fita basu ga kowa ba gurin, “ina yake bawan Allah ni ban ganshi ba to?”
   “Wlh yanzu fa muka barshi a nan a jikin motarshi, may be ya tafine,”   juyawa Ummu tayi tana kallon Sumayya da mamaki sosai a fuskanta “dama har yanzu akwai sauran masu tausayi a duniya diyar Albrka,  ta karishe maganar mamaki karara a fuskarta, “hakane Ummu kila Allah ya dubemu ne bisa halin da muke ciki ya kawo mana taimako,” komawa ciki sukayi suka tarar da  Maryama rike da wata farar takarda  da Sauri suka kariso kusa da ita, “rabin rai wannan takardan fa,?”
  “Yauwa rayuwata zoki gani a jikin Rafar kudin nan naga takardan kun san me aka rubuta a ciki,?
  “A,a sai kin fadamana,!!  Cikin kosawa da jin meza tace musu, “Ummu cewa akayi wai mu koma makaranta nida rayuwata  in mun koma gida za’a turo wanda zai dunga mana lesson, kudin nan dashi zamu koma makarantar, “to waye wannan mutumin wai?”
   “Allah kadai yasan ko waye, Allah mun gode maka burina zai cika Rayuwata, rungume juna sukayi, gaba daya yan dakin tsayawa sukayi suna kallon su, sun ba kowa tausayi da sha’awa irin yanda suka nuna ma junan su Soyayya da kulawa,
***********************
“Mammah kin san bazan taba iya rayuwa ba in ban samu doctor Saif ba kin san sbda shi nake zuwa Asibitin nan, but badon haka ba mai zai kaini, kuma kin san shidin sai mai sa,a matashi mai tashe, shi matsalan shi ba ruwanshi da talaka da Mai kudi baida girman kai gashi ya cika tausayi, bai san wulakanci shiyasa duk in aka kawo patient a gaban shi nakanyi pretending akan nafi kowa tausayi da Imani, sbda fa ya soni Mammah Amma har yanzu ko kallo ban ishe shi ba, Saif kenan daga mataimakin shugaban kasa, shi Ikram ke mutuwar so a rayuwarta shiko bai san tanayi ba, Asalima duk fadin Asibitin ba wanda ya tsana irinta saboda duk wani rawar kanta da iskanci da wulakanta jama’a din datakeyi duk yana sane, kawai kallonta yakeyi, “please Mammah ki ban shawara taya zan mallakeshi, ni ina son ko bai aureni ba in dandani zumanshi,”
   “Hhhh kai Baby baki da kunya a gabana kike fadin haka kidai bi Maza a hankali, ni nafi son ma ki aureshin but bari Papa ya dawo daga Ethorpia zamu san yanda za,ayi ina tunanin zamuje gurin boka dan tsito ne, a shawo mana kanshi don ba abunda yafi karfin Boka tsito,”    “yauwa my Mammah shiyasa nake sonki, rungumanta tayi ta bata peck a goshinta, ta juya da gudu zata haye sama, “Baby”   “yes Mammah lafiya,,?   “Yauwa wai ina kawar nan taki Lailah ina son ganinta ne wlh,”
    “Mezaki mata Mammah wai kina nufin yar gidan Commissioner Of Police din nan, wlh fada mukayi da ita randa naje gidan su Daddy ta ya nemi yamun akuyanci shine na zageshi fa shine taji haushi,”   “gskya Baby baki kyauta ba, to meye a ciki ai tsofaffi sunfi dadin harka,  wawiya a banza kyaje ki ba kwailayen yara, to kizo ki ban Number ta,”
“Wai Mammah mai zakiyi mata ne?”  “Ke wai ina ruwanki ne ha’a ko ni Inkina harkanki ina samiki idone, karisowa tayi tana kun kunai ta ba ta Number, ta juya tayi gaba abinta, niko nace ikon Allah wannan wani irin gidane ba ruwan Uwa da harkan da  ya’yanta wai wannan ne freedom, Allah ya tsaremu da irin wannan rayuwa, Ameen ya Allah.
************************
Bayan kwana biyu Maryama ta warke yau ne ya Kama za’a sallamesu, Doctor ne ya shigo, tunda ya shigo gaba daya ward din aka bishi da kallo sbda zaban haduwan shi, farine shi irin farin nan na larabawa  daga ganin shi kasan halfkass ne wato ruwa biyu kenan, ga wani kwantaccen gashin shi dayaci kudi sai sheki yakeyi wanda ya zagaye dogon fuskan shi ya kara zagaye karamin pink lips nashi, sai ya bada wani style ta kasan gemunshi, yayin da gemun ya sauko dan daidai ga dogon hancin shi, hade da sexy Eyes nashi masu Kama da Mai jin barci gasu farare tas dasu, gaba daya ya tafi da Imanin Sumayya, gaba daya ta kasa tantan cewa tsakanin shi da Mujaheed wayafi kyau, karisowa yayi kusa da gadon su, “yadai kanwata ya jikin naki?”
Jin muryan shi yakara rikitar da Sumayyah Muryan shi iri daya da na Mujaheed dadin muryan su ko wata mace albrka,
“Alhmdulillah na warke yau zaka sallamemu koh Doctor,?”
Rubuce rubuce ya cigaba dayi a file nata sai da ya gama ya dago yana kallonta”meke miki ciwo yanzu?” “Ba komai Doctor,  to Alhmdulillah  ga wannan takardan magunguna ne dazaku siya, sannan a dunga kula mata da magani, ki kula da kanki sosai kar ki dunga shiga sanyi Kinji, “to doctor insha Allah, “Yauwa Ummu Allah kara Lafiya kuyi kokari ku sayi magungunan, zaku iya tafiya, “ok doctor mun gode sosai,
Haka yaci gaba da duba marasa lafiya har ya gama yazo zai fita, kasan cewar gadon su Maryama a bakin kofa yake, sai ya tsaya ya kalli Sumayya yana murmushi “yadai kanwata ko kin sanni ne?  Ya fadi haka yana daga mata gira, ya fice abunshi yana murmushi, kunya taji ya rufeta ashe yana kallonta, ta rufe fuskanta da hannunta. “Yar albrka ki tashi ki nemo mana abun hawa, to Ummu, fita tayi don samu musu Napep din dazai kaisu gida, Fitowanta get ke da wuya suka Hadu da me Napep din nan  dai “da Fatan ban makara ba ranki ya dade? Kallon shi ta tsaya yi tana mamaki, ✍️✍️✍️✍️✍
Share
Comment
Vote
Follow
Please 🙏🙏
Yar mutan zazzau 😍😍😍
Part one free
💞💞💞 WAZAN AURA 💞💞💞
(CONTINUATION THE STORY 2)
Fictional 😩
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY:
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY:
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR
💗💗GIDAN GADO 💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din nakune   kannin Ummata
Aunty Amina Allah ya raya Zuri’a
Aunty Asma’u Allah ya kara miki lafiya ya raya baby Aseeyat.
Ina sonku irin sosai dinnan.
💘💘PAGE 15 TO 16💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
“Kina mamaki ne Hajiya?” Kawai muka rasa ciki kice su Ummun su fito, samun kanta tayi da kasa mai musu juyawa tayi ta shiga cikin Asibitin don kiran su Ummu su fito, “yauwa Ummu bari in fara rage kayan sai ki kamo rabin rai mu je koh”
  “To yar albrka” kwashe kayan ta farayi tana fita dashi, har ta kammala kwashewa, tazo suka kamo Maryama suka fito suka dorata akan Napep din sannan suka shiga suka sata tsakiya, ya tada Napep din suka Kama hanya sai Gida.
   Nan da nan suka iso kaman kiftawan ido su kansu Sunji Mamakin isowan su Ungwan tun daga nesa suka fara ganin sun doshi wani Gida wanda baiyi Kama da nasu ba, “kai Mallam wancan gidan su waye?”
  “Hajiya gidan kune ai, to waya gyara mana haka?  Nidai ban sani ba dazu nazo wucewa naga Ana muku gyaran, suna cikin magana sai ga Mudi ya kariso gurin Napep din yana washe baki, “Ummu Sumayya da Fatan bakiyi fushi ba wlh ina ta sa ranar da zanzo in duboku wlh ban samu zama ba, ga wannan key din gidan kune kawai tashi mukayi mukaga an rushe gidan cikin dare daya an canza ginin Bayan sun gama ne sukayi sallama dani suka bani key din sukace yau za,a sallamoku in kun dawo a baku, kawai binshi da kallo sukeyi dukansu su uku cike da mamaki, “ku sakko mana bari in bude muku gidan, sakkowa sukayi suna binshi a baya kafin su kariso har ya bude musu, ita kuma Sumayya ta tsaya kwaso musu sauran kayayyakin su, shiga sukayi ciki gaba dayansu harda Mudi yana ta santin gidan yana basu labarin a cikin kwana daya aka gama ginin kowa yayi mamakin a unguwan, dakin da suka gani suka shiga falo ne Babba ba komai a ciki sai carfet dake malale a tsakar dakin sai kuma wasu dakuna guda biyu ta gefe, shiga dakin sukayi sukaga yar katifa guda biyu a dakin da drawer a jikin bangon dakin budewa sukayi suka ga kayane na sawa masu kyau dai dai talaka gefe da gefe kowanne gefe da Sunan Mai shi, Abun nan ya bar Basu mamaki tsoro ma ya soma basu, gefe guda kuma takalma ne Kala Kala aka ajiye ta gefen drawer, fitowa sukayi suka shiga dayar dakin, shikuma katifa daya suka gani a dakin sai drawer shima, da Alama nan ne dakin Ummu, fitowa sukayi suka tarar da Mudi yana zaune yanata zuba a waya, Sumayya ta kalleshi ta girgiza kai “Mudi iyayen surutu, fitowa tsakar gida sukayi wani daki guda biyu suka hango wani hanyar Kofar gida wani kuma kusa da Falon su, na kusa da Falon suka fara shiga, suka ga Ashe kitchen ne ga buhun Coal nan a gefe har da abin  girki na Coal ga kayan abinci harda kayan miya, komai na girki an ajiye musu, fitowa sukayi suka shiga na hanyar zaure suka ga Ashe bayi ne, suna fitowa Ummu ta rungume su Allah mun gode maka, wahalar mu ta yanke dukkan wanda yayi mana wannan abu indai don Allah yayi Allah ya biyashi da mafificin alheri, Ameen Sumayya da Maryama suka fadi a tare tabarma suka dauko suka bqzashi a tsakar gida suka zazzauna suna hiran gidan da santin shi,.
*************************
BIRNIN MISRA
“Haba Mujaheed taya kake tunani Saka Soyayyar Bil’adama a ranka Bayan na fadi maka, iya abun da nake so game da yarinyar nan kuma kasan indai aka samu Matsala burin mu bazai taba cika ba duk da da Allah muka dogara, Amma dole ka cira wannan abun a ranka, domin cikan burin Mu, dan tsohon ya karishe maganar shi cikin bacin rai, tsohone ya tsufa sosai zai kai irin shekaru duba daya da dari biyar a duniya, yana zaune ne a wani lafiyayyen Dausayi na sarauta wanda bazaka taba tunani ganin irinshi a duniyar nan ba, wani hadadden kujera ne da akayi shi da jan Alharini da danyar Diamond aka hada sai kyalli yakeyi, yayin da gefen shi kuma wata kyakyawar Mace wanda kyawunta bazai taba misaltuwa ba, tana zaune a gefen tsohon na hagu, yayin da shi kuma wannan saurayi da tsohon ke Mai fada yana zaune gefen damanshi dukan su sunsha fararen kaya na alfarma, yayin da budurwan nan take ta aikama saurayin da Harara, shiko bai san ma tanayi ba, “kai kuma Mahbub Aikin ka na kyau ka tabbatar duk inda zata kana tare da ita da duk Ahalinta duk da bazamu iya canza kaddaranta gaba daya ba Amma zamu yi iya Abunda Ubangiji ya bamu iko domin ganin cikan Burin Masarautar nan, “Angama ya shugaba”
      “Zaka iya tashi ka tafi,  “godiya nakeyi shugaba na barku lafiya, ke kuma Gimbiya Zaherat ki kiyaye kar kishi ya rufe miki ido ki jawo mana Asaran Abunda muka dade muna jiran shi, “Afuwan ya kai Jaddi Abdullah insha Allah zan kasance mai biyayya,”   yauwa Amaryata, kai kuma Yarima Mujaheed a kiyaye gaba Allah ya muku albrka, Ameen suka hada baki gurin fadin haka,.
*************************
“Burinka bazai taba cika ba matukar baka kawo mana abunda mukace maka ba wato Nonon budurwa wadda bata cika shekara Ashirin ba da idon ta da harshenta, sannan sai kayi Anfani da yaro dan shekara shida, to indai ka aikata haka to tabbas zaka ci Zaben Senator  kuma akwai Budi da harka mai yawa a cikin shi, kuma ga Zabe ya karato, kayi kokari, Tashi ka ban guri na gama dakai, kai nake jira, da sassarfa Mai girma Govnor ya fito daga bukar yanata Sauri. ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Follow
Please 🙏🙏

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements