WAZAN AURA Page 21 to 30 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / WAZAN AURA Page 21 to 30

WAZAN AURA Page 21 to 30

WAZAN AURA Page 21 to 30

Wai dama Ammy haka so yake ban taba tunanin haka Soyayya yake ba sai yanzu, Wlh Ammy zan iya komai Sabda in Sameta Matukar bai Sabama shari’a ba,

“Calm down my Namiji Insha Allah zata soka sosai, kaji yanzu ka tashi kaje kayi wanka, kazo na dafama favorite food naka, Tuwon shinkafa miyan Egusi kaji,”
      “Ammy banjin yunwa, ni wanka kawai zanyi,
“My Namiji dole fa sai kaci ko in maka dure,
   Haba my little baby,!!
    Come to your Ammy,!!
        Ammy give u favorite food  oh oh oh
Please my Baby
       Oh oh oh
Ta karishe mai wakar tana Murmushinta mai kayatarwa,
    Dariya sosai ya saki ya rungume Ammy nashi “I love you too My sweet Ammy ur Little baby eat d food,
      “Don’t worry my Ammy na, bari inje inyi wanka,
Fita yayi zuwa Mansion din shi, wanda haduwan Mansion din bazai taba misaltuwa ba, Komai na Falon nashi white and pink colour ne, yana bude Mansion din wani kanshi ne ya bigi hancina, tafiya yayi sai gashi a wani falon da ban dana farko, yafi na farko haduwa da komai, wani corner ya nufa Ashe kofa ce a gurin matsa wani Abu kawai yayi Kofar ta bude ya shige Dakin Ya Salaam reader kunga haduwan Dakin kuwa na barmuku kuyi hasashen haduwan Dakin da kanku, Bed din shi na kallah an gyarashi kaman mutum bai taba kwana kai ba, gashi ya sha Fari bedsheet fentin gadon da komai na Bedroom din sky blue ne, har grass carfet din dake kasan Dakin sauri sauri yayi ya cire kayan shi, matsa wani na’ura yayi sai ga closet din shi ya bayyana ko wani side da, da kalar kayan da ke ciki, juya closet din yayi sai ga jerin Towel Kala kala, sun kai kala Ashirin, wani pink One ya dauko ya Daura, ya danna wannan na’urar ya koma ya rufe kamar ba komai a gurin,
Bathroom din shi ya shiga, ya Salaam reader kunga haduwan Bathroom din kuwa, ta Wani gefe can wani glass ne zagayayye a cikin shi akwai Jacuzzi shower da dai sauran kayan wanka, bude gurin yayi ya shiga fara wanka yayi yakai kusan Awa daya yana wanka, kafin ya fito ya shirya cikin wani Armless  t shirt da three quarter sunyi mai bala’in kyau, but Amma har ya dan fada daka kalleshi kasan baida walwala,
Saukowa yayi ya fita zuwa Mansion din Ammy shi, yana shiga ya tarar da ita da Hand bag dinta tasa hijab nata har kasa colour hijab nata suck nata, da Nikab din dake hannunta duk kalansu daya, Pich colour sunyi Matukar Amsanta kayan sai yanzu na kare mata kallo da kyau daka ganta Kaga balarabiyar Asali, Hausarta ma Kwata Kwata bai fita, duk datake Matar mataimakin shugaban kasa baisa tayi watsi da shigar ta na Musulunci ba akasin matan shuwaga bannin mu na yanzu da zakaga suna shiga tamkar ba matan Aure ba, farace sosai irin farin larabawan nan kwantaccen gashinta da yake saukar mata har gadan baya, in ka ganta ba zakace ita ta haifi Saif ba, reader tsayawa lissafa muku kyanta ma bata lokacine,
    “My Namiji sai yanzu kake fitowa har ina Barin ma Hairan sallahun inka fito ga Food naka nan a Dining, Sbda yanzu Matar mai girma shugaban kasa ta kirani zamuje Kaduna wani Taro, tana maganar tana Daura Nikab nata, please Son kaci Abinci kaji Naso in baka da kaina ne my Namiji, but please kaci kaji,
         “To Ammy safe trip I love you dear Musabaha sukayi,
Har ta juya sai ga Hairan nan ta fito da gudu tana kiranta “Ammyt dina karisowa tayi ta rungumeta ni ban son ki tafi, I miss you alot,
       “Oh ni jikar larabawa yau kuma wata shagwaban ne ya tashi, light kiss ta bata a goshi, Oya my Baby kiyima Ammyt din ki Addu’a,
    Addu’a ta zauna ta dunga ma Ammyt dinnata har sai datace ya isa haka, bye bye, My sweet Namiji sai na dawo,
Sai a lokacin Hairan ta waiga taga Yayan nata, da tun farko bata lura dashi ba,
       “Marhaban bika ya Halwa Akheey, Mata yar ji’a bait?
       “Fis sa’atis Ashiraty Sabahan fi dair,
“Shine ko ka fadimun, Halwa Akheey, Ana tagadab,!! Tana fadi hadi da juya baya, Alamun tayi fushi Halwa Akheey dinta,
        “Ana Asfun ya Jameelatu Ukhteeh, yana fadin haka ya kariso ya rungumeta ta baya, da sauri ta juyo ta daneshi,
“Oya ni ka juya dani kamun wakar da kukemun sannan zan hakura,
       “Haba Jameelatu Ukhtee baki san kin girma bane yanzu bazan iya daga kiba,
  “Nifa sai kamun,!!
Nan ya fara juyi da ita a tsakiyar falon yana mata wakar “Anta Jameelatu Ukhtee,
          Ukhtee Nazifatuun,
Ukhtee Habebaty Ammyt
      Ukhtee Habebaty Halwa Akheey,
Dariya sosai tayi ta bashi light kiss a goshi, sannan tace “Halwa Akheey ta’al ilah huna, kaci Abinci, binta yayi suka isa Dining suka Zauna ta bude warmer din Abincin ta zuba mishi ta fara bashi yanaci,
*************************
KANO
“Ummu sai na dawo,”
“To diyar Albrka a dawo lafiya kiyi Addu’a, Allah ya bada sa’a ya taimaka ki kula da kanki Kinji,
      “Rabin raina sai kin dawo, Allah ya bada sa’a kina da kudin da zaki Hau abun hawa koh?
“Ameen ya Allah Ummu,  Ameen rayuwata, ina dashi, ta karishe fadin haka tana tafiya zuwa Kofar gidan nasu,
     Tana isa ta tsaya ta fara karanto Addu’a fita gida,
BISSMILLAHI TAWAKKALTU ALAL LAHI WALAHAULA WALA KUWATA ILLAH BILLAH, sai data Karanta shi sau bakwai Sannan ta fita,
************************
KAUYEN WURNO
“Oga dukan su an basu Wara daya daya, sannan wannan Mutumin dai da Iyalinshi suka gudu har yanzu akwai sauran Numfashi tare dashi kuma har yanzu shekaru kusan  biyar kenan fa bai farfado ba, ya kamata kawai a karisa shi,✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Vote
Comment
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
WRITTEN BY :
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U  (UOM KHADY)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din gaba daya nakine shugaba ta Gari Aunty Hauwa(maman Uswan)   Allah ya barmana ke, ya kara lpy da Nisan kwana,
PAGE 31 TO 32
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
KAUYEN WURNO
“Baka da hankali ne in har muka kashe mutumin nan kasan Asarar dazamuyi ne, to burina ya farfado domin akwai burina a kan Mutumin nan, akwai wani sirri da baku sani ba, Wai ina Shatu ne,?  Lpy yau bata fito ba ya kamata ace yanzu ta gama mana girki fa,
      “Oga bari na dubota nufan wani daki yayi don dubo wanda aka kira da shatu,
Isan Zankadaziyyatu kenan sansanin Barayin taji suna Maganar nan sauri tayi ta isa Dakin da suke magana akai kafin ya iso,
Tana shiga taga yarinyar da aka kirata da Shatu kwance cikin jini da alama Ciki gareta kuma ya zube, runtse ido tayi tana fadin wasu kalamai can sai ga wasu kuyangu sun bayyana, Umarni ta basu, “ku dauketa ku tafi da ita Asibiti Zaria, akwai wata likita, Mai Suna Doctor Nusaibat Habibullah Fulani, yau zata shigo daga Yola ku tabbatar taga wannan yarinyar don itane zata taimaketa, sbda ita ma ta taba taimakonta a baya,
     “Angama ya Sauraniyar MISRA uwar gidan Yarima mai jiran gado, bacewa sukayi tare da Shatu, ita kuma rikidewa tayi ta koma Shatu dama kafin su tafi sun tsaftace gurin cikin Second abunka da Aikin aljanu, kwantawa tayi tamkar mai Bacci, buga Kofar aka farayi kamar za’a ballah Kofar, da sauri ta taso tazo ta bude Kofar,
      “Oga yace meya sa baki fito yau ba,?
“Wlh banjin dadi ne Amma yanzu zan fito in girka muku kuyi hkr, juyawa yayi don fadima ogan su abunda tace.
*************************
KANON DABO
Lecture akeyi gaba daya hall din yayi shiru Ana lecture, can na hango Maryama zaune a sit dinta, tana yi tana jotting kasan cewan ta Sabon zuwa ita kadai ne a sit dinta kuma ita kadai ne a Hall din da Nikab, sauran daga masu gyale sai Abaya, gashi duk itace karama a Class din kasan cewan ta mai karamin jiki, sbda laluran dake damunta, na Sickle cell, yawanci masu irin ciwonta dama zaka samesu da tsamurarren jiki, to itama hakan ya kasance a gurin Maryama Amma itama Allah ya wadata ta kyau don black beauty ce, itama ga shape kamar Coca cola kuma tana da cika sosai don ita nata yanayin ciwon ba mai rama bane, kamar yadda yake ma wasu ba, ga gashin da Allah ya wadata ta dashi har gadon bayanta, shine suke tattarewa su tarashi tamkar Acuci, ita da Sumayya,
Watane ta shigo class din da sauri itama taci copyn hijab nata har kasa da Nikab, lecturer ne ya dakatar da ita,
     “Heey stop kin Kali agogo kuwa dazaki shigo mun class late,!!?
“Mallam kayi hkr wlh ban samu abun hawa bane shiyasa, kuma muna da nisa,
Gaban Maryama ne ya fadi jin Muryan wanda tayi maganar kamar muryan Rayuwarta gashi har tsawon su da jikin su iri daya, ko barci ta tashi taji muryan nan sai ta gane, ba Nikab Rayuwarta zata sa ba ko me zata sa sai ta ganeta,  to Wacece wannan ita kuwa,?
    “Ok next time in kika kara zuwa mun late bazaki shiga ba,
“Thank You sir, shigowa tayi ta nufi gurin da Maryama take zaune ta zauna kusa da ita, “sannu yar uwa Amma ke Sabon zuwa ne koh,?
      “E,,,,h eh ni sabuwa ce jiya na fara zuwa, Maryama ta fadi haka Muryanta na rawa tsaban rudanin da ta shiga, muryan yarinyar ne ya kara katse mata tunanin da takeyi,
“Ni Sunana Fasihat Nuruddeen kefa mene sunanki?
     Mamaki ne ya kara kamata, tace mata “ni sunana Maryama Nuraddeen Wurno,
“Lah yar uwa Sunan Baban mu daya ashe, daga yau kin zama sister ta, ta mika mata hannu sukayi Musabaha,
      “Hey zaki fitamun a class kin zo late zaki damemu da surutu koh?
       “Sorry sir”
Haka aka cigaba da musu lectures har suka tashi, jerowa sukayi suka fito tare da Fasihat, suna fitowa ta hango me Napep dinta Sallama tayi ma Fasihat ta nufi inda yake, sai Fasihat din ta kwala mata kira “sister na inzo don Allah ku ragemun hanya,?
“Eh ba matsala zo muje mana inji Maryama haka suka shiga, sai ganin mai Napep din tayi ya sauko jiki na rawa ya sunkuyar da kai yana gaidasu, “barkan ku da rana”
“Kai Mallam mai Napep lafiyanka kuwa, da sauri ya mike kuma kamar an tsikareshi, ya shige Cikin Napep din ya tada suka tafi,
*************************
“Wai kai Brother me kake jira da Yarinyar nan bazaka daukan mun matakin bane, tana magana tana maye alamun ta kora syrup,
     “Nifa matsalata dake Baby wannan shaye shaye, Nifa I don’t like it ya karishe maganar yana janyota jikinshi,
    “Kai kuma Brother matsalata da kai Akuyanci, duk kai ka fara koyamun iskan cin nan, kai fa ka yagemun budurcina kasani bin Maza, ni kawai na gaji kana ganin sau Uku muna zubar da Ciki, fa, ni na gaji,
    “Kefa matsalata dake kenan Baby in ba ki rufamun Asiri ba wazai mun da inje in nemi wasu a waje ba gunda in nemi kanwata, in kin hanani kyaje ki ba wasu yan iska a waje, banza karamar yar iska tashi ki ban guri kuma bazan yi miki daukan fansar ba,ya karishe maganar cikin fushi,!!!
     Da sauri ta kamoshi “matsalata da kai Bross saurin fushi, shikenan kawai muje in baka, ko anan falon kake so ko mu shiga Bedroom ne,?
   “No mu shiga ciki Kinsan Mamnah nanan yanzu sai ta takura mana ta ragemana jin dadi,
   “Kai dallah share Mammah nan itama tana can tana rage zafi da Lailah kawata, kasan jarabar Momy ta wannan Lesbian din in batayi ba ji take kamar zata mutu, tana maganar ya dage ta yayi hanyar Bedroom da ita saboda ma gani yake zata bata mai lokaci,
Niko nace wannan wani irin gidane wannan baga Uwar ba, ba ga Uba ba, baga Ya’yan gidan ba,
WA IYAZUBILLAHI
Ace Duniya kawai suka sama gaba, ba ruwansu da lahiran su, sunada mulki sunada dukiya, sai suyi Anfani dashi ta hanyar Bauta mishi hakan ne zai nuna cewa ka godema ni’imar da Allah ya baku, wai irin wadannan Mutanen sune shuwagabannin mu, Ya Allah ka kawo mana agaji, badon halin mu ba,
Da sauri ta shigo gidan ko Addu’an shiga gida bata tsaya yi ba,
“Ummu ina Rabin rai?
Gaba dayan su suka mike a tare sbda suna zaune Suna jimamin abunda suke ji a radio yanzu, gaba daya shigowanta a hargitse ya kara tsorata su,
“Lafiya Rabin rai meke faruwa,?
“Ummu bayan fitana Rayuwata ina taje,?  Ta jefo ma Ummu wannan tanbayan,
 “Ba inda taje muna tare da ita yanzu ma nake cewa bari in aiketa gidan Guggon Hanne ta siyo kayan miya mu samu mu dafa ko danbu ne, wani ajiyar Zuciya ta sauke,
“Wlh Ummu wata na gani irin su Daya da rayuwata, duk da Banga fuskanta ba, fuskanta da Nikab, Amma har yanayin sa Nikab dinsu iri daya,
Murmushi Ummu tayi tace karki damu, Ni Sumayya ta ita kadai na haifa, sai kuma tayi shiru fuskanta ya sauya sosai, zuwa damuwa, ku kadai kuka ragemun a Duniyar nan, rungume ta gaba daya sukayi, suna mai jin kaunar uwan tasu a ran su,
MONTH LATERS
Sosai sabo ya shiga tsakanin Fasihat da Maryama har waya sunayi ga Maryama ta kara gogewa sosai, ga kokari ko wani lecturer da Students sun  sansu a Faculty of Law Ustazai Biyu ake cemusu, kuma har yanzu ba wanda ya taba ganin fuskan su,
Ranar sun fito Lecture kenan kuma sun kama hanya don tafiya, gida suna kokarin fita get, su samu abun Hawa yau Mai Napep nasu bai Zo ba sun kira layinshi bai tafiya, Wata hadaddiyar Motace ta tsaya a gaban su fara tas da ita, dai dai Wayar Fasihat tayi kara da sauri ta dauko wayar a jaka, ganin wanda yake kiranta da sauri ta juya kamar kiftawan ido ta bace a gurin ita kuma Maryama hankalinta ya dauke gurin kallon Motar da tayi parking gabanta, kawai ji tayi anyi ciki da ita sai cikin motar aka rufe mata fuska,✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U   (OUM KHADY)
MABUCIYAR
GIDAN GADO
AND NOW
WAZAN AURA
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page my sweet Bakano Comment dinka na tsumani ina yinka, Sageer Saleh kano
Page 33 TO 34
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
“Ya Subhallah bayin Allah mai namuku ne, wai don Allah kuyi hkr ku fadimaun abunda na muku, lafiyayyun Mari wani a cikin su ya bata tare da cewa “karki kara magana anan badai ke baki da mutunci ba har ki Daga hannu ki Mari yar Govnor bakece Sumayya ba,
Gaban Maryama ne ya fadi jin sun anbaci Sunan yar uwarta, wato Sumayya ce tayi musu laifi, Tabbas ya zama mata dole ta Amshi laifin nan don Ceto yar uwarta Daga wadan nan azzaluman, zata iya bada rayuwarta akan Sumayya,
“Ke malama ba magana muke miki ba,?
“Eh nice don Allah kuyi hkr kuskure aka samu bazan kara ba, ta karishe maganar tana fashewa da kuka gunin ban tausayi,
     Dai dai sun kariso guest house din Aslm horn suka danna mai karfi mai gadi da gudu yazo ya bude musu haka suka budeshi da kura, girgiza kai yayi inda sabo ya saba da halin su Aslm, yau kuma wata mai tsautsayin suka dauko, bai gama tunani ba yaga sun fito da wata yarinyar fuskanta sanye da Nikab, suna janta a wulakance, tana Ihu, har suka shige da Ita tsohon nan ya Daga Hannu, yana hawaye “Ya Allah kayi ma Yaran da kuke lalatawa sakayyah, ya koma gurin Zaman shi ya zauna, yana dada jiyo ihunta,
Suna shiga suka yarda ita a falon Aslm tasowa yayi ya fara kwance belt ko takan cire mata hijab bai yi ba shidai kawai burin shi ya keta haddinta, Yaran su kwantar mai da ita suka daddan neta ko takan cire Nikab din nata basuyi ba, dukan su sai da sukayi Raping dinta, tun tana sani inda kanta yake har ta fita a hayyacinta, ta sume sannan suka kyaleta, haka suka daukota a Mota suka kawota har gidan su a haukace suka shigo layin kida na tashi a Motar su inda ya jawo hankalin duka yan Unguwar, daidai Kofar gidan su suka tsaya da Motar daukota sukayi tamkar da Matacciya suka shiga gidan ko Sallama babu suka wurgar da ita a tsakar gida dai dai Ummu ta fito Daga toilet, da sauri ta Nufo gurin Sabda ko cikin dubu taga yaranta sai ta ganesu balle ga hijab din datasa ta fita Yau,
      “Ku suwaye mai kuka ma ya’ta eyehh!!! Ta karishe maganar cikin fushi, tana jijjiga Maryama, KB ne ya kalleta shekeke “hukunci ta karba kin gane koh wurga mata rafan kudi sukayi Gashinan ta gasa jiki, dai dai lokacin da Sumayya ta shigo gidan saboda Ummu dama ta aiketa ne, duk kuma taji maganar da KB yake yi batasan lokacin datayo kukan kura ta chakumo wuyanshi ba, ta hadashi da bango “me kukayi ma yar uwata, don cin mutunci shine zaku shigo har cikin gidan mu,
      “Heyyy!!  heyyy!! Dakata yar Matsiyata  cewar Aslm bai gama rufe baki ba ta dauke da Mari taje ta dauko  bokitin ruwan da ke ajiye zata wanka ta juye mishi a jiki hadi da hankadashi “ku bar mana gidan mu kuma wlh sai Allah ya bimana hakkin mu, an gaya muku, kudi hauka ne, wlh duka sai na dau fansa a kanku,!!! Ta karishe maganar tana huci inda Ummu gaba daya ta rasa nayi tunda ta juya Maryama ta gane fyade sukayi mata, sbda jinin da yake zuba a jikinta  har yanzu,
  A zuciye Sumayya ta dauki kudin da KB ya jefama Ummu ta jefeshi dashi, hadi da kada dan yatsanta biyu,
       “Kai kuma Daga kai har Bunsurayen Abokanan ka, ina mai tabbatar muku da sai na dauki ma yar uwata Fansa a kanku duka ku biyar dinan ku jiraye Fansar Sumayya, duk da haka zan kaiku gurin Hukuma don gudun daukan mataki da Kai duk da nasan mu talakawa ne bamu da arzikin da zamu iya shari’a daku, ta karishe ta watsa musu harara,
       KB ne ya Zaburo zai dauke Sumayya da Mari Aslm ya rike Hannun shi, “gay kyaleta tabbas karfin halin Yarinyar ya birgeni, kuma ina da tabbacin ita ta Mari Baby ba wannan innocent Baby dake kwance ba, ku kyaleta ni na san mai zan mata,
         “Kamar yadda nima nasan me zan maka ba, ta fadi gami da kara hakadasu ta maida Kofar gidan su ta rufe kirjinta na bugawa tsaban tashin hankalin da take ciki,
     Suna fita duk sun jike kasancewar Ruwan data watsa musu, bude Motar su sukayi suka figeta dai dai Mudi ya shawo kwanar layin kadan ya rage suyi sama dashi ya kauce da gudu yabi motan da kallo, yaci gaba da tafiyanshi,
     “Ummu sun kasheta ko Rabin raina in kika Mutu nima binki zanyi,
“Kiyi shiru diyar albrka bata Mutu ba, kamata mu shiga Toilet na hada mata ruwan zafi, haka suka shiga da ita Toilet Ummu ta cika katon bahon su da ruwa, suna shiga da ita suka sata a cikin ruwan kara ta saki tare da bude idonta da yayi mata wani nauyi “Ummu zasu kasheni, ta fadi haka tana kara runtse ido, saboda Azaban da takeji na ruwan zafin nan, nan da nan ruwan ya rine da jini, Ummu kuka Sumayya kuka, haka Ummu ta gama gasata suka fito ta samata kaya, Ummu ta bata abinci da kyar ta iya cin loma biyu ta kawar da kai, samata Hijab tayi Ummu ta daukota suka fito, Sumayya taje ta taro musu abun Hawa, Mai Napep na zuwa suka shiga suka fadi mai Asibiti zai kaisu, yaja suka tafi,
    Suna isa Ummu reception ta nufa ta basu hand card dinta tun dama tana dashi, aka ciro file din suka je ganin likita, Sumayya tana Addu’an Allah yasa ba wannan mare mutuncin Doctor din nan zasu gani ba, hope dinta suga mai kama da Mujaheed dinta,,
Suna shiga suka ga wata Doctor ce Mace gata black beauty, Matashiya ce, fuskanta da kamala,  sosai Doctor Raleeyat Ya’u sukaga an rubuta jikin dan wani abu da yake makale jikin lab coat nata,
Ajiyar zuciya sukayi A tare duka su biyu, har sai da yasa hankalin likitan ya dawo garesu, Murmushi ta musu hadi da nuna musu gurin Zama,
      “Sannunku koh, waye Mare lpy a cikin Ummu ta Nuna Maryama datake rike a jikinta tana sharban kuka, Meyake damunta,?
    Kasa magana dukansu sukayi sbda kukan da sukeyi, har Doctor din ta tausaya musu matuka, da kyar Sumayya tayi karfin halin cewa fyade akama yar uwata,
Da sauri Doctor ta dago kanta, hadi da cire glass din fuskanta
“Suko wasu marasa Imanin ne suka mata basu tausaya ma situation din datake ciki ba a matsayinta na Sickle cell, tashi muje ki hau gado in dubaki, lallai ma kina da karfin hali, Ummu ne suka kamata suka dorata akan gado, tasowa Doctor din tayi,
   “Ya Subhallah Amma ba mutum daya yayi miki fyaden nan ba, gskya kina da bala’in karfin hali da dauriya,  yanzu sai anyi miki dinki, sannan bazan kwantar daku ba zaku koma gida, sannan zan rubuta muku Magani,
Godiya suka mata, sosai sbda tayi musu mutunci sosai,
*************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
dai dai sunga isowar Motan ta, suka tashi suka ruko Shatu Kwata Kwata bata san inda kanta yake ba, sai jinin dake zuba ta kasanta, da sauri Doctor Nusaibat Habibullah Fulani ta fito Daga motar ta ta iso gareta, “bayin Allah  lpy me ya sameta, Duk da Shatu tana cikin Halin ciwo bazata manta da wannan muryan ba, Da sauri ta dago kanta bakinta na rawa gurin furta “HAJJO!!!
Cikin tashin hankali Doctor Nusaibat take kallonta, tana Nunata da yatsa, “Sha,,,tuuu!!
Kece haka???? ✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Like
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu9333
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U   (OUM KHADY)
 PAGE 35 TO 36
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din nakane Masoyin Asali true love Never end, Allah ya barmun kai ya tsareka ya kareka  a duk inda kake, fatan Alheri (Mubzeey)
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
“Dama kina raye baki mutu ba, da sauri ta kira Nurses suka zo da emergency bed aka dorata akai, nan da nan ta shiga motar ta ta bisu,
Ana shiga da ita Dakin Doctor Nusaibat tana karisowa, dama already Dama an gama hada mata komai da zata bukata tana Zuwa, ta fara dubata ta tabbatar miscarriage tayi kuma tana bukatan jini, nan da nan tayi waya aka kawo mata blood Daga lab tayi mata allurai tayi mata Setting na Blood, fitowa tayi tana tanbayar ina wanda suka kawota aka cemata ba’a gansu ba, komawa Office din tayi ta zauna ta kurama Shatu ido duk ta Rame ta yi baki kamar ba Shatun Baffa ba Fara kaman a taba jini ya fito, gata yar duma duma Amma yanzu ta zama tamkar skeleton,
     Allah ya tashi kafadunki Shatu ta fadi haka, hadi da kallan wayanta da ake kira, dauka tayi hadi da karawa a kunne
       “Hello Yes I am NUSAIBAT HABIBULLAH FULANI, oh sorry  wlh na manta da wanna Meeting din but zanyi kokari inyi Sending my P.A na ta wakilceni dama already yau zata sauka a Abuja Daga Dubai, jirgin karfe biyu, zata sauka,sai kuje ku tareta a Airport, ok  tom bye,
*************************
After three weaks later
Su Sumayya suka koma Asibiti domin kara ganin Likita, bayan sun gama komai da ya kamata suka isa ga Doctor, Suna shiga ta tarbesu da fara anta “well Come my patient yau da kanta ta hau gadon ta kwanta, Doctor ta fara dubata, dago kai tayi cikin tashin hankali “ya Allah Maryama what happen, kamar Yoyon fitsari naga kinayi hawaye ne ya zubo ma Maryama, “tace Aunty tun randa muka koma gida bayan na zauna na tashi sai naga na jike gashi Kwata Kwata ban rike fitsari, hankalin mu gaba daya ya tashi,
     “Ya Subhallah Innalillahi wa innah ilaihirraji’un, tabbas kin kamu da Yoyon fitsari, kuma sai an miki aiki akalla zai iya kai Dubu dari da Hamsin indai anan za’a miki, cikin tashin hankali gaba daya suke kallonta inda Sumayya ta duke a gurin tana ta kukan da ba sauti,
      “Amma taimakon da zan muku dayane shine akwai wata Kawata, Doctor Nusaibat Habibullah Fulani da take zuwa A.B.U teaching hospital Zaria, tana yin wannan aikin kyauta fisabilillahi ga irinku marasu karfi, zan rubuta muku takarda ku tafi Zaria Kuna zuwa ku nemeta ku bata takardan nan kucemata Doctor Raleeyat ta turoku, don dai ni yau zan bar kasan ne, akwai wani Business da Mijina zai fita yi a  kasar Ingila, da tare zamu tafi daku Allah ya bata lpy, but Matukar ta ga Doctor to Insha Allah zata mata aiki kuma Za’a samu nasara tunda ita kwararriyar likitan Matane, karku damu kunji, komai yayi tsanani maganin shi Allah,
     “Mun gode Doctor Allah ubangiji ya saka da alheri ya daukaka ki, in Ana samun irinku masu tausayi a cikin Al’uma da bamu shiga halin da muke ciki a kasar mu ba, mun gde sosai.
Bayan ta rubuta musu takardan da zasu tafi dashi Zaria ne suka mata salama suka juya zasu tafi, sai Sumayya ta juyo da sauri tace “Aunty don Allah kibamu Number ki,
   “Ok ta rubuta mata a paper ta bata, sukayi mata sallama suka tafi,
***********************
BIRNIN MISRA
“Jaddi meyasa zaka hana Zuwa garesu Alhalin yanzu ne suke bukatar taimako?  Ya karishe maganar yana bata rai,
     “Ya kai Sadaukin Jarumi kasani shi Bawa bai taba tsallake kaddaranshi to kaddaransu ne haka kuma Ubangiji bai bamu daman taimakon su, shiyasa Kaga na hanaka in har Bawa kuma yace zaiyi shishshigi cikin lamarin Ubangiji sai Allah ya karbi Rayuwarka, kawai kayi hkr mu ga ikon Allah, Fasihat ne ta shigo a hargitse ko lura da Mujaheed batayi ba,
     “Jaddi ka fadamun ni Wacece, wai Dama ni ba yar gidan nan bane,?
“Yar Albrka waya taboki, duk wanda ya fadamiki haka karya ya fadamiki don ke din nan kinfi kowa iko a gidan nan kuma kina da Babban al’amari a tare da rayuwarki, wanda zan bayyana miki nan bada dadewa ba,
Mujaheed ne yazo ya dagota, hadi da share mata hawaye, “karki damu Seeehat komai yayi farko zai zo karshe Kinji, mubi komai a hankali, har lokacin da Jaddi zai warware mana al’amarin nan,
“Yauwa Jaddi Maryamah kawata tana bukatar taimako,
“Na sani Amna bamu da halin taimakonta,
   “Meyasa ya Jaddi zakace haka,?
“Bana san yawan tanbaya zan shiga Daga ciki,
“To a fito lpy, tashi sukayi suka tafi Mujaheed na mata bayanin yanda sukayi da Jaddi, dai dai Zankadaziyyatu ta iso tana huci ta bangaji Fasihat kasan cewar tafi Fasihat karfi da komai yasa tayi baya zata fadi Mujaheed ya riketa, tuni ta bace kaman walkiya, karkada kai kawai Mujaheed yayi, suma suka bace,
***********************
KAUYEN WURNO
“Kunajina koh yau ina son mukai hari zuwa kauyen dake makotaka damu, domin ina bukatar Karin garuruwa, a cikin garuruwan da muka kwace, angama ya shugaba,
***********************
BIRNIN KANO
GIDAN GOVNOR
“My Excellency game da maganar fitan Aslm UK ne zuwa shakatawa yace yana so su tafi Shida Abokanan shine, to Kaga dole za’a hada musu Visa su dukan su, sai kudin kashewan da zasu bukata,
    “Eh munyi magana da Mai kula da shige da fice na kasa da kasa cewan ya gama hada musu Visa, kudi kuma yanzu zanyi mai transfer na Ten millions I hope zai isheshi,?
“Eh ya ishesu my Excellency nima dama ina bukatar kudi zan danyi wasu hidiman dasu,
“Hajjaju me zakiyi da kudi ina ce kwanan nan aka muku Salary naku na matan gobnoni, kuma kin san Zamu fita Campaign kwananan tunda kin san Zabe ya matso koh, shi kuma talakar kasar mu tamkar kaji ne da an watsa musu tsaba shikenan sun mance zaluncin da ka musu a baya kinga dole kuwa, mu saki kudi duk da Zanjabiluuu ya bani tabbacin kakkau ya ce mune da nasara Amma in kana da kyau ka kara da wanka,
   “Hakane My Excellency nima ina son inje maka gurin Boka dan tsito ne kasan shima sha yanzu magani yanxu ne,
   “Pappah!! Pappah tana tafe tana tangadi ta kariso inda suke kamar zata fado ma iyayen nata akai, Nima ina bukatar kudine zanyi Birthday, ta karishe maganar tana zama a kusa da Uban nata,
    “Wai Ikram yaushe zaki bar shaye shayen nan ne iyeeh nace miki bana so fa, nawa kike bukata?
“Ai My Excellency bazata daina ba ya zama jinin jikinta,
    “Dallah Malama ba ruwanki na kulaki da na shigo ba gara ni Shaye Shaye nakeyi ba, ke da Pappah wayasan me kuke aikatawa,
“Kinga Baby rabu da Mammah nan naku nawa kike bukata,?
“Million Ashirin zaka bani kacal,
“To baki da matsala zan tura miki Kinji yan matana, tashi tayi tana tafe tana tangadi, har ta shige bedroom din dake falon ta haye gado ko cire takalmi batayi ba, sai barci,
Aslm ne ya shigo ya Tara uban gashi a kanshi ga wani sarka da yasa da dan kunne a kunin shi ga ear phone daya makala a kunnen shi, ga gashin ya mai tiri ga wani aski da akayi ba ko tsari,
    “Hi Pappah Hi Mammah I hope an gama mun abunda na fada miki Mammah, don ni ban so in kai two a Nijaa,
“Gaye dan gata ba dole ba ai an kammala komai yanzu tafiya ya rage aje a huta kayi komai ba komai gay son in kana da kudi ka wuce wulakancin Duniya, kai harma dana lahira,
Niko nace wa’iyazibillah Aiko Mammah kin tabe, ai lahira ba Duniya bace,
Ranar da Ubangiji ne kadai mai mulki mai iko,
Kamar yadda ubangiji yake fada a ranar alkiyama
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
LIMANIL MULKUL YAUM
sai dukkan halittu suyi shiru ba mai amsawa sai Ubangiji ya Ansa da kanshi yace
LILLAHI WAHIDUL KAHHAR,
to ita dai Mammah ta manta da wannan Nafsin kam
Allah kasa mu gama da Duniya lafiya ya rufamana Asiri Duniya da lahira🙏masu hali irin na Mammah Allah ya shiryesu,✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U   (OUM KHADY)
 PAGE 37 TO 38
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din nakine karamar uwa Abokiyar wasa Baba Zulai ina yinki sosai Allah ya barku tare😍😍💖💖
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Isan su Airport kenan Shida Abokanan shi, suka samu gurin Zama don jiran lokacin da flight nasu zai tashi,
Karfe biyu dai dai aka fara announcement na passenger su matso kusa, Aslam ya fara mikewa,  yace ma su KB su taso su tafi in ka kallesu bazakace Yaran musulmai bane, sbda yanayin shigan da sukayi,
Sun isa su ko tantancesu ba’ayi ba suka shige jirgi, dai dai zasu shiga jirgin Sumayya ya hango tana mai wani irin mugun kallo na tsana, murza idon shi yayi, yaga tabbas fa itace to meya kawota Airport, daurewa yayi ya shige jirgi, yana sake sake a ranshi shidai a sanin shi yasan ba abunda zai kawota airport,
Tunanin shi da ganinshi da hankalin shi ne sukayi mai tafiyan wucin gadi sakamakon Sumayya da ya gani a cikin jirgi zaune kusa da sit dinshi, karfin hali yayi ya karisa kusa da ita ya Zauna, duk jikin shi yayi sanyi, Abokanan shi nata magana shidai kawai yayi shiru, yana kallon Sumayya da ko kalan shi batayi ba, tana ta Karatun Azkar dinta a cikin hisrul Muslim, tasha dogon hijab dinta Popul,
Gaba daya ji yake soyayya yarinyar da kyawunta yana ratsa jijiyoyin jikinshi, burin shi kawai baifi ya mallaketa ba, Dis is d first time da Aslam ya fara tunanin Aure a rayuwar shi, gashi yaji yana bala’in shakkar Yarinyar, da tsoronta ga kuma wutar sonta a ranshi, gashi ya zaluncesu yasa bazata taba sonshi ba,
Waigowa yayi suka hada ido da ita, wani matsiyacin kallo ta mai, wanda sai da gabanshi ya fadi, sai yaga ta kara wani masifaffen kyau,
Niko nace aiki ya ganka Aslam muje zuwa dai,
Haka jirginsu ya tashi ya Lula cikin sararin Samaniya sai UK yayi da Aslam gaba daya hankalin shi ya tafi ga Sumayya inda ita kuma ta dukufa gurin Karatun Hisrul Muslim dinta sai ince readers sai mun hadu a UK don dauko muku me zai faru a can,  inda sister Oum khady zata cigaba da koro muku bayanin yan Nigeria, nidai nayi UK don dauko muku shaw, Daga nan inga gari😂
*************************
Ummu ne ta fito da shirinta ita da Maryama duk tabi ta rame,
     “Wai me kikeyine diyar Albrka kiyi ki fito mu tafi Kinsan ina so mu isa Zaria nan da wuri ne inda zamu samu muga likitan nan da wuri,
    “Ummun mu ganinan zuwa yanzun nan ina duba takardan data bamu ne wanda zamu dashi ta fadi haka tana fitowa tare da Daura Nikab din dake hannunta,
Jerowa sukayi suka fita hade da kulle kofan gidan, suka gangara da kafansu kasancewar Asubace ba’a dade da idar da sallah ba gari ko gama wayewa baiyi ba, shiyasa sai da suka gangara bakin titin layinsu da kyar suka samu Taxi din dazai kai su inda zasu hau Mota,
 Suna isa tasha suka tarar da motan dama sauran Mutum uku ne a Tashi, suna zuwa suka dauki hanyar Zazzau birnin Shehu,
***********************
ZARIA GARIN ILIMI🙈🙈
“sannu Shatu, I hope yanzu ba’abun da ke miki ciwo, yanxu tsawon wata uku kenan kina jinya, sannan Mahaifarki ta samu Matsala bazaki kara haihuwa ba,
“Shatu har yau kinki bani labarin abunda ya faru dake, in na tanbayeki sai ki kama mun kuka don Allah ki fadamun,
Share hawaye Shatu tayi ta dago rinannun idanuwanta ta zubasu a kan Doctor Nusaibat,
     “Hajjo rayuwata ta shiga cikin kunci da garari bayan rabuwar mu dake, yan kidnapping din nan basu kasheni ba kamar yadda mukayi tunani ni dake, sai suka daukeni Daga wannan dajin zuwa dajin Birnin gwari suka mai dani tankar baiwa girki da duk wani abun da suke bukata ni zan musu, sannan na zama abun korewar sha’awar su a rana sai suyi Anfani dani fin sau goma tun ina suma har nazo na daina, kuma duk kansu wanda yaji sha’awarshi a kaina yake saukewa, sun min ciki yafi a kirga yana zubewa, ta karishe maganar cikin kuka, da takaici yayin da Doctor Nusaibat itama take kuka, bayan wasu shekaru da Jami’an tsaro suka taso yan uwansu wanda suke Zamfara da Sokoto sai sukayi gangami suka tafi Sokoto don su taya yan uwansu yaki da Jami’an tsaro, haka suka tasani muka tafi randa muka isa Sokoto komai ya dawo mun, don bazan taba mancewa da garin Wurno ba, inda aka kashe mun dukkan ahali Daga ni sai Baffah na muka tsira Daga baya suma suka kashemun Baffa, bayan tsawon watanni da sukayi Ana fafatawa tsakanin su har suka samu galaba akan Jami’an tsaro kasancewar duk wani shiri da Jami’an tsaro zasuyi suna da Wanda ke fadamusu, sbda suna daurin gindi a gurin wasu manyan yan siyasa da Jami’an tsaro da sarakunan gargajiya, duk da suma anyi musu barna sosai don ankashe su da yawa, ciki harda ogan mu, Daga nan na cigaba da Bauta har ranar da Allah ya kawo ni nan don nidai bazan cemiki ga wanda suka kawoni ba, don ban san halin da nake ciki ba.
Kuka sosai Doctor takeyi,
“A kullum ranar Duniya sai na Samu case din fyade wa Mata da kananan yara, da Case din bata yara Maza, da case din rashin tsaro, kai Duniya ina zaki damu  gashi mun kasa kawo sauyi a kasar mu komai Kara tabarbarewa yakeyi, ko kayi yunkurin daukan mataki Daga sama za’a kiraka a dakatar da kai, Allah ka dubemu da idon Rahma ka kawo mana wanda zasu kawo chanji a kasar mu, Ameen ya Allah,
      “Yanzu na riga nama Driver na magana zai kaiki gidan mu dake cikin City, ki zauna gurin Kakata Hajiya yayah, sbda ni yanzu ina son zanje Kaduna ne Daga can zan wuce gida sbda Na kwana biyu a nan sbada jinyarki Insha Allah Next time in na dawo sai muyi mgna a tsanake, Kinji ki saki jikin ki tamkar kina gida Kinji, wayar ta ne tayi kara ta Daga “haba Cherry Kaima kasan I miss u too much ina yan biyu na da Aunty su a shafamun kansu, kai ni ba ruwana ai da Hamman sun nan baifa kirani ba don nayi mai fada nace yazo ya duba Mamansu bata da lpy, shine yaki zuwa yaki kuma kirana zan dawo ai sai naci gidan su kam,
To naji na hkr amma yayi abunda na sashi, ok by I love you too my Cherry, ✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA’U   (OUM KHADY)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
PAGE 39 TO 40
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
UNITED STATE OF KINGDOMS
Sun sauka a kasar UK kimanin karfe Hudu na yamma direct gidan Pappah dake cikin kasar suka wuce yayin da ya dunga raba ido yaga ta ina zata bullo gaba daya ya nemeta ya rasa, har suka wuce gida,
Suna isa suka tarar da duk wani kayan maye da suke bukata an tana darmusu ga yan matan turawa nan kala kala, suna isa ba maganar Sallah suka hau Shaye Shayen su, suka kure kida a gidan inda kasan gidan Club yan matan nan sai rawa sukeyi abunsu, gaba daya sun bige, nan da nan kowa ya ja nashi budurwan suka fara badala.
*************************
NIGERIA  WURNO
“Ke wai meke damunki ne kwana biyu duk kin canza in mun bukaceki sai mu nemeki mu rasa?
    “Kayi hkr Oga banda lpy ne,
“Shine baki magana ba kina ganin Doctor jiya yazo ya dubamun yarana wanda sukayi rauni, mtswww tsaki yayi ya kara gaba, lallabawa tayi kasancewar darene ta fito Daga dan bukkan da take hura musu wani abu tayi wanda suke gadin gurin sunata kaiwa da dawowa, ga haske a gurin kaman rana tana huramusu suka bingire da barci, da sauri ta karishe cikin wani bukka, ta shiga wani mutum ne a kwance shiba matacce ba shi ba rayayye ba,
   Wani ruwa ta fito dashi a wani kwarya, ta fara tofa Addu’a a ciki Bayan ta gama ne tayi bissmillah ta fara yayyafa mishi, tana wasu Addu’oi can ya fara motsi a hankali a hankali ya gama bude idon shi, da sauri ya tashi yana salati, ya fara waige waige,
       “Zankadaziyyatu me ya faru me mukeyi anan?  Ya jero mata tanbayoyi,
    “Alhmdulillah da ka farfado lpy lallai kaidin dan baiwa ne ba kowa za’a soka ma wannan takobin ba yayi wannan tsawon shekarun yana kwance kuma, ya farfado hankalin shi bai gushe ba, Abunda nakeso da kai ka cigaba da zama haka, don Matukar suka san ka farfado duk wani aiki namu zai dawo baya, burin su zai cika mu kuma namu bazai cika ba,
        “Hakane tabbas kin kawo shawara mai kyau haka za’ayi,
“Ni kuma zan dauki duk wani dawainiyar kawo ma Abinci ko sau dayane a rana, gudun karsu gano mu, ficewa tayi da sauri ta koma makwancinta,
***********************
ZAZZAU BIRNIN ILIMI
Sun isa zaria karfe takwas na safe inda suka isa cikin Asibitin koyarwa na Ahmadu bello teaching hospital karfe Tara da minto ci, bayan Isan su Asibitin ne suka tarar da Security gurin suka mikamai takardan da Doctor Raleeyat ta basu, bayan ya gama duba takardan ne ya dago yana kallansu a wulakance yace musu
“Irinku ne yan san banza bazaku nemi kudi ai muku aiki ba sai dai ku tsaya jiran na bati, to Hajiya ta koma Yola yau ita da dawowa ma sai nanda wata uku in tsaku biya kudi ku biya don ni Banga alamun rashin kudi a tare daku ba, in kuma zaku tsaya san banza to, bai kai ya rufe baki ba Sumayya ta fisge takardan tana huci,
    “Har kai ka isa ka ajiyemu ka dunga fadamana magana wlh munfi karfin banza kawai wanda basu san darajan dan Adam ba, ba dole Ubangiji ma ya hadamu da shuwagabanni dai dai da mu ba, ace hatta talaka bazai Tausaya ma dan uwanshi talaka ba, ko yaya ya samu dama sai izgili, Kaima Allah ba yafi sanka bane akan mu Yasa ya baka wannan matsayin ka gane koh,!! Ta karishe maganar cikin fushi hadi da cema su Ummu kuzo mu tafi,
Juyawa sukayi jiki a sanyaye suka fito Daga Asibiti kowa ranshi ba dadi,
      “Yanzu Ummu ya zamuyi?
“Tom hakanan zamu koma gida haka Allah ya kaddaro, har nan da wata ukun sai mu dawo,
“Haba Ummun mu yanzu haka zamu zurama rabin rai ido tana fama da wannan laluran har nan da wata uku, gskya bazan iya ba,
Haka suka dunga tattaunawa tsakaninsu har suka fita titi suka hau taxi zuwa hawa motar komawa Kano,
*************************
KANO TUNBIN GIWA
“Mai girma Zanjabiluuu zabe nata karatowa muna fatan mai girma kakkau yasani,?
    “Kakkau ya riga ya tabbatar maka da cewa kai keda nasara Karka damu,
“Ngd mai girma Zanjabiluuu babu wani mai girma sai kai, kai ne mai yin yadda kaso,
Wa’iyazibillah niko nace Allah ne kadai mai girma kuma maiyin yadda yaso,
Bayan ya gama surkulenshi ya gama bokan ya bace, ya cire jajayen kayan jikinshi ya maida ainihin kayan shi, ya fito ya maida Kofar ya rufe,
“Excellency akwai fa matsala fa sbda talakawa sun fara bore game da rashin cika musu Alkawari da ba’ayi ba gashi har tenure namu ya kusa karewa,
“Hhhh kar ka damu Wakili muke da Nasara kai dai kawai ka zuba ido ka gani, ina son yanzu a bugo foam kaman Miliyan daya ace ma talakawa za’a basu tallafin Dubu dari dari kowa zai samu, bayan an raba foam din kar ya wuce mutane dari biyu zasu Amfana da tallafin kudin a tabbatar ko wace Local government dake cikin birnin kano An samu kamar mutum biyar biyar ko goma dasuka samu tallafin Kaga da munyi haka mun gama dasu kamar sun zabemu sun gama,
Ya Allah kira ga yan uwana mata da Maza haka fa shuwagabannin mu suka daukemu tankar kaji, duk wani wahalan dasuka sha Daga an watsa musu dawa sai su fara wawa su mance da su wayesu, ku zabi shugaba na gari kar kudi ya rudeku ku manta suwaye ku, ko don inganta rayuwar Yaran mu dazasu taso a gaba, sannan Muma mu gyara halayen mu, sbda duk wani hali da muke ciki mu muke jawo ma kan mu, mun saki Ubangiji mun kama rayuwar Duniya mun mance da cewa zamu mutu, Zinace Zinace yayi yawa Madigo, lud, zubar da jini kuma wai duk saboda Duniya mukeyi, duk wani zunubi da Mutanen da suka gabacemu sukeyi Ubangiji ya halakar dasu, to mu duka mun hada taya Allah bazai jarabcemu da masifu da bala’i kala kala ba,
Ubangiji yana cewa Daga lokacin da bayina su kauce hanya na gari suka fada hanyar bata ni kuma sai in jarabcesu da shuwagabanni wanda zasu dunga Azabtar dasu dai dai da abunda suke aikatawa, Koda sun zabi shugaba na gari ne, sai mu karkatar dashi ya koma Azzalumi wannan shine sakamakon mutane batattu,
Kamar misalin kasar mune da shugaban da muka zaba, mun kyautata mai zato munyi tunanin zai tsamo mu a cikin kangin talauci da wahala, sai muka ga akasin haka, kar muga laifin shi laifin mune da mu bijire ma Ubangijin mu, sai Allah ya barmu da halin mu,
Ya Ubangiji ya shiryamu yasa mu gyara halayen mu, Abunda na fada dai dai, da Wanda nayi kuskure Allah ya yafemun, duk wanda kuma maganata bai mai dadi ba yayi hkr,
********************
sun iso kano dukkan su shiru ba wani magana a tsakanin su, bayan sun bude gidan ne sun shige Maryama ta wuce daki tana shiga ta fada kan katifa ta fashe da kuka “ya Allah Kaga halin da nake ciki ka fitar dani ka yayemana  damuwar mu, da sauri Sumayya tazo ta rungumeta “kiyi hkr Rabin raina duk laifinane ni na jefaki cikin wannan halin da sauri ta share hawayenta ta rungume yar uwan nata, “haba rayuwata kidaina fadin haka wannan shine kaddarata dama kuma bawa bai tsallake kaddaranshi haka Allah yaso, wash Inna lillahi wa innah ilaihirraji’un Rayuwata kafata wayo Hannuna ki danna mun hannuna ki matsamun ya Allah😭😭Rayuwata ciwona ne ya tashi ina ji a jikina mutuwa zanyi,
*************************
“Insha Allah Ammy ina sa ran nakusa kammala aikina da najeyi a kano, kafin in dawo in koma Depot namu sannan bazan dawo ba sai da Soyayyar Sumayyat,
“Allah ya baka sa’a Namiji ka zama mai gskya a duk inda kake kar ka tsartar ma da mutum hunkuci sai ka tabbatar da laifinsa, nasan yarona mai sa’a ne akan Duk wani bincike da yasa ma gaba, easy Sir ta karishe fadin haka tana dariya, Hairan ne ta kariso gurin Agent Akheey CBI fatan Alheri, peck kiss ya bama Ammy sannan ya ma Hairan ita ma yace musu Bissalam yana musu bye bye, “Halwa akhey don’t forget d prayers any time, “thank You Jamelatu Ukhtee,
Tofa shin za’a ma Maryama aikin kuwa?
Shin waye wannan mutumin da ya farfado a garin Wurno har suke magana da Zankadaziyyatu?
Shin ya Soyayyan dan gidan Govnor da Aljana Sumayya zai kasance?
Shin dama Saif jami’in bincike ne,kuma binciken mai yaje yi kano?
Wai ya Soyayyar Saif da Ikram da kuma Aljana Sumayya?
Shin menene sirrin da Jaddi yake boyewa yace zai warware mana?
Shin Sumayya zata dau fansa kuwa,?
Garzaya ka nemi WAZAN AURA kashi na biyu don jin karshen wannan riki rikitan labari mai cike da tausayi da soyayya da shugabanci na zalunci da daukar fansa tsakanin mutum da Aljan duk a cikin Novel din WAZAN AURA KASHI NA BIYU.
Aslamu Alaikum
Ina masoya ina sonku sosai a duk inda kuke yau na kawo karshen Novel dina mai suna WAZAN AURA part one
Ina fatan zaku nunamun soyayyanku da kaunar ku gurin siyan Novel dina part two akan kudi kalilan ba mai yawa ba 150  hakan ne zai sa in gane soyayyarku a gareni kuyi hkr ba wai banjin dadin comment dinku da like naku bane da Soyayyar da kuke nunamun bane wlh ina jin dadin hakan sosai dole ce tasa haka sbda yanayin garine ne Some time ma mutum zai tashi ko Data bai dashi, Hankalina bai kwanciya har sai na samu na muku posting, ina yinku da fatan zaku nuna mun kauna ga duk masu bukatan Novel dina part two zaku iya   Tura kudin ku ta wannan Number  MTN
08037420816
Ko ta wannan Account number
6019964818
Zainab salihu Yarima
Kar ku manta in kun tura zakuyi screen shot sai ku Tura ta wannan Number Insha Allah zan saku a cikin group dina na WhatsApp, ngd Daga taku
Yar mutan zazzau ina sonku
Share
Vote
Comment

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements