WAZAN AURA Page 41 to 50 (The End) » Naijagisthub

Advertisements

Home / HAUSA NOVELS / WAZAN AURA Page 41 to 50 (The End)

WAZAN AURA Page 41 to 50 (The End)

WAZAN AURA Page 41 to 50 (The End)

Sallama akayi hadi da knocking, Ummu ce ta fito daga daki taje ta bude Kofar, “a’a Ustaz Mansir kai ne a gidan namu… Sannu da zuwa shigowa yayi ya zauna suka gaisa da Ummu sannan yace “Ina yaran naki suke?”    “Aikuwa sun fita koyan tukin Mota ” ok dama makullan sauran Mota ne guda biyu na kawo musu daya nata daya nashi wanda zasu dunga zuwa Makaranta, “Allah ya saka da Alheri ya kara budi ya rufa Asiri duniya da lahira “Ameeen ya Allah Ummu ni zan koma sati mai zuwa zasu fara zuwa makaranta ita zata karanci fanni shari’a shi kuma fannin jami’in bincike, “to Allah ya taomake mu. Ameen ya Allah ya Amsa hadi da mikewa don tafiya Ummu ta rako shi har bakin gate din gidan.

*************************
Zankadaziyyatu yau ta gama duk wani shiri da ya kamata suyi ita Bawan Allah da ke gurin yan garkuwa da mutane akan yau zata dauke su gudo saboda duk wani sirri da binciken da suke bukata sun sameshi, sai dai abun da ba’a rasa ba domin har takardun nan yana hannun Zankadaziyyatu. “Ranka ya dad’e shugaba tashi nice, da sauri ya tashi daga kwancen da yake “yauwa kaga takardun da nake fada maka Duk sun kammala, Saboda haka yau zamu bar gurin nan karfe ukun dare ka zauna cikin shirin ka komai ka gani Karka ji tsoro. “Ba matsala duk yanda kika ce haka za’ayi.
*************************
Preety da Jidda yau sun sauka a UK  dai dai lokacin da Fasihat ta sauka tasha wasu riga da wando pencil inda ta sa wani black glass da ya kusa rufe mata face  da Ear piece a kunninta tana taunar cewgum tana jan trolley din ta dai dai tazo kusa da su Jidda wani kura ta tada kafin ta iso gab dasu duk da gurin ba kuran fes fes yake kowa yayi mamakin daga ina kuran ya taso sai a kan fuskan su Jidda da suke tsaye suke jiran Driver su ya iso.  A fusace pretty ta juya “wannan wani irin iskan ci ne za…. Kasa karisa Maganar tayi saboda wani irin kallo da Fasihat ta bita da shi ta kada mata hannu gaba daya ta tafi da Imanin ta bata san lokacin da ta furta “Wowww!!”   “Dallah malama in kin gama banzan cin da zubar mana da aji kizo mu tafi. Jiddah ta fadi haka had’i da fincikar Hannun Pretty suka shige Mota. “Jiddah kinga kaya kuwa ai dole in samu Yarinyar can don zatayi dadin harka.ta karishe fadi tana kashe ido hadi da lashe baki. “To banza yar akuya wai yaushe zaki daina wannan Akuyanci Iyeh?, ni wallahi Banga abun sha’awa a jikin yar uwata mace ba, “eh naji,  Dadin Abun dai bana shan komai koh. Ta karishe Maganar hadi da ballama  mata harara, ai wallahi gunda inyi Shaye Shaye sau dubu da inyi Madigo. “Naji din kiyi rayuwar ki inyi nawa ina ruwanki iyehh ta fadi haka cikin masifa har sai da driver yaja birki, Haka suka dunga Masifa har suka iso gidan su kowa tayi hanyar d’akin ta.
*************************
“Mommah ina jin yunwa fa”ok my daughter bari insa a kawo miki abinci ya jikin naki? “Da sauki to, Yauwa taso ga abincin can a dining area jerawa sukayi suka isa Dining din suka zauna tana bata Abincin a baki har ta koshi ta kwantar da ita a jikin ta tana ta shafata kyace lallashin  ta keyi ita ko Mommah manufar ta da ban, yanzu  gaba daya Ikram ta zama sai yanda Mommah Aslam sukayi da ita Mommah ta huta da ita da Safe kafin ta fita shi kuma Aslam ya kwana da ita a dakin shi duk ta rame, gashi bata son abunda suke aikatawa da ita Amma bazata iya musu Magana ba kuma bazata iya fada ma komai ba, ko Pappah ya tanbayeta meke damunta sai tace ba komai sai ramewa takeyi gashi Mommah bata barin ta tayi sallah tana son yi Amma ba hali.
*************************
ONE WEEK LATER
EGYPT
“To Ummu mun tafi sai mun dawo to yan Albrka Allah ya taimaka ya bada sa’a. Amsawa duka sukayi da “Ameen ya Allah suka fita kowa ya shiga motar shi. Sai Makaranta. Sun fara lecture inda Class din su Sumayya ya kasance daya da Hairan, inda Hairan tunda ta ga Sumayya taji ta burgeta kuma tanajin wani abu game da ita Saboda Tana mata kama da wata Amma ta rasa dawa take Kama. Yayi da yan Class nasu sukeyi musu kallon yan uwa saboda kaman da sukayi Sai dai ita Sumayya fara ce yayin da Hairan take black beauty. Haka Hairan dai ta dunga bin Sumayya har sai da suka zama friends gashi duk Department din nasu an sansu suna kawo light sai daga Baya Sumayya ta gane cewa Hairan Ashe yar mataimakin shugaban kasa ne taji Mamakin rashin girman kanta. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya a Egypt.
    “Kai Ummu zan iya wannan karatun kuwa?  “Haba rabin jiki dan Uwa Karka bada Maza mana. Dariya Ummu ta kwashe dashi “a to kadaiji yar uwanka ma ta fadi balle in fada kumin taron dangi. Turo baki yayi hadi da cewa “kinga kin sa Ummu tana mana dariya koh!  “Sorry my sweet rabin jiki nifa wasa nakeyi ma. Tashi yayi ya tafi d’akin shi ya bugo kofa da karfi Alamun yayi fushi, da sauri ta tashi ta bishi tana cewa “kai Ummu kinga kin hadamu koh? “Ni ba ruwa na kinga ni in tashi ma inje in dan mike kafin lokacin sallah yayi. Zuwa bakin Kofar tayi tana ta bugu tana bashi hakuri akan ya bude Kofar yaki budewa.
**********************”**
Sun samu sun fita lafiya kalau inda suka isa birnin MISRAH a cikin dare. a lokacin Ana tsakiya da fadanci. Da sauri Jaddi ya mike ya kariso gaban su ya rungume mutumin Marhaban bika ya kai D’a na Tabbas yau wani yanki daga alkawari na ya fara cika Kwanan nan sauran Burina zai cika Tabbas sai na damka masarautan ka a hannunka Ahalinka zasu dawo gareka komai zai Zama tarihi a gareka.
*************************
“Hello Abokina kana ji ko Komai yana tafiya yadda muke bukata yanxu haka ma muna Egypt tare dasu.. Eh har da Ummu ma haba dai Abokina kar ka damu muna tare ai Hhh kasan nace Sunana Mudi ne but daza’a samu Makarantar nan na fadi ainihin suna na Mahmoud.
Like
Comment
Vote
Zeey yar mutan zazzau ce 😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
29 AND 30
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
“Kun san abunda nake bukata ina son a kawo mun Yarinyar nan fa da Aslam yake so…. Saboda yan zu duk kwadayi na da target dina akan ta yake.
   “Gskya Hajiya ni banjin Yarinyar nan suna garin nan ma saboda munje gidan su yafi tashi hudu  gidan a kulle. Kuma munyi iya kokarin gurin sanin inda suka je bamu samu mun gane hakan ba.
      “To yanzu meye Nufinku kun san ni ban taba Neman abu a duniya ban samu ba ta karishe fad’in haka tana danna wani kofa ya bud’e ta shige abun ta.
    “GB gaskiya na gaji da bautan Sab’a ma Allah mu kawo mata yaran mutane ta lalata Shima Mijin ta mu kawo mai yaran mutane Maza ya lalata, shin ya makomar yaran mu Muma wai kuma duk saboda duniya suke wannan abu Allah yayi wadaran irin Wannan Zuri’a  kuma wai sune shuwagabanni mu😭.
     “To ya kake so muyi TK Sai dai kawai Allah ya yafe mana.
*************************
“Wai me kuke Nufi ne!?  Ya za’ayi ace wai an neme su an rasa duk kuna aikin me da zasu gudu banzaye kawai dabbobi kun san wannan guduwan da sukayi mai zai jawo ma kasar nan to rigima ce zai faru bama iyakan kasar nan ba har da wasu kasashen, kun san waye wannan mutumin kuwa?  “Oga sun fa dauke takardun nan sun gudu dashi. “What!” Sun gudu dashi zufa ya fara karyo mai.
*************************
UK
lecture akeyi a Class lokacin da Pretty ita kuma gaba daya hankalin ta na kan Fasihat da tasa wani Mini skirt da wani riga ko cibi bai rufe mata ba kuma rabin Nonuwan ta duk waje suke, ta tufke gashin kanta ta gefe ga wani uban takalmi hill da ta sa. Sai kad’a  kafa takeyi gaba daya ta tafi da Imanin pretty har ta fara tunanin gata suna tare suna aikata Less. Har a ka gama Lecture din pretty bata fahimci komai ba. Da sauri ta bi Fasihat tace mata”Hi” Sai da ta kare mata kallon Sama da kasa sannan ta yamutsa fuska tayi gaba abunta. Wannan shine first Time da wata ko wani ya wulakanta ta a gaban jama’a ga mutane an taru wasu ma dariya suka kwashe mata dashi.
*************************
EGYPT
Da sauri ya maida wayar da ya dauko Cikin wata jaka karama ya kara turashi cikin kasan drawer shi saboda buga Kofar d’akin nashi da akeyi, “kai Rabin jiki dan uwa wai me kakeyi ne a dakin eyeh? Ni wallahi na gaji in bazaka rakani bane in hakura. “Haba rabin raina kiyi hakuri ga ninan zuwa. Ya fito yana hada Hannun shi  Alaman ban hakuri juyawa tayi tana zunb’ura baki ta tafi ya bita “Sorry Baby Ummu”da sauri ta waigo tana hararanshi sai kuma ta tsaya tana kallonshi gaba daya taga ya Canza kaman ba Mudi ba ya kara kyau sosai, Shima kallon nata ya tsaya yi ta kara kyau sati biyu kawai da zuwan su lallai komai nasan hutu. Gashinan ta fito Sak balarabiya. “Fitowar Ummu ne ya katse musu tunanin su. “Wai bazaku zo ku wuce ba, kun san ban san ku kai Dare kasa ba namu ba”  “to Ummu ba Rabin jiki dan uwa bane ya ke ta bata mana Lokaci”
      “Ba waninan Ummu bani bane fa, “ni dai naji ku wuce ku ban guri Sai kun dawo Allah ya tsaremun ku. “Ameen ya Allah Ummu bye.
   “Tafiya sukeyi suna hira a cikin motar su gwanin sha’awa har suka isa gidan su Hairan wannan shine karon farko da zuwan ta gidan,  yayin da Hairan tazo yafi sau uku gidan su, gori tayi mata akan cewa bazata kara zuwa gidan su ba in bata je nasu ba. Shine fa yau suka shirya suka je gidan. Nocking tayi hadi da Sallama bude Kofar a kayi ai Da gudu Hairan tayi Tsalle ta rungume ta hadi da kwala kira “Ummy ta’al ilah huna Sumayya fi baity! Da sauri matar ta fito daga kicin rike da Seving spoon a hannun ta Cak Sumayya tayi ganin wata Mata mai Bala’in kama da Ummun ta. Itama matar tsayawa tayi tana kallon Sumayya.
*************************
“Daddy yau ina son zan tafi UK don akwai wani aiki da zanyi a can,”
  “Ok daga nan kaje ka dubo kaninka a Makaranta.
“Eh dama Daddy zanje sai dai banso ka fada musu zanje Kaji Daddy please 👏. “Karka damu bazan fada musu ba ko Momsy dinku ma bazata ji ba, balle ta fada musu.
“Tare da Saif zamu daga nan zamu wuce Egypt mu dubo Hairan. “Ok to ba damuwa sai kun dawo.
Comment
Vote
Like
Zeey yar mutan zazzau ce 😘😘😘😘
WAZAN AURA PART TWO
31 AND 32
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
“Wace ce wannan Kawata?”
       “Wai Ammy kanwar Mama ta ce ai, a gurinta nake zaune kin san meye wlh Ummun ki kama suke da da Ammyt dina na Nigeria shiyasa nake daukan ta kamar Mahaifiya, “haba Hairan haka ake tarbon baki ke baki bata gurin Zama ba balle ruwa kin kuma cika ta da surutu. Duk da harshen larabci take mata Magana, “Oh Ammy mancewa fa Nayi, kawata zauna bari in zo kicin ta Nufa ta kawo mata kayan Motsa baki  da Abubuwa masu sanyi.
 Sun zauna sun fara hira Hairan ke tanbayar ta ina Rabin jikin ta ne. “Wallahi shi ma ya kawoni yace zai dawo ya dauke ni shine bai shigo su gaisa da Ammy na ba. Haka dai suka sha hiran su har lokacin tafiyar ta yayi Mudi ya dawo daukan ta haka kuma kiri-kiri yaki shiga yace Yamma tayi kuma Ummu zatayi fada.
   Washe gari haka Suka shirya bayan sun gama cin abinci a Dining sukayi ma Ummu Sallama kowa ya dauki Motar shi, ba wanda ya kula wani saboda duka suna fushi da juna ita dai Ummu nata ido, don tasan in ta shiga ma kunya zataji.
*************************
ABUJA NIGERIA
Dukan su suit su ka sa bakake hadi da Sun glass   suka isa Airport din hadi da Body guard din da suke take musu baya private jet zasu biya shiyasa suna shiga Airport din kawai Hawa jirgi sukayi suka daga sai UK.
*************************
KANO
“Kai Alhmdulillah da ace haka Gwamnati take yi ma talakawan ta aiki ai da munji dadi, don Allah dubi inda a ka gyara mana Titina Asibitoci wuta lantarki 24hours kai Allah ya biya dai. “Uhmmm kasan meye nafa ji ance wai yaron gwamna ne yake wannan aikin ba gwamna ba kuma wai saboda wata Mace ce”
“Kai haba da gske Amma wannan yarinya ta kyauta da zamu ganta da mun jinjina mata hadi da kyauta, Amma ko yanzu ma zamu bita da Addu’oi mu. “Hakane wallahi.
GOVERNMENT HOUSE
A bige ya shigo gidan yana tsayawa ko parking bai gama yi ba ya fito daga Motar ya shige gida. Da sauri Mammah da take shirin fita don zuwa Secret Room dinta da ke gida ta kauce mai saboda ya kusa bige ta. “Haba Son wai meke Damunka ne kasan nace duk abunda zakayi kar kayi Shaye-Shaye saboda lafiyanka. “Dallah Malama matsa ki ban guri ban son hayaniya. Bangaje ta yayi ya wuce.
Yi tayi kaman zata fadi da sauri ta rike kofa, “Oh ni Mariya yaro ya na neman ya illata ni kar ka bari raina ya baci wlh in jiyo kanka zaka sani. Tsaki tayi ta wuce abinta.
************************
WURNO
Karan Harbin bindigu ne da ihun jama’a ke tashi nan da nan makotan da ke garin suka fara gudun Hijira don ceton rayukan su don kisa sukeyi kan mai Uwa da wabi. Kana nun yara ne suke ihu da tsofaffi wanda bazasu iya gudu ba gunin tausayi  nan da nan kasa ta dauka. Can an dasa Boom, an sace mutane, Shanu, “Oh ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifan da ke damun kasan mu👏.
*************************
ABUJA
“Wai Alhaji Mai Nera akwai taron kungiya karshen watan nan ko? Saboda an dade ba’a zauna meeting ba ga Abubuwa nata tabarbarewa. “Ai dole ma mai girma Kakkau ya kira taron gaggawa gskya, ko da naji kasan ta fara hargizewa kwana biyu. “Ai kasan mu haka mukafi bukata in kasa na zauna kalau taya zamu samu kudin shiga. “Kai Alhaji Bukar wato kai kudin kawai kake hange ba halin da talakawa zasu shiga ba. “To kai in banda abunka Alhaji Dala talaka na da wani Anfani ne a garemu in banda su dangwala mana kuri’a. Dariya gaba daya suka kwashe dashi hadi da tafawa😂.
************************
UK
Su Saif ne suka sauka a Airport din UK suna kokarin hawa Mota ne kawai sai ga Fasihat ta shigo Airport din taci wata have gown din riga wanda iya kanta gwiwanta ta baza gashinta an mata wani hair style ya sauko ta gaban fuskan ta tasa wani Hill Shoe da ya zama takalmin sawanta yau bata sa glass din ba ta rata ya wata jaka da ya sauko mata har gurin kugunta  bazaka taba cewa ba baturiya bace gaba daya da Saif da Irfan a tare suka dago kowa yana suprise din ganinta….. ✍️✍️✍️
Comment
Vote
Like
. yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
INA BUKATAR ADDU’OI A GAREKU MASOYANA ALLAH YA YAYEMUN DAMUWANA
33_34
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
“Me ya kawo ta nan….?  kuma kodai gizon da ta saba mun ne take mun yanzu. “Besty wai me kace.?
“No bance komai ba. Kasan meye kawai muje ga driver can ya iso. “Ok wai meyasa duk ka wani rude ne? kodai ta tafi da Imanin ka ne? Kasan meye Besty na?  “Sai ka fad’a. “Wannan Beb din ne na ganta fa a kano kwanaki wasu police sun biyota, kuma taci dogon himar kamar mumina Amma kalleta a nan irin shigar da tayi, lokacin da na ganta ta birgeni saboda kamalanta da tarbiyan ta, saboda lokacin kawai aka sami missing na danyi kisss nata aiko ta dunga mun masifa harda su Amai… “What kisss!! Fa kace Saif ya juyo a fusace kamar zai daki abokin nashi wannan ne first time da ya taba daga ma abokin nashi murya tun suna yara. “Mai da wukan my besty ya fadi haka had’i da murmushi kwance a fuskar shi, daga nan ba wanda ya kare cewa komai har suka isa gidan su jidda saboda Suprice  visit suke so suyi musu. Kuma Irfan nada makullin gidan a hannun shi, shiyasa ko knocking basu yi musu ba suka shiga gidan tun daga falo suka fara cin karo dasu bra da panties can gefe kuma kwalaben syrup ne baza baza ga jidda a gefe tana ta barci daga ita sai wani yalolon riga ko cinya bai rufe mata ba da sauri Saif ya juya ya fita, shima Irfan kau da kai yayi. Da sauri yayi hanyar upstair din gidan tun kafin ya karisa yake jin wani irin Numfashi da alamu ba Mutum daya bane a dakin, da sauri ya karisa Kofar dakin har yana tuntube da wani takalmi, bugar Kofar dakin yayi dakin ya bude kwance ya gansu tamkar da dabbobi su gurin biyar. Bai san lokacin da ya rufe ido ba yana karanto duk Addu’a da tazo bakin shi, lokaci daya ya zare belt din wandon shi, duk basu san Yanayi ba don sunyi nisa basa jin kira, aiko ya koma ya rufe Kofar dakin nan ya fara laftan su sai a lokacin suka dawo hayyacin su, suka fara ihu shi kuma haka yaci gaba da laftan su daki ya karade da ihu sai da yayi musu lilis sannan ya kyalesu ya bude musu daki yace su bace mai da gani kowa ta kwashi kayanta a hannu, pretty ta tashi zata fita ya riko ta ya hadata da gado. “Ke dama abunda kukeyi kenan ba karatun ba to ku tabbatar yau zaku koma Nigeria kuma wlh duka Aurar daku zanyi shegu yan iska kawai.  Ball ya farayi da ita tun daga dak’in har falon ita ko Jidda nata barcin Asara, ita ko pretty tun tana kuka har muryan ta ya dushe, yana zuwa falon ya hada da jidda ji kawai tayi saukan duka ba shiri ta mike tana tangad’i suna hada ido da yaya Irfan ta watssake haka ya hada su ya musu dukan mutuwa sai da Saif ya shigo ya kwace su idon shi ya juye gaba daya yayi jajawur. Zama sukayi gaba dayan su Saif ya dubi Irfan yace mishi “yanzu meye mafita?  “Kawai zan barsu a nan zan kira doctor ya dubasu muje Egypt mu dawo, in mun dawo zan kwashi tsinannun mu koma gida muna zuwa Aure zan musu ya karishe fadin haka yana furzar da iska daga bakin shi. “But kasan halin Momsy wlh taji wannan aikin da ka ma yaran ta, sai ran ka ya baci. “Sai mene to tayi duk abun da zatayi wlh dai dai nake da ita. Gaba daya ya Amshe wayoyin su. Haka suka tafi suka bar su.
*************************
ABUJA NIGERIA
Guri ne ya cika ya baste don har wanda basa zuwa taron kungiya ranar sun zo in har kaga Mutanen da ke gurin sai kaji mamaki don wanda baka taba zato ba zaka gansu gurin. Kungiya ne da ya hada jinsin bakaken fata,  da farare,  da larabawa, kowa yasa bakaken kaya, kowa ka gani a gurin fuskar shi a daure take, inko ka kalli mai girma Zanjabiluuu nan ne zaka san ran maza ya baci saboda fuskar nan ba Rahma ko kadan. A fusace cikin kakkausa Murya ya fara fadin “Kakkau! Kakkau! Kakkau!!! Suma mabiya kungiya suna Amsawa. Bayan ya kammala fadin haka sai ga wani mummunar Halitta ya bayyana a tsakiyar gurin har sai da wasu daga cikin yan kungiya suka tsorata saboda wannan ne karo na farko da Dodon tsafin nasu ya bayyana. Jini aka fara gabatar mai na al’umar da aka karkashe na garuruwan da basu da kwanciyar hankali. Bayan ya sha jini ma ishi har yayi guzuri, nan ya fara magana da wani Murya mai Amon sauti mare dadin ji. Yayin da yake maganar mai girma Zanjabiluuu yana fassara musu cikin harshen turanci da Hausa.
“Ina so ku sani kungiya tana cikin wani hali sbda akwai wasu Matsaloli da suke tasowa, akwai wasu jajirtattun mutane da suke da Matukar hadari ga wannan kungiyar, kuma Matukar ba mu dauki mataki ba zasu kawo karshen kungiya. Wanda hakan yana dai dai da rasa mukaman ku, kunga kuwa wannan babbar koma baya ne a gare ku da abun kunya a idon duniya, muko da mu ji kunyar duniya gara muji na lahira. Ni ko nace wa’iyazibillah Aiko kun tabe sosai. “Kuma akwai wasu daga cikin yaran ku  wanda zasu bada gudunmuwan su game da haka but mai girma Kakkau har yanzu ya kasa gano daga ina wa innan yaran zasu fito sbda haka dole kusa ido akan yaran ku gaba daya. Kuma mai girma Kakkau shima zai tsaurara bincike don ganin ya gano su. Akwai wani taron nan da sati biyu don mu Kara tattaunawa gurin kawo karshen matsalar kungiya. Nan guri ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakin shi. Haka taron nasu ya watse batare da sun samo ma kansu mafita ba.
*************************
KANO
Ikram ne kwance kan kujera tana kallon sama ta shiga Duniyar tunani. “Ya Allah na tuba abun da na aikata a baya Allah ka yafe mun, ka kawo mun mafita. “My daughter kina nan ashe? Ta fadi haka tare da Zama a kan kujeran da Ikram take Zaune hadi da jawota jikin ta. Nan gaban Ikram ya fadi don tasan abun da Mamma take so. Gashi wani Bala’in tsoronta takeji bazata iya mata musu ba. “Eh Mammah kin tashi?  “Eh my sweet heart hade bakin su tayi guri daya ta fara lalubanta. Wayan Mamma ne ya fara ringing Tsaki tayi ta dauki wayar hadi da sake Ikram da gudu Ikram ta gudu dakin ta. Ta haye gado ta rushe da kuka Ya ubangiji ka kawo mun dauki.ji tayi an dafata da sauri ta mike jikin ta na rawa don tasan ta rufe kofa kafin ta shigo, nuna ta ta farayi “kece taya kika shigo dakin  nan me ya kawo ki? Murmushi Fasihat tayi hadi da Zauna wa a kujerar da yake Bedroom din nata ta dora kafa daya kan daya ta fara karkadawa, “don Allah kiyi hakuri karki cutar dani kuma ki yafe mun abunda nayi miki kila ma alhakin abun da nasa aka yi ma yar uwar ki ne yake bibiyata. “Dakata ni bashi ya kawo ni ba… Kina bukatar taimako na? “Eh wlh ina bukata. “Zan taimake ki Amma da sharadi.”
“Ina jinki ko wani sharadi ne wlh zanyi.
*************************
EGYPT
Shekarar su Sumayya biyu yanzu a Egypt sun zama yan gari ga wani mugun shakuwa dake tsakanin Mudi da Sumayya wanda Ummu tafi kowa farin ciki da haka, saboda wasu dalilai da ta boye a ranta. Yau Summaya ta tashi da shirin zuwa gidan su Hairan saboda suna so su dan fita su zaga gari kuma zasu gidan Sarautar garin kasancewar gidan kakan nin Hairan ne. “Yauwa Ummu tayani Zabe cikin wa innan kayan Wanne zan sa? Wani pitch perfect Colour hade da ratsin goldin a jiki Ummu ta nuna mata tace ta sa wannan, aiko ta juya daki taje ta sa doguwar rigan nan kaman don ita akayi shi gashi bata wani heavy Make up ba powder kawai tasa sai tozali saboda ita duk kwalliyar ta sai tasa tozali ta zizara eye liner a saman idon ta tasa lip gloss. Wani goldin fost da wani takmi mai tudu tasa shima goldin ta feshe jikinta da Turare nan da nan d’akin ya dauka da kanshi key din mota da wayoyinta ta dauka ta fito lokacin Mudi na falon yana yin breakfast suna ta hira da Ummu, kanshi turaren ta ne da takun takalminta yasa duka suka waiga kwarewa yayi da tea din dake bakin shi ya wani kafe ta da ido Ita ko Ummu murmushi tayi tace “Yar albarka kinyi kyau ta fadi haka hadi da mikewa ta bar falon. “Kai Rabin jiki wannan kallon haka fa😏ta fadi haka tana murguda mai baki. Fuskewa yayi hadi da cewa “ke zan tanbaya kin wani sa Mutum ya shake, wai ma tsaya Ina zaki da wad’an nan kaya kaman wata mai shirin zuwa gasar Sarauniyar kyau. “Yes nasan nayi kyau Rabin jiki ma ya kyasa. “Dallah ba wani kyau din da kikayi nidai bazaki fita a haka ba kije ki canza kayan nan ko kuma kisa hijab da Nikab. “Tab wlh ban yarda ba tafara kukan shagwaba, aiko Mudi nan da nan ya rud’e yana lallashin ta badan yaso ba haka ya hakura sukayi ma Ummu Sallama suka tafi zaije ya kaita.
Suna shiga gidan su Hairan ta buga tsalle ta rungume ta tana murnar ganin juna shiko Mudi ya tsaya yana kallon su sai da Ammy ta fito ta gansu ta hau su da fad’a ni ban san ranar da zaku girma ba, kun bar mutum a tsaye kunata shirme, kaji Mahmoud zauna. Murmushi yayi yace to ai na riga na Saba da shirmen su Ammy. “Ai naga alama kana fama da wad’an nan kannin naka, bayan sun zauna ne suka fara hira Ammy ta cika musu gaban su da kayan ciye ciye.
“Kasan wani Abu da Agent Mahmoud na gari ne da a gidan shi zamu sauka kawai Cewar Saif, “gskya kam don ni ban son Zama gidan Ammy sai in ta jin kunyar ta. “Sai kace wata surikar ka. “To waya sani. Sun kariso gidan Ammy sukayi Nocking sai Sumayya ta tashi da sauri taje ta bud’e Kofar. Kamewa dukan su sukayi suna mamakin Kara ganinta a nan hada baki sukayi gurin cemata “You again! Ita ma din mamaki takeyi Dama zata Kara ganin Doctor mai kyau. Matsawa tayi ta basu guri suka shigo hadi da sallama kowanne a cikin su da abunda yake sakawa, Wani Karin mamaki ne ya ishe su. Mikewa yayi da Sauri. Kamewa sukayi gaba dayan su, suna Sara mai.
*************************
“Dana komai na tafiya yanda nakeso sbda a yanzu haka Su Agent Saif sun hadu da Sumayya kuma dukan su suna Son ta, ga kuma Aslm can shima haka, da wannan daman zamuyi Anfani. Angama Jaddi.✍️✍️✍️✍️
Vote
Comment
Like
I love you my Masoya na nagode mu ku da fatan alheri😍😍😍
Yar mutan zazzau ce iya wuya muna tare.
WAZAN AURA PART TWO
35_36
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
“Sharad’i na shine duk wani abun da na buk’a ta a gurin ki zaki bani had’in kai sosai.? “Eh wlh zan baki bazan boye miki komai ba. “Ok good akwai wani kundi a dakin Mahaifin ki da nake buk’atar ki dauko mun shi… Zaki iya dauko mun.? “In dai zaki taimake ni zan dauk’o miki. “Akwai hatsari sosai game da daukowan Amma, but zan baki kariya sosai da wasu Addu’oi da indai kin rike zaki d’auko lafiya ki fito ni kuma na miki alk’awarin zan kai ki har inda Mahaifiyar ki ta ke. Da sauri Ikram ta dago kai tana kallon Fasihat mamaki kwance a fuskan ta. “Nasan kina mamaki da nace zan hadaki da Mahaifiyar ki koh?. To Mahaifiyar ki na nan da rai bata Mutu ba. Buga Kofar da a ka fara yi ne ya katse musu zan cen su, nan da nan Fasihat ta b’ace.
*************************
EGYPT
“Sannun ku da zuwa Brothers. Mudi ya fad’a hadi da musu magana da ido nan da nan suka shiga taitayin su suka fahimci mai yake Nufi, sai suka mika mai Hannu  domin yin Musabaha hadi da cewa yauwa Brother ya gida ya aiki bayan sun gama gaisawa ne kowa ya Zauna aiko Hairan ta na ta farin ciki ta ce ma Sumayya “Sahiba ta ga my akhee wannan kuma Yaya Irfan Aminin kuma dan uwan Akhee dina, wanda nake yawan baki labarin su..  Akhee ga Sahibata Sumayya wanda nake baku labarin ta ita ma a Nigeria take daga Kano State but ka ganta kaman balarabiya. Sumayya ne ta dan doketa hadi da ce mata “haba Sahiba kin cika surutu kiyi shiru haka mana. Sai ya kasance gaba daya gwarazan Samarin Falon idon su na kan Sumayya. Yayin da gaba daya shi kuma Mudi hankalin shi na kan Saif saboda irin kallon da yaga yana aika ma Sumayya da shi zallan Soyayya ne a kwayar idon shi, shiko Irfan kawai kallon tsaf ya ke mata don ya kasa Samo banbancin wannan da wancan da suka gani a UK. Gaskiya ya shiga rud’u banbancin kawai da ya iya ganowa shine wannan tana da innocent face ita kuma wancen totally idon ta a bud’e yake. “Ya Ilahi! Ya furta yakin da kowa na falon ya waigo yana kallon shi. Firgigit yayi bai san maganar ta fito fili ba. “Ke tashi mu tafi!! Mudi ya fad’a cikin b”acin rai da Tun da suke da Sumayya bata taba gani ba ita dai tasan Yayan mai harka ne baka tab’a ganin fushin shi, wai yau shi yake daka mata tsawa. Da sauri ta mike jikin ta na rawa ta kama hanyar fita. Shima mikewa yayi ko kallon inda suke baiyi ba. Sai sune suka ce “Brother sai anjima bai samu damar Amsawa ba. Kuka Hairan ta fashe dashi da yasa duka suka waigo suna kallon ta da mamakin mai yasa ta kuka. “Akhee tun zuwan ku na lura kun bata ma Rabin jikin Sahiba rai gashi kunja yama Sahibata masifa gashi ya hana mu zuwa inda zamu. “Haba my jameelatu ukhtee wallahi ba laifin mu bane ba musan me mukayi mai ba. Shidai Irfan nacan ya shiga Duniyar tunani.
Tun da suka fita ranshi yake a dagule ba abun da yake tunawa sai irin Kallon da Saif yake ma Sumayya. “Oh my Allah ya buga sitiyarin Motan wanda sai da Sumayya ta tsorata. Ta Kara fashewa da kuka, dama kukan takeyi kasa_kasa. “Will You shut up ur mouth u disturbing my ear.! Da sauri ta had’iye kukan nata. “Kawai kin je kina ta wani ba wasu Banzaye murmushi saboda rashin kamun kai. Kin ban mamaki Haka Ummu tayi miki tarbiya tun kafin aje ko ina har kin fara zubar da tarbiyan. Har suka iso gida yana mata Masifa. Aiko ko gama parking baiyi ba ta fice a motar kaman zata fad’i tayi shigewar ta gida ko Sallama batayi ba balle Addu’a shiga gida, kuma lokacin ba kowa a falon Ummu na Sallah. Shima hakan take a gurin shi kasancewar yanda yakejin zuciyar  shi kaman zata fad’o. Amma a hakan yake jin kaman ya bita ya bata hakuri don bazai iya jure fushin ta ba. Kawai sai ya wuce d’akin shi yana zuwa ya shige toilet ya sakar ma kanshi Ruwa saboda yanda yake jinshi. Karan kiran wayan da yaji ne ya maido dashi hankalin shi yayi sauri ya kammala wankan ya fito ya dauki wayar “Hello Abokina”Lafiya lau sai dai fa akwai Matsala don naga alama in banyi da gske ba ina shirin rasa ta wlh. “Ya akayi haka? Meya sa ka bari ta fara Soyayya t? “Ka bari kawai Abokina ina fa tunani Wani Abu fa Anya ban dani ba wanda yake bibiyaan rayuwar su Ummu nayi iya bincike na don in gane waye wannan wanda ya biya mana karatun nan na kasa ganowa. Kuma duk wani plan da muka shirya kafin mu gabatar dashi sai inga anje anyi. Abun na daure mun kai. Kasan ma wai wa ya ke Son Sumayya? “Sai ka fad’a mun Aboki. “Agent Saif Mahmoud Jarumi. “What! Tabbass akwai Matsala Aboki na🤔dole mu nemo Mafita,  sun ganku kuma tare sun kuma gane ka duk da badda kaman da kayi? “Ai kasan waddan nan yaran Mayu ne kaman masu wankin ido. “Oh shirt dole a Nemo Mafita kuma kasan yanzu Dole Agent Irfan sai ya bincike akan abun kasan shi da bin kwakwafi, dole zuwa gobe zan samo mana Mafita. “To shikenan Abokina Allah ya kaimu sai na jika. Duk maganar da sukeyi cikin harshen larabci sukeyi, niko Mamaki ya kashe ni wai waye Mudin nan ne?  Na kasa ganewa😂.
*************************
MISRA
Sallama tayi had’i da shigowar katon falon da yaji kayan alatu da more rayuwa kamar baza’a mutu ba Jaddi ne kishin gide a kan wani tuntu irin na sarauta, gaban shi cike da kayan Marmari, Fasihat ta samu guri ta Zauna tace barka da hutawa ya Jaddi.  Murmushi yayi hadi da cewa “yauwa Sarauniyar Jikata da fatan kina lafiya kuma komai na tafiya dai dai? “Sosai kuwa ya Jaddi don ita Yarinyar nan bazamu samu matsala da ita. Kasa karisa maganar ta kasancewar wani irin kallo da yake mata ita ma sai da taji gaban ta ya fadi, kura mishi ido tayi. ✍️✍️✍️✍️✍️
Like
Comment
Vote
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
37_38
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
“Jaddi waye wannan Bil’adaman.?  Ta fad’a cike da mamaki. Waigawa Jaddi yayi yana kallon Mutumin fuskar shi dauke da murmushi. Shikan shi wanda Fasihat take maganar shi ita yake kallo fuskar shi d’auke da Mamaki. “Jaddi wa nake gani kamar Sumayya”.  ya fad’i haka yana Zaunawa kusa da Jaddi. “Wannan ba Sumayya bace zan fad’a maka ko ita Wacece Amma ba yanzu ba…kema zan miki bayani ya ke Sarauniya ta. Zankadaziyyatu ne tayi Sallama ta shigo falon had’i da ballama Fasihat harara🙄. Samun wuri tayi ta Zauna. “Barka da hutawa ya Jaddi…brka da hutawa ranka ya dade. “Brka dai Gimbiyar MISRA. Wani murmushin farin ciki tayi had’i da kallon Fasihat. Kauda kai Fasihat tayi, tayi kaman bata ganta ba. “Ya Jaddi kwana biyu Banga Yarima Mujaheed bane”? “Ya Jaddi zan tafi sbda muna da shiga Aji karfe biyu”. “Ok d’iyar Albrka Allah ya bada sa’a. “Ameen ya Allah” bacewa tayi a gurin. Yayin da Jaddi ya maida duban shi ga Zankadaziyyatu, “Ya ke Gimbiyar MISRA Mujaheed yana Duniyar Mutane a cikin Abuja yaje mun wani aiki game da Matsafan nan domin Sauk’ak’a ma Su Irfan da Saif da Maumoud gurin bincike su da zasu gabatar. Zaro ido tayi had’i da cewa”Haba Jaddi kasan hatsarin da wad’an nan matsafan suke dashi Amma ka tura shi. Ta karishe maganar ta da damuwa a fuskan ta. “Karki damu ya ke Gimbiyar Misra sai da na shirya Yarima da Addu’oi, shi kuma Addu’a takobin Mumini ne. Na kuma san Yarima Jarumi ne ba Abun da Zai bashi tsoro a yanzu.
*************************
EGYPT
“Ukhtee ki bani labarin kawanki mana.”? “Akhee mai yasa kake son jin labarin ta ne wai.? Labarin kawata abun tausayi ne Asalin su yan Maiduguri ne a garin Baga yakin boko Haram ne ya dawo dasu Zamfara da zama a kauyen Wurno. Tana tare da Mahaifinta da mahaifiyar ta da yayyinta biyu Adnan da Maryama to ita Maryama tana dauke da sikila. Haka dai ta wanzu tana bashi labarin ga abun da ya baro dasu daga kauyen Wurno har suka rasa Yayan su da Mahaifin su ya zama daga Maman ta sai yar uwan ta Maryama suka rage inda suka dawo kano Mahaifiyar ta ta dunga fad’i tashin gurin samun abun yi har ta Tara yan kud’i ta siya musu karamin gida suke Zaune da dadi ba dadi. Haka dai Hairan duk taba su Irfan labarin Su Sumayya har da sanadiyar mutuwar Yayan ta Maryama gaba daya su Saif ransu ya b’aci jin abunda su Aslm suka ma Maryama. Saif ne ya mike a fusace ya naushi iska, “sai na koya mai Hankali dan akuya kawai. Sai na nuna mai talaka ma yana da y’anci a k’asata. “Calm down mutumi na, ni fa I have alot of question da nake son inyi miki Kanwa ta.”
“Ina jinka Yaya”.   “Shin k’awarki batayi tafiya zuwa wata k’asan ba tunda tazo nan k’asan karatu? “Gaskiya Yaya ba inda taje Asalima bata taba zuwa wani k’asa ba sai nan kasar. “To shin meye alakar su da wanda suka zo tare da naji tana cemai rabin jiki.? “Eh Makocin su ne a Nigeria sannan kuma yana Bala’in son Yayan ta da ta rasu ka ganshi nan Dan fulani ne Asalin su suma daga Taraba suke. Shine suka dawo kano da Zama kuma sun saba sosai shiyasa da wanda zai biya musu karatu a nan Ummu ta roki alfarman a had’a dashi, shine fa suka zo tare. Sai dai naga kaman yanzu Shima ya fara son ta. “Stop ba’a tanbaye ki ba inji Saif.  da tunda  Irfan yake mata Tanbayar bai ce komai ba sai yanzu. Kallon shi dukan su sukayi suna Mamaki musamman ma Irfan da yake hango tsantsan kishi da Soyayyan Sumayya a idon Aminin nashi. Gaban shi ne ya fad’i tuna cewa shima fa tunda ya ga Yarinyar nan yaji Son ta a ranshi. Gashi yana tunanin alkawarin da yayi ma Saif.   ko ba don Alkawarin da ke tsakanin shi da Saif ba ma bazai taba iya son Abun da Aminin shi ya ke so ba dole ya janye ya danne zuciyar shi don farin cikin Aminin nashi. A bangaren Saif shima tunanin da yakeyi kenan. “Yanzu in har maganar da Hairan ta fad’a gskya ne meya kaita UK? Kai Impossible bama ita bace. “Yauwa Uktehh bata taba fad’a miki cewan su yan biyu bane?
“Gskya ni bata taba gayamun ba. “Ok Besty muje koh.
*************************
KANO
Takarda ta mik’a mata rubuce da Addu’oi a ciki da hausan boko da na larabci. “Ina so ki haddace wannan Addu’oin kafin sati daya sannan zan baki wani Sallah da zakiyi shi sati d’aya zaki dunga tashi biyun dare kina yi don wannan lokacin, lokacin ijaba ne in har kika rike wannan sallah insha Allah kafin sati sai kin ga biyan buk’ata ga sallar kaman haka(raka’a biyu kowacce raka’a zaki karan ta fatiha bayan kin karan ta fatiha zaki ce Subhallahi, walhamdulillahi, Wala ilaha illah lah zaki fad’i haka sau Arba’in da biyu, haka raka’a ta biyu ma zakiyi bayan kin idar kinyi tahiya sai ki karanta Subhanallahi, Walhamdulillahi Wala ilaha illah wallahu akbar  sau arba’in da biyu. Bayan haka sai ki roki duk bukatun ki Allah zai Amsa babu hijabi.)  “Nagode Sosai y’ar uwa ki yafemun abun da na yi miki insha Allah zanyi kokari gurin yin sallah nan. “Ba komai…sannan ki yawaita istigfari domin shima yana da falala sosai. Ni zan tafi bazan Kara dawowa ba har sai sati ya cika bayan kin gama Addu’oi da na baki da Sallah sannan muga wani irin Nasara muka samu, sannan ki rike wannan Addu’a ko da yaushe ki dunga karanta ta a bakin ki (Wallahu galibun ala Amrihi) duk wani makiyin ki sai ya koma yana fargabanki Insha Allah.”
“Ngd sosai.
Washe gari Mammah ne tazo dakin Ikram din da Asuba, don bokan ta yace mata akwai Matsala fa Asirin jikin Yarinyar nan yana shirin karyewa. Don yanzu ta fara ibada tasan yanda zatayi ta hanata ibadan nan. Shine ta yi sammakon zuwa d’akin Ikram din don taga me Ikram din ta keyi. Zaro ido tayi ganin Ikram a kan sallaya da tasbahan ta a hannu. “Me zan gani waya baki iznin yin Sallah a gidan nan😲!?. Ta fad’a cikin daga murya. “Mamma”!! ita ma ta fad’a da karfi. “Meye Nufin ki Ibadan ma don zanyi sai kin bani dama to bazai yuwu ba. Ta juya ta cigaba da jan tasbahan ta. Mamaki ne ya cika Mamma. Kwafa tayi ta fice. Ajiyar Zuciya Ikram tayi had’i da cewa “wai Allah ashe dai zan iya maida mata Magana.
*************************
EGYPT
“Wai yaushe kuka shigo gidan nan ne?  Ko sallamar ku banji ba. Balle kuyi min kun dawo. “Wallahi Ummu na gaji ne shiyasa, me kika girka mana.?  “Ina kanwar taka ne.?  “Tana d’aki wai kan ta na ciwo ta kwanta zatayi sleep kafin La’asar. “Ok to bari in zuba maka Abinci ita in ta tashi taci. “Yauwa my Uwa ta gari. Wucewa tayi ya bita da kallo yana jin matar har cikin zuciyar shi. Anya bai Munafurce su ba. Sun yarda da shi yana cin Amanar su. Haka dai yake ta tunanin har Ummu ta dawo bai san ta dawo ba sai da ta tabe shi, yayi firgigit. “Tunanin me kakeyi Dan albarka? “Ba komai Uwa ta gari.
Safa da marwa yake tayi a d’akin. Shi kuma Irfan yana kwance ne kanshi na kallan Sama kowa da tunanin da yake yi. “Saif dole ne a garemu mu bi diddigin abun da yake wakana. “Ni kasan abun da ke damuna ma na rasa ta inda zan fara ne. Ga binciken wadan nan kudaden da Abbie ya sani na rasa wa zan fara bincike a ciki. Ga wannan matsalar ta Yarinyar na don ina ji a jiki na akwai wani Sirri mai karfi tattare da ita, kuma akwai gudumuwar da zata bamu a cikin aikin mu.
GIDAN SARAUTA EGYPT
Tankashe shen falo ne da yaji kayan Alatu wanda baki ma bazai iya Zama lissafashi ba. Wani  Had’ad’en saurayi ne a tsakiyar falon yana ta kai kawo yana naushin iska “ya ilahi”
“Yallabai”.  waigowa yayi a fusace “what meye ne dallah fita daga nan ban son ganin kowa anan. Juyawa tayi da sauri. “Ranki ya dade wallahi koroni yayi kuma yau kwana biyu bai ci Abinci ba. Daga gani yana cikin Damuwa kuma Matukar Ummi ta lura da yawan zuwa na shashin akwai matsala kin san komai zai iya faruwa. “Ni wannan ba Matsala ta bace, matsala ta shine ki tabbatar yaci Abincin. “Allah ya huci zuciyar gimbiya. Juyawa tayi ta fice.
************************
ZARIA NIGERIA
“Shatu yanzu kin zama yar Gida koh? Jira nake Ummimi tazo sai muyi magana ko Makaranta zaki shiga. “Aikuwa Hajia Yaya nima dazu da muke waya da ita haka naso in ce mata, sai dai Nace bari ta zo tukunna.
************************
ZAMFARA
Wani Mahaukaci ne yana tafe yana tsince tsince. Yayin da in yaga Mutane sun taru sai yaje gurin su ya fara ce musu”don Allah baku gansu ba?  sai kuma ya fashe da kuka. Sai mutane su ce mishi ka bi ta can hanyar suna nan. Sai ko ya ruga da gudu.
Vote
Comment
Like
Luv you too masoyana 😍😍😍😍
Yar mutan zazzau ce 💖💖💖💋💖
WAZAN AURA PART TWO
39_40
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
Lungu da sakon na gidan tsafin nasu yake shiga cike da rashin tsoro da addu’a a bakin shi.bayan ya gama binciken duk abunda ake yake bukata ya tattara komai game da yawan kofofin gidan da dakunan gidan.  da hanyoyin da ya kamata a shiga gidan da ranar da zasuyi babban taron su Wanda sukeyi duk bayan shekaru uku Wanda yanzu ya rage sauran shekara daya da wata goma Wanda zai zo dai_dai da kammalawan karatun su Sumayya da wata shida. Da ita da Fasihat da Mudi. Har ya juya zai fita Sai naga ya juya cikin hanzari fara binciken dakunan yakeyi da alama akwai wani Abu mai muhimmaci da yake Nema. Dai_dai wani kofa yazo naga agogon gold din dake hannun shi yayi haske. Da sauri ya kutsa cikin d’akin hadi da addu’a, wata Mata ce ya gani d’aure da Wasu sarka Matar ba abun da ya ke fita a bakinta Sai jini yana shiga cikin wani container. Rufe idon shi yayi ya bude Gashi an aske mata kai Matar ba kaya a jikin ta. Jakar da ke bayan shi ya ciro, ya fitar da wani ruwa a gora ya fara karanto mata du’aus sihir yana tofawa a cikin ruwan nan ya kai Awowi yana addu’a a cikin ruwan zam_zam din nan ya Kara bude jakar shi ya dauko ganyen magarya ya zuba a cikin ruwan. Nufan ta yayi don watsa mata ruwan nan da nan ta rikid’e ta zama wani mummunar hallita ta fara mai feshi da Wuta ya fara karewa da wata takobi dake hannun shi tare da addu’a, a haka Sai da yaci nasarar watsa mata ruwan addu’a take a nan ta zube a kasa ta koma siffanta na ainihi. Sai gata a kasa Tana fitar da numfashi sama_sama da sauri ya bude jakar shi ya fito da wani mayafi ya sanya mata. Ya d’agata ya bata Wannan ruwan addu’a tasha nan da nan ta fara Amayar da Wasu abubuwa ba kyan gani daukan ta yayi nan da nan suka bace dashi Sai Gashi sun bayyana a Kasar Misra.  nan da nan aka zagayesu Ana ma yareema kirari. Nan da nan gidan sarautan ya d’auka da bushe_bushe na murnan yarima ya dawo. Wasu kuyangu ne suka zo suka dauki Wannan Matar suka wuce da ita Asibitin gidan sarautar don bata taimakon gaggawa. Yayin da shi kuma Mujaheed ya shiga gurin jaddi don ganawa dashi game da Nasarorin da ya samu, da Neman izinin gareshi don yaje ya dubo su Sumayya. Sun tattauna da Jaddi sosai a lokacin yaga bakon da Zankadaziyyatu tazo dashi yaji bala’in mamaki kaman da sukeyi da Fasihat. Kawai dai yayi shiru ne don yasan jaddi bai son yawan tanbaya  akwai lokacin da zai warware musu komai.
*************************
EGYPT
“Aboki na Kasan har yanzu su Saifudden da Irfan suna Kasar nan kuwa basu koma ba…don ko jiya na gansu a Makarantar mu. But Kasan munyi magana da Chief Security na Kasar Egypt din gaba daya akan cewa bana son a bari ko waye yasan ina Kasar nan ko da Abbie ne. Amma Kasan jiya da na fita da Sumayya mun had’u da little Haidar shi da Ummyna ya kaita shopping Sai kallo na yakeyi Kasan little Haidar akwai brain da sauri naja Sumayya muka bar shopping din har muna fad’a da ita akan bata gama siyayya ba”.
“Oh ya Allah komai Nasan ya kwabe mana Kasan Abu ya karbe kwamfiyuta na saboda ya gano ina hada Wasu bayanan sirri game da bacewar Abbie da Ummu, da kuma wad’an nan takardun da Abbie ya tafi dasu don ina zaton da kyar takardun suna hannun shi. “Wait Abokina Sunce fa Abbie ya rasu. “Karya ne Aboki na Abbie na nan da rai a wani binciken da nayi nayi kutse cikin na’urar Abu na fara gano Wasu abubuwa kafin ya farga ina bibiyan shi sai ya toshe duk wani kafa da Zan Kara mai kutse, nayi kokarin gano location d’in mutumin da suke magana da Abu ban samu ba Amma tabbas maganar Abbie sukeyi kuma naji yana cewa har yanzu yana hannun Wasu mutane a ajiye. Matsalata takardun nan duk wani sirri Wanda ya kunshi gidan Sarautar Egypt yana ciki da duk wani kunbiya kunbiyan da Abu ya shirya. Abbie ya rubuta Kasan Abbie Dan Jarida ne to lokaci daya Abbie aka wayi gari bashi ba labarin shi shida Ummu da Sauran iyalan shi. Ni kadai na rage sakamakon lokacin bana Kasar. Lokacin ance Ummu Tana goyo karamar yarinya don Jaddi shi Yasa ma yarinyar Suna, ance a gaban shi aka haifi yarinyar anyi anyi ya tashi yaki har sai da Ummu ta haihu yama yarinyar huduba yana kuka. Kafin suna ya rasu tun daga lokacin rikici ya yawaita a gidan Sarautar da rashin zaman lafiya. Har dai aka wayi gari An nemi Abbie an rasa Wanda a lokacin jama’ar Kasan Egypt shi suke so ya maye gurbin Jaddi don halayyan shi gaba daya irin na Jaddi ne lokacin duk muna yara. Bamusan komai ba. Abbie su biyu Mahaifiyar su ta Haifa Ummi Habibatu itace  Babba sai Abbie bayan an haifi Abbie Mahaifiyar su ta rasu, inda Ummy Habibatu tacigaba da rainon Abbie inda jaddi ya dauki son duniya ya d’orama Abbie saboda maraicin rashin uwa. Har Ummy Habibatu tayi Aure har ta haifi yarinyar ta girma sannan Abbie yayi Aure ya Auri kanwar Mijin Ummy Habibatu mace mai hakuri da ilimin Addinin musulunci da boko bayan bikin ta da Abbie aka Aurar da babban yarinyar Ummy Habibatu a Nigeria. Bayan shud’ewar shekara Ummu ta haifi Akhee Adnan, bayan haka aka haifeni sannan aka haifi kanwata Wanda tunda aka haifeta bata da koshin lafiya, daga ita sai aka Haifa mana Autar mu kuma gimbiyar mu. Murmushi yayi had’i da Wasu zafafan hawaye da ya zubo mai. Bayan haihuwar ta ne komai ya faru muka rasa Jaddi kuma na rasa iyaye na da yan uwa na. “Sai yaushe Zan gansu Aboki na?  Yaushe Zan kawo karshen zaluncin da akeyi a gidan Sarautar mu. “Kayi hakuri Abokina komai ya kusa zuwa karshen don tabbas sai mun kawo karshen zalunci da Azzalumai. Akwai wani Aminin Abbie da suka gudu tare shima har yanzu ba’a ganshi ba, shima shi da yaran shi uku. Allah zai bayyanasu gaba dayan su. “Allah ya bayyana su. Ameeen ya Allah. “Zamuyi waya anjima, naji Ummu na kirana. “Don Allah in kana kusa da ita ka kunna wayar ka inji muryan ta ko zanji farin ciki. “Karka damu Aboki na Zan iya yin komai don sama maka farin ciki.
“Hairan kizo in aike ki gidan Ummy. “Kai Ummi na nifa banson zuwa gurin tsohuwar nan ta cika fada komai kai mata baka kyauta ba. “To ya zamuyi Hairan nima tunda Ummy ta haifeni na taso na ganta cikin Wannan halin saboda batan Dan uwan ta da Matar shi, Wanda ta kasance kanwa ga Abul bait din mu kwata_kwata family din mu ya zama ba Happy Family ba kasancewar har yanzu ko labarin su ba a taba ji ba. Shiyasa zaki ga Ummy haka kiyi hakuri da ita. Kinji tashi kije ki dubo min ita. “To Ummi sai na dawo”.  To ki dawo lafiya diyar Albrka.
************************
Kano Nigeria
Ikram ne zaune ta dora kafa daya kan daya tana taunan chew gum, Mammah ne ta fito hanun ta rike da key din Mota.  ganin Ikram a falon sai da gabanta ya fadi saboda gaba daya yanzu yarinyar tsoro take bata. Ita ko ikram yanzu cin uban Mammah takeyi ita da Aslam. Yayin da Suna dunfaro ta da bukatar su Suhailat zata shiga jikin ta ta musu Dan banzan duka tun da sukayi haka sau biyu dukan su suka kiyaye ta. Mammah tayi ma bokanta magana yace ai aljanu gareta kuma sun fi karfin shi bazai iya dasu ba. Haka ta dawo da gudirin sai taron karshen shekara zata bayar da shegiya a kungiya kyauta ta huta da masifa. Don yanzu Ikram masifa ne a gareta.
*************************
Abuja Nigeria
“Yauwa Daddy da Momsy abun da Yasa na kiraku anan in sanar daku next month Zan Aurar da pretty da Jidda kuma ba Wanda ya isa ya dakatar dani daga abun da nayi niyya. Saboda ina da kwakkwaran hujja na. Na fada muku ne ma don sauke hakkin ku a matsayin ku na iyayen su. Na barku lafiya.
“Wlh bazai yuwu ba kawai yaro ya zama kaman wani shi ya haifemu iye da zamu dunga kallon shi yana mana iko. Ai duk kai ka sangarta shi sai kace Wasu dabbobi y’ay’an nawa ne za’a musu Wannan Auren wulakancin.? “Wai Excellency ina magana kana jina baka ce komai ba.!!!  “To Hajiya Murja in banda abinki me kikeso na ce miki. Bayan Yayan su ya gama magana. Ihu tasa ta tafi d’akin ta ta kulle.
*************************
“Jaddi Matar da aka kawo tana bukatar jini kuma na bil’adama irin ta. “Dana in ba Matsala kaje ka bada a sa mata. “Ba damuwa Jaddi muje ko. Suna shiga Asibitin  ya zaro ido “Marfu’at kece.!
Haka dai aka samata jini kwananta uku Ana bata addu’oi da magunguna tana sha. Har ta warke sai Dan sauran abunda ba’a rasa ba. Shiko har yau Wannan bakon ya kasa tanbayar Jaddi game da Marfu’at ita kuma ta mance kowa da komai da ya faru da ita.
*************************
Zaune yake karkashin bishiya yayi tagumi. Wasu gun_gun yarane suka doso shi suna fadin “Dan Balarabe an gansu. Firgigit ya tashe yace musu a ina suka ce mai a can layin da gudu ya diba yabi hanyar da suke nuna mai.
Like
Comment
Vote
Love you too my Masoya ma💖💖😍😍💋💋💋💖💖😍😍
WAZAN AURA  PART TWO
41_42
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*************************
WANNAN PAGE DIN KYAUTA NE A GAREKU YAN WAZAN AURA PART TWO NOVEL FANS SOYAYYANKU A RAINA BAZAI FADU BA INA MATUKAR YIN KU INA JIN DADIN COMMENT DINKU LOVE YOU TOOOO💋💋💖💖💖💖.
***********************
A gurguje kwanaki sun tafi. watan ni ma sun shud’e. inda shekara ya zagayo. inda Abubuwa da yawa sun fara ciki har da Aurar da su jidda da Irfan yayi, kuma duka ga Masu rufin Asiri ba Wasu manyan mutane ba. inda Momsy tayi fadan har ta gaji da dangana ga Allah. Saboda ba yanda zatayi da shi. Ita kanta shakkan Irfan takeyi kuma bata son bacin ranshi. Shiyasa yake mata katsalandan a rayuwa. Duk da cewar su jidda sun kintsu yanzu sun zubar da komai sun rungumi mazajen su. Yayan nasu ya basu jari gaba dayan su har da mazajen nasu suna jujjuyawa. Inda pretty take Aure a Kaduna ita kuma Jidda tana Katsina.
*************************
Inda fannin Marfu’at kuma ta dawo dai dai ta tuna da komai Amma jaddi ya nemi da ta yi shiru sai ranar da yake bukatar ta bayyana Abun. Yayin da suke rayuwa ita da Nuradeen cikin jinsin Aljanu har sun saba.
*************************
In kika duba fadin Hall din gaba daya Al’umma ne a cike a gurin yayin da Mujaheed ma ya halarci Wannan taron don taya murna ga Sumayya. Bazaka sha Mamaki ba sai na fad’a muku Wanda na hango ba kowa na hango ba face Jaddi da shi da tsohuwar Matar shi Wanda ta raini Fasihat. Yayin da gefen su Fasihat ne a zaune taci Ado kayan su iri daya da Sumayya don Mujaheed ya kawo mata yau da suka sauka can na Kara hango Ustaz Mansur. Ban gama mamaki ba naga su sister Maman Ahmad, da sister Adama,  da sauran yan WAZAN AURA fans suma sun halarci Wannan gagaruman taron.  Don taya Sumayya da Hairan murnar kammala karatun su, sun fito a cikakku Baristoci Wanda suka Amshi lambar yabo da yawa, inda kotuna Masu zaman kansu da yawa na kasashen duniya suke rububin mika musu k’ok’on baran su don suyi aiki da Kasar su, yayin da taro yayi taro mai martaba Abduljabbar shi zai mika kyaututtuka ga D’alibai, tashin farko Hall din ya karad’e da kiran SUmayya Nuradeen Wurno inda kafin Sumayya ta tashi Fasihat ta mike, Mujaheed yayi sauri ya ruko Sumayya da ke shirin tashi Domin lokacin da suka shiga Hall din anyi musanyan kaya yar Saman da su Sumayya ke sawa Jaddi Yasa Fasihat ta cire ta dora a jikin ta ta kuma je inda aka tanadar ma D’alibai Wanda za’a yaye su zauna, ta zauna gurin yayin da ita kuma Sumayya su Jaddi suka boyeta gata dai a Hall din Amma ba mai ganin ta sai Fasihat ake gani a madadin ta. Haka ido gaba daya ya dawo kan wacce a ka Kira yayin da ta tashi tana tafiya d’ai d’ai har ta isa gaban Hall din, Yayin da sai da Sarki ya zaro ido yana kallon yarinyar da aka Kira da Sumayya in har ba gizo take mai ba Yarinyar kaki Nurrudini. Har ta iso gaban shi bai san ta iso ba sai da yaji sanarwa Ana cewa “ku tafa mata itace d’aliba mafi kwazo a shekarar nan Wanda ta ziyarci shari’a mai sarkakiya kuma ta ci nasara. Nan da nan Hall ya d’auka da ihu Masu daukan ta pic nayi Masu zuwa suna gaisawa nayi haka ta dunga samun kyaututtuka daga mutane mabanbata.  inda wani Matashin Saurayi mai ji da tashen kyau Wanda sukaji Ana cewa yaron Sarkin ne. Amma bashi ya haifeshi ba yana matukar ji dashi shiyasa ko fita ma bai son yanayi kowa yaji mamakin ganin shi a Wannan taron, inda ya taso ya bata kyautan Wani agogon Gold ta Amsa shiko kallanta kawai yakeyi. Ya rasa meyake ji a zuciyar shi farin ciki ko akasin haka. Shidai kawai yana ji a jikin shi komai ya kusa zuwa karshen. Haka Sumayya tasha kyaututtuka Kala Kala. Daga nan aka Kira Hairan Mahmoud inda ita ma tasha nata kyautan don Sarki ma kyauta na musamman ya mata a matsayin shi na kakan ta. Duk abun nan dake faruwa su Saif suna gurin suma. But gaba daya hankalin su nakan Family din Sumayya da suka gansu yau da yawa. Taro ya watse cike da dinbin Nasarori inda basu Koma gida ba sai karfe biyar na Yamma. Bayan anyi Sallar isha’i Jaddi yace yana bukatar ganin kaf Ahalin gidan. Bayan kowa ya hallara ne. Jaddi yace ma Mujaheed ya bud’e musu taro da Addu’a, bayan Mujaheed yayi Addu’a Jaddi yace ma Fasihat ta fito kowa na falon ya waigo yana kallon Fasihat, tun ba Ummu da Sumayya ba da Mudi. Sumayya ko mikewa tayi tana kallon Wannan Budurwan mai kama da ita. Umarnin Zama Jaddi ya basu, bayan sun zauna. Jaddi ya fara magana kamar haka:-
“Da farko dai Ummu Sumayya ina son in bayyana miki abun da baki sani ba duk da ba yanzu ya kamata kiji ba. Ya kamata ace gaki ga Nurruddeen Zan bayyana muku abunda ke rufe tsawon shekara Ashirn da Uku Wannan Mata ta ce Sunan ta Khairiyyat Wannan jika nane shine Babban jika na Mahaifin shi ya rasu, Wannan yarinya da kike gani Fasihat yarinyar ki ce ga abokiyar Haihuwar ta nan Ya nuna Sumayya.  da ta zaro ido, taya za’ayi ace su yan biyu ne, Alhalin Ummu bata taba fad’a mata ba. Ita kuma Fasihat mamaki takeyi ya akayi Bil’adama suka haifeta ta rayu a jinsin Aljanu🤔. “Nasan zakuji Mamaki ko to kuyi hakuri Zan warware muku komai bayan kun Koma Nigeria. Saboda a yau karfe sha biyun dare jirgin da nayi muku booking zai tashi zuwa Nigeria. Saboda in har kuka Kara Kwana a garin nan akwai Matsala. “Amma Bamuyi Sallama da kowa ba fa kuma akwai sauran takardu na da Zan karba. “Karki damu yar uwanki zata karbo miki. Bayan haka. Kowa ya tashi ya hada kayan sa. Kai kuma  Mudi ina son magana da kai. Sai da gaban Mudi ya fadi Amma ya dake. Yace “to ranka ya D’ade. Bayan kowa ya watse ne ya kalli Mudi yayi Murmushi “Mahmoud Al-akbar Husainiyu da fatan na Fad’a dai dai.? Zaro ido Yayi yana kallon Jaddi. “Nasan zakayi Mamaki koh? To ba abun mamaki bane ga hukuncin Ubangiji, Domin tun Haihuwar Sumayya har zuwa rana irin ta yau ina bibiye da rayuwar su don Sudin Amana ne a gareni. Duk Wanda ya shigo rayuwan su sai nayi bincike mai karfi a kanshi, kai din yaro ne ga Al-akbar Alhusainiyu Shugaban Kasar Egypt. Kunyi karatu tare da Yaseer a Kasar India. Inda ya kasance abokin ka ne na kud da kud inda daga baya kuka rabu ka karanci harkan bincike inda shi kuma ya karanci na’ura mai kwakwalwa. Inda ka fito a babban Jami’in bincike na kasa da kasa, inda kake wakiltar kasashe biyar. Yayin da Yaseer Nurruddeen ya naimi taimakon ka akan ka binciko mai iyayen shi da ya rasa shekara Ashirin da daya. Kasancewan ka iya yaruka da yawa saboda yanayin binciken ka,daga nan ka ajiye aikin ka bisa Neman izinin zaka wani course a wata kasa. Daga nan ka wuce Nigeria inda da taimakon yarona Dana tura ma har ka isa inda su Sumayya suke daga nan ka Nemi Iyayen bogi ka siya gida kusa da nasu Sumayya ka canza wata fuska da ban da Wanda a ka san ka a haka ka maida kanka sakarai ka dunga shiga rayuwar su, har zuwa rana irin ta yau da kake gabana. Girgiza kai ya fara yi “tabbas Kasan komai game da ni Amma taya Kasan Wannan Abun? Ni na fara kokwanto a kanku Anya ku mutane ne kamar kowa sabo duk kwarewar mutum a bincike bazai taba binciko Wannan sirrin nawa ba, saboda na toshe duk wani hanyoyin da za’a fahimci haka. Sai Gashi kai ka fadamun komai. 😍😍😍😍
Comment
Vote
Like
Yar mutan zazzau ce😂😂💖💖💖💋💋
WAZAN AURA
43_44
WAYYO NI DADI YAR MUTAN ZAZZAU FARIN CIKI LULLUBENI IRIN WANNAN RUWAN COMMENT HAKA INA GODIYA ALLAH YA BAR MUN KU 💃💃💃💃😍😍😍.
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
ZAMFARA NIGERIA
Sun sauka  da Misalin karfe Tara na dare agogon Nigeria. Inda kafin su isa har sun tarar da Motocin da zasu dauke su. Bisa umarnin Jaddi wani gida aka kai su tsayawa fadin kyan gidan ma bata lokaci ne, lokacin da suka shiga gidan kowa da tunanin da yake yi a zuciyar shi. Ita ko Fasihat tana tare da yar uwan ta tana ta mata surutu yayin da ita kuma gaba daya hankalin ta baya tare da ita, ta kasa sakin jiki da ita. Daga Ummu sai Sumayya sai Mudi da Fasihat suka dawo Nigeria a jirgi. Inda suka bar su Jaddi a can, su tafiyar su ta manya ce.
Washe gari sun wayi gari da su Jaddi, inda basu san da zuwan su ba Amma sun wayi gari da su. Bayan sun yi breakfast ne Jaddi yaba Fasihat da Mujaheed da Zankadaziyyatu Umarnin suje suzo da Wa inda ake bukatan su a nan gurin. “Sumayya ina so ki fita yanzu ki bi ta Bayan gidan nan kiyi tafiya kadan. Zaki ga wani Mahaukaci a kasan Bishiya yana kwance kina Zuwa ki ce mai Adnan zo mu tafi. Karki sake kiji tsoron shi ki ruko mishi hannu ku zo. Ummu ce ta dago tana kallon Jaddi tana girgiza kai hawaye na fita daga idon ta. “Dama Adnan na nan a duniyar nan bai mutu ba.”
“Tabbas Adnan yana nan a raye tsawon shekarun nan. Tashi kije Sumayya bamu da sauran lokaci in har kika Kara minti biyar baza mu ganshi ba. Da sauri Sumayya ta fita.  yayin da Su Mujaheed sun dade da tafiya. Kamar yanda jaddi ya fad’a mata haka tayi, don bazata tab’a mancewa da Yayan ta mai son ta ba kuma mai ji da ita. “Adnan! Adnan!!. Da sauri ya mike ya nufo ta yana fad’in “an gansu ne?” Eh tace mai had’i da rike hannun shi gam suka fara tafiya. Yana biye da ita har suka isa gidan shigowan su yayi dai dai da shigowar su Abbie da Mujaheed, sannan Zankadaziyyatu da Marfu’at, sai kuma Fasihat da Ikram. Gaba daya falo ya hadu sai kallon kallo akeyi kuma Jaddi yace bai ba kowa Umarnin magana ba. Sai Adnan ne da suka shigo da Sumayya yaje da gudu ya kankame Ummu yana kuka yana “Wallahi na ganku ina kuka gudu kuka barni.?  Kukan da yake yi Yasa kowa kuka a falon in ka cire Jaddi da Matar shi da Jarumin Jarumai Mujaheed. Shiko Abbie duk da girman da ya kamashi bai hanashi gane Matar shi da yaran shi ba. Jaddi ne yayi gyaran Murya ya fara magana :-
“Kowa yayi hakuri Zan warware muku komai. Don kaddarar ku ce haka, kuma ba Wanda ya isa ya hana ubangiji ikon shi walau mutum Walau Aljani. To Alhamdulillah komai na da lokaci kuma insha Allah yau Zan warware muku komai. Da farko dai Nurruddeen ga Matar ka nan Aslamiyat yau Ubangiji ya Kara hada fuskokin ku, Aslamiyat ga Mijin ki nan Nurruddeen. Sannan ga yaran ku nan Sai dai kun rasa yarinya daya Allah yaji kanta ya gafarta mata. Da “Ameen”.  suka Amsa gaba dayan su. “Sannan ga wata yarinyar taka Wanda baku san da ita ba, Nasan kai Nurru ka sanni ka san ya muke da Mahaifin ka, Matar ka ce Nasan bata sanni ba a lokacin da Aslamiyat ta Haihu Mahaifin ka yana gefenta yayin da Mata ta ita ma tana gefe Gimbiya  Fasihat ta fado duniya itace yarinya ta farko, Bayan fadowanta lokacin mai karban Haihuwar ta fita duk a tunanin ta yarinya daya ce, Mahaifin ka ya dauki Fasihat ya bani tare da mata huduba da Suna Noor Domin ya fadamun yana ji a jikin shi ita din Haske ce ga Ahalin shi kuma akwai wani mummunan Al’amari da zai faru da zuri’an Nurru Amma yarinyar nan da yar uwan ta Su zasu warware komai da taimakon Wasu zaratan Samari guda Uku, sannan yana Neman alfarman cewa in raini Noor ta zama tamkar Jinsin mu. Kuma kar in fallasa Wannan sirrin har sai lokacin da Noor da yar uwan ta suka kawo karfin da zasu karban ma kansu Yanci. To Alhamdulillah yau Gashi Noor ta Zama cikakkiyar likita. Yayin da Yar uwan ta kuma ta Zama cikakkiyar Lauya. Kuma Tabbas Zaratan Samari sun mata caaa a kai kowa ita yake so yanzu Zabi ya rage naki Gimbiya Sumayya. Waza ki Aura a cikin su?.
“Ke kuma Marfu’at yarinyar Baffan ku ne Ahmad Sudes Wanda suka taho daga Egypt tare da Abbie Aminin shi ne tun suna yara yayin da Matayen su suka zama kawayen juna.  Sun so su hada Marfu’at Aure da Adnan sai Allah ya warga zamuku burinku yayin da yan ta’adda suka wargaza komai, shekaru da dama tun farkon fara zuwan yan ta’adda garin Maiduguri  Marfu’at ta bace, Bayan bacewan ta ne, govnor Kano ya ganta ya Ceto ta daga hannun yan ta’adda shine ya Aure ta kuma a lokacin yana da Mata, Bayan Auren ta dashi ba dadewa ta haifi yarinyar ta Mace. Kishiyar ta ita take mata komai kasancewar ta mace mai kissa da munafurci. A haka har ta saki jiki da ita. Bayan Wasu lokuta Hajia Mariya ta gama shirya plan din komai don kashe Marfu’at, sai ta hada Marfu’at Da wani Amintaccen yaron tace suje suyi mata shopping Bayan fitan su, dama shima govnor ya gama plan din shi kan cewa zai bada Marfu’at a kungiya a matsayin kyautan Shekara saboda yanzu ita yafi so a Family dinshi. Bayan fitan su da Driver ne govnor ya mika mai wani jan kyalle ya yarfa mata a fuska shikenan haka da ya basu labarin har ranar da Mujaheed ya dauko ta. Aikuwa da gudu Ikram taje ta rungume Mahaifiyar nata tana kuka. Jaddi ya cigaba da Fadin cewa “Marfu’at Mahaifinku ya rasu gurin ba yar uwan ku kariya, yar uwan ki Shatu tana nan a Zaria Bayan ita ma tasha gwagwarmayan Rayuwa a gurin yan ta’adda ku haka kaddaran ku yake. ✍️✍️✍️✍️
Vote
Comment
Like
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
NA KUDINE
45_46
RAWA DA GIRGIZA ZANYI GABAN KU IN JUJJUYA NA MUKU ALBISHIR NAYI DACE DA MASOYA, SANNAN ZAN ZAME MUKU FARIN CIKI NA NAN DUNIYA ZANYI RUBUTU KU KARANTA KU FAHIMTU A SON KU NAYI MOREWA😘😘💋💖💖😂😂💃💃💃💃.
da fatan na iya wakar😂😂😂🏃🏃🏃wannan page din kyauta ne a gareku masoyan Asali
MAMAN AHMAD
SISTER ADAMA
MY SWEET BAKANO
SISTER NA MANCE SUNAN KI🙈🙈sorry kema ina yinki. ina jin dadin comment din ki.
iya wuya muna tare love you All💋💋💋.
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
“Ke ikram ina takardun dake Hannun ki na gurin Mahaifin ki.? “Gashi nan Jaddi. Mika mai tayi ya karba ya dudduba su, ya tabbatar sun cika sannan ya mika ma Marfu’at Wannan takardun kadarorin Mahaifin ku ne yanzu kece Babba dole ke za’a ba. Yar uwan ki kuma zaku shirya gobe in Allah ya kaimu kuje Zaria don dauko ta saboda dole ku bar Kasar nan a cikin satin nan zaku Koma Mahaifan ku keda ita. Ita kuma yarinyar ki zabi ya rage nata ko zata biku ko zata tsaya don bada nata gudun muwar gurin Daukan fansa. Abbie ne ya dubeta yace “ke Kazan turawa”. Gaba daya falon aka kwashe da dariya. “Wato naji Mamaki wai Marfu’at ne ta haifi yarinyar nan🤔. Wai yanzu shekarar ki ma nawa?. Turo baki tayi hadi da cewa…”nifa ba kazar turawa bane Shekara ta sha takwas in Wannan month din ya shiga fa. “Ikon Allah kuma a haka har kin gama University kin fara aiki, ko da yake aiku yaran Manya ne. Zan zauna anan don Ba da Nawa gudun muwar ga Aunties dina. Tana fadin haka ta tashi ta Dawo kusa da su Sumayya. “To ni ban gane waye ma a cikin ku na mara ba in Kara bata hakuri. Hararan ta Fasihat tayi hadi da Cewa “ai ni Ukhtee ta birgeni da ta gyara miki Zama.. Mare kunyar banza kawai. “Kai Aunty kiyi hakuri mana ai ya wuce ko Aunty Sumayya.?  Tashi tayi ta Koma gurin Ummu ta rungume ta tana kuka…Don Allah Ummu ki yafe mun nice sanadin da kika rasa yarinyar ki. In har baki yafe mun ba zuciya ta baza ta samu sukuni ba, rarrafawa tayi taje gurin Abbie shima tana Neman gafarar shi. Ba Wanda bata ba Tausayi a falon ba. Ummu ma kuka takeyi sosai haka Sumayya tana jin wani zafi a ranta da wutar daukan fansa da ke cin ta. Da gudu ta tashi ta bar gurin yayin da Mahmoud (Mudi)  kenan ya tashi ya bita don bazai iya jure jin kukan ta ba. Ummu ne ta rungumo Ikram tace “na yafe miki har Abada, haka ma Su Sumayya da duk Ahalina na sun yafe miki saboda Ana son mutum mai yafiya. Allah ya yafe mana. Gaba daya falon aka Amsa da “Ameen”.
     “Jaddi ina da magana ni yanzu ya matsayin Rayuwata.?  Zan cigaba da Zama cikin jinsin ku ne ko jinsin Ahalina.?  “Karki damu Gimbiya Noor zaki Koma Ahalin ki daga lokacin da komai ya dai-dai ta. Bayan kun ga Bayan dukkan Makiyan ku. Domin yanzu Makiya ne gaba da Bayan ku. Abu din ku tunda ya ganki gurin taron nan hankalin shi ya kasa kwanciya Yasa a binciko mishi ke ko a Mace ko a raye. don yana zargin cewa ke jinin Nurruddeen ne. Baicin haka yan ta’adda na nan suna cigiyar Nurruddeen saboda sun sanar da Abu cewa ba’a ganka ba.  Sannan Wannan takardun da kuka kwaso a gurin su, duk wani sirri da duk wani Kadarori Mahaifin ku yana cikin takardun. Akwai sauran Wasu sirrika da ba Wanda ya sani sai kai shiyasa Suke ajiye da kai na tsawon shekarun da kayi a gurin su. Suna bukatar ka farfado ka fad’a musu. Sai a fad’a ma dan uwan ka Abu daga nan sai su kashe ka.  Don su tunanin su Ahalinka sun dade da Mutuwa. Lokacin da yaga Sumayya a Egypt ya girgiza. Shiyasa yanzu daga Egypt har Nigeria Neman ku akeyi wanted. Don bayyanar Wannan sirri dai dai yake da tonan Asirin Wasu daga cikin manyar shuwagaban nin ku. Sannan nan da wata goma akwai wani gidan Matsafa Wanda had’a manyan shugabannin kasashe. Wanda nake so mu had’a karfi da karfe mu kawo karshen Azzalumai. Domin kawo muku Zaman lafiya a cikin Al’umman Bil’adama. Wanda dole sai da Taimakon Mutane Hud’u. Kuma Dole ku zaku jawo su cikin Tafiyar, bana bukatar ku bari su san ku yan biyu ne so nake kuje musu a Matsayin mutum daya. Ba kowa bane wad’an nan Mutane Face :-
Saif
Irfan
Aslam
Mahmoud.
Wanda gamu tare dashi sai Ikram Wanda dole da ita za’ayi Wannan tafiyar. Dama kuma Mujaheed shine Shugaban Tafiyar. Dukan su dagowa sukayi suna kallon Mujaheed. Wanda Shima su yake kallo. Tabbasa baiji Dadin cewan Fasihat ba jinsin su daya ba. Don shi yana matukar son Fasihat Sai dai yanzu yasan tayi Mai Nisa. Ita ma a gurin ta haka ne don taso Mujaheed sosai, Amma ba yanda zatayi sai dai gaba daya Soyayyan da take mai taji lokaci guda ya Koma kan Saif. Yayin da Sumayya take nata Tunanin itama. Gaskiya ita ma taso Mujaheed. Ashe ba Mutum bane. Sai ta tuna da Saif lokacin da ta ganshi a Asibiti ya hadu Sosai, tunawa tayi da Aslam sai taji ranta ya baci, Zuciyar ta ne ta ingizo mata Tunanin Mahmoud (Mudi)  Tabbas rabin jiki fa shima So na yakeyi. To WAZAN AURA a cikin su.
To readers ku bama Sumayya Amsa wa zata Aura ne cikin wad’an nan Jaruman😂😂😍😍😍. Sai na jiku✍️✍️✍️.
Vote
Like
Comment
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍.
WAZAN AURA PART TWO
47_48
ALHMDULILLAHI GODIYA  GAREKU MASOYANA.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
*************************
6 Month later
Abubuwa da yawa sun faru. Ciki har da komawar Marfu’at da yar Uwan ta Shatu Egypt.  Inda Jaddi da kanshi ya maida su ga dangin su.  inda Sumayya taje har gidan su Hairan a Abuja, kuma sun had’u da Saif inda har ya furta Soyayyar shi a gareta, haka kuma ta samu Nasaran shawo kanshi gurin taya ta bincike inda Soyayya Mai karfi ta kullu tsakanin Hairan da Irfan. Barayi guda kuma Soyayya sosai ya kullu tsakanin Fasihat da Aslam. In da yanzu ya kasance su suke Mulkin kano. Tabbas talakawa yanzu suna jin dadin Mulkin Sosai. Sai Abunda Fasihat tace ake aikatawa a jihar inda Aslam ya zama ma iyayen shi kadangaren bakin tulu, gashi ya kwashe duk wani documents na Mahaifin nashi. Inda gaba daya hankalin Mammah ya tashi ga bala’in sha’awar Fasihat da takeyi yanzu ji takeyi kaman ta danne ta.Don yanzu Fasihat ta maida gidan su Aslam kamar gidan su. Ga Tashin hankalin rashin ganin Ikram da batayi ba ta rasa ina ta shiga a cikin gidan don dai tasan irin tsaron da tasa mata bazata taba fita daga gidan ba. Ga shi tana bukatan taje gurin Bokan ta. Boka Dan tsito. Saboda yanzu gaba daya madubin tsafin ta ya daina aiki. Ta rasa dalili ga shi Govnor yana neman juya mata baya ta rasa gane kanshi. Shima Kwana biyu yana cikin rud’ani saboda yanzu gaba daya Aslam ya girgiza Asusun gwamnati har ya fara shiga cikin kadarorin shi. Gashi yanzu ba halin zuwa gurin Mai girma Kakkau, saboda an kusa taron sabuwar shekara…. Kuma dole sai lokacin kowa zai gabatar da bukatun shi.
*************************
ABUJA
“Haba Mai girma shugaban kasa taya Kake tunanin zan aikata haka.? Wallahi D’ana ne dashi da wata Hatsabibiyar yarinya suke mana wannan ta’asan gashi gaba daya na kasa daukan Mataki saboda yarinya wani kwarjini take mun ga tsoron ta da nakeji a duk lokacin da na ganta. Sai in ga tana mun siga da aljanu”.
“Wannan ai zancen Banza ne Kake son fadamun yaza’ayi ace yarinya k’arama ta dunga tsorata ku tana juyaku daga kai har d’an ka!!! Nadai fad’a maka dole ka d’au Mataki kafin komai ya lalace mana. Ya tashi ya bashi guri.
Kayataccen falo ne da yaji kayan Alatu suna zaune ne a kujeru na alfarma.kowan ne cup ne a gabanshi da drink a Ciki. Wani mutum ne a cikin su yayi gyaran murya had’i da fara magana”Mai girma Mister President ina so ka sani Dole sai mun kawar da Alhaji Mahmoud daga kujeran nan saboda ko da yaushe shi yake kawo mana cikas a cikin harkan mu wai shi Mai gaskiya. Sannan nifa kwata kwata ban yarda da alakar yaran ku ba. Wato Irfan da Saif. Anya baza su zamo mana matsala ba kuwa?. Domin ni yanzu sun fara bani tsoro. Sannan in ka lura Kwana biyu sunata kai kawo tsakanin Egypt da Nigeria. Wayace tayi k’ara duk sukayi shiru. President aka kira, picking yayi had’i da sawa a Hands free inda kowa zai ji. “Hello President kanaji na kuwa ina son inji ina muka Kwana game da maganar d’an uwa na da iyalan shi har yanzu kun kasa d’aukan matakin komai a kai ko so kuke sai Asirin mu ya tonu  ne. Yanzu haka fa Hukumar bincike ta kasan Egypt ta fara bincike game da B’atan d’an uwana da iyalan shi.!! “Garin ya hakan ya faru bayan Mai girma Kakkau ya ce an gama da wannan Matsala. Mun shiga uku gaskiya akwai Matsala. “Sosai ma kuwa gashi yanzu ba karb’an Uzuri ko damuwa sai ranar bikin shekara gashi saura wata hud’u. To yanzu fa?.   Nifa yanzu gaba daya kaina ya kulle, ku tafi kawai sai na nemeku.
ZAMFARA
“Wash Ummu na dawo.  wlh duk na gaji. “Sannu da dawowa yar albarka, Ina yaron kirkin?  Aiko ya wuce Abuja yanzun nan saboda Yaya Irfan ya kirashi cewan akwai wani documents da yake son bashi don yau zai tafi Egypt. Rabin jiki yana son ganin shi. Amma gobe zasu dawo harda Hairan da Ammyn su. “Da gske tare zasu zo da Ummulkhairi Ashe zanga y’ar D’an Uwa na😭sai ga hawaye a idon Ummu kai Ummu ki daina kukan  nan mana bayan komai yazo karshe lokaci kad’an ya rage ki koma cikin yan Uwan ki.Abbie ne ya shigo falon shi da Yaya Adnan Wanda alamu sun  nuna  cewa ya warke sarai. Sun dawo  daga Masallaci. “Autan mu yaushe kika dawo ne.?  Inji Yaya Adnan. “Wallahi yanzu na shigo Yaya. “To Sannu da dawowa da fatan komai na tafiya Dai dai ko?   Ana samun cigaba game da bincike? “Sosai ma Yaya don yanzu mun gama tattara duk wani Sirri da zamu gabatar Abun da ya rage kawai game da gidan tsafin nan nasu Wanda har yanzu Yaya Mujaheed yana kan bincike a kanshi. Saboda duk da zuwan da yayi wancan karan. Yanzu gaba daya ya rasa hanyar zuwa gidan kuma ya kasa gano cewan gidan na wani k’asa ne. Kasan tsafi gaskiyan me shi ne Yaya. “Tabbasa kuwa kanwa ta insha Allah kuma sai Asirin su ya tonu. “Abbie na ko sannu da gajiya baka mun ba. To nayi fushi. “Haba Autar mu ayi mun Afuwa naga ai kina hira da Yayan ki ne kar in sa muku baki. Dariya duka sukayi dai_dai lokacin da Fasihat ta shigo Falon Had’i da Sallama. Da gudu Sumayya ta tashi taje ta taro ta..✍️✍️✍️✍️
Yar mutan zazzau ce😍😍😍😍
WAZAN AURA PART TWO
49_50
SECOND TO THE LAST PAGE.
BISSMILLAHI RAHMANIR RAHEEEM.
*************************
Yanzu watan su Sumayya Tara kenan da dawowan su daga Egypt karatu. Inda Sumayya take aiki da Babban kotun kasa dake Abuja. Yayin da Soyayya mai karfi ya shiga tsakanin ta da Saif. Inda komai zasu yi sunayi ne a tare. Yayin da bangaren Fasihat ita ma komai na tafiya dai dai domin Aslam ya zama tamkar bawan ta don duk wani Abu da take bukata a jahar tasu shi akeyi Yayin da Mai girma gwamna ya zama hoto. Gefe guda kuma Soyayya mai karfi tsakanin Zankadaziyatu da Yarima Mujaheed,  tun da suka fahimci komai sai kowa ya zubar da makaman yakin shi ya rungumi Abokin rayuwarshi.
Sumayya ce zaune ita da yar uwanta suna duba wasu takardu. Ikram ne ta shigo falon d’auke da Sallama a bakin ta. Amsawa sukayi, Yayin da Sumayya ta d’auke kan ta daga kallon ta. Saboda ko da yaushe in har taga Ikram sai taji zuciyar ta na mata k’una tanaji a ran ta baza ta tab’a iya yafe musu ba ita da Yayan ta. K’arisowa tayi a sanyaye ta zauna had’i da fad’in “Sannun ku da aiki Aunties. Fasihat ne kawai ta Amsa mata Yayin da Sumayya ta fara tattara takardun nata, “Masoyiya ki sameni a d’aki. “Kamar ya kuma muna cikin aiki kin tattara takardu kince in sameki a D’aki. “Eh kawai na gaji da zaman Falon ne. “Ok sai na shigo Masoyiya. “To sai kin shigo. Ta fad’i haka had’i da hayewa sama. “Aunty don Allah yaushe Aunty Sumayya zata dai na fushi dani ne? Ubangiji ma muna mishi laifi ya yafe mana balle d’an Adam. Kullum binta nakeyi ta yafe mun taki saurara ta, ta karishe fad’in haka hawaye na gangaro mata. Kamo ta Fasihat tayi ta rungumeta tana lallashin ta. “Kiyi hakuri Baby insha Allah komai zai wuce. Sallaman da akayi ne yasa su yin shiru suna kallon Mai shigowa. “A’a Rabin rai kai ne da daren nan.?  “Aunty mu nine wlh wani aiki ne na shigo yi kuma cikin daren nan ya Kama ta inyi binciken. “Kai ya akayi ka gane ni.?  Ta fad’i haka tana mai murmushi. “Habawa Aunty mu ai Sai kice ban cika jami’in bincike ba indai ban bambance tsakanin ke da Rabin rai na ba… Tashi muje ina tunanin zaki ban wani taimako kin san ke Jaddi ya bud’e miki ido kin fi mu ganin abu… Bari in gaida Ummu da Abbie suna falon Sama ko.?  “Eh suna sama har da Yaya Adnan. “Ok bari in sauko, Amma kije ki shirya kafin in fito. “To baka da Matsala sai ka fi to Sir. Dariya sukayi gaba d’aya. Ikram ne tace”uncle ina yini. “Oh Ikram kece a nan ai ban ma ganki ba, Mom naki tace in gaida ku. Muna Amsawa. Ya haye Sama.
*************************
“Tsaya_tsaya naga kamar wata cika ne fa take tafiya da alamu ma kamar a bige take. “Kai Haba bobi ni fa kasan a matse nake. Dai dai gaban ta suka tsaya ga kid’a da yake tashi, “Wowww kai Beb d’in fa ta had’u komai yaji. “Kace zamu kwashi gara. “Ni matsala na ma Aslam baya nan. “Ai bar banza don naga gaba d’aya yarinyar na ta juyar mai da kai, sai abunda take so yakeyi. “Hi Beb”.  “Hi me kuke bukata lift ne? “Eh muje kawai d’aya daga cikin su yana shirin rungumo ta, sai ta zamiye ta shige cikin Mota front seat. Suka shige suka figi motar suna cikin tafiya ta kafa mai bindiga a wuyan shi tace mai “stop ko yanzu in fasa kanka da bindigan nan. Wani wawan birki suka taka. “Ke Baby ya haka ne.?  “Oya open the door bud’e kofar suka farayi kowa hannu a sama. Suna fitowa Mudi na isowa dashi da yaran shi. “Oya ku Kama su haka aka tattara su a kayi gaba dasu. “Good Aunty mu aikin ki na kyau, kin san su waye wannan.?  “A’a sai ka fad’a. “Sune suka yi wa Sahiba Maryama fyad’e. Hawaye ne ya zubo mata. “Meyasa baka fad’a mun ba in ci Uban su kafin a tafi dasu. “Sorry Aunty mu, ai iyayen su sun b’oye su ne  sai da suka ga komai ya lafa suka dawo kasar. Yau ma iyayen su basu san sun fito bane, ina can aka kirani wai yau zasuyi faty  kuma dole zasu halarci faty…. Muje gida saboda gobe insha Allah Abuja zanje. “Ok tom. Shigewa Mota sukayi suka Nufi gida a Mota yake Fad’i mata cewa tun jiya Ashe su Kb da Bobi suka shigo Zamfara karfe biyun Dare kuma yau da sha biyun dare zasu bar garin su koma Abuja.
*************************
One month later
Kowa ya hallara a gurin ga Mujaheed, ga Irfan, ga Saif, ga Mahmoud, ga Ikram, ga Zankadaziyatu, dukan su cikin shiri ga Jaddi a zaune ga Abbie ga Ummu, can gefe guda kuwa Yammata Ummu ne d’aya cikin shigar kayan likitoci, d’aya kuma cikin kayan lauyoyi….. ✍️✍️✍️✍️✍️
Yar mutan Zazzau ce ku cigaba da bina. 😍😍😍😍.
WAZAN AURA PART TWO
LAST PAGE
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
51_52
ina godiya a gare ku masoyana. naji dad’i da karamcin da kuka Nuna mun da k’aunar ku a gareni. Bazan taba mancewa  da ku ba Masoyan Asali, Comment din ku shi ke karama mun kwarin gwiwa. Ina yinku baki bazai iya lissafa k’aunar ku a gareni ba love you lodi lodi.
Godiya ga d’aukacin yan group din Arewa Writers Association. Allah ya kara had’a kan mu gaba d’aya. 🙏🙏
Bayan kowa yayi shiru kawai Jaddi suke sauraro. Ya fara musu Bayani kamar haka “gurin da zakuje guri ne Mai matukar Had’ari saboda kun san ance tsafi gaskiyar mai shi… Addu’a da taimakon Ubangiji shi zai kai mu ga yin Nasara  a cikin wannan tafiyar tamu, ku tabbatar kun rike addu’a a bakin ku Yayin da muka Nufi gidan, saboda kafin na gano inda gidan yake nasha matukar wahala. Gidan yana kan iyakan Nigeria da Ghana ne, kuma akwai muggan k’ungiya_k’ungiya na yan ta’adda hatsabibai Wanda suke aiki da tsafi Wanda duk karfin ka Addu’a ne da taimakon Ubangiji zai kubutar da kai Daga garesu. “Wannan takobin da yake d’auke da sunan Allah dashi zamu iya kawo karshen shaid’anin dodon kungiyar nasu, bayan munyi nasarar gamawa da wad’an nan y’an ta’addan sannan sai muje ga yan tsaron gidan…. Gidan na da kofofi guda goma Sha takwas,  ko wanne da irin Hallitan da zaku gani a kowani siffan Hallita kuka gani kar kuji tsoro ku tunkareshi kawai da sunan Allah da Addu’a zaku ga sun b’ace, haka zamuyi ta ratsa kofofi har sai mun kai kofa na sha takwas nan ne Masifan yake, domin sun ajiye jarumai majiya karfi Wanda suke aiki da tsafi sun kai su Ashirin Wanda duka ko wuka ko bindiga ko mashi bazaiyi musu illah ba sai manyan Addu’oi, saboda haka kowa ya rike addu’a da kuma dakiya da jajircewa don wannan Abun tamkar jihadi ne. Da fatan kun fahimce bayani na.? “Mun fahimta insha Allah zamu kiyaye, sannan akwai yaran mu ma’aikata da zamu tafi tare dasu. “To shikenn ba Matsala duk rintsi duk wuya daga yau zuwa gobe nake bukatar mu isa saboda gobe ne Babban taron su. “To yanzu a jirgi zamuje ko Mota Jaddi.? “Jirgi ko Mota bazai tab’a kai mu gurin ba, sai dai da iko da k’uduran Ubangiji da ya ni’im ta mu dashi. Kabbara Jaddi yayi. Gaba d’aya suka Amsa. Addu’a Abbie da Ummu suka fara kwararo musu da fatan samun Nasara kasancewar bada su za’a ba. Adnan ne ya fito d’auke da karamar Camera d’inshi da ID card nashi na matsayin cikakken D’an jaridan kasar Egypt, kasancewar Dama kafin su baro kasar su. Addu’a Jaddi ya fara a take a nan suka b’ace gaba d’ayan su. Kuka Ummu ta fashe dashi ta rungume Abbie “Hasken rayuwata sai ina jin kamar bazasu dawo ba. “Haba Habibaty Addu’a ya kamata ki musu ni ina da tabbacin zasu je lafiya su dawo lafiya da yardan Ubangiji. “Allah ya dawo dasu lafiya ya basu Nasara 🙏. “Ameen ya Allah “.
*************************
Wasu samudawan mutane ne majiya karfin Wanda da ka kallesu kasan basu da d’igon Imani Nama suke gasawa sun zagaye wutan kowa da wuk’an shi a hannu suna yanka suna ci ban kara tsinkewa da al’amarin su ba sai da na matsa kusa dasu Naman mutum naga suna gasawa gefe guda kuma jini ne a katon roba suna ci suna korawa dashi. Nan da nan jiki na ya d’auki rawa saboda firgita. Na juya da sauri, “oga naji kaman kanshin mutum nake ji a gurin nan. “Wayyo Allah my bakano, Maman Ahmad, sister Adama kuzo ku ceceni, Ciki na naji ya juya Anya zan iya chigaba da bin su Jaddi d’auko muku rahoton nan kuwa? Kai ina ga zan hakura ne in Yaya Adnan ya dauko mana a Cameran shi ma kalla tare da ku. Isowar su Jaddi yasa naji wani karfin gwiwa cigaba da d’auko muku yanda zata kaya da wad’an nan Sanudawan. Jaddi ne yake gaba sai Mujaheed sai su Sumayya da Fasihat da Ikram sai Zankadaziyatu, sai su Saif da yaran su da zasu kai su Hamsin. Kowa ka gani Addu’a ne D’auke a bakin su. Fiyuuuu sukaji wucewan wani Abu a kusa dasu, Jaddi ya bada umarnin a tsaya Tabbas yanzu sun san da shigowar mu Dajin nan, saboda haka kowa ya Kama wannan Addu’a :-WALLAHU GALIBUN ALAH AMRIHI.
WALLAHU YA’A SIMUKA MINANNASI.
AUZU BIKALMATILLAHI TAMMAT MIN SHARRIN MA KHALAQ.
Nan da nan kowa ya Kama Addu’a. Suka cigaba da tafiya.
“Oga mun samu baki fa a Dajin nan kuma ciki harda wani shehin Aljani tare da yaran shi uku. Wanda suke musu jagora. “Duna bincika mun ina zasu Meya biyo dasu tanan hanyar?  “Oga bincike ya nuna cewa zasu Kakkau falace ne, “yihuhuhuhu!! Ina wani shege ina wani dan banza shugaban matsafan duniya Kakkau waya isa ya ja da kai kowaye shi sai ya bakun ci lahira. Ku Kamo mun su a raye nake bukatar su.
Gani kawai su Jaddi sukayi an zagaye su. Murmushi Jaddi yayi, Yayin da wasu daga cikin yaran su Saif da Mahmoud jikin su ya fara rawa Addu’a ya fara guduwa suna jawoshi. Wani raga suka watsa musu, suka nannad’e su a ciki a ka kaisu gaban ogan nasu. Kallon su Yayi d’aya bayan d’aya “wato zaku ja da Kakkau zaku kawo karshen k’ungiya. K’ungiyar da ta kai shekara Hamsin to karyan ku ta sha karya. Wani Addu’a Jaddi ya fara yi nan da Nan net din ya fara watsewa. “Kai a tarihi kune Wanda na sama net din nan suka fita ba tare da kunsha Azaba na ba. Nan fa aka fara fafatawa tsakanin wad’an nan Samudawan. A wannan fafatawa sun rasa mutane da yawa kafin su kawo karshen wad’an nan mutanen ikram ma ta taka rawar gani ita da Fasihat Yayin da Jaddi da Yaya Adnan suna gefe Yaya Adnan yana D’aukan duk abun da ke faruwa. Sumayya aka zo yan ka inda Ikram tayi Sauri ta tare aka yanke ta a gefen ciki sai dai bai shiga sosai ba. Amman wukar mai guba ne nan da nan Fasihat ta rirrik’eta ita da wani Jabeer fito da kayan aikin ta tayi ta fara mata treatment. Cikin mintoci ta kammala. Dai dai da gamawa da yan ta’addan. Amma fa sunji jiki. Wanda suka mutu sukayi musu sallah suka birnesu. A nan suka kara samun wasu sirrorin  a gurin su, sun isa gidan karfe goman Dare, inda suka zauna zuwa da Safe.
Washe gari bayan sunyi Sallah sunyi Azkar sun nemi taimakon Ubangiji haka suka durfafi gidan. A taikaice dai sai da ya rage daga Jaddi sai su Saif da Mahmoud da Irfan dasu Sumayya sai Jabeer sai wasu yara biyu Amma kowa yaji jiki sosai masu rauni Sun kai kofar karshe anyi bata kashi inda sai da suka ci bak’ar wuya kafin suka Samu shiga gidan Inda Ikram aka kara yan kanta a gurin da aka yanke ta a farko haka Sumayya taji ciwo sosai, kowa dai a ciki ya sha da kyar ban da Jaddi da Adnan inda duk wani kariya Jaddi ya ba Adnan don kawai ya d’auki duk abun da ke faruwa don ya zama musu hujja a kotu. Rarrabuwa sukayi.
“Kakkau! Kakkau! Kakkau! “Uhmmmm hall d’in ya cika makil fararen fata ne bakake ne mata da Matsa, nan da nan Adnan yaje ya dunga manna Camera a kusurwan ko wani guri, Dama kuma sun riga sun saita komai da gidajen TV  kasashe hud’u ciki kuwa da Nigeria, Egypt, Ghana, Cameroon, Nijar, Marfu’at itama Dama ma’aikaciyar jarida ne don tare sukayi karatu da Adnan, ita take kula da Na kasar su. Jidda na gani a Babban talbijin na k’asa Nigeria tana gabatar da shirin gaba d’aya hankalin yan k’asashen ya tashi.
Nan da nan su Saif sukayi waya sukace a kawo musu k’arin jami’an tsaro. Nan da nan Jami’an tsaro suka zagaye gidan had’i da speaker kowa ya tsaya a inda yake, karya motsa nan fa hankali ya tashi aka fara guje guje da harbe harbe. Nan aka dunga bata kashi in da a ka Kama na kamawa aka kashe na kashewa. Abun Mamaki Irfan wani Mutumi ya Cafko da yake shirin guduwa ya buga mishi kan bindiga, dago shin da zai yi kawai sai ganin Dad din shi yayi. Fashewa yayi da kuka yayin da Saif yayi Sauri ya rike Abokin nashi yana bashi hakuri da kyar suka janye Irfan aka tasa keyan Daddy yana ta borin kunya. Gaba d’aya haka aka dunga ficewa dasu yayin da Ikram tana rirrike a hannun su Fasihat aka zo wucewa da Pappah din su, da kyar ta iya Bud’e baki tace “Pappah Allah ya isa tsakanin mu da kai. Kuka ya rushe dashi. Bayan kowa ya fita an rik’o Oga Zanjabilu wani katon inyamiri ne. Wanda da ka ganshi bai da Imani. Gurin Dodon tsafin Mujaheed ya nufa Addu’a d’auke a bakin shi d’aga takobin hannun shi yayi ya shiga Artabu da Dodon tsafin, kasancewar ance tsafi gaskiyar mai shi, da k’yar Mujaheed ya samu sa’a Saran shi dashi, take ya Kama da wuta, gidan ya fara girgiza nan da nan Mujaheed ya bace. Lokaci guda gidan ya fara girgiza yana kamawa da Wuta.
*************************
Bayan Sati uku Sumayya ne take Zaune a falon Ikram kwance a kan cinyar ta duk ta rame. Sallama akayi duka suka daga kai suna kallon mai shigowa, Su Saif ne da Mahmoud da Irfan suka shigo Irfan da ka kalleshi kasan yana cikin Damuwa saboda ya rame sosai. Zama sukayi dukan su Sumayya ne ta kallesu cikin girmamawa ta gaidasu, Ikram ma gaidasu tayi, suka mata ya jiki. Ta Amsa musu da Sauki. Irfan ne ya dubeta yace “Mutum ce ko aljan?  Gaba d’aya dariya sukayi, da yake tunda sukayi tafiyan nan ne suka fahimci Ashe su yan biyu ne kuma sukaji labarin su, sai Irfan yake tsokanar su duk in yaga D’aya daga cikin su, sai ya ce “mutum ce ko Aljan din. “Ku Zauna bari in kawo muku ruwa. Tashi tayi taje d’auko musu Ruwa da drinks. Kawai ji sukayi ance Musu “Sannun ku fa. “Wayyo Allah nayi gamo, ka gani ko shiyasa na tanbaya Mutum din ce ko aljana, ashe Mutum din ce ga Aljanar nan ta iso dariya duka sukayi. Tab’e fuska Saif yayi don shi jininshi bai wani had’u da Fasihat ba. “Mallam ka cika mu da surutu fa, muyi Abun da ya kawo mu, Uhmmm Sir Mahmoud Bissmillahi. “Bata rai Mahmoud yayi saboda wani kishi da yake taso mishi saboda irin kallon da Saif yake Ma Sumayya. “Ok Abun da ya Tara mu a nan shine Next week zamu shiga kotu kuma duk mun Tara wani shaidu da zamu gabatar a kotu yayin da Barrister Sumayya da Hairan Su zasu wakilci Nigeria, Yayin da Kanwata Barrister Kubrah zata wakilci kasata Egypt domin akwai wasu manyan gwamnati na Egypt ciki kuwa har da Abu. Saboda haka yanzu duk mun gama kammala shaidun da zamu gabatar.
A gurguje anje kotu anyi shari’a inda Su Sumayya suka taka rawar gani a cikin shari’a suka tsaya tsayin daka gurin ganin anyi adalci, inda kotu ta yanke ma Shugaba Zanjabilu kisa ta hanyar rataya, Sukuma sauran Members din aka yanke musu D’aurin rai da rai ciki har da Shugaban k’asa da Govnor inda Mammah tanaji ta yanke jiki ta Fad’i, shiko Aslam ko a jikin shi, don yace shi ya jama kanshi, tun da yana tare da Masoyiyar shi. Bayan gama shari’a da sati d’aya jama’a sukayi shawaran bama Saif shugaban ci k’asa don sun yaba da Adalcin shi da jajircewan shi, ba kowa ya kawo wannan shawaran ba sai Vice president Mahaifin Saif. Aiko kowa yayi Na’am da shawaran inda, shima Abbie Sauratan gidan su ya koma hannun shi duk da har yanzu yana Nigeria.
Falon ya cika inda Jaddi ke zaune kowa na falon yayi shiru shi suke saurare, “Alhmdulillahi dukkan godiya ya tabbata ga Mad’aukakin sarki da ya kawo mun wannan lokaci a yau zan Sauke sauran Nauyin da ke kaina, Wani ruwan Addu’a ya ba Fasihat yace ta shanye bayan ta karba tayi bissmillah tasha nan da nan ta fara rawar sanyi tana jijjiga tamkar zata mutu, har tazo ta fara ragewa a hankali har ta dawo dai dai. “Bace mu gani Fasihat. Yunkurawa tayi tayi tace “Jaddi na kasa. “To Alhmdulillahi a yau kin dawo gimbiya Noor. Gaba d’aya falon akayi kabbara. Bayan komai ya Lafa sai Jaddi Yaci gaba da magana. “Zan yanke hukunci nasan zai ma wasu dad’i wasu bazai Musu ba…. Ke Noor zaki Auri Saif ke kuma Sumayya zaki Auri Mahmoud. Nan da nan dukan su suka d’ago kansu suna kallon Jaddi yayin da shi kuma Yaci gaba da maganar shi”Adnan zaka Auri Yar uwan ka Marfu’at shi kuma Yaseer zai Auri Kubrah. Na gama zance duk Wanda hukuncin bai mai Dad’i ba ya yafe mun. Yau shine karshen had’uwar saboda tsufa ya kamani yanzu ina son zan zauna in huta. Haka dai kowa ya watse.
Three Months Later
Wata Mata na gani a gadon Asibiti an yane ta da wani mayafi tsutsotsi na fita a jikin ta d’akin da take sai wari yakeyi da na Kara kallon ta da kyau sai naga Ashe Mammah ce ta zama haka. Nace Allah yasa mu dace ya mana karshe mai kyau. Gurin ganin likita na je naga wani saurayi duk ya kod’e ya jeme. Da na kalla da kyau sai naga Aslam bayan ya shiga ganin likita na bishi, likita ya fara tanbayan shi”ya jikin naka me kakeji yanzu.?  “To likita gskya ina jin zuciya ta ta kusa bugawa, ga Mammah rai a hannun Allah jiya da naje gidan yari Duba Pappah yana nan yana fama da ciwon b’arin jiki gashi Masoyiya ta gujeni. Nan da nan ya fara Aman jini nan da nan likita ya fara danna kararrawan kiran Nurse a kawo Emergency Bed aka dorashi a kai. Nace Allah ya kyauta.
EGYPT
Taro yayi taro an cika gidan Sarautan yau ake  Nad’in Sarautan Abbie had’i da d’aura Auren Su Sumayya inda ya samu halarta d’inbin jama’a daga k’asashe Amare sunyi kyau kamar ka sace su ka gudu inda Hairan ma tazo bikin.. Sai ta koma za’ayi nata bikin Da Irfan a ranar rantsar dasu shida Saif a matsayin president da Vice. Anyi biki lafiya an gama inda aka kai Amare gidajen su, inda aka kai Noor Nigeria, ita kuma Sumayya aka kai ta gidan shugaban k’asan Egypt shi kuma yaya Adnan a ka ware mai part guda shi da Yaseer  inda Ikram kuma zata ci gaba da zama gurin su Abbie.
Six months later.
NIGERIA
Wani had’add’en Falo ne can na hango wata Hamshakiyan Mace taci Ado iya ado tana cin fruit tana Danna waya tana ta zuba Murmushi daga gani tana jin dad’in Yanayin da take ciki, “Hurul ainyyy!! I am back” da sauri ta ajiye wayan taje ta rungumeshi ta bashi peck a goshin shi. “Well come back my Excellency.I hope ka dawo lafiya ya jama’a? “Lpy lau first lady. Shafa cikin ta yayi yana Murmushi “ya ajiyata gimbiya Noory.?  Sunne kan ta tayi a kirjin shi. “Muje kayi wanka kazo kaci abinci. “To shikenn Noory, haka suka shige D’aki rungume da junan su.
Sallama ake tayi a Fallon yayin da Masu Falon suke ciki, sai daga baya wata mai aiki ta fito daga kitchen “a’a ranki yadade kece a gidan namu Barka da zuwa. Shigo bari in kira ta. “Ok tom. Guri ta samu ta Zauna. Da na Kara kallo da kyau sai naga ashe Hairan ce ita ma ta Kara girma tacika sosai can sai ga Mijin nata ya shigo “A’a Hayaty ina masu gidan? “Suna ciki sun shanyamu. “Bari in kira ogan. Daga wayan shi yayi dai dai da saukowan su rungume da juna cikin wasu kananan kaya sunyi Anko  ga cikin ta ya fito chas. “Bakin dare Mukayi zuwa ba Notice haba ranka ya dad’e kawai kun wani zo ku takura mana. Ya karisa maganar cikin zolaya. “Hayaty kinji ko kin Matsa muzo gashinan munzo suna mana gori tashi muje. “Ayyah Sorry my Jameelatu Ukteee wasa fa Habiby yake miki haka suka zauna suka sha hira. Sai dare sukayi Sallama suka koma.
Egypt
“Wayyo Rabin rai ni fa D’an wake zanci. “Ya salaam yanzu in banda rigima irin naki rayuwata ina za’a samu d’an wake ga dare ga shi ruwa akeyi. Kuka ta saka mishi tana kai mai duka da filo.
One year later
Falon ya cika da jama’a kowa ka gani yana cikin Farin ciki wasu kyawawan jarirai nagani a hannun su Ummu da Ummi kakan su Hairan can sai ga Su Abbie sun shigo gaba d’aya kowa ya hallara, Su Sumayya ko wa da Baby shi a hannun yayin da Mahaifiyar Ikram Matar yaya Adnan take da tsohon ciki. Family gaba d’aya suna cikin Farin ciki Happy Family.
TAMMAT BIHAMDI LILLAHI A YAU NA KAWO KARSHEN LITTAFI NA MAI SUNA WAZAN AURA DA FATAN YA FADAKAR KUMA YA NISHADAN TAR.

 

About Godswill

Check Also

SARAN BOYE Page 61 to 70

SARAN BOYE Page 61 to 70 Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan …

Advertisements