WAZAN AURA Page 31 to 40 » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / WAZAN AURA Page 31 to 40

WAZAN AURA Page 31 to 40

WAZAN AURA Page 31 to 40

“ya Allah Rayuwata ni inaji a jikina tabbas bazanyi tsawon rai ba kuma, ke din akwai wasu boyayyun Al’Amari a tare da ke, ga Amanar Ummu nan duk da dama na san ke jajirtacciya ce kiyi kokari ki cikamun burina na Zama Barrister mai gaskya wanda zaki kwato ma duk wata yarinya wanda aka mata fyade hakkinta, Nasan kanwata Jaruma ce, Ashh ya Allah ciwon kafan nata ne ya kara motsawa sai ga hawaye tanayi tana cigaba da rike kafar nata can hannunta ya dauka shima, “Ummu na Mutuwa zanyi ku yafemun duk abunda nayi muku,

“A’a diyar Albrka bazaki mutu ba cuta ba mutuwa bace,
      “Tabbas hakane Ummu Amma ni inaji a jikina Mutuwa zanyi, Kuma mutuwata a gareku shine zai zama haske a gareku sbda lalurana ba mai warkewa bane, sai dai nai ta wahalar daku, gashi Allah bai wadatamu da hali ba, ko masu hali ma suna gudun irin laluran mu, balle mu da bamu dashi, please Rayuwata ko bayan ba raina ki dage ki yi karatu don inganta rayuwarki dana Ummu, karkice zaki danganta rayuwarki da daukan fansa ni na yafe musu har Abada, kara tayi tana karan to Addu’oi da ke bakinta,
     “Kiyi hkr Rabin rai Amma bazan taba iya kyalesu ba batare da na dau fansa ba, kuma na miki alkawarin duka sai na cika miki burinki, rungume su duka Ummu tayi tana kuka taba kafar nata tayi taji ya dau zafi sosai Ruwa taje ta dauke shiba mai dumi ba shi ba mai Zafi ba ta fara mammatsa mata kafanta da hanunta yayin da ita kuma Sumayya take tofa mata Addu’a, har barci ya kwasheta,
************************
ABUJA NIGERIA
GIDAN PRESIDENT
“Excuse me”
“Yes Baby whatsap akwai labari ne,?
“Kedai bari Jiddah kin san Meye?
“Sai kin fada”
     “In gaya miki yau akwai wani show daza’ayi a Maitama Hotel, dan Minister Ilimi ya hada murna zagayowar haihuwanshi, yanzu burina ta yanda zamu Samu muje Kinsan indai Yaya Irfan na kasar nan bazamu jeshi ba sbda duk Dad ya daure mai gindi ya dunga takurawa rayuwar mu,
    “Dallah kyaleshi Mami ai tana nan kawai muje mu kama kafa da ita har muje mu dawo ba wanda ya sani, kinsan ma wani abu kuwa,?
   “Sai kin fada”
“Wannan shegiyar yar Govnor Kanon zatazo shiyasa nake so muje mu goge raini Kinsan wai Yaya Saif takeso,
   “Kutumar Uba Jiddah bata gama rufe baki ba pretty ta lailayo Ashar ta kunduma, wlh yaya Saif yafi karfin ta, Yaya Saif nawane ni kadai, ke kota halin kaka sai munje Birthday din nan wlh,
*************************
OFFISHIN SHUGABAN KASA
“Mai girma excellency akwai kudade da aka Samu anyi sama da fadi dashi, wanda aka tura domin yin aikin hanyar nan da ya tashi Daga Plateau state zuwa Zaria,
    Sannan maganar Karin Albashi na maikata da aka rattaba hannu anfitar da shi ga shugaban kwadugo na kasa baki daya, zuwa watan January za’a fara biyan su akan Sabon tsarin Albashin, game da bukatun gobnoni kuma nacewa budget din da akeyi ake tura musu duk shekara ya musu kadan gurin gudanar da ayyukan dasuka ma jama’ar kasa alkawura suna bukatar kari,
       “Masha Allah duk naji  bayaninka sectary,
Batun kudin gyaran hanya da aka ce anyi sama da fadi dashi, zamu shirya kwamitin bincike don binciko wanda suke da Hannu a cikin Almundahana,
Sannan maganar Karin Albashi ga ma’aikata bazai Samu a fara biiyansu Watan January ba sai dai zuwa karshen wata October,
   Maganar kuma budget Zamu duba irin kokarin da sukeyi ma talakawansu sannan muga abunda ya kamata,
    “Ok My Excellency  Thank you, fita yayi shikuma yaci gaba da rubuce rubucen shi,
*************************
“Nifa Alhaji Mai Nera lamarin Vice president na bani mamaki dole fa musan yanda zamuyi dashi sbda yana kawo mana cikas a harkokin mu, “Nifa Alhaji Dala ba’abun dake damuna irin yaron nan nashi Saif da kake ganin shi hatsabibin yaro ne gashi ya iya binceka na karshe, kuma kasan Excellency yace za’a kafa kwamitin bincike game da kudin gyaran Hanyar nan, Kuma kasan Vice president zai dora akan binciken, shi kuma ya dora wannan takadirin yaron nan nashi Saif,
     “Ai yana can sun turashi wani bincike a kano kuma Game da Govnor Attahiru ne, shiyasa na kirashi nace yayi taka tsan tsan da yaron,
    “Kai dole mu dauki matakin gaggawa zamu hadu dai a kungiya Anjima da dare, Mai girma Zanjabiluuu yana kiran taron gaggawa,
   “To sai Anjiman in mun hadu, Musabaha sukayi suka tashi kowa ya hau Motar shi Security dinsu suka rufamu musu baya,
***********************
Sauri take tayi ta dawo Daga Chemist din kasan layinsu ta siyo ma yar uwanta magani, Kacibus sukayi da Mudi,
    “A’a Ustaxiya Sumayyatu Daga ina?
“Wlh Mudi naje siyo ma rabin rai maganin tsugine kasan ciwonta ya tashi,
     “Allah sarki Maryama baiwar Allah, wlh jiya nake cewa kwana biyu na rabi da ganinku ko gurin fanfo diban ruwa, Ashe ba lpy ne, Insha Allah zan shigo in gaidata anjima innaje na Anso bashin kudin aikina a kasuwa Nera Dari sai in siyomata ko Lemon talatin ne, dama Omo nakeson in siya in yi dauraya,
     Dariya Sumayya tayi tace “to Allah ya kaimu Malam Mudi bari inje kar Ummu tajini shiru, ✍️✍️✍️✍️✍️
Kar ku manta na kudi ne please kar ku fitar mun da Novel na rokeku🙏
Comment
Vote
Like
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
Part two na kudine
3and4
Please show me love don’t share my Novel ina sonku Masoyana Allah ya bar kauna, na tabbatar iya wuya muna tare 😍😍😍
“Haba sweet heart  kasan kwana biyu da ban ganka tamkar banda lpy nakejina, kawai sai ka tafi ba Sallama, tana maganar tana shirin Zama a kujeran dake Office din,
        “Who dare u da kike shirin Zama min a kujera who allow u to seat down!!! Get out ni zaki shigoma Office ba Sallama kinyi shiga kaman na kilaki ba Sallama sannan ki zauna mun akan  kujera,
    Get out in my Office!!!!
“Wlh bazan fita ba yau sai anyi ta ta kare kai waye dazaka dunga wulakanta ni a Banza a wofi don Kaga ina Sonka, iyeehhh to wlh ni Ikram nayi Alkawari ko da Masifa da Bala’i ko zaka Aureni ne ka dunga dukana kullum sai ka Aureni wlh, I will tell u Rubbish  Man mai kake daukan kanka ne ko dun Kaga na nace ina sonka, ina da dalilin da yasa kuma burina na cika a kanka shikenan, wani tsaki ta ja mtssswwww ta juya ta fita tayi mai banging Kofar,
Kawai tsayawa yayi yana kallonta kuma yana juya kalamanta idon shi ne ya kada yayi jawur, Mussaman da tace Koda Bala’i da Masifa sai ta Aureshi, sannan sai burinta ya cika a kanshi, tabbass itama yarinyar nan da Alamar question a tattare da ita dole ya samata ido sosai ya baza Security a kanta, juyawa ya fara yi akan kujerar shi idon shi rufe,
Daga  ganinta kasan yana cikin tension Firgigi yayi ya jawo phone nashi,  danna kira yayi ya kara a kunne,
     “Hello Officer Junaid,
Ina son ku Samun ido akan yar gidan Govnor Sosai, sbda ban yarda da ita ba, yes ok tom well done, ya kashe phone din yaci gaba da abunda yake yi,
*************************
Darene ya tsala sosai inda Hausawa ke cewa Dare Mahuta Bawa, to a gurin Su Sumayya da Ummu ba haka bane domin jikin Maryama yayi tsanani kuka takeyi tamkar ranta Zai fita, inda Ummu tana rike da hannunta tana tofa mata Addu’a ita kuma Sumayya tana rike da Kafafuwanta tana tofa mata Addu’a,
“Innalillahi wainna ilaihirraji’un Ummu ku yafemun mutuwa zanyi kafata kamar Ana kwanmwatsamun kasusuwana kamar Ana kunna musu wuta, waiyo Allah ni kadai nasan me nakeji, wani Kara tayi tana Kara danne kafan wasu zafafan hawaye na zubo mata sai gab da Asuba barci mai dadi ya dauketa, gwanin ban tausayi,
Asuba ta gari, gaba daya sun tashi ba walwala saboda yanayin da suka kwana a gidan, gashi sun tashi ko abunda zasu ci basu dashi, Sallah sukayi suka zauna Zaman yin Azkar,
      “Rabin Rai”!!
Kiran da Maryama ta kwala ma Sumayya ne yasa ta tashi, ta isa dakin kwanan nasu,
“Rayuwata kin tashi?
“Meyasa baku tasheni ba nima inyi Sallah tare da ku, kika sani ko shine Sallah ta karshe da zanyi daku, “haba rabin rai ni ban son kidinga fadin haka, cuta ba mutuwa bace, fita tayi ta dauko mata buta da bowl don tayi Alwala, haka ta dunga zuba mata ruwa tana alwala har ta gama, hijab tasa mata ta jingina ta a jikin Bango ta dubi gabas ta kabbarta Sallah,  ita kuma Sumayya ta zauna tana kallonta harta idar da Sallah, sai ga Ummu ta shigo rike da Hisrul Muslim a Hannu ta mika mata karba tayi ta fara Azkar,
    “Ummu yanzu ya Zamuyi?
“Kije gidan su Guggon Hansai ki karbo mana kullun kunu na Hamsin da gawayin Talatin, “to Ummu, tashi tayi ta dauki wani dan kofi mai murfi ta sa hijab dinta ta fita,
*************************
KAUYEN WURNO
“Tashi ga abincin, “tom Ansa yayi ya fara ci da sauri da sauri, kura mai ido tayi tana mai jin tausayin shi gaba daya rayuwar shi dana iyalan shi da dangin shi suna cikin gararin Rayuwa, wai meyasa Bil’adama suke haka ne, “ngd sosai Zankadaziyyatu ina ji a jikina Burin mu ya kusa cika, “hakane Ranka ya dade Insha Allah don jiya munyi magana da Jaddi Abdullahi but akwai Masifo da zasu faru da yawa kafin Komai ya daidaitu, kai Bil’adama bala’i ne wlh,
      “Ki bari kawai haka dai suka wanzu suna hira, har ya kammala cin abinci shi, ta karbi plate din wani Addu’a ta mai kawai sai ya koma kamar  yadda yake, da sauri ta lallaba ta fita tana fita ta bace abunta,
************************
MAITAMA PALACE HOTEL
Hotel ne da ya Amsa sunanshi Hotel wanda sai wane da wane suke Zuwa,
     Wani Hall ne da ya Amsa sunanshi Hall duk inda ka duba wasu manya Motocine masu Nunfashi 😜wanda sai wane da dan wane zaka gansu dashi,
Yarane matasa mata da Maza suke ta parker Motocin su,
Can na hango Jiddarh da Pretty   Sun shigo a wata Aljannar Car, ban kara  tsinkewa da al’amarin su ba, sai da suka fito wani matsiyatan kaya da suka sa, wanda dashi da Babu duk daya musamman ma Jiddarh, fitowa sukayi nan da nan yan mata da Samari suka tsagayesu suna musu ihu,
     “Sai Babban yara, Yaran Excellency, ganin ku tamkar Gani Zarah ne da wata, nan da nan Jiddarh ta bude Jakarta ta fito da kudi tana waza musu, Yesss fara mai farar Aniya duk wanda ya ganki ya zama milloniya Ana kara fasa mata kai,
In ka kalli Harabar Hotel din zaka dauka rana ne,
Ikram ne ta shigo itama Anata Motar ta parker ta fito, itama yehooo aka fara mata, “indai kayane akwai kaya, ina gwanin wani ga tawa kina takama ko kana takama da kasan kan daga kwalba to ga shugaban ku, Wani yamutsa face takeyi ta cire No respect din glass din ta da yake fuskan ta,
    “Laila  a raba musu dukka wata yar Hannu  a basu kayan aiki 3 battle plus syrup per each Person,
“Yeeeeeessssssss munayinki Attahiru Daughter 😂😂😂,
Ana haka dan Govnor Kaduna ya iso shima da nashi tawagar, a haka a haka suka dunga zuwa guri ya kaure da Hayaniya, hall ya cika makil kowa naji da kanshi yanaji Ubanshi wani shege ne a kasar,
. high Table aka ba su Jiddarh, ta dayan side din kuma Ikram ne da nata tawagar sai Harare harare suke Aikawa junan su,
*************************
“Gskya ni bana bukatan Alhaji Mahmud a cikin tafiyar nan kasan munyi munyi ya shiga kungiya yaki, Kuma shi kullum Wa’azi ni fa gskya dole a san yanda za’ayi  Excellency ya sauki Alhaji Mahmoud a kan mataimakin shugaban kasa, Alhaji Dala muke bukatan ya maye gurbinshi, kuma na mance jiya da’aka taru taron kungiya inyi Magana,
“Kasan meye akwai matsala fa don Kaga Wannan Irfan din dan gidan Excellency shima ra’ayinsu daya fa da yaron nan Saif to ni abunda ban gane ba shine, wai shi meye aikinshi, da fatan shima DSS din bane, wlh ban sani ba,
Niko na ce bazaku sani ba kuwa shegu Azzalumai kawai Allah ya fiku🙄😏
*************************
“Ummu  Rabin rai!!! Da gudu suka shigo dakin ganinta sukayi cikin jini Face face ga shi sai juyi takeyi a tsakiyar Dakin barcin nasu✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Karku manta na kudine please kar ku fitar mun da Novel na rokeku🙏
Comment
Vote
Like
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu9333
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
5and6
Ashe da rai nake son ku masoya bada zuciya ba komai ruwa da iska akan ku baza nadena typing ba idan na samu Comment naku baza nadena typing ba ni Banga mai Harara ba balle na waiwaya eh eh😂😂😂
Maman Ahmad, sister Adama da fatan na iya wakar nan koh
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
“Mun shiga uku Ummu jini ne fa yake zuba, kar jininta ya kare,
    “To ya zamuyi Yar albrka dagota Ummu tayi, yayi dai dai da fadowar gudan wani Abu daga kasanta, “Ummu kalli wani Abu ya fado da sauri Ummu ta kalli gurin da Sumayya take Nuna mata inna lillahi wainna ilaihirraji’un kaman gudan jini, kaddai ace Bari kikayi Maryama, dukawa Ummu tayi tana kallon Abun Tabbas Bari kikayi Maryama, Allah mai iko Dama ciki Gareki, bamu sani ba,
     “Ummu ciiii kiii fa kikace Rabin ran nawa Allah ya isa tsakanin mu dasu wlh Sai na dandakesu da hannuna yan akuya kawai, wani Kara da tayi ne yasa duka suka kara riketa wani gudan ne ya kara fadowa, Sai guma jini ya kara ballewa kaman an bude fanfo rasa yanda zasuyi sukayi gaba daya, kawai Sai ganin wata Mata sukayi ta shigo da kayan likitoci ko Sallama babu da Jakarta a hannu,
“Ku kamata mu kaita toilet kunada ruwan Zafi?
     “Eh eh muna dashi to ke Sumayya yi sauri ki kawo mana toilet nan da nan suka wanke mata jiki suka samata kaya tamkar matacciya suka dawo da ita daki kayan Aiki ta dauko ta fara mata Alluran tsayar da jini sannan ta samata Drip ta samata Alluran Karin jini cikin drip din, ta mika ma Ummu Magunguna a Leda a tabbatar a dunga bata waddan nan magunguna sannan ta dunga tsarki da ruwan zafi sosai sbda Bari tayi, kafin a gama, Sumayya ta tsaftace dakin tsaf ta kunna turaren wuta a dakin ita kuma likitan ta juya zata tafi Ummu tace Baiwar Allah baki cemana komai ba,
      “Sorry ni likita ce a can Sabon Asibitin da aka bude har na fito zan tafi gida Sai ga wani saurayi yazo mun a rude yana in tai maka mai Matarshi zata mutu, shine fa muka taho tare, yana nan a waje ai, ni kuma don Allah na muku,
     “Mun gode Allah ya saka da alheri suka biyota a baya suna fitowa Mudi suka tarar ya zauna yana ta sharban kuka yana ganin su ya taso, “likita bata Mutu ba koh taji Sauki,?
   “Karka Damu taji sauki Sai anjima ku Allah ya kara lpy,
    “Da sauri Mudi ya karisa kusa da Ummu, yana fadin “Ummu Masoyita tana jin jiki wai yaushe zata daina ciwo ne, ni banso inga bata da lpy, nima sai inji kamar banda lafiya, zan iya shiga in ganta,
   “Kayi Hakuri Mudi tayi barci kuma likita tace kar a tasheta, to bari in zauna in jira ta tashi,
    “A’a kadai je kila da abunda zaka ma Guggon ku, zuwa anjima Sai ka dawo in ta tashi,
   “Kai Ummu bazan iya tafiya in barta a haka bata farfado ba ni kawai Sai ta farfado tamun magana zan tafi, “to shikenan kaje ka fadama Guggon ku kana nan anan gidan in anzo Ana Nemanka, “to bari inje in fada mata fita yayi da sauri don Zuwa gidan nasu,
*************************
“Yanzu Ana bukatar ganin Babban yaro Haisam zai zo Shida Abokanan shi su yanka Cake kafin a dan rausaya reader ku tayani Gani wani Bakin Matashi ne tsaka tsaki tsayinshi ga hanci ga wani Aski da yayi irin wanda suka san kan duniya sukeyi an aske gefe da gefen kan sannan akazo aka sama kan wani Colour ga dankunni Zinare ne a makale a kunnanshi jikin shi duk an tsane mai da tattoo ga wasu sarka da ya zuba a wuyan shi, ga wando ya zazzago tamkar zai fado, wai duk cikin gayu ne haka, gaba daya Hall din ya dauka da ihu Haisam!! Haisam!! Haisam!!  Shi kuma yana wani Kara takun kasaita yana daga musu Hannu har ya isa gaban Cake din Yan matane suka taso duuu duka ba wanda tayi shigan Mutunci a cikin su, tamkar da tsirara suke, kowa tazo zata rungumeshi ta bashi peck a fuska Sai ta mika mai gift ta mai Happy birthday a haka Duk suka gama akaje dif aka kashe light din gurin a Kuna flash light ya hasko ya koma aka kunna Candle nan guri ya dauka da da Happy birthday to u Haisam hure Candle din yayi duka yan matan nan suka zo suka rike mai Hannu aka yanka Cake din nan fa guri ya Kara yamutsewa kowa kokarinta ta gutsiro Cake ta bashi, daga nan fa aka fara Shaye Shaye da raye raye, Kowa ya fara jan abokan harkanshi less, Hamones, Sex, Drug abuse, niko nace Wa’iyazibillah gurin nan yafi karfina, na tattaro na fito,
Basu suka tashi ba Sai Hudun Asuba ba, Su Jidderh ansha anyi tatul da yake ita pretty bata shan komai ita dai batta da Less, ita ta ja Motar sukayi gida tana jin farin ciki sbda New Catch din datayi Beb din ta hadu, gashi ita ta fara harka da ita, sun iso President House Karfe hudu da rabi, ko Horn basuyi ba Security kawai sukayi ma waya ya lallabo yazo ya bude musu get, suka shigo parking sukayi fitowa tayi ta jawo Jiddarh da har yanzu bata dawo Normal ba, Sai surkullenta takeyi Alamun mutum na cikin Maye, sun kai dai dai side nasu zasu shiga wani tsawa da yayi musu Sai da ya girgiza su, har Jidderh datake cikin Maye Sai da ta dawo Normal😜
*************************
“Hello Excellency Wai Aslm ne yanzu aka kira ake cewa bai da lafiya yanata kiran sunan wata yarinya, Doctor mu na can kuma ya duba shi yace Heart Attack ne kuma indai ba’a bashi abunda yakeso ba zai rasa ranshi, u know Su kadai garemu daga shi Sai kanwarshi please Excellency Ka dawo mu tafi UK nan musan me zamuyi, inji yar gidan Uban waye ita da take Neman kashemun yaro, Ok tom Sai kazo ✍️✍️✍️✍️
Comment
Like
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍
7and8
I am not felling better  ku sani a Addu’a,
A haka nake sonku Masoyana Kuna raina,
*************************
~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM~
“Daga gidan Uban wa kuke iyeeehhhh!!  Tsuru tsuru sukayi suna kallonshi,
     “Don Allah Yaya Irfan kayi hakuri,
“Shi na tanbayeku cewa nayi daga ina kuke ya fara zaro Belt din da ke jikinshi yana biyosu, duka ya fara musu kaman yana jibgan wasu Barayi ihu suka sa suka dunkule guri guda,
    “Kai!! Kai!!  Kai!!   Dakata Irfan bafa zaka tasamun Ya’ya a gaba kana jibga ba kaman kasamu jakuna,Eheeee ta karishe maganar cikin karaji,
Ko kallonta baiyi ba yaci gaba da jibgansu sai da ya tabbatar ya musu jini da Majina sannan ya kyalesu,
Ihu ta saka tana tsitstsine mai albrka da zagi kala kala “wlh bari Uban naka ya shigo tunda bakajin maganata ka rainani abunda kaga Dama shi kakeyi a gidan nan kabi ka takurama yarana ka sasu a gaba iyee rayuwarka ko rayuwarsu,
   Tana Wannan Masifan ya raba ta gefenta ya wuce, hadi da Ballara musu harara “Next ku kara abunda zan muku sai yafi haka don wlh sai na kakkaryaku shegu yan iska,
“Ga kanan babban dan iska kai wayasan uban da kake shukawa shiyasa kaki Aure har yanzu, tana fadin haka hadi da kwala ma mai aikinta kira Ruth Come and take my Child and take good care about us,
     “Ok Mah”   kama su sukayi ita da wata suka shiga dasu da kyar ma suke Numfashi,
  “Where is d Security!!!??
“Yes Sir ya kariso da gudu gurin shi ya Sara mai, Who allow that stupid girls out in this House!!!?  Kame kame ya fara I am asking you fa?
    “Wlh sir bani bane Daniel ne ya bude musu ya karishe maganar muryan shi ba rawa,
“Where is Daniel??
“Sir yana kariso wa ya dauke shi da Mari sau biyu, duk randa ka kara barin Yaran can suka fita a bakin aikin ka kuma sai na hukunta ka tukun kafin in koraka, I are u get it?
“Yes Sir, Sorry sir, Thank u sir, duk ya jero su a haka,
Juyawa yayi ya shige Mansion dinshi, ya barsu a nan tsaye,
    “Amma kai mugu ne kuwa haba Badamasi kai baka iya rufin Asiri bane,
“Ina ruwana lokacin da suka baka kudin tare muka raba da zan rufa maka Asiri tab, to ai shikenan tunda hakane,
*************************
Wani Babban tashin Hankali kuma Maryama ta farfado da ciwon Convulsions tsinkau tsinkau haka take jijjiga tana daddatse bakinta idanuwanta na kakkafewa sai kakkamewa takeyi Ummu kuka Mudi kuka, Sumayya ce kawai mai karfin Halin rarrashin su, sun rasa yanda zasuyi, Addu’a duk wanda yazo bakin su shi suke tofa mata, haka ranar suka yini tana cikin Wannan hali komai ba wanda ya iya ci a cikin su har su Guggon Hansai duk sun shigo, but ba wani wanda zai iya bata taimako haka suka tasata a gaba, Sallah kawai ke tashin su Mudi ko ya Maya Asibitin nan yayi sau biyar baiga Wannan likitan na jiya ba karshe ma koranshi sukayi suka cemai kar ya kara shigo musu Asibiti,
   Haka ya dawo ya zauna ya rike Hannun Maryama gam kamar zata gudu ta barshi, “don Allah Meramu na karki tafi ki barni, in kin mutu binki zanyi kamar taji mai yace ta bude ido tana kallan shi, “ina rabin rai na? “Gani Rayuwata waigowa tayi ta kura mata ido, Ina sonki Rabin raina ga Mudi nan ki kula dashi zai baki gudunmuwa a rayuwarki zai taimakeki gurin daukan mun fansa, Nasan Mudi Masoyinane na gskya nima ina sonka Mudina ta fadi haka tana Murmushi, Farin ciki ne ya lullube Mudi yau Meramun shi tace tana sonshi, kara rike  Hannun ta yayi sosai “bazaki Mutu ba Meramu zaki Tashi Muyi Aure har mu haifi yara ya fadi haka yana rufe ido irin Yaji kunyar nan, Asusu na danake Tara kudin Auren mu ya kusa cika, yana cika zamuyi Aure, Murmushi tayi mai, duk da karfin haline Kawai takeyi, itako Sumayya hawaye take tayi Amma taki yarda Ummu su ganta, juyowa Maryama tayi tana kara riko hannun yar uwar nata, “Rabin raina Tabbas nasan in na tafi na tafi da rabin rayuwarki, Amma na barmiki Ummu da Mudi, Sannan duk randa Ustaz Mansir ya dawo ki fada masa ina son sa sosai, ciwon ne ya kara dawowa ta fara kakkamewa tana datse harshenta lebenta jijjiga takeyi suna rirriketa nan ta fara Salati da sauri Ummu ta fita daga dakin tana fashewa da kuka,
*************************
UK
Saukan su UK kenan harda Ikram duk ta rude sbda Son da take ma Dan uwan nata direct Asibiti Suka Wuce, suna isa suka tarar dashi ya yi figai figai gashi an samai Oxygen don ceto Numfashinsa, da gudu Ikram ta je bakin gadon ta fa she da kuka please Beb Karka tafi ka barni ka tashi, Ita ko Hajia Mariya sulalewa tayi a gurin tana kuka, Alhaji Attahiru ne yayi karfin halin cewa “haba First Lady yazaki tasashi gaba kina kuka kamata yayi ki Tashi mu nemo mai Mafita, to wai shin ma ina su friends nashi da sukazo tare ne, sai dai ka kirasu Alhaji, waya ya ciro cikin Aljihu Number KB ya kira dauka yayi Alamun ma yana buge ne,
   “Hi daguss ya akayine kun shigo ne muzo airport din mu dauke ku,
“Haba Son Kuna ina kuka barshi shi kadai, mu yanzu haka ma muna Asibiti, “ok gamunan zuwa 1hrs kit ya kashe wayar, lokacin kuma shi KB na tsaka da jin dadinshi Pappa ya katse mai cigaba da badalanshi yayi, sai da ya kammala sannan, suka shiga sukayi wanka ko a Bathroom din sun bata gurin Awa kafin su fito, yazo ya tarar da sauran friends nasu suna ta Shaye Shayen shisha da wiwin su suna Kuma Caca abun su ga kida na Tashi, “Hi gays Dagus din Aslam fa sun sauka tun dazu suna Asibiti,
    “To me zamu musu just tunda sun zo Muma mun huta sai su cigaba da kula da dansu, ko ya kukace Babah, “eh kawai share Mucigaba,
   “Amma gays baku da mutunci fa at least kwaje ku gaidashi, kuma kukara duba Aslam din da jiki, “hey hey don Allah KB ware kawai Karka damemu, kai dakaga zaka iya zuwa sai ka tafi,  juyawa yayi ya tafi sukuma suka cigaba da Cacan su,
“Gskya Mammah ni yanzu na mance ma gidan su Yarinyar a Nigeria kinga dai pic nata kuma itama tana nan a kasar nan but bamusan masaukinta ba,
    “Ya zama dole yau a Nemo yarinyar nan indai tana kasar nan, Abunka da masu Hannu da shuni nan da nan aka Baza pic din Sumayya a UK, duk wani tashoshin TV, haka ta aika da pic din Nigeria shima tace a Baza pic din duk wanda ya ganta zata Bashi gida da Mota da kudi kimanin Miliyan biyar,
*************************
“Kai Oga kwana biyu mun rabu da kai Hari ko ina sannan naji fa, wani News wai UK na neman wata matashiyar Yarinya sbda ankamata da safaran miyagun kwayoyi kuma ni yarinyar ma fa is too young Oga wai an kamata ta gudu, Abu ya bani mamaki fa Wannan yar  karamar yarinya ne take Safara, kuma wai gomnatin kano ma tana Nemanta ta kai Hari gidan Govnor,
   “Kai Hamid ya isheka na gaji da jin Wannan shirmen Banza, Wannan maganar akwai makarkashiya ina son a samo min ainihin gskyan labarin nan da kwana uku daga Nigeria har UK, kuma ina bukatan nima akawo mun  ita nan kuma a Raye cikin koshin lpy, a kiramun Shatu  ta sameni a a dakina ya juya ya shige, “angama oga shima ya juya,
************************
“Please karki mutu Rabin raina ita ko sai fadin kalman shahada takeyi✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
9and10
WAZAN AURA na kudine ngd sosai da kulawarku gareni masoyana yanxu kam na fara Samun sauki Alhmdulillah Insha Allah zaku dunga jina yanzu.
~BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM ~~
“Lah ilaha illa lahu Muhamadur rasulillah sallal lahu Alaihi wasalam tana kaiwa nan jikin ta ya sake fuskanta dauke da Murmushi idanuwan ta bude tamkar tana kallon Sama, fuskanta cike da Annuri,
“Innalillahi wa’innah ilaihirraji’un Ya Allah kulli Nafsin za’ikatul Maut Ubangiji Laifin mai mukai maka ne, Allah mun tuba mun kuma yarda da kaddarar mu, Ka kawo mana karshen jarabawar nan, Allah ka sani muna San Maryama Amma da yake kafi mu sonta sai ka  dauketa ka barmu da kewanta, Allah kasa Mutuwa ta Zama hutu a gareta, Fashewa da kuka tayi tana cigaba da fadin Allah mun tuba,
Ummu ne ta shigo da gudu tare dasu Baban Mudi, “tana Nuna musu ita don Allah ku dubamun ita kar ku cemun ta Mutu ta karishe maganar tana fashewa da kuka, Baban su Mudine ya tabe ta ya dudduba duk gurin magudanar Numfashi ya tabbatar da Maryama ta rigamu gidan gskya, Ummu Sumayya sai dai kuyi hkr don Maryama ta rigamu gidan gskya,
    “Wai ni bangane me kuke cewa bane BABA cewan Mudi Wlh Meramu na bata Mutu ba ku kalla fa ku gani Murmushi take mun fa, haba haba karasawa gaban gawan nata yayi yana jijjiga ta Meramu na ki tashi ki fada musu baki Mutu ba da Gudu Sumayya ta karisa ta rungume Ummu da take shirin Faduwa, Baban Mudi ne yaje ya riko Mudi, haka suka fita dashi yana ihu yana fadin shi Meramun shi bata Mutu ba, gunin tausayi, nan da nan gida ya cika Makotan su duk sun shigo, Ummu haka ta zama ba um ba um um Sumayya ne tayi karfin halin yi mata wanka da taimakon Matan da suka shigo aka yima Maryama sutura karfe biyu aka ma Mata Sallah aka kaita gidanta na gskya inda Mudi Suman shi Uku itako Ummu Alwala tayi ta dauko littafin Addu’oi ta dunga yi inda Sumayya ce kawai mai Amsa gaisuwar mutane in anzo musu gaisuwa, ranar shi ya kasance musu a cikin jerin ranakun bakin cikin da suke fuskanta a rayuwarsu Allah ya basu ikon cinye jarabawar ya kawo musu dauki a rayuwar su ya sauya musu kaddarorin da zuwa alheri,
*************************
Tsaye take bakin hanya tasha gayu taci space da wani riga da ya sauko mata har gwiwanta da wani pencil wando da tasa tayi rolling da wani mayafi tasa glass da ya kusa rufe mata face tasa wani hill shoes taunar chew gum takeyi, tanayi tana duba agogon dake hannunta,
     “Pappah wait wait wlh ga yarinyar can wani birki driver ya taka suka dawo baya da sauri dai dai ita Kuma ta tari taxi KB ya sha gabanta zata shiga taxi “excuse me yana shirin rike mata hannu da sauri ta ja baya tana mai wani matsiyacin kallo “kai baka da hankali ne kake kokarin tabani ko Bunsurancin nakane ya motsa zaka sauke a kaina ta karishe maganar tana rabawa ta gefe zata wuce, da sauri ya riko hannunta bai gama dai daita rukon da yayi mata ba Yaji wani Saukan Mari da bai ga zuwan Marin ba kawai jin Marin yayi har Barayi biyu, nan da nan fuskan shi ta kunbura ya rasa ganin shi na wucin gadi, hakan yayi dai dai da isowar su Pappah da Ikram sbda ita Mammah sun barta Asibiti, Ikram tana zuwa batayi wata wata ba ta daga hannu zata Mari Sumayya, aikam caraf ta rike Hannun tana mata wani kallon uku saura Kwata, ihu Ikram tayi tana fadin dallah Malama sakeni, kallon raini Sumayya ta bita dashi, “ke jaka yar akuya banzo kanki ba tukunna Kuma kinyi kadan ki daga hannu ki mareni, sbda ke ba tsaran yina bane, Wannan tsohon Matsafin Kuma Azzulumin uban naki shine dai dai ni, wurgar da hannun tayi, ta kallesu gaba dayan su tace musu,
     “Ni Sumayya nafi karfin in Auri dan Akuyar yaronka, ba wai kun bada cigiyata ba to zan ga wanda zai kamani, mahaukatan banza da wofi kawai ta shige taxi tayi gaba ta barsu a gurin gaba daya an rasa mai cewa kala, sai Ikram da take kuka kasa kasa sbda Azaban da hannun nata yake mata, shiko KB nan da nan halittan fuskanshi ya canza, sai da tayi Nisa pappah ya zabura yana ta tafi fa ya akayi bamu kira Security ba,
Niko nace ku za’a tanbaya
*************************
“Oga wato yarinyar nan ashe wai dan iskan yaron nan ne dan gidan Govnor kano yake Santa, nanda ya bashi labari gaba daya akan abun but Abunda ya daure musu kai ance yarinyar bata da Uba Kuma bata da masu tallafa musu Kuma ance sun kara haduwa da yaron a UK,
    “Gskya ina son sanin cikakken bayanin akan Yarinya “ok Oga zamuyi kokari sosai sbda ina Zargin wani abu game da yarinyar Anya ba ita bace yarinyar da muke bukata kasan in har bamu ganta ba fa burin mu bazai taba cika ba, “gskya ne oga nima na fara zargin haka, but zamuyi iya kokarin mu,
*************************
Yau Maryama ta cika kwana uku da rasuwa yayin da kowa ya watse sai dai Mutanen gidan yayinda Mudi ya maida dakin su Maryama da katifanta gurin Zaman shi da kyar suke lallabashi in dare yayi ya tafi gida, Asuba nayi kuwa shi zai buga musu kofa, hoton ta ko shine Abokin hiran shi, yau Sumayya ta tashi ta Same Ummu akan maganar zata sai da wayar Maryama ta sayi Keken dinki kasancewar dama sun iya dinki rashin keke ne, sannan ta roki Ummu da Su saida gidan nan su canja Unguwa hakan zai rage mata radadin rashin yar uwanta, Ummu batayi Musu ba kuwa, a ranar aka nemo masu siyan gida suka siya gidan nasu, a ranar Baban su Mudi ya siya musu wani gida a can tarauni gidane karami bai kai ma girman gidansu ba daki biyu ne sai dakin Kofar gida a zaure sai shago a Kofar gidan sai toilet da kitchen, gidan duk siminti ne, Washe gari suka shiga makota sukayi musu Sallama kowa baiji dadin tashin su ba sbda an saba, Mudi ko cewa yayi tare zasu koma haka KO akayi tare suka koma gidan ✍️✍️✍️✍️
Like
Comment
Vote
I love you too my fans
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍
WAZAN AURA na kudine don Allah kar kiyi mun sharing Novel ina sonku Masoyana,
*************************
~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ~~
11 and 12
“Alhaji Dala ya batun kayan da akayi oder din nan ne, na aikin  Company da za’a bude maka ne,
     “Wlh kai dai bari wlh Company ne ya fita mun a kai sbda EFCC suna so su sani gaba, game da kudaden gyaran Hanyan nan, ga shegun Yaran nan Irfan da Saif inda kasan suna aiki da Aljanu, shiyasa nace zan dakatar da Bude Company sai komai ya lafa,  gskya kam nifa ya kamata mu Samu mister Prisedent game da maganar nan don wanin tafiyan fa ba irin na da bane, ni ban san meyasa aka saka Hatsabiban Yaran nan ba a cikin harkan tsaro, kaga in har hakan ya cigaba za’ayi walkiya fa Asirin kowa zai tonu, Hayaniya ne ya kaure tsakanin Dattawan da ke zaune a haraban gurin shakatawan da sunkai su goma, ku dakata gskya ya kamata mun kai sunayen Yaran nan gurin mai girma kakkau sbda yayi mana Maganin su, gskyane kuma Alhaji Rufa’i haka zamuyi kawai taron nasu ya tashine bayan kowa ya Amince da shawarar Alhaji Rufa’i.
*************************
“What ban gane ba Sumayya ne ta kai hari gidan Govnor, Imforsible wlh I swear akwai wata a kasa, bama ance Govnor din da iyalanshi suna UK ba, dolene Junaid ka binciko mun gskyan lamarin, but ni tunda na dawo ban sata a ido ba ku har yanzu taki Amincewa in san gidan su, Ina son sanin ko ita Wacece dole kamun wannan kokarin kai da Jafar,
       “OK sir insha Allah, yana gama fadin haka ya fita, shi kuma ya fara zarya a Office din,
************************
“Ummu zanje in shishiga makota in gaya musu muna saida Abubuwan provision, sannan muna dinki koh,?
“Eh hakane ki sauri dai ki dawo to Ummu, Kallon Mudi tayi da ya zauna ya kurama guri daya ido, “dan Uwa zo muje ka rakani mana, Bai maji abunda tace mai va tsaban tunanin da ya shiga, sai da ta dan tabeshi sannan yayi firgigit yana binta da kallo “lpy Rabin raina sunan da ya koma kiranta kenan tunda Maryama ta rasu, Shiru tayi tanajin sunan har cikin jinin jikinta sai mutuwar yar uwar tata ya dawo mata Sabuwa, da sauri ta fice gidan sbda bataso suga Hawayen da ya taru mata a Idon ta yake kuma shirin zubowa,
Fitowan ta kenan ta shiga gidan da ke kusa dasu, ta fito a haka dai duka sai da ta shiga gidajen unguwan nasu har ta Bayan layinsu ta shiga Fitowanta daga wani gida yayi dai dai da Zuwan wani Mutum da Police yana fadin wlh gatanan itace nan kuke nema ku kamata muje a bani kudina 😲zaro ido tayi tana mamakin maganarshi sbda bata san inda maganar ta dosa ba Aiko batayi wata wata ba ta tattare hijab nata ta Ruga da gudu, sai tabi wani hanya don bazata yarda taje gida ba balle suga gidansu,
************************
Saukan shi kenan a airport na kano saboda kiran da Abokin nashi ya mishi sbda yana bukatar taimakon shi, Mota aka kawo mai kasancewar shi mutum ne wanda bai son a san shi waye bai yawo da Security, kuma bai son kowa ya tukashi yafi bukatar yayi komai da kanshi, bayan ya karbi makullin motar ne, yace musu zasu iya tafiya, sai da suka kara salute nashi sannan suka tafi,
 Motan ya hau ya kama hanyarshi yana tafiya yana jin kira’a Ahmad Sulaiman, kwana yayi dai dai Titin tarauni aka kirashi a waya da sauri yayi parking motarshi sbda shi mutum ne mai kiyaye doka, bude murfin motan yayi ya fita yana Answer wayar daga gani Magana mai muhimmaci yakeyi, Harbi Yaji ta bayanshi da sauri ya waiga hadi da ciro bindiganshi can ya hango wata yarinya ta shige motarshi da sauri kaman walkiya, can sai ga police da wasu Mutane sun rufe fuskokin su daga gani yan ta’addane Ana musayar wuta, can wani yayi Magana a cikin yan ta’addan “ku tabbatar kun nemo yarinyar nan don Oga yana bukatan ta a raye,
      DPO ne yake Magana ga yaranshi “karku sake ku bari su tafi da yarinyar nan don Zai iya zama a bakin aikin mu,
Shidai kawai ya tsaya yana kallon su, sunata harbe harbe, kuma Yaji duk abunda suke fada a tsakaninsu, sai Yaji yana bukatar ya taimaka ma Yarinyar nan, da sauri ya karisa gaban Motanshi ya hau Motar ya ja da sauri, ya bar gurin✍️✍️✍️✍️
Vote
Comment
Like
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
WAZAN AURA part two na kudine kar kiyi mun  share din Novel please
   Luv you too masoyana
13anda14
~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM~
*************************
“Me kika musu? Tanbayar da yayi mata kenan gabanta ne ya fadi jin Maganar da yayi mata dama ya san da ita a Motar to ina zai kaita,
     Duk a zuciyarta take wannan tunanin, katse mata tunanin ta yayi da kara fadin “meya hadaki dasu are u Criminal?
Da sauri ta tashi daga durkushen da take a cikin Motan ta koma kan seat ta zauna cikin jarumta da Nuna rashin tsoro, tace mai “I am not a Criminal Asali ma ban san su ba bansan mai suke Nema a tare dani ba, Muryanta da yaji ne gaba daya ya rudashi Yaji yana bukatar ganin fuskan yarinyar, tsayawa yayi cak tare da Waigawa, kureta da ido yayi yana tunanin ina ya taba sanin Yarinyar nan, Yarinya ce da bazata wuce 17&18 ba, gata da kwarjini ga kyawu kamar ita tayi kanta duk da hijab ne a jikin ta bai hanani tantance yanayin cikar zatin ta ba, yayi mata wannan kallon ne da tunanin duk a cikin minti goma,
       “Wai Mallam lpy kake mun wannan kallon? Allahuma inni Auzu minka in kunta takiya,
 Zaro ido yayi yana jin mamaki da karfin halin da taikacin yarinyar duk a lokaci guda, “ke me zan kalla a jikin ki iyeh ya fadi haka cikin fushi,
   “Abun da ake kallo ta fadi haka hadi da murguda mai dan karamin bakinta, bata ankare ba taji bakin shi kan nata, tureshi ta farayi tana ihu But ya matseta yaki bata daman ko motsi tayi sai da ya gama kissing nata son ranshi sannan ya saketa, yana sakinta ta fara zagin shi, Abunda bata tabayi ba zagin babba, Amai ne ya taso mata aikuwa ta fara kwara Amai sai da tayi mai isanta ta zauna tana maida Numfashi sai goge bakinta takeyi da hijab nata, tana zubar da yawu,  tanayi tana Allah ya isa dan iska kawai kuma ya bude mata kofa ta fita ko tayi mai ihu,
     Shiko tun da ya saketa ya koma ya jingina da seat din motar ya rufe idonshi yana mai jin Haushin abunda yayi gashi duk ta bata mai Car da Amai, gashi ba abunda ya tsana irin Amai don shima yanzu sai ya farayi, ga wani kunya da ya rufeshi,
    Dafata taji anyi da sauri ta zabura zatayi Masifa, maganar ne ya koma lokacin da taga wanda ya tabata, Nunashi ta farayi da Hannu zatai Magana yasa mata yatsa a baki alamar tayi shiru, dafata ya karayi, kawai sai gasu a Kofar gidansu tsaro ido tayi Hadi da kallonshi zatayi Magana,
   “Ban son jin komai daga bakin ki, Tabbas ni ba mutum bane, nasan tanbayar da zaki mun kenan koh?
     Kasa Amsa mishi tayi sai karkada mai kai da tayi,
“Ki shiga ki fadama Ummu anzo gaidata, sannan karki sake ki fada mata abunda ya faru, kinji ko, karkada mai kai tayi Alaman amsawa,
    “Summy Ummu wai yau kurma kika zama ne?  Ni nasan Sumy ba Matsoraciya bane, a hakane zaki daukan ma rabin rai Fansa kina tsoro, to dole in cire miki tsoron nan, ko kin manta nan ba da dadewa ba zaki zama Jami’ar bincike, kuma ki zama likita sannan ki cika Ma Maryama burinta na Zama Barrister kuma duk cikin aikin nan ba na rago bane da Matsoraciya, dole ki zama Jaruma jajirtacciya ki cire duk kan wani tsoro a ranki, kin ji Summyta? Ya karishe fadin hakan yana mata wani hadadden kallo mai kara ma masoya kuzari da tafiyar da damuwa, da sannu Sumayya ta dago tana kallan kwayar idonshi a hankali take jin wani abu daga idanuwanshi zuwa idanuwanta, take ta ji duk wani tsoro da fargaba da yayi saura cikin zuciyarta ya tafi, wani Sabon jarumta ne da wutan daukan fansa yake ruruwa a cikin zuciyarta wanda Tabbas zata iya yin komai don ganin ta dauki fansa wa yar uwanta da Ahalinta,, juyawa tayi ta shige gida ba tare data kara cemai komai ba, da Addu’a da Sallama a bakinta ta shiga gidan da sauri Ummu da Mudi suka taso suka zo gurinta hadi da tanbayarta Lpy suka ga ta juma ga unguwar Ana ta harbe harbe,
    “Karku Damu Ummu ina lpy da fatan kuma kuna lpy, ta karishe fadin haka tana shigewa daki, da kallo suka bita gaba dayan su,
*************************
“Mai girma mister President ya kamata kayi Magana a bisa harkan tsaron nan, sbda gskya Garuruwan Zanfara, Sokoto, katsina, da Borno, da Kudancin kaduna suna bukatar tsaro, ya kamata a zauna da manya manya na harkan tsaro domin tattauna yanda za’a kawo karshen wannan Abu,
     “To Alhaji Mahmoud sau nawa zan fada maka cewa harkan tsaron nan kullum sai munyi Magana da Minister tsaro kuma yana fadamun Ana nan Ana Samun galaba akan yan ta’addan, to mai yayi saura kuma ko jiya an fitar da Kusan Hundred Billion dollars a kan haka,
    “Mister prisedent for what reason, me akayi da  Hundred Billion dollar, su wa aka ba kudin nan?
“Wai kai Alhaji Mahmoud me kake tunanin ne, duk in nace an fitar da kudi don wani aiki sai ka dunga bin diddiga, ko angaya maka ban san mena keyi bane? Ya karishe maganar yana tashi yana barmai falon,
    “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Allah ka gani ina iya kokarina gurin ganin mun sauke Nauyi talakawan mu a kan mu don Karka kamani da laifi, Allah ka ganar da wannan Bawa naka, niko nace Ameen ya Allah
*************************
Shigowanta Asibitin kenan, ta tanbayi ina aka ajiyeshi, ba wanda ya ganeta kasancewar tasa Nikab, direct dakin ta Nufa, sai ta tarar an rufe kofan an hana shiga wai Waigawa tayi taga ba kowa a gurin kawai ta bace sai gata a cikin dakin jikin gadon da yake kwance ta je ta tsaya tana karemai kallo, a hankali ta yaye Nikab din fuskanta tace mai “Masoyi Aslam ka tashi gani kusa da kai a hankali ya fara bude ido da sauri ya karishe bude ido yana kallonta rufewa yayi ya kara budewa yana kara murza ido kar yazo gizon da ta saba Maine sai yaga ita din ne, gashi tana ta mai murmushi, da sauri ya mike “Mine kece please karki kara tafiya ki barni,
“Wait kana sona dai koh?
       “Yes wlh I so much love you,
          “Ok inada sharadi kuma dole ka bi in har kana so na kasance da kai,
“Ina jinki princess, sai Yaji gaba daya ciwon da yakeyi ya tafi itace matsalarshi kuma gashi ga ta, kuma she promise zata Aureshi in har ya cika sharudanta dole kuwa ya cika ko wani irin sharadine,
“Kanajina koh Sharadina na farko shine✍️✍️✍️✍️
Vote
Like
Comment
Zeey yar mutan zazzau ce luv u too my fans😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
Na kudine please karki min share din Novel luv u too my fans,
*************************
~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM~
15and16
“Kanajina koh?
“Yes I am listing to u Princess,
“Ina son yau dinnan ka koma Nigeria, sannan kuma ina bukatan a gyara Asibitoci guda Ashirin da uku dake cikin da kauyakunka gari a cikin sati biyu, sannan ina bukatar a rabama matasa Motocin Haya da zasu dunga Neman kudi, sannan akwai gyaran titi dake cikin gari da magudanar Ruwa, ina bukatan  gyarashi sannan kuma a samar da bohole bohole na ruwa birni da kauyuka, duk wadannan ayukan inaso ayishine a cikin wata biyu kuma  duk aikin da akayi ina bukatar ka dauki pic nashi ka turamun ni kuma zanje da kaina in tabbatar, in har ka cika wadan nan sharuda na maka alkawari zan Aureka,
          “Ai indai wannan ne sharudanki mai sauki ne, Angama princess ur Comment is my wish, karki damu indai wannan ne,
       “Ok good for u mu hadu a Nigeria yau din na, juyawa tayi ta bude Kofar ta fita, wayanshi ya jawo ya kira pappah, “where are u, please ku hada mana Visa yau zamu koma Nigeria,
   “Aslam kaine kaji sauki ne?
        “Eh pappah na warke oya ka nemi private jet yanzun nan, ok I am waiting,
*************************
A hankali ya bude idonshi ya waiga, kara zaro ido yayi yana kallan inda ta zauna bata ba Alamanta sai murfin motan da yake  a bude, sai Aman da tayi, “oh god ya akayi na bari ta tafine wai, to ya akayi ma ta bude Kofar ta fita, wayan shi ya dauko gaba daya yaji shi Wani iri sai wutar Soyayyar yarinyar da lokaci daya ya cika mai zuciya, kallo daya yayi mata yaji ya kamu da sonta ya Allah ina zan kara ganinta? Daga wayar yayi ya kira cikin second aka dauki wayan,
    “Bringing me New car
Location
Tarauni road opposite Zoo road, yana gama fadin haka ya kashe phone din, yaci gaba da zama yana rufe ido yanajin gaba daya heart nashi na mai Wani irin zafi ga Wani faduwar gaba da yakeji, cikin minti Ashirin aka kawo mai mota basu makullin Wannan yayi yace aje a wanketa shi kuma ya shiga wanda suka kawo mai ya tafi,
*************************
Zaune yake a babban falon ya kurama Kofar falon ido, bai gama kauda kanshi ba aka budo Kofar da sauri ya Mike, ya nufi wanda ya shigo shima wanda ya shigo din da sauri ya kariso suka hade a tsakiyar Falon rungume juna sukayi, a hankali ya sakeshi yajashi zuwa seat ya mika mai d most favorite drink dinshi, karba yayi yana shan drink din yana kallon Abokin nashi duka kuma ba wanda yayi Magana har yanzu a cikin su, niko nace ikon Allah to su wadan nan kurame suka zama ko mene?
     Sai da suka nishadantu suka gama zaman kuramen sannan Saif ya bude baki da kyar kaman bai son yin Magana yace mai”what happen to u dear I see like something happen to u?  Bazaki taba cewa shi yayi maganar ba sbda idon shi a rufe yake kuma yana jingine da kujera bai kalli inda Abokin nashi yake ba,
       “Dear share kawai what about our issues?
“Ok gskya ina bukatan taimakon ka Dear sosai kuma akan Wani Case ne  but, before that na Samu matar Aure fa, da sauri Irfan ya tashi yana bude ido da gaske kakeyi  a ina take? Kaman basu ne suke Magana kamar basa jin yi ba,
    “Calm down Dear let me show ur pic,
*************************
“Ina zaki Diyar Albrka ina zaki ne, “Ummu ina son zanje Wani gurine karki damu Ummu kimun Addu’a, kawai ta juya ta fice mamaki ya kama Ummu, daga jiya zuwa yanzu Sumayya ta canza daga inda ta Santa, Kofar Mudi ta buga da yake cikin zauren gidan fitowa yayi, cikin shirin shi, bazakice Mudi bane don Wani coat ne a jikin shi yaci no respect da Wani Cover baki, da wata sanda a hannunshi ya fito tankar da makaho,
    “Ya to Rabin rai yayi koh?
“Good dan uwa yayi sosai Allah ya bamu sa’a,  suna fita wata mota ta parker✍️✍️✍️✍️
Comment
Vote
Like
Luv you too masoyana
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍
WAZAN AURA PART TWO
Na kudine please don’t share my Novel  love you too my fans
************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
“Yauwa kasan meye munyi Magana da Jaddi jiya ya sanar dani cewa mun kusa barin gurin nan sbda yana bukatar Ganinka, Amma bazamu taba barin gurin nan ba har sai an kamo wata yarinya mai suna Sumayya, A lokacin ne Aikin mu zai fara, Sbda da taimakon ita Yarinyar zamu bar gurin but gskya kuma baza’a kama yarinyar ba sai nan da shekaru hudu masu zuwa, kaga kenan lokacin ya kusa zuwa,
     “Tabbas lokacin ya kusa zuwa yaku Jinsin Aljanu mu kuma gamu bil’ama ai lokaci ne mai tsawo a garemu, “Karka Damu insha Allah zamu san yanda zamuyi mu takaita abun Sbda yarinyar tana bukatan Ilimi kuma fanni uku, shine Jaddi yakeso tayi a cikin shekara hudu da munso ita da yar uwanta ne, to yar uwan nata ta mutu, yanzu ita kadai zatayi karatun a cikin shekara hudu ko shida, sai dai yanda ya kama, mu kuma kafin lokacin zamuyi iya binciken mu don ganin mun san sirrikan su, da Manufarsu  da wanda suke da hannu gurin basu daurin gindi abun da suke aikatawa,
     “Hakane insha Allah zan baki goyan baya dari bisa dari don burina a rayuwa mu kawo karshen ta’addancin dake kasan mu,
************************
Shiga motar sukayi aka ja Motar, ” ina muka nufa? Cewar Sumayya,
     ” Princess  Airport zamuje yanzu yaron Govnor zai sauka shida Ahalinshi, ina son wasan namu ya fara yanzu, “Ok ba damuwa prince,
     “Dan uwa da fatan ka shirya ma wasan don fage ne na daukar fansa?
“Sosai ma ranka ya dade ai a shirye nake da wannan game din,
*************************
Mikewan da zaiyi don dauko mishi pic nata ne, aka kirashi a phone, da sauri ya dauka sbda kiran Mai muhimmacine, “Yes sir ok sir, juyawa yayi yana kallon Irfan da shima kallonshi yakeyi,
    “Dear akwai Wani aiki da mai girma President ya turamu right know, akwai wasu kudaden da mai girma Govnor Lagos yayi sama da fadi dasu, yana bukatan ayi mai bincike sosai anyi aiki da kudin ta inda ya dace ko kuwa, anbi da su ta Wani hanyar,
         “To how about aikin da zamuyi anan?
“Kabar wannan aikin Zan dora Junaid akan aikin I know he is good in job,
     “Ok indai kasan baza’a samu matsala ba ai is ok,
Sun shirya tsaf don bin jirgin karfe biyu zuwa Lagos, Mota suka shiga suka kama hanyar Airport,
*************************
“Mahbub yanzu aikin ka zai fara, Fasihat ke zaki wakilce Sumayya a dukkan fannin karatun da zatayi, a makarantun sbda zuwanta makarantar Hadarine, Sbda inda ake farautar ta A yanzu haka,
     Kai kuma Mahbub duk  Wani karatu da Fasihat zatayi hakkin kane ka koyama Sumayya ta iya sannan fannin Practical dole ku dunga ziyartar Asibitoci da Kotuna don ta dunga daukan Experience, Fannin bincike kuma dole ka koya mata duk Wani fasaha game da bincike, nafi bukatan ta kware a wannan fanni sai fanni Law shima muna bukatan ta kware a kai, bana bukatar A samu akasin hakan, Karka bata mana aiki fa,
      “Insha Allah ya Jaddi komai zai tafi dai dai yanda kake bukata godiya nake ya shugabana,
      “Fasihat”
“Na’am ya Jaddi karki Damu nasan har yau kina bukatan kisan ke Wacece koh? Kar ki Damu lokacin sanin naki ya kusa zuwa, ina bukatar ki tabbatar kin kware gurin harkar kiwon lpy Sosai don cika Wani boyayyen buri namu, kije Allah yayi miki Albrka,
    “Ameen ya Allah Jaddi”
*************************
Kungiyar ne yau ta cika fiye da ko yaushe har wanda bakayi tunanin ganinsu a kungiyar ba yau duk sun hallara,
   Oga Zanjabiluuu ne ya fara Magana
“Yakuu kungiyar Kakkau!!!
“Uhmmm uhmmm!!
“Tabbass kungiyar mu tana gab da durkushewa sbda wata shaidaniyar Yarinya data kusa bayyana wanda zata rusa dukkan Wani ikon ku, da Mulkin ku, tare da hadin gwiwan wasu daga cikin yaranku, Duk Wani buri da kuka dade kuna shiryawa, sai ta rushe shi gashi bazamu taba samu galaba akanta ba har sai an nemo sassan jikin makusancinta kamar kanwarta ko Mahaifiyarta ko mahaifinta ko mahaifiyarta ko yar uwarta,
A halin yanzu mun kasa tantance a Wani gari take da Zama, kuma ya kamaninta yake, in har mukayi kokarin binciko haka, sai muga Madubin tsafin mu na shirin tarwatsewa, Sbda haka kungiya na cikin matsala da Barazana rushewa da tonan Asirin mu, Sbda haka kowa ya zauna cikin Shiri, Don Yarinyar nan tafi Shaidan shaidananci, ✍️✍️✍️✍️
Vote
Comment
Like
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
Na kudine don’t share my Novel please, I LOVE YOU TOO MY FANS
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
19and20
“Fita gasunan sun fito daga Airport din, da sauri Mudi ya fito daga cikin Motan yana dogara sandar shi tamkar da makahon gske Motoci ne sunkai goma suka shawo kwana dai dai Mudi ya shiga tsakiyar hanya, sai da Motocin ya kusa isowa gab dashi kaman an danna musu stop gaba daya suka Wani irin cin birki kuuuuuu kit duka Motocin suka mutu, da sauri su Aslm suka dago don ganin meke faruwa, da sauri drivers din suka fito,
      “Haba Mallam makaho kasan ba gani kakeyi ba ai sai kace a tsallaka da kai, Amma zaka shigo titi kanka tsaye,
   Hajiya Mariya ne da su Aslam suka fito rai bace,
    “Kai Wani irin dakikin makaho ne da zaka shigo titi kamar gidan Ubanka, duk abunda suke fada mai Bai sa ya ce musu kala ba, kuma Bai motsa daga gurin da yake ba, Security ne ya zuciya yaje zai tsinka mai Mari sai ji yayi an rike Hannun shi,
    “Kad ka kuskura ka tabamun dan uwa, gaba daya gurin aka juya Ana kallon mai maganar yayin da ta dage Nikab din da ke idon ta Mamaki ne da tsoro ya kama wasu daga cikinsu,
Aslam mamaki yakeyi yaushe ta iso Nigeria, Ikram da KB da Excellency kuma tsoro ne ya kamasu don bazasu mance wannan fuskar ba, inda ita kuma Mammah taji duk duniya ba yarinyar da take so sai Wanna kyakyawar yarinyar don daga ganinta zatayi dadin harka,
Shiko Security Musa mamaki ne da tsoro ya bayyana a fuskarshi don bazai mance da fuskar nan ba yarinyar da tayi mai daurin goro har cikin dakin barcin shi ta kuma kusa illatashi,
Wani dogon tsaki da taja ne duka ya dawo dasu daga duniyar tunanin da suka tafi na wucin gadi, kamo sandar Mudi tayi suka juya suka tafi suka barsu tsaye nan cirko cirko da yake hanyane ba wanda aka cika wucewa ba shiyasa har suka gama abun su ba abunda ya gifta ta gurin, sai da su Mudi suka bar gurin ne kowa ya koma Mota, kowanne da tunanin da yake sakawa a ranshi,
“Wash wlh ganin su da security da bindigogi fa na tsorata yar Uwa kawai da security nan ya daga hannu zai mareni shima kawai na sadakar jiran saukar Marin kawai nake jira,
😂😂dariya Sumayya da Mujaheed suka fara mishi harda rike ciki, tsayawa yayi yana kallon su don tantance Wanne dariyan yafi mishi kyau cikin su biyun,
     “Haba dan uwa ina zan bari haka ya faru, to baka ji tsoro ba lokacin da Motocin suka doso ka a guje,?
“Kai wlh shima naji tsoro har da Wani zufa da yake keto mun, dariya suka kara mai, gyaran murya Mujaheed yayi duka suka natsu suna jiran jin me zai ce,
      “I hope aikin mu yayi kyau, Kin tabbatar duka sunyi mamakin ganinki koh, ya bayanin Mahaifiyar tashi, kwadayinta ya fito fili na sani,
   “Sosai ma kuwa don duk sun rude har kanwarshi din nan da ita da Maman tasu sun ma fi rudewa,
“Ok gud wasa ya fara muje zuwa, da sannu zamu cimma burin mu,
*************************
“Haba Alhaji taya zaka ce wai hankalin mu zai kwanta kasan inda ake ganina da kima da mutunci a Mazaba na, in har Asirin kungiya ya tonu tamkar da tonuwar Asirin mune fa, Ni na fara tunanin in fita kungiyar sbda in har bazata iya bamu kariya ba da dukiyar da siyasar mu, da mutuncin mu ba, Banga Anfanin ta ba,
   “Kai kasan ne kake fada kuwa Alhaji Idi kamance dokar kungiya ce in an shiga ba’a fita, sannan ba aibanta kungiya in ba haka ba fushin kungiya ya sauka a kanka,
************************
Sun isa Lagos da Yamma, shiga yayi tamkar da mahaukaci ya ce to dan uwa Nayi gaba, shikuma kayan yankan kunba ya dauka Irfan duk suka tafi suna ma juna fatan Alheri,
Dai dai gurin dan dazon wasu mutane yaje yanata tsince tsince yana yan suratai kace mahaukacin gaske, Mutanen suko sai hiransu sukeyi yawancin hiran nasu da broking English sukeyi, kasancewar dama Lagos sun fi Anfani da irin Wannan turancin, kun san Mai girma shugaban kasa ya fitar da miliyoyin kudi don gyaran gadan da yake anbaliyan ruwan nan, “to ai kai baka sani ba kwaskwarima kawai akayi ma gadan kaga shekara mai zuwa sai ya kara rushewa, sai a kara fitar da Wani kudin,
   “Kai talaka bawan Allah rijiya ya bada ruwa guga ya hana ina laifin ma su dan gyara, kai talaka bawan Allah, Allah dai ya kawo mana karshen wadan nan shuwagabanni,
“Ameen yoh, shi dai Saif na jinsu kuma yana record a recorder nashi da yake makale a kanshi,
*************************
“Wai Ana sallama a Kofar gida inji Ustaz Mansir, da sauri Ummu ta mike tana kallon yaron”jekace mai ya shigo, ✍️✍️✍️
Thank you 😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
Na kudine don Allah don’t share my Novel my fans luv u too.
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
21 AND 22
Da sallama ya shigo gidan, Ummu ta dago kai tana kallan shi, nan da nan hawaye ya fara zubo mata ba abunda ya fado mata a rai sai Wasiyar Maryama, “Ummu duk randa Ustaz Mansir yazo ki fadamai ina sonshi kar ya manta dani.
   “Zauna mana Mallam Mansir, Zaunawa yayi yace “ina yini Ummu ya bayan rabuwa?
“Lafiya lau Alhmdulillah Mallam Mansir ya’akayi ka gane gidan da muke?.”
“Naje can gidan ne ban sameku ba a kacemun kun tashi shine wani makocinku ya rakoni.”
“Ayyah wlh kuwa mun tashi mun dawo nan”.
“Ummu ina su Mutumiyata ne Maryama da Sumayya? Nayi kewansu sosai wlh.
  Shiru Ummu tayi na wani lokaci take damuwa ya bayyana a tare da ita,
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta fada mai, yayi jimami sosai, sannan ya tanbayeta yanzu ina Sumayya tace ta je Unguwa Amma tasan yanzu haka suna hanyar dawowa, bata gama rufe baki ba taji Sallaman su ita da Mudi.
    “Yauwa kaga ma gasunan sun dawo.
“Kai Ustaz Mansir kaine a gidan namu tana fadin haka tare da yaye Nikab dinta tana zama kusa da Ummu, yayin da Mudi ya dauko kujera dan tsugune ya zauna.
Mika ma Ustaz Mansir hannu yayi suka gaisa, itama Sumayya ta gaidashi, bayan haka ya kara musu gaisuwa rashin Maryama, sannan ya fara maganar Abunda ke tafe dashi.
   “Dama nazo ne game da karatun su Sumayya, ga result nata An Sama mata Admission zata tafi Egypt karatu, A fanni Law  insha Allah Ummu zaku tafi tare, an riga an gama mata Visa da komai da komai yanzu saura naki Ummu.
    “To gskya  banki taka ba gaskiya bazamu iya tafiya mu bar Mudi ba, shima yana bukatar mu, Muma muna bukatar shi, Saboda yana da kyau duk inda kake ka zauna da Namiji saboda halin rayuwa.
“Hakane Ummu maganarki gskya ce,  to shin shi yayi  karatu?.
“Eh nayi Amma iyakata Secondry School, kuma result dina yayi kyau Sosai.
“To masha Allah zan fadama mai gidana in yaso sai a saman maka gurbin karatu a fannin jami’in tsaro na sirri saboda a cikin tafiyar mu muna bukatan hakan, dole yanzu za’a canza Visa a sake Sabon shiri, insha Allah nan da wata daya zaku tafi, ga Number wayata nan zamuyi Magana duk abunda ya kama.
   “Ustaz Mansir ai bamu da waya yanzu, Sumayya da tun lokacin da aka fara Magana bata ce komai ba sai yanzu.
   “Ok ba matsala ga phone dina ku rike a hannun ku, duk abunda ake ciki zan kiraku.
   Ummu ce ta fashe da kukan farin ciki, “Ashe da rabon zan kara Zuwa Mahaifata, Ya Allah Alhmdulillah, Inama ace Sahibul Hayati kana raye, gaba daya tsayawa sukayi suna kallonta suna jin Mamakin kalamanta don basu san inda zancen nata ya dosa ba da sauri ta goge hawayenta tare da waro ido Alaman bata san maganar da take a zuciyar ta ya fito fili ba.
  “Ummu wai me kike cewa ne?
 “Ba komai yar Albarka farin ciki ne Yasa fadin Abunda ban san me nake cewa ba, ita dai Sumayya jin Ummun nata kawai tayi domin bata yarda ba kuma tayi alkawarin sai ta binciko gaskiyar maganar, Haka dai ranar suka wanzu cikin farin ciki, bayan tafiyar Ustaz Mansir ne, Mudi ya tafi gidan su don sanar da Guggon Hansai Abunda ke faruwa.
*************************
“Ammy Nayi farin ciki Sosai da Abbi ya Amince da tafiyata zuwa Egypt karatun nan, Ana jalasa fi Baiti Ummity Halima, kai Ana fi shukrallahi ya Ammyt.
Murmushi Ammyt tayi tace, Uskut ya Habibaty Hairan, turo baki tayi hadi da cewa, kai Ammyt baki farin ciki bane, da zakice inyi shiru.
    “Lah ya Habibaty Hairan kawai dai zanyi kewarki ne shiyasa, wani Course ma kike so?
  “Ammyt Shari’a Law mana, har kin manta Best Daras nawa ta fadi hadi da juyawa Mahaifiyar Baya, Alamun fushi.
    “Haba ya Jamilaty, Habibaty Hairan lah tagadab ni, tana fadin haka hadi juyo da ita gareta, rungume ta tayi, Hadi da cewa “Ana Asfun ya Habibaty, dariya tayi inda kyawawan hakoranta suka bayyana, hadi da dimple nata, tace “Ana Ahabbaki ya Ammyt, “me too ya Habibaty.
Kuyi hakuri fa iyayi irin nawa larabcin nan ba iyashi mukayi ba, in kun ga ba daidai ba ku gyaramun😂🙈.
*************************
“Momsy Ankusa komawa School fa, kuma har yanzu Dad bai ce komai ba.
    “To in banda abunki Jidda ko yau kuka tashi komawa school kun san baku da matsala akwai private jet da zaku tafi a ciki.
     “Hakane Momsy wai pretty ina taje ne? Don taga ba Yaya Irfan shine har ta samu kafar yawo ko?.
    “To ko yana nan ma ina ruwanshi ai na riga na fadamai ya fitamun harkan yara, har da ubanshi na hadashi, in ba haka ba kuma in tsine mishi yabi duniya ehe!!.
    😂😂😂”kai Momsy kin mana dai dai Wallahi duk yabi ya takura ma rayuwar mu, Muna Yaran shugaban kasa bazai barmu mu wataya ba, ya dunga takura mana thank you Momsy, kina wuta muna binki da petur, give me five, tako miko mata Hannu suka tafa, niko nace anyi Asara wallahi.
*************************
“Lokaci yayi da zamu fara bincike game da waddan nan takardun da suke Hannu Oga miko, ranka ya dade.
“Gaskiyanki Zankadaziyyatu, yanzu ta ina Zamu fara? “Eh zan yi Magana da Jaddi a daren yau Insha Allah, “to shikenan duk abunda ake ciki sai ki fadamun, “ba Matsala.
*************************
Kas kas kas “mai yankan farce Come and cut my nail woo, “Ok sir karisowa yayi, ya fara yanke mai inda suke cigaba da hiransu,   “Ojo ni kasan me ke bani Mamaki?  Wanda aka kira da Ojo yace “sai ka fada Ojojuwa, “wai jiya mun fita da mai girma Govnor kasan ina mukaje?   “A’a”
“To Hotel nashi mukaje ya ba wata karuwa nashi kwangilan gina gidan karuwai da kudin da gwamnatin kasa ta fitar don gyara Babban Gadan Sama da ke Main road na Lagos, “Oh our Country what wrong with our Leaders ne wai?  Kai god change our  leaders, “Ameen woo, “why did u give her Advise?  Zaro ido yayi, “are u Mad Ojujuwa, u forget I am only Govnor Driver ne fa, ni a waye, so kake in rasa aikina? Tab, ina I love my work, is d only way I have to Support our Family woo, “sir na gama,  “ok ya zaro Two Hundred Naira ya bashi, “Thank You sir, ya tattara kayan yankar kunbanshi ya tafi,ya cigaba da Kas, kas, kas.
***********************
Ku cigaba da bin yar mutan zazzau ce ✍️✍️✍️✍️✍️
Luv you too masoyana 😍😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
INA BAKU HAKURI MASOYANA NA JINA SHIRU DA KUKAYI DALILIN JARABAWAR DA NAKEYI BUT INSHA ALLAH ZAN DUNGA KOKARI INA SAMU INA MUKU POSTING KO SAU DAYA NE A WEEK KO FIYE DA HAKA INA SONKU DAGA YAR MUTAN ZAZZAU DINKU NE😍😍😍
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
23 AND 24
“Yauwa Jaddi maganar takardun da ke gurin miko wanda suka Amshe  a hannu Ranka ya dade ya za muyi gurin Amso su.?
    “Yauwa batun takardu dole zaki shawo kan na hannun Daman shi din nan don ya san komai game da takardun.Ki tabbatar kin samu bayani akan takardun.”shikenan angama.  Tashi tayi tare juyawa.
************************
Kwanci  tashi ba wuya a gurin Ubangiji yau wata daya kenan da maganar tafiyar su Sumayya Egypt inda duk wani shiri da ya kamata su yi sun kammala komai Duk sun gama sallaman makota Shima Mudi ya gama sallaman danginshi gobe in Allah ya kaimu zasu daga zuwa Egypt, “Ummu wai yanzu mune zamu hau jirgi Zuwa wani kasa.  Kai Alhmdulillah ba-abunda za muce ma Su Ustaz Mansir sai godiya. Ta fadi haka hadi da Nuna farin cikinta bayyane a fuskanta.
“Ai koni Ummu ban taba tunanin haka ba a rayuwa ta wai wa yaga Mudi a jirgi.?  Sai kuma ya bata rai farin cikin da ke fuskar shi ta bace, “lafiya dai Rabin jiki dan uwa.?  Sumayya ta tanbayeshi, “na tuna da Maryama Sarauniya ce da yanzu tare zamu tafi gurin nan. “Hakane kam Rabin jiki dan uwa.  haka suka Zauna sukayi shiru shiru.
*************************
“Ya za’ayi ace duk kudin da Gwamnati take tura muku bakwa abun da ya dace ne? Iyeeh yaushe rabon da ace Boom ya tashi, yaushe rabon da ace kun tashi gari duk irin kayan aikin da kasashen da muke hadin gwiwa da su gurin yada ta’addancin nan suke turo muku?  Haba kuna nufin Jami’an tsaron mu sun fiku karfi ne ko sun fiku Makamai ne iyeeh tell me?!!!. Ya karishe maganar cikin fushi.
Duka kansu na kasa ogan ne ya fito tsakiyar gurin hadi da gyaran murya zaiyi magana:
“Ranka ya dade gaskiya akwai Matsala don wallahi gaba daya an samu rabuwan kai tsakanin mu da yan uwan mu na garuruwa. Ni ban san meke shirin faruwa ba gashi gaba daya yanzu mun kasa fita Operation ko mun fita ba wani nasara. “To Ya Maganar Mutumin nan na kasar Egypt wanda suka bamu Contract a kanshi.?  An samu takardun dake hannun nashi? Sannan dole yanzu ku san yanda zakuyi ya farfado don muna son Karin Bayani game da takardun. “An gama ranka ya dade. Niko nayi iyaka kokarina don ganin waye wannan mutumin Amma na kasa gane shi Reader may be ku ku gano mana ko waye shi😂.
*************************
“Son wai me ke damun ka ne ance ma Soyayya hauka ne iye? Da zaka dunga dibar mun kudade kana almabazzaranci dashi da sunan yima talakawa aiki wa ya fada maka Talakan Nigeria nada yanci iyehh?!!!  Ya karishe maganar shi cikin fushi kamar Zai bugi Aslam, shiko Aslam kaucewa yayi hadi da cewa “Pappa ya za ka zo kana mun shouting a kunne.  a tuna nina kudin nan dama na talakawan ne mai ye Anfanin su ai musu aiki dashi. Saboda haka wlh sai anyi in kuma ka ta kuramun zan iya batar da kai.  ya fadi haka hadi da mikewa yai ficewar shi, ya bar Excellency a tsaye da Mamaki a fuskanshi wai yau shi dan da ya haifa yake cema Zai batar dashi Tabbas gata mugun ciwo ne, Zama yayi dabas a kujerar da ke falon duk da Ac dake Falon bai hanashi yin Zufa ba.
*************************
“Ikram dole ki bani hadin kai fa in ba haka ba burinki bazai taba cika ba. “Haba Mamma ko da nake Son Saif Bazan taba iya aikata Lesbian akan shi ba. Lesbian din ma da Mahaifiya ta Abun yayi muni kuwa. Ta karishe maganar ta hawaye na zubo wa a idonta, jikin Mamma na rawa ta jawo ta jikin ta rungume “kiyi Hakuri Ikram wannan abun taimakon juna Zamu yi ni da ke burinki Zai cika nima nawa zai cika. Ta karishe maganar tana kokarin yaye rigan da ke jikin Ikram din, tunkude ta tayi Ikram din hadi da cewa “tirrr da halinki Mamma kinyi Amai kina so ki lashe walahi burinki ba Zai cika a kaina ba. “Wlh ke baki isa ki hana burina cika ba Ikram ko ta halin yaya sai na cika burina a kanki. Wani abu kawai ta danna sai ga wasu Mata sun bayyana, Nuni kawai tayi musu da Ikram din suka Nufeta suka rirrike ta, ko motsi ta kasa dariya Mamma ta fara yi sai da tayi mai isar ta sannan ta taso tazo har gaban Ikram data runtse idon ta tana jin wani zafi a ran ta wai Mahaifiyarta ne zatayi rapping nata, maganar Mamma ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi”Yarinya man kaza ke a tunaninki Mariya zata Nemi abu  ne ta rasa.  To bari in fada miki abunda baki Sani ba ni ba Uwar ki bace Aslam shi kadai na haifa ke Yar kishiya tace da na dade da kashewa saboda mu bama zama da kishiya ni nasa Aslam ya lalata ki ya mai dake tamkar Matar shi, kinyi tunanin ban san me kuke aikatawa bane to ina sane, Asali ma ni na sa shi, an fada miki a banza nake Zaune da Excellency dole yanxu in cika burina a kanki na dade ina kwadayinki sai yau na samu sa’ar ki. Ku farke mun rigarta haka Ikram tana ji tana gani sukayi badala da ita daga Hajiya har wannan Matan sai da ya kasance ko Numfashin ta da kyar yake fita sbda Azaban da tasha a gurinta suna gamawa Mamma ta fesa mata wani Abu sai barci ya dauketa.  gaba daya suka kwashe da dariya😂😂”sai ke Hajiya shugaban Madigo.
Comment
Vote
Like
Please
Luv you too my fans
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
WAZAN AURA  PART TWO
25 AND 26
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
—————-Sun isa Airport da karfe takwas na safe jirgin su Zai tashi karfe takwas da rabi, A can suka tarar da Ustaz Mansir duk wani shirye shirye da ya kamata matafiyi yayi duk ya kammala musu, tafiya kawai ya rage musu. Gurin da aka ta nada don Zaman fasinja suka Nufa suka Zauna wannan shine karon su na farko da suka shiga har cikin Airport, Zaman su da mintoci a ka fara kiran su, bayan duka fasinja sun kammala shiga jirgi, jirgin su ya daga sai Egypt. Sai mu Allah ya kai ku Lafiya Su Ummu.
************************
“Inna lillahi wainna ilaihirraji’un!!  gasu nan fa sun shigo garin masu garkuwa da mutane ne yau ma sun kara kawo ma kauyen namu hari ne? Bai gama rufe baki ba ya ji Saukan bindiga a kanshi gaba daya Mutanen da suke rumfar mai shayin ne suka tarwatse kowa na gudun ceton rai, haka garin nan suka kwana cikin tashin hankali da kashe kashe anyi waya an fada ma Jami’an tsaro Amma basu ba labarin su. Kura bata lafa ba sai da gari ya waye sun kashe na kashe wa sun dibi na diba, Wani abun takaici sai da suka tafi ne
sannan Jami’an tsaro suka iso k’auyen inda yan kauye suka dunga jifan su, suna fad’in musu basu da Amfani.
“A daren jiya ne Masu garkuwa da Mutane suka shiga wani kauye dake kan iyakan Zanfara da katsina, inda suka kashe kimanin mutane Hamsin da biyu suka raunata mutane da dama inda su kayi garkuwa da Mutane. Mai magana da yamun Jami’an tsaro shiyar Katsina ya fad’a mana cewa insha Allah suna iya bakin kokarin su gurin an kawo karshen ta’addanci da ya addabe Al’umma kasa. Karshen labaran kenan.
“Aikin banza kullum Maganar kenan Amma an kasa kawo karshen Abun”wani matashi ya fada a dandalin su da suka Zauna, “Haba Danlami ku daina dora Alhakin Wasu abun akan shuwagaban nun mu fa, Muma harda halin mu yake ja mana,”. “Dallah ga fara Hashimu su waye suka jefa kasar ta mu a cikin wannan halin in ba shugaban nin na mu ba shegu matsiyata Allah ya isa tsakanin mu dasu, Haba Dallami a matsayin ma na mai hankali bai kamata muna zagin shuwagaban nin mu ba Addu’a ya kamata muyi musu don in muna tsine musu kara tabarbarewa sukeyi, kuma mu zamu ji a jikin mu,”.  “Sai kaje kayi ta musu Addu’a don wlh nidai bazan ce Allah ya shirye su ba, in Allah ya shirye su duk wahalar da suka bamu sun ci banza kenan kai ina!. Ya fadi haka tare da mikewa “na barku lafiya”haka dai matasan suka tashi daga Majalisan Baram Baram saboda sabanin ra’ayi.
*************************
Sun sauka Egypt karfe hudu na yamma.  inda suna sauka wani yazo ya domin daukansu  rufe ido Ummu tayi ta bude tana Mamakin wai ita ne yau a Wata Kasa, gaba daya Sumayya da Mudi sun zama yan kauye har Ummu ta fisu rashin kauyan ci, Sauri takeyi tana ta waya cike da shagwaba, yawanci da Larabci take Maganar tana hadawa da Hausa kadan kadan, dai dai Sumayya ta dago kawai sukayi karo da juna, “Wayyo Dallah! Malama bakya gani ne?.  Sumayya ta fadi haka ga Hairan, dago dara daran idon ta tayi ta dorasu akan Sumayya ji tayi gabanta ya fadi ita ko a ina tasan fuskan nan… “Dallah Malama ina magana kin wani kureni da kwala kwalan idon ki ta fadi haka cikin takaici da irin kallon da Hairan take mata, dariya Hairan din tayi “Sorry Aunty Masifa wannan irin Masifa, ni ban lura da ke bane kiyi hakuri bye see you later”. Ta fad’i haka had’i da daga mata hannu ta wuce ta tafi dai dai karisowan su Ummu da Mudi da suka je gurin kayansu, yadai Rabin rai na ganki haka?” Kakalo Murmushi tayi ta ce musu ba “komai mu tafi ko?.  Driver ne ya kariso ya nuna musu ID card nashi sannan ya kwasan musu kaya ya sa musu a Mota sai gida.
*************************
“Yauwa president Maganar komawar su Jidda makaranta kasan yau ya kamata su koma kasancewar baka a kasar ne, kuma Irfan baya nan yana Lagos shiyasa basu koma ba.   “Ok gobe in Allah ya kaimu sai su shirya su tafi da Yayan nasu don Zai je wani aiki Shima A UK.
     “Uhmm nace ba Daddy mai Zai Hana kayi ma su jidda Aure, Sannan karatun nan su dawo gida Nigeria suyi shi, kaman zaifi na gani koh?.  Ko gama rufe baki baiyi ba Momsy ta taso mishi “to dan bakin ciki wallahi ka fita ido na in rufeka, ba wanda ya isa ya Aurar mun da yara kuma makaranta baza su yi a Nigeria ba, Suna yaran shugaban  kasa guda ai sun wuce haka. Ta karishe Maganar tana haki kasancewar tana da Asma. “Haba Hajiya Haulat meye na daga hankali a Maganar Irfan daga bada shawara kina neman ki tado ma da kanki Ciwo… Son Karka damu zan duba abunda ya dace. Tashi Irfan yayi ya bar cin Abinci da yakeyi yayi gaba, “to wa ka barma Abincin da kaki ci? Kasan dai baso nake ka dunga Zama da yunwa ba!  “Eh banci ya isheni ya bude fallon yayi ficewar shi, “yanzu Alhaji kana ganinshi ya fita bai fa ci komai ba!. “To Hajiya ya kike so inyi mai kin san halin Irfan sarai in a ka bata mai rai. “Yanzu Alhaji meye abun bacin rai a cikin na, shikenan ai cikin shi.
*************************
Isan su gidan an gama komai har abincin da zasu ci nan da Next week zasu fara attending School a cikin satin ake so su iya Mota shi da Sumayya don har an tanadi mai koya musu, kuma an ajiye musu Motoci Biyu wanda zasu dunga zirga zirga, bayan kowa ya shiga dakin da ya zama mallakinshi sunyi wanka sun shirya sun fito domin cin abinci. Bayan sun ci abinci ne suka Zauna Mudi ya fara Zuba, “kin san wani Abu rabin rai?, “a’a sai ka fada rabin jiki dan uwa, “wallahi lokacin da muka shiga jirgin nan Zai tashi kaman zanyi fitsari a wando don tsoro, 😂dariya Sumayya ta fara “kaga ni wallahi komai banji ba, Ummu ne ta katse musu hiran da ce musu “ku tashi kuje ku kwanta dare yayi gashi gobe in Allah ya kai mu zaku fara koyan Mota, kowa yayi Addu’a kunji yan Albrka. “To Ummun mu Uwa ta gari✍️✍️✍️.
Comment
Like
Vote

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements