WAZAN AURA Page 11 to 20 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / WAZAN AURA Page 11 to 20

WAZAN AURA Page 11 to 20

WAZAN AURA Page 11 to 20

“Wai ke meye nufin ki Zankadaziyyatu in har Soyayyan zanyi zanyi dake ne iyeeh daki kazo kika kawo karata gurin Jaddi me kike tunani a ranki, ina so in fada miki wani abu daya ki daina bibiyan rayuwata kina samun ido!!!” Ya karishe magana cikin fushi,

  “To sai me don na bibiyi rayuwarka kar ka manta Baka da matar Auren data wuce Zankadaziyyatu ko kaso ko karkaso,!! Itama ta karishe maganar ta cikin daga murya hadi da bacewa a gurin gaba daya,.
Juyawa yayi zai tafi suka hada ido da wata Hamshakiyar Mace datake kishin gide a kan wani lafiyayyen carfet gabanta cike da kayan marmari, Murmushi tayi mai, gami da yafito shi da hannunta Alamun yazo gareta,
Karisowa yayi ya nemi guri ya zauna.
“Ya kai Yareema mai jiran gado sai yaushe zaku daina wannan fadar kai da yar uwanka ka sani Jaddi bai magana biyu ya riga ya fada maka cewa Zankadaziyyatu itace matarka, meyasa dukan ku bazaku kwantar da hankalinku ku fahimci juna ba,”
“Yake Ammiyat kisani cewa duk duniya bacin ke da Jaddi ba wanda nake so sama da Fasihat Amma Jaddi ya rufe ido yace bazan Aureta ba ba Aure tsakanin mu, wai ba jinsin mu daya ba, Abun da ke ban Mamaki taya ta kasance a cikin mu Alhalin ba jinsin mu daya ba, kuma taya ta kasance kamar su Daya da Sumayyah wanda Jaddi ya dorani bisa aikin da nakeyi yanzu,?”
“Kayi hkr ya kai Yareema banda hurumin Amsa maka wannan tanbayoyin naka, sai ranar da Jaddi zai baiyana komai tashi ka tafi,.
Tashi yayi jikin shi a mace ya wuce domin fita kilisa ko Yaji sanyi a ranshi.
*************************
KANO NIGERIA
“Meye Anfaninku iyeeh sai lalai wannan yarinyar iyeh duk fadin kano Ace kun rasa yarinya wadda bata kai shekara sha biyar ba, ga yan mata nan Mayun kudi wanda zaku yaudaresu da kudi ku samu abunda kuke so, na baku nan da Awa Ashirin da hudu in ba haka ba, ya karkada kai ya juya zai tafi, sai kuma ya wai go “Markel”   “sir”
 “A samo mun yaro dan shekara shida inda bukatar shi, ka tabbatar ba wanda ya ganka lokacin dazaka dauko yaron,”
“To Sir ba damuwa angama, “dukkan ku ku tafi na sallameku ina son shiga meeting da zamu yi da yan majalissu ku tabbatar kafin in fito komai ya kammala, sbda wannan aikin ne fa yasa na dawo Nigeria don gskya da ban dawo yanzu ba sbda ban gama hutawa ba, “OK sir Karka damu komai zai tafi Normal suka hada baki gurin fadin haka, juyawa yayi yashige abunshi sukuma suka fita,
*************************
“Yar albrka kizo ki duba a Kofar gida dawa ake sallama,”
   “To Ummu, fitowa tayi rike da hijab dinta a hannu tana sawa, tayi hanyar Kofar gida, tana fitowa wani mutumi ta gani sanye da farin jallabiyan shi kar kar, murmushi yamata tare da fadin brka dai,    “yauwa brka”
      “Sumayyah koh,?
 “Eh nice lafiya daga ina?
“Irin wannan tanbaya haka Malama Sumayyah Wanne zan Amsa miki a ciki, rufe ido tayi tana murmushi,  “yi hkr bawan Allah duk na kosa ne in san kai waye harda kasan sunana,  karki damu Mahaifiyarku na ciki da yar uwanki, ki nemamun izini zan iya shigowa, “to tace hadi da juyawa cikin gida ta sanar ma da Ummu Sakon shi,.
“To dauko tabarma a daki ki shinfida sai kije kice mai ya shigo,”to  Ummu dauko tabarman tayi ta shinfida ta Kama hanyar fita don bama bakon nasu izinin shigowa, ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Follow
On whatpad
ZainabSalihu933
Please 🙏🙏
Yar mutan zazzau  ce😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA 💞💞💞
(MAI GYADA GIRL)
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY:
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY :
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR
💗💗GIDAN GADO 💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
Wannan page din nakune Iyaye masu kwadayi ku dorama ya’ya tallah ba ruwanku da wani hali zasu shiga kudai kawai aka wo muku kudi, ya kamata Iyaye mu kula da Yaran mu Amanace Allah ya bamu kuma zai tanbaye mu game da Amanar da ya bamu, ba yara mata kadai ba Yanzu har yara Maza ma abun lura ne, Allah ka karemu ka kare dukkan mysulmin duniya Ameen.
💘💘PAGE 19 TO 20💘💘
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Bayan shigowan shigowan su ya nemi guri ya zauna, suka gaisa da Ummu,
“Dama an turoni ne domin in dunga ma su Sumayyah karatu dana Addini dana Zamani sai dai ban san ya tsarin zai kasan ce ba,?  Ya karishe maganar yana kallon Ummu,
“Ikon Allah Kai ko bawan Allah waya turoka? Ka taimaka ka fadamana ko zamu samu muyi mai Godiya sbda irin dawainiyar da yakeyi damu,.
“Ayyah karki damu shi baya bukatar godiyanku, abunda zakuyi mai kawai shine Addu’a da barin su Sumayyah suyi karatu mai zurfi shine burin shi kawai,  don ganin sun zama wani abu nan gaba hakan shine burin shi,.
“Insha Allah ni kuma nayi Alkawari ni Ummu zan barsu suyi karatu indai hakan shine farin cikin bawan Allah nan,  yanzu kullum ne Karatun ko sati sati?”
“Kullum ne Ummu sbda kinga an wuce su sosai kuma jarabawa zasuyi ita Maryama na gama secondary ita kuma Sumayyah na aji ukun Secondary duk ita ya kamata ta tafi din don bamu da lokaci sosai Amma sai dai in naga yanayi kokarinta.”
“Tom Allah ya taimaka mun gode sosai sai zuwa gobe kenan zaku fara?  “eh insha Allah,  tashi yayi yama Ummu sallama ya tafi,
Fitowa duka sukayi suka rungume Ummu “Alhmdulillah Muma mun kusa zama yan makaranta Ummu”
“Sosai kuwa yarana Allah dai ya biya wannan mutumin da mafificin Alheri Ameen suka Amsa dashi gaba dayan su.
“Bari in tashi in doramana Abinci Ummu kafin lokacin shan maganin Rabin rai yayi,
“Godiya nake rayuwata da kulawa, gashi dai burin mu ya kusa cika Amma sai inaji a jikina na kusa tafiya in barku, ni nasan nawa burin bazai taba cika ba sai dai kanwata zata cikamun burina😀” ta karishe maganar tana murmushi.
“Don Allah rabin raina ki daina fadin haka kina sani cikin fargaba da tunani, in har da ace mutuwa na shawara da zan ce ta daukemu tare don ban son in mutu in barki cikin wani hali,
    “Don Allah yan albrka ku bar zancen nan kuna dagamun hankali duk lokacin da kuke irin wannan hiran, Maryama kece Babba kuma ke kike fara tado wannan maganar don Allah ki daina hakan na dagamun hankali duk da nasan Mutuwa dole ce, Amma ina Fatan inga Auren ku harda jikoki ma, gaba daya dariya sukayi suna rungume mahaifiyar tasu,
    “Insha Allah Ummu mun bari bazamu kara ba tare suka shiga kitchen suna kokarin yin Dan wake, sunayi Ummu na basu tarihin fiyayyen Hallita da irin gwagwarmayar da yasha da kafiran makkah,
Hakan ake son Uwa ta gari ta kasan ce da ya’yanta Koda yaushe ya kasan ce hiran abunda zai karesu zata dunga musu ba gulmace gulmace ba,
Har suka kammala suka wanke komai suka dora ruwan dazasuyi wanka ita kuma Maryama na yanka musu Albasa da tomatoes da cabbage din dazasu ci dashi, Bayan sun kammala  Ummu ta fara wanka sai Maryama sai Sumayyah tayi ita ma,  sukayi sallah kasan cewar lokacin sallah yayi, sukayi Addu’oi wa Mahaifinsu da yayyinsu da dukkan sauran yan Uwa Musulmi baki daya,
Fitowa tsakar gida sukayi suka shinfida tabarma Sumayyah taje ta zubo musu Abinci a faranti,  ta dauko yankakken Salad din nan da Mai da yajinsu wanda Yaji hadin tafarnuwa da sauran kayan Yaji, ajiyewa tayi suka yaryada salad din da yaji da Mai,  Bissimillah sukayi suka fara ci.
*************************
“Ke mai gyada kawo mana, karasowa tayi da farantin gyadanta dafaffe tana wani karairaya daga ganin ta kasan tasan duniya, kuma karamar yarinya ce wanda batafi sha uku ba taci adon ta da janbaki har saman idonta, “gani na nawa kake bukata?”
      “Yauwa dan zagayo ki shigo kiji kudi ya nuna mata yana kashe mata ido tsaro ido tayi tana washe baki, waige waige ta fara don ganin ba mai kallonta nan da nan ta shige Motar,
” kai mallam sai kamun bayani ba gyada kake bukata ba mai gyadan kke bukata, ta karishe maganar tana washe mai bakin ta da yaji jan baki,
 Shiko tukin shi kawai yakeyi burin shi ya isa gurin Ogan shi ya sauketa don shi duk ta isheshi da surutu,
Suna isowa yace mata fito,
    “In fito da farantin gyadan ko in barshi ciki da Fatan ba dadewa zamu yi ba kuma Ni Dubu biyar ake ban,
    “Duk baki da matsala ni dubu dari ma zan baki gashi ya jefota da Rafar kudi yayi gaba yace ta biyoshi, daukan kudin nan tayi tana murna yau bata san Wani irin albarka Inna zata samata ba in ta kai mata kudin nan,  niko nace yarinya kin kawo kanki gurin ajalinki ne,
Binshi tayi da gudu suka shiga wani falo dataga ya hadu iya haduwa sai kalle kalle takeyi, “ki zauna ina zuwa yace mata ya shige wani daki, can suka fito da wani katon Mutum mummuna dashi, “kai GB ka iya zabe fa, kafin akai ga aiwatar da aiki sai na dan huta da ita, shigamun da ita daki kaima in kana bukata in na kammala sai Kaima ka dana, duk maganar da sukeyi da turanci sukeyi shiyasa mai gyada bata gane abunda suke cewa ba,
    “Tashi muje koh”
“To tace jikin ta ne kuma ya fara yin sanyi kasancewar ganin mutumin nan datayi sai taji tana tsoronshi don duk iskan cinta da yan yara takeyi, Ina zata kai wannan katon, niko nace yarinya kwadayinki ya kawoki, suna shiga dakin yasata ta tube kayanta sai tana neman yi musu gardama
   “Ni na fasa don Allah ka maidani inda ka daukoni, ta karishe maganar tana mai fashewa da kuka,
  “Ke yima mutane shiru, haka tanaji tana gani kattai har biyu sukayi Anfani da ita✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
And
Follow
In whatpad
ZainabSalihu933
Please
Yar mutan zazzau ce😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(MAI GYADA DIE😭)
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love 💖
Story
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY :
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR :
💗💗GIDAN GADO 💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page sadaukarwa ne gareku yan biyu kyautar Allah  Hassan and Hussaini ATK ina godiya Allah ya bar zumunci.
💘💘PAGE 21 TO 22💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Sai da suka ga ta daina numfashi sannan suka kyaleta, “GB je ka dauko mun askan nan,”    “to oga juyawa yayi ya bude drawer dake dakin ya dauko wasu kananan wukake guda biyu, ya miko mai janta sukayi kiii kaman kayan banza suka kaita toilet din dakin, suna isa ba Imani ba komai yasa wukar nan ya yanke breast din yarinyar nan suka kwakule mata ido a takaice sai da suka cire duk abunda suke bukata a jikin Mai gyada, abun ba kyan gani, haka suka maida gawarta cikin wani buhu suna jiran dare yayi domin suje su maida inda suka daukota,
Horn din da sukaji yasa duka suka fito kasancewar sun san mai zuwa gidan yana zuwa, Bayan ya fito ne suka take mai baya zuwa cikin gidan,  Alhaji Attahiru Lado kenan mai girma Govnor kano kenan mai ci yanzu, Bayan ya zauna ne yake kallon Yaran nashi,
     “Da Fatan komai ya tafi yanda nakeso ko an kammala duk abunda nace an kuma samo mun yaron da nace,?”
      “Eh ranka ya dade an kammala yaron kuma na nan a ciki,”
   “Ok gud aikin ku na kyau,  shiga dakin yayi ya tarar da yaron gaba daya ya takure a karshen gado yana ta kuka, yanajin an bude Kofar ya tashi da Sauri jikin shi na rawa,
     “Don Allah ku kaini gida Ni kadai na rage ma Mamata babana ya mutu nima kar ku kasheni!!”
   “Kwantar da hankalin ka ba kasheka zanyi ba in har ka bi umarni nina ina gama abunda zanyi zan sa a maidaka in baka ma harda kudi kaji koh,
    “To to wlh zan bi ni dai kawai kar ku kasheni,”
“Yauwa gud Boy, haka Alhaji ya tube gaba daya kayanshi a gaban yaron nan ya cire ma yaron kaya shima, nidai da Sauri na juyo kasancewar idona bazai iya kallan wannan zaluncin ba, ihu yaron ne ya dawo dani daga duniyar tunanin da na shiga, wai yanzu duk wannan abu akan duniya ake yinta, Mutane na manta cewa duniyar ba matabbata bace,
Allah ka sa mufi karfin zuciyar mu, yasa Imanin mu ya rinjaye zuciyar mu Ameen ya Allah,
Can sai ga Alhaji ya fito yana share zufa ya hada uban zufa, “Markel a yayyafa ma yaron ruwa in farko ku maidashi inda kuka daukoshi, kufa kiyaye da kyau kar ku bari a ganku aiki ya lalace mana, “Angama ranka ya dade, Kama hanya yayi yai ficewarshi kasancewar lokacin sha biyu na dare ne,
****************
Washe gari  Su Sumayyah ne da Aunty ta sun fito gida domin zuwa diban ruwa a Fanpon ungwarsu,
  Can suka hango taron mutane Anata rirrike Maman Hansai kanwar Mudi Guggo mai gyda tana ihu kamar Mahaukaciya, da Sauri suka karisa gurin don ganin meke faruwa, Hansai kanwar Mudi suka gani kwance cikin jini an cire wasu sassa daga cikin jikinta, Ihu Maryama ta saka tana kankame yar uwanta data kasa ko motsi a gurin
    “Rayuwata ki kalli Hansai ne fa an keta mata haddi, an kuma cire wasu abu a jikinta kai duniya ina zaki damu, Wai Mutane suna mantawa da za’a mutu ne iyehhh, An maida rai ba’a bakin komai ba, tabdijam,
    Ruwan da basu debo ba kenan suka juya gida suna fadama Ummun su abunda ya faru, da Sauri Ummu ta dauki mayafi suka rufamata baya don zuwa gidan su Mudi,
Anyi ma Hansai sutura Ana jiran Babanta ya iso ne kasan cewar bashi gari yaje kauyen su,
 Dandazon yan jarida ne suka cika Kofar gidan su Mudi don jin yanda akayi Guggone take magana cikin Kuka,
    “Kawai na dora mata tallan gyadane gurin karfe goma sha daya na safe ta fita nasan kuma duk dadewanta bata wuce karfe biyu sbda Hansai akwai kan kasuwa zaka ganta ta dawo, shiru shiru har biyar na yamma tayi nan Hankalina ya soma tashi nace ma Yayanta gashi ya fita ya nemo min ita, tunda ya fita sai gurin Tara na dare ya dawo yana fadamun cewa bai ganta hankalin mu gaba daya ya tashi ba wanda ya runza a gidan, har gari ya waye, Bayan Yayanta ya fito sallah Asuba ne, shine fa akayi kacibus da gawanta a Bayan Massalaci ta karishe haka tana fashewa da kuka,
      “Mama kiyi Hkr insha Allah zamu yi iyakan kokarin mu gurin binceken wanda sukayi muku wannan aika aikan ita kuma yarinyar Allah Yaji kanta, haka dai akayi jana’izan Hansai aka kaita gidanta na gskya,
Sai muce Allah ya jikanta ya rahamsheta,
Zaune suke duk sunyi tagumi Mutuwar Hansai ya gigiza yan Ungwar gaba daya,
    “Ummu ni gaba daya ma sai naji duniyar ta fitamun a rai,
“Karki ce haka ko kin mata gwagwarmayar da muka sha a bayane, kin mance Cewar a gaban mu aka kashe  Ahalinku, kafin mu zo Nigeria lokacin muna Mali da cikin ki ke Maryama muka yo gudun Hijira zuwa Nigeria,  A Maiduguri muka fara zama, Haka da wahala yai Wahala a Maiduguri, Muka dawo Zamfara a cikin karamar hukumar Wurno, nan kuka girma kuda yayyinku,  kafin hakan ya faru muka dawo Kano da Zama, duk wannan abun Nafila ne akan Abunda ya faru daga rayuwar mu,
       “Hakane Ummu Allah ya jikan Hansai,
“Ameen suka Amsa gaba daya, ku tashi muyi sallah isha sai muyi Azkar koh,
“To Uwa ta gari fadin Sumayya tana murmushi, tashi sukayi  suka yo Alwala suka fara sallah, Bayan sun idar sukayi Azkar,
  Sannan suka dauko Abinci dare suka fara ci gaba dayansu ya riga ya zama dabi’ansu cin abinci tare,
*************************
BIRNIN MISRA
kishingide take ga wasu kuyangu sun zagayeta Suna mata fita, shin reader kun san wa na gani Sumayyah ce fa, cikin kaya irin na sarauta gaba daya kaina ya kulle, ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow on whatpad
ZainabSalihu933
Please
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(THE EXCELENCY GOVNOR)
Fictional 😥
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY:
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR :
 💗💗GIDAN GADO💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Na sadaukar da page din nan ga dukkan Masoyan Littafin nan ngd sosai da kulawanku gareni inayinku irin sosai din nan Mussaman yan group dina na Facebook One Love💋💋💋
💘💘PAGE 23 TO 24💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
**********************
BIRNIN MISRA
“Gimbiya Fasihat dazu naji gimbiya Zankadaziyyatu tana wani magana, shine nace bari in garzayo in fadamiki”!! Cewar kuyangan data bayyana a gaban matashiyar Budurwan datake kishingide akan wani Dadduma na alfarma inda wasu kuyangu suka zagayeta, masu mata fita nayi masu mata tausa nayi,  matashiyar tayi kusan minti Ashirin bata bude baki tayi magana ba, har wannan kuyangan tacire rai da Uwargijiyan nata zata amsa mata, gashi har ta gaji da tsugun nawan datayi,
      “Yazali”
“Na’am Gimbiya”
“Ba na hanaki kwaso mun gulma ba, bance duk abunda kikaji ki barma cikin kiba iye ta karishe maganar cikin daga murya hadi da Nuna mata hanya Bace ki ban guri kina gab da fuskantar hukuncina duk ranar da kika kara zuwamun da gulma”!!
     “Tuba nake Uwargijiyata mai adalci da sanin ya kamata, Masoya a gurin Yareemah mai jiran gado Allah ya kara daukaka ya cika miki burinki na alheri, tana gama fadin haka ta bace,
      “Suhailat”
“Na’am Uwargijiyata ki tattara kayan nan ku shiga dashi ciki, zanje duniyar Bil’adama yau aikina zai fara, Binti dake zamuyi aikin nan kuma ban son matsala a tafiyata, ke kuma Hauliya ki zauna cikin shiri Kinji?!!”
    “To Uwargijiyan mu Insha Allah bazamu baki matsala ba,”
Bacewa sukayi ita da Binti.
*************************
NIGERIA BIRNIN KANO
“Yauwa Mama ni Sunana Doctor Raleeyat  Ya’u wannan kuma kuma Sunanta Doctor Nusaibat Habibullah Fulani,  shugaban kare hakkin Bil’adama daga Majalissan dinkin Duniya tare da ita akwai Mataimakiyar ta Doctor Fatima Zahra Ahmad Fulani, Insha Allah  Zamu tsaya tsayin daka don ganin an bi muku hakkin ku,  sannan dole Government zata biyaku Diyya akan abunda ya faru,”
“To Hajiya mun gode Allah ya saka da alheri,
” kuma Jami’an tsaro zasu shiga maganar don ganin an binciko wanda suke da Hannu a cikin wannan Al’amarin,”
Tashi sukayi Bayan sun gama rubuce rubucen su da daukan duk wani rahotan daya dace,
Ni sai a lokacin ne ma na kallesu Matane masu aji sun Ansa Sunan su a manyan Mata sun kai karshe matuka gurin kyawu da hutu,
   Sis Adama kuzo ku tayani kallo kaddai ace Ummimin Guggone haka ita da kawayenta,
Suna fita wasu hadaddun Motoci ne kiran Mercend mai black tintect,
Driver ne ya bude ya taso da Sauri ya bude musu mota suka shiga, ya tada Motan yayin da  sauran masu tsaron lafiyansu suma suka shiga Motocin su suma suka mara musu baya,
*******************
“Rabin rai kizo Ustaz fa yazo,”
     “Wlh yau Rayuwata banjin dadi ne, kin san yau garin da sanyi,
“Allah dai yasa ba ciwonki ne zai taso,
“Ameen ya Allah ta fadi haka gami da fitowa rike da takardun su, muje,
Jerawa sukayi gurin Ustaz Haleem Suna isa suka zauna gefen tabarman,
“Ina kwana Ustaz”
“Lafiya lau Yaran albrka, Yau Ummu bata nan ne,?
     “Eh wlh yau anyi bakwai din Hansai, ta shiga Addu’a,
     “Ok Allah ya ji kanta yau Karatun Ahadari ne zamuyi koh?
   Babud daharatii
“Eh Ustaz
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
SHI KANSHI MENE NE TSARKIN?
TSarki shine gushewar Najasa daga jiki ko tufa ko gurin Zama,
Shin tsarki ya kasu kashi nawane?
Tsarki ya kasu kashi biyu(2)
1:daharatul habasi
Tsarkin habasi
2:daharatul hadasi
Tsarkin hadasi
Insha Allah gobe zamu dauki ko wanne daya daga ciki muyi bayani,
“Allah  ya kaimu Ustaz,
Haka dai suka dunga lesson dinsu, Suna mai tanbayoyi yana basu Answer,
     “MashaAllah Ke Maryama result din ki ya kammala, yanzu Admission ya rage za’a nema miki,”
“Alhmdulillah mun gode Ustaz,   burin ki Rabin rai ya kusa cika na Zama Barrister,
**********************
“Ya zanjabiluuuuuuuu ya kakkarau ya mai biyan bukata gani na iso ka Bayyana ka biyamun bukata na,
Wata goguwace ta turnike gurin bakakirin Bayan ta lafa sai ga wani Mummunan Mutum ya bayyana da katon kanshi,
Tsirara ba wani kaya a jikinshi can sai ga wasu Mutanen ma sun bayyana dukan su bakaken kaya garesu, wata bakar kujera ce ta Bayyana mai siffar kwarangwal darewa kan kujeran Mutumin yayi ya zauna kafin dukansu suma su zauna,
 Wani surkulle ya farayi suma Suna Ansa mai can sai ga wani Halitta ba kyan gani ya bayyana,  gaba  daya zubewa sukayi Suna mai sujjada Bayan sun dago ne, Shugaba zanjabiluuu ya fara magana,
“Attahiru da Fatan ka kammala abunda aka saka batare da kuskure ba,
    “Eh shugaba komai ya tafi yanda akeso,
“Hahahahaha hahaha bukatarka ta biya zaka koma kujerar ka na Govnor,  kakkau ya baka albishir”
“Wani Hanzari ba gudu ba kungiyar kare hakkin Bil’adama fa sun shigo Maganar nan, Kasan wannan shegiyar kafaffiyar Matar nan ne shugaba kuma zata iya aikata komai akan ta binciko wannan maganar shine nake so kakkau  ya rufe maganar har duniya ta nade,
“Angama kakkau ya biyama bukatan ka haha haha gaba daya suka Kama dariya nan suka fara shan jinin su,
Kowa ya gama fadar bukatun shi Kakkau na biyamusu, ✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow on Whatpad
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(COMFUSSION)
Fictional 😥
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR
💗💗GIDAN GADO 💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din kyautane gareki Sister Adama ina yinki irin sosai din nan Allah ya bar zumunci, Comment dinki na tsumani💖💖💖
💘💘PAGE 25 TO 26💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
************************
“Yauwa Ummun Na kammala duk wani abu daya dace, kiyi mana Addu’a Allah ya bamu sa’a yau zamuyi Exam din nan daga shi sai Admission basai kiga na Zama yar Jami’a ba lokaci daya kiji an fara cemun Barrister Maryamah Nuraddeen Wurno, dukansu dariya sukayi,
“Allah ya Amsa diyar Albrka,”
“Ameen dukansu suka Amsa,”
“Ni naji Ustaz din ma dazaku tafi tare shiru, bai iso ba,”
“Kila Ummu wani Abu ya tsare shi Amma nasan yana hanya, wai Rabin rai mai kikeso ki zama ne nan gaba,?  Baki taba fadamana ba ko Ummu?
“Aikuwa Autan Ummu matso kusa dani ki fadimun me kikeso ki Zama nan gaba,?
“Ummu Ni abun da nakeso in zama sunada Yawa, kinga na farko ina so in Zama D.S.S wato jami’ar tsaro na fararen kaya sbda in je har Wurno in tada yan ta’addan dasuke garin,  kuma ina so in Zama Doctor sbda in dunga kula da lafiyan Rabin Rai,  sannan ina so in Zama matar wani Babban Soja kuma in Auri dan shugaban kasa ko Govnor ko wani Hamshakin dan siyasa, sbda inga Bayan duk wasu Azzalumai dasuke Kasar nan,
Gaba daya sakin baki sukayi Suna kallonta Suna Mamakin irin tunanin Sumayya gata yarinya Amma har take da wannan tunani, duk da shekarunta sha uku a duniya but, wannan tunanin na yar shekara Ashirin da wani abune, da kyar Ummu ta iya bude baki tace:
“In banda abin Auta diyar Albrka kin taba ganin inda Mutum ya Auri Maza da yawa haka, kuma inake ina Zama jami’ar tsaro kina Mace, kuma ina muka ga kudin dazakiyi wannan Karatun dakika lissafo su, dayan ma badan wannan bawan Allah ba ina naga kudin dazan dauki nauyinku haka, kidai Zabi daya,”
“To Ummu na zabi Zama likita saboda rabin raina Amma innayi kudi sai na Zama jami’ar tsaro  Ummu kawai kimun Addu’a Allah ya cika mana Burin mu,”
“To Ameen diyar Albrka Allah ya cika muku burin ku dukan ku,”
     “Ameen,  To Ummu Wazan Aura  Dan Govnor ko babban Soja ko dan shugaban kasa ta fadi tana dariya🙈tana rufe idonta,”
“Inyeeh Autan Ummu tana son Aure Ashe, to wazata Aura ne,
Sallaman da’akayine ya katsemusu hiran su,
       “Kiyi Hakuri Nanah Maryama na rashin zuwa da wuri da banyi ba, ki tashi muje Amma komai ya kammala muna zuwa kawai Admission Number zaki karba mu dawo, basai kinyi jarabawar ba,”
“Alhmdulillah Ustaz mun gode sosai Allah ya saka muku da gidan Aljanna,
     “Ameen Ummu ngd da Addu’a,”
“Ustaz nima yaushe zanje Jami’ar ne? Ta karishe maganar tana turo baki gaba,
      “To Autan Ummu karki damu kema Next year Insha Allah  kin shiga Jami’a  Medicine zaki karanta koh?”
    “Eh Ustaz”
“Tashi sukayi suka musu sallama, Maryamah ta Daura Nikab dinta da dogon Hijab dinta da Ustaz ke siyo musu ita da Sumayyah,
************************
Tsaye take bakin hanya tasha hijab dinta dogo har kasa da medical glass dinta da ya Amshi fuskanta yayin da gefenta wata Yarinya ce daza su zo sa’a daya itama tasa hijab din har kasa duka Suna rike da kur’an da littafai da Alama daga Islamiya suka dawo, Suna hira sama sama, shin kunsan wa nake gani Sumayyah ce fa,
         Wata Motace kirar
Benz AMG GT tasha tinted glass baka hango na ciki, yazo ya parker a gaban su, gaba daya hankalin su bai kan motar, sai da kawar tata ta tabota,
       “Masoyiya gafa mutumin naki can ya iso,”
“Kyaleshi ni wlh ban son Mutum mai naci haba,”
Tana rufe baki yana fitowa, kuramishi ido nayi niko ina nasan wannan,
Kai I remember Doctor Saifuddeen ne wanda ya duba Maryamah a Asibiti, wanda Ikram yar gidan Govnor take bala’in so, tofa, mai kuma ya hadashi da Sumayya,
Kafin ya kariso gurin kanshin turarenshi ya iso gareta cikin takunshi daya zama mai jiki takunshi na kasaita ya kariso gurin dasuke tsaye,
              “Haba Summyta ya kike so ki dunga wahalar da zuciyata ne kece mace ta farko dana fara so a Duniya, duk matan da suke mun rububi na kasa kula kowa cikin su ke kadai ne Hasken zuciyata farin cikin rayuwata, yau ya kamata in Koma Abuja Amma na kasa komawa saboda in ganki please kiyi Accept dina mana ko zuciyata ta samu sukuni, pleasseee ya karishe maganar yana dora mata shanyayyun idanuwansa,
Kau da kai gefe daya tayi gami da yamutsa fuska,  dai dai lokacin da Ikram ta doso a Motar ta don bin Bayan Doctor don tun daga Hospital take mai mgana yana kin kulata ya shige motar shi yayi gaba shine ta biyoshi, dai dai lokacin da shi kuma yake dukawa a gaban Sumayya,
   “Haba Baby doll dina Accept mana abunda kunni Ikram yaji mata kenan, yasata taka wani wawan birki, Kut dama takan wannan yar matsiyatan Saif ke wulakantata yarinyar data tsana a duniya wlh da sake kuwa, sai tayi maganin Yarinyar nan kuwa,
Ita ko Sumayya tana hango ta tayi wani killer Smile taja hannun kawanta sukayi gaba suka barshi a nan durkushe, kafin kace Maine sunyi nisa sosai,
Ikram na zuwa ta tsaya a gabanshi ga wani irin kishin shi dayake azalzalanta,
      “Wallahi Saif kaji kunya duk matsayinka da ajinka da kimarka ka tsaya akan wannan yar karamar yarinyar yar matsiyata sadakayallah to wai ma meta fini iye ka fadamun mana?!!
“Ke dakata karki kara zaginta ta fiki hankali natsuwa mutunci da kamala ke infact ma tafi ki komai, ya karishe maganar cikin fushi nan da nan yaji kanshi na amsawa saboda shi inda abunda ya tsana a rayuwar shi hayaniya shi Mutum ne mare son hayaniya,
Cakumo wuyan rigar shi tayi tana karaji,
       “Wlh baka isa ba sai ka soni dolenka ka Aureni Saif, hankadeta yayi tare da bata lafiyayyun Mari guda biyu,
“Kar ki sake wannan banzan tunanin naki ya dunga baki zan taba Aurenki, banza Mahaukaciya kawai, ya karishe fadin haka yana tsagayeta ya shige motar shi ya figeta da gudu,
Durkushewa tayi a gurin hadi da fashewa da kuka tana sunbatu “wlh yarinya zaki gane kin shigo rayuwata, sai nasa an illataki sannan in batar dake, inga ta tsiya, kawar tace itama ta kariso gurin, ta parker Motar ta ta fito ta kariso da sauri, ta dagota “haba kawata mai akayi akai Namiji, dazaki zauna kina kuka a kanshi, shiyasa nace ki shigo cikin mu wlh ni zan Aureki bake ba bakin cikin da Namiji kince A’a kina ko tattare da bakin ciki wlh,
“Kinga dakata Laila ni duk iskanci na bazan iya Neman yar uwata mace ba to mai zanji a gurinta, dadi  ko wahala, bazan iya ba, kawai ki rabu dani duk inda zanyi sai na Auri  Saif Lailah, “shikenan kawata Allah ya baki Sa’a ga wannan kidan kora ko kyaji sauki a ranki ta fadi haka tana miko mata wani syrop a cikin kwalba, tana karba ta kafa kai ta Shanye ta kara mika mata wani ta shanye, nan ta kamata ta sata a Mota dama su biyu sukazo, “ke Fa’ization rike key din nan ki tuko Motan nan ki kaimun gida gamunan zuwa✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
(VICE PRESEDENT  SON)
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY :
RALEEYAT  YA’U. (OUM KHADY)
MARUBUCIYAR :
💗💗GIDAN GADO💗💗
AND NOW
💞💞WAZAN AURA 💞💞
Wannan page naka ne kyauta Alhussain Abu Sameer Allah ya bar kauna Ana tare irin sosai din nan💝💝💝
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
💘💘PAGE 27 TO 28💘💘
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Rikota tayi suna tafiya tana maye tana surkullen magana,
       “Wlh sai naga bayan su dukan su dani Ikram yar govner suke magana, har ita nan yar matsiyata, kawata ki bari kawai nifa sai na Aureshi, kota halin yaya, kin ji ai,ta karishe maganar tana tafiya yuuu kaman zata fadi da sauri Lailah ta tarota,
       “Kai kawata ni wlh sakin ki zanyi, in baki tsaya ba wlh zan sake ki duk kinbi kin gajiyar dani,
“Sorry Lailah duniyar ce kawai ke dan juyamun inajina ina yawo a gajimare, haka dai suka cigaba da tafiya har suka isa part dinta, kasancewar itama part dinta daban ne, shiyasa take abunda take so,
Suna shiga ta zube a kujeran falon ita kuma Lailah ta shige kitchen dinta bude fridge nata tayi ta dauko fresh milk kasancewar Ikram na san shi sosai ta taukowa ta tsiyaya a cup wani tab naga ta dauko a cikin bag dinta ta balle tasa mata cikin drink din, tana Murmushi, “yau dolenki kawata in dandani zumanki kamar yadda Uwarki ita ta fara koyamun less kema sai kinyi wlh, in har baki ba Ubana ba, ni dole ki ban yarinya, kizo mu shana Kinje kin wani nace ma wani banza can shida ba sonki yakeyi ba, gani nida nake mutuwar sonki kina mun wulakanci, Ikram dole Nima ki soni har muyi Aure bake ba wani da namiji sai na san duk hanyar dazan bi, don ganin burina ya cika a kanki, wani dariya ta kwashe da shi kamar Mahaukaciya, fitowa tayi ta sameta inda ta barta, harta fara barci,
      “Kawata tashi kisha fresh milk dinki mana, ta karishe maganar ta sigar lallashi,
“Ki bar fresh milk din nan Lailah barci zanyi,
          “No saifa kinsha sai mu shiga ciki muyi wanka basai kiji dadin barcin ba, tana fadin haka tana dora mata a mouth dinta ai tanajin sanyi a cikin bakinta bata san lokacin data shanye tass ba,
    Tana gama sha Laila ta kamata suka shige ciki, Nan da nan Ikram ta fita hayyacinta, saboda wani iri datake ji a jikin ta, Lailah ta lura tab dinta ya fara aiki, sai cewa tayi,
     “Kawata muje in miki wanka, suna shiga bathroom din labari ya canza, burin laila ya cika,
Wa iyazubillah Allah ka karemu da Masu Hali irin nasu Lailah da Hali irin na matar Gobna,
*************************
“Ummu kinga Jami’ar kuwa ba ruwan kowa da kowa, sai harkoki ake yi, lokacin da mukaje aka mana interview wlh nasha bazan iya amsa tanbayoyin ba, kawai Ustaz Mansir na dunga hangowa yana karamun kwarin gwiwa, kawai jinayi ina Amsawa ko su kansu Malaman sai da na burgesu, yanzu dai Nima na zama student a B.U.K, Next week zamu fara lectures,
    “Yeeeeh Rabin raina tsalle tayi ta rungumeta, Alhmdulillah, Nima Next year Insha Allah muna tare ko har na hangoni nasha farin glass Ana cemun Doctor Sumayyat Sumytah,
Gaba daya dariya suka samata,
       “Kai Auta baki da dama wlh Allah ya nuna mana muna rayayyu, “Ameen duka suka Amsa, to kije kiyi Sallah sai mu zo muci Abinci,
    “Ayyah Ummu baku ci Abinci ba dama Kuka zauna jirana, “yaza’ayi muci mu barki,
Sun zauna suna cin abinci tana kara bama su Ummu labarin makarantar su, “wlh Nima rabin rai har na kosa in ga next year tayi, lokacin inada 14 yrs fa zan shiga Jami’a, kinga zan gama ina da twenty years kenan fa na zama doctor,  ke ko Rabin rainazaki gama karatu kinada shekara Ashirin da biyar, kai Ummu Yaushe Rabin Rai zatayi Aure, ni zan Zabama rabin rai Miji, “to mare kunya, wato ke zaki zabamun miji koh,?  Ai ni nariga na zabi Mijina, “to da Yaushe hakan ta faru bamu sani ba iyeh Ummu?
      “Uhmmm Nima dai ban sani ba, sai dai mu tanbayeta yanzu muji waye Mijin nata,
  Rufe ido Maryama tayi tana Murmushi, “Ummu Nifa Ustaz Mansir nakeso ban sani ba ko zai soni kin san ba kowa ke son Mace mai irin lalurar mu ba, ta karishe maganar kamar zatayi Kuka, Zuwa Sumayya tayi ta rungumeta “haba Rabin raina ba wani Namiji dazai kusheki a rayuwa ba kowa ma zai san kina fama da wannan laluran ba in ba an fada ba, kuma nasan Ustaz Mansir bazai taba wulakanta ki ba, sbda yasan darajan dan Adam kuma yana da hankali tabbas nasan zai rikeki Amana, ta karishe maganar cikin karfafama yar uwan nata gwiwa, “rabin raina ake Auran ma masu kanjamau balle ke da bashi gareki ba, karki damu ni da kaina ma zan fada mai,😀 iyeeh rabin rai ta fada lanbun Soyayya, dukan wasa ta kai mata ta kauce tana dariya,
    “Uhmmm wato abun ma yar wariyane an wareni koh yar Uwarki ma kike fadima, tasowa gaba daya sukayi sukazo suka rungume Ummun “haba Ummun mu Uwa ta gari Allah ya barmu tare,
“Ameen yan Albrka Allah ya albarkace ku, ya baku Mazaje Na gari, Maryama sarauniya naji dadin abun nan Nima na dade da sha’awar hakan sbda na yaba da hankalin shi, duk da har yanzu bamusan kowa game da yan uwanshi ba, Amma ni na yarda dashi sosai Allah kuma ya tabbatar da Alherin sa,
   “Ameen Ummun mu Uwa ta gari, suka fadi hakan a tare, Maryama na kara rufe fuska Alamun kunya, “yauwa Ummu na mance ma mun biya fa ya siyamun waya baki ganta ba ta hadu, bari in dauko ku ganta, daukowa tayi ta kawo musu, nan fa suka kara wani farin cikin, nan da nan Sumayya ta dauka, tashiga bubbude mata Abubuwa daya danganci Social media, Kasan cewar Ustaz Mansir duk ya koya musu, haka dai suka cigaba da hiransu cikin farin ciki,
*************************
BIRNIN MISRA
gaba dayan su zaune suke akan kujerar Alfarma sai wasu dana gani suna zaune kasa sun duke baka ganin fuskan su, Jaddi ne yayi gyaran Murya ya fara Magana
         “Kai  Annur ka gama aikin ka daga yau, sai ranar da Sumayya zata fara Zuwa school zaka koma, ka dai tabbatar ka basu ilimin daya kamata, kuma ka tabbatar sun iya turanci da larabci sosai?
      “Eh ya shugabana dayake ruwan maganin daka ban in zuba musu a ruwan gidan na zuba kuma yayi aiki sosai don ya bude musu brain dinsu da kyau, Abunda ya kamata ayi shi a shekara Shida anyi shi a wata shida Kaga Maganin yayi aiki sosai,
     “Hakane to Masha Allah, hakan yayi, but kasan yarinyar ta fara sonka kuwa, kara sunkuyar da kai kasa yayi,
“A gafarceni ya shugabana Nima ba’a son raina haka ta faru ba,  “ok tashi kaje, kai kuma Mahbub yanzu aikin ka ya fara, ka tabbatar kana kai Yayanta Makaranta ka daukota, sannan nasan shiriritanka kar ka sake ka batamun aiki kaji na fadi maka,
    “Insha Allah ya shugabana za’a kiyaye, na barku lafiya,
Wai reader kun san su waye kuwa, To Ustaz Mansir ne da Mai Napep din nan da yake daukan Sumayya,
“Kai kuma Mujaheed Soyayarku da ita zai farane bayan ta fara zuwa School,
Ke kuma Fasihat da Fatan aikin ki na tafiya dai dai, koh? “
“Eh ya Jaddi don  Yanzu haka dan mataimakin Shugaban kasa ya kamu da Soyayyar Sumayya sosai, sannan yar gobna ta gan mu dashi,” ta karishe maganar tana dukar da kai alamun girmamawa,
     “MashaAllah diyar Albrka Aikin ki na kyau Sosai, ke kuma Zankadaziyyatu Aikin ki zai farane bayan wasu makwanni, a garin Wurno,”
     “Angama Jaddi, Amma inace an tashi garin sai yan kidnapping?  “yes ai aikin ki a kansu zai fara, “tom Jaddi,
    “Ku tashi ku tafi,
“Mun Barka lafiya Jaddi suka hada da wani yare da ni banji mai suke fadi ba,
Suna fita daga Fadar Zankadaziyyatu ta kalli Fasihat ta Harareta itako Fasihat Murmushi tayi mata, “kanwata kenan mai Abun dariya,
Wani dogon tsaki data ja sai da Mujaheed ya juyo ya kalleta, kamo Hannun Fasihat yayi hadi da cewa “Zo muje kiji Kalbil hayaty😀 niko nace wani irin Sunan love ne haka Mujaheed, sister Adama kuyi course 😜,
Aiko jitayi kaman sun waza mata barkono a zuciyarta saboda tsaban haushi, suko hanyar Lanbun gidan sukayi,  suna tafe suna hira,”.
*************************
ABUJA NIGERIA
“Wayyo Ammi tace bata sona, taki ta saurareni zuciyata zafi take mun,
    “Haba Namijina kaifa jarumine ko a fagen fama to anan ma ka zama jarumi kar Mace tasa ka zama rago mana tana fadin haka tana shafa kanshi, shiko Kuka yakeyi bilhakki da gaskiya.
Niko nace su Saif an fada kogin Soyayya😂kamar inda Prince Isma’il ya fada kullum sai ya ishemu da posting din love, 😜😜😜Au sorry Yaya prince🙈🙈,
Kudai cigaba da bin yar mutan zazzau don jin ya zata kasance ✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Like
Vote

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements